Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ban taba gani ba, wallahi ni ba wai Maheer din ne bana so ba tsoro nike kada asiri na ya tonu a silar aure na da zaiyi".

"Da wannan dan wannan" Mama ta fada tana sa hannu ta goge gumin daya keto mata a goshin ta , wani kallo Zuby ta bits dashi da ita kadai tasan ma'anar sa, kamin ta tashi ba tare da tace komai ba tanufi dakin ta, wayar ta ta d'auka number Sadeeq ta shiga nema har sau uku tana kiran sa amma bai dauka ba

Shi kuwa Sadeeq zaune yake a dakin sa yana kallon kiran ta amma sai yaki dauka saboda ba karamin mamaki ta bashi jiyannan ba, gashi bata kirasa ba tun jiya bare ta basa hakuri shine yanzu zata kira sa tai masa dadin baki dan ta mayar dashi dan iska, Sam bazai dauka ba har sai tayi nadama yanda ko nan gaba baza ta maimaita makamancin sa ba.

Turo kafar dakin a kayi ko sallama batai ba ta shiga, a dai dai lokacin kiran Zubyn ya kara katsewa

Saida na turo dan karamin baki na nace "yaya gani yaya Farooq ne yace kana kira na".

Ganin yadda nike cika nike batsewa naba wa yaya dariya sai da yai Murmushin sa mai isar sa wanda yake kara baiyana ainihin kyawun sa yace "zo kiji magana zamuyi kika zo daure da dan kwali a kugu sai kace wacce tazo filin daga".

Sai alokacin na tuna  da dan kwalin da naci dan mara dashi ni kaina dariya abun yabani saboda na dade ban yi hakan ba kwan cewa na shiga yi yaya yace "a a ki bar abin ki ya miki kyau". 

Dan nesa dashi ta zauna yace "ikon Allah wai ni kike gudu to bari ni nazo na same ki na fada miki ba dukan ki zanyi ba magana ce zamuyi ". Ya karasa maganar a lokacin da ya zauna kusa da ita hannayen ta ya kama gami da tallafo habar ta  hada ido sukai cikin sauri tayi kasa da nata ba wai dan tasan kunya ba amma sai taga ya kara mata kwarjini bazata iya cigaba da kallon kwayar idon sa ba , shiko Sadeeq tausayin Siddeeqan  ne ya kama shi a karo na farko a cikin rayuwar sa tun bayan ta fara tasowa, wallahi bai taba tunanin akwai ranar da zata zo yaji tausayin ta ba sai gashi rana kwatsam wai tana bashi tausayi, bai san sanda ya rungume ta a kirjin sa ba yana jin bai kyauta mata ba, Siddeeqah dai ta zama kamar mutum mutumi cikin ta har ya duru ruwa tsoro ya kamata tasan yauma aljanin yayan nata sun kuma tashi, tana so ta dago tana tsoro, saida ya gaji dan kansa ya sake ta yana shafa bayan ta yace "dan Allah Siddeeqah kiyi min wannan alfarmar ki daure ki tafi wannan makarantar wallahi saboda ina son ki ne nayi miki wannan gatan".

Da sauri Siddeeqah ta dakatar da shi ta hanyar fadin "ya isa haka yaya duk maganar da zamuyi a tsakanin mu kada ka ambaci so domin babu shi a tsakanin mu har abada ka fada min ba zaka taba sona ba kamar yadda nima ban taba jin sonka dai-dai da rana daya a cikin zuciya ta ba, na yarda zan tafi idan har kayi alkawarin za kabi duk wani sharadi da zan fada maka".

Bakin Sadeeq na rawa Yace "naji fada min zan bi duk abinda kika ce".

Ta cigaba da cewa "na yarda zan je idan har ka yi alkawarin zaka sake ni idan nagama karatu lokacin na girma na kara wayau ta yadda zan samu irin mijin da nike so na aura, amma ni wallahi Sam ban dace da kai ba yaya". Ta fada tana dago kan tu suka hada ido tayi sauri tai kasa da nata saboda kwarjinin sa.

Yana mamakin Siddeeqah lokuta da dama idan tayi wata maganar ko babbar mace albarka koda yake ba abin mamaki bane zamani ne dan ga yaran da basu kaita nan ba suna abin da ba kowace babbar macen ba itama dan ta taso a kauye ne shiyasa take da wayan kauye

yace "in dai wannan ne mai sauki ne zan sake ki tunda ke ce kika bukaci haka amma me zaki cewa su Daddy da Momy idan suka bukaci sanin dalili?".

Sai da ta tashi daga inda take tayi tsallan murna tace "bani ce zan basu amsa ba kaine ya dace da ka basu amsa ko dai ka fada musu gaskiyar bama son junan mu ne ko kuma kayi musu karyar da har abada bazasu gane ka ba kaga sai ka je ka auri wacce kake so, nima na auri wanda nike so".

"to". Kawai Sadeeq yace dan tafara gundurar sa da wannan maganganun nata da yake daukar su kamar tatsuniya

Bai san ita kuwa siddeeqah har cikin ranta take fada masa wannan maganar ba

Tace "ko kaifa yaya  hannu ta mika masa tace mu kulla abota yaya nayi maka alkawari daga yau zan dunga jin maganar ka zanyi kokari na zama mai nutsuwa kamar yadda kake so zan dunga yin duk abunda kace nayi ina son wannan abotar tamu ta fara daga yanzu zuwa lokacin da zaka sake ni".

A tunanin Sadeeq Siddeeqah ce bata da wayau dan shi gani yake ya gama da ita shiyasa komai tace yake yarda, yanzu ma ya yarda su kulla abota din har zuwa ranar da zata kare secondary school din nata ya bata takardar ta

Hannun sa ta kama tace "yaya tashi muje falo ka fadawa su Daddy na yarda".

Mikewa yayi kamar yadda tace ta shiga jan hannun sa suka soma tafiya tana gaba yana biye d a ita a baya a haka suka fara taka step suna saukowa, tuni suka fara daukar hankalin wasu daga cikin mutanen falon da suka lura dasu kama daga Daddy Umar Jiddah da Ummee banda Farooq da Khadija da suka zauna akan kujerar da tabawa step din,  Momy kuwa bata gurin tana bedroom taje daukowa Daddy wayoyin sa daya manta, gaskiya sun burge sun bada sha'awa kuma sun dace da junan su

Ahaka suka karaso fuskokin su dauke da nishadi
Ba karamin mamaki Momy tayi ba alokacin da ta gan su, haka ma Daddy da sauran yaran gidan  

Koda suka karaso falon kan kujera Siddeeqah tai wa Sadeeq masauki inda itama ta zauna kusa da shi hannun ta na sarke da nasa sai Murmushi take tana kara shige wa jikin sa shi kuwa Sadeeq daure wa kawai yake dan bai saba da wannan sabon al'amarin ba yana so yai mata tsawa yana tsoran ta birkece masa

Momy da Daddy kuwa addua suke acikin ran su Allah yasa lokacin haduwar kan yayan sune yazo Allah yasa su d'aure ahaka

Comment
Share
Vote

NI DA YAYA SADEEQ

·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Chapter 28

______Shi kuwa Farooq tsabar mamaki sai mutsuka ido yake yana budewa gani yake kamar a film yake kallon su.

can Daddy ya numfasa yace "dama kai niki jira yanzu nike cewa Umar yaje ya kira min ku  dan lokacin tafiya ta yayi".

"Siddeeqah". Daddy ya kira suna na cikin wata murya mai nuna ana jin tausayin wanda akai wa ita".

"na'am" nima nace bayan na zare hannu na daga jikin yaya na daga kai muka hada ido da shi

Ya cigaba da cewa "shin kin amince zaki tafi makarantar kwana?".

Ina wasa da yatsaun hannu na nace "eh na amince Daddy".

Sai alokacin Momy dake tsaye ta zauna tana fadin "Alhamdu lillah Allah yasa hakan ne yafi alkairi".

Take yaya Sadeeq ya sauke ajiyar zuciyar da ko wannen mu sai da ya dago kai ya kalle shi, ni kuwa takaici ne ya kamani ganin yadda yake murna zai rabu dani sai kace zai rabu da musifa, lallai ma yaya tabbas zan nuna maka nima macace kuma zan iya yin duk wani abu da mata suke yi wajen burge mazajen su, sosai nayi nisa cikin tsara yadda abubuwa zasu kasan ce, fir gigit nai a dan tsorace na dawo hayyaci na  sakamakon tabani da kafa da yaya yai.

Daddy yace "Siddeeqah lafiya tunanin me kike yi haka? bayan na hana ki yin dogon tunani irin wannan, kina yar karamar ki  Ko so kike hawan jini ya kama ki? Ki mutu tun kamin lokacin ki yayi?".

Baki na narawa nace "A a Daddy insha Allah na daina daga yanzu".

Yace "Masha Allah, Allah yai muku Albarka ni zan tafi ki kula da kanki banda kula kwayen banza karatu ne ya kaiki shi zakiyi "

Nace "to Daddy nagode insha Allah bazan baku kunya ba".

Sai da ya sallami duka yaran gidan, dama Momy ya ruga ya sallame ta, kana yabi ko waccen mu da kudi masu kauri, Gaba dayan mu muka dunguma zuwa harabar gidan saboda muyiwa Daddy rakiya saida muka ga tafiyar shi sannan muka dawo gida, Momy ta daura daga inda Daddy ya tsaya nasiha take min mai ratsa zuciya jiki na duk yai sanyi, son Momy da kaunar ta yana dad'a ratsa ilahirn jiki da bargo na, saboda yadda take kula dani, da nuna min so da kauna.

Bayan ta gama min nasihar tace "naje na kara shiryawa".

Kallon Ummi da Khadija nai muka hada ido naga jikin su yai sanyi Umar kuwa harda kwalla, jiki na a sanyaye na mike  na haura sama ba wani wankan na sake ba kaya kawai na sauya  i zuwa riga da sikel na atamfa dinkin bai min yawa ba kuma bai kamani ba, sannan na dauko hijabi na nasaka ko da na sauko a tsaye na samu Yah Sadeeq da Farooq da wani katon akwati a gaban shi, yana Murmushi yace "yauwa muje ko, ke muke jira".

tuni kwalla ta fara wanke min fuska ta nace "amma yaya baka kira min Inna ba".

Shafa keyar sa yai  yace "ai na manta gwara da kika tuna min".

Hannu yasa a aljihu ya ciro wayar sa, amma sai ya rasa wa zai kira sanin Inna babu waya a hannun ta dama da ta Farooq suke gaisawa "saida ya dan bata rai yace "kina da rigima Siddeeqah sanin kanki ne Inna bata da waya"

Goshi na dan dafe, tuna cewar batada wayar.

Yace "amma dai ki bari zan san abin yi tunda ni yau zan koma zan baki number ta idan kinje makarantar sai ki bama wata senior ta kirani sai na hada ku kuyi magana".

"to" kawai nace

har bakin get su Momy suka rako ni, in rungume wannan in saki wannan haka dai nan ta kuka Khadija da Ummi da Umar suna tayani, yayin da Momy ke bamu hakuri kamar kar mu rabu da juna saboda sabon da mukayi,  sabanin Jiddah da ko Allah ya kiyaye hanya bata ce ba sai kallon banza da take bi na dashi, tana cika tana batsewa, yi  nai kamar ban gan ta ba saboda yanzu ba lokacin fada bane a gurina.

Da kyar yaya ya lallashe ni na shiga mota inajin raina babu dadi, tuni daman yah Farooq ya shiga sannan shima sadeeq din ya shiga mai gadi ya wangale get muka fice, su Momy nayi mana Allah ya sauke ku lafiya.

Yaya Farooq ne ke tukin yayin da Sadeeq ke kujerar me zaman banza ni kuma ina gidan baya ji nike gabad'aya rayuwar ta dagule min tafiya ta fara yin nisa dan barci har ya fara dauka ta

* * * * * * *

Zaune take kan dan madaidaicin gadon ta hannun ta rike da wayar ta sai cije lebe take tana tsaki wai ita Sadeeq zaiki dagawa waya to wallahi bai isa ba tun da yace yana son ta sai ya aure ta ta fada afili yayin da tayi  kwafa.

Number Lubansy ta danna ta  kira har tafara ringing sai kuma ta kashe saboda tasan itama fushi take da ita baza ta d'auka ba idan tana son su shirya sai dai fa ta shirya taje gidan su, gashi ita kuma yanzu bata jin zata iya fita saboda zuciyar ta babu dadi, safa da marwa ta cigaba da yi gabad'aya ta rasa me zatai, can ta tuna da group din su na madugo aran ta yltace "bari na dan hau online ko na samu na rage damuwa" gefan gadon ta zauna kana ta dauko wayar ta shiga cikin whatsapp din nan ta tarar da sakonni masu yawa amma duk bata tsaya bi ta kansu ba, abinda ya kaita kawai shi take so tayi, bayan ta shiga cikin group din a hankali tafara karanta sakonnin da akayi bata nan bata jima tana duba chart d'in ba ta fahimci cewa fada a keyi sakamakon wata da tayi left cikin sauri da sauri ta cigaba da duba sakonnin har zuwa inda aka tsaya da firar take ta fahimci Baddy ce tai left kuma ana kyautata zaton yar leken asiri ce gabad'aya hankulun officials da members din gidan a tashe yake saboda idan asiri ya tonu ba karamin yaki za ai ba, tuni Zuby ta shiga cikin firan inda har take bada labarin tayi magana ma da yarinyar har take ce mata "hajiya Tubalas ce ta kawo ta"

Hajiya Tubulas da jin an ambace ta, ta shiga auna ashar tana cewa "kada ayi mata sharri ita yanzu ko wuqa a ka sa mata a wuya a kace ta siffan ta kammannin Baddy to sai dai a yanka ta dan bata san ta ba".

Shugabar kungiyar madugo tace "ya kamata a hada meeting na gaggawa saboda a kawar da wannan gagarumar matsalar".

Tubulas tace "gaskiya bazai yuyu ba saboda a cikin dokokin kungiya ba a meeting sai ranar litinin din da tazo a cikin karshen wata, kuma kunga yau talata 28 ga wata, nasan kunsan cewa  karya doka daya ta wannan kungiyar dai dai yake da tonuwar asirin mu gabaki daya".

Sai alokacin Turai ta tuna da wannan dokar kuma gaskiyar Tubulas ne karya daya daga cikin dokokin kungiya babban laifi ne dan har gwara su dauwama a cikin wannan tashin hankalin da suke ciki, amma abin dubawa anan shine wata uku da suka wuce duka watan bai kare da litinin ba, kuma da alamar wannan ba ba da litinin zai kare ba, tunda yau talata.

Duk kannin su sunyi na'am da batun Tubulas saboda haka suka ce a nemo wata mafitar amma haka sukai ta fama duk inda suka bi sai suga babu hanya

Zuby dai gajiya tai ta sauka daga online din tana mamakin yadda Baddy ta ci amanar su, tasan tabbas kungiya bazata bar ta a haka ba sai ta dauki mummunan mataki akan ta.

Kofar dakin ta taji ana bugawa da sauri taje ta bude ba tare da ta tambayi wanda yake buka kofar ba, koda ta bude Lubancy ce ta shigo tana wani shan kamshi bakin ta dauke yake da chingom tana taunawa yana kara kas-kas haka dai tai ta yamutsa baki tana yauki, bayan Zuby ta maida kofar ta rufe tazo ta rungume ta tana cewa "aminiya nayi missing din ki". Lubancy taso sharewa amma saita kasa saboda a matse take tuni itama ta rungumo ta tana sauke ajiyar zuciya, basu tsaya wata wata ba suka shiga cire ma juna kaya suka fada kan gado suna nishi tuni suka fara shafe-shafen juna suna sauke ajiyar zuciya.

idan kida ya sauya, rawa ma canza ta ake yi ganin abin yafi karfi na yasa na fito daga dakin naja musu kofa, ina yi musu adduar Allah ya shirya su dan wannan dabiar bata mutanen kwarai bace wace irin musifa ce wannan da mace take neman yar uwar ta mace yayin da shima namiji yake neman dan uwan sa namiji, shiyasa annoba bazata rabu damu ba saboda aduk lokacin da akasumu saukar annoba to sabon Allah ne yai yawa akasa, kuma duk masu wannan dabiar a wuta zasu dauwama.

wa'iya zu billah.

* * * * * * * *

Yunwar da ta fara kwakular ciki nane ta tashe ni daga nannauyen baccin daya dauke ni na manta a mota nike saboda haka nai mika gami da yin juyi, ai kuwa cikin rashin sa'a na fada sakon mota inda ake saka kafafu, ihu na fara ina kiran sunan yaya da duk ya bi ya gaji sai mita yake wai Farooq baya gudu ". Shi kuma Farooq na cewa" in ba sama kake so na tashi ba ai wannan gudun ya isa ".

Ihu na ne ya katse musu firar su da sauri yaya ya juyo da kansa cikin motar yana fadin "subhanallah garin yaya haka ta faru maza tashi". Ya karasa maganar yana zuro da hannayen sa da kyar na iya temaka masa ya daga ni, bayan na gyara zama na akan kujera nace "yaya wai har yanzu bamu kai ba ni na gaji yunwa nike ji". Na karasa maganar cikin sigar shagwaba, nuna min Farooq yai yace "duk laifin shi ne kwata kwata baya sauri tafiya yake kamar wanda yake tsoran taka kwalta".

Nace "to ni yaya yunwa nike ji"

Yace "to bari mu karasa can gurin ina kyauta ta zaton karamar kasuwa ce sai muje baza'a rasa abin tabawa ba". Ya fad'a yana nuna min wani guri da nike hangan mutane

"To" Nace yayin da na hada kaina da gwuiwa ta

Ba mufi minti 7 ba muka karasa bakin gurin, kasuwa ce yar karama mata da maza sai zurga zurga sukeyi, yara da manya Farooq yace "banda abinka Sadeeq me zamu samu anan da zamu ci?".

Yace "mu fita ahaka ba zamu gane ba kuma can ma kamar masallaci ne mayi sallar azahar gashi ma kamar ana kiran la'asar duka sai mu sauke nauyi,

Yah Sadeeq yace" ki zauna a mota bari mu fita mugani ko zamu samu abinci".

Ban bashi amsa ba suka fita harda rufe motar

Basu wani jima ba sai ga Yah Farooq ya dawo da kwano a hannun shi da kwarya, bayan ya bude motar ya miko min na amsa, shi kuma ya juya 

Koda na bude kwanon danbu ne na gani yaji gyada da zogale yayin da ita kuma kwaryar fura ce acikin ta me rai da lafiya

Ba tare da nayi bismillah ba na shiga cin danbun, duk da yawan danbun saida na kusan yin rabin shi saboda ina mutukar son danbu a rayuwa ta, bayan na koshi kuma na dauki kwaryar fura itama na fara sha saida naji na cika cikina dam, har inaneman gurin numfashi sannan na hakura ba don bakina ya koshi ba sai don cikina da ya koshi

Gyatsa nike so nayi kozan dan ji dadin ciki na amma taki zuwa saboda haka nai ta bude baki ina Jan iska

Can saiga su yaya nan sun dawo hannun Yah Sadeeq dauke da gorar ruwa bayan sun zauna yace "kin rage dan bun?".

Nace "eh".

"yauwa miko wa Farooq danni bazan ci ba furar zan sha ai itama kin rage?"

"eh nace yayin da na miko mai kwanon danbun dana furar

A mota suka ci bayan sun gama  suka je suka mayar da kwanon da kwaryar

Daka bisani muka kuma daukar hanya

" Nace yaya amma dai mun kusa zuwa ko?"

" eh mun kusa bai fi sauran mu 30 minutes ba mu karasa, ya nuna min wata katan ga da muke ta shigewa yace "nan kinga duk makarantar ce, zaro ido nai nace" kai yaya gari guda haka ".

Yace" eh har tafi haka girma bari muje ki gani".

Haka dai nai ta yiwa Sadeeq surutu yana biye min duk da fuskar sa babu wal-wala amma duk tambayar da nai masa yana bani amsa, a raina nike cewa "nasan yana tsoron nace na fasa ne shiyasa yake amsa min".

* * * * * * * * * * *

Aban garen Zuby kuwa bayan sun gama sheke ayar su tashi sukai suka shiga wanka kamar kullum nan ma saida suka bata lokaci suna tsotse-tsotse kana suka fito fiskokin su dauke da nishadi suka shirya cikin wata doguwar riga me ruwan kwai tana da laushi matuka Lubancy tace "ina zamu yau?"

Zuby tace "gurin shakatawa man, yauwa naga baki hau online ba meyisa".

Lubancy tace "banida data ne, wani abun ya faru ?"

Zuby tace "kwarai ma kuwa ina wannan yarinyar da kika sameni ni da ita jiya?".

Tace "eh na tuna ta".

Zuby tace "ashe yar lekan asiri ce yanzu haka tayi left a kungiya kuma ni fa cemin tai turai ce ta kawo ta ashe karya tai min".

Lubancy tace "nifa shiyasa tun na kalli yarinyar naji batai min ba kwata-kwata kuma yanzu wani matakin aka dauka?".

"Har yanzu dai ba'a samu mafita ba kasancewar wa'innan tsinannun dokokin kungiyar na aiki, ke nifa abun ya fara isa ta gashi yanzu wlh ina cikin damuwa" Zuby ta fada tana sauke ajiyar zuciya

Kusa da ita Lubancy ta matso ta ce "kawa ta me ke damun ki fada mun naji ko zan iya miki magani".

Nan Zuby ta kwashe labarin komai yadda sukai da Abba ta fada mata hankalin Lubancy a mutukar tashe tace "da matsala gaskiya ya zama dole a fada wa yan kungiya saboda su taimaka mana da shawara kinsan a ka'ida ko aure kai baka daina wannan harkar da zaran ka bari kungiya zata tona maka asiri kuma kinga Maheer ba kalan mazan da zasu dauki raini bane".

Gwauran numfashi Zuby ta sauke tace "wallahi kawa ta shiyasa duk na bi na damu amma dai mu dan jinkir ta kafin mukai maganar kungiya idan Abba ya dawo zan roke shi".

Lubancy tace "to Allah yasa a dace".

"Ameen" ta fada yayin da ta mike ta dauki katon hijab din ta gami da fiddo nikabin ta a jaka tace "kawa tashi ki shirya mu tafi".

"To" Lubancy ta fada yayin da itama tai shiga kamar yadda Zubyn tai kana suka fito

Mama mama Zuby tai ta kwala mata kira daga can ciki Mama ta amsa

Zuby tace "kina ina ne Mama?"

tace "ina kitchen"

Shiga kitchen din sukai inda suka tarar da ita tana nuna ma mai aiki wani abun gasa kaza da aka siyo shi sabon yayi.

Fuskar Mama dauke da fara'a tace "sai ina kuma?"

Lubancy tace "wallahi Mama mun gaji da zaman gidan ne shine zamu fita ba jimawa zamuyi ba".

Tace "to adawo lafiya"

"Allah yasa".

* * * * * * * * * * *

Wangala-wangalan get yaya Farooq ya wuce guda biyu, kana yai tafiya marar tsayi a bakin wani guri yai farkin danaga an rubuta staff room, kasan cewar na iya karatu amma ban san ma'anar shi ba,

Shiru yadan ratsa mu kana yaya Sadeeq yace "mu sauka man".

Yah Farooq ya fara fitowa sannan sai yaya Sadeeq, bayan ya fito yazo ya bude min kofa yace "fito mun kawo, bayan mun fito office-office mukai ta shigewa har muka isa wani office dan madai-daici, shiga mukai da sallama dauke abakin su yaya, inda muka sami wani malami a zaune da takardu a gaban shi yana ta dubawa, da alamar shine abokin yah Farooq ganin su yaya Sadeeq ya aje abinda yake, yah Sadeeq ya mika masa hannu, yana Murmushi ya amsa, hakama yah Farooq bayan sun gama gaisawa yai musu nuni da su zauna akan wasu kujeru da aka tanade su saboda baki,

Babu abinda nike sai zaz-zare ido ina kara shigewa yaya.take naji bazan iya zama a wannan dokar Dajin ba gaskiya to wai ma in banda  abun mutane taya za azo dokar daji ayi gini ace wai makaranta, ni dai gaskiya bazan zauna ba.

Da turan ci malamin yai min magana, ban san me yake nufi ba yaya Sadeeq yace " ya sunan ki yace?"

Nace "Siddeeqah Suleiman".

Yace "suna mai dadi, ku tashi na raka ku ofishin shugabar makarantar".

"to suka ce yayin da suka mike a tare, muka fito ina ta ganin dalibai na wucewa dai-dai haka, wani office din muka kuma shiga ba laifi ofishin babba ne kuma an dan kawata shi wata mata ce muka gani zaune akan kujera fuskar ta dauke da gilashi ba laifi matar ta dan manyan ta fara ce sosai kamar ka taba jini ya fito, dagani hutu ya zauna a jikin ta, tana da kyau dan irin doguwar fuskar nan gare ta tana da manyan idanu da dogan hanci ga dan karamin bakin ta, sanye take cikin kayan alfarma tana dan juya kan kujerar da

1 Comments On NI DA YAYA SADEEQ
avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment