Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kutsa ya shiga cikin gida, bayan yan sannu da dawowa sun iso suka kwashi tsaraba zuwa cikin gida wato kaltum da kannenta kenan daga yanda alhaji Adnan ya amsa mata da yadda ya kalleta ya watsar tasan ba haka ya saba yi mata ba, tabbas akwai dalili daga yanda malam saleh yaga yau alh Adnan baya fara'a yasan ba lafiya, don haka sai hankalin kowa ya tashi,
alh adnan yafito kofar gida batare dayayi bayani ba,
tabbas malam saleh ya zargi ko yan gulma ne suka fada masa cewar samari sunzo neman kaltum shekaran jiya.
alh Adnan yakarasa har jikin motar abba a inda ya iske shi a tsaye yayi masa sallama ya mika masa hannu suka gaisa,
alh Adnan ya dubi Abba yayi murmushin karfin hali yace kaltum kake nema ko?
daga ina yayi?
murmushi yace sunana barista Abba Tukur a unguwar yankaba nake .
alh Adnan ya kura masa ido yana dubansa can yayi ajiyar zuciya yace naji sunanka yaro sai kuma inji dalilin nemanta da kake yi, daman ka santane kokuma tasan da zuwanka?
abba yayi dariya domin yaji tambayoyin sunyi masa kama da tambayoyin da lauyoyi sukeyi wa mai laifi a kotu, ya ce kaltum tasanni amma batasan yau zanzoba nazo shekaranjiya mai gadinku ya hanata zo wajen mu dalilin zuwana bawani abu bane illa dai ina so tazama ido na ko ince itace fitilar da zata haskaka min hanya wajen neman allura cikin duhu.
alh Adnan ya dago da sauri ya dubi Abba yayinda ya caka masa mashin harara ya fada cike da gadara yaro ban fahimceka ba?
Abba ya girgizakai yakara yin wani siririn murmushi yace ranka dade karkadamu nazo neman alfarmane a wajen ku kanwarka kaltum ne tazo min da labarin ta baro matata a sudan tana can tana bara shine nake so tamin kwatance ko ta taimakamin ta rakani inda Madina take mu dauko ta don mu mun rasa inda take har mun zata ma ta mutu...
alh Adnan yakatseshi tunkafin yarufe bakinsa
cikin sakin fuska da dariya yake magana don ya fahinci abba ba zance yazo ba yace yi shiru yaro na fahince kana so kace min kaima matarka tana cikin yan gudun hijira ko ince masu tarar aradu da ka masu tafiya makka da kafa ko?
to sai dai mu musan abunyi domin kaltum bazata sake leka wa sudan ba da sunan takawaba ba balle rakiya, kai da kasan wahalarda nasha kafin akawo min ita ai da bazakace zaka nemi izinin rakiyarta ba, kaltum karatun jarabawane a gabanta banaso a dinga maganar sudan da ita saboda ina ganin alamun damuwa a tattare da ita idan aka ambaci sunan sudan don haka banaso ka sake sakata ma acikin maganan duk abunda kakeso ko kake nema ka nemeni nayi maka alkawari zan taimaka maka iya taimako saboda nasan yadda kake ji.
ba karamin tashin hankali bane ace an gano matarka ko yarka ko kanwarka awata kasa tana bara ba, sai sunyi bara sannan suci abinci mace musamman budurwa ai bala'in yayi bala i sai fatan Allah ya kiyaye gaba, yanzu dai ka rubuta numban wayata ka kirani gobe da safe muyi magana daga abuja nake yanzu nagaji,
sai godiya abba yakeyi ba iyaka yayinda farin ciki ya mamaye zuciyanshi yaji tamkar ance masa ga Madina nan adaki za a fito masa da ita, ya dauko waya alh Adnan yana karanto
masa yana rubutawa ya fada cike da ladabi wani suna zan saka?
alh adnan yayi murmushi yace ka rubuta kaltum Adnan.
Abba ya maimaita sunan kaltum Adnan...
alh Adnan yace karka damu ka rubuta haka sai kafi ganewa,
ya juya ya bar Abba a tsaye cike da mamaki yayinda yabishi da kallo har saida ya shige cikin gida zuciyarshi cike da tambayoyi shin wannan mutumin yaya yake da kaltum?
Gashi dai sunso suyi kama amma yace shi ba yayanta bane kuma baici ace babanta bane don shekarunsa baici ace ya haifeta ba ita ba matar aure bace bare kuma ace mijinta ne to ko kawunta ne ?
Amma da gatanta to meyasa suka bari ta tafi sudan ?
Gara ace Madina ace rashin gatane kodayake a labarin ta ta ambaci wata tsohuwace ta tafi da ita ta ambaci wani masoyinta abar kaunanta mambela don haka wannan ba mijinta bane koma dai wanene wannan yana sonta kuma yana kula da ita sosai tabbas yana tattalinta..
tunanin da abban Madina yake yi kenan a zuciyar sa har ya iso gida bai iya barci ba daga ya rufe ido sai yaga kamar Madina sai yayi sauri ya jawo hotonta yaga Madina ta lalace ta susuce ta fita hayyacinta idan yayi kuka saiyayi adduar Allah ya bayyana masa ita amma jikinsa yakanyi sanyi idan ya tuna Madina zata iya zuwa taci gaba da bujirewa aurensa.
bayan gari ya waye Abba waya yasa agaba yana kirga awannin yana jiran goma na safe yayi sannan yakira kaltum bayaso yadoka masa sanmako.
alokacinda agogon alh Adnan ya buga karfe goma da wayar Abba tare suka isa kunnuwansa alokacin da yake tautaunawa da mai gadinsa malam sale a katafaren falonsa ya dubi agogo ya juya ya dubi wayarsa baisan lambar ba dan haka bai damu da sai ya amsa ba yaci gaba da bayanansa amma wayan bata daina ruri ba da zarar ta gama saita kara daukar kururuwa dole tasa ya saka hannu ya amsa ko dai wanene tabbas bakone don duk wanda yasanshi yasan dokarsa ba ayi masa waya kafin karfe 12 rana, alh Adnan ya amsa
sallamar mai yi masa waya sai ya kasa kunne yana sauraronsa Abba ya fara da gabatar da kansa dakuma inda yake da alama har yanzu alh Adnan bai gane ko wanene ba daga yanda yake amsa masa Abba ya fahimci haka don haka sai ya bashi labarin yadda suka hadu jiya cewar mijin Madina da take sudan tareda kaltum sai yanxu ya fahimce shi don haka sai ya saki ransa suka gaisa cike da faraa,
cikin fargaba Abba ya tambaye shi yace alh kace yau inkira zaka bani shawara ka taimake ni alh in samo madina kamar yanda Allah Ya taimakeka ka tsinto kaltum.
alh Adnan yayi murmushi yace samari ka kwantar da hankalin ka zan taimakeka abu daya ne nace bazan iya yi maka ba shine daka roki alfarmar kaltum ta raka ka sudan wajen Madina, bazan barta ba saidai zan hadaka da wanda na sani acan su taimakeka.
Abba ya yi godiya sannan ya gyara zama yana sauraronsa yayinda farin ciki ya lullubeshi...
malam saleh yakara tura hula keya yaci gaba da durgushewa yana sauraron abunda bai taba sani ba arayuwarshi wato maganan kaltum da Madina, koda wasa kaltum bata taba basu labarin rayuwarta a sudan ba saigashi alh Adnan ya sani harma suna tattauna da wani akan haka.
alh Adnan yabawa Abba labarin yadda akayi aka kawo kaltum gida yayi masa alkawari zai tuntube alh saadu yaji yan da za ayi ya nemo musu Madina a bur sudan ayi ciniki ya fadi yanda za a biya shi, ya umurci Abba yakirashi da yamma don yaji yanda suka tattauna.
Abba yayi farin ciki matuka yanata godiya har suka kashe wayan malam saleh ya jinjina kai
yayi murmushi yace wata yar gudun hijira ce ake nema ?
Alh Adnan ya kyalkyale da dariya yace yar gudun hijira ne kawar kaltum,
malam saleh yayi dariya ya sake lankwashe kafa yace daddy amintar nan taka da kaltum sai Allah kaga harta fada maka labarin kawarta a sudan mukuwa agida bata taba bada labarin tasan wata asudan ba ko da wasa bata taba zancen sudan da wani acikin mu ba, ka santa da miskilanci dakai kadai take hira shine kwanaki muke tattaunawa da sofi muke cewa ga kaltum ta kusa gama sakandari a cikin watan nan zasu gama, samari har sun fara biyota ranan ma saida na fita na fatattaki wasu a kofar gida bana so taci gaba da karatu a gida gara tayi jami'a agidan mijinta idan mijin ya yarda, saboda dandazo gidan nan zai zama dan ma bata kulasu shine mukayi shawara da zaiyu kuma idan kanada ra'ayi da sai na damka maka kaltum duniya da lahira hankali na zaifi kwanciya babu wanda zata aura yafi kulawa da ita fiye da kai duk da dai madam saliha ta kufula yanzu in taji zatace cin amana ne amma ai bai haramta ba, Alh sunan mun haifi kaltum ne kawai amma kai ka rainata da wahalhalunta dukka da taimakon Allah da taimakonka ne kaltum ta zama mutum,
badan haka ba ai da tuni ko a kwabo ba wanda zai dauke ta, saboda a kauye ko a sudan ta dauwama tana bara tunda bamuda kudin da zamu dauko ta, banida abunda zan iya saka maka taimako da rufin asiri da kayi min nida zuriata aduniya bazai misaltu ba, don haka na dauki yarinyan nan sukutum na baka nasan duk da haka ban biyaka ba kuma har abada bazan iya biyanka ba, ranka ya dade a duba maganata sosai agani idan da yuwuwar yin hakan ayi idan kuma nayi kuskure a cikin maganata na bata maka rai ayi hakuri kasan zuciya da sake-sake ni da sofi ne muka shawarta haka.
alh Adnan dai yayi shiru kansa akasa baya murmushi haka bai bata fuska ba da alama dai yana sauraro kuma yana nazari.
malam saleh ya mike cike da tsoro yace alh na barka lafiya zan koma bakin get naji motsi,
alh Adnan ya bashi amsa da to madallah sai anjima,
daga dukkan alamu dukkansu biyun sun shiga halin tunani da sake-sake kala-kala acikin yinin wannan rana, don tun wannan lokacin alh Adnan bai tashi daga kan kujera dayake zaune ba har karfe daya da rabi na rana, motsin shigowar danladi direba ne dajin muryan kaltum ita ta katse masa tunaninda ya dulmuya aciki,
kaltum ta gaishe da mahaifinta sai ta juya ta dubi motar alh Adnan ta tambaye shi Abba daddy bai fita ba yana nan ?
Malam saleh ya amsa cike da farin ciki, yau bai fitoba yana falonsa ta juya da sauri ta nufi falon alh Adnan fuskarta cike da faraa bakinta cike da magana da alama wani labari ta kunso masa,
malam saleh yayi tsaye ya hada hannu yana mamaki mai hade da fargaba yana tsoron kada maganar da yayi wa alh Adnan dazu ta bata masa rai ya juya musu baya, taimako da fara ar da yake musu ya daina, kada kuma ya dauka turo kaltum sukayi da tsigar yaudara..
ta shiga falo shiga falon.
yanzu kada fa ya dauka kwadayin dukiyar sa suke yi shine suka kakaba masa 'ya?
zuciya da sake sake haka ya dinga sakawo malam saleh wadannan tambayoyi InnaLillahi wa inna i ailaihi raji'un kalmar da malam saleh ya fada kenan a bayyane yayinda ya dora hannu aka ya shiga dakin gadi ya kasa zama sai leke-leke yake ta jikin labule yana so ya gada wanne irin yanayi kaltum zata fito, da farin ciki koda bacin rai idan ya Koro ta, ya shiga zargin kansa da kansa me yasa ma ya furta wannan kalmar?
gashi zai raba zumunci musamman idan
saliha taji.
kaltum ta isa cikin falon da sauri gami da rada sallama yayinda suka yi kayi ido hudu sai kowannensu yayi murmushi ta karasa gabansa ta durgusa ta gaisheshi ya amsa cike da fara a gami da mamaki hade da zumudin jin abunda zata fada,
ta bude jakarta ta zaro wata doguwar takarda ta mika masa ta ce daddy yau math mukayi na fada maka daman nafi iya maths in shaa Allahu ''A'' zanci don na amsa dukka.
Yayi ajiyar zuciya ya lumshe ido gami da wani
laulausan murmushi ya amsa mata cikin tattausan murya, yayi kyau kaltum Allah Ya yi miki jagora nikuma nayi miki alkawari idan kinci jarrabawar ki sosai zankaiki duk inda kikeso kiyi karatu a fadin duniyar nan inhar kina so, zan saya miki duk abunda kikeso.
dadi ya lullube zuciyar kaltum ta rufe ido da tafukan hannayenta tayi godiya ta mike cike da murna, zata tafi kamar daga sama taji ya kira sunanta ta dawo da sauri ta tsuguna a gaban sa tana sauraron abunda zai fada,
ya dube ta yace kaltum wacece Madina?
waye kuma Abba?
saitaji kirjinta ya buga don fargaba sai hankalinta ya tashi, tayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa yayinda aka fara daukar dauki ba dadi tsakanin harshenta da labban bakinta, magana daya sak ta kasa fitowa daga bakinta ya sake maimaita mata tambayarsa
haryanzu ba ta sauya zani ba, amsa ta gagara sai kame-kame takeyi.
ya tsuke fuska yayi magana cikin kakkausar murya Yace zauna kaltum ki nitsu ki fahimce tambaya na kibani amsar gaskiya, inaso ki bani labarin, saboda in sani kafin inshiga maganar, bansan kida karya ba ada ban san ki da munafunci ba bakya boye min komai koda kin boyewa malam saleh da sofi, kada kiyimin karya don bana tare da mai karya bana shiri da mutum mai kame-kame nafi shiri da mai gaskiya.
saita durgushe ta zauna a sanyaye yayinda idanuwanta suka cika taf da hawaye ta tabbatar alh Adnan yaci karo da su Abba a jikin get, fargabarta kada ya zargi ko saurayinta ne,
muryanta na kakkarwa ta bashi labarin Madina kakaf sannan ta gangaro ta fada masa dalilin da yasa ta nemo Abba,
daga yadda ta fahimci alh Adnan ya tausayawa Madina kamar yadda ta san shi da makurar jin tausayi, saita fara sakin jikinta tana koro bayanai, yayi shiru tsawon yan mintina yana tunani,
yayi ajiyar zuciya ya dubi kaltum yace lallai Madina tanada mutunci kuma ta taimake ki ya kamata itama ataimaketa yanzu idan taji Abba bai mutu ba ai zata yarda ta dawo ko?
ma'ana idan na aika alh sa'adu ya daukota.
.ADON DAWA 39
.
TRUE LIFE STORY
.
Kaltum Tace bazata yarda ta dawo ba har sai dai idan anje da Abba, idan ta ganshi kila ta yarda ta dawo saboda zuciyar ta tariga ta daskare ta sawa ranta har abada tabar kasar nan bazata dawo ba.
alh Adnan ya gyada kai yace gaskiyane ke kika santa kika san ra ayinta, da shawarwarinki za'a yi ampani, jeki ngd za a dawo da madinarki,
tayi murmushin jin dadi tayi godiya ta mike cike da farin ciki zata fice harta kai bakin kofa zata fita taji yakara kiran sunanta sai taji hankalinta ya tashi mamaki ya rufeta ta dawo cikin sanyin jiki ta durgusa agabansa tana sauraron sa,
yayi murmushi yace kin bani labarin rayuwarki a bur sudan kakaf keda Madina da irin taimakonda Madina tayi miki amma koda wasa baki ambaci mambela ba?
daga inda yake yana juyo ajiyar zuciyar da tayi, saitayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa tayi shiru,
yaci gaba da cewa ni tuntuni nake jira ki maimaitamin abunda kika fadamin a waya kin samu miji dan ADON DAWA zaki bishi garinsu bur sudan, mutuminda ya taimakeki tun zuwanki bur sudan ya biki har Khartoum yana shirin mayar dake bur sudan ya aureki ai bai kamata ba har ki gama bada labari baki ambace shi ba,
Sai yaga tana kuka share-share da hawaye batada shirin magana don haka ya kyaleta ya hakura dajin amsarta ya umurce ta data tashi ta tafi gida,
ta mike jiki a sanyaye ta fice, a bakin baranda ta tsuguna ta sharbi kukanta ta goge hawaye sannan ta gangara ta shiga gidansu,
haryanzu mahaifinta yana labe a jikin labulen
dakinsa yana kallonta hankalinsa yayi matukar tashi daga yanda yaga tafito tana kuka, abunda yake zargi ya tabbata cewar ya tafka kuskure daya furtawa alh Adnan zancen ya auri yar sa kaltum gashi nan ya jawo mata tsana tunda daga lokacin yasawa ransa zamansu ya kare a gidan nan sai ya shiga tunanin ta yanda zamansu yakare agidannan sai ya fara tunani inda zasu fara babu gida babu gona babu sana a.
fitar kaltum keda wuya alh Adnan ya jawo wayar sa ya kira lambar alh sa'adu ta Nigeria yajita a kashe saiya kira layinsa na sudan sai kuwa ya same shi bayan sun gaisa yake shaida masa akwai wata mata da akeso anemo musu ita mai suna Madina a bur sudan amma ana tunanin matar bazata yarda
tazo ba har sai an tafi da mijinta,
alh saadu ya zabura yace kai haba kamar bani?
aiko a daure zan daukota kamar bakasan dauki ba dadin da mukayi da wannan bararojin ba mambela?
ai koshi kace in kawo maka duk da kasarsu ce sai na kawo shi da karfin tsiya balle yar ci rani wacce ba kasarsu ba kuma mace ai karamin aikine wannan, alh ka bani wuka da nama ka turo kudin jirgi kawai shine aikinka idan nakawota sai kabiyani yadda aka biyani waccan karon, nikuma sauran aiki ya rage nawa nasan bur sudan nasan gidajenda mutanenmu suke zama na tabbatar idan naje na tambayi sunanta za'a nuna min ba boyayyiya bane tunda kowa yasan kowa a tsakaninsu.
alh Adnan yayi dariya yace karka damu da wannan zan fita anjima zanje banki zan turo maka kudin komai ammafa kayi mata a hankali, ban saka dukan matar mutane ba koka daureta da igiyaba, cikin lumana zaka tahoda ita idan taki kabata waya zanyi mata magana in sha Allahu zata yarda ta biyoka, alh sa idu ya rusuna yayi godiya gamida yarda dabin umurnin alh Adnan, suka yi sallama suka ajiye,
missed calls biyar ya gani da sunan Abba yanata kokarin nemansa a lokacin da yake waya da alh Sa'adu ya amsa kafin Abba yayi magana ya bashi tabbacin cewar ya kwantar da hankalinsa za'a kawo masa madinarsa har gida ba sai yasha wahalar zuwa ba, Abba yaji labarin alh Adnan kamar tatsuniya bai fahimce shiba ma kwata-kwata sai ya shiga jero wa alh Adnan tambayoyi cikeda magiya
yana neman alfarma ya taimake shi yadda Allah Ya taimakeshi,
alh Adnan ya fahimci Abba bai gane abunda yake nufiba baya da haka baisan waye alh Adnan ba, shiyasa yake kokonton abunda ya fada masa, maganar karshe da alh Adnan yayi itace Abba kabani sati daya za a kawo maka Madina insha Allah.
Abba yayi godiya suka ajiye waya batare da Abba ya yarda da abunda alh Adnan ke fada ba kai har yanzu bai fahimci komai ba don haka sai hankalinsa yatashi, kamshin zuwan madina da ya fara ji ada ya gushe, ya kwanta yaji kwanciyar ba dadi ya tashi zaune yaji zaman ya gagareshi saiyayi zumbur ya mike yayi waje, a falo ya hadu da mahaifinsa ya zauna agabansa ya fara koro masa bayanan da alh Adnan yayi masa,
sai mahaifinsa yace to ai shikenan mu jira zuwa sati dayan,
ba haka Abba yake son ji ba, yafiso mahaifinsa yace ya shirya yaje sudan din,
su kuwa mahaifansa da en uwansa bazasu taba barinsa yaje sudan yadda sukaji labarin cewar Madina tace har abada ba zata dawo Nigeria ba to tabbas idan Abba yaje taki biyoshi waje zai samu ya zauna da ita shima bazasu kara ganinsa ba.
Abba ya mike jikinsa a sanyaye ya shiga dakinsa ya dade a tsaye ba tare da yasan abunda zaiyiba can ya dauki makullin motarsa ya fita da sauri ya kuwa ci sa'a babu kowa a falon ya fizgi moto sai kofar gidan alh Adnan,
a wajen get ya ajiye motarsa ya fito ya nufi cikin gidan shigarsa keda wuya sukayi kicibus da maigadi, malam saleh ya dubi Abba shima ya dubeshi sai hankalin malam sale yayi matukar tashi saboda ya gane wannar fuskar, saurayin nanne dayazo wajen kaltum ranan su biyu, malam sale ya tsuke fuska ya tambaye shi a fusace waka zo nema ?
Kamar yadda saleh ya gane Abba haka Abba ya gane mai gadinda yakoresu rannan ne don haka shima afusace ya amsa masa wajen masu gidan nazo,
sale ya hasala yace kai yaro ba inda zaka wuce in har baka fada wajen wacce kazo ba.
Abba yace mai ya hadani da mace ai wajen mai gidan nazo alh Adnan yanzun nan muka
gama waya dashi kashiga kace masa barister Abba Tukur ne daga yankaba,
sai sale yayi sauri ya rabe ajikin get,
Abba ya wuce batareda wani ya sake magana acikinsu ba.
baisan kofarda zaibi yashiga wajen alh Adnan ba shikuma bayaso ya tambayi wannan mara mutuncin mai gadin nan sai gashi Allah Ya
jeho masa kaltum ta fito daga cikin gida dauke da bokiti zata yi shanya a igiyar dake daure a farfajiyar gidan kamar kullum daga ta dawo daga makaranta zata fara aikin wanke kayan kazantan goggo fattu tana ganin Abba saitayi turus tana dubansa cike da mamaki yayinda shi kuma farin ciki ya lullube zuciyarshi yayi dariya yace yauwa kaltum ashe kinanan, yayanki kuwa yana ciki?
ya fadi hakane don yanaso yasan dangantakarta da alh Adnan,
saita dubeshi duba na rashin fahimta shima ya fahimci haka saiyace alh Adnan nake nufi, sai tayi ajiyar zuciya ta nuna masa kofarda zai shiga jikinta a sanyaye maimakon yatafi sai ya tsaya yana dubanta yana duban kayan shanyarda yake hannunta yana duban kannenta da suka baibayeta yana duban mahaifiyarta datake daka agefe ga goyo don ko ba a fada masa ba yana duban sofi yasan itata haifi kaltum da alama nan boys quaters
shine gidansu amma kuma babban gidan ta nuna tace nan ne inda alh Adnan yake ciki, tambayoyi fal acikin zuciyarsa babu damar tambaya saiya wuce zuwa bangaren da ta nuna masa ya tura kofa yayi sallama sai suka
ci karo a tsakiyar falo har alh Adnan yayi wanka ya shirya da makullin moto a hannunsa zai fice, yayi mamaki da ganin Abba don haka suka dunguma suka koma wajen kujeru suka zazzauna,
alh Adnan dakansa ya dauko masa lemo da ruwa acikin firij sannan suka fara tattaunawa.
malam sale tsaye a bakin get har yanzu yana zullumi, zuciyarsa tana ta tsaro masa karya da gaskiya yace aransa wato dai alh Adnan yasan wannan saurayin kaltum ne don haka ya aika akirawosa zai ba shi ita tunda shi bazai iya auranta ba amma tayaya zandauki yata inbawa wannan fitsararren yaronda yake yi min magana cikin gatsali ba mutuntawa?
saidai kuma bazan iya yiwa alh Adnan musu ba akan duk hukuncinda zai yanke akan yar nan don shi yayi wahalarta, ni wani tsausayine ma yasa na furta masa wannan kalmar taya auri kaltum?
malam sale ya nufi gida da sauri ya iske kaltum na shanyan har yanzu sofi na daka ya dafe kirji ya fada cike da damuwa kaiku tsaya da aikin nan,
gaba daya suka sankare a tsaye suna sauraronsa cikeda fargaba yace wata katobara nayi wacce ta dameni ga ta zata zame mana matsala, game da zancen yarinyan nan kaltum da alh Adnan,
kaltum ta dafe kirji tace Abba lafiya?
mena yi?
ya juya ya dubi kaltum yace ina kika samo wancan yaronda ya shiga cikin gida?
kaltum agigice tace Abba ne ai wanda zai auri Madina.
wacece Madina zaki fara boye-boyen nan naki ko?
don ba a taba jin cikinki ba, basu bane kwanakin baya na koresuba?
saita fashe da kuka tana rantse-rantse,
sofi tajashi cikin daki don taji kan labarin saboda kar su alh Adnan din suji yanda yake magana da karfi a fusace yayinda kaltum tazo ta labe a bayan wundo tana jiyo duk abunda mahaifinta yake fada ya zayyanewa sofi duk yanda sukayi da alh Adnan da kuma hukuncinda yake zargi alh Adnan zai zartar yana zargin Abba saurayin kaltum ne wajenta yake zuwa kila alh Adnan ya kirawoshi yabashi ita donshi ya zame ya fita...
.
To jama'a wannan episode din yana nuna mana kuskure na mal saleh da matar sa Sofi da aka daura su na rashin jituwa da er su da pahimtar juna,
Da akwai kyakkyawar mu'amala tsakanin su da er su da ba'a kawo nan ba, da tun wuri sun sake da ita da ta basu labarin komai, kuma da sun san komai da ya shape ta maimakon ta sanar da wani,
Wasu yaran tsabagen babu puska a wajen iyayen su abokai suke baiwa labarin kukan su da daria, idan akayi rashin sa'a abokin bana gari bane sai ya basu shawara marar kyau,
Ana so iyaye lokacin da dan su yake taso wa xuwa shekara 7 su nuna masa soyayya, daga 7 xuwa wani 7 su nuna masa abu mai kyau da marar kyau (ma'ana su tarbiyyar tar dashi,) daga wani 7 din kuma su mai dashi abokin su, ta haka ne baxai na boye musu komai ba, xasu san irin halayen sa da irin abokan sa kuma xai koyi irin halin su.
Amma wasu iyayen sunan sun aihu ne kawai, sai su barwa dunia ta raina musu 'yaya.
Sai kaga uba bai san halayen yayan sa ba, bai san abokan yayan sa ba, banda gaisuwa babu abun da yake hada sa da su balle a samu lokacin hira ya pahimci damuwar su ba.
Ina mai Jan hankalin iyayen mu mata da maza ake shiga lamarin yaya, a jasu a jiki, ba sai abu ya kwabe ba azo ana dana sani, wani kapin a ankara

Please Login or Register in order to submit comment