Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mambela ya kaiga sonta da kula dakai bai kaiga yadda ka kula da rayuwar kaltum ba itama ta sani kowa anan ya sani ba kaltum kadaiba koni danazo a baya bayan nan kayimin halacci da ko dangina ba aminba nida mijina Abba babu irin addu ar da bama maka, saita fashe da kuka.
malam saleh yace alh mudai kai muka sani, kai muka bawa babu kyau mayarda hannun kyauta baya, yanzu mudai ba mu san da wannan saurayin nata ba, ko baxa ka aureta ba bazan bashi ba tunda ban san asalinsa ba, ba yarenmu daya ba kuma ba kasarmu daya ba....
alh Adnan yayi caraf yace amma addininku daya ko?
mambela mutum ne mai nitsuwa wanda yasan ya kamata, mai amana da tsoron Allah na yaba da halayyarsa kuma na yarda yana son kaltum zai riketa amana ko bayan ranmu.
sai kowa ya zubawa alh Adnan ido suna duban sa duba na rashin fahimta ko basu furta ba tambayarda suke jerowa azuciyoyinsu bai wuce kai ina kasan mambela da har ka shaida shi da irin wadannan kyawawan halaye?
alh adnan yayi murmushi ya dubesu daya baya daya yace zaku tambaya ina nasan mambela da har na shaideshi?
to ba almara bace kuma bana duba amma zan iya rantse muku da Allah duk halayyan nan dana zayyano muku mambela ya hadasu dukka.
kaltum tayi ajiyar zuci yayinda kwakwalwarta ta kasa tantance abunda alh Adnan yake nupi ta tambayi zuciyarta shin ko Madina ce ta bashi tarihin mambela?
sai Madina tace alh abunda kake fada akwai daure kai don kaltum ta baka labarin abun alkhairinda yayi mata shine ka gama tantancewa har ka shaideshi?
ko kuwa alh Sa'adu ne ya fada maka haka?
alh Adnan ya girgizai ya kwashe da dariya yace ga kaltum nan zaune ki tambayeta nida ita mun taba zama munyi labarin mambela?
tun a waya da ta ambaci sunansa bata sake ambatonsa ba a gaba na ba, haka Sa'adu babu wanda yaki jini irin mambela sbd har hanci ya fasa masa a garin kwato kaltum suka yi dambe har yau zaginsa yakeyi yace sanda yaje dauko Madina ma sun hadu ko kallon juna basu ba don haka zancen ko wani ne yabani labarin ma ki cire.
ni na san mambela kuma na zauna dashi har tsawon shekara uku ina ta gwada shi a bangarori daban daban kuma yaci jarabawata kuma ya cancanci ya auri kaltum .
Sai sofi da malam saleh suka daura hannu akai suna ambaton InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un.
yayinda kaltum taji maganar alh Adnan tamkar almara ko kuma mafarki ta rasa dalilin dayasa taji zuciyarta ta kamu da farin ciki Mai tsanani ta tsunkuyar da kanta kasa tana jinjina hikimar ubangiji tana mai gaskata
addu ah bata faduwa kasa komin daren dadewa Allah Ya na amsa addu ar bayin Sa duk abunda suka rokeShi, ta kagu taji karshen labarin.
madina ta tambaya cike da mamaki alhaji ina ka hadu da mambela?
kaje bur sudan ne?
alh Adnan yayi murmushi yace ko sudan air port din nan ban taba hawa ba balle in yada zango a airport din Khartoum tunda nake a rayuwata amma saiga Allah Ya hada ni da mambela tun bayan dawowar kaltum da wata
guda,
membela ya kirani a waya kasancewar bayajin turanci balle hausa sai malam Abdulkadir yayimin magana da hausa.
kaltum tasan malam Abdulkadir din, malaminda ya basu masauki a Khartoum wajensa mambela yaje ya karbi lambata saboda a ranarda nakira sa'adu ya bani malam shima munyi magana daga baya malam din ya kira ni da lambarsa nima nakirashi to bai goge lambar ba yana da ita, mambela yayi masa bayani shima kuma yayin min bayanin komai game da soyayyarsa da kaltum ban dauki abunda muhimmanci ba a nan na bar zancen, saida aka kwana biyu mambela ya sake kirana wannan karon kuma abokinsa ya bawa waya mukayi magana donshi yanajin turanci, sake rokona sukayi wai in ba shi izini yazo ya auri kaltum, amsar da na basu shine ai kaltum ba yar tsana bace, na kashe wayata na sharesu mambela dai bai daina kira ba wani lokaci in fahimci larabcin da yakeyi nima in gwamutsa
masa nawa ya fahimce abunda ya tsinta bayani dai dayane kaltum ta dawo gida bata koma garin ADON DAWA ba, yar makarantane bazata auri wanda bashida ilimba, kunsan saboda maganarnan dana fada masa ya bazama burni neman lesson teacher da zai koya masa turanci, anyi watanni da dama banji mambela ba sai gashi ranar ya kirani yana magana da turanci duk da bai kwareba amma zaka fahimce shi yace min ya shiga makaranta saboda kaltum don na yarje mishi ya aureta, saina fara gaskata soyayyarnan dayake ikirarin yana yiwa kaltum, don haka saina tambayeshi meyakeso yanzu?
Yace min so yake abashi izini yazo da iyayensa Nigeria su nemi auren kaltum.
sai nace masa a a kada yazo da iyayen sa yazo shi kadai tukunna, nayi masa hakane don na kure shi naga ko bazai zo ba sai kwasam najishi a waya yana tambayana adireshina na Abuja, bayan kwanaki biyu da yin wayarsu saiga mambela dan ADON DAWA a ofishina an rakoshi.
Madina tayi kabbara gami da cewa Allah mai iko Allah mai hada soyayya, yanzu mambela sai daya zo Nigeria saboda kaltum?
ashe bai hakura ba?
malam saleh ya gyara zama yana sauraron irin wannan abun al ajabi yayinda sofi ma ta buga tagumi tana sauraro, Abba ma yakura wa alh Adnan idanu yana kallon hikima da dabaru irin na mai ilimin da yake amfani da iliminsa,
kaltum ta dade da bude duk wata hudarda dake jikinta tana sauraron labarin, ta kasa tantance karshen abun da zai faru taji ta sake son mambela ta sake girmama alh Adnan tabbas ko baban ta daya tsuguna ya haifeta ba zaiyimata irin wannan kiwon da tattalin ba irin yadda a alh Adnan ya damu da rayuwar ta ba.
saiyaci gaba da cewa sai gani ga membela mun hadu muna kallon kallo ko kadan bantaba zaton haka membela yake ba, wayayyen mutum natsattse mai ilimin addini shine babban abunda yasa na fara sauraronsa nan bayan nabashi abinci da ruwa ya huta saina shiga yi masa tambayoyi game da tarihin rayuwarsa banajin ya boye mini komai, ya bayyana min koshi wanene da turanci duk muke magana saidai idan turancin ya kakare ya mako larabci duk ina fahimtarsa, yayi labarinsa ya gama sannan nace meyasa ya tsallake duk yammatan sudan kyawawa ya makalewa kaltum?
saiyace ba ruwansa da kyau ko kudi shi dai yana son kaltum don Allah sai kuma halayyarta ta gari da nutsuwa yasa yaji baya son kowa sai ita, zai kuma dauwama cikin damuwa idan bai auri kaltum ba yayi kokarin rabuwa da ita
tunda ta tafi zuciyarsa ta kasa daurewa ya
shaidamin a shirye yake wajen yin duk abunda aka umurce shi don ya sami kaltum, na zayyano masa dokoki masu yawa kuma masu tsauri da wahala sai ya amsa da cewa zaiyi duk abunda na umurce shi, sharadi dayane baiji dadinsa ba danace bazaiga kaltum ba har sai an shekara uku cur saiya gama cika duk rukunnan dana gindaya masa kuma sai kaltum ta gama makaranta sannan zasu hadu.
ya rokeni da nabarshi ya ganta ko sau dayane, nace mai ai kaltum bata garin nan tana kano garin kano kuwa da nisa daga Abuja, don sai an hau jirgi kafin aje.
Abba ya gyara zama yayi murmushi yace alh wanne irin sharuda ka gindaya masa haka?
alh adnan yayi dari ya yace ce masa nayi idan ya auri kaltum a ina zai ajiye ta?
saiyace a Khartoum zai ajeyeta bazai kaita kauyen su ba saboda suna da gidaje a burni,
sainace a'a bazan bar kaltum ta zauna a Khartoum ba saidai idanshi zai dawo Nigeria ya zauna,
Sai yace min iyayen sa bazasu yarda ba amma in bashi dama yaje ya gina rayuwarsa a dubai saboda yanzu abunda yan kasarsu suke yi kenan, kawunsa ma yana dubai ya ginu yayi kudi yana kasuwanci ta jirgin ruwa yake tura kaya sudan dama yanada sha'awar yin hakan, don haka yakeso ya sayar da gidanjensu guda biyu a Khartoum ya ja Jari, iyayensa bazasu hana shi ba.
nace yaje dai ya shawarci iyayensa idan sun amince yazo zan hada shi da abokan ciniki na na gari wadanda zasu saka shi a harkar kasuwancinsu a can dubai din, na shaida masa nima ina kasuwanci a dubai harma na mallaki gida a dubai a jamaira so nake d'ana Mashkur ya kammala karatunsa a London ya dawo dubai ya kula da harkokina na can, sai mambela yayi murna ya kwana bakwai tare dani a Abuja, hotel na kama masa duk yamma ina daukarsa in zagaya dashi gari har yake sha awar kasarmu yana cewa ashe Nigeria kasace mai kyau haka mai dimbin arziki amma mutanen kasarnan suke zuwa sudan suna bara ana korarsu suna kin tafiya tamkar karnuka?
nace masa mutuwar zuciyane kawai da rashin hakuri da kaddara, munada arziki akasarmu rashin shugabanni na garine babbar matsalarmu a kasar.
membela ya koma kasarsu bayan watanni naga ya kira ni da lambar dubai ya shaidamin ya dawo dubai harya fara kokarin gina sabuwar rayuwar sa, na sake shawartarsa daya nemi ilimin boko don bashida ilimin boko, ya shiga wata makaranta mai kama da diploma kuma yaki da jahilci ce amma zaka fita da satifiket dinda za a iya baka aiki, abur Dubai makarantar take ana koyarda turanci da larabci, lissafi dakuma kompita tamkar yanda ake koyawa yara yan aji daya kuma da karfe shida na yammah zuwa karfe takwas na dare ake zuwa aji, don haka tundaga safe har yammah mambela yana kasuwancinsa, karatun na wata shida ne kacal saidai in dai kanaso kaci gaba akwai makarantar da zaka shekara kanayi ita ma satifiket da za a baka, ya kirani a waya ya shawarceni cewar ya gama wannan makarantar yanaso yaci gaba da karatu nace yaje ya shiga ya shiga yaci gaba da karatu na shawarceshi ya shiga makarantar koyar tuki dake quasis don y huta da zirga zirgan hawan bus daga ajman garinda yake zaune zuwa bur dubai inda makarantar take idan yaje ya tafi makarantar koyan boko, saida ya shekara cur a dubai sannan naje dubai na yi masa shigar ba zata awajen container inda ake lodi na iskeshi ya tube yana loda kaya har abin tausayi, muka gaisa naje har gidan da yake zaune shi da yan kasarsu nayi masa kyautar bata taka kara ta karya ba na taho abuna.
mambela yake fadamin a hira cewar yasha yi min zargin ni mugu ne banida tausayi na rabashi da iyayensa na kawoshi yana wahala kuma dakyar in zan yarda ya auri kaltum yaudararsa kawai nake yi sai daga baya ya fara ganin alfanun abun, daman masu iya magana na cewa bayan wuya sai dadi, dai dai
sanda ya gama makarantar koyan tukin moto ya sami driving liences abune mai matukar wahalar samu a dubai daga nan sai ya sayi moto wacce ba abune mai tsada ba a kasar sannan ya sami sakamakon babbar diploma,
da sakamako mai kyawun gaske yadda zai iya samun aiki a dubai sannan ya kware wajen magana da turanci da iya rubutu da turanci, ya iya amfani da computer.
sannu ahankali saiga mambela ya goge a dubai yasan komai ya sami alkhairai masu yawa harta kai ta kawo shima yana da yaranda suke yi masa aiki suke samun alkhairi a wajensa.
ya shekara yana aiki a wata ma'aikata da take garin NASIR KAIMA daga baya ya daina da yaga kasuwancin yafi ci, sunata tura kaya daga Dubai zuwa sudan nan danan ake juyewa a hada masa kudinsa, koda yaushe mambela yana tuntuba ta awaya yana shaidamin duk irin cigabanda ya samu nikuma sainayi masa addu ar fatan alkhairi. naje dubai naga canjin da ya samu a rayuwarsa yayi min hidima tamkar yanda ake karrama gwamna ko shugaban kasa haka shida abokansa da kawunsa sukayi min, bayan abubuwan arziki da suka hadamin nida kaltum nace suyi hkr bazan iya daukar abunda suka bani ba nagode na taho na bar musu kayansu duk da basuji dadi ba dole ce tasa don babu inda zankai himilin kayan nan tunda ni kadai nake abuna kaltum bata sani ba, a wani bangaren kuma nasa malam Abdulkadir na Khartoum yaje ya binciko min asalin mambela, su waye iyayen sa, yaya rikon addininsu yake.
ya kira ni bayan ya gama binciko min asalin mambela dan asaline karewama su suke rikeda sarautar garin su ba boyayyu bane kowa ya sansu kuma gidansu gidan malamai ne masu riken addini ne.
da lokaci ya cika na gama tabbatarwa da abunda nake so in tabbatar gameda mambela sai na umurce shi yazo Abuja yasameni muyi magana.
abangaren kaltum na binciketa kuma nasa kaninta ya taya ni bincike muka tabbatar har yanzu tanason mambela idan ta kebe ita kadai tana koke koke tana yawan saka hoton mambela a gaba tana kallonsa, Abdul ya shaida min ni ma kuma na lura da haka na dai amsa muku ne kawai zan auri kaltum amma ni a zuciyata nasan wanda ya dace da ita, aikina shine in tabbatar mun aura mata miji na gari wanda zai riketa amana ko babu idanun mu.
.
ADON DAWA 48
.
TRUE LIFE STORY
.
na dai amsa muku ne kawai zan auri kaltum amma ni a zuciyata nasan wanda ya dace da ita, aikina shine in tabbatar mun aura mata miji na gari wanda zai riketa amana ko babu idanun mu.
AlhamduLillah na cika alkawari dana dauka, na cika amanarda na kudira a raina zancika shine na aurar kaltum ga mutumin da ya dace wanda zai riketa amana ta dauwama a cikin farin ciki, mambela ya dace da ita da kyakkyawan zato zai rike ta amana in shaa Allah,
Allah sarki alh mungode Allah Ya biyaka, kanuna mana kauna, sofi ce ke fada yayinda take zubarda hawayen farin ciki kaltum ma kukan takeyi ta rasa kalmar da zata yi amfani da ita wajen godewa wannan bawan Allah.
madina ta dubi Abba tace kaji wata hikima ta ubangiji ko?
Allah sarki rayuwa ashe akwai mutane masu koyi da hali irin na sahabbai irinka alh ?
Alh Adnan yayi murmushi yace bancika son kuna godemin ba nayi ne don Allah ina neman sakayyah awajenSa duniya da lahira, ku saurareni zan shiga daki na fito, saiya miki ya tashi ya shiga dakin sa.
kaltum ta rugo tazo ta rungume Madina tasa kuka, Madina ta shafa kanta tana ta bata baki sai kuwa sukaji motsin fitowar alh Adnan suka daga ido su dukka suka dube shi sai suka ga su biyu shida mambela, idanuwan mambela akan sofi yanata kallonta domin yaga sunyi kamada kaltum sosai kamar daga sama yaji kaltum ta kwalla kiran sunansa yah mambela!!
ya waigo da sauri sai yaga abar kaunarsa kaltum saiyaji ya gigice gaba daya saboda ta goge tayi kyau kamar ba kaltum dinda ya sani ada ba yaji tamkar ya sureta ya cafe saiya daure ya koma gefenta ya zauna cike da farin ciki, cikin harshen larabci yace kaltum daman ina da rabon in ganki a rayuwa ta?
AlhamduLillahi ko bazan aureki ba na godewa Allah da Ya nuna min ke a rayuwata kafin in mutu, sai hawayen farin ciki ya surnano daga idanuwansu dukka biyun.
madina ta ambaci sunansa cikeda farin ciki sai ya juya da sauri ya dubeta sai yanzu ya shaida Madina ce, itama ta canja ta goge kamar ba ita ba sai mamaki mai dimbin yawa ya rufeshi ya fada cikin yarensa na ADON DAWA a ah yaya naganku kunzama tamkar larabawa dama kunfi jin dadin a kasarku kukaje kasarmu kuke wahala?
dubi yanda kuka zama fa?
kaltum da Madina sai dariya sukeyi kawai donsu kadai sukeji abunda yake fada.
Madina cikin harshen turanci ta gabatar masa da Abba, mambela ya mika masa hannu suka gaisa cikin harshen turanci yace Abba na dade inajin labarinka ashe baka rasu ba?
Madina ta gabatar masa da saleh da sofi cewar ga iyayen kaltum, da taga mambela na kokarin mika masa hannu sai tayi masa larabci tace ya durgusa ya gaishesu al'adarmu ba a hannu da surukai don haka mambela yaje gabansu ya durgusa ya gaishesu da larabci suka amsa da hausa ya dawo ya zauna a kasan kafet kusa da abar kaunarsa kaltum,
alh Adnan yayiwa mambela bayani cewar ya fada musu komai kuma in shaa Allahu babu matsala komai zai dai daita yanzu abunda ya rage shine idan ya koma kasarsu ya taho da iyayensa mata da maza da duk kayanda akeyi na al adarmu ta hausa wajen nemar aure,
mambela ya tambayeshi me ake bukata a auren hausawa?
alh ya nuna kaltum yace ga amarya ka tambayeta ta yadda akeyin komai amma kafin atashi daga wannan zaman inaso inbawa iyayen kaltum dama ko suna da abun fada ko korafi ko suka gameda hukuncinda na yanke saboda kunada hakki akan yarku, wlh duk abunda baiyi muku ba ku fada zan cenza ra ayina kuma bazan damu ba.
saleh ya girgiza kai yace ko da wasa baka taba zartar da hukunci akan kaltum wanda zai zama ba dai dai ba ko wanda zata yi nadama daga baya ba, ka fimu ilmi kafimu tunani kafi mu kula da rayuwar yar nan sunan mun haifeta ne kawai babu wata matsala wallahi fatanmu Allah Ya bada zaman lafiya kaikuma Allah Ya saka maka da alkhairi,
sofi ma irin wannan addu ar ta dinga zazzago masa,
Abba da Madina ma sunyi masa addu'a da godiya a bisa kyakyawar niyyarsa.
kaltum ta durgusa a gabansa tayi masa godiya haka ma mambela sannan ya umurci kowa ya tafi sai da safe kuma,
suka duguma su dukka suka fita daga falon,
alh Adnan kadai aka bari a zaune fuskarsa cike da fara a da alama yafi kowa farin ciki da Allah Ya nuna masa ranar daya cikawa kaltum burinta.
Madina da Abba suka raka har motarsu suka shiga suka tafi sannan sofi da saleh ma suka shiga gida,
mambela da kaltum ne a zaune akan kujera a farfajiyar gidan suna rera hirar yaushe gamo hirar so da kauna suna masu godewa Allah daya sake hadasu badon sunaso ba sai don dare yayi sukayi sallama kaltum ta shiga gida mambela ma ya shiga gida, alh adnan dama ya nuna masa dakinda zai kwana anan ya ajiye akwatinsa tun sanda sukazo yadda bacci ya gagari idanuwan mambela haka ya gagari kaltum juyi kawai sukeyi suna tunanin juna yayinda farin ciki yayi musu katutu a zukatansu kamar wadanda suka hada baki a alokaci guda suka ayyana aransu tunda bacci ya gagara gara su tashi suyi alwala suyi sallah su godewa Allah dayayi musu wannan
babbar kyauta.
Madina ma da Abba suna can a gidansu sun raba dare suna hirar wannan abun al'ajabi ashe sofi ma da saleh farin ciki ne ya hanasu
barci suma suna daga daki suna tattaunawa sai dai duk rabin hirar tasu addu a ce suke jerowa alh Adnan suna yi masa fatan Allah Ya biya shi da gidan aljannah.
daya bangaren kuwa alh Adnan ne kwance kan gadonsa ya takure yayinda kuka ya kece masa yana addu ar Allah Ya kara masa dangana da juriya rabuwa da kaltum domin yana sonta har cikin ransa kuma yayi niyyar auranta saidai ya fuskanci zai tauye mata rayuwa saboda akwai wanda takeso bashi ba don haka ya sadaukar da son da yake mata ya bata wanda takeso donta sami nutsuwa arayuwarta shiya yarda da duk wani tsanani da zai shiga na sanadiyar rabuwa da ita,
juyi kawai yakeyi yayinda zuciyarshi ke tafarfasa don tsananin tashin hankali da yake addabarsa, yana kiran InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah Ka yayemin abunda nakeji kada in dauwama dason kaltum a raina har gara in mutu da in dauwama cikin wannan hali ,
ahankali yaji zuciyarsa na sanyi saiyayi wuf ya tashi ya shiga bandaki yayi alwala yazo ya kwana yana sallah yana neman hakurin dangana da neman sauyi mafi alkhairi,
washe gari da safe sofi da kaltum suka dinga hidimar dafe dafen abinci kala kala don su bawa bakonsu, sun san halin alh Adnan ba cin abincin safe yakeyi ba kofin shayi dayane zaisha saikuma da rana ko sun kai sunsan bazai ci ba saidai mambela.
kannen kaltum ne suke jerawa kan daning table dinda ke falon alh Adnan yayinda alh Adnan da mambela suke zazzaune a falon suna tattaunawa da alama alh Adnan shiryo tafiya zaiyi harda yar jakar kayansa a gefensa, ya umurci mambela daya cigaba da zama a gidan kamar na sati biyu ko uku Madina ta zayyano masa komai sai ya tafi ya shirya suyi waya su fadi ranar da zasu zo sai a buga katin gayyata anan a rarraba suna zuwa sai a daura aure ayi biki gaba daya.
farin ciki ya rufe mambela ya rumgume alh Adnan yayi godiya suka dungumo suka fito zuwa bangaren su kaltum.
sofi da saleh suka fito da sauri suka durgusa suka gaishe shi, alh har zaka koma Abuja da sassafe haka ko karyawa bakayi ba?
sofi ta tambaya cike da kulawa,
alh adnan yayi dariya yace ai yau akwai aiki saboda mambela nazo amma zan barshi anan ya zauna har sawon sati biyu ku saba sosai kuma ya gana da amaryarsa sannan sai ya tafi daga nan basai yaje Abuja ba idan ya shiryo sai yazo da iyayensa a daura aure ayi biki akai ta dubai shi kenan, yasaka hannu a aljihu ya damko kudi ya ambulowa saleh a hannunsa yace ka rike wannan saboda cefene ya karu adinga dafawa mambela abinci mai kyau kuma kala kala ina kaltum din ne?
kaltum tayi wuf tafito daga daki sanye da hijabi tazo ta durgusa ta gaishe shi yayi dariya yace kin iya abincin zamani kuwa kosai tuwo irin na sofi?
donshi shi tafi kwarewa kullum kaga sofi to muciya ce ahannunta tana tuki ba a yin soye soye mijin kuma dan gayu ne ya saba da snacks da shawarma, kazar kfc, mr biggs, mcbanas, pizza a dubai ba ya cin tuwo idan baki iya ba kije Madina ta koya miki tun wuri nasan ita ta iya.
kaltum da iyayenta suka tunzure da dariya yayinda mambela yake tsaye yana kallon bakinsu ba tare da yasan abunda suke fada ba cikin harshen hausa, yaji yanaso ya koyi yaren hausa domin yanajin dadin sauraronsa tun ba yanzu ba.
daga yadda alh Adnan ya fuskanci mambela yana yawan kallon kaltum ya tabbatar yana sonta matuka har kamar zai hadiyeta, zuciyar sa na ayyane ayyane sai alh Adnan yaji kishi ya turnuke shi babu yadda zai yine kawai yaga kaltum ta kara kyau dariyarta ta zame masa lu'u lu'u a idanunwansa sai ya dinga karanta a'uzubiLlah minal shaidanir rajim kuma ya gaggauta barin wajen, da mambela ya rakashi mota sai alh adnan ya damko kudi ya bashi yace ya sayi duk abunda yake sha'awa, da farko mambela yaki karba yace yana da kudin Nigeria daya canza kuma yana da dalar.
alh Adnan yace saiya karba dole don haka mambela ya karba yayi godiya,
alh adnan yaja mota ya tafi yayinda hawaye mai radadi ya dinga fita daya bayan daya har saida ya ji turnukukin da yake damunsa ya ragu saboda karatun kur'ani daya kure a rediyon motarsa, addu'ace maganin masifa
haka hakuri maganin zaman duniya ya isa gida kuma ya iske matarsa na jiransa domin sai yanzu yan gulma suka kawo mata labarin aurensa da kaltum ta ayyana a ranta tafiyarda ya tarka da tsakar rana zancen auren yaje don haka tace ya zaba ko ita ko kaltum don bazata zauna da kaltum a matsayin kishiyarta ba.
saiyaji ya kasa magana kallonta kawai ya zauna yanayi saboda babu ciwon da yafi aibu irin jahilci ya yarda jahilcine ke damun salaha
kamata yayi ta tambayeshi gaskiyar magana tunda bayayi mata karya ai zai fada mata gaskiya saita yarda da gulmarda yan gari suka fada mata ta zartar da hukunci yasan hankalin mata tunanin su ragagge ne a matsayinsa na namiji sai bai kula ta ba tayi ta fadanta harta gaji ta daina.
kaltum da mambela sun kasance koda yaushe suna zama tare a kan wasu fararen kujeru a farfajiyar gidan sallah da cin abinci ne kadai yake tashinsu hira kawai suke yi cike da farin ciki marar misaltuwa idan dare
yayi kowa ya shiga barci sai su dinga magana a waya har assalatu sannan su tashi suyi wanka suci ado su fito su kafa kujera su zauna hira.
sofi da saleh suna ganin ikon Allah yarinya ta iya hira rairairai duk da larabci suke yi basa fahimtar abunda suke fada amma suna ganin murmushi da kashe ido da muryar da takeyiwa masoyinta ko ba a fada musu ba sun san sai yanzu kaltum ta sami wanda takeso wanda take ganin ya dace da rayuwar ta.
dan ladi direba ya zagaya

Please Login or Register in order to submit comment