Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai tunani can ya
nisa yace tunda haka kikafiso bari nafara ganin sa tukunna sai inji a ra'ayinsa game da shawarar da kikayanke idan naga yanada hankali kuma yanason auren sai kuyi ku zauna inbashi jari ya rike ki in Allah yasa kuntara kudi saiku shiga makka.
fatsuma ta kwashe da dariya tace bari inkirashi awaya ma yazo yasamemu anan asibitin, nasan yanzu yataso daga gun aiki.
mambela yace har aiki yakeyi kenan aibakuda matsala ma sosai.
fatsuma tace eh dako yakeyi akasuwan markadi anan muka hadu bari na kirashi ka ganshi ta zaro wannan gwabjejiyar wayanan ta ta wanda sai andaki bayanta take kawo wuta takira abun kaunarta musa ta fara koro masa bayani kenan yahango ma'aikatar jinya sun riko hannun kaltum suna fitowa da ita daga dakinda akayi mata aiki dan haka yataso da sauri ya iso garesu cike da kulawa kalma daya ne ya fito daga bakin shi shine sannu ,sannu kaltum da ciwon har yanzu ko ya daina?
da sauki tafada a kunyace
fatsuma ta taso da sauri ta rike hannun kaltum suna hada ido sai suka tuntsure da dariya wannan dariya tasu tabawa mambela mamaki dominshi ya rasa abun dariya anan.
magunguna cike da leda ya saya mata suka dunguma suka fito daga asibiti,
tafiya sukeyi ahankali saboda dingishinda kaltum keyi, fatsuma na rike da ita mambela kuwa a gabansu yake yana tafiya a hankali suna isa bakin titi sai mambela ya nufi wani katafaren kanti a tsallaken titi, su dai suna biye dashi suna jiran suji abunda zai fada musu suka shiga ciki sai suka iske kata faren waje ne a lailaye da tiles fari mai dauke da teburi kashi-kashi masu kujera hurhudu a
kowani teburi fulawowiyi ne a kowace kusurwa ga A.C mai sanyi da fankoki kana tura kofar gilashi sanyi da kamshi ne zai bugi fuskarka, da alama kamshin abinci ne na alfarma ke tashi,
ma aikata suka taresu da fara'a yayinda aka
nuna musu wajen zama suka zauna doguwar
takarda aka mikamusu mai dauke da hotunan abinci kala-kala da sunayensu da farashin ajiki ma'ana su zabi wanda sukeso sai akawo musu,
mambela ya zaba ya nuwawa ma'aikaciar, sannan ya mikawa su kaltum,
fatsuma ta zaba, kaltum kunya ya hanata ta zaba don haka mambela ya zabar mata, shinkafa da taliya mai tiriri aka fara kawowa farati uku sai ga farantin miya kala-kala, kifi ne a bankare game da wasu dakwalen kaji sun yi rashe-rashe akan faranti , salad ne hadadde gami da kayan marmari a yanyanke wato fruit salad . lemuna (freshe juice )a kofuna aka kawata shi da tsinken tsotsa.
kamar a mafarki haka sukejin kansu yayinda
farin ciki ya baibaye zuciyoyinsu,
mambela da fatsuma basu jira komai ba suka fara ba cikinsu hakkinsa yayinda nauyi da kunya ya hana kaltum ci ya juya ya dubi fatsuma yace me ya hana kawar ki cin abinci ?
Fatsuma tayi dariya tace tun dazu take taka min kafa tana mintsinina wai intashi mu
chanza tebur ba zata iya ci a gaban ka ba,
mambela yayi dariya ya dauki farantin abincinshi ya canja tebur ya juya musu baya
sannan kaltum tazage ta dinga tura abincin nan, kasancewar da dad'addiyar yunwa ce atattare da ita rabonsu da cin abinci tun na jiya da rana basuci ba suka kwanta da safe suka farka da gagarumar rigima a gidansu, don haka da kyar suka tsira babu zancen nemo na karin kumallo,
suka ci suka yi nak duk cikinsu babu wanda bai yi cinda da kyar yake juyiba.
mambela ya biya kudi mai dunbim yawa saboda restaurant ne mai tsadar gaske yana daya daga cikin wajen cin abinda yake tashe a babban birnin Khartoum,
kai saye bakin titi suka nufa a inda suka tsayar da taxi suka shiga suka zauna kamar dazu,
mambela ke zaune a gidan gaba ya juyo ya
dubi fatsuma fada masa sunan anguwanku da mu saukeki, nida kaltum zamu wuce tashan jirgin kasa zuwa bur sudan,
cikin fargaba ta dafe kirji tace '' yanzu da kaltum zaka tafi yaya zanyi ni kadai?
sai hawaye ya surnano daga idanun ta, kaltum kuwa farin cikine mara misaltuwa ya kamata sai itace tafadi sunan anguwan domin fatsuma ya hanata magana, kaltum ta dafata tana lallashinta game dayimata tayi idan tanaso ta biyosu ta kaura bur sudan suje cen suyi zamansu,
fatsuma ta girgiza kai cikin harshen hausa tace aure zamuyi da musa bari ma insake kiransa awaya kafin ku wuce yazo kofar gidanmu su hadu da mambela, yace yanason
ganinsa zaiyimasa zancen auren mu idan da gaske yana son aurena mambela yace zai bamu jari mu zauna,
farin ciki ya rufe kaltum ta mika mata hannu suka tafa ta ce ai shikenan tunda duk muna tare anan, kizo nima inzo,
fatsuma tayi murmushi dadi ya lullubeta tazaro wayanta ta bugawa musa kafin tayi magana yace na shirya ganinan zuwa wanne asibiti zanzo yanzu?
fatsuma tace kazo gida ka same ni yanzu mun taho yama fi kusa,...
.
Allah sarki, har mambela ya bani tausayi, yadda naga yana ta rawar jiki akan kaltum bai sai ina dap da kwace ta ba..
Yayi abu mai kyau tunda yana kiwata min mata

ADON DAWA 30.
.
TRUE LIFE STORY.
.
fatsuma tace kazo gida ka same ni yanzu mun taho yama fi kusa,
suka isa kofar gida yayinda mambela da direba suka tsaya a mota, fatsuma da kaltum suka nufi cikin gida harsun kusa shiga gida mambela yayi kiran sunansu suka waiwayo atare sai suka ga mambela ya tunkaro inda suke,
suka tsaya suna dubansa suna mamakin Kiran, yakaraso inda suke yace kaltum ki shiga kiyiwa mutanen gida sallama kifito mu tafi kada mu rasa jirgi, duk tarkacen kayan nan na tsummakarai kibarsu zan saya miki wasu a can,
kaltum da fatsuma suka hada ido suka tuntsure da daria,
kaltum ta ce wanka zanyi da sallah kawai na fito,
mambela yace nidai bazan sallami direba ba bari inje nima inyi sallar azahar kafin ki fito...
kafin mambela ya rufe baki fatsuma tace lah ga musa yazo kuzo mu gaisa, musa ya karaso inda suke gami da mika wa mambela hannu suka gaisa, musan sun kuwa dace da fatsuma dai-dai gajere bakikirin shan koko daukan rai shine wanda takeso duk duniya bata ganin ko wanne namiji da gashi sai shi, shine gwaninta, musa babu kamarsa musa ya mikawa mambela hannu suka gaisa duk da fatsuma ta fara masa bayani amma bai gama fahimta dukka ba don haka sai ta fara kara masa bayanin tunda gashi ga mambela, wata murya ne abayansu akace yauwa ga kaltum din don haka dukkansu suka waiwoyo atare cike da mamaki,
mariya sukagani daya daga cikin yan dakin su kaltum tare take da wasu dattijai guda biyu mai kiba da siriri senye suke da manyan rigunan malum-malum da alama dai hausawa ne, tafiya suke suna sabe riga suna sauri kamar zasu kifa da kasa, da alama awahale suke mariya tace kaltum ina kika shiga wadan nan mutanen tun tsafe suke neman ki?
kaltum ta dubesu cike da mamaki amma bata san su ba don haka sai ta zura musu ido tana sauraro taji meke tafe dasu haka mambela ya sankare a tsaye yana sauraronsu kafin su yi wata magana sai wayan mai kibar ta fara ruri yayi sauri ya duba sai ya latsa gami da cewa AlhamduLillah ga kaltum din muna tare da ita sai yanzu aka nemo mana ita, rike wayan ya mikawa kaltum waya ta mika hannu ta karba a sanyaye kafin ta daura a kunne sai ta kalli mambela ya gyada mata kai alamar ta amsa sannan ta daura waya a kunne tana sauraro batare da tayi magana ba, kaltum ta zazzaro ido ta dafe kirji da alama zuciyarta ce ta buga saboda mummunan firgitan da tayi, kan kace kwabo ta fara karkarwa idanunta ya kawo nan take su zatonsu mutuwa aka fada mata, mambela ya fada cike da damuwa cikin larabci kaltum lafiya dawa kike waya?
meyake faruwa?
Ta katse wayar da sauri dan gigicewa ta fashe da kuka.
yaya kika kashe wayan bayan baku gama magana ba?
inji katon mutumin ya karbi wayan ya sake latso lambar ya mikawa kaltum a fusace ya fada cikin fushi ki amsa waya malama ana nemanki tun tsafe meyasa zaki kashe wayan?
ta karba ta sake karawa akunne haryanzu batayi magana ba sauraro kawai take mutuminda yake mata magana awaya ya sake magana yace hello kaltum kina ji kuwa?
ni ne alhaji Adnan daga kano kitattaro kayanki ki biyo wadannan mutanen yau din nan ku taho Nigeria, nabasu kudi zasuje office din immigration ayi miki passport ku hawo jirgi ku taho gida kinji na fada miki kada ki yarda ki sake subucewa a rasaki arasa yan aike.
kaltum ta juyo ta dubi mambela ta cigaba da sauraron abunda alhaji Adnan yake fada yayinda tashiga rudani mai yawa takasa tantance yanda zuciyarta ta karkata, saboda tana matukar son mambela tanaso ta zauna dashi don tana da kyakkyawar zato akansa zai riketa amana, ta yarda da tsantsan sonda yake mata saboda Allah haka bataso ta sabawa alhaji Adnan a matsayinshi na mutum da yake kulawa da ita wanda bayaso yaga ta tozarta, mutuminda yake ta salwantar da dukiyansa wajen kokarin nemota ta dawo gida, ya damu da ita kamar yar da ya haifa ta cikinsa shine cinta da shanta iliminta da lafiyarta, magana yake mata cikin damuwa da fargaba don kada ta subuce..
kwakwalwar kaltum ta dinga jujjuyawa a kokarinta na tantance da tattace abunda zaifi alkhairi a rayuwarta don gudun fadawa dana sani nan gaba, sai ta tuno kyakkyawan kulawa da alhaji Adnan ke bata tasan tabbas idan ta koma Nigeria makaranta zata koma ta karasa sakandari harzuwa jami'a, babban burinta kuwa a rayuwa shine ta ganta a jami'a ta hada digiri amma data tuno halin ko inkula da iyayenta ke mata da irin gallazawa irin na goggo fattu da take mata don kadan daga cikin halin goggo fattu ta dawo daga makka tace zata dauketa sukoma makkah iyayenta kuwa ko musu bazasuyi mata ba yarda zasuyi,
sai ta dubi dayan bangaren kuma wato mambela mutum ne mai kyauta da kyautatawa yana sonta yana bata duk abunda takeso basai ta roka ba sannan ta tuno rayuwarta da madina a bur sudan rayuwar yanci dajin dadi wasa da dariya da tsalle-tsalle, abinci ya wadata babu yunwa ko kishir ruwa tace aranta bazan koma Nigeria ba gara ingama rayuwata a bur sudan...
alhaji Adnan ya katse tunaninta data tsunduma tanayi yace kaltum magana fa nake miki bakice dani komai ba?
cikin kuka da sanyin murya tace na'am dady,
jin muryan kaltum ne yasa alhaji Adnan doguwar ajiyar zuciya game dayin hamdala a cikin zuciyarsa domin sai yanzu dayaji muryanta ya tabbatar da cewa da kaltum dinsa yake magana saboda yana kokonto ko ba ita bace, ya yi farat ya mike daga luntsimemiyar kujerar daye juyi a babbar offishinsa dake Abuja babban birnin tarayyah yafada cikin zumudi da farin ciki kaltum kece ?
To naji dadi yanzu abunda nakeso dake shine ki biyo alhaji sa'adu da alhaji jabiru ku taho nigeria sauran bayanai in anzo za ayishi wahala da gallazawa da su Fattu suke nuna miki a da ya wuce rayuwa ce mai kyau da kyanciyan hankali zaki samu a Nigeria, me zakiyi da rayuwar wahala har bara akace kinayi ni, alhaji Adnan ina raye a duniya kaltum kiyi bara?
InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un..
sai kaltum ta fashe da kuka ta girgiza kai tace daddy ka yafe mini banyi niyyar saba maka ba, nasan kokarin da da kayi akaina amma bazan iya dawowa Nigeria ba, yanzu zanbar Khartoum inkoma bur sudan inda nafi sabawa dasu zan auri mambela domin shine mai taimakona..
acan alhaji Adnan ya dafe kirji yafada cikin gigita kaltum waye kuma mambela ?
Kaltum ta sharce hawaye tace mambela dan ADON DAWA.
ne alhaji Adnan ya sulale yayi zaman dirshan a kafet yayinda yasa hannu ya fisgo hulan kansa don tayimasa nauyi a halin yanzu wayar ya ajjiye a gabansa yana duba batare dayasan abunda zai yi ba, ji yake tamkar ya huda wayar ya ganshi a Khartoum kusada kaltum ya damkota ya dawo da ita gida, zufa yaketa hadawa duk da babbar rigace a jikin sa ai akwai sanyin split A.C a offishin,
tsabar tashin hankaline kawai kaltum ta mikawa mai kibar wato alhaji sa'adu wayansa ta koma bayan mambela ta labe har yanzu mambela acikin rudani yake don bai tsinci kalma daya ba a cikin duk wannan bayani da akeyi ba, ya juya ya dubi kaltum cikin harshen larabci yake tambayanta wai meyake faruwa ne?
saita rushe da kuka yayinda kukanta yake sake daga masa hankali.
alhaji sa'adune ya duba wayarsa har yanzu sekonni na tafiya ma'ana alhaji Adnan yana kan layi saiya kara wayar a kunnensa ya dinga magana sautin maganan ne ya ankarar da alhaji Adnan cewar su kaltum nakan layi basu kashe ba, saiya rarumo wayar ya kara ta akunnensa muryan alhaji sa'idu yaji yana magana, alhaji sa'adu yace yanzu ranka ya dade haka za a kyale yarinyar nan tayi abunda ta ga dama ?
Mufa da muke zaune a sudan mu mukasan wahala da wulakanci da mutanen mu suke gani,
alhaji Adnan yayi tambaya cikin fushi wai wani irin yare takeminne naji tace mambela zata aura kuma wai daga ADON DAWA anya kuwa ba aljanine ya auri yarinyannan ba domin a bil'adama babu mai suna mambela kuma aduniyan nan kakaf ban taba jin wata kasa ADON DAWA ba saidai in a garin aljanu, don haka kuriketa kada tashiga daji bada mutum take zama ba.
alhaji sa'adu yayi dariya ya subuce masa yace ranka ya dade mutum ne mambela, ADON DAWA kuwa kabilarsu ce, a bur sudan suke.
alhaji Adnan yace kai ya akayi ka sani ?
kana ganin mambela da idonka ko itace take fadamaka ?
Alhaji sa'adu yace ina ganinsa alhaji.
"alhaji adnan yace ka tabbata shi mambela datake fada kana ganinsa?
Alhaji sa'adu yace tabbas mutum ne saidai idan kuka kuskura kuka bar yarku ta auri wannan dan ADON DAWAn to mu'amalanku da ita har abadah, a cikin dawa suke rayuwa gidan katako da 'kaya, abincin su dabino da madarar shanu ce kawai.
hankalin alhaji Adnan yakara tashi baisan sanda ya yaye babbar rigar sa ya wurgarba ya mike saye yana magana cikin daga murya da dukan bango har ma' aikatansa suka dinga rugowa a guje zuwa offishinsa don suga abunda yake faruwa sunsan ba lafiya ba, basu tabajin yana irin wannan hayaniya ba da daga murya kasancewar mutum ne mai sanyin magana cikin kamilalliyar murya, mutum mai hakuri da fara'a yau bacin ran kaltum yana sashi ruri tamkar zakin da yaga nama,
alhaji Adnan yace alhaji sa'adu da kai da alhaji jabiru nabaku amana kuma kun karba nace ku yanke da kanku yawan kudin da kukeso da kanku kunyi kokari kunnemomin kaltum kamar yanda kukace inyi zamana basai nazo ba zukuyimin komai gaku ga kaltum ga kuma aljanin saurayin ta mambela kuna tare ni ina Nigeria sannan zaku dinga tambayana abunda zakuyi?
alhalin kunsan ra'ayina shine ku kawo mini kaltum gida ko tana dariya ko tana kuka duk yanda zukuyi kuma duk yanda za ayi karkubar kaltum ta subuce muna bukatarta anan, idan kwatarta zai muku wuya to ku kira yan sanda su kaiku kotu a fara shari ' ah nikuma kan a gama zanshigo sudan din ayi dani kungama aikinku.
alhaji sa'adu ya tuna makudan kudinda alhaji Adnan yayimusu alkawari mai dumbin yawa sai jikinsa ya hau makyarketa kaikace dan taure ne.
yace alhaji Adnan kwantar da hankalin ka daman ra ayinka nakesonji ko ka canja kuma ina neman izini kar rigima ta kwabe kace baka sani ba ace mana mu masu satar mutane ne hukumar sudan kuwa tanada zafafan hukunci akan masu aikata irin wannan kazaman laifi, kabani nanda minti goma zan sake kiranka kaji halinda ake ciki sannan suka kashe waya.
mambela ne ya fusata ya damko gashin kaltum ya wujijjiga yana magana cikin gigita dazubo da hawaye mai yawa yace kifamin abunda yake faruwa anan kunzamar dani mushe a tsaye bansan meyake faruwa ba kuma gashi sai anbaton sunana akeyi wai shin laifi nayi dana baro garinmu nafito nemanki a Khartoum don in ceto rayuwarki da kuma nuna miki kaunar da nakeyi?
kaltum ta rusa kuka harda kurma ihu kaikace rai ake fitar mata,
fatsuma ta karaso da gudu ta kwaci kaltum a hannun mambela abun mamaki saiyaga fatsuma kukan takeyi sannan ta fara yi masa bayani abunda yake faruwa,
data kira sunan alhaji Adnan sai ya tuno da sunan wato kishiyarsa don haka sai yayi shirin gagarumin rigima a zuciyarsa yasan yau za ayi dayan biyu koya kashe ko akasheshi wajen kwatar kaltum,
sai yayi wani irin dariya mai ban mamaki ya juya yadubi kaltum wanda har yanzu tana rungume ajikin fatsuma yace kaltum kije kishiga cikin motar can taxi ki zauna gani zuwa..
jikin kaltum na karkarwa ta juya aguje ta nufi inda motar take yayinda alhaji sa'adu ya cire babbar rigarsa ya hada da hular dake kansa ya wurgar akasa ya damkara da gudu ya damko kaltum ta baya saiya fisgota tamkar kaza saboda rashin nauyi..
da mambela yaga haka sai ya fusata ai ko sekon daya ba karaba ya kaiwa alhaji sa'adu wani dankareren naushi a hanci yayinda jini ya wanke masa fuska nan da nan ya saki kaltum ya rike hanci ya durgushe.
da abokinsa alhaji jabiru yaga haka sai shima ya ya fisgo hannun kaltum ya tura keyarta cikin gidan su,
mambela ya yunkura zai hana sai alhaji Sa'adu ya mike a fusace ya cafki mambela da dambe...
.
Yayin da ni kuma Dan Aunty na tsaya kallon mafadata akan abar kaunata,
Wannan shi ake cewa '' kura da shan bugu... ''
A gama komai nazo na aure ta, shi kenan.
ADON DAWA 31
.
TRUE LIFE STORY
.
jama'a suka farga kan kace kwabo an shiga tsakaninsu,
mata da maza sun firfito, masu wuce a kafa, babura ,keke da masu motoci duk sun tsaya kallo da neman ba'asi don a sulhuntasu,
zage zage ake tsakanin mambela da alhaji sa'adu yayinda dukkansu jikinsu na tsuma sunaso a sake su su kaure, zuciyoyinsu sun hargitsa karfine yazo musu yayinda hannayensu ya hau kaikayi, naushi kawai sukeso sukaiwa junan su,
larabcine ke tashi inda mambela yake dukan kirji yana cewa kaltum tasa ce babu mai dauke masa ita,
shima alhaji sa'du yana ikirarin baban yarinya ne mahaifi yasa a dauko masa ita don haka duk kotun da za aje sai dai aje amma bazai bar kaltum ta subuce masa ba, bayan watanni shida da suka kwashe suna nemanta a Khartoum gida-gida,
malam Abdulkadir aka kira ya fito daga gidansa da sauri hankalin sa atashe ance yazo ana wani fada a kofar gidansa,
dazu mata ne yanzu kuwa maza ne ke casuwa ransa abace sai karanto InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un yake, yana ta jan dogon carbinsa, yana karasowa ya dubi mambela ya juya ya dubi alh.sa'adu yaga babu wanda ya sani a cikinsu, sai bacin ransa ya fadada cikin harshen larabci yace kukuma su waye daga ina ku kazo kofar gidana kuna dambe?
Dazu yan sanda sun zo ana can ana shari'ar fadan dazu ba a gama ba yanzu ma an ce antafi kira suzo su iske a kofar gidan ne kuma ?
Yanzu daman abun alkhairi zai zama sharri?
don nace duk mutanenmu wadanda ba su da gida suzo su zauna kyauta sai in zama abun tozartawa a garin nan?
sunan gidana ya shiga tsinuwa a bakin jama'a ?
Alhaji sa'adu ya fara jawabi cikin harshen hausa ya yiwa malam dalla-dalla akan abunda ake ciki
Kowa ya gamsu don haka kobin ta bakin mambela ba ayiba malam ya yanke hukunci nan take kaltum baza tabi mambela ba, kasarsu za a mayar da ita domin shima babban burinsa kenan, duka manyan matan nan da yammata da kananan yaran dake zube a gidansa su wa kansu fada su koma kasarsu cikin gata da yancin kai.
kaltum tanajin haka saita kurma ihu ta fadi tana kuka, fatsuma na riketa itama kukan take taya ta, sauran matan gidan kuwa hayaniya sukeyiwa kaltum suna dungure mata kai suna cewa keba dadinki bane da har kika sami iyayenda suka damu dake su aiko a daukeki ko ba kece mai kuka da ihuba a sanda kalah ta karbi kudin iyayenki ta arce ta bar kiba?
Me ya yi miki zafi da zaki koma bur sudan da rayuwa kauyen da babu wuta babu ruwa babu wayar sadarwa, kakaf garin babu gidan siminti sai na katako, amma ki koma Nigeria kasarki a najeriyan ma a babbar birnin kano ai kin caba don haka ki tashi kibi mutanen nan kawai.
cikin kuka kaltum tace saceni zasuyi malam bazan bisuba.
sai jikin malam yayi sanyi ya dubi Alh.sa'adu yace da kamshin gaskiya idan anbi ta barawo sai abi ta mabi sawu, ku su waye ?
Kuma daga ina kuke ?
Alh sa adu yace nima mutumin kano ne amma bazan ce muku komai ba bari na hadaku da mahaifinta awaya kuyi magana, ya latsa number alhaji Adnan nan da nan ya amsa alhaji sa'adu ya ce alhaji rigima fa aketa tafkawa yanzu haka an fasamin hanci yana jini saidai yarinyan tace bata san mu ba saceta zamuyi shine nakeso kayiwa wani dattijo bayani wanda kusan kaltum a hannunsa take don ya gamsu, a gabansa abawa kaltum waya kayi mata magana don idan ita bata san mu ba mu barayin mutane ne kai ai baza ta kiraka barawo zaka saceta ba, alhaji sa'adu ya mikawa malam Abdulkadir waya suka dade suna magana daga karshe malam Abdulkadir ya fahimci ashe kaltum jikar fattu ce, fattu kuwa tare sukayi wasa a zangon Daura .
don haka ya yarda kaltum tabi wadannan mutane,
da yan sanda sukazo malam ya kora musu bayani cewar ba rigima bace don haka basai an tafi police station ba,
mambela yanaji yana gani aka tafi da kaltum cikin gidan malam tana waiwayensa yayinda shi kuma mambela a tsaye, musa da fatsuma da mai taxi suna lallashinsa hawaye yana zuba daga idanunwansa zuciyarsa kamar zata fashe dan tsananin tafarfasar da takeyi,
fatsuma ta sharce hawaye tace da mambela yayana mambela zantaimake ka ka sami kaltum, kamar yadda baka san mu ba ba nida musa ka kudiri aniyar zaka taimake mu.
mambela ya koma ya zauna a cikin taxi gidan gaba yayinda ya jingina da kujera, ya daga kansa sama ya cije lebe wannan shine ake kira ga samu ga rashi ya samo kaltum da kyar amma ta subuce masa yana ji yana gani,
mambela ya yunkura zai tashi a fusace musa ya mayardashi,
yace da musa kabarni inshiga cikin gidan malamin nan muyi duk abunda za ayi kosu kasheni ko in kashe su saboda alkawari nayi saina lahanta duk wanda zai rabani da kaltum...
musa da direba su kayi kukan kura suka danneshi ya koma ya zauna,
sunfi minti talatin suna bashi baki sannan ya yarda zaitafi,
Su fatsuma suka shiga motar suma aka tafi dasu zuwa tashar jirgin kasa ta zuwa bur sudan,
cikin hawaye mambela ya zaro kudi mai yawa ya bawa mai taxi, farin ciki ya rufe direba ya dinga yi masa addu'ar Allah Ya bashi kaltum Ya kwato masa ita daga hannun wadancan. mambela ya amsa da Ameen ya juya ya dubi musa da fatsuma yace ina yi muku fatan alkhairi a shirin aure da kuke yi, kuma ina baku goyon baya dari bisa dari nayi alkawari zan taimake ku ba ku kadai ba ma duk wasu masoya da suke son junansu zan taimaka masu duk rintsi su auri junansu duk na sadaukar wa kaltum.....
sai hawaye ya kara kwaranya harya kasa ci gaba da magana.
saisuma suka fara kuka don tausayinsa, can ya juya ya dubi musa yace a halin da nake ciki yanzu bazai bari muyi wata magana ba
saidai kawai duk sanda ka shiryo kazo wannan tashar kahau jirgi kazo Khartoum Tutti ka gangaro bur sudan kusa da ruwa zakaga garin yan kasarku hausa, sai kace sununa maka garin yan ADON DAWA gidan sarki kokace musu mambela kake nema, ko karamin yaro ka tambaya mai shan nono indai ya iya magana to yasan sunan mambela, idan bana gida to za a rakoka bakin kasuwarmu Jim Arab nanne kadai wajen zuwa na, kazo mu zauna muyi magana game da auren ku, nayi alkawarin zancanja muku rayuwarku da izinin Allah amma da sharadi guda daya, idan har kasan bada gaske kakeson fatsuma ba yaudaranta kake kada kazo inda nake, kaga fatsuma amanace a wajanka inhar ka yarda ka aureta kaine uwa Kaine uba a gare ta, don batada kowa a kasar nan, tunda wuri ka fadamin gaskia sai inbiya mata kudin jirgi tabi kaltum su koma Nigeria.
nan take suka zaburo don tashin hankali saboda suna kaunar junansu baza su iya rabuwa ba sai su duka suka durgusa a gaban mambela suna rantse-rantse cewar zasu zauna amana,
sai mambela ya sake shiga damuwa yasake tausayawa kansa da kaltum,

Please Login or Register in order to submit comment