Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take zaune, da Sallama muka shiga, fuskar ta dauke da fara'a ta amsa kana ta nuna mana kujeru tace mu zauna,  tunda na kalli matar naji ina son ta ban taba haduwa da wanda naji ya kwanta mi  arai lokaci daya kamar ta ba,

To aban garan Hajiya Aisha ma haka lamarin yake dan kuwa tana kallon Sadeeq da Siddeeqah taji gaban ta ya fadi, ga kuma kwarjinin da sukai mata har taji  son su da kaunar su ya shiga ran ta.

Tana dariya tace "Malam Naseer suwaye wa'innan?".

Yace "ai ranki shi dade sune wa'inda na miki maganar su wannan itace kanwar tasu da akai ma register".

Tace "masha Allah" yan mata ya sunan ki?" Hajiya Aisha tai maganar tana kollon Siddeeqah

"Siddeeqerh" na bata amsa yayin da muka hada ido ta sakar min Murmushi tace "sunan ki babban suna ne kuma nima sunan yarinya ta babba ce".

Nace "Ammi da gaske kema kina da yarinya me suna na?".

Bani da na fadi sunan ba ita kanta Hajiya Aishan yanayin ta ya nuna taji dadin yadda na kira ta shi kuwa yah Sadeeq mamaki ne ya kama shi

Tace "da gaske nike yata amma a halin yanzu bama tare".

Nace "to Ammi tana ina?".

Idon Hajiya Aisha ne ya kawo kwalla ganin haka yasa yah Sadeeq yace "ke Siddeeqah ya isa haka kin cika tambaya".

Jikina a mutukar sanyi nace "Ammi ki yakuri na daina".

Handkerchief ta d'auka ta dan yi sama da glass din ta ta share kwallar data cika mata ido tace "babu komai yata".

Ya Sadeeq ta kalla tace kai ya sunan ka?". Nai sauri nace "Sunan shi Sadeeq yaya na ne kuma dashi Daddy ya daura min aure yace Wai alkawarin kanwar shi ne data...".

"Ke!!!" Yah Sadeeq ya daka min tsawar da saida naji yayan cikina sun kada a tsorace na dago kai na kalle shi inda na hangi tsan tsar bacin ran sa ture ni yai daka kusa dashi ya tashi ya fita  fuu kamar zai tashi sama.

Farooq yace "ranki ya dade ki yaquri haka yake zuciya gare sa".

Hajiya Aisha da ke saka abubuwa bar katai a ranta tace "ba komai, amma abinda ta fada gaskiya ne dan ta tuna min da wani dana shima haka yake kamar wannan?".

Farooq yace "eh gaskiya ne".

Daga haka babu wanda ya kuma furta wata kalmar

Malam Naseer ta duba tace "Malam jeka dasu office din ka kaina ya fara min ciwo ka bata ajin da ya dace da ita"

"To" yace muka fito, yah Sadeeq na hanga acan jikin mota, harara ya wurga min nima na rama harda murguda baki, a zuciya ta nike cewa ba zai taba canzawa ba".

Bayan mun zauna a office din

Malam Naseer yace "

"A jin ki nawa a makarantar da kika baro?"

Nace "Js 1"

"Shekarun ki fa?"

"sha hudu 14" na bashi amsa a takaice

Wata farar takadda ya dauko ya danyi rubuce-rubuce kana ya shiga yin magana da turanci yah Farooq na bashi amsa bayan sun gama ya miko min wata yar takadda yace "zan sa students su zo su tafi dake yanzu hostel din ku, dan yanzu dalibai suna aji ana karatu amma ke bazaki samu damar yin karatu yau ba saboda an kusa tashi ".

" to" nace bayan na amsa takaddar

Bayan mun fito da gudu na isa gurin yah Sadeeq na kan kame shi ina kuka nace "yaya yanzu tafiya zakai ka barni? saboda ba ka kauna ta, kalli fa kaga ni dai na fasa bazan iya rayuwa anan ba".

Rage tsayin sa yai ya tsugunna yace "kowa da haka ya saba kema zaki saba karatu ne kuma ba'a samin sa a sauki saboda haka ki jure sannan banda rashin kunya dan akwai ban banci tsakanin makarantar kwana da ta jeka ka dawo, idan senior tace kiyi kiyi banda kin ji dan idan kika ce zaki rashin kunya wuya zaki ci".

Hawaye ne masu zafi suka cigaba da wanke min fuska na kara rungume shi, yah Farooq yazo yace "sake shi Siddeeqah saki shi haka nan, ki hakuri ba wani jimawa zaki ba zaku tafi hutu".

Ban sake shi ba na cigaba da kuka na "da kyar ya Sadeeq ya dago ni yana cewa" nace ya isa haka ki daina kuka muje na baki number na kuma insha Allah idan na samu lokaci zan zo na duba ki, kuma idan lokacin ziyara yai su Momy zasu zo".

Nace "to yaushe ne ziyarar?".

"an kusa". Ya bani amsa yana Jan hannu na muka nufi gurin mota

Bayan motar  ya bude ya fiddo wannan katon akwatin kana ya maida ya rufe

Yace "yauwa wannan shine akwatin ki duk abinda kike so akwai a ciki".

Kanshi ya dan dafa yace "Farooq munyi mantuwa fa"

"ta me?". Farooq ya tambaya

"Uniform din ta mana".

  yace "a haba na dauka ka dinka mata ne bari naje in karbo".

Cikin office din da muka baro ya koma bai wani jima ba sai gashi ya dawo da leda a hannun sa

Wasu students ne guda uku suka zo inda muke da turan ci suka gaida su yaya suka ce Sir Nazeer ne yace muzo mu kaita hostel din ta, yah Farooq yace "to gata nan dan Allah amana ku kula mana da ita".

"insha Allah suka ce".

Kana ya Sadeeq ya ciro kudi ya bani nace "bana so yaya wanda Daddy ma ya bani suna gida na baro su".

Yace "ki amsa ki nada bukatar su".

Duk yadda yaso na amsa ki nai ba yadda ya iya wasu kudin ya ciro yabawa yan matan yace "wannan naku ne ku raba wannan kuma nata ne idan tanada bukatar wani abun sai ku bata".

"To" suka ce yayin da suka shiga Jan akwati na

yah Sadeeq yace ce "to Siddeeq zo ki amsa number kada na manta mota ya shiga ya dauki memo da biro ya rubuta number ya miko min na amsa

yace" sai na dawo duba ki Allah ya bada sa'a".

Ameen yah Farooq yace inda shima ya shiga mota hannu nai ta daga musu har saida naga sun Kule min sannan na daina na kalli wa'innan yan matan guda uku nace "ina zamu yanzu?"

Ba wanda ya tanka min suka cigaba da Jan akwatin da kamar na daina bin su sai dai nace bari naga gudun ruwan su

* * * * * * * *

Sanarwa
      Sanarwa
            Sanarwa

Follow

Comment

Vote

Dan Allah kada amanta ayi following dina sannan ayi min comment da vote please kuma ku min uzuri akan rashin jina akai kai abubuwa ne suke min yawa amma insha Allah zaku dunga jina

kasancewar bana typing kullum na manta wasu sunaye danasa to za kuga na canza suna insha Allah idan nagama littafin zan gyara🙏

taku har kullum Sbeeuty

NI DA YAYA SADEEQ

•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Not edited

              Chapter 29

_____Iska ce mai dadi take ta kadawa tako ina saboda yawan bishiyoyin gurin, dalibai sai zirga zirga sukeyi, can na hangi wasu dalibai su biyu durkushe akan gwuiwoyin su, wata budurwa ce mai Jan dan kwali ke ta zabgar su kamar ta samu bayi da alamar yaran da ake duka magiya suke a kyale su saboda naga sai daga hannu sukeyi alamun ban hakuri, sai da muka matso dab da wa'innan matan naga wata zabgegiyar bulala ce ta darbejiya a hannun mai dukan, take naji na tsane ta raina yai kuna zuciyata na yin radadi, yaran da ake duka duk sunyi laushi idan su ya furfuto waje, adai-dai inda mai dugan taje wa'innan yan matan da aka hadani dasu suka tsaya, ba shiri nima naci burki.

Wannan firifet din tana ganin mu tayo kan mu tana dariya tace "sista Zamra daga ina haka". bata lura dani ba, dan kuwa na dan boye a bayan daya daga cikin wa'inda aka hadani dasu

Wacce aka kira da Zamra tace "wallahi daga staff muke"

Daya daga cikin matan da muke tare tace "ke dai Jamlah kullum kina cikin duty ko gajiya bakyayi wallahi da akwai kanwar ki a makarantar nan sunan ta sorry dan ta gama kadewa".

Wacce aka cewa Jamlah tace "hhhmmmm Saudat kenan ai shiyasa naki bari a kawo Sajida yanzu haka kano aka wullata".

Wacce nike bayan ta ce ta goce sai alokacin Jamlah ta lura dani dago kai nayi muka hada ido take naji gaba na yai mummunan faduwa har saida na sa hannu na dafe kirji na saboda yadda yake buga min.

Ita ma a bangaren Jamlah kusan haka taji faduwar gaban, sai dai bai kai nawa bugawa ba kallon kallo mukayi har saida Wasilah tace "yaya dai Jamlah kin San ta ne?".

Da sauri Jamlah ta dauke idon ta daga gareni tace "a a ban san ta ba naga dai tana kama da Wanda nasani ne".

Zamra tace "koda naji dan new commer ce yanzu haka hostel zamu kai ta".

Murmushi Jamlah tai daya kara fito da kyawun ta tace "yakamata ku han zarta kaita dan kuwa dole muyi mata welcome to......". Bata gama karasawa ba Wasilah tace "wai ke Jamlah wace irin muguwa ce? na lura Sam bakya jin dadi idan baki ci zalin yayan mutane ba to wallahi wannan bazaki dake ta ba idan ko kika dake ta duk abun da ya faru dake ke kika ja ma kan ki"

Tana gama fada tajanyo hannu na muka fara tafiya ganin haka yasa senior Zamra da Saudat suka biyo bayan mu Jamlah taji zafin kalaman da Wasilah ta fada mata don haka ta kuduri aniyar ramawa tako wani hali ne dan ba'a yi yar da zata gaya mata magana ba, kuma saita daki bushashshiyar yarinyar taga uban waye ya tsaya mata da har suke taqama tasan indai kudi ne ba za'a fi uban ta ba, ranta bace ta wuce batare da ta kumu kallon wa'innan yaran da take duka ba.

Munyi tafiya mai nisa sannan muka zo bangaren hostel din wani dogon daki ne muka shiga ba laifi dakin yana da girma bashida wani fadi can amma akwai tsayi, gadaje ne ajajjeri ko wanne gado sama da kasa mun samu tsira run dalibai a ciki, mun danyi tafiya a cikin hostel din saida muka kusan zuwa karshen shi sannan muka tsaya a saitin wani gado hannu senior Zamrah ta dora a saman gadon ta taba tace "Alhamdu lillah wai me sunan ki ne?" nace "Siddeeqah".
Sadaut na dariya tace "masha Allah sunan kanwata ne wacce take bina insha Allah zan kula dake kamar yadda zan kula da kanwa ta" sannan ta nuna min saman gadon tace "kin ga wannan gadon shine gadon ki" ta kuma nuna min kasan tace "wanna kuma na Fadila ne ita ce makociyar ki, wani dan soko ta nuna min dayake tsakanin gado da gado a gyare na ganshi tsaf kamar dakin amarya yaji ado da kyale kyale harda sif tace" nan kuma corner ce anan zaki aje akwatin ki naga baki zo da bokiti ba a kudin ki da yayan ki ya baki zan sa a siyo miki ".

To nace yayin da nafara taka matakalar da zan hau saman gadon ina dariya na dare abu na sai naji kamar mafarki nike saboda wannan sabuwar rayuwar.

Akwatin suka ajiye a cikin corner din sannan sukai min sallama suka wuce

Wata yarinya naga tazo ta zauna akan kasan gadon mu, hakan yasa naji ajiki na ita ce Fadila Saukkowa nai na mika mata hannun mukai musabaha tana dariya tace "sannu Sista ni sunana Fadeela kefa?" ta kare tambaya ta tana kama hannu na ta zaunar dani a bakin gadon ta

Bayan na zauna nace "nikam sunana ba na yayi bane ke nifa da ana canza suna da tuni na canza dan wallahi ji nike idan an kira ni kamar tsohuwa aka mai dani"

Fadeela na dariya tace "ba wani nan halan ma sunan ki yafi nawa fada min dai naji sai na yanke hukunci"

Nace "wai Siddeeqah fah".

Rungumoni tai tace "sister sunan ki mai dadi wallahi sunan ya min sosai ina kuma son mai sunan, ke in takaice miki in Allah yasa nai aure na haihu sunan zan sama diya ta kin San ko saboda me?"

Girgiza mata kai nai alamar "a a"

Tace "saboda in faranta ma Ammi sunan babbar yarinyar ta ne data bata har yau mun kasa gano ta, ko dayike gaskiya ba wani bincike mukai ba, saboda ko maganar Ammi ba taso da anyi mata maganar duk annurin da yake a fuskar ta za kiga ya dauke, amma idan ka nutsu da kyau ka lura da yanayin ta zaka fahimci tana cikin damuwa lokuta da dama idan na kalli kwayar idon ta ina hango soyayyar diyar ta a tare da ita duk da kamin Daddyn mu ya rasu ta haihu dashi yan biyu mace da namiji yanzu haka zasu kai shekara bakwai kuma kasancewa ta marainiya gaba da baya yasa Ammi ta cigaba da kula dani, saboda mahaifiyata ta a gurin haihuwa ta Allah yai mata rasuwa, kafin Daddy na ya auri Ammi yar aiki ya barwa ragamar kula dani saboda ita kanta mahaifiyata marainiya ce bata da kowa sai Allah, ba karamar wuya nasha a gurin Atine yar aiki ba saboda Daddyn mu ba mazauni bane idan yana gari kar kiga yadda Atine ke kulawa dani tun ban da wayau har na fara wayau bayan wasu shekaru na saba da wuyar da Atine ke bani duka da zagi wanka da ruwan sanyi horo da yunwa saka ni aikin da yafi karfi na, kwatsam sai wata rana na kwanta rashin lafiyar da banyi tunanin zan kuma bude ido na na ganni a duniya ba, da farko Atine tayi banza da lamari na ta cigaba da da tsangwama ta, bayan kwana biyu tazo ta sameni a bayi na kwance ko numfashi bana yi ruwa ta dibo ta shiga kwara min, amma ko alamar farfadowa banyi ba, kusan sau uku tana kwara min amma ko motsi banyi ba hakan yasa ta kwarma ihu game da fadin waiyo ni Atine na shiga uku, takai ta kawo ta rasa mafita can dabara ta fado mata akan ta gudu ta barni tasan idan aka kama ta baza ta tsira ba, haka kuwa akai tuni ta shiga dakin ta bata dauki kaya ba sai jakar ratayawar ta kamar mara gaskiya ta fito ta danyi waige waigen ta kana ta fara tafiya cikin sanda koda ta fito harabar cikin gidan sai tai tozali da abinda yasa zuciyar ta ta buga, wato Daddy ne ta gani tare da escorts din shi da alamar yanzu ya shigo gidan, tana sosa kai ta karasa inda yake kamar yadda ya saba yi mata aduk sanda suka hadu haba haba duk da kasancewar shi babban attajiri amma Sam baya kyamatar talakawa hasali ma kullum cikin kyautata musu yake tare da marayu, bayan Atine ta gaishe shi yace "ina zaki ne haka Atine naga kamar shirin fita ne a tare da ke? keda tunda kike a gidan nan baki taba fita ba saida izini na gashi yanzu ma ba dan mun hadu ba sai dai naga ba kyanan to ina kika bar min er leleta? mummunan mafarki nai a kanta shiyasa na dawo nigeria duba lafiyar ta saboda na samu nutsuwa"

Tuni gumi ya fara karyo wa Atine kan kace me saman kan hijabin ta ya jike jagab kasancewar a tsakiyar rana suke alhaji bai kawo komai ba ganin Atine bata da amsoshin shi yasa yace "wai lafiyar ki ko mutuwa akai miki naga ba kamar yadda na saba ganin ki ba".

Muryar Atine na rawa tace "eh ranka shidade Baba ta ce dama ta rasu to shine zan....."

Bata karasa ba ya daga mata hannu gami da fadin "haba Atine Ince ba yau nike da ke ba, ai bai kamata ki tafi haka ba da kin sanar dani ko a waya ne sai nasa a kai ki, amma yanzu muje na sallame ki tunda ina gari sai ki bar min shalele ta".

Gaban Atine na faduwa ta juyo cikin gidan tasan yanzu bata da halin fita tako ina masu tsaro ne gwara ta shigo in yaso ko bariki ne sai tai mishi da wannan shawarar ta samu nutsuwa, da karfin ta ta dawo gidan duk kuwa da karfin hali take kar ki tona kiji kasan zuciyar ta.

Akwai kofa ta musamman da Daddy yake bi saboda haka tanan yabi bai zarce ko ina ba sai ban garen sa inda ya gaji da kayatuwa dan zubin gidan sarauta akai mai kayan kawa kuwa da alatu ba'a magana saida yai wanka ya kintsa sannan ya fito dama ka'idar sa indai yana nan daukata yake mu tafi gurin cin abinci, aduk irin ranar sai najini sakayau kamar ina aljanna motsi kadan zanyi Daddy na zai ce me kike so saboda yana mutakar so na da kauna ta kuma tunda nike ban taba bude baki nace mashi ga abunda Atine take min na rashin kyautatawa ba

Koda fitowar sa sunana ya shiga kwala kira shalele shalele haka Daddy ke kirana, jin shiru yasa ya zauna akan daya daga cikin kujerun falo ya dauki rimot ya canza channel, sunan Atine ya shiga kira a karo na uku sai gata ta fito daga dakin ta da injin shara a hannun ta tana ja tace "Alhaji kira na kake dan na kunna inji kasan kara bazai bari inji ba"

"eh" Daddy yace mata
"shalele zaki kira min dan ina ta kiran ta naji shiru nasan yanzu ba lokacin baccin ta bane"

Duk da Atine taji mugun faduwar gaba amma sai ta dake tace mai "to"

TA shiga bangare na ko bayin da nike bata kalla ba ta danyi shawaginta ta dawo harda durkusawa akasa tace "Alhaji ban ga Fadeela ba na duba ko ina kuma da zan fita anan falo na barta tana kallo kuma nace karta je ko ina"

Da sauri Daddy ya mike yana fadadin "what? bazai yuyu ba Sam wannan ba mai yuyuwa bane"

Wani madanni yaje ya danna a jikin bangon falon , kan kace me saiga escorts dinsa nan sun shigo ce musu yai "Fadeela ce ta bata ku nemo min ita tana cikin gidan nan nima zan tayaku dubata"

Atine ya kalla yace "ina da ina kika duba?"

Bakin ta na rawa tace "ranka shidade iya bangaren ta kawai na duba"

Gyada kai yai alamun gamsuwa kana ya dubi daya acikin escort din yace "kai da ita ku tsaya anan ku kuma ku shiga ko ina ku duba banda bangare na"

Haka sukai ta binceka lungu da sakon gidan in takaice miki har farfajiya suka fito amma basu same ni ba, daya daga cikin su ne yai bangaren siminful shiga ciki yai wai ko zai sameni amma shiru, cikin rashin nasara duk suka hallara a falon idon dadi ya kada yai jawur saboda tsananin tashin hankali, iya kaduwa Atine kam tayi, dan kallo daya zakai mata ka fahimci rashin gaskiya atattare da ita

Komawa kan kujera Daddy yai jikin sa babu laka tagumi yai ya rasa ina zai sa rayuwar sa kadde ace mafarkin da yai ne ya tabbata idan kuwa hakane ya ci amanar Maryama wato mahaifiyata kenan gaban sa ya cigaba da tsanan ta bugu, can yai zunbur ya mike yana fadin "kun duba toilets kuwa?"

Gabad'ayan su suka bashi amsa da "a a"

Kafin yace suje su duba tuni kowa ya fad'a ciki duk inda suka san da bayi sai da suka buda kwatsam Daddy ya buda toilet din da ke daki na mai zai gani gudan jinin sa ce kwance a bandaki ko numfashi ba tayi, cikin jarumta ya qarasa ciki, zufa na keto mai dago ni yai kaina yai baya luu, cire mun jikakkun kayan jiki na yai kana ya fito dani durowa ta ya bude ya fiddo min wata doguwar riga fara kyal ya sanya min a kan gado ya shin fidar dani tsabar rudewa ya rasa me zaiyi, can ya tuna da wayar sa daya bari a falo, futowa yai ya dauka bai tankawa kowa ba ya dawo daki na, number Dr Tameem ya shiga laluba ringin biyu ya dauka Daddy bai wani tsaya amsa gaisuwar da Dr Tameem ke masa ba ya shiga shaida masa dalilin kiran nasa da cewa lallai-lallai yana son ganin sa yanzu.

To bayan Daddy ya kashe wayar zirga-zirga yashiga yi, yana cikin wannan yanayin Dr Tameem ya shigo ya iske sa, bayan Dr ya kalli fuskar Daddy ya dauke kai saboda kallo daya zakai wa daddy ya baka tausayi, inda nike kwance Dr ya nufo dama da akwatin gwaje-gwajen sa yazo nan take ya shiga dubani da bani kulawa ta musamman, cikin kwarewar aiki irin na Dr Tameem, da farko yaji tsoro sakamakon jin numfashi na baya harbawa, cikin ikon Allah da ambaton Allah da yake ya kara daukar hannu na ya kai kusan 4 minutes kana ya saki hannun yana mai godiya ga Allah jin bugun zuciya ta ya dawo, da sauri da sauri ya cigaba da dubani yana kuma fahimtar inda matsalar take kan kace me tuni yasa na fardado daga dogon suman da nai amma ban bude idanu na ba Daddy ne ya matso kusa dani yace "shalele ki yakuri kada ki tafi ki barni bani da kowa sai ke".

Naji abunda Daddy ya fad'a amma bazan iya bashi amsa ba saboda baki na yayi nauyi

Dr Tameem ne yace "kar ka damu Daddy da ikon Allah zata warke harma tafi da lafiya yanzu baza ta iya magana ba saboda rashin kuzarin da yake tare da ita bari na gama duba ta saboda naga abunda yake damun ta".

Nan gefe na Daddy ya zauna yanzu ya dan samu nutsuwa sai dan abunda ba'a rasa ba.

Atine kuwa tunda taga shigowar Dr take ta zagawa ban daki dan ta zaga yafi a irga, ta ruga ta san kashin ta ya bushe.

Bayan wasu awoyi da basu haura biyu ba Dr Tameem ne zaune akan sif din gefan gado na yayin da Daddy ke zaune a bakin gadon Dr yace "nayi mamaki da na sumu Fadeela na dauke da cutar ulcer da limoniya gashi ulsar har tana nema tazama kuronik".

Shiru Daddy yai saboda ya rasa abunda zai ce ido ya kura min yana jin tausayi na har cikin ransa ledar ruwan da ake kara min ya kalla ko rabi bai yi ba ido na a limshe ina bacci saboda allurar baccin da akai min.

Kallon Dr Tameem yai yace "na dade ina zargin wannan nanny din bata ba Fadeela abunci, saboda aduk lokacin dana fita da ita restaurant karka ga yadda take cin abinci kamar wata mayunwaciya, amma saboda na kara tabbatar wa zanje na duba ctv camera na".

Dr yace "yafi ma dan wallahi idan muka ga itace silar wannan ciwan sai na Illata ta, saboda wannan tsantsar rashin imani ne da butulci kaduba irin wannan ni'ima da take ciki komai fa yi mata kake Daddy". Ya kare maganar cikin takaici

Numfasawa Daddy yai yace "Tameem kenan har yanzu kai yaro ne baka gama fahimtar macece duniya ba to acikin wannan duniyar da kake gani akwai mutane masu son zuciyar su, marasa godiya ga ubangijin su, acikin su akwai wanda da ubangiji zai bashi gabad'aya arzikin duniya, baza su taba gani bare su gode masa ba,  da za su samu haram ci za suyi saboda zalinci da son kan su, shiyasa a kullum nike kara godewa Allah dayasa inada ga cikin bayin sa masu godiya saboda kaga duk wanda baya godewa mutane to baya godewa ubangijin sa".

Dr Tameem yace "Hakane Daddy wallahi son zuciya yai wa mutane yawa ko a gurin aikin mu ina ganin masu mutukar son kansu"

Daddy yace "Allah ya ganar dasu damu baki daya"

"ameen" Dr ya fad'a

Kiraye kirayen sallar la'asar aka shiga yi saboda haka Daddy ya Kalli Dr yace "kaje kai sallah ni yau bazan samu damar zuwa masallaci ba, idan ka fita falo kace wa escorts din suma suje suyi sallar amma abar mutane uku su tsare Atine".

"to" ya fad'a yayin da ya mike ya fice, kamar yadda Daddy yace mai haka ya sanar musu kana ya bar gidan.

In takaice miki labari koda Daddy ya idar da sallah bayan Dr ya dawo ya bar masa ni shi kuma ya

1 Comments On NI DA YAYA SADEEQ
avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment