Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafi bangaren sa, da shigar sa inda yake aje computer dinsa ya nufa bayan ya dauko ta ya nemi gefen makeken gadon sa ya zauna, dayike komai na gidan asete yake da kwamfutar sa, ba tare da bata lokaci ba ya shiga dubawa bayan wasu a wanni saiga idon daddy na zubar da kwalla, cikin sauri ya rufe computer saboda annune inda Aitene tasa kafa ta shuta ni na bugu da gini sai ga kaina ya fashe yana jini hakan bai ishe ta ba sai da ta kara min da duka, har yanzu Daddy mamaki yake bai taba zaton Atine ba yar halak bace kan sa ya dafe yace "oh ke duniya ina zaki damu ace duk wanda ka bawa amana sai yaci babu masu tsoran Allah, a gidan ka kana tsoran iyalan ka a waje kana tsoran mutanen da kake mu'amula da su, saboda rashin amana da yadda.

Mikewa yai jiri na diban sa ya fito bai daki na ya dawo inda ya samu Dr na ta faman danna waya, da ganin Daddy ya aje wayar saboda yanayin Daddy ya nuna yana cikin damuwa.

Dr ya dade yana tambayar Daddy, amma Daddy ya gaza cewa komai.

Saida ya zauna ya samu nutsuwa kana yace "ka kira min Dpo Babawo kasanar dashi yar aiki tayi yunkurin kashe yarinyar da take kulawa da ita".

Hannun Dr na rawa ya lalubi wayar shi, tuni shima idanuwansa sun kada sunyi jawur, number Dpo Babawo ya lalubo ya danna kira ta dade tana ringing sannan ya dauka, daga can bangaren yai magana da turanci, shima Dr cikin turancin ya mayar mishi.

To bayan ya kashe wayar ba'a wani bata lokaci ba sai ga motocin rundunar yan sanda tazo, da yike anguwar manya ce kullum cikin jin jiniya suke saboda haka mutanen unguwar basu kawo mai laifi aka zo kamawa ba.

Ita uwani tunda taji jiniya hanyar cikin ta ke kadawa sai muzurai take, bata gama sarewa ba sai da taga yan sanda sun shigo mata biyu maza uku, tana ganin su ta mike tana fadin "na tuba ku yafe min Alhaji Alhaji dan Allah kayi magana a kyale ni, a dai-dai lokacin Daddy ya fito daga daki na Dr na bayan sa kallon tsana Daddy yabi Atine dashi yace" tur da halin ki dama tsintacciyar mage bata mage, da izinin Allah sai kin girbi abinda kika shuka ku tafi da ita idan kun gama binciken ku ku mika ta koto dan sai na tabbatar da na kwatar ma yarinya ta yancin ta".

Tuni yan sanda suka tasa keyar Atine zata tsaya mu gaddama suka tara mata gajiya tare da saka mata ankwa a hannu suka ce mata "indai ta kara magana sai sun harbe ta". Da haka suka kashe bakin ta amma da sai ihu take tana ta fadin "ta tuba"

bayan yan sanda sun tafi da ita sunyi binkicen duk da yakamata kuma sun kama ta da laifi dumu duma, saboda haka suka mika ta koto inda aka yanke mata hukuncin shekara 25 agidan yari tare da horo mai tsanani kuma babu beli.

Tun daga nan Daddy shi ke kula dani duk wata dawainiya ta shine dan ya hakura da fita kasashen da yake shike kaini makaranta kuma ya dauko ni, bai yadda da kowa ba gani yake za'a kuma cutar dani.

Kafin kice me nayi kyau nayi bul-bul dani da kuwa kamar ki hure ni na fadin

Bayan wasu watanni Daddy ne a cikin masallaci bayan sun idar da sallah Ladan yace yana da magana, wasu aciki sun fita yayin da wasu kuma suka zauna, acikin wa'inda suka zauna harda Daddy na ladan ne ya fara jawabi kamar haka "sama da shekaru biyar da suka wuce na tsinci wata mara lafiya cikin ikon Allah nai ta nema mata magani saboda na lura sammu ne akai mata, to Alhamdu lillah yanzu ta samu sauki amma na tambaye ta ahlin ta tace bata da kowa to shine nike so naji ko akwai wanda zai iya cigaba da dawainiya da ita, saboda naga bata sakewa a gida na uwar daki na kullum cikin tsangwamar ta take, Duk da Daddy na tsoro bai hana shi cewa ba "ala gafarta malam babu damuwa zan dauki nauyin ta". Kasancewar Ladan yasan Daddy yasa yace "ah Alhaji Hamza mai zai hana ka aure ta tunda naga baka da mata ga marainiyar diya kana tare da ita, duk da na ga abinda ya faru kwanakin baya a labarai da mai aikin ka ta kusa kashe ta, yanzu sai ka sama mata uwa ai"

Gabad'aya yan masallacin sunyi na'am da batun sukai ta bawa Daddy kwarin gwuiwa, "to ba'a kin ta mutane" daddy ya fad'a ya kuma dora da cewa "amma ni yanzu tsoran matan nike gani nike kamar duk daya suke"

Nasiha Liman yai mishi daga bisani aka daura auran Daddy da Ammi abisa sadaki mafi karanci, bai kuma dawo gida ba sai da amaryar sa wato Ammi.

Sanda Daddy ya shigo na gansa da Ammi tambayar sa nai wace ce? Yace "Ammin ki ce". Da gudu naje na rungume ta ina jin son ta da kaunar ta har cikin raina, tunda ga ranar nima nai uwa farinciki na da wal-wala ta ya karu banda wata matsala saboda yadda Ammi ke bani kulawa ko mama ta na da rai iya abinda zatai min kenan, sosai nike jin dadin zama da ita kuma tana iya bakin kokarin ta akan tarbiya ta, har ta samu ciki, duk da itama wajen haihuwa taji jiki har nafara tunanin ko itama zan rasa ta ne, sai kuma Allah ya tashi kafadar ta, ta haifa min kyawawan kannai Wudat da Walid

Wannan shine takai-taccen tarihin Fadeela

Ci gaban labari

Kallo na fadeela tai tace "kin San wani abu kuwa?"

"a a". Na bata amsa

Tace "kina kama da Ammi har muryar ku iri daya wallahi"

Zanyi magana kenan saiga firifet sun shigo da bulala a hannun su, daya daga cikin su tace "eh lallai kune ferarrun yan iska ko da ba zaku wuce kitchen ku karbi abinci ba tun dazu aka buga ringing"

Yo ni dai ban san ya abin yake ba hakuri Fadeela ta shiga basu, yayin da ni kuma sai zare ido nike,duk magiyar da Fadeela tai musu bai sa sun kyale mu ba

Wata gutunwa a cikin su tace "wallahi baku isa ba Kuje ku karbi abinci kuzo kuyi mana wanki dan baku isa ba"

Kallon fuskar ta nai kamar kai amai, ban san sanda dariya ta kwace min ba, harda rike ciki, ina cikin yi naji saukar bulala tsui-tsui ban san sanda na kwarma ihu ba ina kiran sunan yah Sadeeq.

Cikin bacin rai tace "idan ma uban Sadeeq zaki kira kin dade baki kira ba da ganin ki baki da tarbiya agidan ku ba'a koya miki ladabi ba kin ja ma kanku wallahi bayan wanki da zakuyi sai an muku wankan jego".

Na bude baki na rama kenan Fadeela tai saurin toshe min baki, ta hanyar sa tafin hannun ta a baki na

* * * * * * * *

Na gaji da typing zan dakata anan kasancewar bana publish kullum yasa nike yin typing da yawa amma don Allah ku aje min comment saboda ta hakan ne zan samu kwarin gwuiwar cigaba da rubuta littafin saboda kun san wannan shine farkon littafi na to yin comment don fadar ra'ayoyin ku shike bani karfin gwuiwa har naji labarin na shigar ku kuma kuna fahimta ta dari bisa dari

Please
following
Vote
Share


NI DA YAYA SADEEQ
•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
No editing
Chapter 30
____fita sukai suna huci, ni kam raina gabad'aya ya gama baci, Fadeelah nadafa ido na cike da kwalla nace "wai dan Allah a haka kuke rayuwa na fahimci da kiyi laifi da karkiyi duk daya, idan jinin ki bai hadu da su ba sai suyi ta jibgar mutum, ni gaskiya bazan iya dauka ba, haka kawai a gidan mu ba'a dake ni ba sai anan wasu katunan banza su rinka bugu na".

Fadeelah tace "uhm Siddeeqah kenan wannan ma kadan kika gani amma ahankali zaki cigaba da fahimta, kuma kamar yadda kika ce idan fa jinin ki bai hadu da su ba kin shiga uku, musamman ma suga kina da kyau to sai kin fi banuwa, tashi muje kar wasu su zo, su ganmu mu kara laifi".

Mikewa nai zuciya ta babu dadi yau daya ko yinin arziki banyi a makarantar ba duk ta gundure ni.

Muna cikin tafiya muka ji ana kiran Fadeelah da sauri Fadeelah ta waiga dan ganin wacce take kiran ta, aikuwa tai sa'a dan batai mugun gani ba school Momy dinta ta  gani, da sauri taja hannu na muka isa gurin ta rungume ta Fadeelah tai tace "Momy Halima wallahi tun jiya nike zuwa room din ku amma sai su senior Dijah su hana ni shiga". Ta karasa maganar cikin yanayi na damuwa

"ke kada ki damu dama naji ajikina kin zo kin barin ki sukai saboda na tambaye su suka dunga yimin hanya-hanya" a cewar Momy Halima

Kallo na tai muka hada ido tace "Fadeelah kenan, ai dama na fada miki dole wataran zaki nemi kawa, gashi ba'a dau wani lokaci ba har kin gaji da yawo ke kadai, amma dai diyar firinciful ce ko dan ga kama nan?" Momy Halima ta kare maganar cikin sigar tambaya

Fadeelah na Murmushi tace "wannan fa sabuwar zuwa ce yau aka kawo ta kuma ba diyar Firinsifal bace amma dai hostel din mu daya kuma sai naji ta kwanta min a rai, yanzu haka kitchen zamu amsar abinci dan su senior Habiba sun rutsa mu a hostel" nai dai ta labarta mata abinda ya faru, cizan dan yatsa Momy Halima tai ta ce " Allah ya saka mata amma ba wani wanki daza kuyi musu ku zo muje room din mu"

Binta mukai muna tafiya tana mana hira sai dariya muke

* * * * * * * * * *

Zaune suke cikin gurin shakatawar, Lubancy ce ta dubi Zuby ta ce "ni kam kawata kin yi waya da Sadeeq kuwa?"

Sai alokacin Zuby ta dago kanta daga danna wayar da take ta ce "a a wallahi nayi ta kiran sa bai dauka ba, banyi tunanin yana da bakar zuciya ba sai da wannan dan abin ya faru".

"kada ki damu nasan bai huce bane amma tunda yana son ki dole idan ya huce zai daga miki kawai dai ki cigaba da kiran sa"
A cewar Lubancy

Kai Zuby ta daga alamun gamsuwa

Suna nan zaune wata matashiyar budurwa tazo wucewa, sanye take da dogon hijab amma bai kai kasa ba kuma fuskar ta sanye take da nikab, ga kuma bakin glass ta sanya, yanayin ta ya nuna kamar tana sauri, saida tazo gab da su Zuby wata leda dake hannun ta ta fad'i, ai kuwa takardun dake cikin ta suka watse, tsugunnawa tai ta fara kwashewa amma sai dai bata gama ba wayar ta ta fara ringing, daga wayar tai ta bar kwashe takar dun ta kuma yi tafiyar ta abun ta.

Gefan kafar Zuby Lubancy ta kalla tace "ke ga wata nan kusan kafar ki".

Zuby ta ce "me?"

Lubancy ta ce "kardun waccan da suka watse dauko mu gani"

Hannu Zuby tasa ta dauko, har zata mikawa Lubancy sai taga kamar rubutu ne aciki sha'awar karantawa taji, saboda haka ta shiga karanta abinda ke ciki kamar haka

"tabbas ranar nadamar ki ta kusan zuwa bama ke ba da duk wasu masu aikata mummunan dabi'a irin taki na rubata wannan sakon ne saboda nasan zai iso gareki".

Ras-ras gaban ta yai mummunan faduwa, mikewa tai cikin hanzari tana fadin ina take ina zan ganta, hanyar da taga wannan matashiyar tabi ta shiga bi, da ganin haka Lubancy itama ta mike ta biyo bayan Zuby tana tambayar ta lafiya? Menene? me yafaru? Haka ta jero mata tambayoyin ajere, Amma Sam Zuby ta kasa bawa Lubancy Amsa har bakin titi suka fito amma ko alamar ta babu,

Mai keke nafef ne yazo wucewa, Lubancy ce ta daga mai hannu yai faking, shiga sukai kana Lubancy ta fada mai unguwar da zai kai su.

* * * * * * * * *

Su Sadeeq ne a hanya sai sharara gudu yake duk da sun shigo garin kaduna amma bai daina gudu ba, saboda yaga Farooq bai gudu shiyasa tun acan, ya amshi tukin motar, kuma gashi sunyi sauri sosai daka kalli Sadeeq zaka san baya cikin damuwa

Farooq ne ya dube shi ya ce "kai mutumi na yanayin ka ya nuna kana cikin wal-wala fa, wai maye sirrin a bani? A sammini nima in tafi ina nishadi" ya fad'a yana duban abokin nasa

Saida ya kara gyara zama ya ce "Farooq kenan bai kamata ka tambayi sirrin farin ciki naba saboda nasan ka sani duk da nayi mata alkawarin ba zanyi aure ba har sai ta gama makarantar ta na saketa, amma wallahi kar ka tona zuciya ta kaji tayi fari kal kamar auduga, dan gani nike kamar yau ne zan rabu da kaya,

Sabalo Farooq yai yana kallon Sadeeq yama rasa mai ze cemai, wato sai yau ya kara tabbatar da Sadeeq gara ne number daya, tunda har karamar yarinya tafi shi wayau da hangen nesa,

Dariya Farooq ya shiga yi yana tafa hannayen sa

Ganin dariyar Farooq ta fara yawa yasa Sadeeq kuluwa, dan shi ya tsani rainin hankali, to inba rainin hankali ba maye na dan ya fadi abinda ke cikin ransa zai tsaya yin dariya.

Cikin kulawa ya ce "kai bansan iskanci, ka bude baki sai dariya kake kamar kaga wawan zama"

Saida Farooq yadai-daita kansa kana yace "wani hasashe nai shiyasa kaga ina wannan dariyar, amma ai har gwara naga wawan zama akan abinda na hango nan gaba kadan inda rayuwa".

Kwafa Sadeeq yai bai kara tanka mishi ba, saboda ya gama lura da Farooq dan rainin hankali ne.

A haka suka isa masaukin Farooq dake nan cikin barnawa, bayan sun wuto gets, fakin Sadeeq ya nemi guri yai, a kusan tare suka fito daga motar kowa hannin sa a sama yana mika, saboda kowannensu ya gaji likis,  ban garan shi suka nufa direct, basu zarce ko ina ba sai bedroom ko takalmi Sadeeq bai tsaya cirewa ba, ya fad'a kan lallausan gadon Farooq yana kiran sunan Allah.

Shima Farooq dan wannan tafiyar data taso mai ne amma da lafiyar gadon zai bi, yanzu kam ba yadda ya iya, takalman sa ya cire ya fad'a bayi bai wani jima ba ya fito, bayan ya gama kintsawa yashiga shirya kayan sa duk wani abu da yasan yana da bukata ko zai bukata saida ya dauka, bayan ya gama shirya komai ya zauna a bakin gadon ya dubi Sadeeq da idanuwan sa suke alumshe kamar mai bacci, ya ce "nifa zan tafi don nagama shiryawa, nabar maka mukullin ne?" Sadeeq kaman bazai kula sa ba, saboda har yanzu bai gama hucewa ba, har Farooq ya fidda ran amsa sai yaga bakin Sadeeq na motsi

" a a ka jirani bari na watsa ruwa sai mu fita tare " wannan itace amsar da Sadeeq yabayar

Kan Sadeeq ya mike wayar Farooq ta fara ringing, ganin sunan abokin aikin su ne yasa ya dauka gami da karawa a kunne, adai dai lokacin shi kuma Sadeeq yashiga bayan gida

* * * * * * * * *

Ahanya muka ci karo da wannan gajerar firifet din, kasancewar bata magana da Momy Halima yasa ta bimu da kallon banza

Kallon Fadeelah nai nace "wai ya sunan waccan abar ne?". Na fada ina nuna inda take

Fadeelah tace "Rafi'a sunan ta, amma Rafsy ake ce mata"

Ina dariya nace "ta ko ci sunan Rafcy din"

A haka muka karasa Room din Momy halima, gado ne guda hudu na gani aciki saboda karamin daki ne, kuma a gyare yake tsaf, ko ina a tsaftace

Har bakin gadon ta muka zauna ta ce" bari na dafa mana Indomie dannima yunwar nike ji".

Wani dan karamin risho naga ta janyo daga karkashin gado, gami da dauko tukun ya, a wani bokiti naga ta dibi ruwa, inda ta bude loka ta dauko indomin, ba awani dauki lokaci ba indomin ta dawu, wani filet ta dauko ta juye mana gaba daya ta ce "Kuje ku wanko hannun ku kuzo muci" to muka ce muka dibi ruwa akofi muka fita, fitar mu keda wuya muka hangi, senior Jamlah inda muke take nufowa, cikin sauri na wanke hannun na dawo room, saboda yadda gabana ke faduwa.

Ko zama banyi ba sai ga Fadeelah tana dariya ta ce" kar dai har kin fahimci Senior Jamlah muguwa ce?". Tai maganar cikin sigar tambaya

Bayan na zauna ita ma ta zauna nace "ba dole ba kin San irin mutanen nan halin su baya boyuwa, koda kuwa sun so boyewa" nan dai na kwashi labarin komai da nagani na fada mata,

Batai wani mamaki ba tace "indai Senior Jamlah ce tayi abinda yafi haka ma, ke wallahi ko ni na tsane ta tsana mai mutakar yawan gaske, kuma kar kiyi tunanin ta taba duka na fa, a a ko daya haka kawai na tsane ta, kuma yanzu haka na hangi kiyayyar ki atare da ita, dan har tambaya ta tai wai maye alakata da ke? Nace mata ba komai, shine ta wuce tai kwafa".

Zanyi magana kenan Momy Halima tace "kubar firar haka ku bari sai munci abinci"

Sosai naci indomin dan dahuwar  tai min dadi

Karrawa naji ana bugawa Fadeelah na kallah nace "ta maye kuma?"

Tace "ta bacci ce maza tashi mu tafi hostel, kuma kada idan munje ki saki jiki kiyi ta sharban bacci, dan wallahi idan lokaci tashi yai baki tashi ba kin kade".

Nace "kai wannan wani irin bala'i ne haka makaranta sai kace wurin horan barayi da kangararru".

Momy Halima tace "kuyi zaman ku anan ke Fadeelah ai kin san ba mai shigowa cikin su koda kuwa karan hauka ne ya cije su ku bari sai la'asar mu fita,

* * * * * * * * * *

Direct Gidan su Zuby mai nafef ya sauke su, ko kudin sa bata tsaya basa ba, Lubancy ce ta biya sa

Koda ta shiga falon gidan babu kowa sai TV da aka bari a kunne yana ta wake wake, zama tai tasa hannu ta dafe kanta, saboda azabar ciwan da yake mata,

Lubancy ce ta shigo, bayan ta nemi guri ta zauna tace "wai don Allah kawa ta meya faru? Ni kin barni a duhu tun dazun sai tambayar ki nike kinyi banza dani, bazan iya jure kallon ki a cikin wannan halin ba, saboda haka zan tafi idan kin shirya fada min kya neme ni, ko ta waya ce "

Ganin Lubancyn da gaske take tafiyan zatai yasa Zuby tai saurin  cewa "dakata zan fada miki". Nan dai Zuby ta kwashe labarin abunda ta gani ta fada mata, cike da mamaki da fargaba Lubancy tace "amma fa wannan lamarin akwai daure kai mutuka, nama rasa ta ina zan fara "

Gwauran numfashi Zuby ta sauke tace "nima tuntuni abin ke yawo a kwakwalwa ta kenan, na rasa me hakan yake nufi?"

Yar aikin su ce tazo shigewa bayan ta gaishe su zata tafi, Zuby tace "kawo mana abin korawa" bayan ta kawo musu Zuby ta dubeta, tace "ina Mama ne? Kota fita ne?".

Rahamatu mai aiki tace " tana ciki ko wata kila bacci take yi" daga haka ta bar gurin

* * * * * * * *

Bayan Sadeeq ya fito daga wanka, durowar Farooq ya bude ya dauki kananun kaya riga da wando na jins, rigar me ruwan blu ce amma lite sai wandon jins baki, yai matukar yi masa kyau daya saka abun ka da mai kyau, bayan ya gama kintsawa ya taya Farooq diban kaya suka sa a bayan mota, suka kuma daukar hanya, bayan sun fito a bakin titi Farooq ya sauke Sadeeq sukai wa juna sallama, saboda ba hanya daya zasu bi ba, Motar haya Sadeeq ya hau inda yace "musu Kawo zasu kai shi" bayan ya sauka a kawo ya kuma tarar motar buruku daga nan kuma bayan an sauke shi ya hau mashin din da yake kaisu cikin kauyen su Inna saboda mota bata shiga, har kofar gida mai mashin ya sauke Sadeeq, inda ya  ciro kudin sa ya bashi, kana ya shiga gida bakin sa dauke da sallama, Inna dake tsakar gida na shan iska tana ganin sa tafara tafi tana cewa "maraba maraba lale-lale da yan birni" karasowa inda take yai, kana ya zauna akan wata kujera data gefan ta, yace "sannu Inna na same ki lafiya?"

Tace "ina lafiya lau mai gida ina yar rigama ta?"

Yace "Inna yar rigimar ki tana nan amma yau kwanan makaranta zatai".

Ido Inna ta zaro waje tace "makarantar kwana ka kaita ne?"

Kai ya gyada alamun "eh"

Inna tace "ina karami? Kuma ya barka ka kai yarinyar nan inda za'a cutar da ita?".

Sadeeq yaso yace "dama ai baiyi dan taji dadi ba" sai kuma ya tuna mitar Inna,  dan kuwa ta  dungi yi har labari ya koma kunnen Daddy, labari kwa na komawa kunnen Daddy ai ya bani

Kara gyara zama yai, yaita yiwa Inna bayini akan makarantar kwana gwargwadon yadda yaso ya shigar da ita, kuma ta shiga tsaf dan sosai ya tsara ta, ya kuma shaida mata yanzu sun daina fada sun shirya da juna, sosai Inna taji dadin wannan lamarin dan haka tace "akwai wata fura dana dama bari na shiga na dauko maka nasan kana mutukar so" mikewa tai takwaf-takwaf taje ta dauko mai kwarya ta kawo mai, karba yai yayi godiya yace "Inna ni a gajiye nike, bari na je dakina na dan huta".

"to" Inna tace

Yayin da shi kuma yanufi  hanyar soro

* * * * * * * * *

Hudu saura Momy Halima ta tasheni daga nannauyen baccin daya daukeni dan na gaji, da kyar na iya bude ido na, kallon gefe na nai Fadeelah na gani zaune idanun ta sunyi mishi-mishi sai hamma take famanyi, mikewa nai zaune nace "Ash dadin gida kenan wallahi"

Momy Halima tace "maza ku tashi yanzu ba lokacin fira bane"

Haka muka fito daga room din muka tafi hostel din mu, kiran sallah naji anayi nace "lah dama akwai massalaci anan ne".

Fadeelah dake kokarin fiddo da sabon silifas a cikin akwatin ta tace "eh man ai nan da kike gani babu abin da babu don kinga har da islamiya ma, kuma har sauka ake yi"

Daga haka ban kuma cewa komai ba, Alwala muka je mukai muka tafi masallaci.

To da dare kuwa gaza bacci nai don kuwa banda juyi babu abunda nike, da yike bacci barawo ne ban san sanda ya kwasheni ba

Washe garin tun shida Fadeela ta tada ni, saboda nai wanka tace "idan banyi da wuri ba zan makara gurin zuwa class, to bayan nayo wanka nazo saka yunifom yace dauke ni inda kika barni, neman duniya ban ganshi ba, Fadeela na fadamawa tace" to ke a'ina kika barshi?" nace nan saman akwati na fa na dora shi"

Cikin takaici Fadeela tace "ai kuwa gwara ki daina wahalar nema dan an sace inada sabo bari na baki, amma kin San daya bazai isheki ba dole sai kinje office din shugabar majar kin karbo wani,

Cikin mamaki nace" ikon Allah mutum ba shi ya aje abu ba yazo ya dauka".

Fadeela tace "wannan ba abun mamaki bane bari na fiddo miki kisa kada mu makara.

Bayan ta fiddo min na saka, kallo na tai tace" Siddeeqah kinga yadda yunifom din nan suka miki kyau?"

Ido na zaro waje nace" ke dai kin cika zolaya wallahi"

Tace "daga fadan gaskiya".

Nace "ba wani gaskiya ke dai tashi mu tafi, tunda mun gama shiri,

" To" Fadeela tace min kana ta Mike  muka fito, kitchen muka nufa, bayan mun karbi breakfast din guri muka nema, bayan mun gama ci muka tafi class.

Wannan kenan

To Kwanci tashi asarar me rai kuma babu wuya a gurin Allah.
NI DA YAYA SADEEQ

•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

No editing

Chapter 31

____Kwanci tashi asarar me rai kuma babu wuya a gurin Allah.

a bangaran su Zuby  abinda ya faru kuwa shine,

kwatsam wata rana suna cikin gidan da suke yin mitin, kamar kullum yadda aka saba,

1 Comments On NI DA YAYA SADEEQ
avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment