Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Yah sadeeq yanada Alheri, bashida rowa, yana so ya kyautatawa na ƙasa da shi, saboda haka ya ciro kuɗi daga aljihun sa ya bawa matashin 'yan Naira Ashirin sababbi gada gal.

Matashin ya ansa yana godiya .

Ban dawo gida ba sai 10:00 pm saura kamar dai jiya, bana kallon gaba na a guje na shigo cikin gidan, yah Sadeeq da ɗauko kular a bincin sa kenan, na buge sa abinci ya zube, koda na lura da abinda nayi ɗakina na shige aguje  na saka sakata, ina maida numfashi.

Su momy sunga abinda yafaru

Gurin Inna ya koma "Inna ina abincin yarinyar nan?". Ya tambaye ta

"Gayi can". Ta nuna masa wani kano dayike arufe cike da shinkafa da miya harda ɗan naman kaza, ɗauka yayi zai fita, Momy tace mai  "dawo mata da abincin ta kafin na  saɓa maka". Inna ce ta katse ta da faɗin "haba Aisha yanzu ai itace da laifi bakiga yadda ta zubar mai da abincin sa  ba, kuma idan ba natan ba mai zaici? kinsan Garba baicin abincin waje, gashi dare yayi bare a sake girka masa wani". Ta cigaba da cewa "mutumin ma da ba lafiya gare sa ba ma, yanzu fa yake ce mana sai da aka ƙara masa ruwa da yaje asbiti, kuma ance saiya ci abinci sannan yasha magani,
tunda ba tajin magana ita ta kwana haka, yi tafiyar ka Garba kaje ka ci abin cinka".
Yace "na gode Inna" ya fice daga falon.

khadija kuwa cewa tayi "wai Inna ina Siddiqa ke zuwa ne haka idan tafita sai  dare take dawowa kuma ba'a sanin sanda take fita".

"Ina kuwa zata in ban da yar kasuwa, ai nan take zuwa taita tsokanar mutane sam bata san zaman gida, karatun ma yanzu taki shi kwata kwata, babu muhammadiya babu na zamani".

"Allah ya kyauta" khadija tace "amma wallahi Sam Siddiƙa batawa kanta adalci ba saboda a wannan zamanin ilimi shine kan gaba".

Momy ce tace "ai gobe Daddyn ku zai zo inaga da ita zamu tafi, Hajiya saidai kiyi haƙuri, tunda bazaki bimu ba, ko yar aiki sai a ɗauko miki, amma karatun Siddiƙa yana da mutuƙar muhimmanci, idan ba abar ta tayi ba, to nan gaba bazata gode mana ba, zata ɗauke mu a matsayin azzalumai ne".

jin jina kai Inna tayi alamar gamsuwa tace "Allah yasa haka shine mafi alkairi".

Umar ne yazo ya buga min ƙofa daga ciki nace "waye anan?".
"Umar ne".

buɗe masa nai ya shigo na maida ƙofar na rufe, kamar dai jiya, yau ma tambaya ta yayi labarin abinda yafaru, na kuwa bashi labari harda haɗuwa ta da yaya Sadeeq, yayi dariya sosai, amma yace min "yayi fushi tunda ban nemeshi ba sanda zan tafi".

Haƙuri nashiga basa da cewa "nima ban san zanyi nisa ba naje siyo alewa ne, shine nabiya ta an, naje da kai gobe".

Yace "uhm abinda gobe Daddy zaizo kuma gida zamu tafi.

Ji nayi gabana ya faɗi, amma saina daure nace "da gaske gobe Daddy zai zo?". Umar yace "eh wallahi nima a bakin Momy naji". Nace "to Allah ya kawo sa lafiya".

"Ameen" Umar ya faɗa

"ina yaya Sadeeq?". na tambayi Umar

Yace "ya ɗauki a bincin ki ya tafi ɗakin sa, kin san baida lafiya".

ban san sanda dariya ta ƙwace min ba,  saboda na manta da abinda yafaru, sai  yanzu da Umar ke fa ɗin baida lafiya na tuna.

"wai lafiyarki. Aunty Siddiƙa?".

Nace ƙalau Umar wani abu na tuna, shiyasa kaga ina dariya".

"Muje tunda wancan mugun benan ko Indomie na girka don yunwa nike ji".

𝐻𝑖𝑚𝑚 𝑡𝑢𝑟𝑘𝑎 𝑡𝑢𝑟𝑘𝑎, 𝑘𝑢𝑑𝑎𝑖 𝑘𝑢𝑐𝑖 𝑔𝑎𝑏𝑎 𝑑𝑎 𝑘𝑎𝑠𝑎𝑛 𝑐𝑒𝑤𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑒 𝑑𝑎𝑛𝑖, 𝑑𝑜𝑛 𝑗𝑖𝑛 𝑚𝑎𝑦𝑒 𝑧𝑎𝑖 𝑓𝑎𝑟𝑢 𝑖𝑑𝑎n  𝐷𝑎𝑑𝑑𝑦 𝑦𝑎𝑧𝑜 𝑎 𝑘𝑤𝑎𝑖 𝑑𝑟𝑎𝑚𝑎 𝑎𝑔𝑎𝑏𝑎✍️


NI DA YAYA SADEEQ
                 

بسم الله الرحمن الرحيم      

               Chapter 08

Yanayin tsarin ginin gidan 2 bedroom ne, amma a ko wani ɗaki anyi kofar da mutum zai iya bi ba sai yabi ta falo ba, sai ɗakuna biyu da suke a tsakar gida ɗayan na hanyar waje shine ɗakin yah Sadeeq,sai wanda idan su Momy sun zo suke sauka a ciki, a kwai kitchen a tsakar gidan da bayi,

Inna bata son amfani da kitchen din ɗaki tafi sabawa da na waje.

Amma ni nakan yi amfani dashi idan zanyi jagwal-gwalo na.

Kitchen ɗin na shiga na buɗe dirowar da nasan muna ajiye Indomie, na dauki guda ɗaya. Gas na kunna ruwa na fara tafasawa, kana nazuba Indomie ɗin, sannan nakawo tarugu 1 nasaka nazuba mangyaɗa a ciki ina cikin juyawa, sai ga Khadija taleƙo, cikin zolaya tace "ga yaya Sadeeq can afalo, yace mai kwatar ki yau sai Allah, Inna tayi bacci tun ɗazu, Momy kuma ta tafi ɗaki, daga ni sai Umar ne a falo.

Hantar ciki na ce tafara kaɗawa, jikina yafara rawa na kasa magana, bani da tsoro amma ina tsoran haɗuwa ta da shi, saboda ba da wasa yake min ba, amma duk da haka idan rashin kunya ta, ta tashi ina yimasa

A kiɗime nace "bari na fasa ihu tun kamin yacinmin kinga su Momy za suji su zosu zo su cece ni".

Saka tafin hannaye na nayi na toshe kunnuwa na, saboda inyi ƙarar iya karfi na, zan ƙwallara kenan tayi saurin toshe min baki da tafin hannun ta, tana ƙyalƙyala dariya, Ta ce "naɗauka keɗin jaruma ce, a she ba haka bane, kamar ba kece shekaran jiya kika cemin sai kin rama dukan da ya miki ba, taya zaki rama kina wannan tsoran?".

Sai alokacin nasaki ajiyar zuciya, nabi ta da duka ta fita tana dariya.

koda na duba Indomie na har ta dawu ta fara kamawa, kashe gas nayi, anan kitchen na zauna, a cikin tukunyar naci, inaci ina santi saboda tayi daɗi kuma nayi mata irin dahuwar da nikeso.

Bayan na gama ci, na buɗe baki na sosai na saki wata uwar gyatsa babu ko alhamdu lillah
Na miƙe tsaye nayi  miƙa.

Ɗaki na wuce inda natar da Khadija na sharar baccin ta hankalin ta kwance, kan gadon nima na hau kusa da ita na kwanta ina jina wani iri kamar wani abu zai faru dani.

Washe gari ban farka da asuba ba sai Misalin 8:9am Khadija babu irin tashin da bata yi min da asuba ba, akan nayi sallah amma naƙi, sai ma ƙara gyara kwanciya ta da nayi, Kamar yadda nasaba tashi haka nayi babu ko addu'ar tashi daga bacci, na sauka a kan gadon, brush na ɗauka, ina tatsa makilin ne Khadija ta shigo fiskarta ɗauke da  murmushi, da ganin bakin ta a kwai magana, "au ashe kin tashi daman ke nazo tasa wallahi". Ta faɗa tana matsowa kusa da ni.

"Eh tashi na kenan, wai yanaga kina ta murmushi ne?".

Tace "ba dole ba Daddy fa yazo, shine ma yace na taso ki saboda ya tambaye ni kina ina". Nace kina bacci".

"Amma wannan karon yazo dawuri gaskiya". Nafad ina ajiye makilin ɗin hannu na.

Tace "Eh naji yana cewa Inna da karfe 2:pm jirgin su da zai wuce lagos zai tashi shiyasa yayi sammakon zuwa".

Jin jina kai na nayi, alamar gamsuwa "to bari nayi sallah" nace tare muka futo  ta nufi ɗakin hajiya Inna, ni kuma na nufi rijiya na janyo ruwa, na zuba a bokitin wanka, na kai bayi saida na fara yin wanka sannan na ɗaura al'wala.

Tawul na ɗauro ajiki na, amma irin 'katon nan ne, kuma na wanke kaina babu ko ɗan kwali haka na fito daga cikin bayin.

Adai-dai lokacin yah Sadeeq ya shigo cikin gidan, haɗa ido mukayi, saida ya ƙare min kallo tsaf, sannan yaja dogon tsaki, shasha ya faɗa afili, kana ya wuce ya shiga ciki.

Saida ya wuce sannan nima na wuce ɗaki, wata doguwar rigar atamfa na ciro mai launin blue da ruwan hoda, baseline na shafa, sannan na saka atamfar, na ɗauki hijabi na nasaka na gabatar da sallar asuba, bayan na idar na nufi falon hajiya, ina jin gabana yana faɗuwa, narasa mai yisa amma tun jiya da Umar yace "Daddy zai zo" gaba na ke faɗuwa, amman yanzu bugun zuciyar tawa yafi tsanan ta.

Daurewa nayi na kutsa kaina cikin falon baki na ɗauke da  sallama, kowa ya hallara, suna karyawa, Daddy da Inna da yaya Sadeeq a kwano ɗaya suna cin ɗan wake,  Khadija Momy Umar. Kuma  waina suke ci.

Daddy ne ya dube ni yace "wa'alaikum'ssalamu ɗiya ta shigo ga wuri ki zauna, ya nuna min tsakanin sa da na yaya Sadeeq, ƙarasawa  nai na zauna, kana nace"ina kwana Daddy".

"Lafiya lau".

"na same ku lafiya?".

"lafiya lau Daddy, ya hanya?".

"Al'hamdu lillah ". yace min, yana mi'ko min cokali yace "bimismilah
me sunan manya".

Ina lura da yanayin yah Sadeeq ya canza tun sanda na zauna, ya wani ɗaure fiska sai mutsu mutsu yake yi, ina saka cokali na cikin kwanan yana cire nasa yamiƙe tsaye, Daddy ne yakalle sa, yace masa "ya-ya ana cin abinci ka tashi?". Na ƙoshi ne Daddy".

"Dawo ka zauna sai mun cinye da kai".

Badan ran Sadeeq  yaso ba, haka ya dawo ya zauna ya maida cokalin sa, ina lura da yadda yake cin ɗan waken kamar yana cin magani.

Misalin karfe goma 10:00am Daddy zaune a kan kujera Inna na kusa da shi Momy na 2 cter, ni da Khadija na zaune  a ƙasa kusa da ƙafar Momy, yah Sadeeq kuma na gefen Daddy zaune a ƙasa, kanshi a ƙasa yana danna wayar sa.

Daddy ne yai gyaran murya, kana yafara da cewa "da farko ina mai ƙara jad-dada godiya ta ga Allah ma ɗaukakin sarki da yabin damar aiwatar da wannan ƙudirin nawa, tsira da aminci ya tabbata ga fiyayyen halitta annabin mu Muhammad (S. A. W). Bakomai ne yasa na taraku anan ba, saidan ke Siddiƙa me sunan manya, ya faɗa yana nuna ni, ina san yau ɗin nan na  ai'watar da ƙudirin mahaifiyar ki akan ki,
Ina fatan zaki yimana biyayya, nasan baki da matsala, saboda mun isa dake ne zamuyi abinda mukesan yi yanzu, ina so kisan bakida Wanda ya fimu a kaf faɗin duniya, bazamu taɓa cutar da ke ba".

Tun da Daddy ya fara magana gaba na ke faɗuwa, shin wani kalan ƙudiri ne wannan da har Daddy ya ambace sa da ƙudirin mahaifiya ta?". Banida wannan amsar saboda haka nacigaba da sauraran abinda Daddy ya cigaba da faɗa.

Daddy ya cigaba da cewa "naso ace sauran 'yan uwanku sunanan, amma duk da haka kuma kun isa shaida,  kuma akwai abokai na guda biyu wa'inda tare dasu  zamu tafi lagos, nayi magana dasu, saboda muhimmancin abinda zan tattauna daku zasu biyo tanan".

Kallon Hajiya Inna yayi yace "Hajiya ko  akwai abinda ki ke san faɗa".

Tace "eh ina da abin faɗa". yace "to muna saura ranki".

Tace "Ƙarami". Haka Inna ke kiran Daddy da Ƙarami "ni abinda ke damu na yadda, Garba ya tsani yarinyar nan , kamar ba ƙanwar sa ba, Kaf ƙauyen nan babu wanda bai san da zaman ƙiyayyar da Garba yaiwa yarinyar nan ba, a gaban kowa nunawa yake, a waje bai sarara mata ba, haka a gida, motsi kaɗan tayi sai duka".

Wani gwauran numfashi Daddy ya sauke, sannan ya fara yiwa Yaya Sadeeq faɗa, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, sosai Daddy yayi wa yaya Sadeeq fata fata.

Kana ya maida kallan sa ga Momy yace "Aisha fa kina da abin da zaki ce".

murmushi tayi irin  na su na manya tace "ai kai da Hajiya kun gama faɗan duk abinda zan faɗa, sai dai aƙara yiwa sadeeq faɗa a kuma ja mai kunne, sai muyi  musa fatan Allah yasa alkairi".

"Ameeen" Inna tace yayin da Daddy yace "alhamdu lillah".

Daddy yace "mai sunan manya matso nan kusa dani kinji". Jikina a sanyaye na matsa kusa na zauna a ɗayan bangaren da ke kallon Sadeeq,   sai bankamin harara yake a sace, nayi kamar bansan yanayi ba.

Dafa kaina Daddy yayi yace "Allah yayi miki albarka". "ameen". Nace

Sannan ya cigaba da cewa "𝚂𝚒𝚍𝚍𝚒'𝚔𝚊 𝚍𝚊𝚐𝚊 𝚢𝚊𝚞 𝚢𝚊𝚢𝚊𝚗 𝚔𝚒 𝚂𝚊𝚍𝚎𝚎𝚚 𝚣𝚊𝚒 𝚝𝚊𝚜𝚑𝚒 𝚍𝚊𝚐𝚊 𝚖𝚊𝚝𝚜𝚊𝚢𝚒𝚗 𝚢𝚊𝚢𝚊𝚗 𝚔𝚒 𝚣𝚊𝚒 𝚔𝚘𝚖𝚊 𝚖𝚊𝚝𝚜𝚊𝚢𝚒 𝚋𝚞𝚢𝚞, 𝚣𝚊𝚒 𝚍𝚞𝚗𝚐𝚊 𝚊𝚖𝚜𝚊 𝚖𝚊𝚝𝚜𝚊𝚢𝚒𝚗 𝚖𝚒𝚓𝚒𝚗 𝚔𝚒 𝚍𝚊 𝚔𝚞𝚖𝚊 𝚢𝚊𝚢𝚊𝚗 𝚔𝚒".

Wata muguwar faɗuwar gaba ne ya ziyarceni, a take naji na fara kyarma, jiki na sai bari yake,
a tare nida shi muka miƙe tsaye, duk kannin mu idan mu a waje alamar rashin fahim ta.

" Koma ku zauna" Daddy ya faɗa, jikin mu babu ƙwari haka muka koma muka zauna, Khadija ma dake zaune mamaki ne yacika ta shiko Umar ko ajikin sa Inna kuwa da momy daman sun san da batun.

"ƙwarai kuwa abinda kukaji nafaɗa hakane ba mafarki kuke yiba, domin wannan shine burin ƙanwata Aminatu". 'Kwalla ce ta cika idonun sa yayin da ya kasa ƙarasa maganar Handkerchief yaciro cikin aljihun sa yana share ƙwalla.

Da irin murayan Wanda yake son yayi kuka, Daddy ya cigaba da cewa "auren ki da Sadeeq shine burin ta, bamu sani ba ko a raye take ko amace, kimanin shekaru goma sha biyu da wasu yan wattani kenan, tun tana goyen ki". ya nunani "nasan kunsan komai ba sai na ƙara tada muku da zancen ba, saboda bana son tada mana hankula".

tuni inna tafara shash-sheƙar kuka momy na faman bata haƙuri, da ƙyar dai aka shawo kan ta tayi shuru.

Da gaske duka family an san labarin ɓatar mahaifiya ta, amma bamu san yadda al'amarin ya faru ba

Daddy yacigaba da faɗin sai dai kiyi haƙuri, naje  har gidan ku da ƙyar nasamu ganin mahaifin ki, na je masa da batun auren ki, yace min shi babu ruwan sa  yama manta dake cikin 'ya 'yan sa, ba tun yauba ai ya faɗa mana ya bar mana ke, idan yankaki zamu yi muyi, shi baya da matsala babu ruwan sa, ya 'kara da cewa ai tun ranar da Amina  tabar gidan nan  na manta da duk wani abu daya shafeta, yanzu haka abinda yasa bazan sa karnuka su fidda min kaiba saboda baka sani ba, amma yanzu tunda kasani kada inƙara ganin ka akoafar gidan a, kai ba kai ba ko Siddiƙa ɗiyata ce tazo sai nasa karnuka sunyi yaga yaga da naman jikinta, saboda haka Get out in my house".

  jiki na babu ƙwari Siddiƙa haka na fito daka gidan ku.

Ban taɓa jin tsanar mahaifina irin na yauba kuka nike sosai ina tir da halayen sa, kowa a ɗakin jikin sa yayi sanyi dady ne ke shafa min kai yana bani hakuri

"Siddiƙa ki cigaba da haƙuri Allah zai miki canji da mafi alkairi, ki cigaba da kai kukan ki gurin Allah saboda shi Allah baya barin zalinci, Kuma kamar yadda nace yau za a ɗaura miki aure da sadeeq idan anyi sallar juma'a babu fashi".

SADEEQ ne zaiyi magana Daddy ya katse sa da faɗin "zan saɓa maka sadeeq, Ko na tambaye ka ne?".

bazan iya musawa su Daddy ba, amma shin meye aure nashiga uku na, yayin da nike jin bugun zuciya ta yana dad'a 'karuwa.

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 09

Na shiga uku ni Siddiƙa Yahya ɗan ƙwambo, anya su Daddy suna ƙauna ta? nasan kaf duniya babu wacce Sadeeq ya tsana kamar ni, amman wai yau ni ce zan zama matarshi.

"Kutashi kutafi Allah yayi muku albarka". Daddy ya faɗa.

Sadeeq yariga ni tashi, saboda ni duk jikina ya mutu babu kwari.

"ji mana Sadeeq, ka kira abokanan ka na kusa a waya ka shaida musu".

Murya acan cikin maƙogaro Sadeeq ya cewa Daddy "ba sai sun shaida ba". Yana gama faɗar haka ya fice fuu.

A masallacin juma'an dake garin buruku aka ɗaura auran *SADEEQ ALIYU MAI GORO* da amaryar sa *SIDDIƘA YAHYA ƊAN KWANBO* ɗumbin taron Al'umma sun shaida ɗaurin auren duk da kasan cewar babu ango da abokanan sa, Daddy ne yayi wakilcin Siddiƙa, inda ɗaya daga cikin abokan Daddy da suka hallar ci taron, mai suna Alhaji Imran yayi wakilcin Sadeeq, auren da aka ɗaura abisa sadaki dubu tamanin, lakadan ba ajalan ba, yayin da Alhaji Imran ne ya biya sadakin.

A kwai 'yan ƙauyen Dande da dama, da suka samu halartar zuwa masallacin, saboda su gabatar da sallar juma'a, da yawan su mamaki suke saboda kowa yasan tsamar dake tsakanin Sadeeq da Siddy amma wai yau ya zama mijin ta, ko dashike daman ance idan zakayi ƙiyayya kada ka tsanan ta haka ma soyayyar, da haka taro ya watse koda Daddy ya dawo gida annemi Sadeeq anra sa kuma an kira wayar sa a kashe.

Siddi'ka kuwa tun sanda ta shiga ɗaki take raira kuka, rarrashin duniya anyi mata amma taƙi barin kukan kamar ma daɗa zuga ta suke yi, haka suka gaji da lallashin ta suka zuba mata ido, saida Daddy ya faɗawa su Inna zai shigo dasu Alhaji Imran Sannan yaje ya shigo dasu, a falon Hajiya Inna suka zauna daman su Hajiya Inna sun girka shinkafa da miya Khadija ce keta hidama da baƙin Daddy Sai da suka ci suka sha sannan Inna tazo suka gaisa, gami da yi mata Allah ya sanya alkairi, anan Daddy yayi mata sallama yace su zasu wuce Abuja dan a can jirgin su zai tashi zuwa lagos.

"To bari na kira maka Aisha ɗin ko". Inna ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa.

cikin sosa kai Daddy yace "ai na riga na sallame su, suma nan bada jimawa ba zasu wuce" mamaki ne yakama Inna saboda ita dai bataga sanda ƙarami yayi magana da Aisha ba, Hajiya Dady ya kira sunan ta "da mai sunan manya zasu tafi nayi maganar yar aikin za a nemu miki nanda kwana biyu".

"Wace yar aiki! ƙarami duk yaran dake cikin ƙauyen Dande basu isa ba har sai an nemo wata, ai ko Ladiyo ƙawar Siddiƙa na yiwa iyayen ta magana tunda yarinyar ta iya aiki, bata da ƙinji irin na Siddeqan baza su ki ba, sai ta dunga zuwa tana tayani ɗan wanke wanke da shara tama dunga ɗebe min kewar siddy ɗin, sai idan wata ya kare ka dunga yi mata ɗan ihsani".

"babu damuwa" Daddy yace yana mai ciro kuɗi daga aljihun sa masu tarin yawa, 'yan dubu dubu ya miƙa mata

"ƙarami kuɗin nan sunyi yawa, na wancen watan ma daka bani suna nan ban taba suba saboda duk abinda nike so akwai a gidan, da ka barshi kawai a gurin ka Allah yama albarka".

Hannun ta Daddy ya kamo yasa ka yan bandir ɗin 1000 guda biyu "haba hajiya ki karba koda sadaka ne kinayi dasu idan ki ka ga mai buka ta".

Albarka taita sanya mai, tanayi mai addu'ar Allah yatsare, ya kare,

"Ina mai sunan manyan take ne Hajiya?". Daddy ya tambaya

"Ai tun sanda ka fita ta shiga ɗaki tana ta faman rusa kuka, gajiya mukai da lallashi muka kyale ta".

"Wani ɗakin?".

"Na can karshe". Ta bashi amsa

Tashi yayi ya cewa abokan sa "minti biyar".

A kan gado ya same ni kwance nayi rufda ciki.

Siddiƙa Daddy ya kira suna na cikin dakusashshiyar murya, na amsa da "na'am Daddy ".

"Inaso kisan duk abinda haƙuri bai ba bawa ba a rayuwa ba, to rashin sa ma ba zai ba da ba, kuma wannan shine burin mahaifiyar ki tin sanda aka haife ki tace "idan Allah ya raya ki ɗan ta Sadeeq shine mijin ki ko bayan baran ta mu cika burin ta, A halin yanzu bamu san awani hali Amina maman ki take ciki ba, zai iya yuyuwa tana nan a raye nesa damu, zai kuma iya yuyuwa Allah ya ɗauki ranta, amma muna nan muna addu'a idan har Amina tana a raye Allah ya bayyana mana ita, nayi hakanne a yanzu saboda bani da tabbacin zan ƙara wasu shekarun nan gaba, nasan ko bayan babu raina na cikawa kanwa ta burin ta za tayi alfahari dani, kiyi mana biyayya amatsayin mu na iyayen ki bazamu taba cutar da ke ba zakiga ribar abun nan gaba".

Duk maganar da Daddy yayi na kasa ɗago kaina, Ko motsin kirki na kasa ina nan a yadda ya shigo ya sameni, shirun da naji ne, yasa naji ajiki na ya fita daga ɗakin, kaina na ɗago ina ƙarewa ɗakin kallo Bansan mai nike nazari ba amma inajin kamar raina zai fita.

Umar ne yashigo hannun sa ɗauke da kular abinci har kan gadon ya hau yace "aunty Siddy please kada kicemin a a don soyayyar da kikewa goggo Amina ki tashi kici abincin nan, nasan dai kina mutuƙar santa kuma duk 'yar da aka ce tayi abu dan iya yen ta to indai tana son su za tayi".

Jin Umar ya ambaci mahaifiya ta na tashi zaune, saboda babu 'yar da zataƙi mamar ta " to mi ƙomin kular". Na faɗa murya a can ciki.

Koda na buɗe shinkafa ce da miya har da nama a ciki, cokali nasa na fara cin abincin amma kwata kwata banjin daɗin shi, hasali ma ji nike kamar ina cin magani.

"Umar wai haka abincin nan yake". Na tambaye sa

"Me yayi?"

"Naga kan infara ci yana ta zuba ƙamshi, yanzu kuma da nike ci wallahi ji nayi kamar inacin magani".

Kallo na yai cikin ido yace "aunty siddy inaga bakin ki ne domin kowa ya yaba girkin nan yadda yake da kamshi haka yake da daɗi abaki ma".

"To iya magana". Na faɗa ina tura masa kular abincin.

"Kaddai har kin ƙoshi?". Yace yana kallo na

"Na ƙoshi mana tashi kasamomin ruwa".

"To" yace ya fice daga ɗakin, jim kaɗan sai gashi da ruwa a cup

yace "Momy" tace "kiyi wanka yanzu gata nan zuwa".

"To". nace

dama akwai bayi a ɗakin, amma tsabar neman rigama yasa bana shiga, kuma da sabo dan munriga munsa ba da bayin tsakar gida tun kafin a maida mana gidan mu ginin zamani.

Yaukam ciki na shiga wanda nike tsokanar ko sunan sa ma bana son inji ankira min.

Ban wani daɗe ba a wankan na fito, kaya na tarar abakin gadon da alamar sababbi ne harda bra da fnt.

Ina cikin mamaki saiga Khadija ta shigo fes da ita cikin wata tsaleliyar atamfa "cikin zolaya tace min amarsu har yanzu baki shirya ba Koda yake daman shirin amare ance yana da daɗe wa, sai kiyi kishir ya dan ke kaɗai muke jira".

a kwati na na nufa saboda na ɗauko kayan da zan saka,

da mamaki Khadija tace "Siddiƙa baga kayan ki nan ba akan gado, da Momy tace su zaki saka".

Hau shin kowa nake ji cikin masifa nace wa Khadija "naji to sai ki ban guri".

Sai da ta ƙyalƙyale da dariya kana tace "haba amaryar mu naji ance, ba'a san a ɓatawa amarya rai, musamman ranar ɗaurin auren ta, dan haka na barki lafiya, idan ni baki buɗe min ba zaki buɗe ma yayana".

Khadija tagirme ni da 2 years nasan ba zata rasa sanin abinda ainihin aure ya ƙunsa ba, tunda ita abirni take kuma tana zuwa makaran ta, saɓanin ni da nike yawan gaɗa a dan dali.

Tana fita na rufo ƙofar, shirya nai tsaf, sannan na zauna a bakin gado, ina ta zubaba ƙamshi, da alamar kan a kawo kayan sai da aka feshesu da turaruka masu ɗan banzan ƙamshi da tsada.

buga ƙofar naji a nayi koda na buɗe Umar ne hannun sa ɗauke da jaka da takalmi da gyale, "ungo ki sanya, Momy tace idan shirya ki fito mu tafi".

Karɓa nayi takalmin irin mai tsinin nan ne, Allah na gani ban iya tafiya da shi ba, amma hakan nan na sanya, jakar tanada yar girma kalar dai ta amare,a kafaɗa na rataya ta, gyalan ko ahannu na riƙe sa, saboda ban saba sawa ba, ai kuwa na soma tafiya.

Umar sai dariya yake min wai ahannu zan rike jakar, ba ratayawa zanyi ba, ko takan sa banbi na, danni yanzu haushin kowa nike ji.

A gaskiya ina son kwalliya a rayuwa ta, tafiya nike ina taku ɗaiɗai, duk da ban iya tafiya da takalmin ba zuwa zuwa ina turguɗewa Amman hakan bai hana ni yin yanga ba.

Afalo nasami su Momy duk sun shirya

"Momy wai ina zamu haka?". Na faɗi haka sanda nike zama kusa da Inna.

"Abuja". Momy ta bani amsa

Zaro ido na nayi nace "Abuja kuma

1 Comments On NI DA YAYA SADEEQ
avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment