Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Tace "to ya jikin naki?" nace Inna da ɗan sauƙi, amma na kasa bacci, dana rufe ido sai na dunga ganin kamar zai zo ya shaƙeni, saboda yace saiya kasheni".

Inna na salati tace"yanzu Garban ne yace saiya kashe ki!?". Eh Inna shi fa, aiba 'karamin mugu bane". Naƙare maganar ina yin hanyar ban ɓaki. Na bar Inna da mamaki.

Banɗaki nashiga nayo fitsari, na fito nazau na a kan kujera, nafara alwala kenan saiga Yaya Sadeeq nan, nayi kamar ban ganshi ba, na cigaba da yin Alwala ta, ta gaba na yazo ya wuce, bayan shi nabi da kallo ina Murmushi, a cikin zuciya ta nace "zaka bawa yan garin ku labari, zaka san kayi da 'yar halak".

Banɗaki yashiga yajima aciki, can saiga sa ya fito, a lokacin nagama Alwala ta amma ban tashi a gurin ba,

Tashi nayi na koma ɗan nesa da inda ya tsugunna, Alwala yafara, ganin ya manta beyi kus kuran baki ba naji sanyi a raina, ɗaki na koma na tsaya a bakin hundo, ina kallon sa.

yana wanke fuska ne naga ya mike kamar wanda aka tsungula gabansa yakama yana murzawa🤣 bansan sanda daria ya kwace minba can kuma yafara kifta ido se yanzu yake tunani tabbas yaji ruwan wani iri lokacin dayeke shakar hanci, abinda yasa baiyi wani tunani ba yaga butar sa ce shi kaɗai babu wanda yake amfani da ita, sosai yake murza idonsa atishawa na biyo baya haka yaita fama 💃 ɗaya hannun rike da gaban sa yana murzawa 🤣.

Dariya nike ina tsalle abin nema ya samu, sosai Yah Sadeeq yazama karamin mahaukaci gashi har an shiga masallaci amma shi ko alwalar be samu ya gama ba.

Sosai abin ke damun sa musamman gabansa yafi sosa gurin, a haka Momy tafito ta same sa, watsi tayi dashi kamar bata ganshi ba, jin motsin da yayi ne yasa ya ɗan buɗe idon sa, saboda yaga waye, wata a zaba ce ta ƙara shigar masa ido, har saida ya saki 'yar ƙara, tsaki Momy taja tagama abinda za tayi nan tabar sa tanai masa kallon mahaukaci. 🤣

Khadija Khadija yah Sadeeq ne ke ƙwala mata kira, barci take yi, ganin yana kiran ta nayi saurin zuwa bakin gadon ina dukan ta,da magagin bacci a idon ta "lafiya?". Tace min 'yar dariya nayi nace "yah Sadeeq ke kiran ki". tashi tayi zaune tana zaro ido kamar ba me magagin bacci ba "yana ina?". tace min "tsakar gida". na bata amsa

Nace "amma fa kiyi a hankali don naga kamar yasamu taɓin hankali"

Jin ya cigaba da ƙwala mata kira yasa ta faɗuwar gaba, babu shiri ta sakko daga kan godon, tayo waje, yadda taga yaya sadeeq ɗin a tsakar gida ba ƙaramar kunya yabata ba, gani Yaya tafaɗa sanda ta ƙarasa gunsa.

"Ɗauko bokiti a ɗaki na ki zuba min ruwan wanka, ki kai min ban ɗaki". ya faɗi haka.

Da "To" tabi shi kamar yadda ya umarceta haka tayi, a binda khadija bata sani ba ina laɓe lungun bayi tana aje ruwan nazuba mai karara nai fitowa ta, tsaye na ganta gurin tana cemai "yaya na kai maka ruwan".

"Kama hannu na to" yace mata, hannun na sa takama har bayi ta kaisa, sannan tafito. Har yanzu Idanun sa a rufe suke, cire jallabiyar jikin sa yayi, sannan ya laluba yaji babu kwandon soson wanka, kiran sunan Khadija yafarayi nikuwa daman ina kusa da bayin, khadija kuwa tayi alwala ta tafi ɗaki sallah, "kawo min sabulu". Yace

Daman Yah sadeeq bai wanka da so so ko kadan sai sabulu kawai, Murmushi nayi naje na dauko mai sabulu wanda na badeshi da zallan tarugun dana ga Inna ta daka sa ta shanya asama jiya.

hhhmmmm nace "ai wallahi tunda ka taɓani sai kasan kayi da 'ya, taka kujera nayi naje fa mai sabuln cikin bayi.

Komawa gefe nayi na zauna inajin raina fes banida wata damuwa.

Har gari yafara wayewa babu sadeeq babu labarin shi nikuma naƙi tashi, domin ko sallah ma banyi ba.

Ya sadeeq kuwa yazama abin tausayi cikin bayi yarasa wannan wani irin bala'i ne, shida yayi wanka domin yasamu sauƙi amma sai a kasin haka, susar jikinsa yake iya ƙarfin sa duk da idan yasosa yanajin wani mugun raɗaɗi a jinkin sa, amma bashi da wani zabin da yawuce susar.

har 7 am be fito ba, Inna ce zata shiga bayin na kalle ta nace "Inna fa da mutum".

"Waye?" tace min "yah Sadiq ne" na bata amsa.

Inna tace "me yake yi agidan har yanzu da bai fita gurin aiki ba, naga da an idar da sallar asuba yake tafiya".

Nace "to Inna kika sani ko anyi musu canji ne kinsan ana canza su ai".

"Haka ne" Inna tace, ɗan matsawa nayi kusa da ita, sannan nace "Inna amma fa yau yah Sadeeq wallahi kamar mahaukaci, domin tun asuba yake abayin nan, kafin yashiga ya daɗe anan tsakar gida yanayin wasu a bubuwa masu kama da na mahaukata". Zaro ido inna tayi
na ɗaga mata gira, nace idan baki yarda ba kuma, Ki je ki tambayi Khadija ko Momy saboda dukan su sun ganshi a cikin yanayin.

♾️♾️♾️♾️♾️
Nagaji da typing atara gobe in Allah ya kaimu domin jin yadda za a kwashe tsakanin Sidda'ka da sadeeq kucigaba da bibiyata nikuma zancigaba da nishadantar daku
♾️♾️♾️♾️♾️

💋💋💋💋💋💋💋
ʏᴀ ᴀʟʟᴀʜ ɪɴᴀ ʀᴏᴋᴏɴᴋᴀ ᴋᴀʏɪᴡᴀ ᴍɪᴊɪɴᴀ ᴀʀᴢɪᴋɪ ᴅᴀᴋᴀ ᴄɪᴋɪɴ ᴀʀᴢɪᴋɪɴ ᴀɴɴᴀʙɪ ᴍᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ sᴀᴡ ᴋᴀᴡᴀᴅᴀ ᴛᴀsᴀ ᴅᴀɢᴀ ᴄɪᴋɪɴ ᴡᴀᴅᴀᴛᴀʀ sᴀʏʏɪᴅɪɴᴀ ʀᴀsᴜʟᴜʟʟᴀʜɪ sᴡᴀ ᴋᴀʜᴀɴᴀ ᴍɪᴊɪɴᴀ ʜᴀssᴀᴅᴀ ᴋᴀʀ ʏᴀʏɪ ᴋᴀʀ ᴀʏɪ ᴍɪsʜɪ ʏᴀ ᴀʟʟᴀʜ ᴋᴀ ᴋᴀʀᴇᴍɪɴ ᴍʏ ᴅᴀɢᴀ ᴍᴜɢᴜɴ ᴊɪ ᴅᴀ ᴍᴜɢᴜɴ ɢᴀɴɪ sʜᴀʀʀɪɴ ᴍᴜᴛᴜᴍ ᴅᴀ ᴀʟᴊᴀɴ ᴅᴀ ᴅᴜᴋ ᴡᴀɴɪ ᴍᴇ sʜᴀʀʀɪ
💋💋💋💋💋💋💋

NI DA YAYA SADEEQ
                     

Page 06

بسم الله الرحمن الرحيم

Jinjina kai Inna tayi, sannan ta nufi hanyar ɗakin da Momy take, ƙwanƙwasa musu kofa tai, ta ɗan jima a bakin ƙofar, kafin Momy ta buɗe ta fito, "lah inna ke ce? Bata jira amsar ta ba, ta ɗora da ina kwana hajiya".

cikin sakin fuska Inna ta amsawa surukar ta, kana tace ya baƙun ta?".

"Lafiya lau". Momy ta bata amsa.

"To alhamdu lillah".
A cewar Inna, ta ɗora da cewa "ki yaƙuri na tashe ki kina tsaka da bacci".

"Ayyah babu komai Inna" cewar Momy.

Inna ta cigaba da cewa "daman Garba ne wai a ban ɗaki, tun asuba gashi har yanzu bai fito ba, Siddiƙa ma tace yau kamar gamo yayi, saboda yana tayin wasu abubuwa irin na taɓaɓɓu, shine nace bari na tada ki muje bayin mugani ko lafiya".

Momy tace "Hajiya Inna badon karkice na raina ki ba da bazani ba tunda shi bayajin magana".

Inna tace "Haƙuri zaki Aisha muje mugani ko lafiya, kinga da ya idar da  sallar asuba yake tafiya gurin aiki, amma yau shuru".

"To". Momy tace badon ranta yaso ba, tabi inna ban ɗakin.

Koda su Momy suka ƙarasa bakin bayin sunan shi Inna takira "Garba Garba". kamar babu kowa a ciki, saboda bai amsa ba, saida Momy tace "Sadeeq wai lafiyar ka?".

Da wata iriyar  murya yace "wallahi Momy nima ban sani ba".

Tace "au daman kana jin Hajiya na kiran ka kayi shuru, saboda ka raina mutane, ai sai ka fito ka bawa mutane guri, saboda gari ya waye".

Yace "Momy bazan iya fitowa ba".

"Saboda me?". Ta tambaya

Momy wlh yau Ban san me ke shirin faruwa dani ba, ko nayi gamo ne tun nafito sallar asuba na haɗu da bala'i ko sallar ma banyi ba". 🤣

Salati suka hauyi Inna natafa hannu kace "baka yi sallah ba, tom wai me kake yi a cikin bayin ne haka?". Cewar inna

Cikin jin zafin tambayar da Inna tayi mai sadeeq yace "Wai baki ji nace ina cikin bala'i bane, amma kike sake tamba ta".

Momy ce ta daka mai tsawa "rufe min baki anan gurin ko na ci maka mutun ci, kuma kafito kabawa mutane guri suna son shiga bayan gida".

Sadeeq yace "Amma Momy...".

Katse shi tayi da "ko baka ji abinda nace maka bane".

"Naji". Ya faɗa a ta ƙaice,

Ɗan matsawa suka yi nesa da bayan gidan.

Ni kuwa da tun tuni nike zaman jiran fitowar sa, da naji Momy tace "ya fito". Sai Na ƙara gyara zama na a kan kurer tsakar gida.

Saida ya ɗauki tsayin minti biyar kafin ya cire sakatar, ya buɗe ya fito, babu ko riga a  jikin sa, sai ɗan gajeran wando, basu Inna kaɗai ba hatta ni da niyi  zaman jiran fitowar sa, saida na tashi tsaye saboda yadda yayi wani iri, kamar ba yaya sadeeq ɗan gayu da ƙwalisa ba, yayi wani wuji-wuji dashi, idanuwan sa sunyi jawur  se mutsuka su yake, ga jikin sa duk ya kar-karce sa da farce, harda shedan jini, ba ƙaramin ciwuka yajiwa jikin sa  saboda susa ba, hatta da fiskar sa bai bari ba akwai alamun karta, duk ya faɗa fuskar nan yayi zuru zuru.

Mamaki ne kwance a kan fusko kin su Momy.

Momy tace "Wai sadeeq me ke damun ka haka kamar me borin jini?".

"Momy nima bansani ba". Ya bata amsa.

Yanzu yaji sauƙin ƙaiƙayin da jikin sa ke yi, sai dai raɗaɗin da fatar jikin sa ke mai, da bala'in zugi.

"To ai saika je ko jallabiya kasa mutafi asbiti". Inji Inna.

"A a Inna ba sai kunje ba don asbitin gari zani kuma da nisa ku zauna a gida". Ya faɗa yana tafiya.

ta kusa dani yazo wucewa, saida muka yi  ido huɗu dashi na kwashe da dariya🤣

Kallan tsana yayi min, sannan ya nufoni, dagudu na miƙe, nanu fi bayan Momy ina haki, biyoni yayi shima,  da hannu Momy ta da katar dashi sannan tace "amma walahi sadeeq kaji kunya kanwar kanwar ka itace abokiyar yinka, ba dole ta raina ka ba,Wallahi ka bada maza wuce kabani guri, kamin kiƙam a gaba kamar wani soja, Ko wannan iftila'in daka faɗa be isheka ishara karabu da yarinyar mutane ba". Ta ƙare tana nuna mai hanya da hannu.

Badon yaso ba saidan yabi umarnin mahaifiyar sa.

Sake haɗa ido muka yi dashi, nayi masa gwalo ina ƙara yin dariya ciki ciki😄

Yace "Zan kamaki  yarinya wallahi zakiyi bayani".

Inna tace"Ai gashinan alhakin tane wannan abin da ke faruwa da kai, saboda Allah ba azzalimi ne ba sai dai bawa ya zalinci kansa".

"Kwarai ma kuwa".  Momy tace

Jikin sa babu ƙwari  ya wuce mu, tashi nayi nima nakoma ɗaki, saboda na gabatar da sallar a subahi, sai a lokacin nayi sallar takwas saura, ina idar wa ko kan sallaya ban sauka ba nahau rawa da juyi, saboda na rama a binda sadeeq yayi min, gado na koma saboda yau bazan je 'yar kasuwa yin tsokanar safe ba bacci zan koma

♾️♾️♾️♾️♾️
Abangaren sadeeq kuwa koda yaje asbiti, kulawa ta musamman suke bashi saboda asbitin su na 'yan sanda yaje, har gado aka bashi sannan aka saka mai ledar ƙarin ruwa, saboda yana bukatar ruwa ajikin sa.

Harda allurar bacci a kamai saboda ya sami hutu.

♾️♾️♾️♾️♾️

Koda na farka daka bacci ƙarfe shaɗaya saura11:00am, naji dadin baccin sosai domin ya ragemin damuwa.

Kamar yadda nasaba idan natashi bacci miƙa nayi  babu ko salati, na sauka daga kan gadon, na ɗauki brush ɗina na fito tsakar gida nayi, sannan nanufi falon hajiya, acan na iske su Khadija suna cin waina da miya.

zama nayi kusa da Momy nace "ina kwana Momy".

"Lafiya lau". Tace min "kin tashi lafiya?".

Nace "eh Momy lafiya lau". Saboda ni bana son doguwar gaisuwa.

Tace "ba inda ke miki ciwo?".

kai na ɗaga mata
"madallah" ta ce masha Allah haka ake so.

Inna na kallah naga ta tasa kwaɗan zogale da kuli a gaban ta sai kaiwa baka takeyi,  ɗan Murmushi na sakar mata,  ita ma ta maido min.

Kana na gyara zama, na saka hannu a kular wainar su Khadija, ina ci ina lumshe ido saboda daɗi, Nace  "Inn wai wannan wainar wane gida ce".

Tace "ta gidan su fulera ce matar ɗan tsoho".

"Haba koda naji". Nafaɗi haka yayin da nike kai lomar waina a baki na.

"Kice kinyi santi" Murmushi nayi kawai na cigaba da ai kawa cikina.

Umar ma cewa "yayi ni rabon da naci waina me daɗin wannan wallahi na manta".

"Umar duk santin ne haka". Inji Khadija.

Yace "ai kokema kinyi tunda naga kunnen ki ɗaya sai rawa yake".

Kowa a ɗakin saida ya dara

♾️♾️♾️♾️♾️

Bayan Sadeeq ya farko daga nannauyan baccin da ya ɗauke sa,  jikin sa babu kwari sam, a za filo yai a bayansa ya jingina, yana jin gabaɗaya jikin sa na mai ciwo, ga wata yunwa da ke ad'dabar cikin sa, da kasala.

Likatan ne yazo ya zauna agaban shi dayike a bokin sa ne kuma shima ɗan sanda ne, yace "wai sadeeq dame kai amfani ne?".

Ɗan shiru yayi kafin yace "nidai a binda nasani natashi da a suba lafiya ta ƙalau, amma da bayan na ɗauki buta ta, naje bayi na dowo nafara jin yanayi na yana sauyawa, koda na fara alwala ko fiska ban gama wan kewa ba, tsarkin da nayi yafara damu na,
Sai nasa aka kai min ruwan wanka, to na ƙarƙare maka zance, daka zuba wannan ruwan a jikina kiɗan ya sauya salo, sai azabar ta ƙaru bayan na sa a miƙo min sabulun wanka, ba ba nasha wuya fa  sosoi, tun asuba nike a cikin bayi nine har ƙarfe takwas saura, wannan raunin duk ni najiwa kaina, saboda ƙyaiƙayin da jikina ke min, idan ban sosa ba bana jin daɗi".

Dariya sosai Dr Farooq yake yi, Sadeeq yace "dr banason iskanci fa, nifa ban baka labari don kayi min dariya  ba, sai dan kayi  aikin ka".

Dr Farooq yace "ba ba wallahi labarin naka ne gunin ban dariya, sai kace a cikin shirin film".

Duka Sadeeq yakai wa Dr Farooq ɗin, amma sai ya kauce yana faɗin "shege ka samu kenan, ɗazun kamar wani lagwani kana ta numfar fashi kamar baza ka kai aniji ma ba".

Saukowa Sadeeq yayi daga kan gadon, Dr Farooq yai saurin miƙewa, ɗakin suka fara zagayewa, Farooq ɗin yaƙi barin sadeeq ya kama sa, dan kansa Sadeeq ɗin da ya gaji ya haƙura, ya janyo kujera ya zauna yana maida numfashi, ruwan sanyi Dr Farooq ya ɗauko a ciki firiji ya miƙo masa, yana faɗin "maganin ɗan iska kenan gobe ma ka ƙara".

Sadeeq ɗin amsa kawai yayi be kula sa ba
♾️♾️♾️♾️♾️♾️👆

𝑑𝑎𝑛 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑟𝑒𝑎𝑑𝑒𝑟𝑠 𝑘𝑢𝑦𝑎 ha𝑘𝑢𝑟𝑖 𝑎𝑏𝑖𝑛𝑑𝑎 𝑦𝑎 𝑠𝑎𝑚𝑢 𝑦𝑎𝑢 𝑘𝑒𝑛𝑎𝑛 𝑏𝑎𝑏𝑢 𝑦𝑎𝑤𝑎


NI DA YAYA SADEEQ
                      

بسم الله الرحمن الرحيم

             Chapter 07

Ya ansa gorar ruwan ya fara  sha, saida ya shanye ruwan tas sannan yace "malam kayi min bayanin matsala ta nasan dai ba waccar matsalar bace".

"Eh ba ita bace" Farooq ya bashi amsa

"Amma a bisa binciken danayi, ya nuna kayi amfani da abu mai saka fatar jikin mutum ƙaiƙayi acikin ruwan da kayi amfani dashi, sannan shima wannan raɗaɗin da kake ji kayi amfani da abu mafi zafi ajikin fata, shiya sa yake maka wannan raɗaɗin". Dr Farooq ne yayi wannan bayanin.

Shuru Sadeeq yay kamar meyin nazarin wani abu, be tuna komai ba, Dan haka ya taɓe baki yace "Nidai nasan ban saka komai cikin buta ta ba amma zanyi bincike, saboda abin da mamaki".

"Dadai yafi". Farooq ya bashi amsa ya kuma cewa "katashi muje akwai magun-gunan da zan rubuta maka zasu temaka sosai, wajen  rage maka raɗaɗin da kake ji".

♾️♾️♾️♾️♾️

Ina zauna a kan kujera a tsakar gidan mu, ina dakan kayan miya yamma ne lilis, saiga Ladiyo kawata nan ta shigo jiki duk kwata, tun daka nesa nike ɗaga mata hannu, saboda kada ta ƙaraso inda nake, bazan iya jure shakar warin kwatar da ke jikin ta ba, ida nuwan ta  jawur dasu, alamun taci kuka ta ƙoshi.

Saida nayi dariya mai isa ta sannan nace " ke Ladiyo garin ya kikayi wanka da kwata a jikin ki kamar sabon shiga hauka?".

Takaici na ne ya ishi Ladiyo na dariyar da nike mata, ga tambayar rainin hankali dana jefe ta dashi.

Cikin shash-sheƙar kuka take cemin "Ummata ce ta aike ni na kai mata niƙa, bayan nakai annuƙo, akan hanyata ta dawo wa gida na haɗu da su Habibalo, itada Larai sukai ta zagi na, naƙi kula su, nayi ƙoƙarin ganin na cigaba da tafiya ta, amma suka hanani wuce wa, wai sai nayi dambe. can saiga Atinen Malam Bala nan Shine tace "wa na kama wai jiya ni dake munwa ƙanwar ta duka, haƙuri na fara bata, amma suka samin dariya, wai wallahi sai sun rama wa  ƙanwarsu dukan da da kika yi mata, shine suka haɗu sukai  min dukan tsiya, sannan suka jefani a cikin kwata". Ta ƙarasa maganar hawaye sabbi suna zubo mata ta ciga ba da faɗin "basu tsaya iya nan ba saida Suka zubar da ƙullun wainar da na markaɗo".

Wata muguwar dariya ce ta ƙwace min ban san da zuwan ta ba, saida nayi mai isa ta.

Sannan nace mata "wallahi Ladiyo ke sakarya ce ki ka tsaya kamar kayan wanki suka jibgeki,
🤣Baki iya koda mintsilun su ba, Hhmm ai da ni ce koda ya ƙushi da cizo saina rama, kindai san halina, ni yanzu da ki kazo ki ka faɗa min inyi miki me? ai da zuwa gida ma ki kayi  Umman ki ta miki dukan da zata miki da tuni ya wu ce, amma a nan kina ƙarawa kanki laifi ne a gun umman ki, kuma kin santa da jaraba".

Wani sabon kuka Ladiyo ta kuma  fashe wa dashi,

Ni kuwa sai ƙyalƙyala dariya nikeyi harda rike ciki abin nema ya samu.

Dundun da naji an ɗuma min a bayana ne ya dawo da ni haiyaci na, Inna ce tsaye tana huci.

Tsuke baki na nayi nace "Inna kin wai me nayi miki ne?".

Cikin jaraba irin ta tsofaffi Inna tace "ja ira ba ke kika ja mata du kan ba, amma tana faɗa miki kina yi mata dariya".

Ta juya ta kalli inda Ladiyo take tace "kema ai da naki laifin, Ladiyo kina san kiyi tsokana amma ba kida ƙarfi, kuma tsokana ta mara tsoro ce, tunda ba zaki iya cire tsoro ba, sai kidena biye mata, idan ba haka ba wataran karyaki za ai".

Jin Inna tace za'a ɓalla Ladiyo yasa na ƙara kwashewa da dariya.

Cikin takaici na Ladiyo tace "ke ai sunce idan suka kama ki ɓaɓɓalla ki za suyi".

Wani ƙaton a shar nayi, Inna dake kusa dani tace "A'uzu billah".

Naci gaba da cewa "ke ma kin sani kaf ƙauyen nan, na ga gari uban kowa, na wuce ayi min harara bare zagi, kinga ina za aje ga duka, ke dai da kike sakarya sai kita tsayawa tunda sun gano lagwanki".

Momy dake jinmu tunsanda Ladiyo ta shigo gidan, tazo ta miƙo min kuɗi 1000k tace "ungo miƙa mata ta kaiwa  mamar ta".

Saida na amsa kuɗin sannan nace "wallahi Momy dan  kece da bazan iya zuwa inda take ba, ba kuji yadda gidan nanan yaɗau ka ba?".

Duka Inna taƙara kai min a karo na biyu, amma sai na kauce ina faɗin "ba zaki ƙarasa ni tun kafin lokaci na yayi ba, da saura na wallahi".

"Shaƙiyiya har Talle ne zai yiwa audi gori?".

"Tab wai me kike nufi?". Nace da Inna "ni kika yadawa magana ko wa? Yo ai ko ke ba zaki nuna min wanka ba bare Ladiyo".
Na ƙarisa faɗa ina murguɗa baki.

Hanci na na toshe da dan kwali na, sannan na nufi gurin da Ladiyo take a tsaye, nesa kaɗan da ita natsaya nace "miƙo hannunki" miƙo hannun nata tayi, na saka mata kuɗin nace "yau Allah ya ƙwace ki wajen Umman ki, da kinci duka biyu".

Godia Ladiyo tayi wa Momy sosai, zata wuce nace mata "mu haɗu a yar kasuwa anjima". da "Tom" tabani amsa

Inna kuwa sai mita take wai Ladiyo bata da wayau, Momy na bata haƙuri tana cewa "sha'anin yara kenan sai  haƙuri".

♾️♾️♾️♾️♾️

A bangaren sadeeq kuwa yana dawowa  gida ana kiran sallar magriba, ɗakin sa yabuɗe ya ajiye ledar maganin da Dr  Farooq ya rubuta mai shi kuma ya siyo, saboda ba suda shi a abitin su kuma yace "zai rage masa zafin raɗaɗin da kaye ji".

  Fitowa yayi daga gidan, yanufi masallaci, anan yayi alwala aka gabatar da sallar magriba da shi, bayan an idar mutane sun fara raguwa ya miƙe, saboda ya biya bashin sallolin da ake binsa, ai kuwa ya fara jero sallolin saida ya idar dasu  kaf, ashe a kwai wani mutum da ya lura da shi, tun sanda yafara sallar, ba ƙaramin mamaki yayi ba da yaga matashi me jini ajika irin sadeeq ya tsaya yana haɗa sallah. Beyi ƙasa a gwuiwa ba, yaje ya miƙa masa hannu saka yi musabaha, kana yace "yallaɓai Allah yasa dai lafiya naga sai salloli kake jerowa kuma ga dukkan alamun ba nafila bace farrila ce, saboda tun sanda ka fara nike lura da kai".

shiru sadeeq  yayi, saida ya gama ƙarewa mutumin kallo tsaf dattijone dan gashin kansa ma a kwai fur-fura, gwauran numfashi ya sauke, saboda bai san ya dattijan zai ɗauki lamarin ba, amma zaifaɗa mai gaskiya tunda shi ya buƙaci jin dalili.

Bayani sadeeq ya shiga yimai dallah dallah, a kayi sa'a dattijan ya fahimce sa, Fatan samun lafiya yayi masa, daga bisani ya miƙa masa hannu suka kuma yin sallama dattijan ya tafi

♾️♾️♾️♾️♾️

Siddeeƙa kuwa bata samu fita daka gida ba sai bayan sallar Isha'i, koda Allah yabani sa'a nafita daga gida, ina tafe a   hanya ina tsokanar duk Wanda naci karo dashi, raina fes saboda Izuwa yanzu nayi tsokana har ba a dadi, nafi tare masu yin talla kuma nace "dole sai munyi dambe". Duk wanda yaƙi biye min, sai na zubar masa da abin tallar na ruga da gudu ina dariya.

Hankali na kwance nike tsokana ta, yanzu haka wata me gyaɗa na tare, nayi nayi da ita muyi dambe amma taƙi ta ce "ba abinda ya futo da Ita kenan ba". Saida nayi shewa kamar ina gidan biki nace "yo ni abinda ya fito dani kenan ko kina so ko bakya so sai munyi damben nan". Na ƙarasa faɗa ina ƙoƙarin kama tiren gyadar, ban lura da kowa a gun ba ido na ya rufe, naji caraf an damƙe min hannu, koda na waigo da kaina saboda nayi masifa, sai naga yayan yarinyar ne fuskar sa a murtuke babu alamar wasa yace "yau me rabani da ke a gurin nan sai  Allah, zakici ubanki daman na daɗe ina Addu'ar irin wannan ranar, sai gashi kin kawo kanki har gida, saboda kin addabe yaran unguwa ko ina yara labarin ki suke yi, kuma gaki 'yar ƙarama bare nace jiki gareki kike tsorata su dashi".

Sai yanzu na ƙarewa layin kallo a she a ƙofar gidan su yarinyar nike.

Inada taurin kai bazan taɓa iya bashi haƙuri ba, ko da kuwa zai kashe ni, cikin ƙarfin hali nace "dalla malam ka sakeni ko nayi maka sharri".

ɗaga hannun sa kenan da zummar ya mare ni, sai yaji ance "'kara mata".

Sai da gaba na yafaɗi, saboda me muryan ko a mafar ki naji yayi magana sai na gane, bare kuma a zahiri.

Zauke hannu sa yayi, ya fasa mari na, ya maida duban sa izuwa inda yaji maganar, saiga yah Sadeeq ya bayyana cikin takun sa na isa da ƙasaita.

Har inda muke ya ƙara so  be tambayi ba'asi ba, yaciro belt ɗin wandon sa, ya cewa matashin "ungo wannan kazane ta dashi nake ga kamar zaifi shigan ta, kuma hannunka baze maka zafi ba".

A tsorace matashin  ya kalli yah Sadeeq saboda ya shaida shi kuma yasan ni kanwar sa ce.

Cikin in-inar magana matashin yace "yallaɓai nama haƙura tunda kayi magana". sai a lokacin ya sakar min hannu.

Da alamar yah sadeeq ba haka yaso ba, so yayi a daka ni, dan yabuɗe baki zaiyi magana kenan na falla da gudu ina cewa "Allah ya isa ban yafe ba ku duka ƙartan banza, masu faɗa da 'yar cikin su". 😄

Duk kansu sunji a binda nace saboda na ɗaga murya ta sosai, kuma dama haka nike so, shi dai matashin mamaki abun ya bashi, a cikin ransa yake cewa "yallaɓai guda nama wannan rashin kunyar, tabbas tunda nawa yallaɓai babu wanda bazan mawa ba".

1 Comments On NI DA YAYA SADEEQ
avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment