Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Momy shine zaku tafi da ni?".

"Eh" kawai tace min narai-narai nayi da ido, take ƙwalla ta fara zubo min, abinka da mai neman kuka, dama koda nai wanka banyi kwalliya ba ko hoda ma ban shafa ba, saboda haka na cigaba da raira kuka na ina share ƙwallar da bayan hannu na.

Inna ce ta kama hannu na tana matsar kwalla, ba tare da tace min komai ba

Cikin kuka nace "Inna kada kibari atafi dani mana, Inna idan na rabu da ke mutuwa zanyi, nayi matuƙar sabo da ke, bazan iya rabuwa dake ba nasan wannan tafiyar ba irin wacce na saba yi bane saboda haka jiki na ke bani, nidai gaskiya bazan je ba".

Cikin sanyin murya Inna tace "to ba gasu Khadija ba acan kuma akwai su bilkeesu baki da damuwa zaki saba kuma duka 'yan uwan ki ne, inaso na inganta miki rayuwa ne". saboda 'Karami yace min idan ban bar ki kinyi karatu ba nan gaba dani zakiyi kuka".

Ina sharar Ƙwalla nace "Inna ni ba zanyi kuka dake ba ki yarda dani da iya gaskiya ta nike magana".

Shiru tai min, nai ta mata magiya.

Momy ce ta kama hannu na ta yima Inna sallama ina kuka ina kallon Inna haka na baro ta

daman driver mu yake jira a bakin ƙofar fita naci karo da Ladiyo data ke ƙoƙarin shiga gidan mu.

A ɗan firgice ta kalleni sai tayi baya.

Bance mata komai ba nashi ga mota idan ta naga ya kawo ƙwalla kuma ta bani tau sayi, a take jiki na yai sanyi, yafito ta nai da hannu, aikuwa da gudu tanufo ni

"Siddi'ka ina zaki haka ko sallama babu?".

"Birni mana".

"inda kike zuwa?".

kai kawai na ɗaga mata

"Amma shine wannan karan ko sallama babu?".

"Nima bansan da tafiyar bane ladiyo kuma karatu zanyi a can ɗin ba yanzu zan dawo ba".

"Karatu fa kika ce Siddi'ka, mai zakiyi da makaran ta?".

"Nima bansan me zanyi da ita ba Ladiyo, amma dai an cemin tana da mutuƙar amfani, kuma nan gaba zai taimake ni, zanji matuƙar daɗi, dan shi ilimi shine gishirun rayuwa".

Cikin sanyin murya Ladiyo tace "to Allah ya bada sa'a Siddi'ka don Allah kada kimanta dani".

Tabani tausayi sosai nasan kaf kauyen nan Ladiyo ba tadakama ta, kuma nima banida kamar ta
Wata ran ma ni zanyi tsoka na amma sai inja mata duk da haka bai sa ta rabu dani ba.

Nace "Bazan manta dake ba Ladiyo zan dawo gare ku Ina yi miki fatan alkairi kema".

"Ki shiga gurin Inna kice injini taba ki kayan sawa na ga baki ɗaya".

"To" tace tayi min godiya mukayi sallama ta shige gidan mu

A lokacin su Khadija sun shiga mota driver yaja muka ɗau hanya.

Comment
Share
Vote

NI DA YAYA SADEEQ
                    

بسم الله الرحمن الرحيم

                 Chapter 10

                GARIN ABUJA

 Bamu wani tsaya akan hanya ba, Dan Momy tace duk mai uzuri yayi haƙuri, ya riƙe har mu isa gida, saboda ance mata hanya babu kyau, Da misalin 'karfe 3:25pm muka isa garin birnin tarayya Abuja, tun daga unguwar zaki san ba irin unguwar nan ce ta kowa da kowa ba sai ɗan wane da wane tunda ga wajen gidan Daddy zaki san gidan manya ne saboda ko fulawowin kansu da aka zagaye gidan dasu abin kallo ne, ba sai ka shiga daga ciki ba, yawancin gidajen un'guwar ginin gidan sama ne, idan ki kaga wannan sai kiga duk yafi kyau, amma kina ganin wani sai kice wancen bai kai wannan ba, to haka dai gidajen unguwar suke, na wane yana wane na wane,

Ba yau na saba zuwa ba amma har yanzu  na kasa riƙe sunan un'guwar Saboda ita kan ta sunan un'guwar na 'yan gayu ce, kuma da turan ci ne 🤔
Gidan su Khadijan ma yana ɗaya daka cikin ƙerarrun gidajen saman dake un'guwar, shiyasa nike son zuwa saboda ina son bene a rayuwa ta.

Driver yayi  horn adaidai bakin ƙaton get din gidan

Me gadi ne ya leƙo ta ƙaramar ƙofa, ganin motar Momy ne yasa shi saurin wangale get motar mu ta sulala ciki, mai gadi ya maida get ya rufe.

Daka bisani yazo da gudu ya buɗewa Momy ƙofa, cikin ladabi yake yi mata sannu , fuskar Momy a sake  cike da annuri ta amsa masa "mun same ka lafiya?". "Lafiya lau hajiya". Mai gadi ya faɗa yana sadda kansa ƙasa, alamun girmamawa "masha Allah babu dai wata matsala ko?". Momy ta kuma tambayar Habu mai gadi, yace "eh Hajiya babu wata matsala komi yana tafiya daidai".

"A kwai kayan mu a bayan mota kashigo mana dasu ciki  kaida Idi". Da "to" suka amsa su duka

A kasalan ce muka fito daka cikin motar muka shiga cikin falo, ko waccen mu tasan ɗakin ta dan haka muna shiga ko wacce tayi inda tasan nan ne dakin ta yake.

A sama ɗakin danike sauka yake don haka na haura abina amma dana murɗa hannun ƙofar sai naji a kulle yake gam.

ɗakin Khadija dake kallon nawa naje shima a kulle yake sai dai naji motsi da alamar ita tuni tana ciki ƙwan-ƙwasa ƙofar na shiga yi, daga can ciki tace "wace".

"Siddy ce". nabata amsa

Jim kaɗan sai gashi ta buɗe, jikin ta ɗaure da tawul da alamar har ta cire kaya wanka zata shiga

"Khadija mukullin ɗaki na nazo ki bani".

"To" tace ciki ta komo sai gashi ta fito hannun ta rike da mukullin na amsa nayi gaba a bina.

"Cikin ɗaga murya ta ce" to matar yaya a huce gajiya lafiya".  Ai kwa da gudu na juyo dan na doke ta, amma sai tai sauri ta maida ƙofar ta rufe tana dariya

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

A bangaren sadeeq kuwa yana barin ɗakin Inna bai zarce ko ina ba sai gidan abokin sa Farooq, bai kirasa a waya ba amma yayi sa'a saboda ya same sa ne yana ƙoƙari fita, nan dai ya bashi hannu suka gaisa Farooq yace "yanayin ka ya nuna kamar kana cikin damuwa, kuma ba ka saba zuwa gida na a irin wannan lokacin ba, kodai kai da mutuniyar taka ce? Saboda nasan labarin gizo baya  wuce na ƙo ƙi, da fita zanyi na gaji da zaman gidan, amma tunda kazo mu shiga ciki ka faɗa min abinda ke tafe da kai".

To bayan sadeeq ya shiga ciki, bedroom suka wuce, saboda yanayin tsarin gidan irin me ciki da falo ne sai bayi da kitchen kuma duka haka gidajen kusa dashi suke saboda duka manyan 'yan sanda ne wasu suna da 1 star wasu biyu wasu uku wasu kuma igiya ce gare su, da dai sauran su kusan unguwa ce ta ma'aikatan 'yan sanda, shi yasa da wuya kaji ance wani abu ya faru a cikin ta ko kamar ace anyi fashi ko an sace wane, saboda a zagaye take da masu tsaro kamar barikin sojo ji shima Sadeeq saboda ansan shine, dan ko bai nuna id card ba ana barin sa shiga.

Kan gado Sadeeq ya faɗa yana maida numfashi, Farooq ya zauna a kan wata kujera dake bedroom ɗin yace "ba ba kaifa nike jira kace wani abu mana ka wani baje a kan gado sai kace wata mace".

Tashi Sadeeq ɗin yayi ya zauna ya shiga jero ma abokin nasa ɗanyen hukuncin da su Daddy suka yanke, Farooq ya san Sadeeq ba zai taɓa yi masa irin wasan nan ba, musamman ma da yasan cewa Sadeeq da Siddi'ka babu jituwa a tsakanin su, saboda haka ya gyara zama yace "Alhamdu lillah gaskiya naji daɗin wannan haɗin, kuma da kace ɗanyrn aiki wallahi sunyi dai dai, Ko ba komai zaka daina tsangwamar yarinyar, kuma shaƙuwa mai ƙarfi zata shiga tsakanin ku, saboda haka ka tashi muje a ɗaura auren da mu, a kwai wata sabuwar shadda na da nasa aka ɗinka min da niyar yau in sata to sai bayan na anso ta daga wurin taila na canza ra'ayi, kaga sai ka sanya ta".

Kwanciya Sadeeq ya gyara a kan gadon yace "ɗan iska mayen mata, to ai sai kaje in yaso ɗaurin auren ma sai ayi da kai, amma ni nan daka ganni babu inda zani wallahi, wai ni za'ama aure kamar wani ƙaramin yaro, arasa ma wa za a haɗa ni da ita sai 'yar ƙaramar yarinya wacce ko gama sanin inda yake mata ciwo batayi ba".

Dariya ce ta kama farooq saboda haka yay ta da rawa abin sa, saida ya gama ya fara lallashin a bokin nasa akan ya tashi ya shirya suje ɗaurin auren, amma Sam Sadeeq yace "bai san da maganar ba". Farooq yana ji yana gani dole ya ƙyale shi, amma ba dan ransa yaso ba.

 

Wayar sadeeq ɗin ce ta hau ringing cikin hanzari ya zaro wayar daga aljihun sa, ganin sunan Ha'sheem yana yawo akan screen ɗin yasa shi jan dogon tsaki yace "kagani ko Farooq abinda nake gudu kenan, yanzu haka kira na yayi ya cemin ashe nayi aure ko gayyata babu". Kiran ne ya katse, yayi saurin kashe wayar gabaki ɗayan ta, wannan dalilin ne yasa da Daddy ya kira wayar Sadeeq ɗin yaji ta a kashe.

Sadeeq ya ci gaba da cewa "ai ni yanzu na shiga uku, Daddy ya gama jamin abun kunya a gari, ni ba mai laifi ba da sai na ringa yawo da abun fuskar da zan sauya kama".

Farooq dariya harda riƙe ciki yace "wallahi aiki ya ganka yanzu za ka fara nidai ɗan kallo ne, saboda ko na baka shawara ba lallai ne kayi amfani da ita ba amma bari na gwada baka".

Sadeeq yace "wallahi Farooq na tsani yarinyar ne ji nike da ma na mutu na huta da dai nayi rayuwa da ita amatsayin mata ta".

"Kana ruwa aboki na, to kai wai me yarinyar nan tayi maka ne haka da ka tsane ta".

"haba Farooq wai har kana buƙatar ƙarin bayani, bayan komai a bayyane yake, kasan nafi san na auri wayay-yiyar mace, mai aji da yanga wacce ta gama digiri dinta, in so samu ne ma ace ta fara aiki, koda kuwa wani iri ne sannan kuma kada shekarun ta suyi 'kasa da 25 to ko bata da masifar kyau in dai tana da wa'innan abu buwan da na lissafa maka zan aure ta".

Zai ci gaba da magana Farooq ya dakatar dashi ta hanyar faɗin dakata malam "ai na ɗauka kabar wannan banzan tunanin da kasa a ranka zaka ro'ki Allah ne yayi maka za'bi mafi alkairi, ashe ba haka bane, to ina so kasan har yanzu Siddi'ka yarinya ce ba a haka zata ci gaba da rayuwa ba, ko kana da yaƙinin cewa baza ta canza ba? Ya faɗa yana kallan Sadeeq d'in".

"Eh Farooq". Sadeeq yace yana ɗaga murya "bazata canza ba a haka zata gama rayuwar ta🤔 saboda irin zuciyar uban ta gare ta, kuma bugu da ƙari rashin jin maganar ta yayi yawa, kaf ƙauyen Dande babu wan da bai san ta ba, ko ina idan na wuce ana nunani, saboda an san ni yayan ta ne, nasan ma dan suna jin tsoro na ne da tare ni zasu dunga yi, nafisan yarinya natsats-tsiya mai kunya, kaga ita kuma duk bata da su".

"Hhhmmmm Sadeeq nidai shawara ta anan ita ce kabi komai a hankali kada kayi gag-gawa, amma ni banga laifin Siddy ba rashin jin magana da kace yarinta ce take damun ta, wataran idan akace tayi zata ce ba tayi ba, sharri ake mata".

"Sa'ar Jiddah ce fa mai yisa Jiddah bata yin duk wa'innan abu bu wan da Siddi'ka keyi?".

"To ai Sadeeq kasan yara kowa da kalan ƙuruciyar sa, idan ka bibiya a kwai abinda ita Jiddahn ta keyi Siddi'ka kuma koda kuɗi akace tayi ba zata yi ba, kuma idan ka lura Siddi'ka goyan kaka ce duk abinda tayi sai ace daidai tayi ba a nuna mata tayi kuskure, amma da ina tabbatar maka da sai tafi Jiddah hankali".

Taɓe baki sadeeq yayi yace "wallahi ina raga mata ne saboda gwaggo Amina, amma yanzu tunda ta shigo gona ta zan koya mata darasi😢 zan nuna mata tayi babban kuskure, da Daddy yace zai aura mata ni, da tace mai A a bata so na ".

Kafaɗar sa Farooq ya daka sannan yace "Allah ya bama mai rabo sa'a". Ya fice a ɗakin

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

          *GARIN ABUJA*

Koda na buɗe ɗakin na same shi atsaftace, kamar yadda nayi zato saboda duk zuwa haka nike samun shi.

Da sallama ɗauke abaki na, na shiga sannan na maida ƙofa ta na rufe, kan gyararran gadon na faɗa ina maida numfashi, wash nagaji matuƙa, daga haka baccin gajiya yai gaba da ni ba tare da nayi sallar la'asar ba, daman sai da muka yi azahar agida muka taho. 

A cikin baccin ne nayi wani mummunan mafarki wanda ban taba yin irin sa ba tun da nike arayuwa ta, ban fahimci me mafarkin ya ƙunsa ba tsabar ruɗanin dake cikin sa,
A firgice na farka amma nakasa yin salati saboda ban saba ba, ina ta zaro ido na alamar tsoro nakasa firta koda kalma ɗaya ina son in tuno abinda nagani acikin mafarkin, amma na kasa, sai wani masifaffan ciwon kai daya saukar min a lokaci daya, sosai tsoro ya shigar min har banason nayi motsi saboda sai naga kamar za a kama ni, bugun zuciya ta ya tsananta, yana bugawa da sauri da sauri sakamakon buga ƙofa ta da naji anayi.

Kara duƙun-ƙune  kaina nayi a cikin bargo,  daka waje naji ana fadin "Ummi ce ki buɗe".

Jin muryan Ummi da nayi yasa nayi  han zarin saukowa daka kan gadon, jiki na ɓari na buɗe ƙofar ta shigo, rungume ni tayi  tana ihu Bata lura da yanayin da nike ciki ba, turanci ta fara su burbuɗa min bayan tasan bawani ji nike ba, amma tsabar iyayin Ummi takeyim shi, Jin ban rungume ta ba kamar yadda muka saba yasa tasake ni, tana kallo na.

tace "sisi kamar bakya hayyacin ki, meke damun ki".

"Bacci na tashi". Haka na tsinci baki na da furtawa, bansan meyisa na ɓoye ainihin abinda yasa yanayi na ya sauya ba.

"Haba koda naji". ta faɗa tana kama hannu na, muka fito daga ɗakin, ɗakin ta muka shiga wanda ya kasan ce a tsaki yar nawa da na Khadija.

"Amma yakamata kiyi wanka sisi kicanza kayan jikin ki, kin ma yi kokari da kika yi bacci dasu a jikin ki ni yaushe zan iya".

"Ai ke ki ka ce Ummi, ni kin san na saba ko a ƙauye kayan da nasa dasu nike yin bacci, duk sabun tar su bana sauyawa izuwa na bacci, duk da ina dasu".

Wata uwar ƙara ta saki a razane na kalle ta "lafiyan ki ƙalau kuwa Ummi?".

"lafiya ta lau sis naji kin anbaci kauye ne kinsan ni da 'kauye amana, don Allah yi ki fito wanka kizo ki bani labarin Dande".

Ban kuma cewa da ita komai ba, na nufi bayin wankan ta masha Allah shine abinda na faɗa bayan na buɗe bayin naga ko mai na cikin bayin fari ne ƙal kamar a zuba abinci a kasan a lashe, saboda yadda kasan tayil din ke sheƙi ga wani sihirtaccen ƙam shi da yake tashi.

A hankali na ɗaga ƙafata na shiga bayin duk da banyi addu'a ba amma na shiga da ƙafar hagu, cikin kwamin wankan na shiga na kunna famfon ruwan zafi da na sanyi na daɗe a cikin ruwan ɗumin sannan na fara wanka ina gamawa na ɗaura tawul, kana nai alwala na fito.

Ina fitowa ana kiran sallar magriba.

A gefen gado nasamu Ummi  zaune tana buga game a laptop.

Saida ta dube ni tace "gaskiya sis kin daɗe sai kace kina  canza fata gashi kuma kina nan yadda kike".

Ban kula ta ba na nufi durowar kayan ta saboda suna yimin dai dai, bayan na buɗe na ga wata doguwar rigar yadi mai laushi me run madara fitet ce ba tada wani kwalliya amma duk da haka ɗin tana da kyau,
ban wani damu da saka bra ba nafi sa haf bes, sif ɗin haf bes na buɗe na ciro, sannan na bude na fant na ɗauko sabo, wanda na gansa da 'yar takar darnan a jiki alamun ba a sa ba, da yake duk nasan inda suke harda na siket din ciki haka na fiddo duk abinda nikeda buƙata.

Sannan na nufi gaban madubi na zauna kan kujerar dressing mirror, na fara shafa mai ina gamawa na ɗauki turarukan ta masu ƙamshi da tsada na fesa a jiki da kaya na, duk kuwa da wasu ba akaya ake fesawa ba amma saboda ni ban sani ba haka nai ta fesawa, saboda a lokacin Ummi ta shiga bayi, doguwar rigar na saka na dakko dadduma don rama sallahr da ake bina sannan inyi wacce muke cikin  lokacin ta

Ina cikin yin sallar Ummi ta fito daman dad dumar na kar kata ta yadda mutane biyu zasu iyayin salla akai

Ko da na idar ban wani tsaya yin addu a ba na cire hijabin.

ƙasa na sauko, anan na tarar da duka 'yan gidan, kowa yana nan harda Aunty Bilkisu da yaranta guda biyu Samahir da da Maheer, Khadija da Umar ga Momy sai Jiddah da ke ta faman danna waya ko me take danna wa? oho, ahankali na ƙarasa saukowa daka kan benan, gurin Momy naje na rungume ta nace "Momy ya gajiyar hanya". Ina mai hawa kan cinyar ta na zauna.

Tace "Siddi'ka rigima ni ban san yaushe zaki girma ba, saboda wani abun idan kika yi ko Umar auta ba zaiyi ba".

Momy nidai naji saboda bazan taɓa girma da hawa cinya ba".

"Sarkin san jiki" Aunty Bilkisu ce tafadi hakan

"La Aunty Balki bari inzo mu gaisa".

"Wai bana hana ki cemin Balki ba? Ni suna na bil'kees". Ta faɗa tana gyara sunan, mu kwa muka  kwashe mata da dariya.

Dai dai nan Ummi ta sauko muka dasa firan da ita Samaheer ce kan cinya ta ina yi mata wasa tana ƙyal-ƙyala daria

Suwaiba mai aikin gidan ce ta shigo tace "Hajiya na kammala yana kan dinning".

"To" Momy tace sannan ta kallo mu.

"Oya kutashi muje muci abinci dan nasan kowa anan yana jin yunwa".

Kamar jira muke duk muka miƙe, muka nufi dinning kowa ya zauna muna ci muna ɗan taɓa fira, taliya ce sai faten dankin turawa da yaji hanta sai farfesun naman kaza mai yaji, babu laifi Suwaiba ta iya girki dan idan Daddy baya nan ita take yin duk wani abu da za aci ko a sha, saɓanin idan yana gida Momy ke girkawa tace su khadija su

bayan mun gama cin abinci muka dawo falo muka 'kara dasa sabuwar fira har aka kira sallar isha'i duk da Jiddih tunda na sauko magana bai had'ani da ita ba saboda ita ta nada jin kai ga san nuna ita wata ce ni kuwa ba zan d'auki iskanci ba dama ba shiri nike da ita ba saboda abu kad'an ke had'a mu mu fara dambe kowa bai san raini


NI DA YAYA SADEEQ
                  

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 11

Bayan mun idar da Sallar isha'i wata firar muka cigaba da yi, idan Khadija tayi nata nima sai nayi nawa hakama Umar, yayin da Jiddah ke faman cika tana batsewa tana jan dogon tsaki, ko ita da wa oho.

yanzu haka Umar ne ke bamu labarin wani Almajiri daya shiga bara gidan wata amarya, sai mijin yace "almajiri kawo kwanon ka". Sai amarya ta leko ta amsa, ta zuba masa abincin, Koda ta miko mai kwano sai ya amsa yatafi zauran gidan yana kuka, sai mijin amaryar yabiyo almajirin, ya tambayesa meye dalilin kukan nasa "ko abincin ne ba zai isheshi ba?". Sai almajiri ya girgiza kai, sai mijin amaryar yace "to meye kake ma kuka?". Budar bakin Almajiri sai cewa yayi "shi ba komai ya sashi wannan kukan ba illah yana tsoran agama aure kyawawan mata kafin lokacin su yai.

" Idan ke/kaine ya zaki/ka yi", haka ya jefe musu tambaya aikuwa nan sukaita tafka muhawara suna shirme

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Sadeeq kwance a kan gado, wayar shi a hannu yana cikin Instagram, sai kallon hotuna yake, kwatsam idanuwan sa suka sauka akan hotan wata yar budurwa, acikin zuciyar sa yace "daga ganin ta tanada aji kuma ba zaka ce mata 'karamar yarinya ba domin zata iya kaiwa 25 years old da haihuwa". Kara shiga account dinta yayi nan take hotunan ta da take dorawa suka bayyana sosoi Sadeeq ke kallon hotunan, sunan account din ta ya kalla yaga anyi rubuta kamar haka *Zuby officially*

"Wow" ya fada afili Suna mai dadi *Zuby* haka yaita maimaitawa bata da wani kyau a fuska, kuma ba wani haske gareta ba, amma dagani ta 'kara  da na kanti, 'kirjin ta cike yake da dukiyar Fulani tana da dirin jiki.

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

*ABUJA*

Ba muyi wata dinner ba, kasancewar bamu dade da cin abincin ba, shayi Momy tasa Suwaiba ta hado mana yaji ni'inal da kayan kamshi, mukai ta kurba kamar wasu larabaw😂
Bayan mun gama kowa ya watse, amma nikam sarkin tsoro d'akin Ummi nayi tana 'ko'karin rufe kofar nai saurin turawa
Da mamaki tace min "sisi yadai". "Anan zan kwana" na fad'a yayin da nike shigowa ciki, ta maida kofar ta rufe

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Ahaka rayuwa ta cigaba a gidan Momy, tsakanina kuwa da Jiddah babu jituwa, zan iya cewa tun nazo gidan magana bai shiga tsakanin mu ba, kuma babu Wanda ya lura a gidan saboda tun asali kowa yasan bama wani shiri, yau kimanin kwana bakwai kenan da aurena da Sadeeq amma har yau ban sashi a cikin ido naba gashi su Khadija har sun koma makaranta.

Muna falo ni da Momy a zaune, sai Suwaiba dake faman zirga zirga ta kai ta komo tana kokarin hada abincin rana, kafin su Khadija su dawo, "dauko min waya ta a bedroom dina" cikin sauri na mike domin Momy batasan simi simi, bayan na dawo nace "Momy gashi nasamu wayan ma tana ringing". "Kawo mugani waye ya kira" ta amsa tana shafa screen d'in wayar sannan ta kara a kunne
"Wa'alaikumussalam". shi ne abinda naji Momy tace kafin tace "lafiya lau". Ta kara da cewa "wallahi Sadeeq zan cimaka mutunci fiye da yadda kake zato, kasan dai yanzu ba kamar da bane kana da nauyi a kanka, amma kayi burus da mu dama gwada ka nayi naga hankalin ka, to maza maza kazo gobe inason magana da kai na fada maka idan kuwa ba haka ba zanyi mummunan saba maka".

Cikin fushi Momy tace "bazan saurare ka ba Sadeeq, baka da abinda zaka fada min na yarda, kaima kasani domin bakada wani uzuri kayi abinda nace maka kawai".

Tana gama fadar haka ta kashe wayar.

Jim kad'an saiga wani kiran ya sake shigowa daga yadda naga Momy ta daga wayar na gane yaya Mubarak ne, d'an yayan ta, na sanshi sosai ya nada mutunci da yana nan ne da zama, amma yanzu yatafi India saboda ya karasa karatun sa a can, kallo na tayi kana tace
"bani ruwa mara sanyi nasha". "To" nace na mike cikin natsuwa koda na dawo har ta kammala wayan.

𝐘𝐚𝐮 𝐬𝐡𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐛𝐚𝐢𝐲𝐢 𝐭𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐛𝐚 𝐤𝐮𝐲𝐢 𝐡𝐚𝐤𝐮𝐫𝐢 𝐝𝐚𝐬𝐡𝐢 𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐡𝐚𝐫 𝐧𝐚𝐠𝐚 𝐫𝐮𝐰𝐚𝐧 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧 𝐳𝐚𝐧 𝐲𝐢 𝐦𝐮𝐤𝐮 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐚𝐧𝐣𝐢𝐦𝐚 𝐢𝐧𝐬𝐡𝐚 𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡

Love you 💖💋💖💋💖


NI DA YAYA SADEEQ
                    

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 12

Washe gari da misalin 'karfe 11am na rana, a lokacin Su Khadija suna makaranta, Momy ma ta fita ma'kota gidan wata 'kawarta Hajiya Nafisa, amma tace ba dadewa zatai ba, zaune nike ni kad'ai a falo kan kujera ina kallon TV, bakin sa d'auke da sallama ya shigo, koda yaga ni ce zaune a falon sai ya gimtse bai 'karasa sallamar ba, gami dap d'aure fuska kamar bai ta'ba dariya ba, ni ma nayi kamar ban ganshi ba, tsawa ya daka min "dan ubanki baki iya gaisuwa bane ko nan d'in gidan uban ki ne? Ko da yike shima ubanki' tarbiyar bata ishe sa ba bare kuma kema ya baki".

Inajin zafin gorin da Sadeeq yake mini har cikin raina a lokuta da dama

ya cigaba da cewa "idan ba mummunar

1 Comments On NI DA YAYA SADEEQ
avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment