Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da marar lafiya ne yana neman taimakon gaggawa.” Na fada cikin mamaki marar lafiya a gidana kuma? Me xan yi masa ni da ba likita ba, kuma ko ni likita ce gidana ya kamata akawo shi ba asibiti ba?
Sai na ji mutumin ya hargitse yana Magana a fusace y ace “ina Magana ne akan mai gidanki daya yi hadari a hanyarsa ta xuwa onisha, gashi nan rai a hannun Allah be san ma a inda yake ba, jini ne ke xuba.”
Na ji gaba daya tunani naya hautsine na rasa me yake fada, kafin in ce wani abu ya kara da cewa “muna nan a kofar gidanki ki xo idan baki xo ba nan da mintina goma sha biyar xamu ajiye miki shi a kasa mu tafi da motar asibiti ce na roka aka kawo mu tun daga onisha dan kawai na ceci ransa ya na gama fada ya kashe waya.”
Kaltum ta dafe kirji t ace inna lillahi wa inna ilaihi ra ji’una, waye wannan marar lafiyar ko dan uwanki ne daga onaca? ”
Madina ta share hawaye t ace “xaki ji ko waye, ki ci gaba da saurarena. Mutumin na kashe wayarsa sai ga lambar mukaddam ta shigo na yi sauri na amsa jikina na rawa. Sai na ji y ace “sister madina wai me yake faruwa ne da Abba? Na ji ana ta kirana da lambar sa idan na dauka sai na ji muryar wasu inyamurai daga karshe ma naji wayar a kasha.”
Na ce “nima ban sani ba, amma ka je gidan su ka duba shi ka gani.”
Sai mukaddam yace “ai Abba baya gida tun da asuba na kaishi tasha yahau doguwar motar xuwa onisha.”
Sai na dora hannu a ka, n ace “inna lillahi wa inna ilaihi raji’una. Mukaddam me Abba xai yi a onisha? ”
Sai y ace “babu yadda ban yi ba kada ya je y ace sai ya je wajen ‘yan uwanki su bashi kwatancen inda xai samu yayanki innamani a enugu, yana ganin idan ya nemo miki yayanki uwa daya uba daya wanda shine kadai dan uwanki wanda rashin sanin inda yake yana damunki to yana ganin xaki dan tausaya masa ki aure shi ki tabbatar da gaske yake sonki da aure. Abba yace kada na fada wa kowa a gidansu baya so ki ji.”
Ai ko rufe bakinsa bai yi bana katse wayar na rusa ihu na yi bakin titi da gudu, saura kiris mota ta kade ni na tsayar da mai babur nahaye da sauri, kawayena da gudu suna kirana tuni mai babur ya figa da ni, ce masa nake kara gudu malam yi sauri bamu tsaya a ko ina ba sai kofar gidana, a inda na hango motar asibiti da marar lafiya a kwance abaya tamkar gawa sai wadansu maxa guda uku. Na karasa gare su ina karkarwa suka bude min bayan motar na leka dakyar na gane Abba daga kafarsa na shaida shi amma babu mai gane fuskarsa saboda ta yi kaca kaca da raunuka. Kunnensa ma an manne shi dan saura kiris ya fadi dan haka fuskar ta kunbure sumtum an nade da bandeji fari, bashi da riga se dan gajeren wando saboda dorin karayar da aka yi masa a hannun hagu da kafar dama kara bibbiyu sai kafadarsa wani katon rauni ne, an like shi da bandeji, sanna duka ilahirin jikinsa babu inda babu rauni jini jage jage, a jikin shinfidarsa farare gasu nan a gefansa a yayyage jawur da jinni tamkar an tsoma su a bokitin jinni a ka tsame su suna ta diga.
Na tsala ihu na gigice ina tambayarsu me ya faru das hi? Ya aka yi haka ta faru, yaya xan yi in kwaci kaina idan Abba ya mutu a dalilina?
Tambayarda na rirrike su nake yi kenan a gigice suka shiga lallashina suna shaida min babu lokacin batawa saboda marar lafiyan nan yana neman taimakon gaggawa a inda suke nuna min suna neman kudin su da suka karkashe wajen kaishi asibiti da xuba mai wajen kawo shi tun daga can har nan. Yayin da gabana ya fadi saboda na san bani da kudi, kudin da ke jakata bai wuce duu biyu ba saboda bikin nan duk na kashe kudaden kakaf.
Na tambayae su cikin kuka me yasa basu kaishi gidan suba suka kawo shinan? Sai suka ce min ai sanda yayi hatsarin yana Magana shine ya fadi sunanki yace matarsa ce, yana so mu kira ki kuma ke ce last call dinsa da muka gani a wayarsa, ke yake kokarin kira a sanda hadarin ya afku shi yasa muka kira ki, baki dauka ba daga nan muka ga wani lambar mukaddam shima mun kira baya jin mu har cajin wayarsa yakare ta mutu shine ya bamu adireshin ki yace idan muka xo kano mu nemi kaxaure mu shiga general hospital staff quarters mu tambayi madina. Sai kuka ya ci karfin madina ta katse labarin.
Nima na huta hannu, Allah sarki Abba, ko ya mutu ne, ya na nan da rai ban sani ba, se mu saurari ci gaban labari.
.
Wai mai yasa Madina baxa ta yarda da Abba ba tunda ba haramun bane dan ta aure sa ba?
Misali idan kece haka ta paru dake xaki yarda ki auri Abba tunda Kinga har yana neman rasa rayuwar sa akan ki?
Misali kuma idan Kaine duk yadda ka nuna mata kana tsananin son ta har kana neman rasa ranka xaka yarda Kaci gaba da son ta kuwa duk da bata son ka?
ADON DAWA
TRUE LIFE STORY
LITTAFI NA BIYU (P 15)
NA JAMILA UMAR TANKO
GABATARWA SADIQ HALIMA (Sadin Maa)
DAGA Al-Hada Hada Hausa Book stories
.
Kaltum ma hawaye take inda ta dafe wuya tace “Allah sarki bai ce a kai shiwajen iyayen sa ba sai ke, gaskiya yana sonki. Amma dai kin tausaya masa da kika gan shi a cikin wannan hali? ”
Madina tayi murmushin karfin hali ta dafa kafadar kaltum t ace “na tausaya masa har na fara nadamar wulakancin da na yi masa a baya. Dan na tabbatar ba son wasa yake min ba. Allah sarki so, shi burinsa na karbi gawarsa ba iyayensa ba don in tabbatar a dalilina ya mutu kamar yadda ko da yaushe yake ce min idan ya mutu in sani a sanadiya ta ya mutu.
Na rasa yadda xanyi dasu sai na kira mukaddam ina rusa kuka ina fada masa halin dana ga Abba. Shima sai ya rushe da kuka yace min mu garxayo dashi asibitin malam aminu kano xamu iske shi a nan yana jiranmu, haka aka yi kuwa, na roke su dasu kaimu asibitin a kano na shiga gidan gaba su biyu suka shiga baya wajen Abba direba ya tuka muka tafi sai xura gudu muke yi kamar xamu kifa saboda su da suke xaune a kusa dashi suna shaida mana cewa yana kokarin cikawa yana bukatar oxygen.
Tsananin kukan da nake rusawa da irin addu’o’in da nake xubawa shi ya ja hankalinsu suka dinga lallashina suna tausaya min kamar yadda suke tausayawa Abba. Muka isa aminu kano, na kira mukaddam na shaida masa mun shigo asibiti sai ya kwatanta mana inda xamu same shi. Kafin mu karaso har ya tanadi likitoci da nurses da leburorin da xasu kula dashi, a tsatstsaye suke suna jiranmu, motar na tsayawa aka dauke shi aka dora shi a gado mai taya aka tura shi aka shiga dashi dakin tiyata.
Abunka da masu hali domin baban mukaddam ma wani hamshakin mai kudi ne ga mulki saboda yayi gwamnan kano a lokacin mulkin soja. Na shaida masa cewar wadanda suka kawo shi suna bukatar a biya su kudin da suka kahse, ya je ya same su suka yi mar lissafi ya dauko kudi masu yawa ya basu, suka shiga motarsu su ka tafi, sai ni sai mukaddam a bakin dakin tiyata, xullumi nake, addu’a muke yi kada ya mutu, idan ya mutu bamu san me xamu fadawa iyayensa ba.
Nayi ta kuka, tamkar raina xai fita ba mukaddam ba, hatta jama’ar da ke wucewa da ma’aikata saida suka taru suke bani hakuri suna kwatantani da marar tawakkali, basu san ba rashin tawakkali ba ne, rashin sanin bayanin da xan yiwa duniya da kaina ne dalilin da Abba ya je ya ragargaje a hanyar garinmu wajen nemo yaya na.
Mukaddam ya dauko waya yana kokarin kiran iyayen Abba xai shaida musu halin daya ke ciki sai na yi caraf na rike wayar na hana shi . tambayata yake me yasa baxa’a fada musu ba, halinda yake ciki ba?
Ai doloe su sani ko bai mutu ba balle yaga alama da wuya Abba ya tashi a yadda yaga numfashinsa yana sama yana kasa. Ni dai na hana shi kira kuma ban san dalili ba, har aka fito dashi daga dakin tiyata likitoci sun duba shi tsaf sun sake dora wasu karayar da ba a dora shi ba da sannan suka sake like ciwukan amma sun hango buguwa a kirjinsa, akwai kashin daya goce a hakarkarinsa sai gobe xa’ayi wannan aiki sannan xa suyi masa hoton kwakwalwa itama su duba ko ta tabu saboda raunin da yake kansa a haka suka kwantar da mu a amenity dakin mutum daya.
Mukaddam yabiya kudin daki mai tsada lafiyayya mai AC, fanka, firij da kujerun alfarma. Mukaddam ya fita ya sissiyo mana abinci da abin sha , shi ma be iya ci ba balle ni, balle kuma shi marar lafiyar wanda babu abunda yake yi sai suma an sakala masa roba a hanci ana xuko numfashi, sai Karin ruwan da ake yi masa leda leda.
Ina xaune a gabansa a kan kujera yayin da nake rike da hannunsa na gaji da kuka sai addu’a nake tofa masa Allah Ya tashi kafadarsa.
Yayinda mukaddam yake lungu yana ta sa addua’ar hankalinmu a tashe bamu Ankara ba sha biyun dare agogon dakin ya buga ya yin da daidai wannan lokaci wayata da wayar mukaddam tadau ruri. Ina duba tawa naga sunan sumayya tukur yayin da mukaddam na duba tasa lambar mami hafsa tukur ce, maman Abba . sai gaba dayan mu muka mike tsaye muka dafe kirji, muka xaxxare ido muka kalli juna. Na ce sumayya ce, yace, mami ce, sai na yi saurin na karbi wayarsa dan kar ya danna . suka yi ta ringing har suka katse yayin da na murtsika wayoyin na kashe gaba daya, duk na bi na rude, ban san me ya kamata na yi ba.
Mukaddam na kokarin nuna min bai dace na kashe wayoyin ba saisu xaci ba lafiya ba ko mun hada baki mun kashe shi musamman idan suka xo suka iske mu tare dashi a asibiti cikin wannan halin, sai na cakumi kwalar rigarsa na matse shi a jikin bango Magana nake yi cikin fushi da kururuwa ina kuka, nace kai ne duk munafukin da ka janyo mana, saboda me xa ka kaishi tasha yahau mota ya tafi garinmu baka sanar min ba, baka sanarwa iyayensa ba?
Dan haka baxa ka amsa wayarsu ba, in kuwa har Abba ya mutu ka sani gawa biyu xaka kwashe domin ni ma sai na kashe kaina.
Kaltum ta tambaya “kuma ke lokacin da gaske kike xaki kashe kan ki? Duk wanda ya kashe kansa dan wuta ne fa.”
Madina ta share hawaye ta yi dan murmushi tace “ba kashe kaina xan yi ba, bacin rai ne kawai da tsantsar jin haushin mukaddam.”
Kaltum t ace “yaya kuka kare? ” madina t ace “kinsan kasa kwacewa yayi daga shaker da na yi masa yana ta bani hakuri har saida Abba yayi Magana. Nan da nan muka dungumo da gudu wajen gadon da yake kwance muna kiran sunansa idonsa a rufe amma sunan madina ya ambata a hankali nan da nan na rike hannunsa na matso da bakina saitin kunnensa na ambaci sunansa nace “Abba, ka ganni bude idanunka ka ganni. “sai yayi ta kokarin bude idonsa amma ya kasa. Hawaye ne kawai yake tsiyayowa daga idanunsa.
Ya fara Magana cikin sanyin murya wacce take fita a hankali y ace madina, ki yafe min abubuwanda nayi miki sannan ki sani duk abunda ya same ni dominki bana nadamar son da nake miki. Burina da fatana ki yadda da gaskiyar son da nake yi miki don kina xaton yaudararki nake, ina so ki kasance akan gawata yayin da Allah Ya dauki raina tamkar yadda mace ta gari take yiwa mijinta addu’a bayan ya mutu nima ki yi min saboda na lissafa ki dan haka na ci burin na aureki Allah baisa kin fahimta ba.”
Na sulale na durkusa na dora hannuna duka biyu a ka ina rusa kuka gami da salati fadi nake Abba na amince xan aureka, ka tashi kar ka mutu ka bar ni. Ya na cikin magana sai jini ya ambulo daga baki da hancinsa, a guje na xura na kira likita. Ya na xuwa sai yace xa su yi masa wata allura kafin gobe a shigar dashi tiyata idan iyayensa sun xo. Dan mukaddam yace musu iyayensa ne xasu saka hannu, tun daga nan Abba bai sake farfadowa ba barci kawai yake bai san inda kansa yake ba.
Jikina ya dauki karkarwa har saida na bawa mukaddam tausayi ya jawo ni ya xaunar da ni akan kujera yayin daya durkusa a gabana yana xubar da hwaye yace, “sister madina, naga kin rikice kin damu da yawa, na san abunda kike tsoro kada iyayensa su xo su ji a dalilinki haka ta faru da shi kin manta da Allah ne Yake shedar bayinsa a nan duniya da gobe kiyama?
Kin manta iyayen Abba musulmai ne, dole su yadda da kaddara mai kyau da marar kyau?
In har bakya so su ji abunda ya faru na amince ba xan fada ba ki dauki jakarki ki fice daga asibitin nan, kafin gobe su xo su ganki.”
Na girgixa kai na ce “idan na gudu shine xa su fi xargina su ce da sanina hakan ta faru saboda dole sai ka fada musu a inda yayi hatsarin saboda ga motarsa nan daya fita da ita a hannunka bada ita yayi hatsarin ba kuma dole likitoci sun dauki statement din yan sanda da suka kawo shi cewar a hanyar onisha suka dauko shi. Don haka gudu ba nawa ba ne duk daran dadewa gaskiya xata fito. Mukaddam, a ganin ka yaya iyayen Abba xasu ji a ransu idan aka ce musu Abba ni yake so har ma dalilina xai rasa rana?
Me yasa ka bari Abba ya jefa kansa cikin wannan hali nima gashi nan ya jawo min? sai na rusa kuka.
Mukaddam ya gyara xama ya bani labarin yadda abun ya faru daga farko har karshe.
LABARIN ABBA.
Mukaddam yace “tun muna yara idan kika lura Abba na sonki, ba son soyayya ba, yana matuakr son ya xauna dake. Baya gajiya da sauraron labarinki haka baya gajiya da kallonki, baya gajiya da yabon kirkin ki ko a bayan idonkine. Haka kawai kike burge shi yadda ya ga kina da tsafta, kina kula da gidanki, yaranki da mai gidanki, yace baki da kwadayi dan bakya roko sai abunda aka baki ki ke karba, baya ga rikon addininki bakya wasa da sallah. Abba ya shaida min cewa ko ya girma xai yi aure sai ya duba mace me tsafta da ladabi irinki sannan xai aura.
Bayan mun girma ya shaida min yana matukar damuwa da irin wahalhalu da wulakancin da mijin ki da kishiyoyinki ke yi miki, hakan bai sa kin fice ba saboda biyayyar aure. Idan muna xaune muna hira, sai ki ji ya tambaye ni yace, “mukaddam, anya kuwa a xamanin nan xan samu mace kamr Madina? ”
sai n ace masa “rabo ne ai, kai dai kayi addu’a kawai. Abba yayi ‘yan mata da yawa amma tun kafin aje ko ina sai dangantakar ta kwabe saboda bata da hali irin na madina. Kinsan gidansu rayuwar turawa ake yi bai tashi ya ga mahaifiyar sa na yiwa mahaifinsa hidima ba komai sai kuku da masu aiki ke yi, ke kuma ya ga komai ke ki ke yiwa mijin ki hatta tsinke xaki mika sai kin taso da gudu kin durkusa har kasa sannan ki bashi haka idan ya kiraki da gudu xa ki bar abinda kike yi ki je ki durkusa. Ba ki da lokacin kowa sai kin salami mai gidanki ko kadan ba kya bata masa rai baki da kiwar aiki.
‘yan mata da dama sun so Abba sai sun fara sai ya daina yace baya son su, har Allah Ya kawo lokacin rabuwarku ki ka bashi tarihin rayuwarki, ki kayi matukar bashi tausayi musamman daya ji kince kin rasa inda xaki nufa baki da iyaye. Sai yace min yana tausayinki yana matukar son yaga ya tallafawa rayuwarki kin koma cikin farin ciki kamar kowace mace mai miji da iyaye.
Daga nan bai sake cewa komai ba sai da aka dade, sannan na lura yana cikin damuwa na, na yi juyin duniyar nan ya ki fada min abunda yake faruwa sai ranar da muka je kaxaure wajen ki kika kore mu nima ranar ya shaida min halinda yake ciki nayi ta bashi hakuri kafin mu rabu yayi min alkawari xai hakura dake amma sai ya kirani a tsakar dare yace ya kasa hakura dake gashi tunaninki ya hana shi barci. Muna ta addu’a amma abu sai karuwa yake yi.
Ya ce min ya fi so ya auri matar daya ke tausayinta dan ya riketa amana. Burinsa ya raya sunna kamar yadda Manxon Allah (SAW) ya auri Nana Khadija a baxawara, ta grime shi, burinsa ya haifar miki da farin ciki, fatansa ya sami soyayyarki, ta iyayensa duk mai sauki ne yasan yadda xai bullo musu su amince kin ki sauraransa ma balle ki fahimce shi.
Sai shekaranjiya ya same ni yace ya tuno wata dubara, xai je garinku ba xai ce ya sanki ba amma xai tambayi inda yayanki innamani yake a enugu sai ya nemo miki shi su xo tare , yin hakan xai faranta miki rai. Na ce kada ya je, yace in kyale shi xai je ko da kuwa xai rasa ransa ne a hanya. Ashe ya fada da bakin mala’iku, haka ta same shi.”
Na juya na dubi Abba, na yi kuka na yi kuka, na ji dama a dawo da rayuwa baya da banyi masa abunda na yi masa ba. Mu dukka bamu runtsa ba har asuba, na yi alwala a bandakin cikin dakin nahau salloli ba adadi kafin assalatu, addu’a nake kada Allah Yasa Abba ya mutu.
Yayinda mukaddam ya tafi masallaci ashe ya dauki wayarsa, yana idar da salla sai ya kunna a inda ya hadu da sakonnin iyayensa da iyayen Abba. Hankalinsu a tashe suke tambayar ina suka shiga shi da Abba tun jiya?
Sai ya yanke shawarar ya kira mahaifiyarsa ya yi mata bayani ita kuma ta yiwa mahaifan Abba bayani. Tun da asuba, kafin gari yawaye xance ya xagaye dangi hankalin kowa ya tashi yayin da motoci na alfarma suka dinga tsayawa a gaban dakin da muke.
Muryar mukaddam na jiyo yan magiya yan bada hakuri game da dogayen bayanai cikin kuka da rawar murya a jikin wundon dakin, na meke da gudu na daga labulen wundon na leka, sai ga en gidan su Abba kakaf da danginsa da ‘yan uwan su mukaddam, yayinda baban mukaddam yaketa sharar masa mari ba adadi da kyar a ka rike shi. Aka sako mukaddam a gaba ya xo ya nuna musu daki, su ka dungumo suka nufo inda muke. Na takure a loko ina karkarwa ina kiran “laa haula wala kuwwata illa billah.”
Suna shigowa suka kalle ni a sheleke babu wanda ya amsa gaisuwata, yayinda suka nufi kan gado da sauri wajen Abba duk wanda ya leka Abba sai yayi baya ya dafe kai yana salati saboda Abba yayi kwatsa-kwatsa. Ina kuka na taso ina shirin in yi musu bayani sai kuwa sumayya tukur ta sharara min mari, sannan ta kira ni da suna karuwa, mahaifiyarsu mami hafsa ta kirani da suna maiya na cinye mata da, wai daman ashe nice na kama shi ya dinga ramewa sannan na yi asirin da sai da ya kai kansa onisha aka tsafe shi dan haka sai hukuma ce xata raba ni dasu.
Alhaji tukur kuwa allurer soja ceta tashi saboda motarsa ya je da sauti ya dauko bindiga yace sai ya harbe ni, abokinsa na rike shi yana fusgewa, sauran ‘yan uwa suka xagaye ni suna yi min cari aka, wai in ba mutuwar xuciya ba da kwadayi irin nawa yaya xa’ayi in tarki yin soyayya da dan yaron nan?
Wai ashe daman yaudarar mutane nake yi ina nunawa ni baiwar Allah ce, daman har yanxu da sauran tsafin da maita a jikina. Ba ni da bakin bayani saboda babu mai sauraro na.”
Sai madina ta rushe da kuka, Yayin da tausayinta yasa kaltum xubo da hawaye mai yawa, tagumi kawai ta yi ta kurawa madina ido , can ta nisa tace ‘gaskiya baki da ta cewa Allah kadai ne xai fitar da ke.”
Madina taci gaba, haka wasu mata biyu daga cikin dangin su Abba suka watso min takalmana da jakata sai gani a gaban tasi’u da yara na Abdul malik da Abdul hakim. Tasi’u yana ta Allah wadai da halina sai kara tunxura su yake yi yana cewa ai shi ya fi sanin wacece madina kuma yaya yake xaune da ni muguwa ce ni.
Alhaji tukur ya fara buga waya yana cewa ayi musu tanadin jirgi xuwa London yanxu yanxu nan xasu fita dashi kasar waje. Mami kuwa wani dan sanda ta bugawa waya tace ya xoya same ta a aminu kano xai kama mata wata mayya. Ban gudu ba kuma ban ji tsoro ba saboda babu kuma wani cin mutunci daya rage min yanxu a duniya wanda ba’a yi min ba, har na fi so ‘yan sandan su kamani su rufe idan Abba ya mutu ni ma a kashe ni na huta.
‘ya’yana da suka ji xa’a kamani sai suka sulalo suka ja hannuna wai sai na tashi mun fice daga asibitin, ni kuma naki tafiya na xauna a barandar dakin nace gara ma a kama ni a kashe ni xai fiye min, da kyar suka ja ni muka tafi,ina jin wasu daga cikinsu suna cewa ga mayyar can xata gudu sai na ji sumayya tace rabu da ita aimun san duk in da xata je yanxu ta lafiyarsa muke yi.
A bakin get din aminu kano ‘ya’yana suka ja burki suka tsaya, sai nima na tsaya a kusa dasu cikin kuka na fara yi musu bayani suma kukan suke yi. Abdul malik ya fada cikin fushi yace “mama ki ja mana abun gori a gari, kin cuce mu har karshen rayuwar mu.” Ya juya ya tafi a fusace, sai na kamo hannun karamin shima ya fusge yace “bana sonki ke ba uwata bace daga yau.” Sai na saki baki ina kallonsu suka tafi suka bar ni a tsaye. Tunda ‘ya’yan da na Haifa a cikin cikina suka fada min haka na san na xama abar gudu a duniya, na san bani da amfani ga duk wata halitta. Na tabbatar na xama abun gudu a duniya, abun mamaki sai na ji kukan da nake yi ya tsaya yayin da na fara murmushi ni kadai na ji ina fadin Alhamdulillah.”
Madina ta fashe da kuka mai tsanani.
Kaltum ta share hawaye ta tambayi cike da mamaki t ace, “me yasa kika ji kin daina kuka kina murmushi? ”
Madina ta dago da luhu-luhun idanuwanta ta dubi kaltum tace “masifa ce tayi masifa amma dukkan wani musulmi da yayi imani ya san Allah ne mai yaye duk wata masifa, na sallama duniya ne kwata-kwata sai na tuna xan mutu in je in tarar da Ubangijina wanda xai yi min sakayya sai naga duk wannan abun kamar ba’ayi ba, shine kawai na ji na daina kuka na yi ta murmushi. Menene dadin duniyar ne?
dadin duniya shine ‘ya’ya, dukiya sai mata, to duk na rasa su a duniya dan haka sai na yi tawakkali na cirewa raina rayuwar duniyar kwata-kwata ina sauraron ranar da Allah xai yanke min wato ranar da xan mutu.
Ina fita daga asibiti na hau acaba na tafi tahsar ‘yan kura, daga can nahau motar kaxaure. Ina isa gidana na xaxxabi ‘yan kayayyakina kadan na xuba a jaka na shiga tunanin inda xan je, bani da inda na sani wanda xan iya kaura. Daga karshe na yanke shawarar nima in tafi enugu in nemo yayana innamani in har yana raye in xauna tare dashi don shi kadai

Please Login or Register in order to submit comment