Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fahimtar komai, takwashi wayoyinsa da lap-top tanufi d'akinta, bata yarda yau tayi zaman wahala da tsoro irinna jiyaba, saita d'auro alwala tazo taita sallah da karatun alkur'ani, wannan yad'auke hankalinta har tayi sallar asubahi sannan tazame a wajen ta kwanta.

Su ya khaleel yauma kwana sukayi akan Momy, Dan jikinma yafi jiya tsanani, dukkan y'ay'anta Na gewaye da ita, harsu hasnah sunanan, Tanana a kira kowa, har baffah, haka suka kwana azaune zubur.
Ya khaleel baidawoba saida gari yayi haske bayan yayi sallar asubahi, saida yalek'a d'akin Aysha sannan, akan abin sallah yaganta kudundune cikin hijjabinta, ga alk'ur'ani a gefenta, tabashi tausayi, ya d'auketa tamkar wata babe ya kwantar a kan gadon, cikin dabara yazame mata hijjab d'in ya lullu6eta da bargo, sannan yamik'e yafice daga d'akin.
Bai kwantaba yau, Dan akwai aikin dayakeson yi ayaud'in, dukda yana cikin hutun angwanci, shirinsa yayi cikin uniform d'in aiki, masu k'ara masa kwarjini da cikar haiba, yashiga d'akin Aysha yana d'aura agogo, haryanzu tanata barcinta, yad'auki lap-top d'insa da wayoyinsa yazuba a jaka, sannan yad'anyi short not ya ajiye mata kan madubi yafice su Adams na jiransa awaje.
Ta gate d'insu yafita, Dan haka babu Wanda yasan fitarsa acikin gidan.
Atare sukayi salute nashi, yad'aga musu hannu damusu godiya akan hidimar bikinsa dasuka tsaya tsayin daka aka kammala lfy.
Adams yabud'e masa motar yashiga, sannan suma duk suka shiga.


___________________________
Aysha bata farkaba sai around 10, ta tashi d'aukeda addu'ar barci abakinta, tayi mamakin Wanda ya maidota saman gadon, aranta tace, "k'ila ya khaleel ne".
A gaggauce ta k'imtsa kanta, saida tazo gyaran d'akin sannan talura babu wayoyinsa da laptop, d'aukar y'ar takardar daya ajiye tayi, written d'in yamata k'yau.

_β€œNad'an fita wani aiki, amma insha ALLAH bazan dad'eba zan dawo.”_
_β€œki kula da kanki.”_

Aysha tayi murmushi, tareda maimaita _ki kula da kanki_ sau babu adadi, kalmar Tamata dad'i sosai, aganinta wannan kalmace dake nuna kulawa akan abinda kadamu dashi, "kenan ya khaleel yadamu da ita?", takai hannunta tana shafa la66anta datuna abinda yamata jiya da daddare, ta sumbaci takardar tanamai lumshe idanunta, ahankali tafurta ina k'aunarka sosai ya khaleel, Dan ALLAH Nima kasoni fiyeda yanda nake sonka, (Dan bazaka ta6a Sanin inasonkaba harsai kafuta soyayyata da bakinka), zan rayu dakai, zankuma mutu da sonka, Abadan inafatan mukasance tare har mutuwa, dukda mugayen dake zagaye da rayuwar aurenmu, amma ALLAH zaimana maganinsu da k'arfin ikonsa.
Haka taita sambatun begensa ita kad'ai, tanayi tana aikinta, tsaf tagyara gidan, ko ina yad'auki k'amshi, har d'akinsa saida takuma gyarawa, dukda babu wani datti, tunda baikwana acikiba.


____________________________

Su ya khaleel kam suna can sunyi fakon Lazarus, babban yaron Ahaji bishasha, Wanda suka sami damar kamashi a babban shagon saida kayan masarufi dake kasuwar suleja, yazo sayen kayan abinci dasukan saya duk k'arshen watanni uku zaikai mafakarsu, ankamashi bisa had'inkai damai shagon yabasu, saboda shima yagaji da cutar dasuke masa, sometimes sukan d'ibi kayan masarufi amma basa biyanshi, idan yay magana sumasa barazana da mutuwa, yanason Barin kasuwar kuma sun hanashi saboda zalunci, since yana Barin wajen zasu kasheshi shida iyalansa.
Abinciken su ya khaleel ne suka gano nanne shagon dash Lazarus kezuwa siyen kaya aduk bayan watanni uku, shiyyasa suka nemi had'inkan mai shagon, dukda daga farko yaso musu k'arya saboda tsoron abinda zaije yadawo, saida ya khaleel ya tabbatar masa zai sassa6a masa kamanni sannan yabada bayanan gaskiya.


Aysha nacikin aiki saiga tasleem dakayan break fast, ita ta taimaka mata suka kammala komai, sannan tagudu, Dan azatonta ya khaleel nanan, dukda kuwa Aysha ta tabbatar mata dabaya gidan, amma tak'i tsayawa.
Aysha tazauna tayi break d'inta, bayan ta kammala takira Ummah suka gaisa, tak'ara mata nasiha. sannan takira mama, tana mata shagwa6ar yaushe zata dawo? Itafa Tayi missing na sosai.
Mama tace, "to daba'a gidan kuka zaunabafa? Kijimin yarinya da iyayi, INA mijin naki kike addabata da safiyarnan?".
" kai mama, wannanne Safiya, 11 fa tawuce".
"Eh duk da hakan, ainasan mijinki nagidan ba aiki yake fitaba shiyyasa".
" to aii mama barci yakeyi bai tashiba, mama kamarma kin daina sonafa?".
Dariya Maman tayi tace, "keni bazan iya da fitinarkiba Aysha, kinga sai anjima, ki gaida mutan gidan".
Kafin Aysha tayi magana mama ta Yanke wayar.
Dira k'afafu tafarayi irinnan shagwa6a tana fad'in kai mama! kai mama!, saikace tana gabanta, a haka mufeedah tashigo tasameta, ta ta6e Baki da sakin tsak'i, tawuce d'akin ya khaleel batareda tayima Aysha maganaba.
Itama ayshan ko kallo mufeeda bata ishetaba, saima fad'i take aranta, "" inama yananan yacimin uwarki, shegiya karuwar gida, lokaci kad'an yaragemin namiki tonon silili, tsohuwar guzuma kawai, badolema kiyi karuwanciba shekara kusan 28 babu mijin aure".
Tana cikin gulma da zuciyarta mufeedah tafito tana cikada batsewa, "k! INA ya khaleel?".
Yatsina fuska ayshan tayi tana kauda fuska, tamkarma batasan dawata halitta awajenba.
Hakan Yakuma tunzura mufeeda kuwa tace, "k! Dan uwarki bak'ya jinane? ALLAH saina lakad'a miki dukan tsiya".
Idanu Aysha tazaro tana fad'in "Kuttt dukafa? Ina matsayin matar yayan taki? Lallai Ashe kuwa zaimiki dukan mutuwa agidannan, aiko Momy tadakeni banyi tunanin zai d'aga mata k'afaba bare ked'in, idankuma zaki gwada bismillah".
Duk maganarnan da Aysha keyi a tsorace take, dantasan mufeeda zata ita zaneta d'in, gashi gida babu kowa, amma Dan k'arfin hali irinnan Aysha saita dake, harda wani girgiza jiki.
Bak'inciki yakume mufeeda takasa magana, sai zuwacan tayi kwafa tareda Nuna Aysha da yatsa, ai wlhy sainaci ubanki agidannan naga mai d'aure miki gindi, dagake har uwarki sai zaman gidannan ya gagareku.
Aysha tarik'e k'ugu tana fad'in tofa babbar magana, wai d'ansanda yaga gawar soja, zaman gida bai gagari karuwar dareba, dakuma dillaliyar kai yara karuwanci k'asashen duniya saimu?, a dai kula kar'a kwaso mana ciwon sida, a6ata sunan gidan dattijo mai mutunci irin baffah.
Shiru mufeeda tayi, Dan maganar Aysha ta birkita kwalwarta, sai kawai ta6ige da borin kunya tana zagin Aysha, saita fad'ama Momy tazo taji dasu ubanda take, a can k'asan zuciyarta kuwa sai luguden Daka yakeyi, tana mamakin a INA Aysha tasan tana fitar dare? Saidai idan d'an gwari mai gadi yafad'a mata, aiko aikinsa yak'are agidannan, gwamma tamai kutu-kutun daza'a koresa kafin ya tona mata asiri, sosai maganar ta daketa, dukkan ga66an jikinta rawa sukeyi.
Tana fita Aysha ta ta6e baki tareda Jan tsaki, tafara laluben number yaya fadeela dansu gaisa.


Mufeeda kam k'arya da gaskiya taje ta zayyanema Momy, amma ita babu zancen ance mata karuwar gida, saidai tafad'i na Momy dillaliyar kai yara karuwanci kasashen duniya.
Anty shukurah tace, "k! Mufeeda kiji tsoron ALLAH, y'ar yarinyarnance zata fad'i haka? Wlhy babu k'yau tada musifa, keda aka aikekima kiran khaleel miye ya had'aki da ita?.
Mufeeda ta turo baki gaba, "kai kajimin Anty shukarah d'innan, bata fad'aba zance tafad'a".
Momy kam takasa cewa k'ala, danba k'aramin dukan zuciyarta Aiken na Aysha yayiba, Anty zuwairah tamik'e tana hucin bala'i, " bara naje naci uban yarinyarnan da kaina, saita fad'i waye dillalin kai yara karuwancin?. Momy tanason dakatar da Anty zuwairah amma bakinta yamata nauyi.
Anty shukrah ta harari mufeeda tana fad'in "hankalinki ya kwanta kin had'a saikijira kuma sakamako daga khaleel, dannasan ba k'yaleki zaiyiba wlhy.
Mufeeda ta tunzuro baki gaba tana k'unk'unin fad'in "yo basai Momy tabarsaba sannan zai dakeni".
Aysha nacikin yin waya da Anty Hafsat Anty zuwairah tafad'o, sallama Aysha taima Anty Hafsat a hanzarce, danbata buk'atar kowanta yasan matsalar gidanta har kuwa da mama dazata dawo, ina arzik'i daga kai amarya kwana 2 aji tana fad'a da dangin miji.
"K! Dan ubanki wakike cema dillaliyar karuwai?".
Aysha tazaro ido waje tana fad'in "kai Anty zuwairah yaushe nafad'a? A ina kuma?".
"bara na lakad'a miki dukan mutuwa saiki tuna to".
"Wlhy Anty zuwairah karki tsananta bincike, Dan ALLAH ma yamana hani da hakan, inkuma kink'i Allura zata tono garmane kawai fa, dan babu ruwana A to Z zan rattafo zance, tawatsema kowa wlhy".
"Barito na nad'eki saiki rattafo zancen dan uwarki", 'tayo kan Aysha'.
Aii da gudu Aysha tashige d'akin ya khaleel da hanyarsa ke kusada ita, takuwa danna makulli a k'ofar. Ahaka su mufeeda dasu hasna suka shigo, dawowarsu kenan daga school mufeeda tabasu labari, shine sukayo gayyar dukan Aysha, saikace wata uwar mata🀣, (bayan duksun girmeta)
Kosu hasnah sunbama Aysha wajen shekara 7-7 ma, bare anty zuwaira data haifeta, dan dakad'an Aysha tagirmi Najwarta.
Sai buga k'ofar suke suna zagin Aysha dacin mutuncin iyayenta, abinda yasaka Aysha kuka shine saka Abbanta dasukeyi, yana kabarinsa kwance, bata jamasa addu'aba sai zagi. Takuma rushewa da kuka.
Ana cikin wannan balahira ya khaleel yashigo gidan, duk agajiye yake, abakin k'ofa Adams yamik'a masa jakkar laptop d'insa da hularsa, yay salute nasa.
Ya khaleel ya jinjina masa kai yana fad'in "Adams kukula fa sosai, koyaya kukaga abinda baimukuba Ku kirani, hutunnan yazama dolene kawai amma daban zaunashiba, saboda d'an tsakaninnan ayyuka garemu sosai a k'asa, amma dukda haka zan ringa lek'owa saboda gudun samun matsala".
"OK sir, agaida Anty".

Zataji Adams, inaso kumaida hankalinku akan Ak'ilu Abbas, dan da gaggawa nakeson sanin masu hannu akan kisan David".
Insha ALLAH Sir, karka damu, ALLAH yana tare damu, zaikuma cigaba dabamu nasara kamar yanda yake bamu akan mak'iya".
" to ALLAH ya tabbatar, kukula sosai".

Tunda yadoso 6angaren nasu yakejin hayaniya, mankine yakamashi, dan yasan duk bak'i sungama tafiya, yabud'e k'ofar falon yashiga, turus yayi yanabin y'an uwan nasa da daketa zage-zage da kallon mamakin............✍





🀧maga Wanda ya khaleel zai goyama baya.





_Ngd sosai da addu'oinku, kuyi hak'uri darashin amsa muku a groups, wlhy messages d'in sunmin yawa, Na PC ma har yanzu bangama amsawaba, ALLAH yabar zuminci, inayinku irin millions d'innan wlhyπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹._






.πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
[9/14, 7:25 PM] Aysha Galadima: *_TypingπŸ“²_*



🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_



*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*



*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🀲🏻😭



*_part 2_*
(littafi na biyuπŸ“•)

_gaisuwa da fatan alkairi Maryam wasagu, Bebe'arth, mummeetie, mzzdaddy, alkairin ALLAH ya iso agareku._
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹



1⃣4⃣

.......Anty zuwairah ce tafara ganinsa tace, "yauwa khaleel aigara dakazo, yau saina zane mara kunyar matarka a gidannan, ita hartayi balagar aikama da momy zagi?".
Shiru yayi yana binsu da kallo d'aya bayan d'aya, Anty zuwairah tace, "wai bakajin minace? naji kayi shiru".
"Naji". 'Yafad'a yana cigaba da tafiya hanyar d'akinsa'.
Sudai su mufeeda baki yamutu, sunyi tsit.
K'ofar d'akin nasa yamurd'a zai shiga yajita 6am. Mufeeda tace, " ya khaleel tana cikifa ta kulle kanta saboda tasan batada gaskiya".
K'ala baiceba, sai harara daya bankama mufeedar, tayi k'asa da kanta tana k'unk'uni.
Yafara kiran " Aee'sha! Zoki bud'e k'ofar nan".
Dukda tagane muryarsace saida tace, "wanene?".
"k'aniyarkice, kibud'emin k'ofa nace!!". 'Yay maganar a tsawace'.
Batareda tabud'e k'ofarba ta jingina ajiki ta fashe da kuka, ''ALLAH ya khaleel nabud'e dukana zasuyi, nikuma tsoro nakeji, kace sutafi sannan saina bud'e".
Huci yafurzar daga bakinsa. yace, "Aee'sha karki bari raina ya6aci, kibud'emin k'ofa, babu wanda zaimiki wani Abu acikinsu ina nan".
" har Anty zuwairah? ". 'Aysha tayi maganar tana kuka'.
Cikin tsawa yace, "k! Wlhy zan sa6a miki idan baki bud'emin nan da 3minutes ba!!".
Su Anty zuwairah kam duk dad'i yakamasu, sunsan saiya yima Aysha dukan mutuwa. k'ilama ya saketa saboda zagin momy datayi, kai da sunji dad'i kuwa.πŸ˜‚
Aysha kam saida taga minti ukun daya bata sunkusa cika sannan tabud'e k'ofar.
Yana niyyar Shiga su Anty zuwairah suka tashi suma, hannu yad'aga musu alamar su dakata, sannan yashige, yamaida k'ofar yarufe harda Murza key.
Aysha tak'ara k'arfin kukanta, tana ja da baya dafad'in wlhy ya khaleel ni ban zagesuba, sunema suketa zagin Abbana, ALLAH Anty mufeeda Ce tahad'a".
Ko kallon Inda take baiyiba, ya ajiye jakkar laptop d'insa da hula akan gado, fuskarnan a murtike, babu alamun wasa, yafara cire ma6allan rigar Uniform d'insa, saida ya 6alle tas sannan yafara k'ok'arin zare belt d'insa.
Aysha tanacan jikin Bango tana kuka, duk zatonta dukanta zaiyi da belt d'in.
Ganin yacire komai, dagashi sai vest da boxer ta rintse idanunta, ya zauna akan sofa yana kwance igiyar takalminsa, sannan yazare har sock's d'in, yana mik'ewa Aysha tak'ara k'ank'ame jikinta, azatonta kanta yayo, saitaga yashige toilet.
Ajiyar zuciya tasauke da baza idanu kozataga key d'in, bataso yafito ya sameta a d'akin, kuma tana tsoron fita sabodasu Anty zuwairah.
Suna falo kuwa sai cika da batsewa sukeyi, suna jiran jin hukuncin da ya khaleel d'in zai yankema Aysha, amma sai sukajiyo tsit, sunsan wani lokacin idan yanacin uban mutum baya barinsa yayi kuka, shiyyasa sukad'an k'ara jira.
Inda yabarta anan yafito ya sameta, sanye yake da lemon green d'in rigar wanka, hannunsa rik'eda k'aramin towul yana goge Kansa zuwa fuska, da'alama wanka yayo.
Aysha tana ganin Yakama igiyar rigar zai kwance tazame k'asa, tareda cusa kanta tsakanin cinyoyinta tana rera kuka a hankali.
Kallo d'aya yamata ya d'auke kansa, cigaba yayi da shafa mai, yasaka k'ananun kaya marsa nauyi dabazasu takura masaba, yad'an yafesa turare.
Inda Aysha take zaune yanufa, yad'auketa cak, aikam tafasa masa k'ara, tsawa yadaka mata, tayi saurin to she bakinta da hannu.
Su Anty zuwairah dake falo suka fashe da dariya, harda tafawa, su duk zatonsu ya khaleel Na punishing d'in Ayshane.
Ya d'orata visa gadonsa, ya haye shima tareda rungume kayarsa, ya lumshe manyan idanunsa dake cikeda barci, mutsu-mutsu Ayshan tafara, yabud'e ido dak'yar Dan barci harya fara figarsa, "k wlhy inbaki nutsuminba zan dakaki ad'akinnan, sannan Na turaki waje su Anty zuwairan suyi duk yanda sukaso dake, stupid girl kawai".
Tsit Aysha tayi, takoma ta lafe a k'irjinsa, Yakuma rungumeta da k'yau, yamaida idanunsa ya lumshe, cikin lokaci k'ank'ani barci ya d'aukesa.
Aysha tabud'e idanunta dasukasha kuka, duksun mata nauyi, fuskarsa take k'arema kallo, yanda yake barci cikin nutsuwa, numfashinsa nafita ahankali, fuskarsa tayi fayau ko'a fili bata zama haka Dan tamkar yana murmushi, wani dad'i ya mamaye zuciyar Aysha, wai itace kwance visa k'irjin ya khaleel yau? abinda ko'a mafarkinta bata ta6a zaton faruwarsaba, "ya ALLAH Na gode maka da wannan k'yauta, shima ALLAH kasaka MASA sona, fiyeda yanda nake sonsa".
Haka taita tunane-tunane itama har barci 6arawo ya saceta.
Afalo kuwa bayansu Anty zuwairah sunji ihun Aysha da tsawar da ya khaleel yaymata sai Anty zuwairah tace sutashi suje, tasan khaleel zai tunkud'o k'eyar Aysha har gaban momy, bayan yagama kir6arta, da wannan shawarar suka koma cikin gida, tareda kaima momy dadd'an labari, wai khaleel nacan na zane Aysha, harda kulle k'ofa.
Momy taji dad'i sosai, har zuciyarta tad'an huce, amma dolene tad'auki matakin gaggawa, inba hakaba Aysha zata musu 6arin makauniya agidannan.
Anty shukura kam hankalinta yatashi, batareda sanin kowaba tanufo gidansu Aysha, tsit taji falon, harta juya amma hankalinta yakasa kwanciya, komawa tayi tacan bayan d'akunansu, talek'a window d'in ya khaleel, kwance ta hangosu manne da juna suna barcinsu hankali akwance, murmushi tayi dafad'in Alhmdllh.
Cikin nishad'i takoma tacigaba da harkar gabanta, tana mai k'arajin k'aunar khaleel d'in aranta, da halayensa masu matuk'ar birgeta.

___________________,,,
Kiran sallar la'asarne ya farkar da khaleel, ya bud'e idonsa akan Aysha dake kwance bisa jikinsa, dagani kasan tanajin dad'in barci, aransan yace, "masha ALLAH, balaifi yarinyarnan k'yak'yk'yawace, komai nata yana tsaka tsaki wajen k'yawun, babu abinda yafi d'aukar hankalinsa sai kwantacce gashin gaban goshinta, Wanda yakusa had'ewa da gira, ga zara-zaran gashin idanu, zaka iya d'aukama ta k'arane amma natane, samun kansa yayi da Sosa saman idonta da d'anyatsansa, yanayi yana murmushi".
Acikin barci Aysha taji kamar ana mata tafiyar tsutsa akan idanu, tabud'e idonta ahankali, yayinda ya khaleel yajanye hannunsa yana wani k'ara had'e fuska, shi a dole kar a kawo masa raini.
Tsaf Aysha tagane shine ke ta6a mata saman ido, dariya abin yabata, amma batayiba ta gimtse, tana kallonsa yasauka daga gadon yashige toilet, itama sauka tayi tana mamakin barcin dasukayi.
Tana nan zaune yafito da alama alwala yayo, yanata shan k'amshinsa yace, ''kitashi lokacin sallah yayi".
Kanta tad'aga masa batareda ta tankaba, itafa yana bata dariya, duk dan kar arainasa yake wannan cika da batsewar.


____________________________

"Aminiya kece agidan namu?".
"Wlhy kuwa nice aminiya, canayi bara nazo namiki barka da tashin bak'i ko".
Baki hajia babba ta ta6e, "kinada abin haushi wataran hajia khaltum, ni namaji dad'in zuwanki, koda bakizoba nidama zanzo".
"Tofa miya farune".
" aminiya yarinyarnan zata zamemana matsalafa, nifa bazan 6oye mikiba inacikin matuk'ar tashin hankali tunda su kubra suka sanar mana yarinyarnance".
"Bake kad'aiba wlhy Aminiya, ingaya miki nakasa zaune nakasa tsaye, akwana biyunnan tufk'awa da warwara kawai nakeyi, dama jira nakeyi bak'i sugama tafiya Nazo muyi magana, matsala biyuce ta tasomu gaba, d'anki da matarsa, Dan kinsanfa duk wani asusun banki na Oga barau yadaina aiki, gashi hukumar shigi da fici sunyi seizing d'in passport nasa, yau yau d'innan aka kama Lazarus".
"Kai haba! Aminiya munshiga uku, waye yakamashi?".
"d'anki Ibraheem".

"Ibraheem fa!?, yaushe yafitama daga gidan? Shida yake hutu".
"Aikamdai yau d'innan da safe, dan gwaska ya tabbatarmin dayaga Ibrahim da idonsa, kinsan kuma yasanshi dai".
Zuface tafara ketoma hajia babba, tace, "shikenan munshiga tara".
"Nifa mamaki kike bani, miyasa kike tsoronsane? ina ganin akwai mafuta".
"Hummm kaltum haryanzu bakisan wanene Ibrahim ba nakula, amma miye mafitar?".
"Kawo kunnenki".
Hajia khaltum tafad'a ma hajia babba abinda nima banjiba.

Tad'anji sauk'in damuwarta, harta zayyanema hajia khaltum abinda Aysha tamusu yau.
"Ammafa yabirgeni daya zaneta, kuma tabbas ayau d'inan zamu kawo k'arshen iskancinta, Dan sha yanzu magani yanzu yafi dad'i, dama binda tayima su kubrah ya 6atamin rai, nakula itafa jin kanta takeyi on top saboda ta auri Ibrahim, shiyyasama takemana barazana, tana wasa damune, duka-duka shekarunta nawa?".
"Ca zakiyi shekarun uwarta nawama bare ita".
"Wlhy kuwa. Kedai yau ki birkice musu kawai, Dan bazasu ta6a kasancewa a inuwa d'ayaba, nasan duk Girman kan namiji saukeshi yakeyi akan mace, duk wannan mazuran dakikaga yanayi tsaf zai iya kwanciya da ita, tom inhar kikayi k'ok'ari yauma yakwana awajenki zamuci nasarar aikinmu, Dan adaran yau su gwaska zasu gama aikinsu akanta".
"Shikuma sai Aleeya tashigo rayuwarsa, Dan yakamata ki tada maganar bikinsa da ita da gaggawa".
"Kinsani farinciki aminiya, amma da zuciyata tamin k'unci, yanzu kam nasamu nutsuwa, shiyyasa banida kamarki duk duniyarnan, ngd ngd".
"Kibarmin godiya, munrigada munzama d'aya aii, kedai kawai kiyi k'ok'ari yauma, Dan wannan ciwon nakine kawai zai hanashi kwana agidansa".
"Gaskiyane, nima aii nasan taurin kansa, Ibrahim murd'ad'd'en mutumne, juyasa saimai basira, tun yana k'araminsa mutumne mai masifar taurinkai, balle yanzu da aikinnan nasa ke k'ara masa masifa da bushewar zuciya".
"Aii bak'aramin kuskure kikayiba dakika amince masa shiga aikinnan".
"Inbanda abinki wayasan mi gobe zata haifar, kumafa alhajine ya d'aure masa gindi".
Hummm like Father like son.
"Aigashinan yazame mana masifa kuwa, amma zamu nuna masa mun rigasa zuwa duniya aii''.
Haka sukaita tattauna batun, da yanda zasu 6ullo masa.




_____________________________
Aysha na zaune gefen ya khaleel dakecin abinci, itama ya tsareta saitaci, turawa kawai takeyi, Dan ko kad'an batason cin Abu mai nauyi tunda tadawo daga turai d'innan.
Tsaf shima ya fahimceta, Dan haka yad'aura d'ammarar dawo da ita kan turbar al'adarta, tanaci tana tunzura baki gaba.
Yi yayi tamkar baisan da zamanta awajenba, cin abincisa yakeyi yana kallon labarai a aljazeerah.
Kamar zatayi kuka, sai Harar gefen ido take masa, wadda tasan inhar yagani sai kashinta ya bushe.
Ahakadai suka gama, ammafa saida ya tsare Aysha taci sosai, da kuka kuwa tacid'in, tana bashi mamaki yanda kuka baya mata wahala ko kad'an.
Suna kammalawa ta tartare wajen, shikuma Yakoma saman kujera ya zauna, k'afafinsa nakan k'aramin table na glass, ya canja tashar zuwa sunnah TV, wa'azin sheaik Kabeer gwambe aka saka, kuma akan aure ake wa'azin.
Aysha tafito data kichin, ya khaleel yana burgeta, zata iya cewa bata ta6a ganinsa yana kallon wak'ok'i ko wani film d'in dabai daceba, kai ko wak'a bata tunanin yanajima, dukda kasancewarsa matashi, koda yaushe saidai kaga yana kallon labari ko wa'azi, Indai kaga yazauna kallon film to tabbas zai k'arune dawani Abu aciki.

Shiru babu mai cema wani uffan, amma suna sauraren wa'azin, saidai kunya takama Aysha sosai, daurewa kawai takeyi.
Wa'azin kam sosai yay tasiri ga ya khaleel, harma yake sak'ama ransa wani Abu daban....



__________________________

Bayan yadawo daga sallar isha'i ya iske

Please Login or Register in order to submit comment