Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'kaddara ba mai zanyi dake kucaka ki kalle ki, ki kalle ni, kin tafka babban kuskure da kika yarda Daddy ya hada auren nan, zan shayar dake madarar azaba, gida na zai zame miki tamkar kabari, ke koda sunana ki kaji an ambata sai gaban ki yayi mummunan fad'uwa ,saboda bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane, ki fara tunanin yadda zaki rubuta littafi mai suna *NIDA YAYA SADEEQ* saboda irin zaman da zakiyi a cikin gida na ya ciki ki rubuta".

Duka wannan maganar da Sadeeq yayi kaina a 'katsa wasu hawaye masu zafi suna gangaro mini, narasa mai nayiwa Sadeeq da har ya tsane ni haka? Ban ta'ba tunanin tsanar da ya kecewa yayi mini ta kai har haka ba, ban tanka masa ba illa mi'kewa da nayi na nufi hanyar sama na fara taka steps kenan ya da katar dani ta hanyar fadin "na tsane ki Siddi'ka na tsane ki, kuma bazan taba sonki ba a duk sanda ki kaji nace ina sonki to kada ki ta'ba yadda dani saboda yaudarar ki zanyi ba gaskiya bane". 😭

Hawaye masu 'kuna suka cigaba da gangaro min a haka na 'karasa haura steps din, Suwaiba da ke faman dafa abinci a kitchen taji duk abinda ya faru tsakani na da Sadeeq

'Dakina na shiga na fad'a kan gado, hawaye mai zafi yana zuba daga ido na, ni da kaina ina jin tausayin kaina saboda a sani na da yaya Sadeeq bai ta'ba cewa zaiyi baiyi ba duk abinda yace zaiyi to sai ya aikata sa

A cikin kukan na d'aga hannaye na sama na ce "ya Allah ka bayyana mahaifiya ta a duk inda take, a fadin duniyar nan, ya Allah kasa tana a raye saboda inason rayuwa tare da ita, ya Allah kada kabama wani bawan ka sa'ar cutar da ita".
Mama. Na fad'a haka yayin da na d'aga kaina sama ina kalla, "bansan maye dalilin ki na cewa ko bayan babu ranki a daura wa 'yarki aure da Sadeeq ba, nayi alkawarin ni Siddi'ka zan zauna da Sadeeq koda kuwa hakan na nufin zai zama ajali na, ha'k'kin ki ne nayi miki biyayya a sanda kike a raye da kuma abinda kika bani umarnin sa koda bayan ranki, Mama ta ina sonki". Na 'kare maganar da wani irin kuka mai tsuma zuciya.

Allah sarki Siddi'ka ni kaina ta bani tausayi ban san sanda na saki waya ta tafad'i a kasa ba saboda ido na ya cika da hawayen 😭 tausayin halin da take ciki da 'kyar na samu na daidai ta kaina na d'auki waya ta na fita daga d'akin naja kofar na rufe

Momy ce zaune ita da Sadeeq a falon 'kasa, sai zazzaga masifa takeyi "Sadeeq kabi duniya a hankali ko ta d'aga ka zata aje ka, Wallahi Sadeeq ina guje maka ranar da zakayi ladama amma kuma ladamar zata kasan ce da ita gwamma babu saboda ka makaro, ka kasa d'aukar kaddarar ka a yadda tazo maka".

Shi dai Sadeeq jin Momy kawai ya keyi amma baiga wata ranar ladamar da zata zo mai ba, kuma ma ladamar ba akan kowa ba sai akan Siddi'ka, yaji takaicin kalaman Momy, saboda har cikin ransa ya ke jin kiyayyar Siddi'ka.

tace "dama akan maganar makarantar Siddi'ka ne yasa nace kazo, tunda kai ba kayi hankalin haka ba, kasan dai an koma hutu, so nike ka kaita makarantar su Khadija saboda akwai koyarwa sosai kuma kaga tana da saurin d'aukar abu bazata sha wuya ba".

Yana sosa 'keyarsa yace "Momy gaskiya ni boarding school zan kaita acan katsina nama gama komai yanzu haka ranar lahadi zan kaita".

Momy bataji dad'in abinda Sadeeq ya aikata ba tare da ya nemi shawar ta kona Daddy ba, saboda haka tayi mai fad'a sosai kuma tace "bata yadda ya kai Siddi'ka boarding ba".

da yake Sadeeq ya iya dad'in baki kamar d'an siyasa yasan kalaman da zai fad'a ayi saurin yadda dashi, nan take ya siye Momy da da'd'ad'an kalamai har ta amince masa.

A zahiri Sadeeq 'karya ya keyi, ba wata register da yai mata, yana dai da burin yin hakan, saboda bai son ya kaita jeka kadawo, yasan su Momy zasu takura masa ne, amma boarding sai idan anyi hutu tazo, ko babu komai zai samu sau'kin abun,
Bugu da kari yana san ya shigo da batun auren sa da Zuby nan bada jimawa ba, saboda a halin yanzu soyayya mai 'karfi ta shiga tsakanin su sun aminta da junan su har sunyi alkawarin aure duk da basu taba ganin juba ba, yau Sadeeq zaije ganin ta saboda itama anan garin Abujan take, kusan karfin zuwan nasa ita ce, domin yana matukar 'kaunar Zuby kuma yana da muradin ganin ta.

Momy ce ta katse shurun da cewa "kuma aji nawa za a sata?".
"Momy ya danganta da yadda suka gwada ta kinsan yarinyar kwata kwata ba tada 'kwa'kwalwa, yanda kika san dusa haka kanta yake, Allah dai yasa ko JS1 ne su d'auke ta".

"Js1 fa kace Sadeeq! Ina laifin 2 idan 3 bai samu ba, to ban lamun ce ba ban yarda ba kayi duk yadda za kayi,ta gama primary School fa, kai kan ka shaida ne akan makaranta da ta gama, kuma kada na 'kara jin kace bata da 'kwa'kwalwa zan sa'ba maka".

"Uhm" dai Sadeeq yace

Daga haka ya mi'ke "Momy ni zan fita a kwai wani aiki da zanyi zuwa anjima zan dawo zan kwana biyu anan kafin na koma ".

β™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύ

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
𝑫𝒂 𝒃𝒂𝒛𝒂𝒓 π’Œπ’– π’π’Šπ’Œπ’† π’“π’‚π’˜π’‚ π’Žπ’π’”π’π’šπ’‚ π’π’‚πŸ’ƒ π’Š 𝒍𝒐𝒗𝒆 π’šπ’π’– 𝒂𝒍𝒍
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹


NI DA YAYA SADEEQ

Page 13
Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β 

˙·٠‒●β™₯ Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… β™₯●‒٠·˙

Ya Allah ina rokonka da dukkan kyawawan sunayen ka ka kiyaye duk wani musulmi daka shiga mawuyacin hali kabamu lfy me amfani kasanya mana haquri da juria ya Allah ka kwantar mana da hankulanmu ya Allah kada kabamu ikon butulcemaka koda ka jarabcemu πŸ™

Page b13

A gaggauce yayi faking motar sa ya fito, ya shiga cikin gidan yayi sa'a babu kowa a falon sai TV da aka bar sa a kunne yana 'kira'ar alQur'ani mai girma, darect sama ya haura bai zarce ko ina ba sai d'akin sa, yana shiga ya aje wayoyinsa ya cire a gogan hannun sa, sannan ya fad'a bayi bai wani d'auki lakaci ba ya fito d'aure da towel a 'kugun sa da wani a hannun sa yana tsane ruwan kansa sa, gaban madubi ya zauna mayuka ne kala kala da turaruka masu 'kamshi da tsada ya shafa wannan ya mutstsuka wancen, saida yabi yagama shafa ko wanne, sannan ya fesa body spray mai sanyin 'kamshi. wata dakakkiyar shadda fara ya d'auko wanda aka 'kawata ta da ado da dinkin zamani, hular zanna bukar ya ciro ya a je a gefe, sannan ya d'auko agogon hannu da safa da ba'kin takalmi mai sheki, a tsanake ya shirya abin sa tsaf sannan ya d'auki wayo yin shi ya fito. Da sauri sauri yake sauka akan step d'in tun kan ya 'karasa saukar yake jin hayaniyar su Momy bai so haka ba, saboda yanzu saita tsare shi da tambayar ina zashi "Momy". Sadeeq ya fad'a alokacin da ya 'kara so cikin falon, gabad'aya yaran jinin jikin su suka sha, saboda basu san ya zo ba Siddi'ka kuwa batayi mamakin ganin sa ba, bakin ko waccen su na rawa suka fara gaidasa ya amsa fuska ba yabo ba fallasa "yau she kadawo gidan sadeeq? Kuma ina zaka haka kaci wannan kwalliyar sai kace sabon ango". Yana sosa 'keya yace "wallahi Momy ban jima da shigowa ba bikin wani aboki na zani anyi daurin auren jiya yau ake dinner shine nike ta sauri kada nayi latti".
"A dawo lafiya".

Tun a hanyar sa ya kira gimbiyar, ya shaida mata yana hanya, 'kara kwatanta mishi unguwar tayi, da misalin 'karfe 8:17 ya isa cikin unguwar, daganin ta ma'aika ne a cikin ta saboda gidajen kusan duk iri d'aya ne kamar quarters haka unguwar take

Bayan yayi faking a gefen wani gida, ya d'auko wayar sa da ke ajiye a gefen sa yad'an shafa screen d'in sai ga number tafito da suna Baby a jiki call ya danna sai da ta fara ringing sannan ya kara a kunne

Ringing biyu ta d'auka ajiyar zuciya ya sauke yace "Baby na" daga can 'bangaren cikin shagwaba tace "my kazo ne?".

Cewa yayi "akasi aka samu Baby, bayan na gama waya dake sai ga kira da ga office din mu wai ana son gani na, to babu yadda na iya kin san aikin gwaumnati, shine na juya a kalar tafiyar hanzu haka ina hanya ban isa ba ha'kuri na kira na baki".

Zuby da ta gama shiryawa zuwan, Sadeeq d'in kawai take jira, batasan sanda kwalla ta fara zubo mata ba, cikin shagwa'ba take fad'in "amma my kasan dai bazan ji dad'i ba wallahi har Abbah na sanar masa kuma yana gida inason ka gaisa da shi ga Momy da tun sanda ka shaida min zaka zo na fad'a mata tasa aka shirya maka abin ci yanzu mai kake so na ce musu?". ta kara sa maganar tana fashe wa da kukun shagwa'ba

Tun Sadeeq yana dariya ciki ciki har saida ta fito fili saboda yadda Zuby ke shagwaba gunin ban dariya ga kuma kasala da yarasa ta maye ta saukar masa duk a lokaci daya

"Haba my wai dariya naba ka?". Niyar fashewa da wani kukan take yi, yayi saurin cewa "gani a 'kofar gidan ku kisa mai gadi ya bud'emin get ko ba shine mai ba'kin get ba?".
Shuru tayi saboda bata yadda da abinda yace ba
Jin shurun yayi yawa Sadeeq yace "ko in koma ne?".
"Wai da gaske My kana 'kofar gidan mu?".
"Na ta'ba yi miki 'karya ne?".

"A a". Ta bashi amsa

"to kisa abud'e min get".

Ihu ta saka 'kamar 'karamar yarinya ta cilla wayar kan gado

SADEEQ da kallo yabi screen din wayar yana mamakin Zuby d'in wani lokaci idan tayi abu saita koma kamar Baby amma duk da haka tana matu'kar burge sa saboda son ta a kullum 'kara dad'uwa yake yi acikin zuciyar sa, a yanzu haka yanajin idan ba ita bazai iya rayuwa da wata 'ya mace a matsayin matar sa ba.

Mai gadi ne ya wangale get d'in Sadeeq ya sulala da motar sa ciki, kana ya nemi guri yayi faking

Bai fito daka cikin motar ba wayar sa ta hau 'kara a kasalance ya d'auka ya kara a kunne, daga d'ayan 'bangaren tace "My ga Rahmatu nan yar aki zata kaika falon baki".

"Banga kowa ba ni".

"to baby ka fito daga cikin motar mana zaka ganta".
Ta fad'a tana 'kara gyara tsayiwar ta a jikin balakona, saboda tun sanda ya shigo take le'ken sa, har kawo yanzu da take waya da shi tsaye take ko motsin kirki bata yi sai Murmushi da take yi zuwa zuwa mai wuyan fassaruwa.

Da ya bud'e murfin motar saida ya d'auki 10 seconds sannan ya fito da 'kafar sa, guda bayan wasu seconds din ya fito da d'ayar, Zuby dake la'be a balakona mamaki jan ajin irin ma Sadeeq take yi, saboda ko ita da take mace bata da kalan sa.

"Wow" shine abinda Zuby ta fad'a a lokacin da taga ya fito, "gaskiya gayen nan 'karshan had'uwa ne kamar shi yayi kanshi, Sadeeq ka riga ka shigo hannu bazan taba bari ka kubuce min ba, ban taba jin ina son nayi aure ba sai akan ka, zanyi iya bakin kokari na wajen jan hankalin ka, kuma zan kiyaye duk abin da zai sa ka gane wace ce ni, bazan bari wata kawa ta ta sanka yanzu ba gaskiya, saboda gudun matsala, inason asa bikin mu nan kusa, saboda kada yan gulma su yimin cikas". Zuby ce ta fadi haka bayan ta gama 'karewa Sadeeq kallo

gaskiya Sadeeq namiji ne irin mazajen da suke da wahalar samu a wannan zamanin saboda ya had'a duk wani abu da ake san namiji ya mallaka, Allah ya bashi yana da tsayi na misali ga kyau da hasken fata ga kudi da ilimi hankali ya iya daukan wanka ya iya soyayya mai daukan hankali duk shigar da yayi sai ta yi masa kyau shiba siriri ba shiba dan lukuti ba gaskiya masha Allah gayan ya hadu ajin karshe neπŸ₯°

Wata matashiyar mace da bazata haura 35 years aduniya ba ta 'kara so gurin sa cikin girmama sa tace "ranka shidade nice Zuby tace na kaika falon baki".

Sadeeq da wani lokaci magana take masa wuya bai amsa mata ba sai nuni da yayi mata alamar babu damuwa ta kaisa, tana gaba yana bin ta a baya har suka isa cikin wani madai-daicin falon da yake d'auke da manyan kujeru masu ruwan orange da baki sai chanis kafet da aka shimfid'a a tsakiyar falon shima ba'ki ne da d'ishi d'ishin orange a jikin sa sai 'katon TV da ya mamaye jikin bangon falon a gefe guda a kwai 'yan 'kana nun tebura zagaye da baba a tsakiyar su gaskiya d'akin ya had'u wani abun ma bazai fad'u ba

bayan Sadeeq ya shiga ya nemi kujera ya zauna a kan 1cter jim kad'an sai ga rahmatu ta shigo hannun ta rike da katon tirai da aka jera kulolin abinci masu kyau da ban sha'awa a kan babban teburin ta jera kulolin, sannan ta fita ta kuma dawo wa da wani 'katon turai din mai dauke da fruit da da kunin aya da zobo ta kuma jerawa ta fice, can sai ga ta ta kuma dawo wa da jok din ruwa a turai da kofuna biyu bayan ta ajiye ta dauki kofi daya ta zuba mai
Ruwan sannan ta saka wani farin abu a ciki kamar 'kankara nan take ruwan ya fara canza color daga fari ya koma ja haka dai yai tayi sannan ta mi'ka masa
Amma sai yaki amsa da taga bashi da niyar amsa sai ta ajiye ta fice, acikin ranta take cewa "ko ina Zuby ta samo wannan kyakkyawan saurayin tunda Zuby ke kawo samarin ta bata taba kawo mai kyau da hankali da nutsuwar wannan ba". Abinda ya daure wa rahmatu kai yadda Sadeeq din yayi shigar kamala yana kama da mutanen kirki a fuska, to mai yakawo sa gurin Zuby, saboda Hajiyar ta ta san duk wani abu da Zuby ke aikata wa, wani lokacin ma ita ke bata karfin gwuiwa sabanin Abban ta da bai san komi ba

β™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύ

Gaba daya mutanen gidan zaune suke a falon sama amma kowa da abinda yake yi, saboda Umar littafi ne a gaban sa yana homework, yayin da khadija da Siddeeqah suke fira, Momy kuwa laptop ce gaban ta tana dannawa, sai Jiddah dake faman danna waya tana cika tana batsewa Ummi kuma Session flm take kallo, sun dauki tsawan lokaci a haka.

Bayan Momy ta gama abinda ta keyi ne ta dube ni "Siddee'ka". saida naji 'ya 'yan hanjin cikina sun kad'a saboda fargabar abinda zata cemin, da hanzari na dago kaina muka hada ido nace "na'am Momy".
"dazun da rana nayi magana da Sadeeq akan maganar makarantar ki". Yace "ya samami ki admission a makarantar kwana, har ya gama komai ranar lahadi zai zo ya dauke ki ya kai ki.

Ba Siddeeqah kadai ba har su Khadija sai da suka dago kai suka kalli Momyn, domin su dad'a tabbatarwa, basu ga alamar wasa afuskan ta ba, duk da Momyn daman ba mai irin wasa da yarannan bace amma kuma tana jansu a jiki ta yadda duk wani abun da yashige musu duhu suke zuwa neman shawara gurin ta.
"Momy makaranta kwana fa ki kace". Siddeeqah ta fada murayan ta a sanyaye.

"Eh". Siddeeqah wallahi makarantar kwana Sadeeq ya nemo miki, naso na hana amma sai yace "ya kashe kudade masu yawan gaske saboda sunan wata a ka cire aka sa naki". Sannan yace "acan sai kin fi dagewa kiyi karatu idan kina gida wasa ba zai barki ba".

"Momy Daddy fa shima ya yarda ko bai sani ba?". Khadija ta tambayi Momy

Sai a lokacin Momy ta tuna ba tayi waya da Daddyn ba dan sanda ta kira sa ta nason suyi maganar yace "mata suna meting idan sun gama zai kira ta".

"A a" Momy tace "zuwa anjima idan ya kira ni za muyi maganar".

"Momy mai yasa yah Sadeeq zai mini haka, gaskiya ni Momy ba zani ba, gwara in koma 'kyauye gurin Inna ta na hakura da karatun bazan wani yi kuku da ku ba".

"Taso kizo kusa dani 'yata". Jiki na babu laka na tashi na koma kusa da ita na zauna na tsaida idanuwa na akan fuskar ta, hannun ta ta daura a kan kafad'a ta cikin lallashi tace "Siddeeqah ha'kuri zaki yi saboda ilimi gishirin rayuwa ne idan Sadeeq yayi haka ne don ya kunta ta miki to insha Allah aniyarsa ce zata bisa saboda ke gaba ta kai ki, Ki kwan tar da hankalin ki babu abinda zai same ki sai alkairi".

"Momy kuma wace makarantar?". Ummi tayi tambayar
"Katsina" yace "zai kaita wai akwai kanwar Farooq a can" yace "makarantar tana da koyar wa sosai kuma suna da kula da dalibai".

Jikin Siddeeqah yayi mutakar sanyi duk da bata taba jin labarin makarantar kwana ba, amma dai ba tason tayi nisa da gida ita da take so duk bayan 2 weeks tana zuwa Dande ganin Inna, gashi yanzu za a kaita wani garin ba garin da take ba

Da kyar Momy ta shawo kanta ta amince, amma ba dan ranta ya so ba, sai dan ganin girman Momy da take yi, Momy ta cigaba da bata baki da kalmomi masu dadi da sanyaya rai har ta amince

β™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύ

Zuby ce zaune a kan kujerar dake kallon ta sa, kura mata ido yayi ko kiftawa ba ya yi.

Cikin shagwaba tace "muni na ka ke kallo ko banyi maka ba ko?".

"ko daya ina kallon irin baiwar da Allah yayi miki ne Kin kuwa san wani abu?".

"A a". Tace mai

"Ban taba ganin mace mai kyau irin kiba, tun da nike a rayuwa ta, ban taba haduwa da wacce na ke so ba har naji ina muradin auren ta ba, sai ke, gaskiya ki kara godewa Allah bai rage ki ta ko ina ba a lokacin da naga kina tafiya sai kikai mini kama da wahainiya hatta muryan ki abar so da kauna ce idan kina magana kamar ana busa sarewa, ga...".

"Ya isa haka my kada kasa na kasa bacci yau amma ka zuga ni da yawa har kasa naji kaina yayi kato".

Duk kuwa da ba karamin dadin kalaman shi taji ba wani d'a namiji bai taba yaban ta haka, duk kuwa da ita mutum ce mai san ana kuranta ta ana zuga ta shiyasa tace "Sadeeq din na musamman ne".

"Ai kin wuce haka Baby na saboda kedin zara ce acikin taurari".

Cikin zolaya tace "Allah My kafi kyau a fili ka dai na wahalar daukan picture's saboda yana rage maka kyau".

"Bawani nan kodai ban miki bane?".

Zaro ido tayi waje gami da dafa kirji tace "wane mutum inji mutuwa".

"amma kinsan labarin zuciya atambayi fuska ko".

"fadamin nason daman dan sanda akwai ku da karantar yanayin mutum".

Zai yi magana kenan wayarsa ta hau ruri Acp Taneem yagani yana yawo a kan screen d'in cikin girmamawa ya kara a kunne ya gaida ogan na su
Ko mai yace masa daga can ban garen oho, Shi dai Sadeeq din yace "okay angama ranka shidade okay okay ahaka dai suka karasa wayar

Ya a je yana kallon Zuby da ta kura masa ido ko kiftawa batayi

"Ya dai" yace mata yayin da ya hura mata iskar bakin sa, sai a lokacin taga rashin dacewar hakan , kunya ta kamata tayi sauri ta sadda kan ta kasa tace "kamar ana neman ka A gurin aiki ne ko ?".

Gira yadaga mata alamar "eh"
"to bari na kira Hajiya ku gaisa sai na kaika gurin dady daga nan saika wuce".

Bata jira amsar sa ba ta wuce bata wani dauki lokaci ba ta dawo tare da wata dattijuwar chocolate din mata ita ba doguwa ba ita ba Gajere ba tsaka tsakiya.
Bata wani kama da Zubyn ko kadan. Hasaly ma Zubyn tana da dan haske. Da fadin fuska.

Cikin mutunci Sadeeq ya russuna ya gaisheta ta amsa mai cikin kula da jin dadi Sannan sukayi sallama ta wuce

"gaskiya Hajiya nada kirki". Sadeeq yace wa Zuby

"Allah da gaske?".

"Ehman ashe ita kika biyo".

Zuby dan dadi har rufe fuska take yi wai yau ita ake yaba haka πŸ’ƒ

"muje na kaika bangaren Abba ku gai sa".
"Muje to" ya fada yana mikewa tsaye

Ta wata kofar suka bi sai gasu a cikin wani madai-daicin falon da babu tarkace a cikin sa da wani datti jo zaune a kan kujera hannun sa da jarida yana karantawa fuskar sa sanye da siririn glass bayan sunyi sallama suka karasa ciki a kan kafet Sadeeq ya zauna ya gaida sirikin nasa Abban Zuby yaji dadi sosai da yaga sadeeq ne zai auri tilon gudan jinin sa, bayan sun gaisa suka dan taba fira Zuby kuwa bakin ta ya ki rufawa farin cikin ta ya bayyana a fili, basu dade ba Sadeeq ya yi masa sallama

babu laifi Abban Zuby yana da hasken fata wata kila agurin sa Zuby ta dauko hasken fatar

Har bakin motar sa Zuby ta rakosa tana yi masa shagwaba kala kala da kyar ya samu ya lallashi ta ta barshi ya tafi

β™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύ

"Ku tashi kowa yaje ya kwanta dare yayi sai kuma idan Allah ya kaimu gobe" Momy ce ta fadi haka yayin da take kallon 'ya 'yan ta "to" duk suka ce masu tarkace suka dauka Ummar da dakin sa yake a kasa ya shige haka Jidda ma nata a kasa yake itama ta ce "Momy good night" tuni mu uku muka dunguma zamu haura sama amma sai Momy ta kwala min kira "Siddeeqah na manta zo ki dauki abincin yayan ku ki kai masa ban garan sa tunda saman zaku haura gab yake da shigowa

*Ash wash kash*πŸ˜‚
_Na gaji hhhmmmm idan ban ga ruwan comments ba za a dade banyi typing ba_ πŸ˜‚

*Kada ku manta*
_Comment kyauta ne haka ma share da vote_πŸ˜‚

Taku har kullum _Sbeeuty ✍️

✨✨✨✨
NI DA YAYA SADEEQ
✨✨✨✨

Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… β™₯●‒٠·˙

Chapter 14

_____"To". Nace wa Momy na nufi hanyar kitchen bayan na shiga na d'auko kular abinci da zobon da Momy ta hada mai akan wani madai dai cin tirai na d'oro su sanda na fito babu kowa a falon har Momy ta wuce d'akin ta, saboda haka nima na haura sama sai da na fara zuwa daki na na sauya kaya na saboda izuwa yanzu nima na fara sabawa da kayan baccin idan ba dasu ba bana jin dadin baccin saboda haka na sauya izuwa wata farar doguwar riga, mai kauri ta bacci akwai wata yar baza mai kamar leshi a gaban ta ina sauyawa na nufi bangaren ya Sadeeq da yake dan nesa da mu saboda saikin bi ta wata kofa sannan zai sadaki da bangyaran sa dake dauke da falo da d'akuna 2 sai bayi da kitchen, nayi sa'a saboda kofar shiga a bude take ina murmushi na karasa ciki saida na gama karewa falon kallo sannan naja dogon tsaki ina ta'ba baki na ce "shi ko kunya baya ji daki sai kace na mace". A bude na bar kofar sannan na wuce bedroom din sa da shiga ta naga gado a gyare luf luf dashi ya lailaye zanin gadon sa ji nayi ina sha'awar hawa gadan saboda haka na ajiye kular abincin a kan wani teburi nayi sufa kan gadon😜 ina 'yan tsalle tsalle na ina dariya ni kadai

β™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύβ™Ύ

Tafe yake a kan hanya tunani ne fal a cikin zuciyar sa ya sa'ka wannan ya warware wancen, duk da tuki yake yi amma yayi zurfi a cikin tunanin sa ta yadda bai san mai yake yi ba Allah ne ya tsare sa da kuma kasan cewar ba akan babban titi yake ba ringing din wayar sa ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula fir gigit Sadeeq yayi saida ya dafa kansa "ya Salam ni Sadeeq mai ke damu na haka wani irin tunani ne kuma akan me nike

1 Comments On NI DA YAYA SADEEQ
avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment