Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aurennan yaga yadace yazo ya gaidashi, shine daya kirashi yasanar masa yasameshi acikin makaranta.
Yakawo Aysharne Dan malaminsa yaganta tunda baida tabbacin zasu sake had'uwa dukda yanada burin malamin NASA yay Iuctures alokacin aurennasa.
Sheaik Al-hasan yaji dad'in wannan ziyara sosai, yayimasu nasiha akan aure da muhimmancin auren kansa, da girmama juna, yanda zasuyi zamantakewar dazasu amfanar dajunansu batareda samun sa6aniba ko k'osawa da junaba, sund'an dad'e sosai a makarantar Dan har saida baffah yakirasa, yasanarma baffah Inda sukaje.
Baffah yace shikenan mukam zamu wuce saikun taho, ka gaidamin da Malam sosai, kace insha ALLAH nima inan zanzo wajensa zuwa Na musaman.
Zaiji baffah, saimun taho, to kutahodai dawuri, karkuyi dare kajiko, Kasan hanya babu k'yau.
Insha ALLAH yanzu ZAMU taho baffah.
Bayan sun Yanke wayar ya isar da sak'on baffah wajen Malam, yaji dad'i sosai kuma ya amsa.
Littatafan addini masu muhimmanci akan rayuwar aure dawasu fannonin yahad'ama kowannensu, sai godiya suke masa.
Ya khaleel ya ajiye masa alkairi mai tsoka sannan sukafito.
Har k'ofar mota Malam yamusi rakiya, saida yaga fitarsu sanan yakoma office yanamai jin dad'in ziyarar, Dan har ransa yana k'aunar khaleel d'in, yarone mai kwazon gaske alokacin daya koyar dashi, ga gaskiya da suffar kamala Na mutanen kwarai batareda yaron, yaga kuma haryanzu halayyar Na taredashi.

________________
Tunda suka d'auki hanya babu Wanda yace uffan, har sunshiga cikin kaduna.
Shi yanata tuk'insa dajin wa'azin sheaik Jafar Mahmud Adam, itama Aysha wa'azin take saurare, yayinda wani 6angaren zuciyarta yatafi wajen tunanin ya khaleel d'in, komai nasa na burgeta, tako ina ya khaleel cikakken mutumne, saidai abinda ba'a rasaba, Dan d'an adama Tara yake bai cika gomaba, babu yanda za'ayi kace wane yakai 100%, dolene saika samu wani d'an taumashe koyaya ataredashi.

Awajenwa kika iya larabci haka?.
Maganarsa ta sauka a kunnenta.
Batareda ta kalleshiba tace a islamiyyar abbanmu, shima yana koya mana.
Alkur'ani fa?.
Nayi sauka, ina izufi 37 a hadda.
Yanzunkam saida yajuyo ya kalleta, banason k'aryafa.
ALLAH ka tanbayi mama.
Kansa ya jinjina, yacigaba da jeho mata tambayoyi akan sauran littatafan addini, sosai take bashi amsa daki-daki, saidai abinda ba'a rasaba, Wanda tasamu rauni akansa saboda rashin tunatarwa, tunda ba islamiyyar take zuwaba yanzun, jiyayi k'aunar iyayenta da kimarsu tak'aru azuciyarsa, dama haka yake burin samun matarsa mai ilimin addini, dukda har yanzu baita6ajin son yarinyar aransaba.
Daganan baikuma cewa komaiba.

Sunkusa fita Kaduna yatsaya wani wajen saida snacks agefen hanya, baicema Aysha komaiba yafita tareda saka mata luck.
Baidad'eba sosai saigashi yafito da leda guda biyu a hannunsa.
Yabud'e motar yashigo yana fad'in Alhmdllh.
Kamar yanda yanuna ya manta da ita a motar haka itama ta shareshi har suka fice daga cikin Kd.
meatpie dake nad'e cikin tessu yafaraci tareda fad'in bismillah.
Aysha tasaci kallonsa ta gefen ido sannan tace a'a ngd.
d'an juyowa yayi ya kalleta sannan yamaida hankalinsa ga tuk'insa, baisake cewa uffanba har suka shiga tsakkiyar dajin tsakanin Abuja da Kaduna.
Wayarsa tayi wringing, saida ta tsinke aka sake kira sannan yad'aga.
Ango kasha k'amshi, har yamzu baku shirya dawowa wajen aiki baneba kaida youseef? Kunbarmu aiki yamana yawa nida taheer wlhy.
Joseph yayi dariya, karka damu my guy, end of this week zanshigo Abuja tareda madam.
OK saikun isoto, agaidasu papa da joy.
Zasujika da k'au, ina amaryarmu?.
Waye amaryarku?.
Hhhh madan Aysha mana.
Aini bamma Santana, kaga sai munyi waya ina kan titine, yay maganar yana yanke wayar batareda ya saurari mi Joseph zai fad'aba.
Abin yak'ule Aysha. Dan taji dukkan wayar tasu, amma tana mamakin dama yana wasa da mutane haka?.
Sun isa jere aka fara kiran sallar magriba, tacikin jere yabi saboda gudun go slow d'in dazai samu idan yabi ta babbar hanya, musamman awajen dei-dei d'innan.
Ganin lokacin sallah zai kwace masa yatsaya a bwari wani masallaci zaibi jam'i.
Harya taka zai fita wayar Aysha tayi wringing, dakatawa yayi yafasa fitar, atare suka kai hannu kan wayar, shiyayi nasarar d'auka yayinda Aysha tayi saurin janye hannunta saboda d'orawa datayi akan nasa.
Ya d'auke wayar daga cinyarta yaduba, Anty meerah yagani a screen d'in, saiya mik'a mata yafita.
Baki ta murgad'awa bayansa sannan tad'aga wayar, harta tsinke ansake kira.
Anty meerah Na I missing you wlhy, kin manta dani kusan 1week bamuyi wayabafa.
Sorry lil sholyna, babynki ce batada lfy, amma tasamu sauk'i.
Wayyo my Raudat shiyyasa nayita mafarkinta, yajikinta?.
Kwantar da hankalinki da sauk'ifa, hak'orane.
To duk kuna lfy? Ya Canada?.
Gatanan k'alau, saidai muna kewarki wlhy, tunda muka dawo kullum sai munyi hirarki agidanan.
Wlhy nima ina kewarku Anty meerah, wani lokacin jinake kamar nayi tsuntsuwa nazo gareku, karki damu, aimun kusa zuwa tunda ga bikinnan nata zuwa ko.
Uhhm, ni Anty meerah kibari kawai, ALLAH yanzun banason aurennan, ya khaleel lamarinsa tsoro yake bani, saboda halin ko inkula dayake nunamin, yanda kikasan ba aurensa zanyibafa.
Karki damu daduk wata shariyarsa, kowane namiji danasa salon, wani bazai ta6a nuna miki color d'insaba saikunyi aure, wasu kuma sununa miki soyayya awaje, idan kunyi aure kiga bahaka baneba.
Shikenan Anty meerah.
Yauwa sweet lil d'ina, yanzu ya'ake cikine?.
Humm abubuwa kam sunata faruwa, kuma Alhmdllh ina k'ara samun bayanai akan su hajia babba, kinsanma wani Abu?.
A'a saikin fad'a.
Hhhhh wlhy mufeedah nakama shekaranjiya around 1:30am Na dare zata fita, batasan nagantaba, nafito d'aukar ruwa nasha, har tsakar gida nabita, naga tanatama d'an gwari maigadi jaraba, yabud'e mata gate kuwa tafita, rok'onsa nayi akan yabarni naga inda zataje.
Kinsan minagani kuwa? Tana fita tacire hijjab d'in jikinta, wlhy daga ita sai bra da pant, saiwata shegiyar riga wadda da'ita da babu duk d'aya.
Motar wani guy tashiga, inanan zan kafa mata wani tarko, ALLAH sanadin haka sai hawan jini yakama uwarta.....
Hango ya khaleel natahowa yasaka Aysha fad'in kibari nakoma gida zamuyi waya, tayanke da sauri.
Motar yashigo suka cigaba da tafiya.



*_2month's ago_*

Kwanaki nata shurawa, bikinsu ya khaleel yamatso gab.
Aysha tanashan gyara wajen Ammah da Anty Mamie, harma da gwaggo bintu ( nace wannan bazai hana ya khaleel dakakibaπŸ˜‚ gwaggo bintu😜).
Ga Anty Mamie tatsaya akanta wajen koyamata girke-girke dazama da miji, abinda ya khaleel keso da Wanda bayaso danta kiyaye kuma taci ribar zama dashi.
Tayi k'yau harta gaji, Ammah ma Na koya mata dabarun zama da miji irinna zamaninsu, sosai Aysha take fahimtar komai daki-daki.


A6angaren hajia babba kam batawani d'auki bikin da muhimmanciba, ko kayan lefe da Shukurah tace zataje Dubai tahad'o hajia babba cewatayi uban Dubai d'in, y'ar talakawar za'a had'ama kaya asu tsada?.
Bazai yuwuba.
Kai Momy, itamafa tazama d'iyarki, yakamatafa kugane khaleel shikad'aine namiji acikinmu, yakamata kuma a auransa mu nuna masa gata, kodan d'awainiyar dayakeyi damu, hakama Anty zuwairah nace nawa zamu had'a masa gudunmawa tace ko sisi bazata badaba, Momy kimata magana Dan ALLAH.
yo maganar ubanmi zan mata, wlhy ina bayanta gara tasiyama y'ay'anta kayan sakawa, idan zaiyi auren gaskiya saita masa, Dan wannan auren rusashshene, kwanakin Dana bashi nacika zan wargazashi.
Inzaki Adana kud'inkima sai aurensa da Aleeya ki Adana, inkuma zaki bashi kekika Sani, dama aii kema salla mammiyarce tamkar shi, karkuma kisake kirana akan bikinnan, dama zakiyi zamanki wajen y'ay'anki yafi miki alkairi basai kinsaka mijinki kashe kud'in jirgi abanzaba, ato kindaiji nafad'a miki.
Hummm amma Momy.......
Ya isheni haka Dan ubanki.
Shiru Anty shukurah tayi, tace shikenan Momy sai anjima, insha ALLAH ana saura sati 1 zantaho.
Kekika Sani kuma.

Ya khaleel dake tsaye abakin k'ofa yanajin wayartasu yajuya dabaya, Dan baya buk'atar momyn tasan yashigoma, wajen aiki zaije shine yashigo gaidata, maybi da yama zaije Gabon, amma dasafe yake sakaran dawowa.
Ko amma bai gaidaba yafice, saboda wayar Momy ta Sosa ransa, su Kansu su Adams sunlura ransa a6ace yake, yarasa miyasa Momy take masa hakane?, yakanji alabarin mutane idan mutum yanada y'ay'a maza dayawa, ya haifi mace 1 tak acikinsu takan samu gata fiye da kowa, hakama idan ya haifi mata da yawa, namiji yazama shikad'ai yakan samu gata fiyeda sauran y'ay'an, amma shi agaresa ba haka baneba, Momy tafi nuna soyayyarta kan y'an uwansa mata, mawuyacine suyi rayuwar sati d'aya Momy batayi abinda zai Sosa zuciyarsaba agidannan, Anty Mamie daba ita ta haifeshiba, nononta kawai yasha, amma yafi samun kulawa da kwanciyar hankali agareta.
Yanzu kokan aurenan itace ta zaunar dashi tamasa nasiha da Nuna masa muhimmancin biyayya ga iyaye, da alkairin datake hango masa a auren, kullum tsaye take Kansu wajen kwantar da hankalinsa itada Amman akan auren, amma ga Momy bahaka baneba.
Wanan wace iriyar rayuwace, shidai basain dad'in uwaba wlhy, gata da ranta amma maraya yafishi jindad'i......
Adams yak'ara magana akaro Na hud'u, sir! Munzofa.
Firgigita yabud'e idonsa, tareda yin k'aramin tsaki, Natafi wata duniyarne Adams, bara naje wajen Oga nafito, kafin nafito kasanarma su fharuk ina nemansu a office d'ina.
OK sir!
Adams yafad'a yana masa salute.

Yad'an dad'e a office d'in ogan nasa, suna tattaunawa akan abinda zai kaishi Gabon, dakuma mutuwar David Wanda khaleel d'in ya tabbatar da anbasa gubane aruwa yasha, kuma anhad'a kaine dawani makusancinsa, tunda bakowane ke shiga inda David yakeba, ya khaleel yace sir!.
Inazargin wasunmu Na taredasu David, Dan a shekaran jiya nafara tatsar wasu bayanai agaresa, Yakuma tabbatarmin zai fad'amin jami'an tsaron dake basu taimako akan harkokinsu, shine jiya muka wayi gari an kashesa, nasaka anrufemin masu tsaron k'ofar, har sai sun sanarmin Wanda yayi aika-aikar, dansunsanshi, amma sunk'i fad'a saboda wani dalilinsu nadaban.
Ha...ha..hakane, yakamata mu tsananta bincike akan kisan nashi, dan.... Dan babu wani bare dazai shigo yayi wanan aika-aikar.
Wani murmushin kasaita ya khaleel yayi, cikin izzarsa yace karka damu sir, y'ar manuniya zata nuna, kuma wlhy kosu wanene saisunyi Dana sanin 6atamin aiki, sannan mutuwar David bashine zaisa su ku6ta daga farautata ba, saima hanya dasuka nuna mini, alk'awarine saina gurfanar dasu bisa guywoyinsu agabana!!.
Y'ar zabura Oga yayi, Dan maganar khaleel d'in tashigeshi.
Batareda sauraren komaiba ya khaleel yay salute nashi yafice daga office.
Ajiyar zuciya Oga yayi (babu zancen fad'in matsayinsa, saboda tsaroπŸ˜‚πŸ‘πŸ»), gaba d'aya ya tsorata da j! d'in, yasan yaron gwarzone, kuma tabbas saiya bankad'osu, zuface tashiga keto masa, dolene su sake taku, kuma sud'au mataki wajen ragema Ibraheem Abdallah j kaifi, amma tayaya?, Dan sunan yaron yarigaya yayi tsawa a hukumarsu, manyan k'asashen duniya sun sanshi, kuma sunayi dashi.
Miye mafita yanzu??....



A office d'insa yatarar dasu Solomon, atare sukayi salutes nashi, yazauna akujera yana binsu da kallo.
Mahmud ya'ake cikine?.
Yes sir, mun kammala komai, kamar yanda kabuk'ata mun tankad'e da rairaye wad'anda sukeda kusanci sosai da barau modibbo, so aranarma da kukaso kamashi akwai wata number da'aka masa massege da ita, cewar gakunan zuwa garesa.
Inaga wananne yakawo matsala harya farga yagudu bayan yaga messenge d'in.
OK wanene mai number?.
Macece gaskiya, yasaka mata hajjaju kawai.
OK. Yanzu mutane nawane kuka tace acikinsu?.
Faruk yace su 37 ne sir.
OK.
Yakamata abisu d'aya bayan d'aya amin bincike akan sana'oinsu, da address nasu, har ita macen da tamasa massage d'in.
OK sir.
Solomon yace amma sir kana ganin lokaci baiyiba dazaku kama barau modibbo?.
Hakane Solomon, zamu kamashi, amma inason kama Alhaji Aliyu bushasha ne first, danshine ogansa nalura, kokuma nace babban dila d'insa, to kafin kuma nakamashi dolene mucigaba da bibiyar barau modibbo dansamun wasu bayanan sirri daga garesa batareda shima yasaniba.
Muna kamashi barau modibbo yanzu, Alhaji Aliyu zai gudu wlhy, kumashi mutumne mai wayon tsiya, baya hud'd'a da wayar tafi da gidanka, saidai yaransa..
Lallai yanada wayo, cewar kausar.
Sun tattauna sosai gameda wasu ayyukan sannan ya sallameshi suka tafi.

Shikuma yacigaba da 'yan ayyukansa, yana son kammala komai akan lokaci, saboda nanda 2weeks binkin taheer, tsakaninsu sati uku ne acal.
Ga aiki yamusu yawa, ad'an tsakaninnan, hankalinsa yarabu biyu. Ga shirin bikinsa shi kansa, damma k'annensa suna tsaye akan komai da baffansa.
Shi satin bikinma yana Saudia, sai ana 3days d'aurin aure zai dawo Nigeria.



Akwana atashi, babu wuya wajen ALLAH, biki saura kwanaki 10 kacal..............✍🏿












πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹β€β€β€β€β€
[9/6, 8:54 PM] Aysha Galadima: *_TypingπŸ“²_*



🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_



*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*



*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🀲🏻😭



*_part 2_*
(littafi na biyuπŸ“•)

*_wannan page nawani duk masoyin ciki da gaskiya ne aduk inda kuke, ngd sosai da k'yauna, ALLAH yabar zuminci, inayinku irin million's d'innan wlhy._*
πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜β€β€β€β€πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹


8⃣

Alhamdulillahi shirin biki ya kankama, anatama Inda zasu zauna fenti, can baya kusadasu ya Sultan, tunda aka saka ranar auren baffah yasakashi za6en yanda yakeso agina masa nasa wajen, yakuwa za6a.
Tun sannan aketa ginin, hargashi ankammala cikin nasara.
Kaf gidan kowa yanata shiryama wannan biki, dukda uban tafiya yace babu wani shagali daza ayi, acewarsa da kud'in daza 6arnatar wajen wani dinner, lunch, mother day.....etc, gamma ataimakama marasa k'arfi dashi.
Baffa yaji dad'in hakan sosai, kuma yasaka masa albarka.
Hajia babba kam ko a jikinta, da ayi dakar ayi duk uwar ubansu d'aya, yarantama basa wani nuna murnar Auren, saboda anhad'a yayansu da Aysha, amma sunata burin sai lokacin bikinsa da Aleeya, sukad'ai sukasan misuka shirya.

Nidai nace uhhhhmmm.😏


______________________
Aysha kishirya gobe idan ALLAH yakaimu zaku wuce Kano keda gwagggonki.
Lah mama da gaske?.
Eh mana, can zaki koma, nasanarma baffanku ma, nima insha ALLAH ranar laraba zantaho gaba d'aya, kokinje Kano karkiyarda wani yabaki wani abin cushe-cushe ko wani ganyen magani kisha, banason shaye-shayen maganin matannan wlhy, Dan abubuwane masu illah, mutanene kawai suka Gaza gane haka, kingadai anan mamien ku tabaki tsaftatatttu itada Ammah, tunda nonon rak'umine Dana shanu sai kayan marmari dasu aya Zuma kanimfari mazarkwaila dafanfar gyad'a dadai sauransu, wad'annan basa cutarwa tunda damacan ALLAH ya halatta mana shansu koda badan wannan manufarba, shiyyasama nahanaki shan nawajen bintu gaskiya.
Nasan Yaya bazata bakiba itama, tunda bataso, kannena kawai nakeji da asma'u sai matar Ahmad, amma Na gargad'i Hafsat da fadeelah, tunda suma sunsan bamumusu wannan shashancin ba.
Damu zauna 6ata lokaci wajan baku wannan shirmen da 6ata kud'inmu gamma mu nutsu wajen koya muku zaman auren da biyayya, maganin mata baya hana d'a namiji ya wulak'antaki idan yaso, idanda matanmu nada hankali dasun gane hakan, (wlhy naga matarda tahad'a kayan mata ta kwankwad'arma cikinta da yamma da daddare mijin yaji dad'insa, washe gari da safe sa6ani yashiga tsakaninsu ya sheshshek'ama fuskarta marika), shin Dan ALLAH maganin mata yayi riba kenan?, alokacinfa dasuke tareda sune kawai sukejin dad'in har miji yamiki wani sambatun banza, dazarar buk'atarsa tabiya shikenan anwuce wajen, wannan bazai hana yaci ubankiba, bazai hanashi cin zarafinkiba, bazai hanshi ya sakekiba, bazai hanashi yimiki kishiyaba, shin mata nawane suke amfani da kayan d'a'a amma basu fita daga cin kashin d'a namijiba, ga cututtuka dakiketa tanadama kanki wanda bazasu bayyana agarekiba sai lokacin da tsufa yazo miki, shin Dan ALLAH miye abin birgewa duk inda kika zauna kika tashi aganshi jik'e da ruwa, wannan wace iriyar masiface?, mutanan da maganin mata sukesha?, bama su sanshiba, amma suna zaune lafiya da mazajensu, wani aurenma sai anyi mace zata San mijinta, miji yasan matarsa, amma saikiga aurensu ana kiran shekararsa 80-70-60, kuma suna zaune lfy, ko sa6ani zakiga baya yawan shiga tsakaninsu.
tsakaninku da ALLAH awannan zamanin aure nawane kekai shekara 10 kacal babu tashin hankali da masifu acikinsa, awannan zamanin inhar mace sukai zaman lfy Na kwana uku da mijinta acikin sati, to wlhy kwana hud'u cikin fad'ane, mafi yawancin abinda ke faruwa kenan, kuma koda yaushe kud'inki nagidan dillaliyar kayan mata, bakiciba, bakiba y'ay'anki sunciba, bakiba iyayenki sun sakamiki albarkaba, baki taimakawa marasashiba, saikije kisha abinda zai ruguza rayuwarki batareda kinsan hakanba, kedai kawai mijinki yaji dad'i, yaringa zunduma ihu lokacin dayake taredake, indan anhad'u gidan suna ko biki kiringa bama sauran mata labarin sambatun dayake miki da ihu, mata suna dariya ana cafkewa da miki jinjina kinci gari.
Haba mata, wannan wace iriyar asarace haka, sirrin aurenkine agidan biki? Kaiconmu wlhy, ALLAH kuma ya tsinema duk ma'auratan dake fallasa sirrin aurensu, wlhy mugyara, keba karuwaba amma rayuwar aurenki tafi ta karuwai fita fili, wa'iyazubillah, Dan ALLAH mu kiyaye mata.
Aysha karki yarda koda da kuskure hakan takasance dake, kada naji kada nagani.
Kuka sosai Aysha keyi, tana jinjinama mama kai, kidaina kuka dan bama ayi komaiba, abinda yasa nabarki saboda kina kusadanine, akoda yaushe zan ringa nuna miki kuskuren abinda ke hana rayuwar aurenmu k'arko awannan zamanin.
Tashikije ki kimtsa komanki, Dan duk za'a maidasu 6angarenku kafin natafi.
To mama, ngd, tafita tana cigaba da kuka.
Mama tabita da kallon tausayi, tana tausayama d'iyar tata da dududu bata wuce shekaru 18 ba, gata da k'aramin jiki, bandama karatun kasashen waje ba irin namu baneba da saifama yanzu ayshar zata kammala Secondary nata, amma gata ayanzu hartana bautar k'asa (NYSC) d'inta


____________________
Yauwa Amatullah, kune y'an zamani, dama zuwanki nake jira, bud'e d'akincan Na bak'i muje kiduba kayancan idan sunyi, idan kuma akwai abinda za'a k'ara ko za'a sake kinga zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu saimu shiga kasuwa, Dan yakamata akaisu ranar alhamis ko.
To Anty Mamie kayan miye haka?.
Mujedai kigani mana.

Woow Anty mamie! Kayan auren ya khaleel ne?.
Sune Ama...
Masha ALLAH, akwati shidda, wlhy sunyi k'yau akwatinan, zama sukayi bakin gado, anty Ama.... tamasu fillah-fillah, kai wlhy komai yayi Anty, komai dama ayishi dai-dai misali yafi, amma nuna fariyarnan bata birgeni nidai.
Aii Ama...ita rayuwa basai ka nuna kaid'in maishi baneba, koda kanada kud'inda zakayi abinda fiyeda nak'asa dakai yayi, karkace saikayi Wanda ya ninninka nasa, wannan shike saka Wanda k'arfinsa bai kaiba burin yin kamar nakan, wannan fariyarce tasaka zaman y'anmata da zawarawa yawa, kowa burinta sai anyi mata abinda akama k'awarta lokacin aurenta, hakama iyayenmu burinsu Aueen y'ay'ansu yafi nakowa, Idan ankawo lefen auran d'iyar makwafta sudinga hura hanci aina d'iyansu yafi, sukansu samarin burinsu suyi bajinta tamkar ta auren wane, shiyyasa saikiga fitintinu sunyi yawa acikin bikin auren, da rayuwar auren kanta bayan anyishi, zakiga ma'aurata burinsu ayi events kala-kala Na k'awa da birgiyewa awajen shagalin aurensu, ad'akko mawak'a masu zamani da tashe su wak'esu, alik'a y'an dubu-dubu bugun Abuja ana takasu, amarya da Ango su d'au k'yalk'yali cikin kayan kece raini Na alfarma, wuyan amarya da hannunta kaga ruwan gwal k'irar Dubai nata k'yal-k'yal, k'awayen amarya da abokan ango da dangi ank'ure wanka cikin kayan birgewa, ga camera man agefe yanata k'yastu, washe gari dukwata kafar media tad'auka anyi auren wance da wane, abinda ke 6atamin raima wai kayan lefen aurenki dazarar ankawo zakifara ganin ana yawo da hotunansu a social media, y'an group ga kayan auren🀣.
Sukuma saisu d'auki shewa, kai amma wance kingama morewa, ALLAH dai ya maidamu danshinki, kai wacece addu'a gareki haka, muma abamu Dan ALLAHπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚, kujifa wawanci.
Kekam anfasa miki kai, kinacan dad'i kamar yakasheki kayan aurenki sun birge mutane😏.
Sai ank'are biki kaf ango yayta sace kayan da d'aid'aya yana maidawa shagon daya aro🀣.
Inkuwa siya yayi dagaske ma da sauk'i, amma dasun k'are kikace wane kayana sun tsufa zaice duk kayan Dana saka miki alefe kice sun kare, kinsan wahalar danaci natarasune? K'ilama y'an uwankine suka kwashe anga banza, to banidashi nikam😜.
Wlhy tundaga k'aryar biki ake fara samo matsaloli a aure, please mukula Dan ALLAH.
Hakane wlhy Mamie, ALLAH dai yasa mudace, amma yanzu wannan baffah ne yasa ahad'a ko ya khaleel.
A'a Ama... Gudunmawa tace, babana yamin magana akan lefen, amma nace masa yad'an saurareni, shima baffan naku dayay maganar haka Na sanar masa.
Yanzu saiki nemo su Amal Ku kwasa kukai wa Ammah kawai tunda komai yayi.
Kai amma kinsha kud'i Anty Mamie, ALLAH yak'ara bud'i Na alkairi, lallai ya khaleel d'an gatan Anty Mamie.
Fita Anty Mamie tayi tana murmushi batace komaiba.

.............................................
Ohni Halima, yanzunan duk bilkisunce ta had'a wad'annan kaya haka? Ya ALLAH ka albarkaci wannan yarinya da zuri'arta, ALLAH yakareta daga dukkan wani sharri itada zuri'arta.
Su Amal sunata amsawa da ameen cikin jin dad'i.
Bayan baffah yadawo Ammah tasaka aka kaimasa kayan, dakanta taje tamasa bayani, shima yaji dad'i sosai, sai albarka yake sakama matar tasa.


Please Login or Register in order to submit comment