Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

HIKAHIKAYAR LAILA DA MAJNUN

maimaici ne√

Hikayar Laila da Majnun an ba da ita kimanin
shekaru dubu da suka wuce, kuma an bayar da
ita ta fuskoki da dama, to amma dukkan
fuskokin sun hadu akan ginshiki daya, watau
tsarkakkiyar soyayya ce tsakaninsu. Ga irin
hikayar da muka rairayo:

Wani saurayi mai suna Qays ibn Mulawwah dan
kabilar Banu Amar. Qays ya kasance mai fasahaf
da basira a makarantarsu, sai dai ya kamu da
soyayyar Laila bint Mahdi Ibn Sa’ad an fi kiran
ta da Laila Amiriya, a hankali ya rika nuna mata
soyayya ta hanyar kulawa da sauran alamu. Duk
lokacin da ta makara zuwa makaranta sai
hankalinsa ya tashi ya rasa sukuni, gaba daya
sai ya zuba wa kofa ido ba ya mayar da hankali
ga karatunsa. Wata rana da zuciyarsa ta cika da
bege, ya ji kirjinsa kamar ya fashe, bai san
lokacin da ya rika rubuta sunan Laila a takardar
rubutunsa ba maimakon abin da ake koya
musu. Dalibai da suka ga haka sai suka
hakikance lallai ya yi nisa wajen kaunar ta. Da
haka ita ma Laila ta soma kaunarsa ya zamana
duk makarantar an san su a matsayin masoya.
Shi Qays kamar tun yana yaro k’arami masu
ilmin taurari suka bayyanawa mahaifinsa cewa
zai kasance wanda rayuwarsa za ta fada cikin
wahala da musiba. Suka kara da cewa idan ba
a yi da gaske ba ma zai iya haukacewa. Tun
daga wannan lokacin mahaifinsa ke samo masa
lak’ani da magunguna da addu’oi. Yayin da ya
data sai mahaifinsa ya dauke shi ya kai shi
Dimashka karatu inda anan ne ya hadu da Laila.
Ita Laila ta kasance ‘yar shugaban kabilar
Sharwaris, wadda a da zamanin Jahiliyya ba sa
ga maciji da kabilar su Qays. Laila da Qays suka
zama tamkar jini daya tsoka daya idan bai ga
daya sai ya kama rashin lafiya, amma Qays abin
na sa ya fi tsanani, domin kuwa har wakoki yake
rubutawa masoyiyarsa yana karanta su a ko’ina.
Daya daga wakokin da yayi mata ita ce:
Na so ki ya mai kyau dan gaske
Wane wata ko tauraro mai haske
Kin shiga ruhina kin mammallake
In babu ke to ni kuwa na hakkake
Ba za ni rayu a duniyar nan ba
A makaranta aka rinka gulmar su ana nuna
Majnun duk inda ya wuce, sai ya kasance idan
ka yi masa abu ka ce masa ya yi hakuri don
Laila, shikenan zancen ya wuce. Da dalibai suka
gano lagonsa, suka rika dauke masa kayan
rubutu suna cewa ya basu domin darajar Laila.

Ba musu sai ya ba su. Maubin (malamin)
makarantar ya damu kwarai da irin wannan
al’amari. Musamman da ya ga Qaysa wanda
yanzu sunan ya bace ya koma Majnun Laila
(Mahaukacin Laila) ya rubutawa iyayensu
takarda yana fadakar da su halin da ‘ya’yansu
ke ciki. Iyayen Laila suka cire ta daga
makarantar aka kirawo wani kwararren malami
yana koya mata karatu a gida. Ciwon so ba shi
da magani! Maimakon hakan hakan ya yi
magani sai ya dada rikita al’amari. Majnun ya
daina karanta komai kullum sai kuka sai waka,
duk abin da ya gani sai ya ga yana masa gizo
da kamannin Laila. Nan da nan sai ya soma rera
wakar so gare ta.
Mahaifin Majnun ya zo takanas ya dauke shi
zuwa wajen likitoci da ‘yan tsibbu da bokaye da
sauran masu da’awar magani duk abin ya zama
tamkar wutar kara ana yayyafa mata fetur.
Abokai da ‘yan uwa na kusa da na nesa suka zo
domin tausasa zuciyar Majnun ya daina tunanin
Laila amma duk a banza. Wani daga baffaninsa
ya ce masa, “wai kai Qays me ka gani a jikin
Laila da ka nace mata haka? Ka zo mu je na
nuna maka mata dubu wadanda suka fit a kyau
da kyan fasali da asali da mulki da dukiya da
sarauta ka zabi wadda ta yi maka.” Majnun ya
dube shi ya girgiza kai ya ce, “idanun Majnun
Qays ba wanda suke so da gani tamkar Laila.”
Ya daga hannu sama ya ce, “Ya Allah! Na san
ba ka yi kyakkyawa a duniyar tamkar Laila ba.
Na tabbata ita tana daga asalin Hurul Aini da
suka zo duniya shan iska. Ya Allah alk’awarinka
bay a tashi, na tabbata daga kan Laila ba zaka
sake wata kyakkyawa ba. Ya Allah ka ba ni
Laila!”

Wani daga kabilarsu ya ba shi shawarar ya
dauki Majnun zuwa Makka ya yi roko a ka’aba
kan Allah ya dauke masa son Laila a zuciyarsa.

Amma saboda tsananin soyayya a yayin da
suka je dakin ka’aba sai mahaifinsa yace masa:
kama tufafin ka’aba ka roki Allah ya cire maka
son Laila sai Majnun ya kama yace: “Allah na
tuba gareka daga dukkan laifi, amma bazan
tuba daga son da nake yiwa Laila ba . . . Ya
k’ara da cewa, “Ko Luqman, babban malami
masani na tabbata ba shi da maganin ciwon
so…Idan ma yana da shi ina fata babu wanda ke
tsakanina da Laila. Ya waka wadannan baitoci:
A Makka na ce da shehin malami,

Wai shin wace ke cutar da ni?
Shin laifi ta ke yi to a sanar da ni,
Shehi ya ce “d’ana bi a hankali,
Azaba na nan zuwa can gare ta
Na yi farat na ce masa “a’a na yafe,
Da azaba ta samu Laila ko a gefe,
Ba ni kauna gara ta same ni a lafe,
Da na daina sonta a barci ko fake,
Gara na mutu da ciwon kaunar ta
Sannan ya ce da murya mai raurawa, “Allah ka
ba ni Laila!”

GO BE ZÀMU DAURAHIKAYAR LAILA MAJNUN...2

Yayin da iyayen Majnun suka ga haka kullum
lamarin nasa k’ara lalacewa ya ke yi, sai suka
ga babu mafita face su je su nemi auren Laila
wurin iyayenta. Wannan shine mataki na k’arshe
da suke ganin zai magance matsalar d’ansu.
Suka tashi jakadu na musamman zuwa garin su
Laila suka bayyana musu irin halin da d’ansu
yake ciki game da soyayyar Laila. Sannan
jakadun suka nemi aurenta dominsa. Iyayen
Laila suka amsa da cewa, “mu a wajenmu abin
da Majnun yake yi domin ‘yar mu wulak’anci ne
mai girma. Kuma duk da yake mun san cewa
Laila tana da ra’ayinsa amma ba zamu iya
aurar da ita gare shi ba. A dalilinsa mun cire ta
daga makaranta, mu a wajenmu, mahaukaci ne
kad’ai zai rik’a irin abinda Majnun ke yi.”

Da haka iyayen Majnun suka ji dad'i tunda su a
tsammaninsu idan har ya daina shiririta za su
amince su aura masa ita. Saboda haka suka
shiga tausasarsa suna ba shi shawarar ya nutsu
ya daina abubuwan da yake. Majnun ya amince
da haka, amma da sharadin za a kaishi ya ga
abar k'aunarsa Laila.
Suka shirya suka tafi tare da wakilansa zuwa
garin su Laila. Aka sauke su a wani babban gida
sannan aka kawo musu abinci da abinsha. An
kawata wajen da fitilu masu launi iri dabam -
dabam. Sannan a kunna turaren wuta ko'ina sai
kamshi ke tashi. An jera kasake masu yawa cike
da abinci da fulawoyi masu k'ayatarwa. Zuciyar
Majnun kuwa ta kasa nutsuwa, ji yake kamar
yayi tsuntsuwa ya tafi ga masoyiyarsa. Bai iya
jurewa ba sai ya mik'e a gaban waliyan Laila ya
rika safa da marwa yana rera wadannan baitoci:
Na yi nisan zango don na gane ki,
Ga shi na zo nan ina ta bid'ar ki,
Ina kike ina kika shiga ne in ganki,
Zuciyata tana ta jidali domin nemanki
Ya ki taho abar begena don Allah nunan kanki
Jimawa kad'an sai ga karen da Laila ke zuwa
da shi makaranta ya shigo gidan. Majnun sai ya
ji ya kasa jurewa, ya zabura wajen karen nan ya
rungume shi yana sumbatarsa yana cewa, "Na
ga rabin Laila saura rabin. Ya karen nan mai
baiwa maza je ka ingizo min Laila." Garin
wutsulniyar da kare yake yi da k'afafu ya ture
farantan abincin, suka bata gaban rigar wani
dattijo mai fada aji a dangin Laila. Shi kuwa
gogan naka sai ya d'auki wani tsiron fulawa ya
mak'alawa karen a wuya yana ce masa, "maza
je ka kaiwa Laila ka mik'a min gaisuwata gare
ta." Duk jama'ar wurin suka yi tsit suna kallon
ikon Allah. Wakilan da suka rako shi suka rasa
inda zasu sa kansu domin kunya. Wakilan Laila
kuwa suka cika da fushi iyakar fushi. Wani daga
cikinsu ya fusata ya ce wa Majnun, "Shin bautar
kare ka zo ko kuwa maganar aure?"
Kai tsaye Majnun ya kalli mutumin ya ce,
"wannan karen a wurina ya fi mutum dubu
daraja, domin a jikinsa ina ganin surar
masoyiyata wadda k'aunarta ke d'amfare a
zuciyata dare da rana." Duk wuri aka d'auki
salati. Jama'a suka rik'a zundensa suna cewa
ya haukace. Dattijon nan da aka b'atawa riga da
abinci ya mik'e a fusace ya fice daga gidan. Duk
jama'a ma suka watse.
Da wannan jama'a suka rika rantsewa cewa
haukan nan dai bai rabu da shi ba, sai ma abin
da ya yi gaba. Daga nan iyayen Laila suka fito
kai tsaye suka ce ba zasu aurar da 'yar su ga
Majnun ba. To daga nan sai duk wani fatan
samun nutsuwarsa ya zama sharon gayya, suka
hakikance ba za su iya magance masa matsalar
ba, don haka suka sa masa albarka suka kyale
shi bisa halinsa. Shi kuwa duk inda ya shiga
lungu da sak'o sai ya rik'a cigiyar Laila ko sun
san inda take da yadda zai sadu da ita. A haka
har ya yi kicibis da wani jakada mai aikin raba
takardu. Ya tambaye shi labarin Laila. Jakada
ya ce masa Laila da iyayenta sun tashi daga
garinsu sun koma wani gari mai nisa, daga nan
garin zuwa can tafiyar mil dari da ashirin ne.
Majnun ya shiga yi masa magiyar yana ba shi
sako zuwa gare. Jakada ya amince zai karb'I
sak'on takarda kurum babu wani abu. Majnun
ya zauna yayi ta rubutun shafuka da yawa, har
jakada ya gaji ya ce masa, "wacce irin wasika ce
haka?" Majnun ya ce, "wasikar soyayya ce bata
da k'arshe."

Jakada ya yi dariya da haka sannan ya ce, "to
samu waje ka d'iga aya ka bani na tafi." Majnun
ya nad'e takardar ya ba shi. Sannan ya nemi ya
yi masa rakiya kad'an. Suna tafe Majnun na ba
wa jakada labarin abar k'aunarsa Laila shi kuma
yana ta mamaki. Sai da suka shafe mil goma
Majnun na tafiya a k'asa Jakada na bisa
rak'umi. Jakada ya ce masa, "to ka koma haka,
ka yi nisa kwarai da gidanku."

Majnun ya juyo
ya soma tafiya sannan ya juya ya ce da Jakada
da babbar murya, "ya kai k'aunataccen abokina!
Wallahi na yi mantuwar wani muhimmin sak'o
da nake so na rubuta mata!" Jakada ya ce, "to
gaskiya ba zan tsaya ba, sai dai ka fad'a min da
baki na fad'a mata. Majnun ya kowa ya same
shi suka rankaya. Suna tafe yana fad'a masa
sak'on har suka share wasu mil goman. Jakada
ya ce, "ka koma haka kada a neme ka a
gidanku." Ya juyo ya soma tafiya sannan ya
waigo ya ce, "wallahi ba domin kada ka ce na
matsa maka ba da na k'ara maka wani sak'on.
Muhimmi ne kwarai na mance da shi. Jakada ya
ce, "to matso ka fad'a min!" Suka sake
rankayawa yana ta fad'a masa sak'o. Haka
suka yi ta yi har kafin su ankara sai ga shi sun
isa garin da Laila take. Jakada yayi mamakin
irin wannan soyayya, sannan ya ce da Majnun,
"Babu buk'atar kai wa Laila sak'o gare ni domin
kuwa ga shi mun zo garin da take." Da jin haka
Majnun ya cika da farin ciki da murna. Ya fad'i
sumamme don tsananin farin ciki.

ZAMUCI GABA INSHA ALLAHU GOBE"
Whatsapp only
08071051138^ LAILA MAJNUN...3 ^•^

Bayan ya farfad’o jakada ya ce masa, “ba na so
a ganka, domin jama’a na iya kama ka su yi
maka wulak’anci kafin ka ga Laila. Ga wani
kango can ka shiga ka zauna a ciki ka huta
domin ka yi tafiya mai yawa. Zan isar da
sak’onka ga Laila yanzun nan.”
Majnun ya yarda da shawarar jakada ya shiga
kangon nan ya zauna zuciyarsa na harbawa
kamar ta tsage. Sakamakon tafiyar da ya sha
duk yayi futu – futu. Tufafinsa sun yi jawur da
k’ura, gashin kansa duk ya kukkulle, ga
kafafunsa sun yi fato – fato da kura da faso da
kaushi. Ga shi nan dai yarbajila da shi. Duk da
haka, da ya tuna cewar yana garin da Laila ta ke
gaba d’aya sai ya ji ransa ya yi fari fat. Ya cika
da murna da farin ciki, zuciyarsa ta cika da bege
ya rik’a rera wak’a yana cewa:
Na aika sako na wajen masoyiya,
Zuciyata da rayukana gaba daya,
Na mika su dukansu wajenki gimbiya,
Ke ce tawa hakika na fadi gaskiya.
Na sallama miki kaina lahira da duniya.

Daga nan sai gajiya ta kama shi, ya ji yana so
ya kwanta. To amma sai ya rika tunanin shin a
wanne bangare Laila take? Domin baya so ya
kwanta inda k'afarsa zata rika kallon jihar da
take domin a wajensa hakan cin amanar kauna
ne. Zai iya shurinta bai sani ba. Ya tsaya yana
tunani, shin tana gabas ne ko yamma ko kudu
ko kuwa arewa? Duk inda ya sa kansa sai ya
tuna kila a wannan bangaren take, sai yayi
maza ya sake waje. Daga baya dai sai ya samo
igiya ya daura a kafarsa ya samu gini ya daura
kafar, yana zamana yana reto kamar jemage. A
wannan yanayi kuma bai fasa rera mata wak'a
ba yana cewa:

Hajjina da Umarata na wajenki,
Makka ta da Madina sune ganinki,
Baitil Mukdis wurina murmushinki,
Arzikina duk ni dai in ga dariyarki,
Na sallama kaina gaba wurinki
Kishin ruwa na damunsa amma babu ruwa a
kurkusa, haka ya hakura wutar bege na hura shi,
tana kone masa sassan jiki da zuciya.
Jakada ya yi sallama k'ofar gidansu Laila ta fito,
ya ce mata, "na yi kokari da gaske domin na yi
miki magana, game da masoyinki Majnun wanda
ban taba ganin tamkarsa ba a fagen so." Ya
kwashe labarin duk yadda suka yi ya fad'a
mata. Sannan ya kara da cewa, "yanzu haka na
bar shi a bayan gari domin gudun kada a
wulak'anta shi idan jama'a suka ganshi." Da
Laila ta ji haka sai tausayinsa ya kama ta. Ta
tafi wajen uwar goyonta ta ce mata, "me yake
faruwa ga mutumin da ya yi tafiyar mil dari da
ashirin a kasa ba tare da ya huta ba?"

Tsohuwa ta ce, "wannan mutumin ba zai rayu
ba mutuwa zai yi."
Laila na jin haka sai ta ji ta shiga damuwa, ta
sake ce mata, "babu wani magani?"
"Magani daya ne a sanina. Dole ya sha ruwan
saman da aka ajiye shi akalla shekara d'aya,
kuma dole ruwan ya zamana maciji ya sha daga
gare shi. Sannan ya daura igiya a kafarsa ya
zamana kansa na kallon kasa zuwa wani lokaci.
Idan ya aikata hakan watakila zai tsira da
ransa."

Da ta ji haka sai ta yi tagumi tana cewa,
"wannan magani akwai wahalar samu, kai ba
ma zai yiwu ba." Ta d'aga hannu sama tana
rok'on Allah ta ce, "Ya Allah mai kulla soyayya,
mai bayarwa mai hanawa ka taimaki Qays
Majnun ya samu wannan magani." Ta shafa
sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce, "soyayya bata
da magani sai ita kanta."

Allah da ikonsa, Majnun na rataye da kafarsa a
sama ga kishirwa na addabarsa sai ya kwance
igiyar ya tafi neman ruwa. Bai samu ruwa ba sai
wani tsohon kasko a wani lungu. Ya tarar wani
zabgegen maciji na shan ruwan. Ya kore shi
sannan ya kafa kai ya shanye ruwan gaba daya.
Ya samu waje ya zauna yana wake - wakensa.

Da gari ya waye Laila ta shirya abinci mai rai da
lafiya ta kirawo kuyanga a boye ta fada mata
komai sannan ta nemi ta kai wa Majnun inda
yake a bayan gari. Kuma ta bata sakon a fada
masa cewar ita ma tana nan tana kaunarsa
kuma tana son ganinsa, amma da zarar ta samu
dama zata zo ta ganshi. Yayin da kuyanga ta je
wajen sai ta tarar da mutane biyu. Daya ya hada
kai da gwiwa kuma duk ya rame ga kansa nan
duguzunzum, dayan kuma mai kiba jawur da shi,
sai dai ya manyanta. Kuyangar ta dube su duka
biyun ta ga babu wanda ya cancanci Laila ta so
shi. Ita kanta ma ta ji duk basu kwanta mata a
rai ba, balle kuma Laila. Duk da haka domin cika
umarni sai ta ce, "a cikinku waye Majnun?" Mai
kibar ne kadai ya ji sai ya taso wajenta ya ce,
"me ya faru?" Sai ta nuna kwandon abinci ta ce,
"cewa aka yi na kawo masa wannan daga
Laila." Nan da nan ya karbe abincin yana cewa
"ni ne Majnun." Ta fada masa sakon Laila ya yi
mata dan wasa haka sannan ya sa abinci a
gaba ya cinye. Ya ragewa Majnun dan kadan.
Daga wannan rana kullum sai ta kawo masa
abinci da sakon baka, shi kuma sai ya cinye ya
rage kadan domin Majnun. Kullum Laila kan
tambayi kuyanga, "me ya ce ki fada min?" Sai
kuyanga ta ce, "wai ya gode madalla da abinci."
Laila ta shiga kokwanto anya kuwa Majnun
dinta ne? Bayan kwana uku dai da ta gaji sai ta
ce da kuyanga, "yaya kika ga kamannin Majnun
din?" Kuyanga ta ce, "wani mai kiba yana da
saje da kasumba...ya manyanta..."

Farat Laila ta ce, "wallahi ba shi ba ne, wannan
jakada ne wanda ya kawo min sakonsa. Majnun
ba tsoho ba ne kuma ba shi da kiba." Ta dubi
kuyanga ta ce, "su nawa ne a wurin?" Kuyanga
ta ce, "su biyu ne." Laila ta yi ajiyar zuciya ta ce,
"to yau ba za a kai abinci ba, amma zan sa ki
musu wata jarrabawa domin mu gane Majnun na
gaskiya." Ta bata wuka ta fad'a mata abin da
zata yi da ita.
Kuyanga ta tafi wajensu Majnun, ta tarar da
jakada na tsaye yana jiranta. Tana zuwa ya
soma yi mata sannu da zuwa. Ya mika hannu
da nufin ya karbi gara, maimako haka sai ya ga
ta fito da wata sharbebiyar wuka. Ta ce, "Laila
bata da lafiya, ana bukatar jinin masoyinta
kwalba daya wanda da shi za a hada maganin.

Shi yasa na zo wajenka na diba." Yana ganin
haka sai jikinsa ya kama rawa ya ce, "to ni dai
ba masoyinta ba ne, kuma ba ni ne Majnun ba,
gashi can a zaune." Ta wuce zuwa wajen
Majnun ta fada masa kamar yadda ta fada wa
Jakada. Yana jin haka ya karbi wukar da
hanzari, ya sumbace ta sannan ya ce, "na gode
wa Allah da ya kaddara cewa jinina ne zai
warkar da ciwon masoyiyata." Ya darzaza
wukar a hannunsa.

ZAMU GABA INSHA ALLAHU^•^LAILA MAJNUN...4^•^

Maimakon jini ya zubo sai wajen kurum ya yai
farat fat, alamar babu jini. Ya sake keta wani
wajen, nan ma babu jinin saboda bai ci abinci ba
ballantana a samu abin da ake buk'ata. Da ya
ga haka sai ya soka wukar a hamatarsa inda
babbar jijiyar jini take, nan jinin ya rika kwarara.
Ya tara ya mik'awa kuyangar wadda tuni tsoro
da mamaki sun hana ta motsi. Yayin da ta
koma gida ta shaida wa Laila irin abin mamakin
da ta gani wajen Majnun, sai Laila ta yi ta kuka
tana tausaya masa.
A cikin gari kuwa, labarin Majnun ya cika gari,
sai aka samu wasu shakiyan matasa suka
dauko kulake suka nufi inda yake. Tun daga
nesa da Jakada ya hango su sai ya hau
taguwarsa ya sulale ya bar Majnun yana wake -
wakensa yadda ya saba. Matasan na zuwa suka
hau bugunsa suna shuri da naushi da yakushi.
Suka daure shi da igiya sannan suka tsaya daga
nesa suna jifarsa. Da Laila ta ji labari sai ta
sheko da gudu ta zo ta kare shi daga bugun
mutane, ta rika zaginsu tana korarsu. Shi kuwa
duk da yana daure ga bugu da ya sha amma sai
ya ji ransa ya yi fari fat da ganin abar begensa
ya rika ambaton sunanta yana cewa:
Laila, Laila, Laila tawa ce,
Domin akanki ne na haukace,
Wasu na kallona wai na karkace,
To amma fa yau na samu dace,
Da ganin haskenki ya masoyiya
Iyayen Laila suka turo aka tafi da ita gida tana
kuka. Da suka ga lamarin ya wuce saninsu sai
suka yi shirin yin balaguro na wani lokacin.
Domin a tsammaninsu idan suka tafo suka jima
Majnun zai gaji da nemanta har ya saduda ya
hakura. Suka shirya kaya suka tafi wani gari da
basu ambata ba, gudun kada ya ji ya bi su can.
To amma kafin su tashi Laila ta rubuta takarda
a boye ta ba wa kuyangarta ta kaiwa Majnun.
Ya bude ya karanta cewar
Masoyina, bulaguro za mu yi wani gari mai nisa,
haduwar mu zata yi wuya anan. Idan zaka iya
mu hadu a zangon farko cikin sahara. Yana
gama karantawa ya ce da kuyangar, "ki gaishe
ta da kyau da kyau, kuma ki fada mata cewar
ina nan tafe."

Lokacin da su Laila suka sauka a zangon farko
ta tafi ita da kuyangarta zuwa inda ta ce masa
ya je zata same shi. A tsammaninta bai isa ya
zo wurin ba a wannan lokacin, domin su a abin
hawa suke, shi kuwa a kasa yake. Tana zuwa ta
same shi ya hada kai da gwiwa yana ta kiran
sunanta, "Laila! Ya Laila!! Ya Laila!!!" Ta karaso
wurinsa tana mai cewa, "Ya Majnunun Soyayya
ga Lailarka ta iso!!l duwatsun kusa da na nesa
suka dauki muryarta tana amo. Nan da nan ya
zabura zuwa gare ta, yana mai cewa, "shin da
gaske ne Laila ke ce anan?" Ta amsa "ni ce!" Ya
mika mata hannu ta rike sai suka ji kururuwar
mahaifanta suna nemanta domin a cigaba da
tafiya. Ta juya da hanzari, ya ce, "Haba Laila
kada ki tafi ki bar ni da begenki!" Ta ce, "kar ka
damu, idan na dawo za mu hadu anan."

"Yaushe za ki dawo?" Ya tambaye ta.
Ta ce, "ban san lokacin ba, amma da zarar mun
taho zan aika maka." Da haka ta tafi ta bar shi
anan. Majnun ya ce a ransa, "idan ta dawo wa
zata aika ya fada min? A ina dan sakon zai
same ni? Kawai bari na zauna anan din har sai
ta dawo." Ya share wuri ya zauna ba shi da
wani abinci sai ganyen bishiyar da ke wajen
yana shan ruwa dake bubbugowa karkashin
dutse. A kullum zancensa shine kiran sunan
Laila da addu'ar ta dawo ta same shi. A haka
har tsiron bishiya ya fito daga 'ya'yan itacen da
yake jefarwa, ganyenta ya nannade masa jiki ya
zama tamkar bishiyar a jikinsa ta tsiro.
A can garin da su iyayen Laila suka je da ita
kuwa, sai wani attajiri ya fito yana sonta da
aure. Nan take ya bawa iyayen rakumma dari
gami da wasu kyautuka masu yawa. Da Laila ta
ga alamar laila za a aurar da ita gare shi sai
ciwo ya kama ta. Ta yi ta fama, iyayen suka yi
nufin komawa gida domin magani alabarshi idan
ta warware sai a yi auren. A hanyar su ta
dawowa suka sauka a wannan zangon. Duk da
tana fama da jinya Laila ta taso zuwa wurin da
suka yi alkawari da Majnun. Ta kusa isa kenan
ta gamu da wani mutum ya ce mata, "yarinya
kada ki je wurin nan da kika nufa. Akwai wata
fatalwa mai kamar bishiya da ta bayyana.

Kullum tana kiran sunan Laila, Laila." Da ta ji
haka sai ta tabbatar Majnun ne bai tafi ba. Ta
karasa wurin da gudu. Yana ganinta yayi
zumbur ya mike tsaye yana mai farin ciki, yana
cewa "Laila kin cika alkawari? Laila ke ce kuwa?
Laila za ki aure ni??" Kasancewar ya jima sosai
a zaune baya mikewa sai jiri ya debe shi, a
lokaci guda kuma zuciyarsa ta buga saboda
tsanannin farin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment