Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ku mike tsaye kada ku damu zaku zauna tare, Allah Ya baku zaman lfy da zuri a ta gari, sukace kaima Allah Ya baka kaltum ya kwatota ta dawo wajenka ka aureta da yardar Allah.
mambela ya girgiza kansa yace ada dana rabu da kaltum zuciyata ta kasa fitar da ran zanganta kuma nazo naganta a halin yanzu banji ajikina zan sake haduwa da kaltum ba har abada, nasan na rasa ta kenan ko bayan mutuwata kuka hadu da ita ku shaida mata ina sonta bazan daina sonta ba kowa na aura kuma kome na zama a wannan dunia,
kuka da hawaye yabe-yabe mambela , musa da fatsuma keyi harsuka rabu.
ya yanko tikiti yaje yahau jirgi ya zauna yayinda suke tsaye agefe suna daga masa hannu basu baro tashar jirgin kasa ba sai da jirgi ya tashi sannan suka juyo gida Jiki a sanyaye.
al amarin malam Abdulkadir dasu alhaji sa'adu kuwa suna shiga gida a falon malam Abdulkadir aka zauna aka sake mayar da magana da alhaji Adnan a waya aka tsayar da shawarar kaltum bazata sake fitowa kofar gida ba, a dakin matar malam zata zauna har tsawon kwana biyu har a gama cuku-cukun tafiya,
malam yace da kansa zai rakasu har filin jirgi yaga tashinsu.
kaltum ce zaune a falon Manal amaryan malam Abdulkadir kenan, budurwa ya aura yar kasar sudan ce,
kaltum tayi kuka ta gaji don haka ta hada kafafuwanta ta kifa kanta ta kanannade don takaici, abinci mai lfy ne a gabanta miya ce nashe-nashe da kaji masu maiko amma ko kallo basu isheta ba balle ta dandana.
Manal tayi larabcin duniyan nan wajen lallashin kaltum don ta daina damuwa taci abincin nan abu bai yiyuba, saita shiga yi mata nasiha akan to ta tashi tayi sallolin da ake binta sannan tayi addu'ar abunda yafi alkhairi.
kaltum batada mafita ita kanta tasan addu'a ce kadai mafitarta don haka ta tashi tayi sallah tana kuka tana fadawa mai duka, amma idan tayi addu'ar Allah Ya zaba mata abinda yafi mata alkhairi sau daya sai ta roki Allah Ya mayar da ita wajen mambela sau goma dan shi zuciyarta tafi so.
kaltum tana son mambela a halin yanzu tafi sota zauna dashi data koma cikin yan uwanta data zauna da alhaji Adnan abun kaunar ta.
tsowon kwana uku kaltum na cikin gidan malam daga daki sai bandaki duk inda tayi ana biye da ita ana zuba mata ido, a cikin gida ma kenan balle a kofar gida inda yake dankare da malamai da almajirai ta ina zata fice ai bazai yiwu ba, kamar yadda ba a bari ta fita ba haka aka hana kowa ya shiga ya ganta, duk irin nacin da fatsuma tayi don a barta taga kaltum ba a barta ba.
ranarda kwanaki uku suka cika a lokacin komai na tafiya ya kammala alhaji sa'adu ya iso gidan malam dauke da tikitin tafiyarsu a hannu, yazo ya nuna wa malam yace karfe takwas na dare ne buking din su,
don haka karfe shida na yamma kaltum dasu malam suka dunguma suka fito yayinda fatsuma da yan gidansu suka yo waje a guje, waje ya dauka da hayaniya cewa ake ku fito na cikin gida kaltum zata tafi...
lah kaltum tafiya zakiyi?
da dai sauran surutai irin na mata.
malam ya umurci kaltum da ta shiga gidansu ta dauko buhun kayanta tazo su tafi, sai ta girgiza kai ta sharce hawaye tace nabarwa fatsuma dukka tayi amfani dasu.
fatsuma ta kamkame kaltum tana kuka tana cewa yanzu kaltum tafiya zakiyi kibarni?
Sai da malam Abdulkadir ya hada da shauda mata carbin hannunsa sannan ta saki kaltum, dan anyi mata maganar duniyar nan ta saketa taki, malam ya dubi fatsuma cikin fushi yace wannan yarinya rawar kanki tayi yawa ke kike sake tunzura kaltum kike kara sata kuka idan bakiyi wasa ba sai na koreki daga gidana yau din nan,
fatsuma najin maganar kora saita nitsu don idan aka koreta yanzu ina zata nufa?
musan nata da take takama dashi su shidane a shago daya suke haya.
a ina za a cashe idan bikinta ya tashi inba a
makeken tsakar gidan nan na malam ba?
saita koma gefe tayi tsuru da ido, da niyyarta dama ta tubure tace saita shiga motar tabisu airport, kaltum ce ta shiga gaban taxi malam da alhaji sa'adu suka shiga gidan baya,
yan gidan suna dagama kaltum hannu itama tana daga musu yayinda direban mota ya fizgi mota,
kaltum kuwa jiniyar kukanta ta barke, malam da alhaji sa'adu kuwa sukace dawa Allah Ya hadamu inbada kaltum ba sukatayi mata surutu har suka kai filin jirgi suna cewa inbanda yarinya da rashin hankali ina za a hada zaman sudan da Nigeria?
ke a najeriyan ma yar gata ce yar gidan masu hali zakiyi iliminki asirinki a rufe ki zauna kina wulakanta kanki a nan?
daga bara sai tsince-tsince a bola.
kaltum dai tayi mukus tana sauraron su kukanne bazata daina ba.
kaltum taga yanda mata suke cin ado a filin jirgin nan na Khartoum ai sai ta raina kanta ta ganta tamkar daddawa a cikinsu duk da wannan pink lafayan nan da mambela ya siya
musu ita da fatsuma ce ta wanke ta saka takalmin ma sabo ne wanda mambela ya saya mata ga matar malam ta bata sabon siket da farar t shirt daga ciki ta saka ta cire yagaggu na da, ashe da bata carallee ba abar gudu da kyama zata zama a cikin jirgi, nan sabon brush matar malam ta siya mata ta wanke bakinta tas turare kawai bata samu ta shafaba saboda yanzu Abbas baya bata, matar malam kuma bata bata ba amma duk da haka kayanta na kamshin koren sabulu na wanki ,
ina laifinta abunda kaltum ta dinga zaiyanowa a zuciyarta kenan don haka ta saki jikinta a cikinsu bayan anyi musu screening sai aka yi bording suka shiga cikin jirgi suka zauna duk da ta taba shiga jirgi tana karama amma sai taga kamar bata taba shiga ba.
Domin ganin jirgin tayi tamkar aljannar dunia do kyau saita tsinci kanta tana mai farin ciki harda murmushi, Alh sa'adu ya juyo ya dubeta ya tabbatar murmushin takeyi ba gizau ba yayi dariya yace ja'ira waya fada miki borno gabas take?
ana so a ceto ki kina ki har kika ja wannan aljanin saurayin naki yake kokarin ya cire min hanci,
sai kaltum ta sha kunu ta tura baki don taji ya fara cewa abun kaunarta mambela mutunci.
kujeru masu zaman mutum uku ne, alh sa'adu ne a jikin wundo kaltum a kusa dashi sai wata matashiyar mata mai suna Hajir a karshe, tunda suka zauna Hajir ta dinga surnanowa kaltum larabci tana jero mata tambayoyi.
kaltum bata bata amsa ba saboda a tunanin Hajir kaltum yar sudan ne hutu zai kaita Nigeria,
Hajir ta shaidawa kaltum cewa ita yar Khartoum ce ta auri wani hamshakin dan kasuwa a kano yanzu haka kakarta ce ta rasu tazo tayi gaisuwa zata koma.
kaltum tayi murmushi tace ni kuwa yar kano ce aure ya kawo ni bur sudan mijin ADON DAWA ne mai suna mambela.
Hajir ta damke baki don mamaki tace keko meya miki zafi da zaki baro kano birnin garin
arziki ki taho sudan a sudan dinma a bur sudan?
alhaji sa'adu ya zabura yace karya fa takeyi bata da wani miji abur sudan.
sai aka hau kalon kalo tsakanin Hajir da kaltum da kuma alhaji sa'adu batare da wani yasake magana ba a cikinsu.
mamaki mara misaltuwa zaka iya gani a cikin idanuwan Hajir, ta shiga tunanin meyasa kaltum zata mata karya irin wannan alhali karyan ma bata dadi bace ?
ko kuwa wannan mutumin ne ya ke karya ?
To ko babanta ne yaje ya raba auren ya dauko ta zai mayar da ita garinsu ita kuma tana son mijin ta?
kwarai haka ne ma don daga gani kaltum anga wanda ta kwaso da talauci. abun da Hajir ta dinga sakawa kenan a cikin ranta kenan,
jirgi ya tashi ya bar Khartoum ya lula cikin gajimare da izinin Ubangiji yayinda fasinjoji suka hau tofa addu ar nan ta matafiya wacce shugaban halitta ya koya mana, '' Allahu Akbar, Allahu akbar , Subahanaanal laziii sakkhara lana hazaa wama kunnaa lahu mukrinina wa innaa ilaa Rabbina lamunkalibuuna, Allahumma innaa nas'aluka fii safarinaa hazaa birra wat tak'waa wa minal amali maa tardha ,Allahumma antas saahibu fis safari wal khaliifati fil ahlil ,Allahumma innii a uzu bika min wa,asa'a'is safari ,wa ka aabatil manzari wa suu il munkalabi fil maali wal ahali.''
yayinda kaltum ta runtse ido hawaye mai zafi ya dinga zubowa daga idanuwanta tana fadin wayyo mambela a zuciyarta.
KANO NIGERIA
misalin karfe shida na safiyyan alhamis jirginsu kaltum ya sauka a malam Aminu international airport dake birnin kano, kaltum ta shaki iskar kasarsu saita lumshe ido taji sanyi a ranta atake taji ta fara farin ciki zataga kannenta da alhaji Adnan, ta tuno mahaifiyarta sofi da mahaifinta saleh sai taji tanaso ta gansu ma, tafi kowa sauri wajen shigewa gaba don saukowa daga jirgi da fitowa daga wajen bincike akayi aka gama suka fito waje inda kaltum take duban kanawa sai hausa sukeyi yayinda suma suke dubanta a matsayin bakuwa ba yar kasarsu ba,
musamman da suka ji ita Hajir sun juye harshe suna larabci, Hajir ta rubutawa kaltum nonbar wayanta a takarda ta bata tunda kaltum ta shaida mata batada waya,
Suna tsaye mijin Hajir da ya yanta biyu sukazo daukar ta, tana murna suna murna ta shiga mota suka tafi, sha'awarsu ta rufe kaltum ta ayyana a ranta dama ita da mambela ne suka sami sukuni haka..
kinsan hanyar gidanku idan muka shiga taxi?
alhaji sa'adu ya tambaye ta,
tayi shiru kamar mai tunani, yace idan bazaki ganeba zansaka layina na MTN na shaidawa alhaji Adnan munzo aiport ya aiko a dauke mu,
kaltum da zabura tace zangane gidan, domin bataso alhaji yazo tsoron haduwarsu take yanzu, kunyan bijire masa datayi takeji domin
ita kanta tasan baikamata ya turo azo daukarta kiri-kiri tace bataso tazo wajensa ba tafiso tabi mambela ba, alhaji sa'adu ya tsayar da taxi ya shiga gaba kaltum na baya tayi tsuru da ido, fargaba ta hadu mata da farin ciki suka cakude da takaicin rabuwa da mambela, tace da direba nasarawa G.R.A zaka kaimu babu bata lokaci direba ya manna da gudu yayinda kaltum ta tsura ido a jikin glashin wundo tana duban kanawa matan su da mazansu yara da manya sai hidindimunsu sukeyi, akasarinsu fara'a garesu kuma duk sun fito neman na kansu ga kasuwa iri-iri, haka ma'aikatan gwamnati kala-kala.
babu inda yafi kasarku dadi da yanci kaltum tafada azuciyarta yayinda ta hango almajirai akan bola suna tsintar gwangwanaye, taga ba'a hana su ba kuma zuwa zasuyi susayar ba bu mai hana su saboda suma yan kasane, sunada yanci ba kamar yadda su aka saka musu takum-kumi aka tsorata su da hukuma ba,
kaltum tana nuna musu hanyan tiryan-tiryan har bakin gidan ashe bata manta ba, a tunaninta ba zata gane ba duk a akwai canje-canje a unguwar da gidan amma bata manta ba, suka firfito daga mota, kaltum ji take tamkar a mafarki data ganta a tsaye a kofar gidansu, alh sa'adu ya fito da naira dari biyar ya mikawa direba sai kaltum ta zurawa kudin ido tana kallo domin ganin kudin tayi bambarakwai ba irin na sudan ba.
Muhammad da makwabcinsu ne yafara ganinta tsohon saurayin tannan nata, da farko baiganeta ba yayi mata kallo daya ya watsar sai tayi masa dariya har ya kawar da kai gefe, saidai yasake waiwayowa ya dube ta domin fararen hakoran nan nata masu haskawa har yanzu basu dafe ba suna kyalli duk sanda tayi daria, yace kamar kaltum?
ta amsa nice, sai da yahau salati yana mamakin yadda kaltum ta zama haka kamar ba ita ba, ta rame tayi baki ta zama bakauyiya, tundaganan jikin kaltum yafara sanyi tasan tazama wata halitta ba irin ta mutane ba tunda har Muhammad bai gane ta ba kuma ya tsaya yana tausaya mata,
suka tura gate sukaji akulle daga ciki ko bude gida ba ayi ba, bugu daya sukayi saleh mai gadi ya fito daga dan dakinsa na gadi ya bude musu da sauri da yake daman sun san da zuwanta don haka yau babu wanda yayi barcin kirki a gidan yaransu da manya, daga sunji motsi sai kowa ya bude ido,
alwalar asuba kuwa sun yi fiye da sau uku sai su ga ashe assalatu batayi ba saboda matsuwarda sukayi gari ya waye suga kaltum.
kallon-kallo ne tsakanin kaltum da mahaifinta, hankalinsa yatashi yadda yaga yarsa ta fige ta zama kaza ita kuma sai taga ya tsufa.
alhaji sa'adu ya fusata yace da malam saleh
matsa mu wuce kazuba mana ido inni ba kasan ni ba ai ita kasanta idan kuma batanan aka kawoka to yar gidan ne, yar gidan alhaji Adnan ce, daga sudan muke yasan da zuwanmu,
sai yaga kaltum da mai gadi sun hada ido sunyi dariya kaltum tace kai alhaji sa'adun nan kaci ka fada, babana ne fa,
ta durkusa ta gaishe shi sai yau yataba ambaton sunanta yana rawar murya yace AlhamduLillahi, kaltum naji dadin dawowarki da kika dawo kafin in mutu, Allah mai amsa addu'ar bayinSa, ki yafe mana kaltum..
sai su dukka suka rushe da kuka malam sale yasa hannu ya tashi kaltum tsaye daga sunkuyon da tayi suka dunguma cikin gida kai tsaye boys quaters ya nufa yana kwalla kiran sunan sofi!!
cewa yake ku fito ga kaltum ta zo, sofi ta manno da gudu abunka da mara kiba tazo ta rungume kaltum kuka take ta sharba ita ma taga uwar bari ko ina kunyar fulanin nan?
yayinda kaltum taga dandazon kannenta manya da yara da wasu guda biyu bata san su ba matane amma ko ba fada mata ba tasan kannenta ne, su kadaine sukayi kama da ita sak ta rumgumesu yayinda suke rera mata wakarda suka dade suna shiryawa ta marhaba da zuwanta, dadi ya rufeta ta shiga cikinsu tana tafi itama tana amsawa babu shakka hayaniyan nan ta isa kunnen makwabtansu ma balle wanda suke cikin gida,
daga ganin luntsumemiyar motar da ke tsaye a farfajiyan gidan kasan mai gidan yana gari wato alhaji Adnan fari mai farar aniya matashin dattijo mai tumbin naira,

.ADON DAWA 33
.
TRUE LIFE STORY
.
.....ganin su duka sun kalle ta sai ta dukar da kai kasa ta gaggauta barin wajen. Ta shiga gida ta iske sofi a gaban risho tana faman tuka tuwon shinkafa kamar kullum, kamar yadda ta saba da yamma. Kallo daya ta yi wa kaltum ta tabbatar tana tafe da damuwa don haka ta tsaya cak da tukin tuwon tana duban 'yar ta tana sauraron abunda zata fada. Cikin sanyayyar murya kaltum take tambayar sofi.
"mama, daman Goggo fattu ta dawo daga makka har ma tana kwance a zangon daura ba lafiya? "
Sofi ta nisa ta ce, "fiye da shekara guda Goggo fattu ta dawo sharkab babu lafiya, babu hannu ba kafa, ai sai a lokacin muka san ba kwa tare da ita, don mu a tunaninmu kuna tare. Sannan ta tabbatar mana da cewa ta baro ki a Sudan. "
Kaltum bata sake magana ba cikin sanyin jiki ta wuce zuwa dakinta ta shiga lungu ta takure, ta rasa abunda yake yi mata dadi. Sai ta ji kuka ya rufto mata wanda yake tafe da sakonnin zuciyarta kala-kala. Ta tuno azabar da Goggo fattu ta gana mata a baya, sai ta tuno da ranar da ta shige jirgi ta kyaleta, ta tuno rayuwarta a Sudan ta wahala, sai ta ji tausayin wadanda ta baro a can a cikin wahala, don haka kuka ya rikito mata ba kakkautawa. Abayyane take fadin, "wayyo madina, wayyo mambela na, wayyo fatsima ".
Daddy da baba Saleh ne ke zaune a falo suna ta shawarwari kala-kala bayan an gama shawarar yadda za a shirya tahowa da Goggo fattu sai aka shiga shawarar shigar kaltum makarantar boko don ta karasa karatunta. Shekaru sun nausa tun da yanzu shekarunta goma sha takwas kuma daga J.S.S 3 ta tsaya don haka shawarar da suke yi ta ina zata datsa.
Alhaji Adnan ya zaro waya ya fara bubbugawa mutane daban-daban yana tambayar tsare-tsaren makarantu daban daban don tantance makarantar da ta dace da kaltum. Ya nemi shawarwarin abokansa masana makarantu ya hada da shawarwarin shugabannin makarantu daban-daban, daga karshe ya yanke shawarar ya saka ta a wannan makarantar da take tashe, wato "crescent". Ajin da za a saka ta ne aka ce sai an yi mata jarrabawa za a tantance, aka tsayar da shawara jibi littinin a kawo kaltum makaranta don zana jarabawa.
Alhaji Adnan ya umurci malam Saleh da ya kira kaltum ya shaida mata halin da ake ciki. Fitarsa babu dadewa sai gashi ya shigo da 'yar sa. Kallo daya zaka yi mata zaka kula da jajayen idanuwanta alamar ta yi kuka. Ta durkushe a kasa kusa da mahaifin ta wanda shi ma a durkushen yake suka nutsu suna jiran abun da uban gidan su zai fadi.
Ya sake luntsumewa a cikin lallausar kujerar da yake zaune, yace.
"Kaltum, kukan me kike yi? Ashe har yanzu akwai abunda yake bata miki rai a duniya? A tunanina kukanki ya kare tunda kika dawo gida ga mahaifan ki, ga mahaifiyarki ga ni nima ina tare da ku. Me nene matsalarki, ko me kike nema kika rasa in yi miki? "
Sai mahaifin ta ya fara zubar da hawaye, yace
"Alhaji babu gata da kulawar da baka yi mana ba, ko mu muka haife ka ko kai ka haife mu iyakacin abunda zaka yi mana kenan. Kukan da take yi kuwa ba wani abu ba ne, maganar Goggo fattu ce da ta ji muna yi cewar, tana kwance babu lafiya, sai dai ta yi komai akwance a kwashe. Ka san kaltum da tausayi shine ta je daki ta fara kuka".
Alhaji Adnan ya girgiza kai, ya ce "Allahu Akbar, haka mutum ya kamata ya kasance. Ya zama mai yafiya da maye gurbin mugunta da alkhairi. Ba komai kaltum, ki daina kuka ki yiwa fattu addu'ar Allah Ya bata lafiya, kuma ki yafe mata domin ta zalunce ki, idan ba ki yafe mata ba Allah ba zai yafe mata ba. Don Allah ba ya yafe laifin wani, ko yafiyarki zata sa ta sami rangwame daga ukubar da take ciki yanzu."
Kaltum ta fada cikin kuka.
"na yafe mata duk abunda ta yi min".
Malam Saleh ya dora da, "Alhamdulillah, Allah Ya miki albarka ke ma, Allah Ya baki 'ya'yanda za su miki biyayya ".
Kaltum ta amsa da, "Ameen ". Yayinda Alhaji Adnan ya shaida mata dalilin kiran da yake yi mata shine, a kan karatu. Ya bayyana mata cewar ta je ta sami 'yar makwabtarsu Nana ta fara koya mata karatun da ta manta kamar "Maths da English" saboda ranar litinin zataje tazana jarabawa don asan ajinda za a sata.
farinci mai baiyani zaka dinga hangowa afuskar kaltum kankace kwabo hawayen kuka ya kafe, idanuwanta sun washe sai
fararen hakwaranta ne ke haskawa afili don
dariyarda take kyalkyalawa, na gode dady inason makaranta daman,
kalmar da kaltum ke maimaitawa kenan ta kaura gidansu nana tana koya mata aikin yan aji biyar domin aji biyar takeda niyar farawa
duk da a kureren lokacine, kwana biyu kawai
amma yin karatun ya tuttuno mata da abunda ta manta abaya dayawa saboda tunda taje sudan ko biro bata taba rikewa ba balle tayi wani abu waishi rubutu, ta kanta kawai takeyi.
ranar litinin duk da alh Adnan baya gari amma yabar musu komai harda Danladi direba don haka sassafe kaltum ta shirya ta shige bayan mota direba ya kaita makaranta ta hadu da yan mata kamarta a cikin makarantar tana yi musu kallon suna jin dadi daman itace su suma sunayi mata kallon yar gata dama zasu sami gatanta yarinya karama da mota da direba.
a offishin shugaban makarantar aka bata jarabawar ta zauna tayi tsaf ta gama ta mika, kwanaki biyu kacal suka bata ta fara zuwa bayan sun duba jarabawanta zasusan ajin da zasu sakata, awaya suka shaidawa alh adnan cewar kaltum tayi kokari ta amsa musu jarabawan su wasu kuma ta fadi don haka a aji hudu ta cancanta a ajiye ta, ya amince yace ba damuwa ya riga ya biya kudin komai don haka direba yaje yakarbo mata kudin uniform da littatafai da yawa,
akace ta fara zuwa duk da haka tayi farin ciki kuma ta kudiri niyyar dagewa wajen gyara kuskuren jarabobi data fadi,
Dan ladi dai a fakaice yazama direban kaltum aikinsa kawai yakai kaltum makaranta da sassafe ya dawo gida ya ajiye mota idan karfe biyu na rana yayi ya dauki mota ya daukota, umurni daga alh Adnan don haka kallo daya zakayi mata ka tabatar rayuwa takeyi mai dadi da kwanciyar hankali yayinda damuwa ta kau sai kwakwalwa ta washe karatu tayi ta shiga babu duka babu zagi babu bauta ga abinci a wadace,
kaltum babu sauran kuka goggo fattu kuwa
ankawota asibitin malam aminu kano ana kulawa da lafiyarta duk da akwai wata tsohuwa a wajen ta kullum sofi sai ta kai abinci, kaltum kuwa duk ranar asabar da lahadi a asibiti take yini tana taimakawa da dagata abata abinci, kwashe kashi da wankin
fitsarin da take yi a shimfida duk da goggo bata iya magana bakinta ya juye amma da hankalinta tana fahimtar komai,
saitayi ta kallon kaltum tana hawaye da alama tana nadamar abubuwanda tayi mata abaya.
BABI NA GOMA SHA HUDU
ranar wata talata da misalin karfe uku na yamma kaltum ta dira a kofar gidan alh Tasi'u tsohon mijin Madina,
kaltum sanye take da riga da wando sai dan hijabi shine kayan makarantarsu sai bakin kamvas da farar safa, katuwar jakar littatafanta ta baro a mota da direba a jikin wata inuwa yana jiran ta, tafiya take tana sanda kamar wacce take tsoro kada akamata
kokuma ince mara gaskiya sai taji tafiya ta bayan ta a lokacin da tashiga zauren gidan tayi firgigit ta waiga ta bayanta wata yar matashiyar yarinya tagani wacce shekarunta bazai wuce shekara sha biyu ba amma kallo daya tayi mata taga kamar Madina, babu tantama yarta ce kaltum taji zuciyarta ta harba don fargaba yadda take duban yarinyar haka haka itama yarinyan take duban kaltum cike da mamaki, kaltum ta fara magana cikin tuntuben harshe batare da tasan abun da zatace ba tace yarinya nanne gidan alh Tasi'u ?
Ta gyada kai ahankali tana mai duban kaltum a tsorace nan ne.
yaya sunanki ?
Kaltum ta tambaya,
cike da murmushi sunana shahida ta amsa mata, sai kaltum ta daina kokonto ta gasgata wannan itace yar autan Madina.
daga makaranta kike ?
Inji kaltum, shahida ta gyada kai tace eh, kaltum ta lura shahida a tsorace take da ita domin idan ta matso kusa da ita saita ja da baya kokorin guduwama takeyi, kaltum tace da ita toki gaida yayyanki Abdul hakim da Abdul Malik, sai shahida tasake dubanta cike da mamaki ta amsa da cewa to zasuji yayinda ta wuf ta fada cikin gida da sauri,
kaltum ta gaggauta barin zauren don kada
taje ta kirawo yan gidan su fito a tutsiyeta da
tambaya ace meya kawota ?
Tana fito wa sai ta dubi katafaren gidan da yake jikin gidansu shahida tana ganin sojoji biyu suna gadi ta gasgata nan gidan General Tukur, gidan su marigayi Abba taci sa a aka wangale get din gidan yayinda wata dambasheshiyar mota kalar (blue black)ta fito daga cikin gidan wani zankadeden saurayi ta gani a cikin motar sanye yake da jeans da tshirt baka hade da wani bakin glass a idanuwan sa, kallonda kaltum take masa na kwakwap shiya jowo hankalinsa ga dubanta shima har ya rage gilashin wundo ya rage tafiya suna kallon juna, kallon mamaki har sunkuyowa tayi tana lekensa bayan ya wuce ta, yayinda shi ma ya saita gilashin mudubin motarsa yana hangenta don yaga me take nema, wacece ita, kuma can yaga ta je a hankali ta leka get din gidansu, sai yaga ta da ka tsalle ta labe da alama ta hango wani da ga cikin gidansu yana tahowa, tabi jikin katangar tana shafawa a hankali yayinda takara dawowa kofar gidansu shahida ta tsaya ta dade sannan ta tafi, yana kallonta ta nufi wata camry ruwan silver ta bude kofar baya ta shiga ta kame direba yaja suka tafi, mamaki ya kama saurayin nan sai yaji ya fasa zuwa unguwan ma gara ya dawo gida domin ya tsorata da yarinyan nan yar makaranta tunda yake ko a hanya bai taba ganin mai kama da ita ba, yayi kwana ya juyo kofar gidansu masu gadi sukayi sauri suka
bude masa get sai ya canja shawarar shiga gida sai yaji gara yabi bayan yarinyan nan yaga daga ina take kuma me tazo nema a gidansu,?
saidai kash da yabi inda sukabi sai yaga wayam ko

Please Login or Register in order to submit comment