Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daukakani da ka tako ka
zo gidana, kar allah ya rabamu da irin wannan
bullowar da karramwa taku. Sannan sai ta zaunar
dashi kan wannan shimfida tace : ranka ya
dade ! yakamata ka tube babbar rigan na da
rawaninka ka saka karamin rigar. Sai ya tube
babbar ragarsa mai tsada irin ta gwamna.

Sannan sai ta bashi karamin riga (singlet) da
kyalle. Sannan sai tace masa : ranka ya dade !
Ai wannan babban riga da kasa na wazirai yanzu
ba lokacinsa bane, kabari idan lokacinsu yayi sai
ka dauka kasaka, amma yanzu wannan lokacin Ai
lokacin kananan kaya ne kayan bacci, .
Da waziri ya karbi kayan bacci ya saka sai suka
zauna a kan shimfida, jim kadan sai waziri ya yi
yunkurin matsowa saboda ya biya bukatarsa, ita
kuma tana kokarin hana sa. Tana ce masa :

ranka ya dade ! ai akoi sauran lokaci kar
kadamu.
To suna cikin haka, sai kawai Aka kwankosa
kofa, komai ya wargaje, waziri ya tsorata ya
firgita ya tamabayi matar yace mata : waye ? sai
tace : mijina ne ya dawo, sai waziri yace : to
yanzu me dabara ? sai tace masa : ka tashi in
shigar da kai cikin wannan drowan sannan in je
in komar da mijina, sai in dawo wurinka in bude,
kar kaji tsoro. Sai ta shigar dashi cikin drowa ta
sa shi a hawa na 3 ta kulle kirip da kwado.

Bayan matar ta kulle waziri a cikin hawa na 3 na
wannan drowa. Sai ta je ta bude kofa. Kawai sai
ga mai alaframa mai marataba sarkin gari ya
bayyana a tseye a bakin kofa. Da matar ta ganshi
atake sai ta zube a kasa ta durkusa tayi gaisuwa
ta bada girma. Sanna sai ta kama hannunsa ta
shigar da shi ciki ta zaunar dashi kan shimfidar.
Sai tace masa"

- cikin murmushi da fara'a da
annashawa - ya mai martaba yau dinnan ka
karramamu ka daukakamu, da zamu dauko
duniya gabadaya da abunda ke cikinta muka
kawo maka To abunda mukayi bai kai ko kadan
daga cikin takowar da ka yi ka karramamu ka zo
wajenmu ba….

Ranar juma,a insha Allahu zan dora daga yarda na tsaya". Yusuf abdullahi A jibaga, ke kawo muku wannan labari"

Whatsapp only
080710511 3803 KAIDI

Bayan sarkin wannan gari ya iso gidan wannan
mata, sai ya kwankosa kofa, matar ta bude, ta
durkusa ta yi gaisuwa ta yi masa marhaba da
zuwa. Sanna sai ta kama hannunsa ta shigar da
shi ciki ta zaunar dashi kan shimfidar. Sai tace
masa : ya mai martaba yau dinnan ka
karramamu, zuwarka ta daukakamu, da zamu
dauko duniya gabadaya da abunda ke cikinta
muka kawo maka, To bai kai ko kadan daga cikin
takowar da ka yi ka karramamu ka zo wajenmu
ba ( wato halacci da kayi mana ba zamu iya
biyanka ba )
Da mai martaba sarki ya zauna akan shimfida sai
tacemasa : ya mai martaba ka bani izini inaso in
yi maka wata magana, sai yace : kiyi maganarki
yadda kikeso na amince miki, sai tace masa : ya
shugabana ! yau dinnan ka zauna a nan ka huta
kayanka, kuma katube wannan babar riga da
rawanin nan naka ka kawo in ajiye maka su......
kuma shima sarkin rigar da ya saka yazo da ita
rigace mai tsadar gaske, tafi ta sauran tsada,
kimarta ya kai DINARI 1000.
To bayan wannan mata ta karbe rigar sarki da
rawaninsa, sai ta bashi karamin riga – na bacci
– (singlet) wanda kimarsa baiwuce DINARI 10
ba.

Bayan haka sai, matar ta soma debe masa kewa
tana dauke hankalisa. Kuma wannan duka yana
faruwane – wato hirar da ake – alkali da mai
girma gwamna da kuma waziri suna kulle a cikn
drowa suna sauraron duk abunda ke gudana –
hira- tsakanin mai martaba sarki da wannan
mata. Amma saidai babu wanda zai iya magana
daga cikinsu.
A lokacin da sarki ya yunkuro ya miko hannunsa
zai daura akan wuyar matar saboda biyan
bukatarsa, sai tacemasa : ranka ya dade Ai da
sauran lokaci, wannan ranar takace kai dadai,
bazata kubuce maka ba, Idan baka manta ba
ranka yadade Ai kafin wannan lokacin na maka
alkawarin cewar zanbaka irin wannan damar,
saboda haka kar ka damu ! zaka samu abunda
zai faranta maka rai awurina….

suna cikin haka suna hirai, kawai sai aka
kwankosa kofa. Sai sarki yace : – cikin takama
da nuna isa – waye wannan ? sai tace : mijinane,
sai yacemata : ki je ki komar mana dashi cikin
ruwan sanyi ( wato ya koma da son ranshi ) ko
kuma in fito ni da kaina in tilasta masa komawa
ko bayaso. Sai tacewa sarkin : A’A ranaka ya
dade baza’ayi haka ba, kawai kaidai kayi hakuri
zanje in yi masa dabara irin tamu ta mata in
komar da shi. Sai yace mata : To ni kuma yanzu
yaya zanyi ? kawai sai ta kama hannunsa ta
daukeshi ta shigar da shi cikin hawa na 4 na
wannan drowa ta kulle krip da kwado, sannan sai
ta je ta bude kofa, sai ga kafinta a tseye a bakin
kofa. Batareda bata lokaci ba, kafinta ya yi
sallama ya kutsa ya shiga. ita kuma Batareda ta
amasa sallamar ba tacemasa – fuskarat a daure
- : wannan wani irin drowa ne ka kera mini ? sai
yace mata : ranki ya dade ! me ya samu
drowar ? sai tace masa : Ai wannan drowar da ka
kera tayi matsi sosai, sai yace mata : ranki ya
dade ! Ai wannan drowan yana da fadi, kamar
yadda kika fada haka na yi, sai tace masa : ka
shiga kai da kanka ka duba ka gani bazata
isheka ba, zata maka matsi, sai yace mata : A’A
ai wannan zata iya daukan mutum hudu ma…
sannan sai ya shiga cikin hawa na 5 saboda ya
goda ya gani ko tayi matsi ko batayi ba. Shigarsa
keda wuya kawai sai wannan mata ta kulle shi a
ciki krip ta dannan kwado.
To Bayan wannan mata ta kulle kafinta a cikin
hawa na 5 na wannan drowa, sai ta kwashe
wadannan riguna masu tsada na wadannan
shuwagabanni dattawan gari. Sannan sai ta dauki
wannan takarda da mai girma gwamna ya rubata,
na kubutar da wannan saurayi (masoyinta) da
aka kulle agidana yari ( prison ) kuma atake
batareda bata lokaci ba ta fita ta nufi gidan mai
girma gwamna, ta shiga ofishinsa ta samu
sakatarensa ta bashi wannan takarda.
Da sakatare ya karbi takarda ya karanta ya
fahimata, batreda wani bincike ko bata lokaci ba
atake ya bada umurni aka bude wannan saurayi
aka fito da shi daga gidan yari.
Sannan bayan wannan saurayi ya fito, sai matar
ta bashi labarin yadda ta yi ta kubutar dashi da
gidan yarin, sai saurayin yace mata to yanzu me
yakamata muyi ? sai tace masa : Ai fita zamuyi
mu gudu ma bar garin nan kawai, saboda
wannan danyen Aiki da muka aikata, zama a
wannan gari ba zaiyu mana. Sannan sai suka
shirya kayansu gabadaya, har dawadannan riguna
masu tsada, suka daura akan doki suka fice suka
bar gari babu wanda ya san abunda ke faru a
gari. … To wannan mata a nan nata ya kare, ta
kwashi rabonta.
Amma su kuma wadannan shuwagabanni da
kuma kafinta, basu gushe ba suna cikin wannan
drowa har tsawon kwana 3, batarda ci ko sha ba,
suka samu kansu cikin matsi da kunci, saboda
kwana 3 basuyi fitsariba. To (da tura ta kai
bango … ruwa kuma ya karewa dan kada) sai
kafinta ya yi fitsari, fitsarin ya tsiyayo kan mai
martaba sarki Da sarki ya matsu abun ya
dameshi sai shima yayi fitsari akan wazirinsa,
haka shima waziri ya fitsari akan mai girma
gwamna, sai shima mai girma gwamna yayi fitsa
fitsarin ya koraro kan alkali wanda kuma shine na
karshe. Da alkali yaga fisari – kala kala – ya
koraro kansa, sai ya daka tsawa yace : kaai !!
wannan wani irin rashin mutunci ne ? wani irin
kazanta da najasa kuke turomini ne ? shin
wannan hali da muke ciki na matsi bai ishemu ba
har sai kunyi mana fitsari a nan ? sai mai girma
gwamna ya daga muriyarsa yace : ya kai ! alkali
ALLAH ya saka maka da alkhairi, . Da alkali yaji
wannan muriya, sai cewa mai girma gwamna ne
da kanshi a nan. Sannan sai gwamnan ya daga
muriyarsa yace".

wannan wani irin kazanta ne
(najasa) ? To sai wazirima ya daga muriyarsa
yace : wannan wani irin kazantane ? sai sarki yaji
muriyar waziri yace : ALLAH ya sakawa wazirin
sarki da ALKHAIRI. Sannan da sarkin ya gane
muriyar waziri sai ya ja baki yayi shiru.
Da waziri yaji anfadi haka kuma baisan cewa mai
martaba sarki bane, sai yace : wannan abu da
wannan matar tayi mana UBANGIJIN ALLAH ya
tsine mata albarka, ta tara manyan dattawan
garin nan gabadaya a cikin wannan drowa ta
kulle saura sarkine kawai ya rage bata
kawoshiba, sai gwamnaa da alkali suka cewa
waziri : hakane kayi gaskiya.
Da mai martaba sarki yaji haka sai daka tsawa
yace : (shut up ) kuyi min shiru gabadaya, Ai
nine farkon wanda ya fada cikin tarkon wannan
la’ananniyar mata.

Da kafinta yaji abunda wadannan dattawa suka
fada sai yace : To nikuma me nawa a ciki ? wani
laifi na yiwa wannan matar da zata yimin haka ?
tace mini in kera mata drowa zata biyani DINARY
4, ? gashi yanzu na gama na zo karba kudin
Aikina, kawai sai tayi min dabara ta kulleni a cin
wannan wuri !! ?. Sannan sai suka cigaba da hira
a cikin wannan drowa, suka debewa sarki kewa,
suka kawarmasa da kunci da muwa dake
taredashi
Ana cikin wannan yanayi, sai makwabtan wannan
gida – gidan matar – suka zo suka samu gidan
babu kowa a ciki, kuma matar bata nan. Sai suka
gayawa junansu " shekaranjiya wannan
makociyar tamu matar wane tana cikin wannan
gida, amma yanzu kuma babu kowa a cikin
wannan gida, bamu jin muriyar kowa. Sai suka
balla kofofin gidan saboda su tabbatar da
gaskiyan al’amarin. Sai sukace : ya kamata mu
bude mutabbatar saboda kar mai girma gwamna
ko sarki yaji labari ya kullemu, daga baya muyi
nadama muce mesa bamu balla kofar mun
tabbatarba ? . sannan sai suka balla kofar
wannan gida suka shiga suka samu drowa ta
katako, kuma suka ji sautin garada a ciki suna
nishi saboda tsananin ishruwa da yunwa. Sai
mutanen suka soma maganganu a tsakaninsu
suna shawara, sukace : shin aljanine a cikin
wannan drowa ? sai daya daga cikinsu yace :
kawai mutara itatuwa mu kette ashana mu kona
wannan drowan. Da Alkali yaji haka sai ya daka
masu tsawa yace musu : kaai ! ! kar ku Aikata
haka ….

Bayan da makwota suka yanke shawarar cewa
zasu tara itatuwa su kona wannan drowa da suke
tsammani kamar aljanu a ciki,,, atake sai alkali
ya musu tsawa yace : kaai ! kar ku aikata haka.
Da mutane ( makwota ) sukaji muriyar mutum
‘DAN ADAM yana tsawa a cikin drowa sai sukace
: babu shakka wannan aljanine yake kamanta irin
muriyar ‘YAN ADAM.
Da alkali yaji maganar da suka fada, atake sai ya
gyara muriyasa ya karanta wasu ‘A’YOYI daga
cikin ALKUR’ANI mai girma saboda ya tabbatar
musu cewar ba aljanu bane a cikin drowar,
sannan bayan ya gama karatun sai yacemusu :
kumatso kusa da wannan drowa da muke ciki, su
kuma basu ji tsoro ba sai suka matso.

Bayan sun matso sai alkalin yacemusu : nine
wane ( ya fadi sunansa ) ku kuma kune su wane
da wane ( ya kira sunansu gabadaya ). Kuma ya
cigaba da cemusu : a cikin wannan drowa akoi
su wane da wane.
Da makwotan sukaji haka sai suka tambayi
alkalin suka cemasa : wayene ya kawoka
wannan warin ? kabamu labari ? sai alkali ya
warwaremusu labarin yadda lamarin ya faru daga
farko zuwa karshe.

To Bayan alkali ya bawa wadannan mutane
(makwota) labarin abunda ya faru, sai su kuma
suka je suka kawo wani kafintan -daban - ya
balla wannan drowa,
Farkon wanda aka bude ya fito shine alkali,
sannan mai girma gwamna, sai waziri, sannan
sarki, kafinta shine a karshe. Kuma kowannensu
ya fito da rigar da ke jikinsa – wanda wannan
mata bashi - .
Bayan sun fito daga cikin wannan drowa sun
tsaya da kafafunsu, sai ko wa daga cikinsu ya
soma kallon dan uwansa, suka soma yiwa
junansu dariya. Sannan - jim kadan - sai suka
soma bincike suna neman wannan mata a cikin
gidan, amma basu ganta ba, basu ga alamunta
ba, ita kuma ta riga da ta kwashe rigunansu –
masu tsada – ta yi gaba da su.
To Sai kowa daga cikinsu ya aika gida aka kawo
masa wata rigar daban ya saka. sai suka fice
daga wannan gida aboye saboda kar wani ya
gansu, sukabi ta cikn lungu – lungo, sako sako,
har suka isa gida.
Saboda haka yakamata ka duba kayi nazari sosai
kaga irin wannan makici da kadi da wannnan
mata shirwa wadannan dattawa shuwagabanni,
kar kayi gaggawar aiwatar da hukuncin kisa akan
wannan yaro ‘(DANKA) saboda maganar da
matarka ta gayamaka. ( waziri na 6 ya ke
gayawa sarkin )
Bayan da sarkin yaji wannan labari sai ya huuce,
ya kuma sauya ra’ayinsa gameda aiwatar da
hukuncin kisa akan (‘DANSA)
Bayan haka, washegari sai matar taji labari,
cewar sarki ya sauya ra’ayinsa, atake ta shiga ta
zugashi tayi ta kuka tace sai ta kashe kanta idan
sarki bai karba mata hakkinta ba.

To sai ta bawa sarkin labari da ke kunshe da
makircin maza, da sarkin yaji labarin sai ya rikide
hankalinsa ya tashi, atake sai ya canza ra’ayi, ya
bada umurni a kashe wannan yaro.
Da waziran suka ji labarin irin matakin da sarkin
ya dauka gameda '(DANSA) sai suka turo waziri
na 7 yazo ya rarrashi sarkin, kuma ya bashi wani
labarin daban gameda makircin mata… haka
sukayi tayi har zuwa karshe labarin.

TO WANNAN LABARI DA KUKA KARANTA, DAYA
NE DAGA CIKIN LABARU FIYE DA 20 DA SUKE
KUNSHE DA MAKIRCE - MAKIRCE DA KAIDI NA
MATA DA NA MAZA…

KAMAR YADDA MUKA
SANAR DA KU - A BAYA - CEWA WADANNAN
WAZIRAI ADADINSU YAKAI 7, KUMA WANNE
DAGA CIKINSU IDAN YA SHIGA WURIN SARKI
SAI YA KAWO LABARI FIYE DA 1 .. DAGA BAYA
ITAMA MATAR TA SHIGA TA KAWO LABARI
FIYE 1.. TO ANAN ZAN TSAYA

Yusuf abdullahi A jibaga' ke kawo muku wannam labari

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

2 Comments On HIKAYAR KAIDIN MATA
avatar
hamisu-6

1 year ago

Reply

I have subscribed to one of your package but still I ca'nt download

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to hamisu-6

have You paid the package Money, if you paid contact me here 08140419490

Please Login or Register in order to submit comment