Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga wani birni.

yayin da suka isa wanna birni da ke bakin kogi, masunci ya yi nufin ya wuce da jirgi bisa ga wannan birni. Sarkin wannan birnin kuwa ya kasance mai tsananin iko ne ana ce da shi Darbas zaki. A wanan lokaci kuwa ya kasance yana zaune tare da d’ansa a fadarsa suna kallon kogin ta taga, sai suka hango wannan jirgin ya taho babu komai a ciki sai matukinsa da yarinya sai ka ce wata a lokacin da dare ya cika cikin tsakiyar dare. Suka dubi jikinta suka ga tufafin alfarma ne, sannan wuyanta na rataye da sark’a mai daraja da tsada. Da haka sarki ya fahimci duk yadda aka yi wannan yarinya tana daga ‘ya’yan manyan sarakuna. Sarki ya sauka waje zuwa kogin, ya tarar jirgin a gacin kogin yarinyar tana barci a gefe d’aya, masunci kuma yana k’ok’arin d’aure jirgin da igiya. Ya tafi zuwa gare ta ya farkar da ita daga barcinta, ta tashi tana kuka, ya tambaye ta, “daga ina kike, kuma ke ‘yar wanene sannan menene dalilin zuwanki nan?” Ta amsa masa ta ce, “ni ‘yar Ibrahima ce, wazirin sarki Shamihu. Dalilin zuwana nan kuwa abu ne mai ban mamaki, amma yadda na zo d’in ya fi ban mamaki. Ta fad’a masa dukkan labari daga farko har k’arshe ba ta rage komai ba. Sannan ta yi ajiyar zuciya mai k’arfi ta rera wak’a cikin murya mai ban tausayi. Bayan ta gama wak’ar ta sake fada wa sarki labarinta daga farko har k’arshe. Da sarki ya ji haka sai tausayinta ya kama shi, ya gane cewar lallai tana cikin halin k’unci na bege. Ya matsa kusa da ita ya ce, “ki kwantar da hankalinki, kada ki ji tsoron komai zan tsaya miki har ki samu nasara wajen cimma burinki.” Ya rera wad’annan baitoci:
Ke ‘yar manya idan kin cimma burinki
Ki ji zancena ki bar jin tsoro ko fargaba
Yau zan aika ki da dukiya mai yawa
Ga Shamiha da rundunar mai martaba
Tare da farar azurfa da farar zinariya
Gami da takarda gare shi don ke ‘yar baba
Don haka zan abotaki wannan sarki
A yau zan zama mai son ki cigaba
Ni kaina na shiga k’unci soyayya
Na san wahalar ta da dadi da azaba,....04 HIKAYAR ANASIL WAJUDI DA MASOYIYARSA ALWARDI FIL AKMAM

Da ya k’are wak’ar ya aika aka kirowa wazirinsa ya sa ya shirya dukiya mai yawa, ya umarce shi ya d’auka ya tafi wajen sarki Shamihu ya ce masa, “sarkina yana gaishe ka, kuma ya ce ka ba da wani mutum ana kiran sa Anasil Wujudi yana son ganawa da shi.” Sarki ya ce, “ku ce masa ina da d’iya wadda nake so na aura masa , saboda haka babu makawa ku taho da shi, idan kuwa kuka gaza to zan tub’e ka daga wazirtaka.” Waziri ya ce, “na ji, na bi.” Ya kwashe dukiyar nan da ta fi gaban k’idayawa tare da jama’a masu yawa ya tafi zuwa birnin sarki Shamihu. Yana zuwa ya wuce fada aka yi masa iso. Sarki ya karb’i takardar sarki Darbas tare da kyaututtukan da ya aiko. Bayan ya karanta takarda ya ga sunan Anasil Wujudi sai hawaye suka kwararo masa, ya dubi wazirinsa ya ce, “ina Anasil Wujudi ya ke? Ya bar wajenmu ba mu san inda ya tafi ba.” Ya dubi wazirin sarki Darbas ya ce, “da za ka nemo min shi da na ba ka ninki biyu na abin da ka kawo min.” Ya yi kuka yana ajiyar zuciya ya wak’e wad’annan baitoci yana cewa:
Ku dawo min da masoyina
Ba ni buk’ata da dukiya
Ban son kyautar jauhari
Ko lu’ulu’u ko ko zinariya
A wajenmu ya fi wata haske
Wajen kyau bare taurariya
K’irarsa tamkar reshe
Da ‘ya’ya na dad’in itaciya Na goye shi tun yana yaro
Ya girma hannuna yaminiya
A yanzu na rasa shi tuni
Ya tashi ya shiga duniya
Ya juya ga wazirin sarki Darbas, “koma ka shaida wa sarkinka cewa Anasil Wujudi ya b’ata fiye da shekara kenan, ubangidansa na neman sa bai san inda ya tafi ba.” Waziri ya ce, “ya shugabana,ai shugabana ya ce idan ban zo da shi ba zai tub’e ni daga sarautar waziri, kuma zai kore ni daga garinsa. Ta yaya zan koma kuwa ba tare da muradinsa ba?” Sarki Shamihu ya ce da wazirinsa Ibrahim, “tafi tare da jama’a ku duba ko’ina har ku samo Anasil Wujudi.” Ya amsa, “na ji, na bi.” Ya fita ya d’ebi jama’a mabiyansa tare da wazirin sarki Darbas shi ma da jama’arsa suka tafi zuwa neman Anasul Wujudi.

Waziri Ibrahim ya fita da mabiyansa tare da wazirin sarki Darbas shi ma da jama’arsa suka tafi zuwa neman Anasul Wujudi.
Suka zama koyaushe suka samu Larabawa na birni da na daji ko wad’ansu mutane idan suka tambaye su, “yalla kun ga wani saurayi mai kama kaza mai siffa kaza?” Sai su ce, “ba mu gan shi ba.” Suka yi ta zagayawa cikin birni da k’auye da daji da kwazazzabai da kwaruruwa suna cigiya ga sarakuna da talakawa da malamai da attajirai, har dai suka isa gacin kogi suka tsinkayi jirgi suka shiga ciki suka tafi cikinsa. Har suka soma hangen dutsen Sakla. Wazirin Sarki Darbas ya ce da waziri Ibrahim, “me ya sa ake kiran wannan dutsen haka?” Ya ce, “an ce a wani lokaci mai tsawo da ya shud’e wata aljana daga aljanun Sin ta kamu da son wani bil Adam sai ta ji tsoron jama’arta kada su cutar da ita da masoyinta. Ta zagaya duniya tana neman inda za ta b’oye shi ba su gan ba. Daga bisani ta ga wannan dutse wanda babu wanda ya san da zamansa tsakanin mutum da aljan. Ta d’auko masoyinta ta kawo shi wanna wurin. Da haka ta kub’uta daga sharrin mutanenta. Takan ziyarce shi a b’oye ba da sanin kowa ba. A haka har ta haifi ‘ya’ya da dama da shi. Idan fatake za su wuce ta wajen sai su rik’a jin kukan yara da jarirai na fitowa daga dutsen kamar kukan jaririn da uwarsa ba ta kusa. Sai suke mamaki suna cewa, “dama akwai sakla a nan?” To da haka aka samu sunan wannan dutsen.” Wazirin sarki Darbas ya yi mamaki da wannan labari. Suka isa dutse zuwa ga k’ubba suka k’wank’wasa. Baba ya fito ya shaida waziri ya durk’usa ya gaishe shi sannan ya shigar da su ciki, waziri ya ga wani talaka a cikin babanni wanda shi ne Anasil wujudi bai gane shi ba. Ya ce musu, “wannan kuma fa wanene?” Suka ce, “bafatake ne wanda jirginsu ya gamu da had’ari, kayansu gaba d’aya sun dulmiya, shi ma Allah ne ya yi da nisan kwanansa.” Waziri ya tausaya masa sannan ya sa aka bud’e sashin da ‘yarsa ke ciki ya shiga, bai gan ta ba sai kuyanginta kad’ai. Ya ce, “ina Alwardi ?” Suka ce, “ba mu san inda ta yi ba. Muna ta jiran ta dawo har yanzu ba mu gan ta ba, domin ba ta jima tare da mu ba.” Waziri ya ji bak’in ciki mai yawa tare da shi. Ya yi kuka sannan ya wak’e wad’annan baitoci yana cewa:
Ya kai gidan nan wanda tsuntsayensa ke yin wak’a
Wanda dukiyarsa da ba ta amfane shi da komai ba
Mai bege ya zo wajen abin begensa bai gane shi ba
Ya tarar da k’ofofin gidan a bud’e ba a kulle ba
Kaicona ina ma za ni san da ilmina da fuskata
Na gano mai wannan gidan wadda ba ta zauna ba
An aje mata komai na dukiya da farin ciki a cikinsa
Amma ta k’i da su ta amfane su ba ta yarda ba
Bayan ya k’are wak’ar ya sake fashewa da kuka yana mai bak’in ciki yana cewa, “babu wanda ya isa gujewar k’addarar ubangiji, kuma babu makawa ga abin da ya hukunta.” Ya hau saman soron sai ya ga tufafi na Sundusu an kekketa shi an d’aura shi zuwa k’asa kamar igiya. Ya fahimci fita ta yi ta wannan waje. Ya zama yanamad’imauci zuwa ga abokan tafiyarsa. Ya waiwaya ya ga tsuntsaye biyu suna wak’a tsakaninsu. Bak’in cikinsa ya k’aru ya rasa inda zai sa kansa. A haka dai ya sauka k’asa yana mai b’acin zuciya yana kuka. Ya umarci bayi da hadimai da su bi gangaren dutsen da kewaye domin neman uwargijiyarsu. Suka fita suka kewaye ko’ina ba su gan ta ba suka dawo. Wannan kenan game da al’amarinsu.
Game da Anasil Wujudi kuwa, yana wajen ake zancen b’atan Alwardi, da ya tabbatar da labarin sai ya yi ta kuka har ya fad’i sumamme, bai farfad’o ba sai da ya d’auki tsawon lokaci har mutane sun soma tsammanin mai fisga ta rik’e shi daga Arrahmanu, ya dulmiya cikin bautar Daiyanu. Tuni sun d’ebe tsammani daga samun Anasul Wujudi, Waziri Ibrahim kuma ya shagala da zulumin inda ‘yarsa ta shiga a wannan dajin. Wazirin sarki Darbas ya shirya domin komawa k’asara ba tare da cimma burinsa ba. Suka soma shirin ban kwana da waziri Ibrahim, ya ce da shi, “ina so na tafi da wannan talaka tare da ni, k’ila sarki ya gan shi ya tausaya masa domin shi mutum ne mai tausayi. Bayan haka zan shirya shi na aika da shi zuwa Isafahanu wanda yake babu nisa da garinmu.” Waziri ya ce, “aikata abin da kake so.” Suka yi sallama da juna, kowa ya tafi zuwa k’asarsa. Wazirin sarki Darbas na tare Anasil Wujudi ba tare da ya sani ba.
A nan asuba ta riski Shaharzad ta katse zancenta mai dadin saurare.
DARE NA 380
A dare na dari uku da tamanin, Shaharzad ta ce na samu labari ya kai wannan hamshaƙin sarki, Wazirai suka yi sallama da juna, kowa ya tafi zuwa k’asarsa. Wazirin sarki Darbas na tare Anasil Wujudi ba tare da wazirin ya sani ba, shi kuwa Anasil Wujudi yana sume bai san inda kansa yake ba har kwana uku suna tafiya sannan ya farfad’o. Ya ce da jama’a, “ina nake anan?” Aka ce masa, “kai kana cikin tawagar wazirin sarki Darbas.” Aka tafi aka shaida wa waziri wanda ya aiko da ruwan wardi da sukari suka ba shi ya sha ya samu k’warin jiki. Suka cigaba da tafiya babu tsayawa har suka doshi birnin sarki Darbas Zaki. Da sarki ya samu labarin zuwansa ya rubuto masa takarda cewa, “idan Anasil Wujudi ba ya tare da kai kada ka dawo har abada.” Waziri hankalinsa ya tashi, ya rasa abin da ke masa dad’i. Shi bai san cewa Alwardi na tare da sarki ba, bai san dalilin aika shi neman Anasil wujudi ba haka kuma bai san dalilin son sarki na had’a surutaka da shi ba. Sannan bai san cewa yanzu haka yana tare da Anasil Wujudi ba. Waziri ya sa aka kirawo masa talakan nan ya ce masa, “sarkina ya aike ni domin wata buk’ata tasa, kuma ya ce idan buk’atar nan ba ta biya ba kada na koma gare shi.” Talaka ya ce, “wace buk’ata ce haka?” Waziri ya kwashe zance duka ya shaida masa daga farko har k’arshe. Anasil Wujudi ya ce, “don wannan kada ka ji tsoro, ka tafi kai tsaye wajen sarki ka tafi da ni, zan tsaya maka a madadin Anasil Wujudi.” Waziri ya yi farin ciki da haka ya ce, “yalla da gaske kake nufin hakan?”
“Da gaske nake.” Waziri ya shirya ya hau zuwa wajen sarki Darbas wanda bayan ya yi masa marhaba da dawowa ya ce masa “ina Anasil Wujudi?” Matashin saurayi ya matsa gaba ga sarki ya ce, “na san inda yake.” Sarki ya ce masa, “Ina yake?” Anasil Wujudi ya ce, “yana nan kusa da kai babu nisa, amma kafin na fad’a maka inda yake ina so na ji dalilin da ya sa kake nemansa haka, zan kawo maka shi nan wajen.” Sarki ya ce, “yanzu kuwa zan fad’a maka amma a sirrince.” Ya tashi ya shiga ciki bayan ya umarci jama’a su ba su wuri. Ya shaida masa dukkan zance daga farko har k’arshe. Saurayi ya ce da sarki, “tufatar da ni tufafi mai kyau, zan tafi yanzun nan na kawo maka Anasil Wujudi.” Ya sa aka kawo masa kayan sawa na alfarma masu tsada ya shirya kansa, sannan ya zauna sosai ya ce da sarki, “ni ne Anasil Wujudi, mai yanke bak’in ciki, mai manta wahala.” Ya waiwayi zuciyars ya jefe ta da hararar k’auna ya yi wak’a mai nuna tsantsar soyayyarsa da halin da ya shiga a baya da wanda yake ciki yanzu.

TALLA

Wannan daya labari' dayane daga cikin HIKAYOYI wanda muke gudanarwa kullum da daddare, a zauren mu na sirri wanda masu rijistane kawai ke samun daman shigaDomin yin rijista kuna iya tura kudinku 200 kacal ta sakon waya kota hanyar transfer'dauke da sunaka na Facebook izuwa 0803276754705 HIKAYAR ANASIL WAJUDI DA MASOYIYARSA ALWARDI FIL AKMAM

Sarki ya yi kururuwa yana mai cewa, “wallahi ta tabbata ku masoya ne na gaskiya , ku ne watanni don kyawo da taurari don haske, al’amarinku da ban al’ajabi, sha’ananinku makad’aici ne.” Sannan ya fad’a masa duk yadda suka yi da Alwardi, Anasil Wujudi ya ce, “yanzu tana ina ya sarkin zamani?” Sarki ya ce tana nan tare da ni yanzu haka.” Ya aika aka kirawo alk’ali tare da shaidu aka rubuta takardar yarjejeniyar aure tsakanin su
Ya bai wa Anasil wujudi kyautuka masu yawa na alfarma ya aika wa sarki Shamihu yana mai ba shi labarin abin da ya wakana, sarki Shamihu ya cika da farin ciki da murna. Ya aiko da amsa cewa, “tunda an gudanar da sha’anin d’aura auren a fadarka, to ina so shagalin bikin da kwanan farko ya zama a garina.” Ya shirya rak’uma da dawaki da mutane ya aika su da su tafi su zo da ma’auratan. Yayin da jakadun suka zo sarki Darbas ya ba wa masoyan dukiya mai yawa ya aika da su tare da jama’a zuwa wurin sarki Shamihu. Ranar da suka zo ta zama babbar rana a garin, domin sarki ya sa an k’awata gari lungu da sak’o. Aka tattaro mawak’a da makad’a da masu rawa da duk wasu masu wasan nishad’i aka hallaro su zuwa fada. Aka yi ta shagulgula ba dare ba rana har kwanaki bakwai, a kowacce rana sarki ya kan fitar da kaya da kud’i ya yi ta sadaka ga mabuk’ata da tufafin alfarma. Bayan wad’annan kwanaki Anasil wujudi ya shiga wajen Alwardi suka rungume juna suna kuka saboda farin ciki da murna. Bayan sun zauna ta wak’e wad’annan baitoci:
Farin ciki ya zo ya kori bak’in ciki,
Mun sadu da juna bayan shan wahala
Iskar had’uwarmu ta sada mu da hanzari
Mun zama abu d’aya ni kai ba zilla
Mun gamu da tasku mai yawa a baya
Yanzu kam ya zam tarihi mai k’walla
Bayan ta k’are wannan wak’ar suka sake rungumar juna suna kuka har suka fita hayyacinsu.
A nan asuba ta riski Shaharzad ta katse zancenta mai dadin saurare.
DARE NA 381
A dare na dari uku da tamanin da d’aya, Shaharzad ta ce na samu labari ya kai wannan hamshaƙin sarki, Anasil Wujudi da Alwardi fil Akmami suka rungume junansu suna kuka har sai da suka fita hayyacinsu. Bayan sun farfad’o, Anasil Wujudi ya rera wad’annan baitoci:
Dad’i ba ya k’arewa sai rai ya k’are
Yau ga ni rungume da masoyiya ta
Saduwarmu ta zama ta tabbata kenan
Rabuwar mu kuwa ta tafi haihata
Zamani ya aikata kirki a gare mu
Arziki ya zama alheri ga zukata
Taruwar mu ta kunyata mahassada
Masu son su ga burinmu bai tabbata
Mun gode Arrahmanu da ya sa haka
Mun yafe duk abin nan da ya gabata
Bayan ya k’are wannan wak’ar suka sake rungumar juna suka nutse cikin kogin bege suka k’unshe kansu a keb’e suna ta nishad’i da shagali da hira da soyayya har kwana bakwai ba su sani ba. Domin ba sa bambamce tsakanin dare da rana. Duk gajiya da wahala da azabar da suka sha ta wuce, sai suka ji tamkar wad’annan kwanaki bakwan kwana d’aya ne kawai ko k’asa da haka. Ba su ma san kwanakin sun cika ba sai da mawak’a da makada suka zo musu a daren Juma’a. Alwardi ta yi mamakin saurin kewayowar wannan rana. Ta tashi ta shiga rera wak’okin soyayya da na farin ciki har kowa a wurin ya cika da murna mai yawa. Bayan ta k’are wak’ok’in, mijinta ya tashi ya sumbace ta fiye da sau d’ari. Ya rik’e hannunta ya rera wasu wak’ok’in sannan suka d’ebo dukiya mai yawa suka rarraba wa mahalarta domin nuna karamcinsu da godiya ga Allah. Sannan ta buk’aci su kad’aice su biyu ciki d’aki. Ya ce da ita, “ya sanyin idona, burina kenan na gan mu biyu a keb’e cikin d’aki.” Ta kama hannunsa suka shiga ciki, suka ni’imtu a cikinsa, sannan suka fito suna masu farin ciki da k’aunar juna. Haka suka cigaba da zama cikin farin ciki da annashuwa har mai rusa jin dad’i, mai rarraba jama’a ta zaike musu. Tsarki ya tabbata ga wanzajje wanda ba ya mutuwa har abada.

HIKAYAR ABU NAWWAS DA KHALIFA HARUNA RASHID
Wata rana Abu Nawwas ya kad’aice a d’aki ya shirya kayan walima na daga dangogin abinci da nama da duk wani abu da baki zai ji dad’insa. Ya fita yana bid’ar masoyi wanda ya kamata ya zauna tare da shi a wannan wuri. Ya ce, “ya ubangijina, na rok’e ka ka datar da ni da wanda ya cancanci zama a wannan wuri wanda zai zama tare da ni a wannan rana.” Kafin ya rufe baki sai ga wasu samari su uku marasa gemu sun zo wucewa. Kyawawa ne kamar ‘ya’yan aljanu, kowannen su yana da wata siffa wadda ta sha bamban da d’aya. Duk wanda ka kalla sai ka yi tsammanin ya fi d’ayan kyau. Sun kasance yadda wani ke cewa, “marasa gemu sun wuce ni, sai na ce ina son ku. Suka ce min kai mai dukiya ne? Na ce musu ni mai kyauta ne.”
Abu Nawwasu ya ce da samari, “ku zo mu je wajena mu yi liyafa.” D’aya daga cikin samarin ya ce, “kai tsoho mai furfura ka nisanci samari kamar yadda wani mawak’i ke cewa:
Idan ka ga tsoho yana bin samari,
Karkataccen tsoho ne mara tarbiya
Kada ka bid’i fari in ba nono ba
Kada ka biye wa tsoho mai son tsiya
Abu Nawwasu ya ce, “ina so ne ku zo wajena akwai ni da nama da abinci da kayan shaye – shaye. Ku ci ku sha ku gode wa Allah ku ji dad’i.” Samari suka amince da maganarsa suka karkato gare shi suka amsa kiransa.Abu Nawwasi ya rud’i samari da zance suka yarda da shi suka bi shi gidansa, suka tarar da duk abin da ya fad’a masu. Suka zauna suka ci suka sha cikin dad’i da nishad’i. Samarin suka ce da Abu Nawwasi ya nuna wanda ya fi kyawu da kwarjini da cikar halitta da madaidaiciyar tsayuwa tsakanin su. Ya yi nuni zuwa ga dayan su ya zaburo ya sumbaci hannunsa yana cewa:
Raina fansa ne ga goshinka,
Zan fanshe shi da dukiya
Alheri ya tabbata ga Allah
Da ya sa ka abin yin nuniya
Ya yi nuni ga na biyu, suka gaisa sannan ya wak’e wad’annan baitoci:
Akwai abin bege a gare shi,
Ni ban ga tabo a fuskarsa ba
Yana k’amshi irin na almiski
Gashinsa na salati ga manzo babba
Ya yi nuni ga na uku, suka gaisa sannan ya yi wak’e yana cewa:
Ya narke kamar kaskon dinari,
Saurayin da ya fi atafa taushi
Ku duba da kyau kwa yarda da ni
Kyawonsa ya fi barewa mara yaushi
Tafin sahunsa na sabon haihuwa
Ku nutsu sosai ku shaida shi
Kowanne daga samarin ya sha kasko bibiyu. Yayin da sha kaskon sha ya gewayo wajen Abu Nawwasi sai ya d’aga shi sannan ya rera wannan wak’ar:
Ka bar shan giya sai a wajen manya
Zab’ab’b’un dangi masu kyan asali
Ka yi koyi da shi a wajen shansa,
Ka ji dad’i da murna mara misali
Ita giya sam ba ta da dad’i ko kusa
Amma mai shan ta ya kan kashe garali
Ya sha kaskonsa, sannan sha ya cigaba da zagayawa har ya dawo kan sa, ya sake rik’ewa ya rera wannan wak’ar:
Aje wa abokin sha kasko a bakinsa
Idan ya shanye sai ka k’ara mai wani
Kada ka sha giya face a wajen babba
Mai kambin kundukuki mara gunguni
Ya sha da yawa har maye ya rinjaye shi, ya kasa bambance kansa da k’afafunsa ya tashi ya rufarwa samari da wahalarwa da kokowa da bugu da kecewar riga da naushi, bai kula da zunubi ba ballantana laifi. Ya rik’a rera wak’a yana cewa:
Dad’i ba ya tare da saurayi mai sha,
Ya isar da nufinmu ba tare da nadama ba
Wannan ya k’are da nan wannan ya fara
Su rayu cikin kasko ba tare da sani ba
Abin nufina ku sani sha ni na shaye ka,
Ya al’ajabi ku so ni na so ku ba da shakka ba
Yana cikin haka sai suka ji ana k’wank’wasa k’ofa, ya tashi ya bud’e sai ga Khalifa Haruna Rashid a tsaye. Suna ganin sa gaba d’aya suka durk’usa gabansa suka d’auki k’asa. Nan take mayen giya ya saki Abu Nawwasi. Khalifa ya ce masa, “yaya dai Abu Nawwasi?” Ya amsa “Labbaika ya Amirul Muminin. Allah ya taimake ka.” Khalifa ya ce, “me kuke yi ne haka?” Abu Nawwasi ya ce, “Allah ya taimake ka, babu shakka gani da ido shi ne maganin tambaya.” Khalifa ya ce, “jiya na rok’i Allah ya ba ni iko na nad’a ka shugaban samari.” Abu Nawwasi ya ce, “ya sarkin musulmi yalla da gaske za ka ba ni wannan babban muk’amin?” Ya ce, “na’am, haka ne.”
“To idan ka nad’a ni za ka ambace ni da ita?”
Khalifa ya fusata da wannan tambayar ya juya a fusace ya tafi, ya kwana ya k’ufule da Abu Nawwasi. Shi kuwa ya cigaba da shagalinsa har zuwa wayewar gari sannan samari suka tafi, shi kuma ya shirya ya sanya kayan zuwa fada ya tafi. A bisa al’adar Khalifa idan ya zo fada ya zauna fadawa za su zauna da bayinsa, sai a kira mawak’a da masu labarai da makad’a kowa ya zauna a wurin zamansa babu mai wuce iyakar inda aka nuna masa. A wannan ranar ya zauna a majalisar kamar yadda ya saba, kowa ya taho ya zauna a wurin zamansa gwargwadon muk’aminsa sai ga Abu Nawwasi ya taho domin ya zauna, Khalifa ya yi kiran Masruru, ya sa ya tub’e masa riga ya d’aura masa fatar akuya, ya d’auki gurarar jaki ya d’aura masa a baya, sannan ya d’auko bak’ar tukunya ya d’ora masa aka ya zarga masa igiya a k’ugu. Khalifa ya yi umarnin a zagaya da shi sashin kuyangi a nuna shi gare su.

Khalifa ya sa ya tub’e rigar Abu Nawwasu ya d’aura masa fatar akuya, ya d’auki gurarar jaki ya d’aura masa a baya, sannan ya d’auko bak’ar tukunya ya d’ora masa aka ya zarga masa igiya a k’ugu. Sannan ya yi umarnin a zagaya da shi sashin kuyangi a nuna shi gare su da sashen manyan mutane masu alfarma da dukkan matattarar jama’a domin su gan shi su yi masa dariya su yi masa ature. Bayan haka a yanke kansa a kai masa. Masruru ya ce, “an gama!” Ya kama Abu Nawwasi ya aikata abin da aka umarce shi, ya tasa shi gaba suka shiga sashin kuyangi yana zagayawa da shi, su kuwa sun kasance adadin kwanakin shekara ne. Abu Nawwasi mutum ne mai barkwanci gwanin ban dariya, duk inda suka ce sai ya ba su dariya su yi masa kyauta. Bayan sun k’are da nan sun juyo aljihunsa ya cika taf da dukiya. Suna wucewa sai ga Waziri Jafaru ya shigo, lokacin da aka zartar da hukuncin ba ya nan ya tafi cika umarnin Khalifa a wani waje. Ya dubi Abu Nawwasi ya ce, “ya Abu Nawwasi yaya aka yi?” Abu Nawwasi ya amsa, “Labbaika ya shugabanmu.”

Wannan hikaya ta ABU NAUWAS' zataci gaba ne daya daga cikin zaurukanmu na sirri wanda masu rijistane kadai ke samun daman shiga
Domin yin rijista kuna iya tura kudinku 200 kacal ta sakon waya kota hanyar transfer'dauke da sunaka na Facebook izuwa 08032767547

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment