Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga sama d'an kwalin ta rike a hannun ta tana susur kanta d'ayan hannun ta kuma rike take da bakin zanin ta daya kwance tayi wani iri da ita yayanayin ta ya nuna alamar tana cikin damuwa

Kallon ta Momy tayi na wasu 'yan da'kiku bayan ta gama nazarin ta tace "Mai gaskiya lafiyan ki ki kayi zuru zuru dake ko kema yunwar ce".
"wallahi Momy nima haka kawai naji ni wani iri ina Ummi take?".
"Ummi tana sama tun da kuka haura tabi bayan ku kin san ta da bacci idan babu makaran ta tana can tana sana'ar".
D'an ta'ba baki nayi nace to ina Khadeeja?".
"ta raka Jiddah asbiti ayi mata dressing d'in gurin da taji ciwo".
"To Momy nima bari naje na huta".
"ba dai ki huta ba kije ki shirya Sadeeq ya kaiki gurin gyaran kai saboda jibi ne tafiya makarantar ki in Allah ya kaimu".
Jiki na ne yayi sanyi ni wallahi da zasuji ta tawa su 'kyale ni na cigaba da rayuwa ta a haka saboda banga aibin ta ba
"Maza mana kije ki shirya Siddeeqah tunanin me kike yi haka". Momy ta tambaye ni "babu komai". na fad'a ina haurawa sama
Maida duban ta tayi ga Sadeeq da yayi kicin kicin da rai kamar wanda akece ga ranar mutuwar sa "ba sai kaje restaurant ba ga kayan da mukayi breakfast can na hana suwaiba ta kwashe kaje ka karya saboda ka kai Siddeeqah wajen gyaran gashi kanta yayi wani iri".

"Haba Momy asa idi driver ya kai ta mana ni inada uzurin da zanyi". ya 'karasa fad'a kamar zai rushe da kuka
Saida Momy ta 'kare mai kallo sannan tace "lallai Sadeeq kana da aiki tana matsayin matar ka ace sai wani driver ya kai ta gurin gyaran gyashi to kai maye amfanin ka da bazaka kula da iyalin ka ba?".
Yana sosa 'keye ya ce "uhm Momy baza ki gane bane amma wallahi ba wani son yarinyar nike ba kawai dai zan hakura ne saboda nayi muku biyayya".
Tabe baki Momy tayi kana tace "ina tausayin ka Sadeeq amma kaje kayi duniya ce"
Ba tare da yaji komai aran sa ba ya nufi dinning tebur
Momy ma d'akin ta wuce abin ta saboda Daddy yana gida

Zuciyar Sadeeq a cun kushe ya bud'e kular farfesun hanta ya zuba a filet kana yaja kujera ya zauna ya d'auki cokali ya fara cin farfesun amma sai yaji kamar yana cin magani saboda magan ganun da Momy tayi masa basu yi masa dadi ba saboda haka ya bar cin abincin ya ciro wayar sa yad'an shafa screen d'in wayar ya danna number Farooq saida Wayan ta fara ringing sanan ya kara a kunne ringing d'in farko Farooq d'in ya daga yace "officer officer". Muyan Sadeeq a murtuke yace "kayi maganar makarantar yarinyar nan kuwa?".
"d'an iska wai saurin me kake yi haka yaushe garin ya waye".
Sadeeq na jin amsar da Farooq ya bashi yayi saurin katse kiran yana Jan wani dogon tsaki "mtssss".
Adai dai lokacin Siddeeqah ta sauko daga sama tayi fes da ita sanye take cikin shigar doguwar riga 'yar dubai mai ruwan hanta ta yafe kanta da mayafin rigar duk da ba kwalliya tayi ba amma tayi kyau abinka da farar mace mai siririyar fuskar da ke d'auke da dogon hanci gaskiya tayi kyau ko ma'kiyi dole yace masha Allah saboda kama take da larabawa

Gaban sa ta tsaya tace "yaya na shirya". Wani mugun kallo ya watsa mata gami da cewa "dan uban ki ni sa'an ki ne zaki 'bace min dagani ko saina tashi na yi ball da ke". Kafin Siddeeqah tayi wani yun 'kuri Momy ta fito daga part din ta. Tana Murmushi ta 'karso gurin Siddeeqah ta kama hannun ta ta kalli fiskar ta tayi fayau da ita masha Allah "gaskiya irin wannan kyau haka kamar zaki gasar kyau". Rufe fuskar ta tayi da d'anyan hannun ta ce "Allah Momy banyi kyau ba ko hoda da kwalli ban shafa ba".
"ai gwara da kika bar fuskar ki ahaka sai ainihin kyanki ya dad'a fitowa masha Allah".
Tana Murmushi tace "Momy da gaske ina da kyau?".
"wata ta ta'ba kiran ki da mummuna ne?".
Waiga wa tayi inda yaya Sadeeq yake suka had'a ido ya balla mata harara Momy na lura dasu idan ta fahimci Siddeeqah Sadeeq ne ke ce mata mummuna. Kafadar Siddeeqah ta dafa tace "rabu dashi mai sunan manya kinfi shi kyau nesa ba kusa ba kishi yake dake amma ko makaho ya shafa yasan kin fita daban kama da larabawa kike yi wallahi da za a kwana yana fad'a ma wani ke hausa fulani ce bazai yadda ba har sai kinyi magana yaji muryan ki".
Murmushi ne kwance akan fiskar Siddeeqah tace "Allah yabar mana ke Momyn mu ta bata fek kiss a kumatu".
Kallan sa Momy tayi tace "tashi mana Sadeeq ka kai ta ta shirya kai take jira".
Kamar zaiyi kuka ya ce "yanzu sai a ganni da wannan abar rigi rigi zan kaita gurin gyaran gashi ai abin kunya ne".
Momy na dariya tace "Sadeeq kenan wani lokaci idan kayi wani abu kamar sai ka dawo kamar karamin yaro Siddeeqah ce zaka ce wannar abar? Allah ya shirya ka amma aga ni na ganin ka tare da ita zai 'kara maka girma saboda iyalin ka ce".

✨✨✨✨
NI DA YAYA SADEEQ
                      ✨✨✨✨

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Chapter 18

______"haba Momy 'yar wannan abar ce zan fita da ita a matsayin iyali na?".
"Eh Ita d'in fa wallahi Sadeeq ka kiyaye ni ka raina ni ko? Duk abinda nike fad'a maka abanza nike fad'i saboda baka d'auka".
"Momy dan Allah kiyakuri na daina ki ce mata ta wuce mu tafi".
"Au bakin ka ciwo yake da bazaka  fad'a mata ba kai? Ko kafi 'karfi ne? Sadeeq ina raba ka da kiwan kyalla kana shige wa kyallah ta haihu". Momy ta fad'i haka cikin dakiya da tsitstsire sa da ido
Kame kame ya fara

Siddeeqah da taji haka tace "Momy sai mun dawo".

"to adawo lafiya 'yar albarka".

Harabar gidan ta fito  taja ta d'an tsaya kamin yayan nata ya fito su wuce,

adai dai lokacin mlm Habu ya wangele get motar su Jiddah ta silalo ciki idi driver ya samu guri yayi faking kana ya fito ya bude musu murfin motar Khadeeja ce ta fara fitowa sai Umar ya fito saida Khadeeja ta zura kan ta da hannayen ta a cikin motar ta kamo Jiddah da kyar Jiddahn ta iya fito wa tana cicci za le'be saboda yadda take cin zuciyar ta na mata daci da radadi akan dukan da Siddeeqah ta mata ita kadai tasan kalan tana jin cin mutuncin da tayiwa Siddeeqah

kallo daya Siddeeqah ta musu ta kawar da kan ta gefe tana dariya ciki ciki saboda yadda taga bakin Jiddah ya yi sun tumeme
Sadeeq ne ya fito shima ganin Siddeeqah na dariya ita kad'ai abin ya bashi mamaki yana shirin daka mata tsawa sai ya hangi Khadija rike da hannunan Jiddah Umar na biye da su suna taho wa
Kallo na yayi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Ya yi gaba abin sa cikin sauri nima na mara masa baya ba tare da na lura ba naji na ci karo da mutum a tsorace na ja da baya ina yarfe hannu na, ganin Jiddah ce na bige "mttsssss" na ja wani dogon tsaki naga sanda Khadija ta yi mata magana da alamar dai mantuwa tayi a mota saboda naga cikin motar ta koma  Idan jidda yayi 'kwala 'kwala murayan ta na rawa tace "wallahi zaki san kin ta'ba ni yarinya zan nuna miki kalar nawa rashin mutuncin banziya d'iyar shegu ke idan....".
"Tas tas". shine 'karan marin da Sadeeq ya wanke Jiddah da shi yana wuci yace "kada na kara jin kin ce mata shegiya duk lalacewar naka naka ne saboda hannun ka bai ru'bewa ka yan ke ka wurgar ita d'in jinjin ki ce nasan kin San da haka. 'bace min dagani kafin na 'ba'b'ballaki".

Jiddah kusan suman tsaye tayi saboda yadda taji saukar marin batayi zata ba lura Sadeeq yayi da Jiddahn bata cikin hayyacin ta d'an ta'be baki yayi ala mun ko a jinkin sa, kana ya kallo ni nayi sauri nayi 'kasa da kai na zaki wuce mu tafi ko sai na had'a dake munafuka kidinga yin abu sumi sumi to ki kaddara aure na dake... ".

Bai 'karasa maganar ba kira ya shigo a wayar sa laluba aljihun sa yayi ya fiddo batare da ya kalli sunan mai kiran sa ba yayi picking call d'in gami da karawa a kunnen sa sannan yayafito ni da hannu ya yi gaba. Sai a lokacin Khadeeja ta iso kallo na take yi nima da kallon na bita yaya Sadeeq har ya shiga mota nima bu'de gidan baya nayi na shiga na zauna sai Sadeeq d'in ya waigo fuskar sa a murtuke yace "ke uban waye diraiban ki zaki dawo gaba ki zauna ko saina miki tsinannan duka".
"uhm" ta fad'a kana ta dawo gaban motar. Habu mai gadi ya buɗe masa get ya fice daga gidan

Khadija na taba Jiddah tayi luuuuu zata zube a 'kasa cikin hanzari Khadeeja ta mai do ta kirjin ta ta run gume ta mamaki kwance akan fuskar Umar yace "wai aunty Khadija mai yasa meta ni ma yan zu na dawo kina tafiya nima naje gurin Habu mai gadi". Cikin kuka Khadija tace "Umar wannan wace kalar rayuwa ce daga wannan sai wannan gaskiya ni na gaji Zan roki Daddy ya barni na koma kaduna da zama wallahi bana son tashin hankali, nasan ita da Siddeeqah ne ko yaya tunda ina zuwa suka bar gurin". Ta 'karasa fad'a tana rushewa da wani irin kuka mai ban tausayi.

Tana kokarin kama Jiddah sai ga Daddy ya fito da alamar masallaci zai je soboda ankira sallar Azahar, hannun sa d'auke da gorar ruwa ta faro, hango 'ya'yan sa daya yi cikin wani hali yasa shi karasa wa gurin su da sauri

Allah sarki mahaifan mu  ko mai zamuyi musu bazamu taba biyan su ba saidai muyi musu adduar Allah ya yafe musu yayi musu sakaiya da gidan aljanna fiddausi 🙏

"Khadija mai yasa meta ne haka na gan ku cikin tashin hankali". Daddy ya tamabaye ta

Murayan Khadeeja na rawa cikin kuka tace "Daddy wallahi nima ban sani ba bayan mun dawo daga asbiti shine na barta anan na koma mota saboda na manta magun gunan da aka bamu nan dai Khadija ta kwashe labarin abin da ta sani ta fad'awa Daddy gorar ruwar  hanun sa ya bude murfin ta ya zuba rawa a tafin hannun sa ya watsa wa Jiddah a fuskar ta nan take taja dogon numfashi ta sauke 'kirjin ta na bugawa da sauri da sauri kara rungume 'yar  uwar ta tayi tana sauke ajiyar zuciya ganin ta farfado yasa daddy cewa "ku shiga daga ciki Umar zo mu tafi masallaci". "To Daddy".

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Aban garen Sadeeq kuwa wani 'katon plaza ya kai ni mai kyau da tsari bakin Siddeeqah a sake take kallon gurin saboda ita tun da take bata ta'ba ganin kasuwa mai kyau irin wannan ba badan taga basuyi tafiya mai nisa ba da sai tace kasar ya bari da ita yana gaba tana bin sa a baya har suka isa daidai bakin wani 'katon shago mai dauke da kofar gilas tafke ke irin wacce na ciki yake ganin na waje amma shi na waje baya ganin na ciki

Wani abun Sadeeq ya danna a jikin bangon shagon can sai ga wata mata ta fito da ganin ta ba bahaushiya bace saboda a kwai 'karin gashi a kanta kuma babu mayafi a jikin ta rigar ta irin mara hanu ce sai wani d'an gajeren siket da take sanya dashi da turan ci Sadeeq yayi mata magana itama ta mayar masa bayan sun gama naga ya ciro kudade masu yawa ya mika mata ta amsa tana godiya yace "bita mana kika saki baki da hanci kina kollo na kamar yau kika taba gani na".

Bayan sun shiga daga ciki Siddeeqah ta ga Mata a zazzaune akan kujeru masu kyau da burge wa wasu kuma an saka musu kan su a cikin wani inji yana kara wuuuu haka dai Siddeeqah tai tabin gurin da kallo kamin ta zauna a kan wata kujera da babu kowa a kusa da ita  tsoro ne fal a cikin ranta saboda yadda taga ana sa mutum cikin inji gaskiya ita baza ta yarda a sata ba aje a fille mata kai ana zaune 'kalau da ido matan gurin suke kallon ta ganin ta suke kamar balarabiya wata a cikin su ce tayi karambani tace "sannu baiwar Allah".
Kallon ta Siddeeqah tayi sai taga babbar maca ce saboda a kalla zata kai shekara 30 a duniya
Adan dakile tace "yauwa sannu Aunty". Saida gaba daya matan gurin suka kalli junan su saboda yadda suka ji muryan ta sanyi ga dadi haruffa suna fita dai dai kamar koyan hausar tayi masha Allah

Saida aka gama ma wasu mata sannan layi yazo kaina mai saloon din ta dube ni "kanwar oga taso ki zo layi yazo kanki".
A tsorace Siddeeqah ta tashi tace "amma ni dan Allah kada ku sani a cikin wancen injin ku wanke mun kaina kawai haka".

"To bazamu saki ba tashi muje" mai saloon tace

Bayan wasu mintocin da basu haura talatin ba saiga shi Siddeeqah ta fito das da ita an gyara mata kanta har kyalli yake bayan kamshin da yake tashi asalin kyanta ya kara baiyayana masha Allah a gaban katon madubi ta saya tana kallon yadda aka gyara mata gashin  duk tsayin sa da cikar sa anmayar dashi guri daya anyi mata faking a tsikayar kai sai shafa kan take tana mur mushi saboda ita kanta tasan tayi kyau. Mai kula da gurin ce tazo tace "kan war oga ya dawo yace kizo ku tafi".
"to". Na ce na yafa mayafi na ta zuge min glass na futo

A jikin motar sa na hango sa hannayen sa dore akan kirjin sa ya zuba min idanu kamar wani maye😅 da ni ke kallon sa haka da yace "uban me nike kallo". ahankali na karaso inda yake bai ce min komai ba ya zagaya yashiga nima na shiga ahanya ya kunna mana karatun alkur'ani mai girma muna saurara naji na kara samun natsuwa sosai kuma hankali na ya kwanta gaskiya alkur'ani rahama ne a tare damu saboda yadda ye samar ma da bawa nutsuwa da kwanciyar hankali

Cikin wata unguwa ya shiga damu mai gidaje iri daya A bakin get din wani gida naga yayi faking sannan ya dauko wayar sa ya dade yana danne danne yana dariya harda yin kiss a wayar ni dai ban ga ya kira kowa ba sai na ga ya aje wayar

Can sai ga Zuby ta fito sanya da d'ikin atamfa riga da siket amma irin dinkin nan ne da ake cema jahannama ga fasinja saboda komai na jikin ta ya bayyana mayafin ta a kafada ta doro shi bakin ta dauke da cingom tana taunawa yana kas

Tabe baki Siddeeqah tayi kana Ta cigaba da da kallon ikon Allah

Bangaren da nike tazo ta bud'e gani na da tayi a ciki yasa tayi turus harara ta buga min taja dogon tsaki ta maida murfin ta rufe cikin masifa ta dawo bangaren da Sadeeq yake tana jijjiga kafa

Tace "wace ce wannan ka kwaso Sadeeq? kamar aljana ko gamo nayi ni Nike ganin ta kai baka ganin ta?".

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Ina mai baku hakuri akan rashin jina da ba kwayi akai kai

Ina godiya da yadda kuke nuna min kauna Allah yabar mu tare ya hada fuskokin mu a cikin aljanna fiddausi

Dan Allah duk wanda yake karanta min book yayi kokari ya dunga yimin comment da share nagode taku har kullum
*Siddeeqatul khairy y faru* (S beauty✍️)
✨✨✨✨
NI DA YAYA SADEEQ
                     ✨✨✨✨

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Chapter 19

______dawo da kallan sa yayi izuwa gare ni ya wurga min harara kana ya kalli Zuby da take cika tana ba tsewa saida ya saki fuskar sa ya fad'ad'a ta da Murmushi yace "uwar gida sarautar mata duk kishin ne haka ko gaisawa kin ki bari muyi ki kwantar da hankalin ki akan wannan abar". Ya nuna mata ni da hannu kana ya cigaba da cewa "ina da ke mai zanyi da ita ko baki kare mata kallo bane? Ko matan duniya sun kare bazan so wannan abar ba danni kallon na miji nike mata".
Muryan Zuby a dakushe tace "to halakar ka da ita da zaka zo gurina sai kazo da ita, ni wallahi har kasa naji na tsane ta saboda ko macen kuda bana son tare beka bare kuma macen da da halakar aure zai iya shiga tsakanin ku, ina kishin ka ina yi maka son da bazan iya kwatan ta maka ba idanuwa basa iya ganin sa dan Allah Sadeeq kada ka ci amana ta ka soni koda rabin san da nike maka ne ". Idan Zuby har ya cika da kwalla, Sadeeq kuwa jikin sa yayi sanyi a ransa yake shawara "shin ya fad'a wa Zuby matsayin Siddeeqah a wurin sa ko kuwa yayi mata karya". saboda ya hango tsantsar kishin sa da 'kiyayyar Siddeeqah acikin 'kwayar idanun ta gwauran numfashi ya sauke yace "Baby ki kwantar da hankalin ki 'diyar mai gadin mu ce fa".
Kallon sa Siddeeqah tayi suka had'a ido ta tin tsire da dariya tace "saboda ka wulakanta ni zakace diyar mai gadin gidan ku ce ni?, to badiyar mai gadi bace kadai fadi wani".
A fusace ya daga hannu zai kwada min mari, Zuby tai saurin ce masa "abinda ta fad'a gaskiya ne shiyasa zaka dake ta na shiga uku Ni Zubadah Sadeeq mai kake nufi dani?".
"ki saurare ni baby wannan yarinyar da kike gani munafuka ce idan kuma kin yarda da abinda ta fad'a shikenan amma ni iyakar gaskiya ta na fad'a miki".
"haba Sadeeq da ganin wannan yarinyar ba d'iyar mai gadi bace jibe ta fa da larabawa take kama fatar jikin ta luwai luwai, wai ka ta'ba kare mata kollo kuwa dan Allah Sadeeq ka kalle ta yanzu". Wai gowa yayi ya kalleni na tsawan wasu yan sakonni kana ya cigaba da kallon Zuby, mi'ko masa wayar ta tayi  tashiga camera tace "kaima kalli kan ka ka gani". Sadeeq bai fahimci inda Zuby ta dosa ba shidai kawai biye mata yake yi bayan ya kalli kansa ya mi'ka mata wayar, tace "ina fatan ka fahimci inda na dosa yanzu?".
Kai ya girgiza mata alamar bai fahimci komai ba tace "ina son ka fad'a min maye Alakar ka da 'yar mai gadi har kake kama da ita? Wallahi ko alqur'ani aka bani zan dafa ita d'in jinin ka ce Sadeeq maiyasa kayimin kar...".
Tsawa ya daka mata gami da cewa "ke ashe bakida hankali? ni zaki duba tsabar ido na kice min makaryaci tabbas zan nuna miki kuskuren ki".
Sai yanzu Zuby taga rashin dacewar abinda tayi a fusace Sadeeq yayi ribas Zuby na kwala masa kira ya amma ina ransa ya riga ya baci figar motar yayi sosai yake gudu akan titi saura kiris ya daki wata mota da ta fito daga wani layi zata hau titi sai Allah ya takaita abun yayi sauri ya ci burki idanuwan Siddeeqah sun yi kulu kulu tsoran ta kada yaje ya kashe ta tasan ya kashe banza wayar sa ce ta fara ringing amma ko ta kanta bai bi ba koda yazo bakin get din gidan su sosai yake danna horn mai gadi a tsoroce ya leko ganin yallabai ne yasa yayi sauri ya wangale masa get din acikin ran Habu yake cewa "ko waya tabo yallabai yau?".
Bayan Sadeeq ya sulala motar sa cikin gidan yane guri yai faking da sauri Siddeeqah ta kai hannun ta da niyar ta bude murfin ta fita sai taji sa a kulle game alokacin Sadeeq ya hada kansa da sitiyarin mota tsoro ne fal acikin zuciyar ta, tana jin yadda zuciyar Sadeeq ke harbawa da sauri da sauri ahalin yanzu tasan ko sunan sa ta kira shake mata wuya zaiyi komawa tai ta zauna itama tayi tagumi hawaye na saukar mata da batasan dalilin zuwan su ba

*Dan Allah duk wanda ya karanta yayi min comment da shera ngd*

✨✨✨✨
NI DA YAYA SADEEQ
                   ✨✨✨✨

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

        _Ku tsaya ku karanta_

*Amincin Allah ya tabbata a gareku masoya na*  _readers musamman na kan wattap daku nike ina fatan ko waccen ku tana cikin koshin lfy ya sanyi to barkanmu da war haka_

_🤙Ni ce dai taku *Siddiqahtul khair y faru* wacce kuka fi sani da *S BEAUTY* a gaskiya bana jin dadin yadda da yawan ku kuke karanta *NOVEL* dina amma ba kwayimin vote da comment uwa uba ma ba kuyi following dina ba gaskiya banji dadi ba ya kamata yadda nike faran ta muku nike nishadantar daku kuma na ilmantar kuma ku faran tamin ta hanyar yimin follow da comment da vote wannan shine ta hanyar da zu biyani domin nima nasamu kwarin gwuiwar da zan dunga yi muku typing a kullum insha Allah saboda inason insha Allah na gama book din kafin mu shiga watan azumin *RAMADAN* saboda akwai program din da zan gabatar muku a cikin azumin insha Allah amma anan wattap kawai saboda haka ku bani had'in kai dan Allah naga canji a wannan karan ngd_

Chapter 20

______Sun d'auki kusan mintuna goma shabiyar a haka batare da d'ayan su ya yi 'kwa'k'kwaran motsi ba sai sautin bugun zuciyar Sadeeq dake sauka fat fat, Siddeeqah kuwa duk da akwai na'urar sanyin dake saka cikin motar sanyi saida ta jike da gumi sharkaf idanuwan ta sun dad'a fitowa waje, dago raunannun idanun sa yayi da suka koma launin gwauta saboda tsabar bacin rai ya sauke su akan na Siddeeqah, da sauri ta maida kanta kasa tana wasa da y'atsun hannun ta zuciyar sa ce take ingiza sa da ya shake mata wuya wata zuciyar kuma ta ce masa "Kul Sadeeq ka kashe gawar da ba taka ba, ka bud'e mata mota ta fita" haka kuwa akai yabi shawarar zuciyar da ta gar gad'e sa soboda haka ya bude mata murfin motar Siddeeqah naji ya bud'e tayi sauri ta bude murfin ta fito har tana neman dungurawa a kasa soboda yanayin Sadeeq d'in yayi mugun bata tsoro da sauri da sauri take tafiya jefa kafar ta kawai take batare da tasan inda take jefewa ta ba, ji tai ta ci karo da mutum a tsorace ta ja da baya ganin Sadeeq ne yabiyo ta d'ayar hanyar da ake iya haduwa da Wanda yabi ta gaban gida, yanda taga yanayin sa har yafi d'azun firgitar wa idanuwan sa sun kara yin jaa kamar Jan gauta, nufo ta ya fara yana d'an Murmushi yana shafa sajen sa, 'kafa mai naci ban baki ba gudu ta fara shima ya mara mata baya cikin ikon Allah saiga Momy a harabar gidan da alamar wani abu take ne ma saboda idanuwan ta a kasa suke, da gudu Siddeeqah taje bayan ta ta 'boye tana nishi "ke lafiyan ki kuwa daga ina haka kamar an koro ki?". Momy ta fad'a tana duban Siddeeqah Bata lura da Sadeeq ba, da hannu Siddeeqah ke nuna mata inda Sadeeq yake sai alokacin Momy ta dube sa, washe baki yai ya wayance yace ma Siddeeqah "ba dai kin ki bari na kama ki ba nima zan rama yarinya, waifa Momy ce mata nayi ta jirani mu taho tare shine ina gama faking ta rigani fitowa shine nabi bayan ta da ta hango ni sai tafara gudu nima shine na biye mata". Siddeeqah kamar sakarya haka ta saki baki da hanci tana kallon shi lallai ya iya tsara labari,

cikin gamsuwa da abinda ya fad'a Momy tace "ai da baka biye mata ba yarinya ce, amma gaskiya kun dade ko ka kaita wani gurin ne? Daddyn ku na ta kiran ka a waya baka dauka munyi tunanin ko ba lafiya ba hankali ya fara tashi".
"Wallahi lafiya lau Momy layi muka tarar a gurin saloon d'in, amma me ya fito dake naga kamar wani abu kike nema?".

"to babu damuwa, eh wallahi

1 Comments On NI DA YAYA SADEEQ
avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment