Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zubewa k'asa war waassss....

Ko kallon gunda take beyiba ya shige d'aki ya janyo biro da takaddah ya rubuta mata sakinta ukku rerasss!.


Fitowa yayi Had"i da wurga mata takardar a saman jikinta kana yace "billahil azim ki gaugauta barin gidannan kamin na dawo,idan ba haka bako!!!!...

Girgiza kai yayi had'i da ficewa daga cikin gidan gaba daya...



Bud'e baki da kyar tayi kana tace "Alhmdllh Allah mungode maka.

Ashe inada rabon sake rayuwa dakai habiby¿¿
Magana takeyi ita kad'e kamar zautacciya..

Sa hannu yayi ya janyeta daga jikin abba kana yace "mom kinsan jikinsa beda k'arfi fa...

Bara na hanzarta naje nazo da malam nata'ala...

Batare daya jira mezata ceba ya juya da hanzari yabar d'akin....

Komawa tayi gefen gadon takama hannayensa duka biyu ta riqe,bakinsa ne yaci gaba da motsawa alamun yana sonyi magana...

Kunnenta takai dai dai saitin bakin nasa domin jin meye yake cewa...


R...u...w....a jin meyake cewane ya sanyata sakin hannayensa tafice da sauri ta nufi d'akinta....

Ruwan zam zam ta dauka kana ta taufa masu ayatul kursum da falaqi da nasi ,jikinta har rawa yakeyi wurin kafa masa kofin a baki....

Saida ta tabbatar yasha sun ishesa kana tasauke kofin daga bakinsa .....

Komawa gefen gadon tayi tayi zaune, hawaye Sai tarara suke faman yimata....



Faɗowa sukayi cikin ɗakin kamar waƴanda aka Koro,kai tsaye gurinsa suka nufa, kama hannunsa malam nata'ala yayi ya rirriƙesa bakinsa saifaman mazari yakeyi......



Kinga beauty a gaskiya ni nashiryawa aurenki Dan haka ki gayawa su baba zan turo da magabatana idan yaso sai'ayi maganar komai d komai lokaci ɗaya...

Washe haƙora tayi kana tace......✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽












*More comment more typing🤸🏽‍♀️.*




~Alƙalamin 🖊️Doctor MARYAMAH IBRAHEEM.~


~tabbas a'ƙalami🖊️yafi takobi🤺.~



*Comment*
*Vote*
*Share*




*_~ƳAR MUTAN {BUBARE} CE!✍🏽.~_*


*👄🤦🏽‍♀️BAKINA YA JIMIN👄🤦🏽‍♀️*
_{ƙalubale garemu mata}_.




*STORY & WRITING BY DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*




*_Marubuciyar👇🏽._*


*TAWA ƘADDARAR KENAN!*


*AUTAR MATA*
_{rikitacciyar yarinya}._


*_And now👇🏽._*


*BAKINA YA JAMIN*
_{ƙalubale garemu mata}._

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*بسم الله الرحمن الرحيم.*



*PAGE 7️⃣6️⃣ ↘️ 8️⃣0️⃣.*





__________Washe haƙora tayi kana tace "dagaske alajina¿

Jinjina mata kai yayi alamar tabbatarwa, ai kuwa nandanan jikinta yahau ɓari , ta matsu yawuce ta samu ta taka rawa kamar ita ace tamallaki wannan mutum da kuɗi suka zaunawa, ashe da rabon itama ta ɗanɗani zumar duniya.....¿

Sama sama aka idar da taɗin nayau domin kuwa gabaki ɗaya hankalin gimbiyar baya jikinta.


Cikin gida tashige kai tsaye ɗakin mahaifiyarta ta shige zaune ta tarar da'ita tana cin ɗumamen tuwo, zama tayi daf da mahaifiyarta kana tace "mama albishirinki.

"Goro , tabata amsa kai tsaye.

"Fari ko jaaah¿

"Ke dan Allah tashi bani guri bana son hauka kinji ko¿

"Shin ma na tambaye ki¿ ni sa'ar kice da zakizo ki sanyani gaba da wani albishirina¿

Zumɓuro baki gaba tayi kana tace "haba mama ki tsaya kiji dame nazo maki Mana.

Lomar tuwonta takai a baki kana tace "oya faɗi naji.

Gyara zama tayi kana tace "dama alajine yace nayiwa baba magana yanason ya turo magabatansa.

Riƙe baki mama tayi kana tace "anya dagaske kikeyi kuwa¿



"Allah da gaske nakeyi mama.

Tsame hannunta daga cikin tuwon tayi kana ta miƙe tace ahafffff, kice banga ta zama ba, Bara naje nagayawa baban naku, ta ƙarashe maganar tana nufar hanyar barin ɗakin.

★★★★★★★★★★★★★★★★

Tattare ƴan kayayyakinta tahauyi sai faman sharce hawaye takeyi domin kuwa ba ƙarya sakin ya girgizata.


Gidan yayanta tanufa kai tsaye janye da ɗan akwatinta gidan tashige sai faman sharce majina da hawaye takeyi.

Ƙwalala sallama tahauyi Muryarta sai faman creaking takeyi alamun tasha kuka harta gaji kenan.

Matar yayanta ce, tafito tsakar gidan sai faman harare harare takeyi, cinkaro da wacce ke tsaye a tsakar gidanne ya sanya fuskarta gaurayewa
Da murmushi, kana tayi haramar isa gunda take tana faman sharce hawayen dake ambaliya a saman fuskanta.

Rungumota tayi kana tace "lafiya kuwa A'ishah¿ Lafewa taƙarayi asaman jikinta kana ta buɗe baki da kƴar tace "Anty hafsat yasakeni wayyoni Allah bala ya cuceni yaci amanata.

Rufe mata baki tayi kana tace "ke lafiyarki kuwa¿ Kiketa faman kuka akan namiji ya sakeki , to miye a ciki¿ Dallah yiwa mutane shuru ai bakanki akafara sakin ƴa mace ba, dan haka share hawayennan kizo muje ki kintsa kamin yayan naki yadawo na sheda masa.

Cikin gida suka nufa , ɗakin yaran gidan ta nuna mata kana tace "ki ajiye jikarki a can kizo kiyi wanka kici abinci kamin ya dawo a san tayi.

Jiki a saɓule tanufi ɗakin , tana tafe uwa wacce bata da lakka.


Raɓen gado taje tayi zaune tana faman sharce hawayen dake ambaliya a saman fuskanta.

Zabura tayi awa wacce aka tsikara ta janyo ƴar ƙaramar jikarta ta janyo wayarta tahau sarrafata .

Number khady ta janyo haɗi da danna mata calling.

Daga can ɓangaren khady kuwa Cikin zaƙuwa ta ɗaga wayar haɗi da karata a saman kunnenta kana tace "hello eshart , gyara zama tayi haɗi da sausauta murya kamar me raɗa tace "albishirinki ƙawata.

Goro mutuniyar kardai kiceman komai ya kankama¿

Wai waye _wai waye tafara ganin ba kowa a kusa yasanyata mayar da hankalinta a kan wayar Kinga khady bara zan shigo unguwarku yau ko gobe akwai story far..!

Daga can khady tace " no mutuniyar just gaya min kina Ina, yanzunnan zaki ganni.

"Okey ina gidan yayana, kizo dan Allah da wuri _ wuri akwai story kinji.

"Okey bani 30minutes zaki ganni.


Ajiye wayar tayi a saman katifar da take
kana ta rafka uban tagumi ta lula duniyar tunani...........✍🏽





*More comment more typing🤸🏽‍♀️.*




~Alƙalamin🖊️ Doctor maryamah!.~


~*_tabbas Alƙalami🖊️yafi takobi🤺._*~




*#Comment*
*#Vote*
*#Share*


*Plx👏🏼.*


*_~ƳAR MUTAN {BUBARE}CE✍🏽!.~_*

*👄🤦🏽‍♀️BAKINA YA JAMIN👄🤦🏽‍♀️.*
_{ƙalubale garemu mata}._




*STORY & WRITING BY DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*




*_MARUBUCIYAR👇🏽._*


*TAWA ƘADDARAR KENAN!.*


*AUTAR MATA.*
_{rikitacciyar yarinya}._



*_And now👇🏽._*

*BAKINA YA JAMIN*
_{ƙalubale garemu mata}._


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com



*بسم الله الرحمن الرحيم.*



*PAGE 8️⃣1️⃣ ↘️ 8️⃣5️⃣.*



________Kinga wannan ba komai bane ki kwantar da hankalinki.

Kinga alaji yace na gayawa Baba yana son ya turo magaba tansa asa mamu rana da zaran ansa rana kinga biki ai ya gurguso idan yaso lokacin bikin ki samu kiyi wuff da wani alaji a cikin abokanan ango....


Shewa suka buga haɗi da taɓa hannu , kana eshart tace "kai gaskiya kanki naja ta hannun dama kinga lafiya launa..

Amman kinsan Allah¿

Wallahi naji ciwon rabuwa da Bala, a haƙiƙanin gaskiya bazan taɓa samun mesona irinsa ba, yanzu matsalar danake ciki itace "nasan muddin yaya yadawo saiya sassaɓani a cikin turmi dan mugun ji da Bala yakeyi.


Mtssssssssass wani dogon tsaki khady taja kana tace "ashe haryau da sauranki, ni nazaci kanki ya fara jaaaa ashe ba haka bane¿

Kinga kiyi watsi da wani waishi Bala kizo mu raƙashe mu wataye.


Kiran da aka kwala wa, eshart a waje ne ya datse firar da suke yi, miƙewa tayi sannu alaikum jikinta yayi sanyi murus domin kuwa ko tantama batayi yayanta ne ya dawo.

Kallonta takai gunda khady take zaune sai faman sarrafa wayarta takeyi.

"Khady jirani ina zuwa inajin yaya ya dawo.

Ɗago kai tayi takai kallonta kan eshart kana tace "okey ina jiran ki idan kuwa kika jima zan fece dan naji ya mama da baba suka kaya batun turo magabatan alajina.

Ba tare da tace mata komai ba tanufi hanyar fita daga cikin ɗakin.



Kira ne ya shigo cikin wayar dake hannun khady , ƙwalalo idanuwa waje tayi lokacin dataci karo dame kiran wayar...

Danna accepting.... tayi kana takara wayar a kunnenta , cike da shaƙiyan ci tafara faɗin "ohh kaga hajiya lawisa matar alaji ɗan tasalle ashe _ ashe anajin ɗuriyar ku, ɗan murmushi lawisa tayi daga can cikin wayar kana tace "haba khady wannan kirarin har ina¿, Ina zamukai wannan kirarin haka¿.

Ɗan ya mutsa fuska khady tayi kana tace "uhmmmm ai kun can _ can ci ko wanne kirari a gareni.

Don ta kawar da waccen maganar ta ɗauko wata tace "amm ba wannan ba khady kwana biyu naji labari a gari cewa aure zakiyi shine ba sanarwa¿.


A'a a'a a'a yanzu har labari yakai gunki kenan¿.


Eh ko aure zanyi insha Allah nan bada daɗewa ba nima zan shiga cikin manyan mata za'a kama da mawa dani ciki da wajen Nigeria.

To Allah yasanya alkheree idan aka tashi kar amanta damu a sanar mamu.

Ba tare da tajira me zata ceba ta katse wayarta don gudun ta jefo mata wata maganar.



*★★★★★★★★★★★★★★*

*After three months later.*


Abubuwa da yawa sun fara tsawon waƴannan watannin abu buwa da dama sun faru, ciki kuwa harda sanya ranar auren khady.

A fannin hameed kuwa shima a bubuwa da dama sun faru a fannin sa , ciki kuwa harda warkewar mahaifinsa sumul harya koma kan harkokinsa nayau da kullum shima ansanya ranar auren sa da wata ƴar uwan mamanshi rana ɗaya dana khady za'a sha shagali kenan..



*taufar 🤔 ranar da muke jira yau gata tazo fa🤸🏽‍♀️.*


*Ina anty Ummu inte....*

*Anty Ummu Affan karki bari a barki a baya fa*


*Wowww harna tsinkayo anty hauwa tasha gwagwaro fa😃 lox.*



*To pans ku biyoni sannu a hankali domin jin yadda shagalin bikin zai kasance😘.*





*More comment more typing🤸🏽‍♀️.*





~Alƙalamin doctor maryamah🖊️.~


*_~tabbas alƙalami🖊️ yafi takobi🤺.~_*






*#Comment*
*#Vote*
*#Share*


*Plx👏🏼.*




*_~ƳAR MUTAN {BUBARE}CE✍🏽!.~_*

*👄🤦🏽‍♀️‍ BAKINA YA JAMIN👄🤦🏽‍♀️.*
_{ƙalubale garemu mata}._




*STORY & WRITING BY DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*


*_marubuciyar👇🏽._*

*TAWA ƘADDARAR KENAN!!!.*


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*AUTAR MATA*
_{tikitacciyar yarinya}._


*And now👇🏽.*

*BAKINA YA JAMIN*
_{ƙalubale garemu mata}._






*بسم الله الرحمن الرحيم.*



*PAGE 8️⃣6️⃣ ↘️ 9️⃣0️⃣.*





________Ayau jummu'a 7/8/2020 dubban juma'ar musulmi suka sheda daurin auren Alhaji rabi'u me daƙaulen kaji da amaryarsa nana Khadija a kan sadaki dubu ɗari cifff!.



★★★★★★★★★★★★



A can cikin gida kuwa , maƙil yake da mata, sai faman sha gul _ gula akeyi.

Shewa najiyo daga cikin wani ɗaki da sauri na nufi ɗakin domin dauko maku rahoto.




Ɗakin maƙil yake da ƴan mata da zawarawa haɗi da matan aure dan kunsan mutuniyar ta mutane ce.


Kinga matar alh me dakwalai , takawarki lafiya, yanzu nan da zuwa wata ɗaya bama ganeki daɗa , dan kuwa hutu idan yaratsa wannan fatar taki baza a gane kiba.

Kinga eshart bana son shaƙiyan cinnan naki miƙomin wayata na kira alaji naji muryasa.

Ai kuwa ɗakin ya dauki shewa da kuwa ce _ kuwa cen su , wata daga cikin zawarawan ce tace "oh ni hafsatu, khady me kikeci na baka na zuba¿, nace dai alajinnan yau dashi zaki kwana a ɗaki ɗaya a gado ɗaya, dan haka yanzu ki barshi cikin al'umman annabi da suka zo tayashi murnar mallakar mace kamarki.

Ki bari har dare yayi wannan kam domin kuwa daren shine lokacin ki, idan yaso saiki cinyesa ki lashe kayanki.

Kwashewa sukayi da dariya gaba ɗayansu ƴan ɗakin , kana eshart ta caɓe zance da cewa "ke hafsy aikinyi kure a maganarki ta ƙarshe , inda kike cewa " ta canyeshi ta lasheshi, ai saidai ya cinyeta ya lasheta dan ingaya maki da ganin wannan alajin kinsan ba dama, yau mutuniya za a zama mace.

Waƴannan dama waƴansu magan ganun ne sukayi ta tashi a cikin ɗakin.

{nikam abin yayiwa kwanyata girma beyiman nauyi ba dana dauko maku rahoto Amman muje zuwa dai}.




Ƙarfe takwas dai_dai aka fara kwasar ƴan matan amarya da zawarawan amarya zuwa wajen dinner daga can za'a wuce da amarya gidan mijinta.

★★★

Kai tsaye *meena event center* aka zarce da ƙawayen amarya.

Masha Allah, wuri ya ƙayatu iya ƙayatuwa , dole ma ya burge duk wata halitta dake wajen.

Anan waje aka ajiye dukkanin mutanen da aka dauko daga can gidanna su, ana jiran amarya da ango domin girmamawa zuwa garesu.


Few minutes later.

Wata hatsabibiyar mota ce, fara sol! ta ƙayatu da jajjayen furanni, hankalin jama'a gaba ki ɗaya saida ya karkata ya koma kan motar.


An dauki tsawon mintuna ƙalilan kamin a wangale murfin motar, kana daga bisani saiga amarya da ango sunfito , taku sukeyu a hankali hannayensu sakale dana juna, nan danan gurin yadauki shewa da taɓi raff_raff_raff kakeji.

Su hajiya khady kuwa kai yaƙara girma, tafiya takeyi cike da taƙama da gadara, domin kuwa anata ganin tafi kowace ƴa mace sa'ar samun miji wanda yatara dukkanin abinda alajinta ya mallaka.


Anci ansha ancashe, haka zalika naira tayi kuka a wajen, ƙarfe 12:00am taron ya tashi.

Kai tsaye gidan angonta aka wuce da'ita.

Gidane daya amsa sunan gida, a waje tubarakallah masha Allah an ƙayata komai da komai Yadda Yakamata a waje.


Cikin gidan aka wuce da amarya darect.

Birki ƴankai amarya su kaja a parlon, ina ganin hakan na kutsa kaina daga ciki domin ganin meke wakana ne¿.

Kujerune guda biyu dasu ƴan filla_fillah dasu a ajiye cikin parlourn, inada yaƙinin kuma ganin sune ya da ƙusar da ƴankai amaryar a parlon.

Ɗan yaƙe , ɗaya daga cikin ƴan dauko amarya tayi kana tace "ah lafiya kuka ja tunga anan kuwa¿.

Muje ciki mana domin sada amarya da ɗakinta mana.

Jiki a sanyaya suka kama hanyar bedroom ɗin , yayinda ga baki ɗaya hankali khady a tashe yake dan kuwa bata san, meke wakana ba, Cox fuskarta lulluɓe take a cikin mayafi.

Canma cikin bedroom ɗin gashinan ga kamar sane.


Ba tare da ɓata lokaci ba kowa yakama gabansa, sai faman tsegum_tsegum akeyi.


Buɗe mayafinta tayi haɗi da fara waige_waige domin ganin me dame, iyayenta sukayi mata¿.

Zumbur ta miƙa , ganin ɗakin nata sai a slow, parlour ta fito domin ganin wace waina ce, aka toya mata a ciki¿.

Birki taja , lokacin dataci karo daƴan kujerun da suke shimfiɗe a cikin ɗakin.

Da gudu ta koma saman gado , tana faman kuka sai kace wacce a kayiwa bushara da wutar jahannama.

Hankalinta idan yayi dubu to ba, shakka ya tashi.


Yanzu wulaƙancin da alaji yayiman ya kyauta kenan¿.

Yanada kuɗi shine bazai sayaman ƴan kayan ɗakin dazai fitar dani kunya ba¿.

Amman bara ya shigo ni dashine wallahi , me rabani dashi sai Allah.

Miƙewa tayi , tafara rage kayan jikinta, tana kammalawa tanemi guri a ƙasa tayi zaune tana faman rera kuka ƙasa_ƙasa.

★★★

Shi kaɗene ya shigo cikin ɗakin, sai faman washe haƙora yakeyi yana faman baza malum_malum a ƙasa.

Kai tsaye bedroom ya shige ba sallama ba komai.

Birki yaja lokacin dayaci karo da'ita dirsham a ƙasa tana faman rera kuka..
...✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽.




*More comment more typing🤸🏽‍♀️.*





*αℓƙαℓαмιи ∂σ¢тσя мαяуαмαн✍🏽.*

~tabbas alƙalami🖊️yafi takobi🤺.~



*#Comment*
*#Vote*
*#Share*


*Plx👏🏼.*


*_~ƳAR MUTAN {BUBARE}CE✍🏽!.~_*


*👄🤦🏽‍♀️BAKINA YA JAMIN👄🤦🏽‍♀️*
_{ƙalubale garemu mata}._




*STORY & WRITING BY DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*





*_marubuciyar👇🏽._*

*TAWA ƘADDARAR KENAN!!!.*


*AUTAR MATA*
_{tikitacciyar yarinya}._



*_And now👇🏽._*


*BAKINA YA JAMIN.*
_{ƙalubale garemu mata}._





*بسم الله الرحمن الرحيم.*


*PAGE 9️⃣1️⃣ ↘️ 9️⃣5️⃣.*


_____Da saurinsa yayi facali da ledar dake hannunsa ya nufi gunta.

Kafaɗɗunta ya riƙe ya miƙar da'ita tsaye ya haɗa da cikinsa, ƙara lafewa tayi a cikin jinnasa sai faman shashshekar kuka takeyi.

Bubbuga bayanta ya farayi alamar rarrashi.

Karo na farko daya buɗi baki yayi magana tun shigowarsa cikin ɗakin yace "meyake faruwa beauty¿.

Ɗago jajajen idanuwanta da suka rine akan kuka tayi takai kallonta a kansa kana murya a dashe tace "yanzu alaji ka kyauta man kenan¿.

Na tabbata ka shigo gidannan kaga kalar kayan da'iyayena sukayi man , amman shine koƙi canja man waƴansu domin kafitar dani kunya.

Allah ka bani mamaki.

Janye ta , daga jikinsa yayi kana ya sanya hannu ya fara cire malum_malum ɗinshi , daga bisani kuwa yace "lallai ma , gaskiya kin can_can ci a baki muƙamin marasa kunyar farko a Nigeria.

Eh mana marassa kunya , idan bashi ba, tayaya zaki zoman da wani banza zance a daren daya fiyeman ko wanne dare muhimmanci¿.

To bara nagaya maki, kuɗina ba kuɗin cii bane!.

Duk wanda zaici kuɗina to tabbas saiya shirya!.

Don haka idan har kinason na canja maki dukkanin abinda iyayenki sukayi maki , to tabbas sai kinyi aiki a ƙasa , aikin kuwa shine,

Kullum safe ta Allah safe, rana, maraice, saina kaiki gun dodon tsafinmu ya sadu dake.

To ingayamaki , ba shakka komi da komi da kike buƙata indai a kwaishi a duniyarnan tamu to saikin mallake shi.

Dalilin gayamaki danayi shine.

Wannan abin ba'a ɓoye ɓoye, fitowa kakeyi fili ka gayama wanda za'ayi sha'anin dashi.

Don haka zan baki lokaci kiyi shawara da ziciyarki...


Be jira mezatace ba yayi ficewarsa daga cikin ɗakin , harya kai bakin ƙofa ya waigo yace "ga abincinan kici kije kiyi wanka kiyi brush kizo ki sameni a ɗakina yananan ƙasa me kallon wannan ɗakin, na baki 30minutes idan bangan kiba, hummm ya girgiza kai yayi ficewarsa daga cikin ɗakin.


Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wayyoni Allah na, yauna shiga ukku na jawa kaina bila'i.

Ya Allah ka kareni da sharrin wannan bawan naka.

Tabbas tun banje ko'ina ba, nafara dana sani.

Haka tayi ta , kururuwa da neman tsari a gurin Allah.

Tafi 20minites a zaune tana tafaman kuka , sai can tamiƙe da saurinta ta sanyawa ƙofa key kana ta koma ta zauna taci gaba da kukanta.



Kai tsaye ɗakinsa ya nufa, ya watsa ruwa kana ya dauko waƴansu magunguna kashi kashi , yahau ɗiɗɗi gawa cikinsa, kana daga bisani ya janyo wayarsa yahau sarrafa ta.

Kallon a gogon kan wayar yayi yaga har 1:30am ba'ita ba alamunta.

Miƙewa yayi a fisace ya doshi hanyar ɗakin nata, jin ɗakin a ƙargame ya sanya shi komawa nashi ɗakin ya dauko wani key ɗin kana ya dawo yasanya ya buɗe ƙofar.

Har yanzu tana zaune a inda ya barta tana faman kukan, da alamu kenan ko wankan dayace tayi batayi ba kenan.

Tana ganinsa ta miƙe da sauri yahau ja da baya.

Hajaran majaran ya nufantota, tanayi tana jaa da baya, hankali a tashe, yayin da shi kuwa yake biyar ta.

Saida tadan ganta kanta da ginin ɗakin kana ta tsaya, kanta a ƙasa tana faman tsiyayar hawaye.


Finciko gashin kanta yayi ya jefata a saman gadon kana ya bita, ya tumur musheta a wa wani tsohon zaki.

{Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!}. Na tsorata iya tsorata ganin ta hanyar da Alhaji ya afkawa khady , sai kace wani tsohon bunsuru.

Jikina na ɓari nayi maza na fice daga cikin ɗakin domin kuwa wannan abin yafi ƙarfina.


★★★



_______Rayuwa ta juyewa khady iya juyewa kuwa , domin kuwa muddin bakayi mata cikakken sani ba, ba shakka bazaka ganeta ba.



Kinga eshart wallahi a halin yanzu ina cikin halin ƙaƙaniƙa a cikin gidannan, wallahi gidanmu ya fiyeman wannan gidan sau dubu , domin kuwa bala'in dake cikinsa yawane dashi.

Kinga gabaki ɗaya alaji ya kassarani, baya saduwa dani a ko'ina saita baya.

Yakan sadu dani ta gaba amman yafi saduwa dani ta gaba, tana maganar tana kuka.

Eshart tunda nashigo gidannan ba safiyar da bana zubar da wayena akan bila'i.

Ya hanani zuwa ko'ina balle na nemi dauki a gun jama'a.

Wannan bala'in dame yayi kana dan Allah.

Tabbas khady kina cikin halin rayuwa dani dake bansan wacce tafi wani ba.

Domin kuwa ingaya maki , tunda na fito daga gidan bala wallahi ba wanda yataɓa zuwa yayi sallamah dani.

Yayana yanzu haka yace ya gaji dani ya gaji da ciyar dani, tunda besan meya aikeni kassara aurena ba.

Wallahi khady ina cikin tashin hankali wanda baya misaltuwa.


Eshart naki me sauƙine ni nina jawa kaina wannan bala'in ba kowa ba, kinsan dalili kuwa¿.

Girgiza kai tayi ba tare da tayi magans.

Eshart nan ba yadda kalar namijin da ban wulaƙan taba, muddin kazo guna na haska idanuwana naga ba mota a tare dakai nake zazzagama rashin m... na wucewata, nice ke faɗar bani ba talakka.

Yanzu ba gashi na auri me kuɗin ba, yazo ya kassaraman rayuwa ba¿.

Kinga ba makawa *BAKINA YA JAMIN* wannan iftila'in.

Rushewa sukayi da kuka su dukan su.

Tabbas kuna cikin halin rayuwa ƴan uwa.



★★★★★

Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, yau kimanin shekaru 3 kenan da auren khady da Alh me dakwalan kaji, rayuwa ta juyawa khady domin kuwa ko waye kai bazaka taɓa gane khady a wannan yanayin ba.

Tayi baƙi ta rame, ƙasusuwane kawai a jikinta.

Zuwa wannan lokacin tayi nadama ba'adadi tayi data sanin kafewa ba'ita ba auren talaka yanzu ga inda auren me kuɗi yakaitanan.



Fitowa tayi daga ɗakin Alh dake kwance ba lafiya ko ita tanajin jikinta ba daɗi ƴan kwana kinnan, dauriyace kawai takeyi.

Freezer ta buɗe ta dauki swan ɗaya haɗi da cup , ta koma juyawa ɗakin Alh.

Taddashi zaune tayi tabashi ruwa yashs kana , ta mayar dashi ta kwantar kana takai kallonta a kansa.

Wai Alh mizai hana , katashi muje asibiti domin a san meke damunka¿.

Shurune ya biyo baya , sai can alamun yana jin jiki , ya kalli khady kana yace "jeki ki gayawa direba ya fito da mota yakaimu asibitin.

Jiki a saɓule ta miƙa ta nufi harakar gidan haɗi da kwalawa direban kiran.

Umurnin fitowa da mota ta bashi kana ta juya ta koma cikin gidan.

★★★


Jinsu aka ɗiba su dukansu a cikin labaran ɗin, kana aka bawa Alh gado , ita kuwa tayi zaman jiran result.✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽



*More comments more typing🤸🏽‍♀️.*



~alƙalamin🖊️ Doctor maryamah.~


~tabbas alƙami🖊️ yafi takobi🤺.~



*#Comment*
*#Vote*
*#Share*

*Plx*


*_~ƳAR MUTAN {BUBARE}CE!✍🏽.~_*


*👄🤦🏽‍♀️BAKINA YA JIMIN👄🤦🏽‍♀️*
_{ƙalubale garemu mata}._

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


*STORY & WRITING BY DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*




*_marubuciyar._*

*TAWA ƘADDARAR KENAN!!!.*


*AUTAR MATA*
_{tikitacciyar yarinya}._


*And now👇🏽.*


*BAKINA YA JAMIN*
_{ƙalubale garemu mata}._
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com





*بسم الله الرحمن الرحيم.*

*PAGE 9️⃣6️⃣ ↘️ 1️⃣0️⃣0️⃣.*

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

_____Kwance yake a saman gadon marassa lafiya, shigowa nurse sukayi riƙe da'ita sai faman tsiyayar hawaye takeyi.

Yana ganin anshigo da'ita yayi maza ya fincike ƙarin ruwan da'ake yi masa yayi gunsu da sauri awa wani tsohon zaki.

Sakinta nurse ɗin sukayi da sauri suka fice daga cikin ɗakin da gudu, domin kuwa sun zaci gunsu yanufa.


Maƙuro wuyanta yayi , Muryarsa cike da ƙaraji da alamun ɓacin rai ya fara magana kamar haka "ke dan gidanku ashe idan bananan yawon sha_shanci kike zuwa ko¿.


Yanzu ga shinan kinje kin kwaso mamu cutar datafi ƙarfinmu.

To wallahi bazan zauna dake ba!.

Yauɗinnan saikin barmin gidana , cuta ce dai kinriga kin cutan Allah saiya sakaman wallahi.

Don haka kije na sakeki saki ukku!.

Be saketa ba, saida yayi mata jina_jina kana ya turata wajen ƙofa.

Likitocin da sukazo kawo a gaji, sune suka dauketa a kaje a kayi mata treatment ɗin gurin daya jigata ta.



★★★★★

Kai tsaye gidansu ta nufa hankalinta a matuƙar tashe domin kuwa bata san irin tashin hankali da mahaifiyarta zata shiga ba, idan har taji irin cutar da take dauke da'ita.


Sallama tayi a cikin gidan haɗi da cusa kanta a cikinsa kai tsaye, ba tare data jira komai ba ta faɗa ɗakin mahaifiyarta.

Ɗago kan da zatayi sai kawai taga mutum tsaye saman kanta tana faman share hawaye.

Boyar Allah daga ina¿.

Ƙara rushewa da kuka tayi kana tace "mama kina nufin baki ganeni ba¿.

Salallami tahauyi haɗi da tasbihi zuwa ga Allah.

Kamo hannunta tayi kana tace "Nana Khadijah lafiya kike kuwa¿.

Meya sameki haka shine kikayi jinya ba'azo a ka gaya mamu ba¿.

Rungume mahaifiyarta tayi , tana ci gaba da ɗarzar kukan da batasan ranar ƙarewar saba.


Sai bayan ta nutsune kana tahau bawa mahaifiyarta labarin halin da take ciki a gidan Alh kana ta daura mata da cewa "mama Alh ya sakeni har saki ukku, dalilin anyi mamu test dani dashi duk an samemu dauke da cutarnan me karya garkuwar jiki.

Kuka mahaifiyarta ta fashe dashi kana daga bisani ta saussauta ta dubi khady tace "a haƙiƙanin gaskiya Nana Khadijah na tausaya maki na tausaya wa , ni kaina mahaifiyarki da mahaifinki.

Cutuwace Alh ya cucemu, ubangiji Allah yasaka mamu.


★★★★★★★★★★★★★★


Zaune take a bakin titi , tasa ce ajiye a gabanta yayin da talula duniyar tunani.



Wata hatsabibiyar mota ce, ta gifta ta gun, sai Kuma gata ta dawo da baya da baya, haɗi da zuge glass ɗin motar, tabbatar da tabbas ita ɗince wacce yake zargi ya sanya shi fitowa daga cikin motar kana ya leƙa cikin motar yace "Habibah zo muje dan Allah.

Cike da mamaki wacce aka kira da habiba ta fito daga cikin motar hannunta janye da wani yaro mai kimanin shekaru 3 a duniya.

Gunda take zaune yanufa , tabbas ita ɗince kuwa yaƙara faɗa cikin zuciyarsa.


Ƙamshin hatsabibin turarensa ne, ya fargar da'ita duniyar tunani data shige.


Miƙewa tayi a matuƙar razane ganin ko waye a gabanta yayin da bakinta ya kasa furta kalma ko ɗaya.


Kallonta yakeyi cike da mamaki da al'ajabi haɗi da ƙarajin tsoron Allah a cikin zuciyarsa.



Hameed!!!.

Tafaɗa cike da tsoro.

Mamakine ya kamashi jin ta ambaci sunansa kai tsaye.


Tabbas Allah ba'abinda ya buwayesa , yau naƙara gasgata cewa ɗan adam bakomai bane a cikin duniyarnan tamu ba, face dana sani dake tattare dashi.


Bazan so jin komiye a dangane da rayuwarki ba Nana Khadijah, domin kuwa ko miye bayada daɗinji anan gurin.

Juyawa yayi gun matarsa kana yace "Habibah kinga wannan itace Nana Khadijah dana ke, baki labarinta a kwanaki, itace mace ta farko kuma ta ƙarshe data taɓa ɗaga hannu ta mareni taciman mutuncin da haryau ba mahaluƙin daya taɓa yiman shi ba.

Ya juya gun khady yace "Nana Khadijah kinga wannan itace matata wannan kuwa ɗanane, sunansa Muhammad.

A haƙikanin gaskiya lokacin da kikayiman wulaƙaci naso na dauki mummunan mataki a kanki, saidai Allah benufa ba.

Amman na yafe maki duniya da lafira, Allah yayafe mamu.

Yasanya hannu a cikin aljihun wandonsa ya zago kuɗin da koshi besan adadin suba kana yace "ga wannan kije ki samu sana'a kiyi , domin kuwa a haƙiƙanin gaskiya bara bekama ceki ba.


Hannu na rawa tasa hannu ta amsa haɗi da godiya.

Batare daya ƙara cewa komai yaja hannun matarsa ya duƙa ya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment