Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'an kunnen Jiddah ne  guda daya ya fad'i sanda suka dawo daga asbiti".

Tace "anan ya fad'i shine nace bari na duba ko zan gani".

"haba Momy ke da kanki ina sauran yaran gidan?".

"Suna ciki Khadija ta ce ta gaji zata shiga ta huta dan ko abincin rana bata ci ba, Umar kuma yana tare da Jiddah, Ummi kuma tun safe ban kuma ganin ta ba".

"Kibar neman haka Momy muje ciki ba rabon ta bane kawai sai asai mata wani".

"dama a cikin irin tsara bar da auntyn kaduna ta kawo musu ne alokacin da ta dawo daga India daham ne yanada tsada sosai yanzu ita kadai ce ba ta da".

"Momy ita ta jawa kanta".

Siddeeqah kamar ruwa ya cinye ta Momy ce ta kama hannun ta tace "muje ciki yau na girka abinda ki ka fi so a bincin gargajiya".

"dan Allah fa Momy?".

"zan miki 'karya ne?".

"a a Momy".

Ta fad'a tana rufe fuskan ta da tafin hannun ta ahaka suka karasa cikin gidan Siddeeqah na mamakin Sadeeq,

Yayin da shi kuma ya ji haushin ganin  Momy a harabar gidan batare da ya ma Siddeeqah matsiyacin duka ba dan so yayi ya mata dukan ban kwana saboda ba lallai ya kuma haduwa da ita ba har sai ta dawo hutun makaranta, yanda bazata manta dashi ba

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Kamar wacce tayi karya takai ta komo tarasa ina zata sa kanta dafa kafad'ar ta akai da han zari ta dago kanta ganin Lubancy ce Kawar ta yasa Zuby sauke ajiyar zuciya tace "kawata kin zo a dai dai dan dama yanzu nike shirin zuwa gidan ku wallahi ina cikin tashin hankali nasan babu Wanda zai fitar dani saike".

"haba ke kuwa kinada ni kike cewa kina cikin tashin hankali kin manta wace ni kin manta kirari na? Bari na na tuna miki".

"a a barshi ban manta ba kai na ne ya kulle na rasa mai yake min dadi, sai yanzu dana ganki na ji sauki a raina nasan ke a wurin ki ba komai bane soboda na shiga matsalar da tafi wannan kuma kin mini maganin ta".

"yauwa yar gari  ashe baki manta da wace ce kike tare da ita ba".

Zuby tace "kawa ta mu zauna na baki labarin abinda ya sa na shiga cikin tashin hankali".

Saida Lubancy ta je ta  bude karamin fridge din dake dakin ta dauko goran lemu sannan ta dawo ta zauna a bakin gado tace
"ina jinki".

"ina wannan gayen da nike baki labari Wanda na had'u dashi a Instagram kwanaki kin tuna shi?".

"Eh anyi haka na tuna to mai ya faru dashi ko shima an fad'a masa halin ki ne".
Lubancy ta fad'a haka tana duban kawar ta

"ko daya kawa ta nan take Zuby ta kwashe duk abinda ya faru ta fad'a ma Lubancy,

tsaki Lubancy taja kana tace "wallahi Zuby kina bani mamaki d'an karamin abu duk ki bi ki tada hankalin ki ba kin ce   yana soki ba?".

"Eh yana sona na gani a cikin 'kwayar idanun sa".

"kuma kince yarinyar suna kama".

"wallahi suna masifar kama abinda ya bani haushi" da yace" min 'yar mai gadin su ce baki ga yarinyar ba kama da larabawa take yi".

Lubancy tace "dadi na dake gajen hakuri da kin bisa a yadda  yace idan ma da wata a 'kasa zamuji daka baya, kince kina son sa kuma auren sa zakiyi kin tafka kuskure da kika ce masa karya yake saboda shine gaba dake, amma ko nan gaba ki kiyaye kisan kalar maganar da zaki dunga gaya  masa, Zan san yadda zamu bullo wa lamarin, saboda nima yanzu tawa ce ta kawo ni tun jiya da muke chart kika fad'a min kin gama al'adar naji kamar nayi tsun tsuwa nazo saboda nayi missing d'in ki ".

"Kawata kenan wallahi bakida hakuri". Zuby ta fad'a tana zuge zif d'in rigar ta,

ita ko Lubancy dama doguwar riga ce ta zumbulo sai undies da ta saka nan take ita ma ta cire doguwar rigar tayi cilli da ita ta kamo Zuby suka 'karasa cire ma juna kaya,

sosai Lubancy ta rikice saboda Zuby Allah ya yi mata baiwar komai bata da makusa a halittar  jikin ta shine ke rud'an maza

sakonni suka fara aika wa junan su sosai suke romance suna ihu. Babu inda basa tabawa a jikin junan su

Wa'iya zu billah lallai halin Zuby sai ita baza taso Sadeeq ya sani ba dan shi kamilar mace yake so ya aura,
ja musu 'kofar nayi ina takaicin rayuwar Zuby

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Ina cin danbun ina side yatsun hannu na Ummi na hango tana sauko wa daga sama dinning din tazo ta zauna da alamar daga bacci ta tashi saboda yadda idanuwan ta sukayi, kallo na tayi tace "maiyar dambu sai kace kin samu wani abun dadin, ko naman kaza baki masa irin wannan santin, ni kuma wallahi na tsane sa dole nike ci nasan Daddy ne yasa Momy tayi dan shima yana son dambu".

Nace "yarinya da kinsan kalan dadin da nike ji alokacin da nike cin dambu da ko magana aka ce ki min bazaki ba saboda idan zan baki amsa a cikin santi zan baki yanzu dai bari na gama sai ki sake maimaita abinda kika fad'a".

Ummi tace "tab sai na tsaya har sai kin gama kamar yarinyar ki bani da wannan lokacin bari naje ko Indomie na dafa dan yau ba zanci danbun ba".

"ke dai kika sani idan za a shekara ana jera yin dambu babu abinda zai dame ni".

"uhm". Ummi ta fad'a ta nufi hanyar kitchen

Umar ne tafe rike da hannun Jiddah tana ta ciza lebe ahankali suka karaso gurin Umar yai sauri ya ja mata kujera tai saurin dakatar da shi da fad'in "Umar mai kake shirin yi haka to wallahi na daina had'a gurin zama da wannan 'yar kauyen muje falo idan ta gama sai nazo muci".

Kallon ta nayi na kwashe da dariya nace "da alamar har yanzu bakin ki bai mutu ba".

Umar na kalla nace "wai ka nuna mata madubi kuwa? na tabbatar da  taga yadda nayi mata da ko suna na taji an ambata gaban ta ne zai fad'i dan Allah idan bata ga ni ba maza je ka d'auko saboda ina son ta san ruwa ba sa'an kwando bane".

"Aunty Siddeeqah dan Allah ku daina wallahi banajin dadin hakan ko kadan". Umar ya fad'a kamar zai rushe da kuka

ganin haka yasa nace "to shikenan kani na ya wuce amma kaja mata kunne kasan ni duk Wanda yai min kan kara na itace nake masa".

Umar yace
"Aunty Jiddah muje".

A masifan ce Jiddah ta kwace hannun ta fuuu ta wuce falo ta zauna tana kananun magan-ganun da ita kadai tasan mai take cewa

🤙 _Hy guys please don't forget to comment vote and follow me on Wattpad join my group on Telegram please please please_ 🥰

NI DA YAYA SADEEQ

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Chapter 21

So sai Siddeeqah take dariya harda rike ciki, tana ayyana yadda zata gyara ma Jiddah zama dan wallahi ta daina daukar rainin hankali

Take Umar ya mara ma Jiddah baya yana ma-ma kin tsanar da suka ma juna kamar ba 'yan uwan juna ba

A zaune ya sami Jiddahn a kan kujera sai cika take tana batsewa tana ganin sa ta daure fuska tace "mai kazo yi wuce ka bani guri munafuki ni zaka raina ma hankali a gaba na za ka dunga yiwa waccan yar kyauyen magana? Har da ce mata aunty saboda munafurci na cin ka". Ta karasa maganar tana nuno masa inda nike

shi dai Umar bai ce mata komai ba sai ma-maki ma da ta kara bashi

Jin kamar ana hayaniya Momy ta fito da Alamar daga bacci ta tashi, a dai dai lokacin Ummi ta fito daga kitchen hannun ta dauke da plate din abin ci, kallon mu Momy ta shiga yi ido cikin ido daga karshe ta sauke su akan Jiddah tayi mata kallo irin na gar gadi, ba tare da tace mana komai ba ta koma ciki abin ta

Ummi kuwa zama tai a dinning din tana fadin "wash Allah na".

Kallon ta nayi nace "kefa raguwa ce daga dafa Indomie sai kizo kina wash kamar wacce tayi abin a zo a gani?".

"Bazaki gane bane". Ummi ta fada tana kai lomar Indomie

Shi kuwa Sadeeq tun sanda suka shigo ya haura sama soboda yana bukatar ya huta dan zubi ba karamin bata mishi rai tayi ba sosai yake ma-ma kin ta dan shi baya son rashin kunya musamman ma idan yasan ya girmi mutum to yana so a girma ma shi, a gogan hannun sa ya cire tare da lalu ba aljihun sa ya ciro wayar sa ya aje a kan madubi kana ya shiga cire kayan jikin sa, wannan ita ce dabi'ar Sadeeq a duk sanda zai shiga wanka sai ya fara cire kayan sa a bedroom sannan ya ke shiga bayi, to bayan ya shiga ya dauki kusan mintuna 43 a cikin bayin yana cuda jikin sa ya zuba wancan ya zuba wannan sai da yaji kam shin ya mishi yadda yake so, sannan ya fito daga cikin kwamin wankan ya zo gurin da tawul yake a rataye ya daura a kugun sa kana ya dauki karami ya shiga goge kansa daga haka ya fito a bayin

* * * * * * *
A ban garan su Zuby kuwa bayan sun gama fasikan cin su suka shiga wanka nan ma sai da suka bata mintoci suna kissing din juna kamar wasu mata da miji Zuby ta manta da wani Hallita mai suna Sadeeq saboda Lubancy ba baya ba wajen romance ta iya solon makirci da yaudara kala kala

Bayan sun fito daga wan kan ne suka shafa mayuka masu kam shi tare da fesa body sprea riga da wando Zuby ta dauko a cikin durowar ta kana ta duby Lubancy tace "sweety wani kalar kaya zan fiddo miki?".

"My love duk wanda kika dauko min zan sa". Lubancy ta fada cikin salo mai Jan hankali

To bayan sun gama shirya wa suka shiga fesa tura ruka masu sanyin kamshi gami da daukar hankalin wanda duk a ka gibta ta kusa dashi,

Hijabi suka zum bula har kasa tare da saka safa a kafar su ke idan ki ka gansu zaki rantse mutanen arziki ne

Falo suka fito inda suka tar da Mama zaune tana kallon BBC World news, ta maida gaba daya hankalin ta da nutsuwar ta akan TV

Kamshin tura-ran tilon diyar ta-ta a duniya ne ya dawo da ita ga barin kallon TV

kallon su tayi cikin sakin fuska tace "kar dai har zaki tafi?".
Mama ta fada tana duban Lubancy wacce ke tsaye tana dan Murmushin tace "Eh Mama zan tafi dama sako na kawo mata".

Kallon Zuby Mama tayi ta ce "iya rigima ina zuwa kuma? ko rakiya zaki mata".

"Eh mama". Zuby ta bata amsa a takai ce

To babu damuwa ki dawo Lafiya amma gaskiya yau kar ki dade kin San abban ki yana gari, motsi kadan yace "kina ina?". Sai dai nayi masa karyan kan ki na miki ciwo kina bacci kin ce kar a tashe ki har sai kin tashi, kiss Zuby ta manna ma Mama a goshi tana fadin "Allah ya bar min ke Mama na I love you". "Love you too". Mama ta fada tana dariya irin ta-su ta manya da yike ita ma irin gogag-gun iya yan nan ne, kuma ta san da duk wani abu da diyar ta-ta take aika wa asali ma ita ce ta sata akan hanyar

* * * * * * * *
To a bangaren Sadeeq kwance yake a kan make kyan gadon sa idon shi a rufe kamar mai bacci amma kuma ba bacci yake ba a duniyar tunani yake

Wayar sa ce ta shiga ringing amma be da niyar dauka har kiran ya katse saida a ka sake kira a koro na biyu ya bude raunan-nun idanun shi ya lalabi wayar ganin sunan Farooq na yawo akan screen d'in wayar ya danna picking kana ya kara a kunne

daga can ban-garen Farooq yace "kai bana son iya shege tun dazun nike kiran ka baka dauka ba, ba yan kasan haka kawai ba zan dunga kiran ka ba".

"Ina jin ka to". Sadeeq ya fad'a yana cin magani

Farooq ya kwashe da dariya yace "dan iska wannan ji da kan naka ba shi zai sa a dunga maka abinda ka ke so ba, ni dai kasan ba tsoran ka zan ji ba ko?".

Cikin jin haushin kalaman Farooq Sadeeq yace "malam ya i she ka haka ka fadi abinda ya kawo ka ina jin ka".

Farooq yace "akan maganar makarantar matar ka ne na gama magana da wannan abokin nawa da yake koyar wa a makarantar ya sama mata admission yace maganar aji sai idan an kaita sun mata interview zasu gane ajin daya dace da ita, saboda haka daga yau zuwa kowace rana zaku iya kaita dan har register yai mata ".

Shiru Farooq yayi ko Sadeeq din zai ce wani abu amma sai yaji a kasin haka,

Bayan wasu yan daki ku Sadeeq yace "ka gama?".

Cikin takai cin abokin nasa Farooq yace "dan iska insha Allah wannan yarinyar da ka ke rainawa sai ta zame maka ciwan ido, yana gama fad'ar haka ya kashe wayar sa

Aje wayar sadeeq yayi gami da daga kafada alamar ko in kula ya tabe baki a can cikin zuciyar sa yana jin dadin zai rabu da ala ka kai

NI DA YAYA SADEEQ

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Chapter 22

To bayan fitar su Zuby gidan su Lubancy suka zarce dake wata unguwa amma unguwar ba ta masu kudi can bace, kuma ita Lubancy iyayan ta sun rasu tun tana yar karama, a gurin kawun ta take, kasance war sa namiji ba ko da yaushe yake gida ba shiya yasa Lubancy ta zama abar da ta zama yanzu duk da matar kawun na kokari amma sam Lubancy ta raina ta bata jin maganar ta, ganin Allah bai bata haihuwa ba kar ta cika matsawa ace dan bata son zafin yara bane shiyasa ma yanzu ta zuba mata idanu, in dai duniya ce wanda bai zo ba ma jiran shi take.

Duk da sun sami matar kawun a tsakar gida, haka su ka wuce ta ba tare da sunyi mata sallama ba, da shigar su dakin Lubancyn suka wuce suna wani  shan kamshi.

A cikin zuciyar ta take musu adduar shiriya dan baza tayi musu mugun fata ba kuma Allah na gani tayi iya bakin kokarin ta dan ta san abin da suke aikata wa ba abin arziki bane, ta bar ma Allah saboda duk zagin da mutanen unguwa suke mata yana dawo wa kunne ta a cewar su "dan ba yarinyar ta bace shiyasa ta barta tana yin abin da ta ga dama". Amma ita ta san d'a a wannan zamanin ko kai ka haife shi sai kayi hakuri da shi.

* * * * * * * * *
To bayan sallar isha'i ne Daddy ya ce wa Momy "ta je ta kira masa yaran gidan zai yi magana dasu". Ba tare da tayi musu ba ta ce mai "to".

Falo ta fito in da ta kwalama Suwaiba mai aiki kira, nan take suwaiba ta zo tace "na'am". Momy tace "haura sama ki kira min yaran nan, ki tabbatar kin fada ma ko wacce su".

"To Hajiya".
Suwaiba ta fada kana ta haura sama

Dakin Khadija ta fara zuwa in da ta shiga buka kofa  ba ta wani bata lokaci ba Khadijan ta zo ta bude kofar ganin Suwaiba tsaye tace "Suwaiba lafiya?".

Suwaiba tace "lafiya lau Hajiya ce tace "tana son ganin ku".

To kice "gamu nan".

Da "to". Suwaiba ta amsa

sai da tabi duka d'akunan yan matan ta sanar musu, sannan ta sauko kasa inda ta tarar da Momyn inda ta bar ta take ta shaida mata gasu nan zuwa kana ta koma bakin aikin ta.

Ku san a tare Siddeeqah da Khadeeja suka sauko dan sun ruga kowa fito wa a lokacin falon babu kowa sai TV da yake a kunne yana karatun Al'qur'ani mai girma

Kusan tare suka zauna kan kujera kowa da abinda yake sakawa cikin ran sa, can dai Khadija tace "sister yau ba magana ne?".

Ita Siddeeqah ba rufi ne da ita ba saboda haka ta mayar wa da Khadija amsar ta da cewa "yo gani nayi kina wani share ni nayi tunanin kina shigar ma Jiddah ne shiyasa ki ka ga ban kula ki ba, saboda na yarda na bata da kowa a gidan nan in dai akan kwatar yanci na ne".

Bata karasa maganar ba Jidda ta sauko ganin Siddeeqah a zaune yasa ta ja dogon tsaki ta ce "sis Khadee me yisa ki ka zauna tare da wannan abar".

Khadija tace "wa fa?".

Nuna ni tayi da yatsa ba tare da ta jiwo ta kalle ni ba,

ganin haka yasa na mike cikin masifa na kama hannun nasa abaki na ganna mata cizo kana na koma gurin zama na kamar ba ni nayi ba.

ai kuwa ta shiga yin kuru-ruwa wanda yai sanadin fitowar su Daddy, Ummi ma da take sama ta ji ihun cikin sauri ta sauko har ta kusan tayi tun tube saboda ko gaban ta bata kalla ba.

Kafin su Daddy su ce wani abu yah Sadeeq ya shigo bakin sa dauke da sallama amma saboda ihun da Jiddah take yi babu wanda yaji sallamar.

Da ma-maki dauke a fuskar Sadeeq ya kara so cikin falon ya ma rasa wa zai tambaya abin da ya faru saboda haka ya jingina da bango ya harde hannayen sa waje guda

* * * * * * * * *
Bayan shigar su Zuby dakin Lubancy ta maida kofar dakin ta rufe da mukulli, kusan zan iya cewa Lubancy bata gajiya da da romance saboda haka ta shiga shafa jikin Zuby take ita ma tsigar jikin ta ya fara tashi nan take suka shiga cire ma juna kaya bayan sun gama suka fada kan katifar Lubancy suna nishi sama sama take suka fara tso-tse tso-tsan juna suna fada ma juna kalamai masu dad'i.

Wa iya zu billah Allah ka shirya mu kashir ya zuri'ar musulmai baki daya

* * * * * * * * * *
Sam sadeeq bai son hayaniya ganin Jiddah bata da niyar yin shiru ya daka mata tsawa, nan take tayi tsit kamar ruwa ya ci ta sai shash-sheka da take yi a kai a kai, sai a lokacin Daddy ya nemu guri ya zauna kana Momy ta zauna ita ma.

Da hannu Daddy ya nuna ma Sadeeq din Kujera alamar ya zauna babu musu ya zauna, an dauki kusan mintuna hudu babu wanda yai magana can dai Daddy yai gyaran murya yace ma Jiddah "ke! Tashi ki zauna".
Saboda a lokacin Jiddah a duke take kan ta a kasa tana sash-shekarar kuka.

Ita ma babu musu ta nemi kan Kujera ta zauna kusa da Ummi sai murza idanuwa take yi.

Bayan ta zauna Daddy yace kafin na fara cewa komai "ku tashi muje muyi dinner".

Gunin sha'awa zaune suke reras a kan dinning din ba ka jin sautin kowa sai karan cokula saboda Momy ce tayi girkin abincin ba karamin Daddy yayi ba jalof din taliya ce da kuma farfesun kaza ga farfesun kifi ga kuskus haka ban garen drink ta hada jus kala-kala dan Momy ba baya ba wajen iya abin ci.

Ina cikin ci Inna ta fado min a rai saboda haka na ijiye cokalin nayi tagumi kwalla na zubo min, Daddy ne ya lura da halin da nike ciki yace "A a mai gaskiya mai kuma aka miki?".

Cikin kuka nace "Daddy Inna na tuna tun nazo banyi magana da ita ba".

Yace "ai ba kuka zaki ba ko Sadeeq ki ka ce ma kina son magana da ita zai kira miki it maza dai na kuka bari mu kammala cin abinci sai a kira miki ita ko".

Ya karasa maganar cikin sigar lallashi nace "to Daddy

 

* * * * *
My Fan's
Please ku cigaba da bani hadin kai saboda shine karfin gwuiwa ta

Dan Allah Wanda beyi following dina ba dan Allah kuyi yanzu sannan ku cigaba da danna min vote kuna aje min comment please show me love 💞❤️
NI DA YAYA SADEEQ

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Chapter 23

 

   Cigaba da cin abincin nayi ina jin dadi har cikin raina yau zanyi waya da inna, saboda zumudi ban wani koshi ba na mike daga kan dinning din

Momy tace min "ina zuwa?".

Naba ta amsa da "na koshi ne".

Bayan na wanko hannu na falo nazo na zauna ina sake sake a raina

can shima yaya Sadeeq ya zo ya zauna, na kalle shi muka hada ido ya banka min harara nima na rama.

Yace "ke da ni ki ke?".

Nace "nima dani kake?".

Ganin ya taso nasan bugu na zaiyi na mike da gudu na nufi dinning ina kiran sunan Momy, ban kai ga karasa wa ba nayi kicibus da ita, da alamar ta tsorata da yadda nike kwala mata kira tace "ke lafiyan ki?". Murya ta na rawa nike nuna mata Sadeeq da saura kiris ya damko ni Allah ya kawo ta.

Sai a lokacin ta lura a tsaye yake sai mazurai yake na rashin gaskiya.

Momy tace "Sadeeq Sadeeq wai sai yaushe zaka girma? To idan ka dake ta me zaka ji?".

Yace "Allah Momy rashin...".

Cikin sauri Momy ta katse sa da fadin "ban tambayeka ba Sadeeq ba tun yau ba nasan halin ka idan aka bibiya kai ne ka fara".

Daddy ne ya zo gurin da muke yace "kai dai Sadeeq anyi katon banza abin kunya ka tsaya kana biye ma karamar yarinya sai kayi ai tunda kaima irin ta ne baka da hankali, ku wuce mu koma falo".

Ya fad'a yana nuna mana hanya Momy ce ta fara yin gaba Daddy yabi bayan ta, ganin da gani sai yaya na kalle sa karaf muka hada ido ya galla min hara ra madadin na rama sai na kwashe da dariya ina yi mai gwalo nace "anji kunya giwa tana fada da shawo inba ga tsoro ba...".

Ban karasa maganar ba ya damko ni ya toshe min baki ya tsats-tsare ni da idanu yace "ke dan uban ki yaushe zaki hankali dan kinga su Daddy na shigar miki shine zaki min rashin kunya dama na dade ina neman wannan damar gashi yanzu na samu zan ragar gaji bakin yarin ya".

Tuni ido na ya raina fata gashi ya toshe min baki bare na basa hakuri

Ana haka sai ga Daddy ya zo wuce wa ganin Sadeeq matse da baki na yasa shi ma-maki dan takai ci bai ce masa komai ba illa  da yace "bani guri na wuce".

Kunya ce ta kama Sadeeq yana sosa keya ya sake ni kana ya matsa a hanya Daddy ya wuce ni kuwa ina ganin Daddy ya wuce na falla da gudu ina haki kamar wacce tayi gudun fan fa laki

Momy tace "keda wa kuma? A ina ki ka tsaya bayan mun taho?".

Sai da na zauna akan kujerar da ke kallon ta nace "kedai Momy ki bari kawai kuna wuto wa ya damko ni ya shake min yuwa tare da toshe min baki, yanzu haka bacin Allah ya kawo Daddy da kashi na ya bushe".

Momy tace "Sadeeq din?".

Nace "kwarai kuwa".

Zatayi magana kenan ya shigo yana dan so sa keya tace "ka kyauta ka nuna bamu isa da kai ba".

Zai yi magana tace "za kai shuru ko sai na saba maka".

Bai kuma magana ba ya nai mi guri ya zauna,

bai jima da zama ba sai ga Khadija da Ummi nan bayan wasu yan daki ku Daddy ya dawo hannun sa rike da na Umar can sai ga jidda nan ita ma fuskar nan tata a kwabe kollo daya nayi mata na kawar da kaina saboda dariya na so ta kama ni zokai zokai tazo ta zauna a kan kujera.

*  * * * * * * * * *

Aban garen zuby kuwa bayan sun gama sheke ayar su, wanka suka kuma yi a gur guje kana suka fito kasan cewar a kwai taron da suke zuwa duk karshen mako, toro ne da manyan mata yan madugo suke sheke ayar su,

sun shirya tsaf cikin wata

1 Comments On NI DA YAYA SADEEQ
avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment