Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ragawa duk wanda ya raba ni da abar kaunata kaltum ba.”
Madina ta girgixa kai t ace, “Allah Yan a tare da mai gaskiya, Shi xai fitar da ni daga cikin wannan dabaibayi.”
Ta sharce hawaye ta wuce, kamar daga sama ta ji mambela ya kira sunanta. Ta waiwayo a hankali ta ganshi har yanxu a xaune a inda ta bar shi, ya jya mata baya kansa a sunkuye a kasa.
Ya ce, “da aka dauki kaltum daga nan ina aka ce xa a kaita!”
Madina t ace, “jirgin kasa suka hau suka tafi khartum babban birni.”
Ya ce, “khartum a ina, wacce unguwa!”
Madina t ace, ban taba xuwa khartum ba, ban san ko’ina ba, dan haka ban tambaya ba. Saboda bas hi da amfani in sani don an tabbatar min da xarar sun isa khartum ba xai wuce kwana biyu xasu yi ba xa su tafi Nigeria, don kudin jirginta da na ‘yan rakiyarta na hannu an turo musu daga nigeria.”
Mambela ya fada cikin fushi, “bana son bayanan ki, ya ishe ni haka, tafi kawai.”
Xungwi-xungwi ta kama hanyar gida ba tare da sake waiwayowa ba. Mambela yaji takaici a ransa har ya fin a kullum. Ya ji wani tsananin son kaltum ya kara mamaye xuciyarsa. Ya ji ya tsani madina, ya ji daman ace xa a wayi gari a ga gawar sa shi ya fi masa sauki. Ya yi kuka, ya dinga kwalla sunan kaltum shi kadai a bakin teku tamkar tababbe ga magaruba ta yi, duhu ya bayyana. Ya tuna ranar day a tare kaltum a dai-dai inda yake xaune, ranar da ta dinga ynakasa da wuka, kuma a ranar ta fara sonsa.
Bai bar wajen ba said a gari yayi duhu sosai. Ya isa gida ransa a bace. Sallah kadai yayi, ya rufe kansa a daki ya kwanta ba don yana jin barci ba, sai don kawai xuciyarsa ba xata iya jure surutun mutane. Xuciyarsa ta raunana, ji yake tamkar ta hadu da lahani tamkar xata buga.
Sarki ya dinga aike a tambayar masa, anya mambela lafiya ya kwanta da wuri! Ta wundo yake bas u amsa lafiyarsa kalau, barci yake ji.
Talatainin dare daf da asuba sannan barci ya dauke shi, sai ya gan shi tare da kaltum a mafarki suna hirar so da kauna. Farin cikin sa a mafarki bay a musaltuwa, amma day a farka ya ganshi shi kadai ba kaltum a xahiri, sai ya ji tamkar ya kurma ihu don takaici.
“me yasa kika tafi kika bar ni kaltum! Me yasa da aka xo daukarki ba ki rugo kin xo kin fada min mun tafi tare ba!”
Haka mambela yake fada a bayyane a cikin yarensa na adon dawa.
ADON DAWA
.
TRUE LIFE STORY.
.
A dan mana hakuri na rashin jin mu dauke da ci gaban littapin nan, abun ne suka sha gaban mu amma ba wai haka muka so ba.
Duba da posting din karshe 24 an samu akasi ba'a tashi daga inda aka tsaya ba yasa na kawo muku shi yanzu...
Sai ata hakuri damu.
BismiLlah
,
sai bayan sallar isha i tafarfado ta tashi zaune daram zuciyarta cike damamaki ganin yadda jama a suka kewayeta mata da maza ta lura da an burbursuna mata wasu
abubuwa a kofar hancinta saita tuno matsalar bugun aljanun da take dasu abaya sannan ta gasgata sune suka tashi sai dai tambayar da take yiwa kanta meyatayar mata da aljanun?
tana tunanin tabbas an fada mata wata magana dazu amma ta manta duban jama'a take daya bayan daya sai kalmar sannu suke ambato mata can ta tabbatar asibiti take tashiga tunanin me yakawota asibiti to ina kalah?
Sannan ta tuna ance mata kalah tarasu sai ta fashe da kuka,
jajanta mata ake ana bata hakuri ana jaddada mata addu'a mamaci ke bukata ba kukaba ta tambaye su ina kalah take?
wata mata ta shaida mata tana matuwari taje ta kira manya domin ta mutu a lokacin da babu wani dan uwanta ko wanda yasanta a wajen
kaltum ta diro daga kan gado ko takalmi bata saka ba tanufi kofar fita caraf aka damketa ta fada cikin sanyayyiyar murya yayinda hawaye daya bayan daya ke kwaranyo daga idanuwanta tace ku sakeni ina cikin haiyacina gida zanje in shaidawa yan gidan mu,
sai suka tabbatar a hankalinta take dan haka sai suka saketa ta tafi tafiya take batare
datasan inda take jefa kafarta ba saboda tashin hankali kuka take wi wi abayyane duk inda ta gifta sai abata hanya kowa ya ganta yasan ba lafiya ba tana isa gidansu tashiga
tsakar gida sai ta kwarara ihu tazube akasa tana fadin InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un kalah ta mutu,
da gudu a dimauce suka dinga bulbulowa daga dakunansu suna rafsa salati masu ihu nataya ta ihu masu hawaye nayi masu tagumi nayi kafin ka ankara gida ya rude da hayaniya har maza daga kofar gida suna lekowa suna tambayar me ya faru?
da zarar ance kalah ce ta rasu saikaga andau salati sannan su buga tagumi, sabo akewa kuka ba halin mutum ba kowa yaji mutuwar kalah kasancewar ta dade sosai a Khartoum tun lami batayi wayoba
malam Abdulkadir shine me gidan su kaltum
suke, kuma limamin masallacinda dake jikin gidan labari yakaimasa cewar kalah ta mutu mata a cikin gida suna ihu suna burgima suna yarda zani duk da wasu ihun gani idone kadan ke kukan gaske,
malam da tawagarsa suka dunguma zuwa cikin gida bayan da aka yimusu bayanin cewar malam zai shigo kowacce ta daura dankwalinta sannan suka nutsu yashigo yace a tattaro kowa yazo sannan ya musu nasiha da wa azi me ratsa jiki game da irin rayuwar jahilcin da suke ciki, rayuwar daya na zaluntar danwansa basa taimakon juna yayi kira dasu kama kansu da mutuncin kasarsu yayi musu
nasiha dasu daina ihu da koke koke idan mutuwa tasamesu don duk wani me rai mamacine daga karshe yace zaitafi asibiti yasa hannucewar kalah yar uwarsa ce ayi mata sallah abinne ta gobe da safe,
bayan rasuwar kalah da kwana uku sannan kaltum ta warware ta tsagaita koke koken
da take yi ni tana kwana tanayi idan ta tuna mutuwar lami da kalah saitaji zuciyar ta bugu buf saboda tashin hankali ita kanta ta rasa shakuwa ko abun alkhairi da suka taba mata a zamanda tayi dasu a lokacinda suke raye,
kaltum taji mutuwarnan sosai kallo daya zaka mata kaga rama da jajayen idanuwanta saboda kuka da sanyin safiyyah kamar yanda kaltum da fatsuma suka saba sallace kawai take sayardasu suna sallamewa zasu zari gwalensu su nufi kasuwar markadi sintar kayan miya bawani abun kirki kaltum ke tsintaba saboda zuciyarta ta harba can tunanin masananciyar rayuwa data tsinci kanta a ciki batason Khartoum haka ba dadin zaman garin takejiba dama-dama ta dan tahadu da fatsuma kawa me kaunasta mai karfafa mata gwuiwa, badan fatsuma ba da rayuwa kara yiwa kaltum zafi a khartum kasancewar BABU RAWAN WANI da rayuwar wani babu....
Sai ku hada da part 24 ya xama daya Kenan.
.ADON DAWA 26
.
TRUE LIFE STORY
.
haka mambela yake ta fada abayyane a cikin yarensa na ADON DAWA.
KHARTOUM
lokacinda mambela yake neman dan rakiya zuwa Nigeria wajen kaltum dinsa ya nema ya rasa badon babu kudin jirgiba ko guzirinda zai rike ba,
ita kuwa kaltum bata bukatar dan rakiyar da zai rakata bur sudan wajen mambela matsalarta shine kudin jirgin kasa take fafutukar tarawa abu yaci tura, duk abunda take samu baiwuci ta ci abinci dashiba sauran tasayi omon wanki da sabulun wanka da sauran su,
idan taci sa a ta tara kudi mai dan yawa tafara tarawa sai wani abu ya bullo mata wanda dole sai takashe kamar sayan magani idan batada lafiya ko idan takalminta silifas ya tsinsinke dole ta sayi wani ko idan rigunanta ko lufayanta sun yayyage dole takai dinki.
yau idan akace maka babu mai taimakonka
kodada loman tuwone komai kaiza nema da kanka to babu sauki, kaltum na aiki tukuru don neman abunda zatasa a yan hanjinta kokuma wanda zata iya shiga jama'a ba a toshe hanciba saboda wari ko datti bata hutawa saboda haka tarame tayi kurket tayi duhu rabonta da kitso tun na bur sudan saboda batada lokaci dakuma wanda zaiyi mata amma ita ta iya kitson har gida gida ake kiranta tanayi ana biyanta.
watan azumi ya kama kaltum bata hutawa yini takeyi tana neman abumda zasuyi buda baki saboda azumi.
yau babu masu zuwa gyaran jiki don haka jawahir ta sallamesu tace su daina zuwa sai a satin sallah sannan zasu dawo saboda haka sukafi mayar da hankalinsu wajen tsinta lemo da abarba sufere wajen rubar sukasa a faranti suje su sayar, kasancewar azumine ba acika sayan kayan miya ba akan da, anfi sayan kayan marnari .
sak almajirai ga yunwa ga kishiruwar azumi gasu sun yini a Kasuwa.
wataran suyi sa'a su sayar wataran su yini suna yawo ba a saya ba, dagaa lasa an ya ruba sai afasa saya daman dai masu rangwamen men kudi ne suke sayen irin wannan masu kudi basa dosar nakan farantin yan talla sai wankanku ajere akan tebur ko acikin firij.
ranarda rana takwabe musu kuwa babu mai saya idan akasha ruwa sai su zauna su shanye abunsu babu kudin cefane bare su dafa abincin buda baki da sahur don haka saisu zarzaya gidanda ake raba sadakar abinci da kwanukansu tun kafin dare yayi abincin sadakan yakare,
kunu dagurasa ko sinasirne sukebin dogon layi ana raba musu shizasuci kobasu koshiba su rage na sahur.
kaltum takanyi kuka cikin dare saboda masananciyar rayuwa da take ciki dumin
a bur sudan tawuce irin wannan rayuwarda ta
fatarar abinci. mambela yakara musu jari ita da madina suna sana'arsu kowannensu abinci ya wadaceshi
sun daina bara asatin da azumi zai kare satin
sallah kenan alokacin watan cinikin jawahir ta
bude ake tururuwan zuwa gyaran jiki da gyaran kai saboda kwalliyar sallah a wannan satin kaltum suka kaura gidan jawahir har kwana suke yi suna aiki saboda jama'a,
dogon layin babu masaka tsinke sakar gidan saboda mata a lokacin kudi yayi ta shigo musu baja-baja duk da jawahir ce mai amshewa,
kalilan da ciki take guntsira musu su ta murna.
wasa wasa kuwa suka tara kudi da yawa ana jibi sallah fatsuma ta shawarci kaltum suje
kasuwa su sayi lafaya da takalmi mai kyau suyi kwalliyar sallah kaltum tace ita tara kudi takeyi akwai abunda zatayi dashi bazatayi kwalliyar sallah ba.
fatsuma tayi tambayarta mezatayi da kudi da har bazata ki sayan sutura da sallah ba wacce ko almajirai suna wanka su canza kaya ballesuda suke kudi mai dama.
kaltum taki fada kuma taki saya fatsuma ce tashiga kasuwa tayi sayayyarta tsaf harda sarka da yan kunne
baya ga lafaya da takalmi coge chanjin kuma
taje kasuwa da ake sayar da wayan tafi da gidan ka (g.s.m)tsohowar waya gwabjejiya wacce aka daina yayinta ta saya aka makala mata sim card yadda zataji dadin waya da musa saurayinda take matukar kauna shima a kasuwar markadi yake dako su suke sauke kwandunan kayan miya daga mota zuwa cikin kasuwa.
ranar sallah kowa ya caba ado cas gwanin sha'awa duk wanda yaga fatsuma sai yayi mamakinta kamar ba fatsumar jiya bace mai
barkakkiyar riga da kanannandaddiyar lafaya
saboda rashin guga kanta duk gunji yau kuwa tayi tsaf bakinta har shekin dangwalin yaba yake.
zanen fuskarta wato bille da uku ukun bakinta sunyi radau saboda jar hoda da ta rarrangada ta dambara baki a bakinta da girarta kaikace tabarya ce masayin kwallin,
ta fito kwas kwas kwas daga dakinsu ta leko dakin su kaltum jama'ar gidansu suka ta mamaki kyawun datayi a yau suna tunanin inda ta sami kudi haka,
fatsuma ta dubi kaltum ta girgiza kai don takaicin kin daukar shawararta datayi datakiyi da tuni sunyi anko yayinda kaltum ta fito daga wanka tana shiryawa a tsaye akan buhun kayanta tsofofin riga da siket ta saka burguza burguza sai ta dauko lafayarta koriya itace mai rangwamen tsufa duk da tawanke tas tayi musu karin guga tana kwana akansu kallo daya zaka yi musu ka tabbatar sofaffi
ne don haka batayi kyauba surutu da gori babu wanda fatsuma bata yiwa kaltum ba akan taurin kan da tayi nakin yarda da shawararta.
kaltum bata damu ba shirinta take yi kawai ta linke dukkanin kayanta ta cusa abuhun ta hada bakin buhun ta daure tace da fatsuma zo muje waje na fada miki wata magana suka fito kofar gida suka tsaya kaltum ta dubi fuskar fatsuma taga yadda tayi wuri wuri tanaso taji labari saita tuntsire da dariya tace fatsuma yau zantashi daga garin nan zan kaura garinmu bur sudan
kaltum ta dafa kafadarta tace ki kwantar da
hankalinki zan dinga kawo miki ziyira akai akai ko kinaso kibini idan naje indawo in daukeki muje can mu zauna?
fatsuma ta girgiza kai tace bazan iya zama
da wadannan mutanen naku na ADON DAWA ba,
kaltum ta harareta tace ADON DAWA ba mutane bane ko ba musulmai bane?
fatsuma tace ADON DAWA saike nikuwa sai ADON BIRNI sukayi daria dukansu.
kaltum tace don bakisan suwaye ADON DAWA bane kike fadar haka musulman cikin su sunada kirki, kyauta, sadaka, zakka, sallah, azumi, tausayi, sunada ilimin addini,
masu kudi kuma kyawawa hanci zuwit..
fatsuma tace tunda kina son mambela fa ai dole kifadi haka nikuma bana son ADON DAWA,
kaltum tace ashe bakya sona tunda ni inason ADON DAWA, a kabila daga hausa sai ADON DAWA nafi so,
fatsuma tace inasonki tunda ke bahaushiyace amma fa banason ADON DAWA gashi kuwa sun janyeki zaki koma wajensu duk abunda nafada miki kinki ji sai kintafi din,
suka isa tashar da kafarsu duk da nisa basu damuba sun saba da tafiyar kafa basajin wahalarta.
suka jira har bayan la'asar jirgi kuwa sai bayan magarib zai tashi kaltum ta umurci
fatsuma tazauna acikin wata rumfa wacce aka tanadar don zaman matafiya gasu nan reras a zauzaune suna jiran jirgi,
zataje tayi fitsari idan ta gama zataje wajen ma'aikatan jirgi ta tambayesu adadin kudin tikiti da yadda ake sayansa,
fatsuma ta zauna da buhun kaya a gabanta tana duban kaltum hartayi nisa ta daina hangota tadade bata dawo ba sannan ta dawo tana zuwa fatsuma ta mike tsaye tace gida zata tafi saboda tafiyar mai nisa ne, ita kadai kada dare ya mata,
kaltum tayi tayi su sake zama suyi yar hira fatsuma taki tace gara ta tafi tayiwa kaltum fatan alkhairi da Allah kiyaye hanya tajuya ta tafi.
kaltum tayi kuri ita kadai taci gaba da kallon
masu wucewa kowa da dan uwansa yana hira amma bata damuba, zama kadanne ya rage mata a shiga jirgi tunda magrib ta kusa farin ciki mara misaltuwane ya bayyana azuciyarta ya huda ya fito ta fuskarta musamman da jirgi ya iso anfara bin layi don yankar tikiti kaltum cike da fara'a tabude bakin buhunta don dauko kullin ledar da ta daure kudinta zataje itama tabi layi ta yanki nata tikitin idan ta tuna jirgi zata shiga yanzu bur sudan tana wayar gari zata ganta kusa da mambela da Madina sai taji farin ciki ya lullubeta jitake kamar rufe ido ta bude idanuwanta ta ganta a bur sudan,
ta kasa kwatanto irin farin cikinda su mambela zasu shiga idan sun ganta ta luma hannu acikin kowane sako lungu da kusurwar buhun kayanta taji har yanzu bata jiyo kullen ledar kudinta ba nan da nan ta fara zazzakulo tsummokaran ciki da sauri tana zazzagawa tana ajewa akasa har buhunya zama wayam ba komai amma babu ledar kudin
don haka hankalinta yatashi matuka ta sake bin kowani zani daya bayan daya ko kudin yamakale ajiki amma shiru kakeji bai fadoba, ta tsake wargaza kayanta akasa kowanne siket riga zani ko lafaya saida ta shimfideshi akasa sanka-sanka babu ledar kudin ta,
saita rushe da kuka na takaici yayinda jama'a suka tabbatar ba lafiya ba tabbas akwai
matsala aka taru ana tambayarta bayani take cikin gigita da dinbun damuwa wasu sun yarda ta ita sun kuma tausaya mata wasu kuma bayanenta yamusu kama da tatsuniya gizo da koki ta mallece kawai domin sun saba ganin irin wadannan mutane wadanda dazarar talauci ya ishesu sai suzo tashar suna ihu suna neman taimako kudin mota suce nasu ya fadi idan aka hadamusu taimakon sai su zame su gudu daman ba motar zasu hauba damfarane kawai,
wake daya yake bata gari inji masu iya magana sun shafawa masu gaskiya kamar yanda suka shafawa kaltum kowa ya kalleta
saiya watsar yawuce abunsa ma'ana sunsaba ganin irinsu tuntuni,
kuka take haikam bayani take bilhakki rokon taimako take yi da duk karfin ta amma dakyar ta samu jine goma sha daya ta garzaya bakin wundon mai sayar da tikiti cikin kuka tayi masa bayani game da fayyace masa abunda take nema agareshi tace tana son ya
taimaketa yabata tikiti tatafi bursudan wajen yan uwanta batada kowa a Khartoum, ansace mata kudinta kakaf sai yanzune ma jama'a suka taimakamata da jine goma shadaya ya
taimaka ya karbi abunda take dashi idan jirgin nan yatafi ya barta batasan yanda zatayiba...
wani takaici yarufeshi tikitin jine dari biyu dahamsin ne zai bata a jine goma shadaya?
kallon tara saura kwata ya mata don haka basai yamata magana ba tasan abunda
ke ransa cikin fargaba ta sharce hawayenta ta sake neman wata alfarma cewar to ya bata rancen tikiti suna isa bur sudan yasawani ya bita gidansu ya karbi kudinsa..
cikin wata dankararriyar murya ya fada cike da takaici ke matsami daga jikin wundo kada ki sake dawowa, kika sake lekowa kika min zancen banza sai nasa yan sandan can sun kamaki, kaji mahaukaciya tikitin gwamnatin ne zan baki bashi ?
Sum sum sum kaltum tayi tabar jikin wundonsa batare da ta sake cewa komaiba daman itama tsausayine yasa ta tambayeshi don daga ganin bakar fuskar nan tasa baki kirin da jajayen idanuwansa tasan bazaiyi mutumci ba ga wani tulelen ciki da kiba da kyar yake juyi kuma tun nan kasa tsinke ka huda yace tush haka yake kamar katuwar balobolonda aka cika da iska saita daina
kuka ta sharce hawayenta da yayi mata face face a fuska batada sauran dabaru ko tunani bata da sauran wani tunani kuma ta cire burinta data kudira saitaje kayanta da ta watsar akasa tana kadewa tana linkewa tana zurawa a buhu jikin ta kalau data gama lenkewa saita koma gefe jikin wani dakali ta jingina da buhunta a gefe tana duban jama ar da Allah ya musu rahma wadanda ya yalwatasu da kudin sayan tikiti sai yanka suke suna shiga jirgi,
dukan uku uku kirjinta takeyi tamkar zata fas
ADON DAWA 27
.
TRUE LIFE STORY
.
ta fito waje yayinda takejin wani jiri na takaici na neman yakayarda ita kasa,
kuka yaki zuwa saboda abun yafi karfin kuka, don idan tashin hankali ya afku akayi kuka to akwai sauran rangwamen masipa, amma idan masifa yayi masifa to kukama takansa yake abun yafi karfinsa,
nasihar Madina ta tuna wacce a koda yaushe take shawarta ta yawaita addu'a tana neman tsari daga masifun rayuwa, wanda ko Allah Ya aiko da masifa zata zo da sauki kuma da maganinta ta shawarceta data yawaita karanta InnaLillahi wa ina ilaihi raju un
ako yaushe musamman sanda wani abu naki yafaru,
nan da nan kaltum ta cafko kalma InnaLillahi
wa inna ilaiyi raju un a harshenta tana fada
tanasake maimaitawa saita farajin wanan kululun nan daya shaketa awuya yafara lafawa, bugun da zuciyarta ke famanyi ta sausauta tanaji tana gani jirgi ya cika ya tashi yatafi ya barta, yayinda kuka ya kwace mata tana yi ta nanata kalmar InnaLillahi wa inna ilaihi raju'un ta dade a zaune anan har karfe
sha daya na dare.
saida wani dan sanda ya zagayo ya sake zagayowa ya tabbatar ba tada niyyar tashi daga wajen nan sannan ya tsaya ya tambayeta lafiya take zaune haryanzu cikin kuka?
tamasa bayani yace to ai gara ta tashi ta koma inda tafito saboda zamanta anan bai dace ba, ga dare ya fara nausawa gara takoma ta tara wani kudin zaifi mata sauki saita dawo ta yanka tikitin ta tafi baki alaikum don ba wanda zai dunkule wannan makudai kudin ya bata, don kowa takansa yake yi,
kaltum ta mike ta daura buhunta aka tana zubar da hawaye tafiya take amma dakyar take jefa kafarta ta isa gida zuciyarta tamkar tafashe taci sa'a duk yawancin ankwanta
saboda gajiyar sallah , ta sadada tashiga dakinsu ta ajiye kayanta a lungu tayi sallah ta kudundune alungu yayinda duk sanda ta rintse ido saita tayhango Madina da mambela sai ta fashe da kuka.
washegari da safe kaltum taci karo da yan gidan a lokacin da ta fito daga bandaki zatayi alwalar sallar asuba, mamaki mara misaltuwa zaka gani a fuskokinsu
musamman ma kawarta fatsuma,
lah kaltum baki tafi ba?
Meyasa baki tafiba ?
Amsa ya gagari bakin kaltum saitayi shiru tana tunanin abunda zata fada sai can tayi dan murmushi karfin hali tace fasawa nayi ai tun jiya da daddare na dawo,
kika fasa meyasa ?
Suka sake tambayarta ko amsa bata basuba taci gaba da alwalarta kawai,
fatsuma tayi dariya tace gaskiya naji dadi dakika fasa don har ina tunanin yanda zandinga yawo nikadai a garin nan gara muyi zamanmu anan, kaltum ga wuta ga ruwa ga titina ga wayar sadarwa ga samarin birni mezakiyi a bur sudan?
kince babu wuta baruwa babu network na waya gaku a zaune a makabarta duk kabarurruka a dakunanku na katako kamar yadda kika fada min...
sai ko wacce ta tsoma bakinta tanayiwa kaltum nasihar tayy zamanta anan kada ta koma kauye suma yan kauyen addu'a sukeyi sudawo birni.
ta mike sam ta shiga daki batare da tare da tayi musu magana ba, takaicinda ya isheta ya isheta kauyen nan da suke kushewa ita yafi mata birninnan dasuke muradi
kamar yadda suka saba kaltum da fatsuma suka bazama neman na abinci duk da sallah ce amma sunyi sammako suntafi kasuwar markadi , ahanya suna tafiya kaltum ta dubi fatsuma ta langwabar da kai gefe tace bakisan abunda ya sameni bako?
Fatsuma ta dubeta cike da mamaki tace bansaniba me yafaru?
Kaltum tayi ajiyar zuciya tace sace min wannan kudin nawa duka akayi ban gan su ba shiyasa bantafi ba .
fatsuma ta zabura ta dauki dogon salati game da dafe kirji ta tambaya cikin gigicewa yanzu wannan kudin an sace su dukka?
Fiye da jine dari bakwai nefa yanzu wa kike zargin ya dauke miki a dakinku ko atasha aka
dauke ?
Hawaye ya sirnano daga idanuwan kaltum
ta girgiza kai tace bansan inda aka daukeba ni dai nasan ko a daren shekaranjiya ana gobe zantafi kenan saida naga kudin harna sake kirgawa na daure na mayar asanda zamu tafi tasha dai ban duba ba wata kilan sanda nashiga wanka aka dauke,
fatsuma tace watakilan sanda kike kirgawa wata ta ganki kina tashi ta dauke,
nidai kina ganin sanda na dauki buhunki bansaka hannu acikiba agabanki na ajiye miki a tasha natafi, kuma niban hudaba nazakulo da Kinga buhunki huje....
kaltumta zabura tace nifa bance kekika daukanmin kudina bafa ko a mafarki nasan
baza ki min sataba,
suka cigaba dajajatawa har suka isa masana'antarsu wato babbar bolan da suke
sintar kayan miya suka fara gudanan da ayyukansu kamar kullun,
Abbas dai yanakan bakansa na naci dabin kaltum aduk inda take, a yau ma ya riskesu a inda yake tunanin zai samesu adaidai lokacin daya san zai riskosu , yakwada sallama cikin wata kamilalliyar murya mai sanyaya zuciya
lokaci guda suka daga kai don gani mai wannan sanyayyiyar murya sai sukaga fuskar Abbas cike da murmushi irin wannan murmushi fatsuma ta mayar masa gami da amsa sallamar itama a yayinda abangaren kaltum akasamu akasin haka, domin jitayi ranta ya baci nan da nan ta tsuke fuska takawar dakai gefe yasake tsungunawa kanta ya rafka sallama don dama ita yakewa sallama, kuma ita yakeso ta ansa ba fatsuma ba,
kaltum ta fusata ta mike afusace tafada cikin fushi Abbas karabu dani kakyaleni in sake saboda ni ina da mijina a bur sudan don haka kaje kanemi wata,
fatsuma tarike baki don mamaki game da
fargaban kada kaltum tajawo musu dan kudin da dan turaren da yake basu ya pasa,
fadi take ke kaltum me haka karya takeyi batada miji a bur sudan,kaltum taji tamkar ta zageshi,
kishi da tsantsar fusata suka damki zuciyarshi yacije lebe yace nikike fadawa wannan magana kizo kasarmu kinacin arzikinmu dan kin samu anasonki shine zaki zageni?
To zan nuna miki ko ni wanene, ya juya yatafi afusace.
fatsuma na kwala kiran sunan shi tana bashi hakuri yayinda kaltum ke tunzurashi tana cewa ya tafi din wazai tsoratar babu abunda
zai sameta sai alkhairi,
fatsuma ta fara yiwa kaltum fada itama dayake zuciyar akusane saita hargitsa suka hau hayaniya kamar zasu cinye kansu,
ranar dai kowa gabanta takama ba a tafi tallar tareba haka basu daura tukunya dayaba sai washegare fatsuma tabiyo wa kaltum suka hadu suka tafi tare kowaccensu ta huce sai hira suke suna wasa suna daria,
gidan jawahir mai kunshi suka fara zuwa don suji sanda zasu fara zuwa aiki tunda tace musu sai bayan sallah zasu dawo sai suka tarar ana zaman makokinta, Allah Ya mata rasuwa ranar biyu

Please Login or Register in order to submit comment