Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa ciki ya miƙo hannu ya janyo ni, Inna  faɗi take "kabita a hankali ba cikakkiyar lafiya gare ta ba".
Ɗauka ta yayi irin ɗaukar da a kewa jarirai, kana ya nufi asbitin,
Inna biye da mu a baya.

Da yike yah sadeeq sananne ne a gari bama iyaka kauyen mu kaɗai ba harda birni, saboda babban ɗan sanda ne.

Wata nurse ce ta  hangomu da sauri ta ƙaraso inda muke, cikin rawar jiki tace "yallaɓai cikin wancen ɗakin zaka kaita zatafi hutawa, babu mutane da yawa a cikin sa". Tafaɗa haka tana nuna mai ɗakin da yatsan ta manuniya, "alright" shine abin da kawai ya faɗa.

Ɗakin da a kace ya kai ni shine ɗakin da ake ji dashi a cikin asbitin, saboda a kwai siminti da gado guda ɗaya tak, mun tarar da mara lafiya a kan gadon  kwance, saboda ya ɗora ni aka sauke mara lafiyar gunin ban tausayi, gashi masu jinyar ta basa kusa.

"yallaɓai ɗora ta a kai". A cewar nurse ɗin data sa aka sauke mara lafiyar.

Be yi mamaki ba, saboda ya saba kawo ni asbitin, kuma irin haka ne take faruwa.

Ɗora ni yayi akan godon, kana ya fice abin sa.

Da sauri Nurse ɗin tabi bayan shi tare da wa'inda suka cicciɓi marar lafiyar da aka sauke a kan gado.

Bai jima ba saiga shi ya dawo tare da  wata nurse, hannun  ta rike da wani ɗan karamin farantin silba, sai kyalli yake, kan wani teburi na katako ta ijiye, sannan ta matso kusa dani, ta ɗora hannun ta a kan wuya na, "a kwai zafi a jikin ta yallaɓai, zazzaɓi ne ya kamata". Nurse tafaɗa tana duban shi, kin tanka mata yai, dan kuwa kunnan uwar shegu yai mata.

"Meke damun ki?". Nurse ta tambaye ni,

"Duka jiki na ciwo yake min, amma kirji na yafimin ciwo".

Fuska ta ta kalla da kyau sai taga shatun hannu tace "kamar dukan ki akayi ko, domin shaidar hannu ya bayyana a kan kuncin ki raɗa-raɗa".

Na buɗe baki zanyi  magana kenan yah sadeeq ya wurga min harara.

Kallon nurse ɗin yai  ya ce "ke maye aikin ki?".

"Duba mara lafiya". Ta faɗa bakin ta na rawa.

saida ya ɗaure fuskar sa babu alamun wasa a tat-tare da shi yace "to kiyi aikin ki, dan wannan bai shafeki ba, kiyi abinda ya dace".

Cikin in-ina ta ce "to ranka shidaɗe na tambaya ne saboda nasan irin maganin daya dace na bata, amma kaya ƙuri naga kamar ranka ya ɓaci".

Be kuma bi ta kanta ba yafi ce daka ɗakin, tasha fama dani sosai kamin na bari tasoka min allurar da za ai ƙarin ruwa, shima saboda naga yah sadeeq ya dawo ɗakin ne.

Banfi minti 25 da samin ruwan ba, baccin wahala ya ɗauke ni, koda na farka bayan wasu awanni da bazu wuce 2 ba, sai naga momy zaune a kan wata farar kujera, irin tarobar nan, da alama daka gida aka zo da kujerar ma, mamakin ganin ta ne ya kamani,  miƙewa nai zaune na jingina filo a baya na, kallon ta nikeyi ina muts-tsuka idanu, ban gama mamaki ba saida naga  Khadija, tashigo ɗakin hannun ta ɗauke da kular abinci, da kwano, Umar, na biye da ita a baya.

tashi Momi tayi tamatso da kujerar ta kusa da gado na ta zauna, tana kama hannu na "sannu kinji Allah zai saka miki ya jikin naki?". Momy ta tambayeni muryan ta ɗauke da damuwa.

Madadin na bata amsa sai na jefa mata tambaya "wai momy yaushe kuka zo? kuma waya faɗa muku bani da lafiya? Inna dai bata da waya yah sadeeq kuwa nasan ko mutuwa nayi bazai kira ku ya faɗa ba".

Ta ce "Babu wanda ya faɗa mana, daka kaduna muke hutun makarantar su Khadija ne ya ƙare, shine zamu koma Abuja, nace mu biyo tanan, can gida muka fara zuwa bamu sami kowa  a ciki ba, kun bar ko ina abuɗe, hakan ne yasa naji a jiki na ba lafiya ba,  shine nakira yayan ku awaya.
Shine ya shaidamin bakida lafiya ne ya kawo ki asibiti. To a take na tambayi sunan asbitin, nan fa ya ce "asbitin Dande". 

daga haka muka yi sallama na kashe wayar.

Sanda mukazo  hajiya Inna ke bani labarin abinda yafaru tana kuka, gaskiya Sadeeƙ bai kyauta ba.

A take na kira sa a waya nayi  masa kaca-kaca, kuma nakira Daddyn ku a waya, na faɗa masa, ya ce mu zauna anan Danden  nan da kwana 2 zaizo.

Ina ƙaƙalo hawaye  nacire hajabin jiki na, nace "Momy kalla kigani fa wallahi babu abinda nayi  masa yayi min wannan dukan, kuma har da cewa kaɗan ma yai min.

Salati Momy keyi tana tafa hannaye "yanzu Sadeeƙ ne yayi miki haka?". Momy ta faɗa tana riƙe haɓar ta.

  gyaɗa kaina nayi alamar eh.

ta ce "kiyi haƙuri Daddyn ku zai zo nan da kwana biyu insha Allah, zai kuma ɗauki mummunan mataki yanda koda kuɗi a kace Sadeeƙ ya sake dukan ki bazai sake ba".

Khadija da tunda ta shigo ta aje kular hannun ta, ta sami gefan gado ta zauna, sai alokacin tace min " sannu Siddeeƙa yajikin naki da sauki dai ko?".

"Babu laifi dai zance amma wallahi na daku gurin baƙin mugun".

"Ina ke miki ciwo yanzu to?". Khadija ta kuma tambaya na.

Nace "Babu sai ɗan abinda baza'a rasa ba".

"Alhamdu lillah". Momy tace

yayin da  Umar yace "aunty Siddeeƙa yajikin naki?".

"Da sauki" itace amsar dana basa, ina miƙa mai hannu alamar yazo kusa dani, ai kuwa ba musu yakama hannun nawa, zaunar dashi a ɗayan gefen gadon nayi suka sani a tsakiya.

dayi ke lokacin da nike bacci ruwan da ake ƙara min ya ƙare nurse ɗin tazo ta cire min.

zubamin abincin Khadija tayi, tana faɗin "sister Siddeeƙa daure dan Allah kici wannan babu yawa, taliya ce fara da mai da yaji".

nace "naƙoshi fa".

da ƙyar Momy ta lallaɓani naci ɗan kaɗan, na ture kwanan.

nace "ni fa na ƙoshi Umar zo kacinye sauran".

Sai alokacin na lura babu Inna "ina Inna wai?". na tambaya ina kallon Khadija.

Ai takoma gida, driver nasa ya maida ta, nace zan zauna dake har sanda zasu sallame mu, a cewar Momy.

"to Momy mu koma  haka ai na warke". Nafada ina sauka daka kan gadon kamani khadija tai tana faɗin "wannan wani irin ciwo ne Siddeeƙa?🤔
Koda yike ke daman haka kike ba kyason asbiti".

"haba khadija ai kwata kwata natsani asbiti, zaman asbiti ai sai dole, to inba dole ba me mutum zaiyi" nabata amsa da haka.

"kinji momy kira driver ɗin kawai, Allah da gaske nike na warke".

Ta ce "bari a fara kiran likita idan tace zamu iya tafiya gida sai su baki  sallama, tunda kin matsa".

dariya ce taka mani sosai nike ƙyalƙyatawa.

"Lafiyan ki kuwa Siddeeƙa". Momy ta tambaya, cikin san sanin dalilin da yasa nike dariya.

Ina dariyar na ce "ai kece ki ka bani dariya Momy, baki karewa asibitin kallo bane halan? To wannan asbitin da ki ke gani ba a sallamar mutum,
idan aka kawo mutum yaji sauƙi kawai tafiya zai yi abun sa. Idan kaga dama ne ma sai kace musu zaka tafi, basa saida wasu magunan kirki, kuma basa wani rubuta maka koda zaka siya wani gurin idan su basu da shi, idan ma sun rubata to abu 2 ne kawai fanadol sai farasitamol".🤣na ƙarasa faɗa  ina ƙara ƙyalƙyala dariya.

Na cigaba da cewa "nifa momy wallahi a gani na duk basu san aikin su ba, gwara gwara ma Aliya. wannan taɗan iya aikin, itace ma tasamin ruwa, idan fa aka kawo mutum bata nan sunan shi sorry, ba ƙaramin jagwal-gwalo yake sha ba".

sosai khadija ke dariya tace "ai ni ban zata ma asbiti bane, domin sam baya kama da asbiti".

"'kwarai ma kuwa". Na bata amsa

Nace "kefa da a ka kawo ni wata a ka sauke a kan gadon a ka ɗora ni, nason don sunga yah Sadeeƙ ne, duk sanda ya kawo ni gado suke bani".

cikin mamaki momy tace "wata fa ki ka ce aka sauke".

"eh mana Momy" nabata amsa.

"to ina suka kaita?". Momy tayi tambayar.

Nace "wallahi Momy ban sani ba lokacin ina fama da kaina".

Cikin hanzari momy ta fara lalubar jakarta tana faɗin "da gaskiyar ki Siddieeƙa bari na kira driver yazo ya kaimu gida kamin kema a sauke mana ke, tunda Sadeeq ɗin ya tafi".

Ina dariya nace "uhm Momy da zamu shekara anan babu wanda zai sauke ni".

"saboda me? Yaya ko?". Khadija ta tambaye ni tana kallon idona.

  Nace " eh, nifa mutane har mamaki suke bani, yadda naga suna tsoran shi kamar wani mala'ika".

Momy tace "ni dai duk da haka gwara mu koma gida, ko wani asbitin na kudi a canza miki, ban yarda da wannan ba za a iya bawa mutum maganin da bashi ya dace ba".

Nace "momy nifa na ma warke babu wani asbitin da zan sake komawa".

Ɗaukar wayar ta tayi ta latsa numbar Idi driver, bugu ɗaya ya ɗauki kiran
kamar tana gabansa cikin ladabi yace "Hajiya na na sauke Inna tun ɗazun".

Ta ce "yayi kyau muma kazo ka ɗauke mu ta sami sauƙi mara lafiyar".

Ya ce "to Hajiya".
sannan takatse kiran.

Ba a fi 15 minutes ba saiga Idi driver yazo.

Da yake ɗazun har dashi aka zo yasan asbitin har ɗakin da aka kwantar dani ya shigo. ya kwashi  tarkacen da khadija tazo dasu yayi gaba.

Sannan mumu muka fito, da Aliya muka ci karo A bakin fita asbitin tana Murmushi tace "mara lafi sauki yasamu kenan?".

"Eh". Na ce

Ta ce "to ba zaku sai magani bane?".

"muna da irinsu dayawa agida" nace mata.

"To shekenan Allah ya ƙara sauƙi" ta faɗa yayin da takai duban ta ga Momy ta ce "Hajiya ya mai jiki?".

Momy tace "mai jiki ta warware ". Daga haka muka mata sallama muka fito cikin asbitin, muka shiga cikin mota Idi driver ya hau titi.

Umar ne ke bamu labarin ban dariya a mota sai ƙyal-ƙyalawa muke yi kamar wasu zararru, Momy dai saidai tayi murmushi idan taji ya faɗi abin dariya.

yanxu ma wani labarin bafullatani yake bamu.

  Yace " wai wani ba fullatani ne, ya siyo lemu, shine aka samai lemun aleda, sai ya saka lemun a bayan keken shi koda ya fara tafiya a kan kwalta, sai ledar lemun ta ɓule,  lemu ɗaya yafaɗi a kan kwalta, koda bafullatani yaga abinda ke faruwa lemun sa ya faɗi kan kwalta, amma se gudu yake yi, sai ya sauka a kan keken ya tsaya ya kwance sauran lemun da suka rage a cikin ledar, ya watsar kan titi, ya ce "a kin banza a she ku kuna ma tafiya kuke bani wahala,  to muhaɗu a gida". 🤣

Comment
      Shear
           Vote

Sbeauty ce ✍️🥰
NI DA YAYA SADEEQ

Love story

             Na
Siddiqatulkhaireey Yahya
            (S beauty ✍️)
             
                 *EWF*📚✍️
_________________________________
                
         Page 04

بسم الله الرحمن الرحيم
        
________Sosai muke dariya Khadija harda rike ciki, ni kuwa ba a magana don har tsalle nikeyi, a haka muka iso gida cikin farin ciki da nishaɗi, a dalilin su Khadija, sai na manta da wani yah Sadeeƙ.

Muna yin faking na kwasa da gudu cikin gidan "Inna Inna". Na shiga ina ƙwala mata kira, but a ce rike a hannun ta, da alamar banɗaki zata, farincikin gani na yasa ta saki butar, ta nufo ni, kan ta ƙaraso na isa gareta na
rungume ta, ina cewa, ya dai tsohuwa ko baki murna da gani na bane, "ja ira". Inna tace tana jan dogon hanci na "banyi murna daganin kiba zaki ce nida nafi kowa san kisamu lafiya".

"To ya jikin Siddeeƙa?"

"Jiki yayi sauki wallahi".

"Haka akeso wancen mugun kuma Allah zai saka miki".

"To". Nace yayin da nike nufar cikin falo, ina shiga na zauna a kan kujera ina maida numfashi, kamar wacce tayi gudu saboda haka ɗabi'a ta take.

Ban wani jima da zama ba sai ga Khadija tashi go, "ke haka ake tarban baƙi?".

"Ina baƙin suke?". na tambaye ta da mamaki, saboda ni dai banga wasu baƙi ba.

"Gamu" tanuna kanta, duka nakai mata sannan nace "wai ɓaki, ku da gidan ku".

"Na ji amma wallahi ba kida kirki Siddeeƙa, ko da yiki na miki uzuri, saboda baki da lafiya". ta ƙare maganar tana zama kan kuje rar danike kai.

Kamar na tambayi me nai na rashin kirkin, amma sai na basar. 

Taɓe baki nai nace "kinsan wani abu khadija?".

"A a sai kin faɗa".

Na ɗora da cewa "wallahi yaya Sadeeƙ bai daki banza ba zan rama, domin kuwa bashi yaci, saboda ni ba kanwar lasa bace".

Cikin zaro ido ta miƙe, kallo na take alamun son ta tabbatar da abinda taji, ba tare da shayi ba na sake maimaita furici na da cin alwashi.

Dafe ƙirji tai kana ta ce "wai da gaske? ".

"Kina mamaki ne?"

"Eh ai dole nayi mamaki, saboda nasan ɗan tsako ya hayke wa shaho".

"Ai kuwa ki bari wannan karon zakiga ni, domin sai nasa shi kuka, muna nan dake". Na ƙare ina fashewa da dariya.

Da ido ta bini da kollo irin bakida hankali yarinya.

Nima nabi ta da kallon naji dai.

"Can dai na ce,"wai ya kike min kallon mara wayau ne? Ko kuma wacce ta fita a hayyacin ta? Amma bari, zan tabbatar miki da a cikin hayyacin na nike".

"Uhm". tace tana cire gyalen ta, gami da ajiye shi a hannun kujera.

Umar ne yashigo bakin sa da sweet yana tsotsa, "la! Umar zo kasanmin". Na faɗa ina miƙa mai hannu".

"Za kisha ne?".

"Eh".

"To bari na kawo miki naki,  yana ɗakin Inna".

Kamin nace to, har ya fice.

"Nima katawo min dashi". Cewar Khadija.

bai daɗe ba sai gashi ya kawo mana, nan ya zauna mukai ta shirme, muna ife-ife, saboda idan muka hau a guri babu dama.

Ana idar da sallar magriba ina sulalewa nabar gidan, da fita ta 'yar kasuwa na zarce, ina tafe ina gaɗa ni kaɗai, a haka har na isa, can na hango ƙawa ta Ladiyo.

Kaf ƙauyen Dande banida ƙawa sai Ladiyo, saboda nafi san a kullum nice shugaba, a komai nafi son ace nice a gaba, sam bana son raini ko kaɗan, sauran duk nayi faɗa dasu, saboda halin mu be zo ɗaya ba, itama Ladiyo tana da hakuri ne kuma kome zan mata batayin fushi.

Ladiyo nakwala mata kira daka nesa, ganin bata ni ba yasa na sake, waige-waige takeyi, har ta juyo ta inda nike, baki ta washe ganin nice, da sauri ta nifo ni, tafawa mukai alamun munji daɗin haɗuwa da juna.

"Ai nazaci bazaki futo ba". Ladiyo tace.

"Caf me zai hana ni fitowa da lafiya ta". Nace mata

"Yo saboda abinda yayan ki yace ɗazun, wallahi na tsorata bazan ƙara zuwa gidan kuba".

Wani dogon tsaki naja "mastsstt kefa sakarya ce, sam bakida wayau, inba sakarci ba taya zaki yarda da maganar sa, shi ba mala'ika ba ba kowa ba, abinda ma yasa baki ganni da wuri ba banida lafiya ne saida aka kaini asbitin bakin gari".

ta ce "baki da lafiya fa kika ce" ɗaga mata kai nayi alamar eh

"To meke damun ki? nidai banga alamar rashin lafiya atare dake ba".

"Ke Allah da gaske bani da lafiya, yah Sadeeƙ ne yaimin dukan mutuwa, ke har fa da ƙarin ruwa akai min".

Ido tazoro waje tana dafe kirjin ta tace  "dukan mutuwa fa kika ce".

Tsaki nayi nace "dube ki kamar ke a kaima dukan, duk kin bi kin firgice".

"To ba dole na firgi ce ba, ɗazu fa da yana min magana wallahi baƙara min tsoro naji ba, tsabar tsorata dana bar gidan ku kafin inkai gidan mu har fitsari nayi, gashi kuma ɗan sanda, mugunta babu wacce be iya ba saboda rannan tsallan kwaɗo naga yasa wasu yara a layin ku, niya ta nazo gurin ki, zuwan da banyi ba kenan". 

Taɓe baki nayi sannan nace "kin san bai daki banza ba ko, domin wallahi bashi yaci, abinda ma yasa nafito kenan neman mafita domin yau ba tsoka na zanyi ba".

"Ai kuwa naji daɗin ganin ki, saboda kar kiga yadda su Mariya da Harira suke tsokana ta, wai inayin magana zasuyi suyi min lis".

"Sakarya kuma kika tsaya kina kallon su". na tambayeta

"Ke! To me kike so nace?".

Kwafa nai, kana nace "bari na gama da yah Sadeeƙ, sai na juyo kansu".

"Yanzu nidai faɗa min me zan mai na huce".

Shiru Ladiyo tayi a lamun tana nazari can tacemin "a dake dai bazai dakun miki ba, sai dai muyi masa mugunta dai-dai da dukan daya miki".

"To wace irin mugunta ce kike ganin zan mai na huce?".

"Eh, kawo kunnen ki kiji yadda zamuyi".

A kunne taraɗa mun aikuwa naji daɗin shawar ta, sosai na saki raina, nayi tsokana son raina, sai gurin tara na koma gida, a ɗakin Inna nasame su, a nata fira da sallama na shiga.

Da ido kowa ke bina, "wai Siddeeƙa daga ina kike ne haka, gurun mutane biyar suka kawo ƙaranki,  Aisha ke basu hakuri  da ɗan kuɗi, take kashe bakin su". Inna ce ke wannan maganar

cikin in'ina nace "Inna daman naje....".

"Daman me" tace min cikin tsawa.

"ina turo ɗan ƙaramin baki na nace, waye yakawo ƙarata ban sani ba". Dubana nakai ga Momy nace "wai haka momy ankawo Kara ta".

"Kinci gidan ku, Hajiyan ƙarya zatai miki kenan? wai Siddeeƙa yaushe zaki girma ne kiyi hankali, kina girma kina ƙara rashin wayau,  Allah dai ya shiryaki".

"Ameen, ina abinci na Inna?".

"Yana kitchen a cikin kula kije ki ɗauka".

Umar yace "nima banci abincin ba, nace sai kin dawo muci".

"To yayi ɗauko mana muci, mai aka girka? na bukata.

Yace "fatan doya ne Momy ta girka".

Nace "yauwa maza je ka ɗauko mana ".
Bayan ya ɗauko mana munaci ina bashi labarin inda naje da kalar tsokanar da nayi, sai cizon yatsa yake, yana faɗin wai meyisa baki min magana ba sanda zaki tafi? wallahi da dani za'ayi, da yanzu ba labari kike bani ba saidai ni na bada.

"Yo ka yaƙuri ban san ai zaka ba, na ɗauka kai ma irin Khadija ne me tsoran tsiya". wa ni? Umar yafaɗa yana nuna kansa, Allah ya kyauta ina namiji intsaya tsoro sai kace mace".

Comment
         Shear
             Vote


NI DA YAYA SADEEQ
                 

              Na
Siddiqahtulkhaireey Yahya
            (S beauty ✍️)

                 EWF📚✍️
_________________________________

Page 05

Bayan gama cin a bincin mu da Umar na miƙe ina hamma alamar bacci nike ji.

Khadija ce ta kalle ni tace "ba dai bacci za kiyi ba". Nabata amasa da "eh kwanciya zanyi".

"Dawuri haka" ta tambaye ni

Da "eh". Na bata amsa

"Yo in banda abinki khadija ai Allah kaɗai yasan inda Siddiƙa taje bayan fitar ta gida, kinga ko dole ta kwanta da wuri". Inna ce dake kwance tace haka, taɓe baki na nayi nace "Momy zan kwanta saida safe".

Wayarta ta kunna ta kalli a gogo ƙarfe goma saura na dare, kallon Khadija Momy tayi tace "kitashi kibita dare yayi goma saura". Umar ma tashi yayi ze bimu amma Momy tace, bata yarda ba tare da ita zai kwana saboda ita batasan kwana ita kaɗai".

Akwai ɗakin da idan sunzo suke sauka acikin sa, duk wani abun buƙata Daddy ya zuba a ciki.

Sai da safe muka ƙara yimusu Khadija ta rigani yin gaba, ina cikin tafiya naji kamar na taka ƙafar mutum dayike lungun ɗakin a kwai duhu, ƙauyen dande kuma ba wuta, jannareto muke kunnawa zuwa ƙarfe goman dare a kashe, to yau yaya sadeeq be kunna ba. Ban gama tabbatar da ƙafar mutum bace a gurin, hakan yasa na ƙara ɗora kafata a kai na murza, 'yar ƙara naji anyi alamun mutum ne, koda na waiga inda nike tsammanin zan sami Khadija wayam babu ita ba alamar ta, zaro ido na nayi da kyau gabana ya soma dakan uku-uku, sakamakon tunawa da nai ba wani bane illah Sadeeq.

A ɗan tsorace nace "la! yaya". Ban ƙarasa maganar ba ta maƙale, sakamakon bige min baki da yayi, gami da shaƙe min wuya,ya haɗani da jikin bango, Yana faɗin me hali be fasa halin sa gwara na kasheki kowa ya huta, sa'anki ne ni zaki murje min yatsa eye?.

Da iya ƙarfin sa ya shaƙemin wuyan, ina son inyi ihun neman ɗauki amma na kasa, cikin ikon Allah saiga Momy da Umar, sunzo wucewa hannun ta ɗauke da hasken fitilar wayar ta, tana haskawa, mai zata gani wani ƙara tasaki saida wayar ta yafaɗi a ƙasa, Inna da khadija rige-rigen fitowa suka yi saboda ihun Momy da suka ji.

Umar tuni ya das-kare a gurin, jikake tas tas ƙaran marin da Momy ta wanke yaya Sadeeq

Amma duk da haka yaƙi sakina, don haka ta ƙara mai wani saida tayi mai mari biyar amma ko gezau, beyi ba dayike yah sadeeq namijin duniya ne, "to idan baza saketa ba sadeeq zan cireka cikin 'ya'ya na".  ta faɗi haka fiskar ta babu alamun wasa.

Jin wannan lafazin na Momy yasa Sadeeq yayi jifa dani, idanuwan sa jajur kamar Wanda yasha wani abun, huci yake yi sosai

Kasa nafadi shirim jikina babu ƙwari, ina fitar da numfashin wahala Inna da Khadija takaici ya hanasu magana, hawaye ne ke gangan garowa a cikin Idanuwan Momy, ta kasa magana hannuna ta kama muka wuce ɗaki na, su Inna na biye da mu abaya, kan gado ta ɗorani, na kwanta yaraf, ruwan fridge me sanyi khadija ta ɗibo min ta ɗaga kaina ta bani nasha ina maida numfashi.

Babu Wanda ya tambayi me ya haɗamu, duk kuwa da cewa zuciyoyin su cike take da tambayoyi, daga haka kowa ya tafi ma kwancin sa.

a raina kuwa saƙa yadda zan wulaƙan ta yaya sadeeq nikeyi, domin wallahi bashi yake ci wani mugun tsanar sa naji ya ƙara da ɗuwa a zuciya ta.

da wannan tunanin bacci ɓarawo ya sace ni.

Kiran sallar asuban fari a kunne na akayi, banida nauyin bacci, tashi nayi na zauna gaba ɗaya jikina ciwo yake min amma wuya na yafi min ciwo.

Tashi nayi tsaye ina miƙa ko salati banyi ba, ba kuma dan ban iyaba saidan tsabar shagala, da wasa da yayi min yawa.

Tsakar gida nafito babu kowa ɗan Murmushi nayi saboda zanyi abinda zanyi babu wanda zai ganni, a irin wannan lokacin ya Sadeeq ke fitowa yayi alwala, kamar yadda Ladiyo ta tsara min haka nayi, a binda kuwa Ladiyo tace min a kunne shine. Na zuba masa karara aruwan alwalar sa, da na wanka, nayi na'am da wannan shawarar da tabani, saboda nasan tanan ne kawai zan iya ramawa.

saɗaɗawa nayi ɓangaren sa, inda yake ajiye butar sa na nufa, "Alhamdu lillah". na faɗa yayin da na hangi butar sa, a jiye a gurin, da hanzari na ƙarasa gurin.

ɗaga rigata nayi na war-ware siketin jikina, na ciro ƙullun ledar karara da nasaka Ladiyo ta sato min na Umman ta da take saidawa.

Murmushin mugunta nayi, yayin da na ɗaga butar naji ta cike da ruwa, buɗe murfin butar nayi na zuba, kana na rufe, na maidata ma'ajin ta.

Yaya Sadeeq baya barin sai zaiyi anfani da abu yanema yana tanadar sa ne tun kamin lokacin amfanin sa yazo, saboda bayason bata lokaci

A jiyar zuciya nayi nabaro lungun, a hankali nike tafiya kamar mara gaskiya, Inna na hango idon ta akaina ƙyar da buta a gaban ta, da alamar alwala ta gama, Murmushi nayi gami da ƙarasawa gaban ta nace "Inna kin fito kenan?".

"Eh na fito, daga ina ki ke?".ta tambaya.

"Daga waje leƙawa nayi, alwala na fito sai yanayin garin ya bani sha'awa shine na leƙa" na faɗa mata haka kamar da gaske

"Amma mai yatada ki daga barci" Inna ta tamba yeni a karo na biyu.

Wallahi Inna baccin ne yaƙi zuwa min sai naji an kira sallah shine nace "bari nayi sallar sai na kwanta".

1 Comments On NI DA YAYA SADEEQ
avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment