Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na masifaba yayi ficewarsa abunshi."

tafiya yakeyi yana dariyar dijama saboda rashin kunya da tayi mata yawa akai ita da kanta tasan bata gane karatu, kai Allah dai ya kyauta."

Yana shanye kwanan gidansu, bai ankaraba yaji ankwad'a masa sanda akai, waiga warda da zaiyi wa zaigani, Buba ne da yaransa sun zagayeshi suna shan taba."

Cike da mmki Mahmud yake kallonsu, zai bud'a baki yayi masu mgna suka kuma yunkurin kuma buga masa sandar a karo na biyu,
Hannunsa ya kara suka yashiga jujuwa yaron Buba ya yarb'ar dashi gefe d'aya,
nanfa danbe yakaure tsakaninsu."

Nanfa Mahmud ya shiga dukansu, baji ba gani
,duk suka zube warwas wasu kuma suka tsere a guje,
Daga cikin masu gudun harda Buba😅

D'aya daga cikinsu daya daku ya kasa iya gudu, Mahmud ya shak'o wuyanshi ya mak'areshi, yashiga tmbyarsa, "waye yasanya Ku?" Menamaku kukeso kuga bayana?"
Jinkinsa na rawa yace dijama ce tasanyamu."

"what dijama?" Yace cike da mamaki,
yanzu dijama bayan rashin kunya harda ta'addaci takeyi?"
Ya wurgar dashi gefe d'aya yayi tafiyarshi, zuciyarsa cike da bak'in ciki d mmki."

Haka ya koma gida Rigarsa rataye a kafad'arsa,
Yana shiga cikin gidan, ya ta rar da dijama tsakar gida zaune,
Tana ganinsa ta tashi da gudu ta tafad'a d'akin tsohuwa.

Baibi ta kantaba yayi shige warsa d'akinsa, yashiga har had'a kayansa, cikin akwati.
Saida ya d'auki komai nashi. Ya tallabo akwatinsa yafito."

Lokaci da yafito janye da akwati, yayi dai dai da fitowar
Tsohuwa daga band'aki ta dubeshi cike da mmki tace "Mamuda lafiya?" Ina zakaje da akwati?"

Mahmud ya dubi tsohuwa yace "gida zantafi tunda naga har anfara turomin "yan iska su dakeni
,watara na maganin b'era za a sanya min a abinci domin naci na mutu,
Dan haka tsohuwa kinga tafiyata sai wani lokacin."

Ya kai dubansa ga dijama dake zatsaye a bakin k'ofar d'aki, ta marairaice fuska,
duk bataji dad'in tafiyar da yace zaiyiba
, yace " toh meye kuma na tsayawa kina kallona?"
Zaki turosu ne su kuma tareni a hanya?",
.
Bata tanka masaba illah ta kuma sunkuyar da kanta k'asa,
, tashiga tunanin kaddai ace Buba sanyawa yayi aka daki yaya Mahmud."

Bai kuma bi takan kowaba ya Yakama hanya yayi tafiyarsa." Tsohuwa ta bishi da Addu'ar Allah ya tsareshi ya saukeshi lfy."

bayan fitarsa tsohuwa ta dubi dijama da kyau,
taga ba gaskiya a fuskarta tace dijama me ke faruwa da mahmud?"

Bata b'oyewa tsohuwa ko maiba tashiga bata lbr abunda yafaru."

Aikuwa tsohuwa tashiga yiwa dijama fad'a ta inda take shiga batanan take fitaba, fad'a takeyi sosai kamar ta daketa,
dijama bata tankaba illah turo baki takeyi."

*******************

*The following day*
Tsohuwa takira dijama domin ta aiketa,
Tafiya takeyi tana rawa a kan hannya tana d'an karkad'a k'ugunta,
Ta k'ofar gidansu Buba tabi inda suke zama suna majalisa,

ta hangosu ta d'aure fuska tayi kamar bata gansuba,
Sai da tazo daf dasu abokanansa sukace Baba ga mutuniyar can,
yana ganin takawo daf dasu ya wangame bakin sa da ya kunbura yayi suntum, yasha duka wurin mahmud."

yayi saurin tashi ya shiga gabanta yana fad'in "dijama ta sai ina hakan?" Ta d'aga kai ta dubeshi taga yanda labbansa suka sundume kamar ganda,
Bata San lkcin da ta tuntsire da dariya ba, tana nuna bakinsa da hannu, tana kuma dariya."

Muzanta Buba yayi,
Yashiga kallon kansa,
yaga metake yiwa dariya?"

Fahimta yayi da bakinshi take yiwa dariya ya, farajin haushi, amma kuma sai ya waske."

Ta kuma karkace kai tana kallonshi had'ida ya motsa fuska, kamar ba ita bace ke dariya yanzun,

Tace wai dama kai ragone?" Ina taurin naka yake wanda kake tsoratar da mutanen garin nan?"

Shin wai meyasa harka bari yaya mahmud yaji maka ciwo, lallema amma dai buba kabani mmki,

Ta kuma kallonshi ta tuntsire da dariya tace " toh Allah ya tsare gaba kaga tafiyata", ta barshi nan tsaye
Ta rab'ashi ta wuce, me abokansa zasuyi inba dariyaba, da suka tuna da gudun dasukaga yayi jiya."

Sukace gskya "oga munfaji kunya jiya wai ya akai hkan ta faru? Musamman kai oga duk kafimu gudu a nan take kashanye kwana,
Nanfa yafara k'uluwa. Ya dubesu ya doka masu tsawa idonsa sunrik'e zuwa launin ja."

Dijama nayin nisa snn tawaigo ta kallesa taga yana nan a inda ta barshi tsaye,
ta kuma b'arkewa da dariya ta d'aga murya ynda zaijita tace "amma dai Buba Kai wawa ne wlh da mace zatasanya kaci duka hka, tunda ma Nagano kai ragone na rantse bazan aurekaba, tun wuri ka nemi matar aure amma ba dijamaba ehe, tana kaiwa nan ta zuba a guje ta b'ace masa."

Aikuwa Buba ya k'ulu iya k'uluwa yashiga zage2, yana d'aga anda yana kirarinsu na 'yan tauri,
Had'ida borin kunya."
"Karya kike dijama na rantse da Allah Indai ina numfashi a garin nan bawani Wanda ya isa ya aureki saini, saini Buba na dijama yar gidan tsohuwa."



*wacece dijama*?" Waye Mahmud?"


Muje zuwa yanzun lbr yake ba'ayi komai ba."
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_😅)



Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)






7⃣







Mahaifin Mahmud da mahaifin Dijama Hassan da Husaini ne,

Hakan suka tashi a tare duk abunda zasuyi a tare sukeyinsa, har sha'awa suke bawa mutanen k'auyen Tofa dake cikin k'aramar hukumar Kano."

Hassan da Husaini sun taso cikin so da k'auna da kulawa a wurin mahaifansu, Malam Adamu da Hadiza,
Wanda a yanzun jikokinsu suka canxa masu suna suka mayar dasu tsohuwa da Kaka

Babu wani Abu dake raba Hassan da Husaini,
ako da yaushe suna tare da juna, a cewarsu a yanda suka fito tare sun d'aukarwa Kansu Alk'awarin baxasu tab'a rabewa ba."

Tun haihuwar Hassan da Hussaini tsohohuwa bata kuma k'ara samun haihuwa ba, wannan dalilin yasa suka d'auki son duniyar nan suka d'orashi a Kansu."

K'auyen Tofa k'auye ne mai tattare da Ni'ima da wadatuwa. Da kuma yalwar makarantun boka dana islama."

Wannan dalilin yasa mlm Adamu ya tashi tsaye tsayen daka domin ganin Hassan da Husaini sun samu ilimi boko dana Islama, kasan cewar mlm Adamu manomi ne, akwaishi da wadatar zuci, da son yaga ya wadatar da iyalinshi batareda sun gani a wani gidan ba."

Hakan kuwa akayi suntashi cikin hazak'a da k'ok'ari Wanda gaba d'aya k'auyen na Tofa, suna Alfahari dasu, suka zama abun sha'awa da kwatance."

Akwana a tashi har suka kammala karatunsu na _secondary_ har suka tafi Jami'ar Bayaro _university_ dake cikin garin Kano."

Shigarsu jami'a ra'ayinsu yarafa banbanta a wurin karatu domin Hassan _Business_ yakeson karanta, shi kuma husaini _mass_ _communication_ yake son ya karanta."

Hakan suka Amincewa junansu amma kuma duk da hakan a cikin mkrantar a tare suke kwana a tare sukecin abinci,
idan har ba saninsu kayiba bzaka tattace Waye hassan ba waye husainiba."

Hakan sukayi karantunsu cikin Aminci da soyayyar juna tare da taimakon mahaifinsu har sukayi masters."

Allah ya taimakeso suka fito da sakamako mai kyau,
Nan take har rugogowar d'aukarsu aiki akeyi."

Hassan aiki baya gabansa yafi ganewa kasuwanci domin tun kafin takardunsu su fito har ya bud'a d'an karamin shago a k'ofar gidansu yana sayarda atamfofi da shamdodi da takalma, wadda yin hakan harda taimakakon mahaifin nasu."

Wani babban kamfani ne na sarrafa motoci, dake cikin garin Kano a can Hassan yasamu aiki inda ya samu matsayin manager campanin za'a dinga yimashi Albashi mai tsoka." murna a wurin mahaifan nasu da kuma d'an uwan nashi Husaini abun ba'a mgna

Bayan kwana biyu da faruwar hakan, garin Lagos suka d'auki Husaini aiki a gidan TV na garin Lagos, inda shima suka bashi babban muk'ami."

Hmmmm Hassan Husaina sunyi bak'in ciki sosai da rashin samun aikin da basuyiba a gari d'aya, inda suka buga Kansu da k'asa sukace sun fasa yin aikin indai ba gari d'aya suka samuba.".

Tsohuwa da Kaka suka Shiga lallashinsu suna basu hak'uri a kan cewa rabuwar aikinsu ai bashine rabuwarsu ba, kuma ai ba'a can zasu dawwamaba."

Da kyar a ka samu suka hak'ura had'ida yiwa junansu Addu'a."

Ranar da zasu fara tafiya wurin aiki, ko wannensu ya shirya kayanshi a akwatinsa,
sunja wuri d'aya sun zauna suka rungume junansu ko wanne idonshi ya cika da hawayen rabuwar da zasuyi."

Tsohuwa da Kaka dake tsaye a tsakar gida suna jiran sufito surakasu, sukaji shuru basuda niyar fitowa, kai tsaye suka shiga d'akin, suka ta tarar dasu a zaune rungume da juna suna hawaye."

Sukansu saida suka tausaya masu ganin cewa tunda aka haifesu basu tab'a rabuwaba,
A yanxun shekara Ashirin da bakwai kenan sai yanzun da girmasu lokaci d'aya zasu rabu tabbas dole suyi kukan rabuwa."

Hakan suka shiga lallashinsu da ban baki da komai sannan suka lallab'asu had'ida yi masu rakiya suna d'agawa junansu hannu sukatafi."

Tsohuwa da Kaka sunyi kewar tafiyar tasu, sai dai daga k'arshe suka bisu da Addu'a Neman dacewa."

Wata d'aya da tafiyarsu suka shiga aiki gadan gadan baji bagani, kuma sun tsare gskiyarsu da Amana,
Kullu suna kiran junansu a waya ko kuma su hau charting suna fira cike da kewar junansu."

albashinsu na farko suka shigo garin na Tofa suka shiga rarrabawa tsofafin garin da masara k'arfi."

Sukayiwa tsohuwa gyaran gida aka mayar mata da ginin zamani, Kaka yacika da murna da farin ciki, suka wadata fahaifan nasu snn daga k'arshe suka koma wurin aikinsu."

Bayan shekara d'aya da fara aikin Nasu, ba laifi kud'i sun zauna masu a rayuwa babu abunda suka nema suka rasa, Kaka ya tayar masu da fitina akan cewa zamansu a hakan ya isa,
Ya kamata kowanne daga cikinsu ya nemi mata domin yayi aure, ko zasu ga jikokonsu tun suna da rayuwa."

Suka amsa gaba d'ayansu da to." daman abunda suke jira kenan."

Bayan wata biyu da yimasu maganar dukansu suka nemo matar aure a garin da suke aiki,
Hassan ya nemo auren Hajara, Husaini kuma ya Nemo auren Bilkisu."

Saida suka turawa junansu photo nan yan matansu dukansu sukayiwa juna sambarka da dacen da sukayi sannan suka isarwa da Kaka umurnin sa."

Kaka da tsohuwa sunji dad'i sosai sunyi murna, cikin sati d'aya aka tsaida magana aka sanya ranar bikin nasu nan da wata d'aya masu zuwa."

Akwana tashi lokacin bikinsu yayi aka shiga hidimar biki gadan gadan, in da Hassan ya k'era k'aton gida naji da gani a cikin garin kano,
Shima Husaini hakan,
gida iri d'aya sukayi duk abunda ke akwai gidan hassan akwaishi gidan Husaini gari kawai ya babbanta Hassan a kano husaini a lagos."

Ansha shagalin biki anyi taron bikin da ba'a tab'ayin irinsaba a cikin k'auyen na Tofa."

Ko wannansu Amaryarshi ta tare a gidansa."
Hmmmmm."

Bayan wata tara da aurensu matar Hassan ta haihu ta haifi d'anta namiji mai kama da Husaini sak👌🏻 mmki kowa yakeyi sai. Sai dai ba abun mmki bane kasancewa jini d'aya ne."

Murna Husaini yashigayi dajin labari, tun kafin ya iso yasanyawa yaro suna *Mahmud* Hassan yaji dad'i sosai domin shi a kullum farin cikin husaini shine nashi. Kuma duk abunda yakeso shima shi yakeso."

Shekarar Mahmud Uku aduniya aka Haifa mashi k'anwa aka Sanya mata suna Asma'u."

Har a lokacin matar Husaini ko b'atan wata bata tab'ayiba."

Ta d'auki damuwar duniyar nan ta d'orata a kanta, inda shi kuma Husaini sai dai ya dinga Addu"a, Allah yabashi mai Albarka idan lokaci yayi."

Wanda a wannan lokacin Hassan kud'i sun zauna mashi ya daina aikin kamfani yashiga harkar siyasa gadan gadan."

Shima Husaini hakan ta kasance a gareshi yazama babban d'an jarida a garin lagos wanda akeji dashi, kud'i sun zauna masu."

Bayan matar Hassan ta yaye Asma'u ta kuma samun wani cikin ta haifi d'anta namiji aka sanya mashi suna Adamu wato sunan Kaka kenan suna kiranshi da Khalil."

Wasa wasa sai da sukayi shekara goma sha uku da Aure sannan Allah yabawa matar Husaini ciki, Wanda yayi dai dai da kuma samun cikin matar hassan haihuwa ta hud'u."

Samun cikin Bilkisu matar Husaini ba k'aramin murna sukayi ba gaba d'aya family musamman Hassan, da yakeji tamkar matarsa ce keda cikin."

Haka sukaci gaba da renon cikinsu har ya kai watan haihuwa, ta haifi 'yarta macce sak Hassan,
Masu karatu kusan dai Hassan da Husaini kamarsu d'aya idanba saninsu kayiba bazaka iya tattace d'ayansuba."

Hassan yayi mata hud'uba yasanya mata suna Nana Khadija wato sunan tsohuwa kenan, inda tsohuwa taji dad'in wannan kara da akayi mata aka sanya sunanta, amma kuma ta shinfid'a sharad'in cewa baza'a canza mata sunaba akirata da ainahin sunanta Nana khadija."

Hakan akayi domin bin umurnita, ba'a canxa mata sunaba da sunanta kowa ke kiranta, amma bnda mahaifan nata sai dai suka dinga kiranta da Ummie." Inda tsohuwa take kiranta da deejamah."

Tunda akazo da Mahmud wurin bikin sunan Nana khadija, yaji yana sonta musamman da duk wanda ya gansu ake cewa kamarsu d'aya a lokacin mahmud yana da shekara goma sha d'aya."
Idan zai kwanta barci dole sai a kusa da ita yake kwantawa. Wnn abun bak'aramin dad'i yayi wa mahaifan nasuba."

Bayan haihuwar khadija da sati d'aya matar hassan ta kuma haihuwa ta haifi 'ya mace aka sanya mata suna Fateemah."

Bilkisu tayi Arba'in d'in Nana Khadija cike da k'oshin lafiya, dijama tayi kyau harta gaji sak kamannunta suka dinga komawa na mahaifinta."

Shiri sukeyi zasuzo Kano yawon Arba'in domin ya d'auk'i huto a wurin aikinsa."

Sun shirya tsaf cikin Shiga ta Alfarma, anyiwa Deejamah kwanliya tayi kyau tana sab'e a kafad'ar mahaifiyarta, Husaini yana janye da a kwati yana k'ok'arin sanyashi a but,
Bayan ya shirya komai suka shiga mota yajasu suka d'auki hnyar kano."

Tafiya sukeyi suna yiwa 'yarsu wasa cike da so da k'auna,
Suna kaf da kawowa Husaini yana yawa da Hassan kan cewa gasunan sun kusan kawowa, domin sai sunfara tsayawa cikin kano wurin hassan idan sukayi kwana biyu sai su wuce Tofa wurin tsohuwa idan suka gama kwanakin da zasuyi sai su dawo gida."

Yana cikin waya da hassan saigani sukayi mai mota ya gifta masu ta gabansu ya daki motarsu,
Tayar motar husaini ta fita ya yanki daji babu abunda sukeyi sai Addu'a domin kuwa yayita k'ok'arin ya tsayar da motar amma yakasa."

Saida takai gindin wani k'aton icce, ta daki icce gaba d'aya motar takife,
Wadda yyi ddai da zuwan mutanen da abun ya faru a gabansu suka biyo bayansu domin ceto rywarsu."

K'ok'arin tsiratar da rayuwarsu aka shigayi, da kyar aka samu a ka fito dasu a k'ark'ashin motar wanda a lokacin ko wannensu baya motsi Allah ya karb'i rayuwar bayinsa."

Cikin ikon Allah Nana khadija ko kwarzane batayiba, koda aka cirota a motar sai wasa takeyi da hannunta alamar tana cikin k'oshin lfy."
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅





Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)





*9*






Gudu takeyi tana ihu,
Buba na biye da ita.

Samarin Antyn lantana ne, suka hangota tana tik'ar gudu suma suka dafo mata dama jiranta sukeyi sunada haushinta."

Tana ganinsu suma sun biyota, ta kuma k'ara gudu tana fad'in wayyo jama'a kufito Ku taimakeni 'yan fashi da makami."

Wani tsoho a kan kekensa yana tafiya yanajin hka yasaki keken ya xuba da gudu ya nemi ma b'oya."

Matan Aure sai kama d'iyansu sukeyi suna rufewa a d'aki suna Addu'oi domin a tunaninsu 'yan fashin ne suka shigo cikin garin."

Dantijawan garin da samaru suna ganin su Buba na gudu tareda dijama,
sun d'auka 'yan fashin sukeyiwa gudu, ai kuwa har 'yan rigaggen gudu sukeyi suna shigewa gida had'ida rufo k'ofa da sanya sakata."

Duk inda dijama ta gifta tana ihu su Buba na biye da ita suna Neman kamata,
Jin ihunta tana fad'in wayyo 'yan fashi da makami, jama'a kufito Ku taimakeni
Kowa ta Kansa yakeyi baya tsayawa saurarenta."

Da kyar tasamu ta kawo gida, tana shiga gida ta mayar da k'ofa ta rufe ta sanya sakata,
Ihun takeyi bakinta yak'i yayi shuru tana fad'in "wayyo tsohuwa 'yan fashi da makami."
A razane Abba ya mik'e tsaye cike da tashin hankali da tsoro ya tallabi Kaka yashigar dashi d'aki,
Tuni tsohuwa ta kai d'aki zaninta a hannu daga ita sai dogon siket, saura kad'an tayi tuntub'e ta fad'a wurin tashi."

D'aki d'aya suka shige suka rufe ko wannensu sai zarar ido yakeyi."

Can sukaji ana dukan k'ofar waje da k'arfi kamar za'a cire k'ofar.'

Jikin tsohuwa ya soma rawa tana kallon Abba tana cewa "yanxun Hassan ya zamuyi?" Karfa su shigo su kashemu."

Abba yace "kwantar da hankalinki tsohuwa baxasu kashemuba,
jin haushina d'aya na baro bindigata a cikin mota."

Kaka kuma ya sunkuyar da kai sai salati yakeyi yana addu'a jikinsa sai rawa yakeyi'

Dukan k'ofa akeyi ba girma ba arziki, tsohuwa ta dinga rawar jiki zanenta a hannunta takasa d'aurawa sai addu'a takeyi idan tasaki wannan ta kwaso wannan."

Dijama ta dubi tsohuwa ta dubi kaka ta rik'e ciki tashiga kwasar dariya, tana nunasu da hannu."

Tsohuwa na ganin hakan ta fara tunanin ko dijamace ta janyo fitina a waje ba 'yan fashin bane."

Tsohuwa tace Hassan ina ganin ba 'yan fashibane dijama ta janyo mana fitina."

Abba yayi saurin waigawa ya dubi dijama da sai dariya takeyi idan ta dubi tsohuwa da kaka.
"Yace dijama suwaye ne? Mekikayi masu?"

Turo baki tayi tace Abba su Buba ne, bata k'arasa maganarba sukaji dukan k'ofar yayi yawa, kamar harda hayaniyar mutane a wajen,
Sai a lokacin Kaka yayi magana yace "ai saikatashi kafita kaji abunda ke faruwa,
Indai wann hatsabibiyar yarinyarce wata rana sai ta janyo mana mgnar da za'a cinnawa gidan nan wuta duk mu k'une gaba d'aya
Yana gama mgnar ya wurgawa dijama harara ya d'aga sandarsa ya zungureta mata k'afa da ita."

Abba ya mik'e da Sauri ya bud'e k'ofa yafita,
Bbu abunda tsohuwa takeyi sai wurgawa dijama harara domin yau ta kaita bango."

Abba yana fita yaga mutane jimjim a k'ofar gida, babba da yaro, tsofaffi da samari,
kowa sai fad'in Albarkacin bakinsa yakeyi a kan dijama,
a gefe d'aya tawagarsu Buba ce da makamai a hannunsu,
d'aya gefen kuma samarin Antyn Lantanane suma rik'e da makamai, rik'e baki yayi yacika da mmki."

Suna ganin fitowarshi sukayi saurin ajiye makamansu suka zube k'asa suna gaida shi."

Bai tambayi abunda ke faruwaba Dan yaji duk abunda suke fad'i, illah yashiga basu hak'uri, tare da rarraba masu kud'i."

Wani dantijo yagani zaune wuri d'aya ya rafka tagumi, kowa yana zuwa karb'ar Kud'i shi yana zaune wuri d'aya baya da niyar motsawa,daga inda yake,
Abba ya isa kusa gareshi yace "Baba lfy meya faru?" Ko wanine bashi da lfy a cikin iyalinka."

Dantijon ya dubi Abba yace "Alhaji dama ciwon ne ai da sauk'i."

Abba yace "Baba meke faruwa?"

Ina kan keke na ina tafiya yarinyar wurinka tadinga ihu tana fad'in 'yan fashi da makami, bansan lokacin da nasaki keken hannuna naba,
wurin intsiratar da kaina,
Kafin in ankara ansace mun keke, kuma wlh Alhaji shi kad'ai na mallaka shine kaddarata."

Abba ya lallasheshi had'ida kirga kud'i masu yawa wad'anda sukafi na keken yabashi had'ida bashi hak'uri,
Hakan Abba yayi bawa mutane hak'uri yana yimasu Alheri suna wucewa daga ciki kuwa harda Buba da yaranshi da saurayin Antyn lantana."

Harda wani magidanci wurin gudun 'yan fashi bai saniba ya ture 'yarshi ta karye a hannu, bai ankaraba saida yaji ance ba yan fashin bane snn ya fahimci Ashe ya karye 'yarshi a hannu."

Shima Abba yabashi hak'uri had'ida bashi kud'i masu yawa da zai nemarwa yarshi magani harta warke."

Sann Abba ya juya yashiga gida yanata mmkin hatsabibanci irin na dijama,
Dijama ta rakub'e wuri d'aya sai zarar ido takeyi tsohuwa sai faman fad'a take mata kamar ta daketa."

Abba shima yashiga yimata fad'a kamar ya doketa abunda bai tab'a yi mataba tunda aka haifeta,

Kaka dake zaune gefe d'aya yace "gwara da Allah yasa ka nan a gaban idonka hakan ta faru,
Kullum a rana d'aya sai sama da mutum goma sunkawo k'ararta tsohuwa ke tare mata,bata son ganin b'acin ranta."

Amma tunda ynxun ka ganewa idonka sai ka d'auki mataki, akai,
Ga ganta nan Ko mkranta bata zuwa gaba d'aya makarantar biyu Arabic da boko duk ankorota, saboda hatsabibancinta gata bata gane komai sai fitina da rashin kunya. Yakai k'arshen maganarshi yana zungura mata sandar hannunshi."

Tsohuwa bata tanka masuba saima taja bakinta tayi shuru, domin yau itama dijama ta kaita bango."

Abba yayi kyaran murya ya dubi tsohuwa yace "inna kiyi hak'uri kibani dijama natafi da ita na nema mata ilimi Wanda zatayi dogaro da kanta tazama abar Alfahari a cikin Al'umma, yin hkan shi zai Sanya mana natsuwa a zuciyarmu ganin mun rik'e marainiyar Allah tsakani da Allah."

Kaka yayi karaf yace "aikuwa wlh da ka taimakemu ka taimaki mutanen garin nan mundun katafi da dijama kabar garin nan da ita,

ni wlh wani lkcin idan na tsaya ina tunanin inda dijama ta gado wnn halin nata sai inkasa tunano kowa a cikin zuri'armu, ina ganin wata k'ila a can cikin dangin mahaifiyarta tayi gadon wnn halin."

Tsohuwa tace "nidai ya isa haka malam kamata yayi kadinga yiwa dijama Addu'a ba aibatataba."

Kaka yace "ni Sam bana aibata dijama a kullum Addu'a ta d'aya Allah ya shirya mana ita, yabamu ikon rik'e amarta da Allah ya d'ora mana a kai."

Abba ya katse zancan da yace "to Ummie tashi kishiga ciki ki had'o kayanki mutafi marece yafara."

Tana murna tana tsalle zataje birni. Ta tashi tashiga d'aki ta fara had'a kayanta."

Tsohuwa bata son tafiyar dijama dan dai ba yanda zatayi ne, dole ta hak'ura tabari za'a tafi da ita."

Sai da ta shirya kayanta tsaf a jaka ta tallabo jakar tana dariya tana jin dad'i, ta fito."

Abba har ya kammala shirinsa ya fito had'ida yiwa su tsohuwa sallama dijama na gabansa Jakarta a hannunta suka nufi hanyar waje,
Tsohuwa dai Addu'a take masu Wanda takejin kanta duk ba dad'i an d'auke Mata dijamarta."

Kaka kuma saboda dad'i kamar ya zuba ruwa a k'asa yashi, domin yasan yau idan ya kwanta barci ba bak'ocin da zai tayar dashi domin kawo shedun dijama."

Har mota suka rakasu, suna yimasu add'o'i."

Mutanene cimjim gaban motar k'awayen dijama suna bangwana, Abba ya bud'a mota yashiga dijama itama tashiga gidan gaba sai wasar baki takeyi tana dariya tana d'agawa su suwaiba hannu."

Murmushi Abba yayi ya kunna mota ya fara tafiya, Dijama ta lek'o ta k'ofar marfin mota tace "suwaiba idan kukaje gonar Audu wurin satar gwaiba,

idan kukaga Buba kuce masa natafi birni amma zandawo don saina rama abunda yayi mun."

Abba yace Ummie na wai meye hkan? Ki zauna dai dai mana karda kiji ciwo."

Snn tayi saurin gyara zamanta Abba yaja mota
Yatafi yana dariyarta, suka d'auki hnyar kano."


_dijama a birni ikon Allah🤔_
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMA*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_😅)



Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)






8⃣





Hassan dake waya da Husaini yanajinsa yana kalmar shahada a waya,
gaba d'aya hankalinsa ya tashi ya fito da saurin shi baibi ta kan kowaba ya shiga motarshi yajata da k'arfi ya mik'i hanya,
ya nufi wurin da yaji Husaini yace masa ya kawo."

Cikin minti talatin ya

3 Comments On YAR GIDAN TSOHOWA
avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment