Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata kafa duk rashin kunyar da zata mai bazai tanka mata ba

"Momy ina kwana". Siddeeqah ta fada lokacin data karasa kicin inda Momy ke wanke fatatus

Cikin sakin fuska Momy ta juyo ta kalleni kana tace "lafiya lau yan makaranta har kin shirya?".

"eh Momy".

"yau ba saikin tayani ba kije falo ki zauna ga Umar can sai kuyi fira kamin mu gama, saboda kada kayan ki su baci kije makaranta a dunga yi miki dariya".

"to nace" na fito falo inda na tarar da Umar shi kadai a zaune, kusa da shi na zauna kana nace "Umar". Da sauri ya dago kai ya kalle ni, na cigaba da cewa "da gaske dai makarantar kwana yaya zai kai ni shikenan bazan kuma sake ganin ku ba sai na dauki tsawan lokaci? wallahi ni an cuce ni an raboni da Inna gashi yanzu kudun da nike gani nike jin dadi za'a rabani da ku". Tuni kwalla ta fara zubomin ban damu na share ba saboda kukan yafi min Alkairi akan shiru, sosai Umar ke lallashi na amma Sam naki sauraren sa kuka na nike wuy-wuy, acikin wannan halin Daddy yazo ya isko mu Tambayar Umar ya shiga yi abinda yasani kuka Umar bai boye masa komai ba ya fad'a masa, Daddy ya ce "haba mai gaskiya indai akan makarantar da zaki tafi ne kike kuka to an fasa babu inda zaki ai na dauka da yardar ki zai kaiki ashe gaban kansa yayi".

Karaf maganar da Daddy yayi sai a kunnen Sadeeq saboda sauko war sa daga sama kenan kan yakara so falon kasa ya tsinkayi kalaman Daddy

Cije leban sa yayi da karfi bai saki ba saida yaji zafi afili yace "wannan wace irin yarinya ce mai naci da taurin kai yanzu mai take nufi ya riga yagama tsara yadda komai zai tafi, amma yanzu Daddy yana neman ya kofsa masa".

Bayan ya kara so falon har kasa ya tsugunna ya gaida Daddy ba yabo ba fallasa ya amsa mai

Kana Sadeeq din ya nemi kujera ya zauna yana kitsa abubuwa da dama a cikin ransa

Haka itama Siddeeqah babu abin da zuciyar ta bata raya mata game da Sadeeq ba sai yanzu take kara tabbatar wa da zuciyar ta cewa tabbas fa yaya ba son ta yake ba, idan ba haka ba mai yisa bai kai daya daga cikin kannan sa ba? Bata wannan amsar amma tabbas ita ko za'a kashe ta bazata wannan makarantar ba ta gwaumace ta mutu a jahilar ta

* ** * * * * * * * *

Kwance take kan gado tayi dai-dai abinta da ganin ta hankalin ta kwance yake sai sharar baccin ta take.

Ringing din wayar ta da ake kira shiya ta data daga nannauyen baccin daya dauketa tun jiya dan ko Sallar asuba batayi ba.

A firgice ta farka ta lalubo wayar ta daga karkashin filo bata tsaya duba wanda yake kiran nata ba ta d'auka ta kara a kunne, daga muryar sa ta gane Abba ne, ban san me yace mata ba naji tace "to Abba gani nan ".

Bata tashi a lokacin ba sai da takara kusan 13 minutes sannan ta tashi tsaye tana mika da hamma da Alamar baccin bai isheta ban daki ta fada tayo wanka a gurguje bayan ta fito ta shafa nayukan ta kana tasaka atamfa riga da zani rafa ta dan fesa turare mai sanyin kamshi ta daura dan kwalin ta ta fito cas da ita, saida ta kalli kanta a madubi irin wanda yake nuna mutum daka sama har kasa kana tayi Murmushi ta fito dakin ba tare da tayi sallar asuba ba wannan dama dabi'ar ta ce hada sallah ko ba abinda take yi bazata taba yin sallah akan lokaci ba sai lokacin ta ya fita an shiga na wata

A falo ta sami Mama da Abba suna karya wa akan dinning zama ita ma tayi suka da Abbah aka shiga karya wa da ita suna dan taba fira akai-akai.

Bayan sun gama mai aikin su ta zo ta kwashe kwanukan kana Abba ya koma kan kujera ya zauna "sha lele tashi ki dauko min rimot". Abba ya fad'a yana duban Zuby da mikewar ta kenan a kan dinning da "to". Ta bashi amsa bayan ta miko mai zama tayi kusa dashi akasa tana ja mai yatsun kafa, saboda tasan Abbah nasan haka

* * * ** *** * *
Kowa na karya wa amma ban da Siddeeqah da tayi ta gumi ta tsurawa filet din gaban ta ido Wanda yake a cike da soyayyan dan kalin turawa da kyau

"Momy tace Wai ke kuwa lafiyan ki lau gaba daya yau ban gane miki ba ko akwai abinda ke damun ki ne?".

Ga dukkan alamu hankalin ta baya tare da ita saboda tayi zurfi cikin tunani, lura da haka yasa Khadeeja dafa kafad'ar ta tace "sisi wai maye haka irin wannan tunanin kina yar karamar ki".

Fir gigit Nadawo daga duniyar tunanin da na Lula ba tare da na gano nazarin me nike yi ba

Kallo na Momy tayi kana ta kawar da kai Daddy yace "ci abincin kinji ki daina irin wannan tunanin babu kyau".

Kai na daga kana na fara cin abincin haka nai ta turawa kamar ina cin magani haka nike jin dan danon abin cin

Bayan mun gama kan mu tashi daga dinning din Daddy ya kalli Sadeeq yace "kai Sadeeq na soke tafiyar Siddiqah zuwa makarantar kwana ba dani ba za'ai wannan zalin cin kaji na fada maka wannan ai zalinci ne, na dauka da yardan ta kayi komai ashe san zuciyar ka ka aikata, na baka daga nan zuwa lokacin da zan yi tafiya ka lallashe ta idan ta yar da to idan kuwa bata yarda ba sai dai ka kaita wacce yan uwan ta suke zuwa, kada kuma ka man ta zuwa anjima zan tafi bayan azahar ".

Daddy na gama fadar haka ya bar gurin

Saboda kaduwa har da zufa ke karyo wa Sadeeq Sam baiyi tsammanin abin zai kai haka ba kallo na yayi muka hada ido na ban ka mai harara cije Leban sa na kasa yayi nima nayi yadda yayi Momy na lura damu bata ce komai ba ta Mike zata bar dinning din yaya Sadeeq yai sauri yace "Momy dan Allah kiyi wani abu akai kice wani abu please nasan Daddy na jin maganar ki".

Tace "kaga Kaga ka fita ido na tun wuri kayi abinda Daddyn ku yace maka dan yanzu kayan sa zan je na shirya babu ruwa na ni".

Ta na gama fada ita ma ta bar wurin

Ya mutsa fuska ta nayi nima kana na Mike tsaye nayi mika harda dan ihu na hada kana na bar gurin ina dariya kasa kasa nasan Sadeeq ya tsani haka da ace Daddy bai ce sai na yarda ba da tuni ya kai min duka

Shikuwa Sadeeq mamaki yake yadda karamar yarinya kama ta ta iya makir ci

Tashi yayi ya haura sama dakin sa ya shiga kana ya dauki wayar sa daya barta akan gado kan kujera ya koma ya zauna kana ya shiga danna nambobin Farook ya ko ci sa'a ringing 3 Farooq ya dauka kiran daga can ban garen Farooq yai sallama inda Sadeeq bai amsa masa sallamar ba kusan ita ce dabi'ar sa ba kowa yake ma sallama ba kuma ba kowa yake amsa wa ba, sai cewa da yai "Malam kana ina ne?".  Ya bashi amsa da "gani na kusan shugowa Abuja dan wallahi anyi min transfer zuwa Yobe shiyasa nazo na dauke ta na kaita da wuri nima na samu na shirya".

"kamar dole a kasa sa yai magana a dakile yace yobe fa kace to Allah ya tsare".

Ran Farooq bace yace "dan iska saboda ba kai bane aka mawa dole kayi min isgili, insha Allah kai ma sai anyi maka in dai transfer ce ruwan dare ce, dan wannan sabon matemakin kwamishinan bashida kir ki".

Ko a jikin Sadeeq yace "to sai me ai dama aiki nace zanyi kuma idan anyi min transfer din akan aiki ne kaga kuwa mai zai dame ni?".

Cikin jin haushin kalaman sa Farooq yace "babu dama yanzu baza kasan inda matsalar take ba sai nan gaba".

"Am kaga wai fa akan yarinyar can na kira ka".

"Wace yarinyar?". Farooq ya tambaya duk da ya gane akan Siddeeqah Sadeeq yake magana amma sai yai masa bariki

Cikin kosawa da maganar Sadeeq yace "wai meyisa ka fiye surutu ne kafi son aita maimaita magana daya, bayan kasan yanzu bani da wata matsala da ta wuce waccan yar kyauyen".

Cikin zolaya yace "kai malam ni bana son gulma ka fito kayi min bayani sai kace matar ka amma sai wani boye-boye ka ke".

"amma kai ba karamin dan iska bane ni zaka raina wa hankali sai anjima na ma fasa fada maka abinda zan fada".

Farooq na dariya yace "matsalar ka ce wannan, nan da 30 minutes zan kara so insha Allah kace mata ta shirya".  Yana gama fada bai jira amsar Sadeeq ba ya kashe wayar

* * * * * * * * * *
"Shalele".

"Na'am". Abbah

Wai kuwa kin tuna aboki na Dr Usman da yake da zama a dubai?".

" Eh Abbah ".

"yauwa kin San ai yana da d'a, da yake karatu a kasar misra?".

"eh Abba kan ya tafi ma ai yana zuwa nan ko ba Maheer ba?".

"shi fa ashe baki manta dashi ba na dauka kin manta dashi to kinsan shi kadai Dr ya mallaka kamar yadda nima ke daya na mallaka".

"eh hakane Abba".

"Masha Allah na zauna ni da Dr din munyi magana har mun gama yanke hukunci zamu hada ku aure kar shen watan nan zai dawo dan ya kammala karatun sa a harkar kasuwan ci, kuma da ya dawo sai biki babu bata lokaci".

"amma Abbah".

"abba me? Shalale a wannan karon ko sau daya ki daure kiyi min abunda nike so duk da nasan kina da Wanda kike so amma ni wannan ne zabi na".

Yana gama fadar haka ya mike gabad'aya Zuby jin ta take kamar ba ita ba saboda tasan Maheer mutum ne mai shegen sa ido da taka tsan tsan akwai shi da tsoran Allah kuma yana son mace mai addini dan yasha fada mata, shin ma cewa yayi yana son ta Ko kuwa dai iyayen su ne suke son su hada auren?
Tashi tai daga zaunan da take ta shiga yin safa da marwa tana zagaye dakin, a haka Mama ta shigo ta cin mata

* * *

Please

Comment

Follow me

Vote

I love you all Allah ya bar zuminci da kauna

Dan Allah kuyu following dina please

NI DA YAYA SADEEQ

TUNATAR WA

Du'aah

Bakyada Miji ?👈🤴
To Allah Ya baki Miji nagari Alfarman wannan watan🤲

aurenki bayan Sallah ne?👈👸
To Allah ya baewa Iyayenki abunda za ayi auren Alfarman wannan watan🤲

Kinyi aure ?👈🧕
To Allah ya baku zaman lafiya da kwanciyar hankali ke da mijinki Alfarman wannan watan
🤲

Bakya haehuwa? 👈😥
To Allah ya baki haehuwa da 'yaya masu Albarka Alfarman wannan watan🤲

Ciki ne dake ? 👈🤰
To Allah ya sauke ki lafiya musha biki Alfarman wannan watan🤲

Kin Haehu ?👈🤱
To Allah ya bar maki 'yayanki ya sa masu Albarka Alfarman
wannan watan🤲

Kina samun sa6ani da mijinki? 👈😫
To Allah ya dae dae ta atsakanin Ku ya sa Ku fahimce junan Ku ya kuma qara gam din soyayya har qarshin rayuwar ku Alfarman wannan watan 🤲

Kina da masifaffiyar kishiya ? 👈😳
To Allah ya hada hankulanku Alfarman wannan watan 🤲

Kinada masifaffiyar Uwar miji ?👈🙄
To Allah ya azirtata da kamuwa da sonki taji dk duniya bata kaunar kowa sae ke Alfarman wannan watan 🤲

Kinada damuwa ?👈😩
To Allah yaye maki wannan damuwar Izuwa Farinciki har qarshen rayuwarki Alfarman wannan watan🤲

Iyayenki suna raye ?👈🧑‍🦳👨‍🦳
To Allah yasa su cika da Imani yasa Ku rabu da juna lafiya Alfarman wannan watan🤲

Mahaefiyar ki ba lafiya ?👈😩
To Allah ya bata lafiya da nisan kwana Alfarman wannan watan🤲

Mahaefinki ba lafiya? 😩
To Allah ya bashi lafiya da nisan kwana Alfarman wannan watan🤲

Mahaefanki basa raye? 👈😥
To Allah yaji qansu da rahma yasa Aljannah ce makomarsu ke kuma Allah ya baki hakurin rashinsu Alfarman wannan watan 🤲
Kinajin azimin yau ?👈🤣
To Allah ya baki hakuri da juriya ya kuma kar6e Ibadan ki Alfarman wannan watan🤲

Kinji dadin wannan addua?👈🙏
To Allah ya farantamin nima kaman yanda na farantawa Aunties dina Alfarman wannan watan🤲👈

Ina rokon ka ya Allah dan tsarkin mulkin ka duk wacce ta dauki hannun ta mai Albarka tayi/yayi

Following #dina

Tayi /yayi #commen

Ku kai min #vote

Da fatan duk munyi Sallah lafiya Allah ya maimaita mana 🙏🌙

* * * * * * * *

·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

CHAPTER 27

"lafiya naga duk kin rasa nutsuwar ki lokaci guda ko wata maganar Abban ya fad'a miki?".
Mama ta tambayi Zuby dake faman safa da marwa a falo dayan hannun ta dafe da goshin ta saboda jirin da take gani.

Cikin sauri Zuby ta juyo ta kalli Mama tace "ina lafiya Mama wallahi ni mutuwa zanyi bana son Maheer Mama ki taimaka min idan Abba yace sai na aure sa mutuwa zan yi".

A dai dai lakacin Abba ya fito daga bedroom din sa da jaka trolley a hannu sa yana ja yar karama, da alamar tafiya zai yi, yaji duka abinda Zubaidan ta fada ransa na suya yace "aikuwa sai dai ki mutu amma ko gawar ki ce sai an kaita gidan Maheer zan can banza zan can hofi, duk laifin ki ne Mariya" ya fad'a yana maida duban sa gare ta "ke kika bata yarinyar nan amma gabaki dayan ku zanyi maganin ku bari na dawo tafiya, kuma kufara shirye shiryen biki daga yanzu zuwa kowani lokaci za'a daura aure". Yana gama fadar haka ya fice abun sa,
Maganar da yayi da Usman jiya ta kara dawo mai sabuwa fil yaji kamar yanzu ake fada masa ita, take zuciyar sa ta fara kuna da radadi tabbas ka haifi d'a ne amma baka haifi halin sa ba idan kuwa hakane Mariya ta dade tana raina masa hankali amma ya godewa Allah da jiya Usman ya ganar dashi, shi dama ya dade yana zargin da akwai abinda suke boye masa ya bari ne saboda yasan dole wataran asirin su zai tonu, ya kuduri aniyar sa ido sosai akan ta saboda yagano abinda take aikata wa, aran sa yace  "ya tabbata Mariya ce ta Lalata yarinyar saboda duk wani abu  da take yi da sanin ta take aikatawa tabbas idan ya gono ba abun arziki bane kashin Mariya ya bushe dan san da zai bata Zubaidan tayi alkawarin bata tarbiya kamar diyar da ta haifa ta cikin ta da haka ya kawar da tunanin ya shiga cikin mota ya bata wuta.

hhhmmmm idan Abba yasan munanan abun da take aikata wa ya zaiji acikin ransa kuma wani mataki zai dauka akan Mama Mariya ? Kudai cigaba da bina sannu ahankali ganin yanda labarin zai kaya

* * * * * *

Da misalin 11:30 am Farooq ne yai fakin din motar sa a bakin wangalelen get din gidan su Sadeeq inda yake dannawa mai gadi hon, da sauri mai gadi ya taso daga kan kujerar sa ya zo ya dan leka ta kofa ganin Farooq ya leko yana daga hannu yasa mai gadi yai sauri yazo ya wangle gate din, yana fadin "yallabai yau kai ne a gidan namu sannun da zuwa gaskiya ka sha hanya kayi sa'a yallabai kuwa yana gida bai fita ba". Shi dai Farooq bai tanka masa ba ya sulala da motar sa kana ya nemi guri yai fakin, mai gadi ya maida get din ya rufe yana kara jinjinawa Farooq hannu.

Jim kadan ya kashe motar ya fito,

A dai dai lokacin ni kuma na fito zan je na kaiwa mai gadi wasu kaya da Daddy yace na bashi, ina ganin sa na karasa gurin sa baki na dauke da Murmushi nace "laa! Yaya Farooq yau kaine agarin namu aradun Allah naji dadin ganin ka dama na gaji da zaman garin nan yanda kasan ina kur-kuku haka nike jina, kafa ta kafar ka sai na bika mun tafi Dan de".

Yana dariya yace "to yar Inna keda zaki tafi makaranta ina ke ina komawa kyauye ko bakya so ki zama yar birni ki dunga turanci ki waye ki zama babbar yarinya?".

Shiru nayi na yan sakwannin da baza su wuce biyu zuwa uku ba kana na ce "yaya Farooq kenan duka wa'innan abubuwan da ka lissafa ina so na zama ko dan na bawa yaya mamaki , amma saboda mugunta irin tasa    makarantar kwana ya sama min  kuma yace kai ne zaka kaini, ko kazo tafiya dani din ne?". na karasa maganar ina gyatsine da jijjiga kugu.

Dariya nabawa Farooq yanda yaga lokaci daya na canza yanayin magana ta zai yi magana  nace" ban tari numfashin ka ba yaya amma ni babu inda zan bika mu tafi wata makarantar kwana jeka ka dawo zanyi na kuma gayawa Daddy kuma ya yi na'am da batu na.

Dan yace " ma yaya Sadeeq in dai yana so ya kaini makarantar kwana to ya fara neman amincewa ta idan kuwa naki aminta sai dai fa ya kaini makarantar su Khadija".

Sajan sa Farooq ya shafa yace" ho ho ni Farooq yanzu ina shi Sadeeq din?". Tace" ban sani ba  amma dai yana gida bai fita ba ".

" To maza je ki kai wannan sakon da aka aike ki kizo mu shiga gidan".  

Nace "ban gane nazo mu shiga ba yah Farooq ni fa na fada maka in dai dan nice kazo gidan nan gwara ka koma dan bazan je ba, ba sai ka tsaya bata lokacin ka ba nasan bazaka rasa abin yi ba"

Ina gama fadar haka na wuce aiken da akai min a zaune na gan sa hannun sa rike da radio kamar kullum ya kure volume kuma ya kara a kunnen sa, bai san nazo ba sai da yaji an kwace radio, a hasale ya jiyo ganin nice yasa yai Murmushi yace " yar gidan Inna ya akai" kayan hannu na na mika masa gami da fadin "wai me kake ji a radio ne kullum da ita nike ganin ka kuma ka kure volume ko ciwan kunne baka ji?".
Yace "banda abin ki yar Inna mai zan ji da ya wuce labaran dunya ai labaran duniya niki ji saboda yanzu lamarin kasar nan tamu abubuwa duk sun rukice sai addu'a".

Nace "hakane Allah ya kawo mana sauyi mafi alkairi ".

"amin" Yace gami da fadin "wannan kayan fa guga zan kai ko me?".

Nace "Daddy yace na kawo maka".

Ai kuwa yaji dadi sosoi dan kayan sabbi ne kala hudu haka dai na baro sa yana ta zab ga godiya kamar wanda akace an gafar ta masa gabadaya zuniban sa.

A inda na bar sa anan na same sa tsaye da waya annu yana dannawa nace "baka tafi ba yah Farooq?".

"ina zani fa ni da nike jiran mu shiga tare".

Nace "to shikenan tunda ka nace halan akwai abunda kake son yi muje".

Ina gaba yana baya har muka karasa cikin katafaron falon gidan in da naci karo da Sadeeq har saida ya turo ni saboda shi zai fita ni kuma na kutsa kai abinka da mara nutsuwa, shi kuma yayi ya dunfaro kofar ne cikin zafin nama, ihu na fara ina kiran sunan Daddy saboda kaina ya dan bugu da bango, shi kuwa yaya Sadeeq yayi tsaki sun fi biyar yana kara jin tsana ta a zuciyar sa yarinya sai tsinannan sharri to shi yanzu mai ya mata da take so ta tara mai jama'a?".

Daga kan da zaiyi sai yaga Farooq a tsaye jingine da jikin ban go ya harde yannayen sa a kirji sai Murmushin mugunta yake wa Sadeeq

A hasale Sadeeq yace" malam maye?".

"Nishadi mana ko kar nayi?". Farooq ya fad'a still kuma yana dariyar sa

"kallon kan ka ka rainawa hankali Sadeeq ya bi Farooq da shi kana yace bani wuri ni na wuce kana bata min lokaci".

A dai dai lokacin Momy ta fito tana fadin "yaya lafiya ke dawa".

Sam bata lura da Farooq ba sadeeq ta hanga a gurin aikuwa ta fara yi masa fada da tana cewa "a haf ai nasan sai kai sarkin cin zali in dai kaji kukan yarinyar nan a gidan nan to ba kowa bane face  kai".

Kallo na tayi tace ke tashi rabu dashi kiyi masa Allah ya isa tunda bazai daina ba Allah zai saka miki ".

Ina gunjin kuka na mike ina fiki fiki da idanu na ina kara matso kwalla a haka na haura sama na wuce daki na na kwanta a kan gado ina kallon sama ina jin zuciya ta babu dadi.

Farooq na shaafa keya yace" Momy ina kwana?".

Sai a lokacin Momy ta waigo inda yake fuskar ta a sake
Tace" lafiya lau  Farooq yaushe kazo ne?".

Yace" shigowa ta kenan "

Tace" madallah ya Hajiyar taku?".

" Suna lafiya suna gaida ku".

"Masha Allah muna amsawa, kar dai tafiya da gimbiyar kazoyi ?". Ta tambaye sa

Yace "eh Momy".

Tace "bai fada maka ta fasa zuwa ba?".

"Eh bai fada min ba amma yanzu dana shigo kan na kara so cikin gidan na hadu da ita abakin get shine take sanar min cewa ta fasa zuwa".

Tace "yauwa sai kusan yadda za'ai dan Daddyn ku ya kusan gama shirya wa kuma yana so yaji matsaya ne kan ya tafi". Tana gama fadar haka ta bar falon.

A hankali Farooq ya kara so inda Sadeeq yake ya dafa kafadar sa yace "aboki na akwai matsala fa amma kana nuna kamar abin bai dame ka ba bayan kai ne mutum na farko daza ka fi kowa shiga damuwa idan har yarinyar nan tace baza ta ba, ni wallahi mamaki kake bani yar wannan yarinyar ta gagare ka sarrafawa sai kace ba namijin duniya ba ko girman kan ne zai hana ka shaho kan ta? To idan shine zai fi kyau ka aje sa a gefe saboda.... ".

"dallah malam dakata ya kake magana kamar kana bani umarni nifa kaga wannan karatun da za tai kanta za tai mawa ba ni ba saboda haka idan ma karatun ne tace baza tai ba kwata kwata ni ba damuwa ta bane bayan ita zan iya auran gudu uku wa'inda suka fita komai, so kada ka tsaya bata yawun bakin ka ".

Farooq yace" nifa ba nufi na ka bata hakuri ba, ba kace yarinya ce bata da wayau ba kuma bata san komai ba, to ai shaho kanta ba zaiyi wahala ba shine nike so kayi mata yan dabaru
ko ka fasa kara auren ne?". Ya fada da alamar tambaya

Yace" ban fasa ba amma kada ta gano ni fa kasan bana son raini".

"haba babu abinda zata gano kawai shiga ciki zan turo maka ita".

Yace "to shikenan kai anan zaka zauna?".

"eh".

Farooq ya fad'a yana mai samun kan kujera ya zauna yace "kasa a kawo min ruwa da dan abin tabawa".

"To" yace ya haura sama.

Khadija ce ta sauko bayan sun gaisa ta nufi  kitchen ta hada masa kayan ciye ciye da ruwa  kana ta dora akan katon tirai tazo ta aje masa akan tebur zata tashi yace "ina zuwa ki zauna muyi fira bana son zama shiru ni".

Komawa tai ta zauna ai kuwa nan Khadija tai ta basa labari yana kwasar dariya

* * * * * * *

Nan Abba ya bar Mama da Zuby cikin jimamin magan ganun sa, tabe baki Mama tayi ta kamo hannun Zuby suka zauna akan kujera tace" wai meke faruwa ne dan ni wallahi ban fahimci inda kalaman Abban ki ya dosa ba".

Sai da Zuby ta sauke gwauran numfashi kana tace "kina nufin Abba bai fada miki suna son su hada aure na da Maheer ba?". Tai maganar ne cikin sigar tambaya

Mama tace "bai fada min ba amma in dan wannan ne ki kwantar da hankalin ki ban ga aibun Maheer ba ni".

"Haba Mama ya kike so nayi da Soyayyar Sadeeq da take dawai niya dani wallahi yanzu haka daurewa nike yi rabo na dashi tun jiya ko awaya bai kirani ba".

"shiyasa nace ki kwantar da hankalin ki yanzu ki fara shawo kan Sadeeq din daga baya sai musan yadda zamuyi da Abban naki".

"Mama kin San bamu da wannan lokacin kuma tabbas Abba da gaske yake dan naga bacin ran sa da

1 Comments On NI DA YAYA SADEEQ
avatar
zainab-2-9-9

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment