Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yin sa mtssss" .yaja dogon tsaki ba shida amsar tambar sa saboda haka ya lalubi wayar sa da yaji tana ringing bai wani tsaya ya kalli sunan wanda ke neman sa ba yana dauka ya kara a kunne.
Daga d'ayan bangar akace "wallahi aboki baka da mutunci daka zuwa Abuja ganin Princess sai ka manta damu, munafuki amma da anyi magana kace baka son yarinya ka tsane ta".

"shege akace maka kowa mayen mata ne irin ka ka rasa dawa zaka hada ni sai da yar karamar yarinya wacce ko...".

"haba malam kada kacika min baki daga karshe kazo ka fada tarkon yar yarinya".

"Wa ni?!". Ya fada yana nuna kan sa da yatsan sa ". Kamar Farooq din yana ganin sa "Allah ya kyauta ai na fada mata duk sanda taji nace ina son ta kada ta taba yadda dani saboda ba da gaske bane".

Farooq baiji dadin yadda abokin sa yayi su'bul da baka ba saboda haka yace "uhm Sadeeq idan Allah ya tashi kama ka bazai maka kadan ba kuma gaskiya bazan ji tausayin ka ba koda zanji sai ka ji jiki, saboda duk abinda ka Shuka shi zaka girba dama na kira ne naji ya kake ya Momy tunda duk kuna lafiya sai da safe".

"Kaga Farooq kada ka kashe a kwai maganar da nike so muyi".

"Ina jin ka to"

"yanzu haka fa a hanya nike naje naga gimbiya ta, gaskiya babyn ta hadu tafi kyau a fili nike fad'a maka komai yaji zam-zam hhhmm nasan ba lallai ka yarda ba tunda kaki ko hotan ta ka gani amma tun na ganta na shiga wani yanayi".

"Haba Sadeeq daman wannan ce maganar da kace za muyi?.

"Eh amma da akwai d'ayar nafi zumud'in wannan shiyasa na fara fada maka ita" kuma kasan nace "Momy ce take nema na ashe akan makarantar yarinyar nan ne to shine nike so ka nema mata admission a makarantar da Sadiya take saboda na cewa Momy na gama komai tafiya ta rage".

Shuru Farooq yayi na wasu yan da'ki'ku alamar nazari can ya numfasa yace "haba Sadeeq wai meke damun ka meyisa kake son ka kuntatawa yarinyar mutane wani irin makarantar kwana ana zaune 'kalau don Allah kajanye wannan maganar kaji tausayinta
Har yanzu fa Siddy yarinya ce karama na tabbatar ma batasan maye aure ba da tasani wallahi da...". Bai karasa maganar ba Sadeeq ya dakatar dashi da cewa "malam don Allah ba shawara na tambaye ka ba
Dan kaga na biyo ta hanyar ka shine zaka tozartani idan baza kaimin ba kawai ka fadamin"

"Allah ya huci zuciyar ka". Farooq ya fada kana yace "aji nawa za a sata?".

"Ko js1 ne asata ba matsala ta bace zan fi son haka saboda na more soyayya ta da Baby na kan tagama karatun"

Farooq nason yace wani abu amma gudun kar yakara laifi yace "babu damuwa zanyi kokari insha Allah ko js2 su kaita".

Daga haka sukayi sallama

Bayan Sadeeq ya gama faking din motar sa ya fito jinsa yake wani iri saboda haka ya haura sama bai kai ga shiga dakin ba yaga kofar abude yayi mamaki bai gama tsinkewa ba sai da ya shiga bedroom din sa ran sa a mugun bace ya karasa kan gadon da niyar fusgo ta amma sai yaji kamar an soka masa kibiya a cikin sa bai san sanda ya zube a kan gadon ba numfashin sa nafita da sauri da sauri Siddeeqah wacce bacci ya dade da sace ta garin juyi ta wurgawa Sadeeq kafa ransa bace ya wur ga mata harara, tuna aikin banza yayi tunda bacci take yi ya shiga kwala mata kira "ke ke uban wa ya ce ki shigo nan?"

Siddeeqah da kamar a mafarki taji ana kiran ta a fir gice ta bude idanuwan ta suka sauka akan na Sadeeq dake mata kallon tuhuma fuskar sa a murtuke babu alamar wasa yace "dan uban ki uban wa yace ki shigo min daki?".

Siddeeqah gaba daya ta rike ce bakin ta na rawa take fadin "lah yah...!".

"Yayan uban ki zakiyi bayani wallahi bazaki sauka ba sai na yi ball da ke".

'Kokarin tashi yake amma cikin sa ya kara murde sa nan take ya rike cikin yana kiran sunan Allah a rude Siddeeqah ta 'karasa gurin sa ta kama hannun sa "yaya yaya meke damun ka haka me yasa meka".

A wahalce Sadeeq yace "cikina". Kama hannun ta yayi ya dora a kan cikin sa ji tayi kamar akan shocking ya d'ora mata hannun saboda haka tayi sauri ta janye yaya bari naje na kira Momy saboda ni bansan mai zan maka ba zata sauka kenan Sadeeq ya kama hannun ta idon sa a rufe yake cewa "kar ki tafi ki banni kizo dan Allah kada ki tafi" cikin karfin hali ya janyo ta ya matse ta a jikin sa yana fitar da numfashi da sauri da sauri

Gaba d'aya jikin Siddeeqah rawa yake ta kasa fahimtar mai Sadeeq din yake nufi da haka kokarin saka mata hannu a riga yake Allah ya bata sa'a ta kwace daga rukon daya mata tace "karamin dan iska ashe daman kai dan iska ne to bari kaji ni ba yar iska bace inace daga waje kake to ba kaje gurin 'yan iskan naka bane?"

Sadeeq jin maganganun yayi kamar ta watsa mai garwashin wuta saboda zafin su gashi baya jin zai iya tashi bare yayi maganin rashin kunyar ta

Saida ta rike 'kugun ta ta dawo gaban sa ta dan jujjuya tayi fari da idanuwan ta tace "karamin d'an iska to duk abinda kayi min sai na fada wa Momy saboda tun muna yara ake jamana kunne akan mukula da maza shine a waje ba a lalata ni ba yanzu kai ka lalata ni" take ta fashe da kuka tana fadin "na shiga uku yaya Sadeeq yayi min ciki innalillahi wa innah ilaihi rajiun Allah kagani ni ba yar iska bace shine ya taba ni waiyo Allah Momy zata yanka ni yaya Sadeeq ka cuce ni azzalumi Allah sai ya saka min". Ta kara rushewa da wani irin kuka mai ban tausayi

Sadeeq bai fahimci mai Siddeeqah take nufi ba shidai yasan ana ce musu ko hannu suka bari namiji ya rike musu zasu dauki ciki to yana ga shiyasa yanzu take cewa yayi mata ciki😂 bai san sanda ya kwashe da dariya ba sai yanzu yake kara tabbatar da yarintar Siddeeqah kallan ta yayi suka hada ido tana rike da 'kugu tana jijjiga 'kirji
a yanzu yaji saukin murdawan da cikin sa ke mai saboda haka ya kamo ta cikin zafin nama tana ta zizzille wa saida ya daidai ta natsuwar sa ya koma mata Sadeeq din da tasani ada yace "ke dan uban ki ni kike cewa dan iska?" ta tsorata da yadda taga yanayin sa saboda haka ta shiga yi masa magiya da bige bakin ta
Yace "babu ruwana ki daina buge bakin ki idan kina so kada na zane ki to kija bakin ki kiyi shiru da abinda ya faru a tsakanin mu ko Khadeeja kada ki fada mata bare Momy idan kika yi haka kin tsira saboda nima bani nayi miki ba aljanu na ne suka miki kuma kin san aljani bai san a dunga talla da abinda ya aikata, sai ya makantar da ke ko ya kurmun taki saboda haka kija bakin ki kiyi shiru kuma ki tabbatar babu wanda ya ganki a lokacin da zaki fita daganan ".

Bakin ta narawa tace "to yaya". Sai alokacin ya sake ta ta nufi kofar futa daga bedroom din duk ta daburce ko dan kwalinta ta manto shi gashi kanta babu kitso sai yanayin ta ya nuna kamar bata cikin hayyacin ta tafiya take tana sand'a a haka ta fito daga ban garen sa tana gaf da shiga dakin Ummi taji ance "daga ina kika fito?". A daburce ta juyo ta kalli Momy da ta tsura mata idanu, cikin in ina Siddeeqah tace "daga dakin yaya nike dazun dana kaimasa a binci na tsaya kallo har bacci ya kwashe ni sai yanzu da ya dawo ya tashe ni".
"Amma ya na ganki a furgice yayi miki wani abu ne?". Da sauri Siddeeqah tace "babu abinda yayi min saboda daga bacci na tashi".
Saida Momy ta kare mata kallon tsaf tace "kada ki boye min idan yayi miki wani abun fa kada daga baya azo asami matsala ki fada min gaskiya". Siddeeqah naso ta fadawa Momy abinda ya faru tuna kashedin da Sadeeq yayi mata yasa tace "Allah Momy babu abinda yayi min ki yadda dani Momy". Badan Momy ta yadda ba tace "jeki kada ki manta da adduar bacci".
"To Momy saida safe"
"Allah ya tashe mu lafiya

Ina jiran kyawawan comment dinku fans 💖💕💋

NI DA YAYA SADEEQ
                 

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Page 15


Washe gari da misalin 'karfe 11:00 gaba d'aya mutanen gidan zaune suke akan dining ana breakfast har da Daddy saboda jiya da daddare ya dawo, kasan cewar yau din asab ranar hutu ce babu school a tsanake muke breakfast d'in mu
tunda ya doso gurin 'kamshin turaren sa ya dake hanci na ya bud'e ilahirin gurin da sanyan yan 'kamshin sa d'aga kaina nayi ai kuwa karaf muka yi ido hud'u dashi tsura masa manyan  idanuwa na nayi ko kifta su bana yi gaskiya yaya Sadeeq karshen had'uwa ne kansa na fara kallah gashin nan na kansa ya gyara sa sai kyalli yake yi masha Allah sajan nan nasa bakinkirin dashi a gyare gunin ban sha'awa da dan gemun sa da bai wuce kamu daya ba 😜yana sanye cikin wata riga blue mai layi layi hannun ta anyi masa ninki biyu da wani botiri mai kyau da 'kyalli sanye yake da wandon jus lite blue mai kyau da tsada kasan bai kama sa sosai ba ban san sanda na bude baki da hanci ba na cigaba da kallon sa ashe  Momy ta lura da ni kawai magana ce bata yimin ba shikuwa gogan da ya 'kara so kan dinning din sai yazo yayi kamar zai wuce ta kusa dani ya take min yatsun kafa ya   murza da karfi yayi gaba kamar bashi ne ba

Wata uwar 'kara na kwalla ina yarfe 'yan yatsun hannu na gaba d'ayan su ido suka zuba min da son jin mai ya same ni wasu hawaye ne masu zafi suka fara kwaran yo min saboda naji zafin murje min yatsun 'kafa da yayi "Sadeeq mai kayi mata". Daddy ya fad'a yana duban sa zaman shi kenan akan kujera ya fito da ido waje alamar firgita yace "ni kuma Daddy yanzu fa na iso ko magana banyi mata ba". Jinjina kai Daddy yayi alamar gamsuwa ya waigo ya kalleni yace "mai sunan manya me  ya sameki ne?".
Ina shash-shekar kuka nace "yaya ne ya murje mun yatsun kafa na kuma ban san mai nayi masa ba".

Gaba dayan su maida kallon su sakayi ga Sadeeq da ya curo waya yake dannawa a hasale Daddy yace "ai kaji abinda tace". Fuskar  tausayi yayi ya dube ni yace "yarinya kiji tsoran Allah zaki mutu ki fad'i gaskiy saboda ni kinga da na shigo ma ko kallan ki banyi ba, ko dai aljani ne yayi miki siffa ta ya taka miki 'kafa saboda ace ni ne?".

Ido Siddeeqah ta 'kura mai sai alokacin ta tuna yace yana da aljani idan ko hakane shine ya aljanin ne ya taka ta Allah sarki bai san yayi ba ashe

Kallan ta ta mayar akan Daddy tace "kamar yadda yaya". Yace "ko aljani ne yayi siffar sa inaga hakane saboda wallahi...".

"Ya isa". Jiddah ta fad'a tana wuci kamar wacce aka mata wani abun ta d'ora da cewa "malama kada ki raina mana hankali na dad'e da sanin ke makar ya ciya ce ba tun yau ba saboda kinga Momy da Daddy suna goyan bayan ki sai ki dunga 'kullawa yaya sharri ke ga annamimiya kina shiga tsakanin d'a da uwa wallahi..."

Tau tau! 'karan marin da Siddeeqah ta wanke Jiddah dashi kowa a wurin mamaki yake! banda Sadeeq saboda yafi kowa sanin halin ta shammatar ta ta kuma yi ta dad'a mata wani tas! 💃Gaba daya ji da ganin Jiddah sun tsaya cak sai wasu tau rari da take gani can kuma duhu ya rufe ta

ran Siddeeqah a 'bace ta cukwuikwuyi wuyan rigar Jiddah "wallahi yau koni ko ke sai naji dalilin da yasa ki ka kirani da annamimiya".

Tuni idanunun Jiddah suka furfito waje saboda sha'kar da Siddeeqah tayi mata daman ita ba wata mai 'karfin azo agani bace sai tsinanniyar tsokana da kin ma'kure ta ta koma fuskar tausayi gashi ita kuma Siddeeqah babu hakuri wani lokacin har jira take ka taba ta tayi rashin mutunci yau jin zuciyar ta take asama saboda haka ta fara kaiwa Jiddah naushi a baki tana fad'in "wallahi saikin fad'a min inda na had'a  d'a da uwa idan ba haka ba mai...".

"ke sake ta kafin na tashi na 'babballaki". Sadeeq ya fad'a yana nufo inda nike ni kuwa bil ha'k'ki naushin Jiddah nike abaki yanzu haka na fasa mata yana zubar jini

"Kada ka sake ka buge ta zan 'bata maka rai saboda tayi min dai-dai tunda ba da ita ake yi ba ta ara ta yafa yanzu Khadija da Ummi da basu sa baki ba ai ba ayi dasu ba". Momy ce tayi wannan maganar zaiyi magana Daddy yace "nima ai tayi min dai-dai saboda haka ko kallon banza ban yarda kayi mata ba".

Khadija dai bazan ce taji dad'i ba saboda ita bata san fitina kana kallon fuskar ta kasan ba a yanayin jin dad'i take ba Ummi kuwa saboda farin ciki bakin ta ko rufuwa bai yi har kai naushi take kamar ita ke dukan saboda ba wani shiri take yi da Jiddahn ba kasan cewar ta ba 'yar Momy ba yar yayan Momy ce wato kanwar Naseer da ke 'kasar India karatu tun sanda mamar su ta rasu ta dawo gurin Momyn da zama a lokacin tana da 7 year's old kuma ita ma sa'ar su Siddeeqahn ce a ran ta tace "da jiya na biyema Jiddah da da ni za a fara" soboda sanda ta shiga kitchen ta tarar da ita tana hada tea bata tanka mata ba ta hau fad'ar magan ganu kamar yadda ta saba

Umar har yafi Khadija damuwa saboda shi harda guntun hawayen

A lokacin da ya 'kara so inda muke caraf ya d'auke ni daga kan Jiddah zai aje ni Momy tace "a a kasan fad'an Siddeeqah baya 'karewa indai aka taba ta to sai ta rama kaita sama cikin dakin ka idan Jiddahn ta haura sama sai Siddeeqahn ta sauko".

Ina ji ina gani yaya ya haura dani sama ba dan raina yaso ba dan ni da so samu ne a bar ni da ita na koya mata hankali saboda tana da raini da jin kai ni kuma bana jure wa dan ko babba ba 'karamin nauyin sa ni keji ba idan har yaga yayi min ban rama ba

Kamar yadda Momy tace bai dire ni a ko ina ba sa a cikin falon sa ya maida kofar ya rufe da dan mukulli sannan ya zare ya saka a cikin al'jihun sa ya nemi kujera 2 cter ya kwanta ya lumshe ido

Sosoi bakin Jiddah ke zubar jini tuni Daddy ya wuce ban garen sa saboda yadda Jiddahn ke rusa ihu kamar wacce aka aikoma sa'kon mutuwa

Khadija dur 'kushe gaban Jiddah cikin tausaya mata take mata sannu kana daga bisani tace "sannu Little sister zaki iya tashi mu tafi asbiti saboda aduba lafiyar ki?".

Bata gama rufe baki ba Momy ta kara so daga tsaye tace ai daman ance jiki magayi gobe sai ki kara, ke kuma kin zo sai faman sannu kike mata ba ita tajawa kan ta ba? Maza d'auko mayafin ki kije ki" cewa "driver ya tada mota saboda ku kaita ayi mata dressing din bakin ta".

"Wallahi Momy ko da ita ce da laifi bazan iya jure kallon ta cikin wani hali ba na kyale Siddeeka ne kawai saboda itama 'yar uwa ta ce amma baki ji yadda zuciya ta ke mini ba a lokacin da abin ke faruwa".

"Ai fa nan dama ke ki ka fi auki wajen  son yan uwan ki nasan ko kanki baki masa san da kike musu abu ne mai kyau amma ina baki shawarar da ki rage saboda kada wata rana ya za me miki matsala".

Idanun Khadija ya kawo 'kwalla ta dubi Momy tace "idan har kuna raye kuna ci gaba da samin albarka bazanyi da na sani akan 'yan uwa ba ba insha Allah ".

"to Allah yasa". Momy ta bata amsa tana barin gurin

Duban Umar Khadija tayi tace "kaje ka cewa Idi driver ya tada mota sannan idan ka dawo ka dakko mini gyale na dana Jiddah".

✨✨✨✨
NI DA YAYA SADEEQ
                    ✨✨✨✨

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Chapter 16

______"To" Umar ya fad'a yana mai mi'ke wa jikin sa babu 'kwari
Khadija sai sannu take ma Jiddah da bakin ta ya kumbura yayi suntum sai zubar jini yake
Umar bai wani jima ba ya dawo "Aunty Khadeeja na fad'a masa bari na haura sama na d'auko muku mayafin"
"To" Umar khadija ta fad'a tana rungume 'yar uwar ta a 'kirji
A haka Umar yadawo ya iske ta ya mi'ka mata ta ansa ta yafa sannan ta yafa ma Jiddah "zaka bimu ne?". "Eh zani". "To muje ko". Tafad'a tana d'aga Jiddah daga jikin ta "sannu sister daure ki tashi na kama ki sai mutafi asbiti ayi miki dressing kada abinda kike rainawa yazama babba da 'kyar Jiddah ta iya kama hannun Khadeeja tana waiyo waiyo ta samu ta mi'ke kallo d'aya zaka yi mata ta baka tausayi saboda yadda bakin ta ya kumbura da taimakon Allah da na Khadija suka fito falon a lokacin Idi driver ya tada mota Habu mai gadi ne ya hango su cikin sauri ya 'kara so inda suke ya bud'a masu 'kofa yana yiwa Jiddah sannu Umar kuma ya zagaya ta d'ayan bangaren ahankali Jiddah ta shiga khadija ta mara mata baya Habu mai gadi ya wangyale musu get suka fice

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Tsaye Siddeeqah take ri'ke da kugun ta sai zum 'bure zum 'buren baki take yi a cikin ran ta take fad'in "kai kuwa matar ka ta bani ayi mutum dun kum ba za ayi fira da shi ba sai kace wani boss kullum fuska daure" "ke mai ki ka ce ina wasa dake?". Abinda Siddeeqah bata sani ba ba acikin zuciyar ta tayi maganar ba sarai sadeeq yaji mai tafad'a

'ko'korin tashi yake yazo ya cim mata sai wayar sa ta shiga naiman dauki da kamar bazai duba ba saboda wannan yarinyar ta 'bata masa rai amma sai wata zuciyar tace "ya duba dai yaga wake neman sa". Haka kuwa akayi dauko wayar yayi daga kan hannun kujera My Baby shine sunan da yake yawo akan screen din nan take ya saki murmushi  harda d'an cije leban sa na 'kasa ya gyara kwanciyar sa da kyau
Baki bud'e Siddeeqah ke kallon sa a tunanin ta aljanin sa ne ya motsa
Amma sai taga ya d'aga wayar ya kara a kunne baiyi magana ba daga can 'ban garan aka ce
_"Amincin Allah ya tabbata a gare ka ina fatan wanda nafi so da kauna a duk duniya ya wayi gari lafiya koda yike naji a jiki na kana cikin koshin lafiya saboda inajin duk wani yanayi da ka ke ciki a jiki na_".

Sadeeq kusan suman kwance yayi saboda shi a rayuwar sa yana son kula wa musamman a bangaren soyayya zai iya 'bata lokaci mai yawa wajen tsara kalaman soyayya saboda shi a yadda yake gani idan bai ba ma soyayya hakkin ta ba bai more rayuwar sa ba

Bakin sa washe kamar tana ganin sa yace _"gimbiya sarautar mata ina fatan amincin tare dake"_
"Na gode My". Jiya na gaji ban san sanda bacci ya dauke ni ba dan Allah kaya kuri ban kira naji yadda ka iso gida ba".

"Kada ki damu baby Allah ya kare miki ni da kariyar sa na zo gida lafiya kema fatan dana baro ki babu abinda ya taba min ke".

Zuby na dariya tace "kana nufin har na kai a bani irin wannan kulawar sai kace wata gimbiya?".

"Haba ke kuwa ai kin wuce gimbiya a gurina ko kin mata da auren ki nike so nayi? Nan da kika ganni akan abinda nike so bani da sakaci ina basa kulawa ta musamman".

Cikin kissa da kisi sina Zuby tace "yanayin muryan ka ya nuna min baka karya ba kana jin yunwa".

Sai alokacin Sadeeq ya tuna ashe bai karya ba
Siddeeqah kuwa duk sona da gulma dole na kyale ta saboda na kasa fahimtar yanayin ta har yanzun a tsaye take idon ta akan Sadeeq kyam shi kuwa bai san tana yi ba ya tafi duniyar masoya

Ya cigaba da ce wa "wallahi Baby na manta".
"My kaman ta fa kace yanzu fa 12:00 gaskiya ka daina barin mun kanka da yunwa saboda ba kan ka ke bari ba ni kake bari idan kuma kanason na cutu ai shikenan".

"Haba Baby na na daina insha Allah zan dunga kula miki da kaina kamar kina gani na dazun ma har zan karya sai wasu 'kannai na suka kama rigama har sukayi doke doken juna to shine duk naji raina babu dadi".

"Ayyah my sorry kasan sha'anin yara sai ana hakuri da su amma gaskiya ka tashi ka je ka ci abinci idan ka gama bayan sallar azahar saika kirani mu daura daga inda muka tsaya".

"To ranki shidade na gode da kulawa I love you". 💖
"I love you too"
"By"
"okay by take care for me".
zuwa yanzu Siddeeqah ta nemi guri ta zauna amma wannan karan ba shi take kallo ba da yatsun hannun ta take wasa saboda yadda take jin ranta babu dadi.

Shi kuwa Sadeeq har cikin zuciyar sa ya manta da wata Siddeeqah a d'akin sa shiyasa ya saki baki ya yi ta suru tu

Kallon sa tayi tace "yaya zanyi fitsari" banza yayi da ita kamar bai ji mai tace ba

Can da taga fitsarin zai iya zubo mata tace "yaya yafa matse ni zai zubo".

Sai a alokacin ya dago kai suka had'a ido sai yanzu ya tuna ashe tana  d'akin nasa, bai kula ta ba ya tashi ya shiga bedroom din sa bai jima ba ya fito hannun sa rike da mukkullin mota ya nufi 'kofar fita  batare da yace mata komi ba  ganin haka tayi sauri ta mike kafar ta a matse ta soma tafiya alokacin shi har ya bude kofar ya fice

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Kwance take akan gadon da ake kwantar da marasa lafiya anyi mata dressing din bakin ta kuma an sa mata ledar 'karin ruwa ga dukkan alamu ma batasan wa ke kanta ba saboda allurar baccin da aka mata Khadija na gefe tayi tagumi Umar ma haka kowa da abinda yake sakawa a cikin ransa

_Na gaji da typing amma idan har naga ruwan comments zan kara yi muku wani typing din anjima_
🙏
✨✨✨✨
NI DA YAYA SADEEQ
✨✨✨✨

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Chapter 17

_____Ringing din wayar Khadija ne ya katse shirun nasu bayan ta fiddo wayar Sunan Momy ya bayyana akan screen d'in wayar da han zari Khadija ta d'auka ta kara a kunne tace "Aslm Momy". Daga can 'ban garen Momy ta amsawa Khadeeja da "W/slm Khadija naji ku shiru ne shine nace bari na kira naji ya ake ciki". "wallahi Momy lafiya lau anyi mata dressing din bakin ta ne sai karin ruwa da aka sa mata".
"sai yaushe kenan zaku dawo?".
"dazaran ruwan da ake 'kara mata ya 'kare saboda nurse d'in tace zamu iya tafiya ba wani ciwo bane kawai buguwan da tayi ne, saboda ce mata nayi fad'uwa tayi abayi ta bige".
"yayi kyau". Momy ta bawa Khadija amsa daga haka suka yi sallama

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Da bibbiyu Sadeeq yake tsallake steps soboda yana son yaje wurin cin abinci kafin a kira sallar azahar kici'bus yayi da Momy a dai dai lokacin da ya gama sauko wa daga steps din cikin sakin fuska Momy tace "ah Sadeeq ga fa abin karya wan ka can fuskar ka tayi zuru zuru nasan kuma yunwa ce kake ji".

"eh wallahi Momy yanzu haka saurin da ki ka ga inayi restaurant zani".

Kafin Momy ta ba Sadeeq amsa Siddeeqah ta sauko

1 Comments On NI DA YAYA SADEEQ
avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment