Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

luhu-luhu a kumbure idan ba an fada maka ita ba ce babu yadda zaka kalleta sau daya ka gane ta. da kyar kalah ta daga hannun ta fada cikin wata shamulalliyar murya marar kuzari, 'zo nan kaltum, zo wajena, kun ga yadda Allah ya yi da ni. na cuce ki, amma kaina na cuta' kaltum ta matso a hankali ta raba ta zauna a gefen gadon kalah tana mata duban tausayawa,hawayen dai bai tsagaita ba daga idanuwan kowaccensu, su ukun har da asabebe.
kalah ta kara da cewa,
'me za'a yi da halina, me za'a yi da zalunci, cin amana da damfara?
kaltum, na damfari iyayenki ,nacuce ki ,najawo kaina.shin me kudin nan dana cuce ku ya karamin yanzu?
mezamu fada wa Ubangijinmu nida lami ?
kuka me yawa ya ruftowa kalah takasa
cigaba da bayani asabebe nashafa hannunta tana bata hakuri tana cewa daina kuka kalah fuskarki duk dinkine kada ya sake kuburi yihakuri kaltum tariga tayafemuku,
kalah ta fara magana cikin nadama Allah ya yafemin ,kaltuma kiyafe min inkinje gida
kicewa alhaji adnan yayafemini domin naci amanarsa akwai wani Inuwa agent dan Daura ne wanda duk shiyakawomu nan shi alhaji adnan yaje yasamo har Daura ya tambayi inda kike inuwa agent yace ya dade baiyi wannan harkarba ta kawo mutane sudan saidai zaisa a binciko inda kike bansan inda
inuwa yasamo labarin bur sudan ba andai tabbatar masa kina cen saisuka shiga tunani yanda za ayi adaukoki da farko shida alhajinne suka shirya tahowa bur sudan dinsu taho dake sai gani kwasam nabugowa inuwa agent waya inaso yakaiwa 'yaya na wayarsa muyi magana dasu don basuda waya sai kuwa yaji dadi daganin numbata
daganan sai labari ya canja cewar intaikesu in dauko musu ke daga bur sudan in dauraki ajirgi kitafi kano nan da nan na kalallamesu da dadin baki danaji maganan kudin jirgi na
nunamusu ciwon 'ya mace na ' ya mace ne, d'a ai na kowa ne, na daukan musu alkawari zan kawo musu kaltum har gida kada ma su bata lokaci da kudin jirgi har na mutane biyu zuwa da dawowa ga wahalar zuwa bur sudan godiya iri iri da shi albarka suka dinga mini basusan abunda na kudurta azuciyata ba
mukayi lissafin kudin jirgin kasanda zai kaini bur sudan da wanda zamu dawo Khartoum ni dake da kudin abincinda za muci a hanya sannan da kudin jirgin sama nawa da naki daga Khartoum zuwa kano hatta da kudin taxi da zamu hau daga filin jirgi zuwa unguwarku saida ya lissafo ya aiko min .
Inuwa agent yasan inda suke tura kudi daga wapa zuwa nan khartum har gida suka bawa mai canjin adireshina da lambar waya ta saigashi yakawo min makuden kudi nan shaidan ya zugani naji bazan iya kashesu ta hanyarda aka umurceni ba abunda nake
nemane ido rufe shekara da shekaru muna fafutuka a sudan mun kasa hade kudi mu karasa saudiyyah .
da gudumawar shawarar 'yata lami na nade kudi na boye nayi zamana na manta da alkawarinda na dauka .yawan damuna da wayar da alhaji.adnan da inuwa agent ke yi ga wa' azi da gargadin da kawayena wadanda agabansu na karbi kudin ke yi shi yasa na canja shawara inje bur sudan in dauko kaltum insakata amota ta tafi kano ita kadai sauran kudin in rike, inasaka ranar tafiya bur sudan natsami mai tafiya Hauwa saina bata sako ta taho min dake zuwan ki khairtum naji
bazan iya cire zunzurutun wannan kudi ba in biya miki kudin motar zuwa nigeria ba don haka nacire numban wayata na yar yadda su inuwa agent ba za su sake samuna a waya ba balle su dame ni da tambaya, domin duk karairayin da nake shirga musu sun kare, ban san kuma abun da zan dinga fada musu ba.''
kalah ta fashe da kuka mai tsanani, yayin da kaltum ta ji kukan da ta ke yi ya kafe, takaici ya ishe ta, ta tsurawa kalah ido tana dubanta tana tuna irin wannan cin amana da son zuciya irin ta mutanenmu.
asabebe kuwa fadi ta ke,
''cafdijam! duniya ina zaki damu?
kalah, kin yi kuskure a rayuwarki. me kudin nan zai yi miki a rayuwa, ki ka sani idan da
kin kai musu 'yarsu su baki fiye da abun da suka turo miki tun da masu hali ne?''
kalah ta jima tana kuka kafin ta ci gaba da
magana. ta ce 'na yi niyyar yin biza ta kirki mu yanki tikiti mu hau jirgi mu shiga makkah yadda doka ta tsara sai kawayena suka bani shawarar kada in kashe kudina. ni da kawayena guda biyu da tshohuwa daya muka shirya tafiya makkah ta barauniyar hanya''
kaltum ta tambaya cike da neman karin
bayani, 'ta barauniyar hanya kamar ya ya?
kalah ta matse hawaye tace
eh ta barauniyar hanyace domin da tsakar dare ake fara tafiya alokacinda jami' an tsaro ke barci ko ince babu kowa a kogin sai ahaye saboda hatsarinda ke tattare da tafiyan da
rashin tabbas ba ama biyan me kwale kwalen harsai yasallakar da ku saboda adayan biyu kuke ko kuhaye ko akamaku, ba makkah zai tsallakar da ku bafa wasu kauyukane agefen ruwan suma en kauyen sana'ar da suleyi kenan kuna isowa cikin dare sai ku biya me kwale kwale kudinsa yacika aikinsa sukuma en kauyen sai su kwasheku cikin sanda da leke-leke sai su shigar daku cikin gidajensu cikin gidanma a cen kuryar daki karkashin gado zasu boyeku saboda jami'an tsaro na iya zuwa bincika ko akwai irinmu idan bakuyi sa a ba aka kamaku to tabbas daku da matafiya da masu gidan zaku fuskanci fushin hukuma ,
kasancewar akwai wasu daga cikin yan kauyen da suke kaiwa jami'an saro gulma idan ansami labari irin wannan sai suzo
sufara bincike gidajen daya bayan daya dan haka ake tsoron boyemu saidai wadanda suka tari aradu da ka ne basu daina ba
kaltum ta gyara zama taci gaba da kurawa kalah ido tanasonjin karshen labari .meya hada duk wannan labari da mummunan
hatsarinda suka samu harda rasa rayuka ?
takaici ya isheta da takejin hanyoyin karya doka da mutanen mu yan nigeria keyi adole sai sun shiga makkah alhali a makkah dimma a wulakance suke koda yaushe askarawa nabin su da gudu suna kamawa suna dawo dasu kasarsu suba ibadar suke samu suyi
ba sai neman kudi yaki halak yaki haram ana kyararsu ana korarsu, kaltum tafi bukatan ta dauwama a sudan da tashiga makkah saboda tasan azabarda tasha awancan karon
kalah ta katse mata tunani taci gaba da cewa kamar yadda aka mana bayanin yadda akeyi idan kukayi kwanaki kamar biyu a boye agidan kauyawan nan idan suka tabbatar yan saka ido sun daina zargin an boye mutane hankalin kowa baya kansu da tsakar dare sai su fito daku ta bayar gari sununa muku hanya ta inda zakubi ku bulla jidda sannan kubiyasu kudin aikinsu to da dabara da boye boye ga yar karan tafiya mai yawa har ku samu kushiga jidda shikenan hukuma batasan kun shigo ba daganan sai kowacce tayi ta kanta idan ajidda zaku zauna to idan mota zaku hau ku tafi makkah ko Madina to yarage naku,
asabebe tace ni abunda banganeba ku a ina
kakayi hatsari har kuka sami raunuka haka ne asudan ko a saudiyyah ?
Kalah ta girgiza kai yayinda ta zubo da hawaye daya cika mata ido tace a sudan abun ya samemu bamu kaiga hayewa ba bamu dade da fara tafiya ba a cikin kwale-kwalen mu biyar ne dukka matane sai matukin ne kadai na miji kamar yadda na fada muku da tsakar dare ake fara tafiya a lokacin da duk wata halitta ke barci a hankali yake tuka jirgin ko tari bai umurcemu muyi ba balle magana muna cikin tafiya kwasam
saiya hango haske daga nesa an haskemu da alamar babbar jirgine na ma'aikata sai mu kaji magana da lasifika ana umurtanmu
da mu tsaya a inda muke kasancewar yanada labarin irin mummunan hukunci da za ayi masa idan aka kamashi sai ya gigice ya fara azazzalarmu yana daka mana tsawa waimu fice masa daga jirgi ganin ya gigice sai muma muka fishi rudewa don haka mun manta a tsakiyar ruwa muke saisu dukansu harda lami suka daka salle cikin ruwa ba a kara ganinta ba saidai mutsu-mutsunsu tunda basu iya ruwaba suduka suka mutu nice naki fita ina ta ihu na dora hannu a kai kiran yata lami nake shiru lami bata amsa ba ta lume cikin ruwa bankara ganinta ba ashe bazan sake ganin ta ba har abada?
Su dukka ukun suka fashe da kuka a lokaci guda cikin kuka kalah taci gaba da cewa baidaina yimini tsawa infice masa daga jirgin kwale kwalensaba amma naki fita gudu yakeyi yana wuce kima musamman dayaga hasken fitilar nan ya nufo mu aguje arashin sani baisan ta inda ya nufo ba ashe wani gungumemen dutse yanufo a gaban ruwa jirginmu ya daki dutsen mu mu duka muka tarwatse mukayi sama muka fada cikin ruwa damu da jirgin namu ni kadai nayi rai gawarwaki biyar aka fitar daga cikin ruwa har da direban mu nice asume da wadannan raunukan
ina fatan nima zan mutu inje inhadu dasu lami don bani da anfanin zama aduniyannan sai kalah tarushe da kuka yayinda kaltum ta sunkuyar da idanuwanta da sauri kasa hawaye yana kwaranya saboda tausayinsu lokaci me tsawo babu wanda ya iya magana a cikinsu can kaltum ta dago da luhu-luhun
idanunta tadubi kalah tana magana cikin marainiyar murya tace kalah na yafe miki nayafewa lami Allah Ya yafe mana
gabaki dayan mu,
sai kalah ta rushe da kuka me karfi har saida
majinyatanda ke kwance asauran gadajen suka firgita yayinda ma'aikatan jinya suka yi tsawa suna cewa kalah ta rufe musu baki tana damun marasa lafiya tamkar xugata suke ai sai ta bude baki gaba daya tana rusa ihu magana take cikin harshen larabci yadda kowa zaiji tace na zalunci kaltum na zalunci
kaina akan abun duniya idan na mutu mezance wa Allah ?
ban mori kudin ba ko sisi ya watse aruwa na rasa yata lami na rasa lafiyata nibanje makka ba kuma sunana yabace a garin mu saboda inuwa agent zai fada wa dangina abun kunyarda nayi
hankalin kaltum da asabebe a tashe suka dinga rufe mata baki suna danneta don kada taci gaba da tonawa kanta asiri saboda abun ya zame mata tamkar tabin hankali daga karshe su ma su kaltum aka koresu waje yayinda aka dannawa kalah allurar barci a cikin karin ruwan da ake yimata tun tana magana har ta fara lunshe ido,
kaltum da asabebe suka fito wajen yan uwansu kallo daya suka taro su suna jero musu tambayoyi, kaltum ba ta iya magana ba
gefe dasu ta tsugunna ya yinda asabebe take kora musu bayanin abubuwan da basu sani ba muryar daya daga cikin ma'aikan jinya ce tace dasu kuje ku suyowa kalah abinci mai ruwa kamar lemo da shayi tunda aka kawo ta bataci komai ba nanfa aka hau kallo kallon aka rasa wacce zata ce wani abu
sai kowannensu tafara cewa ban fito da jaka ba a'a bubu canji da na bayar,
cikin marainiyar murya kaltum ke rokarsu tace dan Allah ku taimaka mata a suyo mata shayi tasha bakin ta ya bushe babu abinci banida kudi ni kuma,
da kyar uku daga cikin suka fitar da wahid jine dai dai salas jine kenan suka ba wa kaltum ta falfala bakin get ta siyo shayi kofi daya da gutsiren biredi ta shiga ta kai wa kalah. Ta iske ta a kwance barci na fisgarta sama-sama amma tana kokarin bude ido
kadan-kadan magana ta ke yi,amma ba a ji,tabbas ruwa ta ke cewa a bata.
kaltum ta daddage ta dago ta zauna zauna gami dayimata weji da filo a bayanta ta dan kishingide duk da karin ruwa da yake hannun ta ga karaya a daya hannun kaltum ta dinga tarfa mata ruwan shayi da cokali a bakinta duk da ta kasa tauna biredi amma ta shanye ruwan shayin tas,
a bandakin dake ciki kaltum tashiga taryo ruwan fomfo a kofi ta kawo ta dinga tarfa mata abaki sannan kalah taji dama-dama kaltum tana gyara mata kwanciyarta saikuwa
tarufe ido ta fara barci mai, nauyi kaltum ta lullube mata jiki da mayafinda ke gefemta sannan tajuya zata fita yayinda tayi arangama da ma'aikaciyar lafiya mai kula da kalah sai ta miko wa kaltum wata zungureriyan takarda ta magungunanda ake
bukatar da ruwanda za a dinga kara mata tana bukatar karin jini kije kukawo,
hankalin kaltum yatashi dataji batun kudi ko
sekon daya bata karaba tace wa matar wallahi banida kudi matar ta harareta tace daman ina kikaga kudi ?
Ki kaiwa iyayenki manya suje su sayo su kawo yanzu,
kaltum tajima a tsaye tana juya takardannan
sannan ta fara tafiya asanyaye ta isa inda har yanzu yan gidansu suke saye ta dubesu daya bayan daya ta fada cike da fargaba saboda shayin jine uku da kyar suka biya balle a ce an ambato irin wadannan makudan kudi tana ambaton musu jerin magungunan suka tabbatar kudin ne mai yawa sai ko waccensu ta fara hada yanata-yanata ma'ana kowaccensu ta zazzage zaninta ta juya ta kalli get din fita kaltum tayi narai-narai da ido kamar mai shirin yin kuka ta fada cikin damuwa ku taimakawa kalah ance bata da jini a jikinta kar ta mutu,
waye mai jini ajiki ?
ai dukkanmu nan idan aka tsaga mu baza a sami jinin kirki ba, shafa'u tafada dai-dai sanda ta fisgi hannun yayayyiyar yarta ta kara gaba ai sai duk sauran suka bi bayan shafau
magajiya ce ma dai ta dan tsaya tabawa kaltum shawara cewa ta taho suyi tafiyarsu kawai tama daina damun kanta kada ma
ta sake zuwa asibitin balle su ganta su tambayeta kudin magani idan sukaga shiru ba yan uwanta gwamnati ce zata dauki nauyinta koda kuwa anzo gida neman yan uwanta kada ta sake tace ta santa ma ko mutuwa tayi sun san yadda zasuyi su bunne ta,
kaltum ta kame a tsaye tana duban ganin
ikon Allah tana tambayar zuciyarta wai ina soyayyanda sukeyiwa kalah a da?
me dalilin rusa kukanda da su asabebe
keyi na tausayin kalah daman bana gaskiya bane ?
idan tausayin ta sukeji da gaske ai zasu siya mata magani donta warke inhar suna son ta rayu,
magajiya ta juya ta tafi da taga alamar kaltum bata da niyar binta sutafi kaltum tayi zaman ta akasa tana rike da doguwar takarda a hannu sai yanzu ta sake tuna madina wacce ta tsaya tsayindaka wajen kula da ita, da haka za a barta a yashe har sai ta zama mushe babu wacce zata taimaki wata da karfinta ba ma da kudinba?
hawaye ya kwaranyo daga idanuwan kaltum tahada kai da gwiwa tana kuka a bayyene take kiran sunan madina da mambela fadi take meyasa aka kawoni garin da wani baya
taimakon wani?
kaltum kaltum ?
muryar wata mace taji daga
wundon gadon da kalah ke kwance tayi farat ta hango ma'aikaciyar jinya a tsaye nanda nan ta mike aguje yayinda zuciyarta ta hau bugawa tana fargaban abunda zata shiga
ta iske tana karasawa kalah ta duba saitaga tana numfashi duk da idanuwanta arufe suke tayi ajiyar zuciya jin dadi tunda ba mutuwa tayiba AlhamduLillah, ma'aikaciyar jinya tadubi kaltum ta yatsune fuska tace kidubi jikin mahaifiyarki ki gyarata,
kaltum ta tambaya cike da rashin fahimta in gyarata kamar yaya?
tayi mata tsawa dakika shigo bakiji wariba?
to kashi tayi gaba daya dakin yakidime da wari kalah fa tana damun marasa lafiyanmu
mun fara gajiya wata ma'aikaciya dake bakin kofa ta toshe hancinta tace wai a tarkatasu mana sukoma kasarsu Nigeria suje cen su karanta, dayan nurse din ta bata amsa, da inafa ?
ai bazasu tafiba ko tsaga jikinsu akeyi da reza kamar baki san su wajen naciba ?
ai ita wannan ko en uwanta sunzo daukarta
baza a bari ta tafi ba saboda yansanda ne suka kawota takardan sammacinta daga kotu tana cikin file dinta da zarar ta warke
kotu zasu shiga ayi shari'a da ita saboda karya dokar da tayi wajen haurawa makkah ta barauniyar hanya,
nandai ma'aikata da leburori harda masu zaman jinya da majinyata suma suka tsoma bakinsu suna Allah wadai da irin rayuwanda yan Nigeria keyi musu akasa jikin kaltum yayi sanyi ta koma jikin gadon kalah ta tsaya tadade a tsaye tana kallonta batare da tasan yanda zatayiba har yanzu ma'aikatan tsawa suke mata wai tsayuwar me takeyi bazata fitar musu da warin nan dake damun su ba ?
kaltum taje gadonda ke kusa da kalah tace don Allah ku bani aron bokitinku idan nacire zani sai in wanke,
nan da nan suka zaburo sukace badai da
bokitinmu za'ayi wankin kashi ba, bazamu bayar ba.
ta sake matsawa gadon kusa dashi tace subata aron bokiti amsar da suka bata tafi ta wadancen muni cemata sukayi ta matsa tabasu waje ko su mareta tasake matsawa dayan gadon tace su taimaka mata da sadakar omo ko sabulu sai taje bakin
fomfo ta wanke shima sukace ta tafi tabasu waje baza subayarba
ranta yabaci yayinda ta fara jin wannan yanayin na ko a ayi rai tabbas da alama kaltum sai ta dawo da halin nan nata na baya na yar agulla sannan zata kwatowa kanta yanci da yancin kasarta ta cije baki ta gyada kai tajuya a fusace ta isa gadon da kalah ke kwance bata damu da ciwuka dake jikin kalah ba sai ta dagata ta fara goge mata jikinta gaba daya zanin jikin ta da mayafinda akafuta ya baci don haka ta warware lufayarta ta raba gida biyu ta tsaga ta daura rabin a jikinta yayinda ta lullubawa kalah rabinta ta cukuikuye kayan kashin a hannunta
ta fice a fusace wari ya turnuke dakin musamman idan ta zo giftawa sai kowa ya toshe hanci tafice daga dakin harta kai baranda waje sai taji an kwalla kiran sunan ta tajuya da sauri sai taga ma'aikaciyar daya ce tabiyota dauke da wani gumtun
sabulu ta wurga mata a wulakance game da cewa ga sabulu nan sai ki dauka kije ki wanke mana zanin gadonmu wani kallon
sama da kasa kaltum tayi mata ta kada kai tayi gaba ko kallon sabulun batayiba mamaki yakama ma'aikaciyar ta rike baki tana mamaki kaltum ta wuce zuwa wani bandaki dake tsakiyar asibiti zata shiga kenan saitaji an dafa bayanta ta juyo da sauri sai taga wata matace wacce gadonta ke kallon gadon
kalah me suna Aishah bata cikin wadanda suka hanata aron bokiti da sabulu amma tana zaune a dakin sanda ake maganar daga dukkan alamu kaltum ta bata tausayi shine ta biyota da bokiti da kullin omo tamikawa kaltum kaltum ta girgiza kai tace banaso kibar shi kawai Aishah tayi kasake da alama bata ji dadi ba dan kaltum bata karba ba tasake bin kaltum cikin bandaki tace ai fushi ma bai kamakiba tunda baki dashi,
kaltum ta juyo afusace tafada cike da takaici tace idan saida sabulunku da bokitinku yan dakinnan zanwanke zannuwan nan to gara asani gaba ace insude da harshena har sai sun fita,
mezanyi da sabulunku ko bokitinku ?
zanfita inyi bara in samo omo tunda daman munsaba sudan bakasarmu bane kunyi
gaskiya nacinda kuke ambato gaskiyane munzo mun nace muku a kasarku bamuda zuciya duk abunda ake yimana mun ki tafiya ku yi hakuri ba dukanmu bane ma....
ADON DAWA 23
.
TRUE LIFE STORY
.
masu son zaman kasarkuba dayawanmu
kaddarace muma badason ran mu ba dolece,
a bakin bandaki aka tsatstsaya ana kallon su kaltum yayinda mamaki ya rufe yan kallo suna tambayar meyake faruwa ne meyakawo zancen zama akasar sudan?
kaltum ta wuce wajen fomfo batare da ta iya tsayawaba tabasu ansa ba Aisha ce ta tsaya tana bayanin abunda yafaru, gaba daya suka bawa kaltum gaskiya suka bawa ma'aikatan da yan dakin rashin gaskiya koba yan kasa bane ba ai musulmai ne, wulakanci bashi da dadi kuma yan sudan nawa ne a nigeria sunacin arziki abun duniya suke tarawa a Nigeria su dawo sudan suna zagawa,
akwai auratayyah asakaninsu dan haka
anzama daya,
aka cika bandaki ana bawa kaltum hakuri akanta karbi bokiti da omo tayi wanki taki karba tace ai ta rantse indai bokitin yan dakinne bazatayi anfani dashiba
saida wata tabata sabulu sannan ta karba na
aishane bazata karba ba tunda tana dakin tana ganin wulakancin da akeyi mata bata fitar da ita kunya ba sai daga baya zata biyota saboda kar yan dakin su tsaneta kome?
kaltum rigima da kyar ta karba sabulun ta wanke taje ta shanya igiyanda dake gaban dakinsu tashigo dakin tana kallon kowa daya bayan daya jira takeyi ayi magana tayi tsiwa babu mai iya hada ido da ita domin Aisha
takawo musu labarin abunda kaltum tafada abandaki
ta isa gadon kalah har yanxu shirkif take cikin barci, ta fada abayyane cikin harshen larabci kalah zantafi cikin gari insamo miki abunda zakici nabar amana agurin ALLAH domin Shi Ya halacci talaka Ya halacci me kudi ya halacci dan sudan ya halacci dan Nigeria
sai kowacce tayi kiri-kiri tana duban kaltum sunsan magana ta yasar musu ta wuce kere-kere ba mayafi kasancewar taraba mayafinta gida biyu ta rufa kalah
ma'aikatar daya ta dubi kaltum ta gyada kai
tace lalle yarinyarnan batada mutunci ashe.
kaltumta murguda baki ta fice yayinda suduka suka bita da kallo kaltum nashiga gidansu matan gidan sukayo kanta suna tambayan yaya jikin kalah an sayi magungunan kuwa?
Wannan tambayan nasu ta bata mata rai don haka bata basu amsar tambayarsu ba ta kada kai tayi daki,
buhun kayanta ta jawo ta bude ta daura wata lafayan tacire ta jikinta, yau zancen wanka babushi tafice ko wacce taja bakinta tayi shiru babu wacce ta sake tambayarta komai sunga ranta yabace kuma sunsan basu kyauta ba kallonta sukeyi harda lekenta akofar gida su ga inda zata nufa asibiti ko
kasuwa,
hanyar kasuwa ta nufa don haka suka gaskata neman kudi zataje
nan suka dasa kujerar gulma cewa banda
yarinta ma meyasa kaltum zata damu kanta akan kalah, matarda ta cuceta takawota Khartoum ta wulakantata ita da yarta , kaltum babu abunda basuyi mataba na wukanci
fatsumace ta hango kaltum ahanya yayinda tafito daga wani gida ta bullo da gudu ta iso inda kaltum ke tafiya ta dafa bayanta firgigit ta tsorata ta waigo da sauri sai taga fatsumace sukayi murmushi alokaci guda fatsuma tace yaya jikin kalah, kin san fa tsoron asibiti gareni shi yasa banbiku asibiti ba,
kaltum ta tabe baki tace bai kamaki bane dole dakinje,
fatsuma tace banda abunkima inake ina zuwa duba kalah duk irin muguntan da tayi miki mezakije kiyi mata koda mutuwa tayi ma ina ruwanki?
kaltum tayi murmushin karfin hali tace muna yiwa Allah laipi muroke Shi Ya yafemana meyasa bazan yafewa kalah ba?
yarta lami ta mutu meyasa bazan taimaketa ba tunda bata da kowa?
fatsuma ta tabe baki tace lallai kaltum dama haka kike da tausayi kamar lokacin Sahabbai?
kaltum tayi daria, saboda na hadu da lalurar rashin lafiya nima Madina ta taimakeni yayinda sauran suka gujeni shiyasa na kudiri niyyar taimakon duk wani mara lafiya acikinmu tunda muna kasar da ba namu ba, babu iyaye babu dangi,
fatsuma tayi ajiyar zuciya tace gaskiyane yanzu ina zakije ?
Kaltum tace kasuwa zanje na nemo wa kalah abinci kafin magariba fatsuma ta yamutse fuska tace mezaki sayar kisami kudi?
kaltum tace bara zanyi .
fatsuma ta dafe kirji tafada a bayyane cike da fargaba bara?
Bara fa kikace kaltum to Wallahi ba'a bara anan sai akamaki akaiki Chad ko maiduguri ayar, nan ba bur sudan bace babban birninsu ne ba a wannan rashin hankali kame akeyi.
kaltum tayi kasake tana tunani to in banyi bara to mezanyi na sami kudi tunda sana'ar tamu ta sassafene kawai muma sau daya samu muci abinci ko sau biyu saikuma wata goben....
fatsuma ta katse tunaninta tace yanzu nan da ganni daga cen gidan nafito nasami sabon aiki da yamma zandinga zuwa kuma kudi da abinci matar tace zata dinga bani kullum.
kaltum ta tambayeta cike da fara'a wanne
irin aikine ?
*fatsuma tayi murmushi tace gidan kunshi ne
da gyaran jiki (alewa da dilke )matane dankar suke taruwa ana bin layi ita kadaice don haka aiki yayi mata yawa take neman masu tayata kamar masu yi mata aikin gida da masu wanke wa mutane lalle da shafa mahallabiya nidai renon jaririyarta neke yi mata yanzu ma aikena tayi insayo mata mahallabiya akasuwa zo muje ki rakani saimuje gidan tare ki dinga tayani aiki idan kikaci sa'a kema saita daukeki aiki,
tafiya sukeyi fatsuma hira takeyiwa kaltum yayinda ita kuma addu'a kawai takeyi azuciyarta tana fatan Allah Ya taimaketa matarnan tadauketa aiki asirinta yarufu ,
akusa da mai sayar da mahallabiya akwai masu sayarda madarar turare anan ne kaltum tahadu da wani farin saurayi mesuna Abbas,
kallo daya ya wa kaltum yaji zuciyarsa taharba ta tsansar kaunanta ya dinga shisshige mata yana tsoma baki acinkin cinkinsu ko kallo bai isheta ba domin ita duk abunnan da akeyi hankalinta na gun aiki da tunanin halinda kalah ke ciki, saida Abbas
yamiko mata kwalbar turare

Please Login or Register in order to submit comment