Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bai tsaya bin ba'asiba yahau jibgarsu.
Aysha tamik'e da Sauri tana kuka, ganin ya khaleel yasakata zuwa da sauri Inda yake ta k'ank'amesa tana kuka da fad'in ka taimakeni ya khaleel zasu cutar dani, karka barsu, azzalumaine su.....
Gaba d'aya arikice take, sai yanzu ya khaleel yaga Aysha, hankalinsane Yakuma tashi, danhaka ya tureta daga jikinsa tareda damk'osu ya gwara kansu, dukansu yakeyi afusace, dak'yar securitys d'insa suka kwacesu, dansunga zaiyi kisankai.
Abirkice yajuyo kan Aysha dake gefe tana mak'yar k'yar sanyi, Dan ruwa aketa tsulawa kamar da bakin kwarya, mari ya falla mata, yana fad'in ubanmi yakawoki nan wajen?!!, nace miya kawoki?!!!!!!!.
Cikin matuk'ar tsawa yayi maganar, Dan harsu Adams saida suka zabura Dan tsoro.
Aysha tarik'e kumatunta tana matsawa baya saboda tsawar daya daka mata, wani Marin Yakuma kai mata Adams yatareshi yana fad'in please sir cool dawn.
Ya cije le6ensa tareda kuma kaimata duka saikuma yafasa ya rumtse hannun yana ciza la66ansa da k'arfi, jiyake tamkar ya had'iye zuciya awajen, ransa amatuk'ar 6ace yake, ya tura hannunsa d'aya a aljihun wandon oxblood d'in suit nasa, dasuka gama jik'ewa da ruwa, idanunsa sunyi jajur, ya watsama Aysha harara yana fad'in Adams kallafa kaga wajennan?, shin miya kawo yarinyarnan har suke shirin k'etaramin gonata? batareda ni Nayi koda gewayentaba?.
Yanzu dabamuzoba mikake tunanin zai farune? Mutuncinafa zasu Shiga saboda Mara hankalin yarinyarnan, Na mauje tama nahuta da ganinta.
Yay maganar yana ture Adams gefe tareda kaima Aysha wawura.
Yanzunma Adams kuma tareshi yayi, dukda bai fahimci zancen ogan nasaba, Dan baisan alak'arsama da yarinyarba.
Budurwannan ne tak'araso tana kuka dabama ya khaleel d'in hak'uri, tamasa bayani akan balaifin ayshar baneba, taimakonta tazoyi, itama a d'aya daga kamfanin take aiki, motartace tasamu matsala, daga Neman taimakonsu shine suke shirin mata fyad'e, Aysha ce ta taimaketa.
Zuciyarsa tad'anyi sanyi, amma bai huceba, Dan saiyaji ubanwa yasakata biyo hanyarnanma mai had'ari?, ina drivers d'in dake gidansu? Dahar ta taho ak'asa.
Ya watsa mata harara dayin kwafa, rigar suit d'insa yazare ya jefa mata, saboda farar rigarta ruwa yajik'ata dukta nuna jikinta, har kalar bra d'inta ana gani.
Jikin Aysha Na rawa tad'auka tasaka, dama Duk kunya tagama isarta.

Dariya nayi azuciyata, Dan hannun rigar yamata tsawo, gata tayi tsumu arigar kamar antsamo zomo aruwa🤣🤣.
Da kansa ya tattara kayanta, bag d'inta da hijjab, sai lemon green d'in rigarta data d'aure k'ugu, ijjab d'in yakuma jefa mata tasaka, dukda gyararren gashinta data d'aure a tsakkiya yagama jik'ewa jalab da ruwa bar d'iga yakeyi.
Yadaka mata tsawa, bazaki shige mujeba saina 6alla kasuuswanki anan......
Bata bari yak'arasa ta zuba dagudu, saida batasan motar dazata shigaba, dolene tajira ya k'araso.
Samuel karaka wannan yarinyar, kukuma Auwal ajeda yarannan kucimin ubansu dai-dai gwargwado, Adams kumuje.
Atare suka amsa,, aka kwashi samarinan dasuka gama fita hayyacinsu saboda duka.
Yana hararta yabud'e mata mota tashiga, sannan yazagaya Inda Adams yabud'e MASA shima yashiga shima.........✍🏿









💋💋💋💋💋
[9/6, 9:21 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*



🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭



*_part 2_*
(littafi na biyu📕)


_Na gaisheki first lady, ALLAH yabar zuminci_.
😍😍😍💋


6⃣

Aysha ta k'ank'ame jikinta tareda takurewa amurfin mortar, sai rawar sanyi takeyi, saboda bak'aramin ruwane yadakesuba awajen.
Ya khaleel ya gallamata harara yana d'auke lap-top d'insa dake tsakiyarsu, takuma k'ank'ame jikinta, harda rumtse ido, dan azatonda dukanta zaiyi.
Tsaki yasaki mai k'arfi, dububeki, dawani kanki kamar curin dankalin Hausa, afuska kamar kinada wayo amma wawuyace ashe, atunaninki ko ina ake nuna jarumta? Amatsayinki Na mace bak'ya tunanin had'ari fiyema da wannan? To dabamu zoba mikike tunani zai faru?!!!!, yay maganar a tsawace.
Aysha takuma k'ank'ame jikinta tana hawaye, wlhy ya khalee......
Ki rufemin wannan d'an banzan bakin naki kafin nazubar da hakwaran cikinsa amotarnan, aii sai kin fad'amin ubanda yasakayi biyo hanyarnan ak'afa Stupid girl kawai.
Acikin ranta tace idan kazubar da hakwaran kaika huta aii, nibanga dalilin wannan bala'iba haka, bakaji tausayinaba ka isheni da jarabarka.
Adai-dai nan suka iso k'ofar gate d'in gidan, Emanuel yay horn d'an gwari yabud'e.
Motar bata gama tsayawa da k'yauba Aysha tafita da gudu tayi cikin gida.
Kwafa ya khaleel yay shima yafito bayan Adams ya bud'e masa k'ofar.
Drivers d'in gidan yashiga kwalama kira, sunata hada-hadar tafiya masallaci saboda magrib data kawo jiki.
Ahanzarce suka k'araso gareshi, Dan sunsan shid'in zumane, ga zak'i ga harbi, gashi yanayinsa ya nuna a harzuk'e yake.
Gaidashi suka shigayi, batareda ya amsasuba yace wanene yake kai yarinyarcan Aee'sha wajen aiki?.
Jikin lawwali Na rawa yace nine wlhy yalla6ai.
Wani kallo ya watsa masa, idan an idar da sallar isha'i ina nemanka.
Maganar daya fad'a kenan yajuya zuwa cikin gida.
Adams ya kalli su lawwali daduk hankalinsa yake atashe, wainikam wacece yarinyarnan awajen boss? Duk nasan k'annensa, amma ban santaba.
Itace zai aura, cewar sadisu murya a sanyaye.
Ido sosai Adams yazaro, aransa yace kutttt shiyyasa Oga yarikice, ashe antynmuce? Lallai kingama morewa y'an mata wlhy.
Kayansa ya kwaso yamik'ama sadisu danya shiga dasu ciki.


Afalo ta Tatar damafi yawan mutanene gidan, jikin Anty Mamie data fito daga kitchen tafad'a tana kuka, a'a Aysha lfy kuwa? Ina kikaje hankalinmu dukya tashi, lawwali yace yaje d'aukarki baigankiba?.....
Anty Mamie nafa kirashi wayarsa akashe, shinefa......
Shigowar ya khaleel takatse mata maganartata.
Yaran gidan sai sannu da zuwa suke masa Dan tsawon wata 1 baya k'asar.
Adak'ile ya amsa musu, saboda ransa a6ace yake.
Anty Mamie tace a'a babana ko tare kukene?.
Kansa ya jinjinama Anty Mamie.
To lfy duk naganku ajik'e haka? Mike faruwane? Mu kun sakamu aduhu aii, ita tashigo tana kuka, kaikuma rai a 6ace?.
Muryarsa cikeda d'aci yayma Anty Mamie bayanin komai, kowa afalon ya tausayama Aysha, amma yanda ran ya khaleel d'in ya6aci sai abin yabasu mamaki.
Aysha tace ALLAH Anty Mamie tausayi tabani shiyyasa Na taimaketa, kumafa badan niba dazasu keta mutuncin tan........
Idan bakima mutane shiruba ALLAH saina zaneki yanzunnan, ke mara hankalin inace? Miyasa bazakiyi kamar yanda tayiba? Zaki wuce ki canja kaya kosaina k'ara kummura wannan janaren fuskar takine?, yay maganar yana matsowa kamar zai mazgeta, Ta k'ank'ame Anty Mamie kuwa.
Baffah dake tsaye yafito dashirin zuwa masallaci tareda y'an uku da Nuriddin yayi murmushi, Dan yaji dad'in yanda khaleel d'in yanuna kishinsa.
Maganarsace tasaka kowa juyowa gareshi, yace to ya Isa haka, mu'azzam amata hak'uri tayi kuskure, kuje kucire kayan jikinku kar mura takamaku.
Aii baffah fiyema damura saita kamamu, duk ruwannan nayau akanmu yak'are saboda sakarar yarinyarnan, yay kwafa tareda shigewa 6angarensu.
Girgiza kai baffah yayi yana murmushi. Yaja hannun k'ananun y'ay'ansa suka nufi massalaci.
Suma sauran kowa d'akinsa yanufa, Anty Mamie kuma tatafi da Aysha d'akinta itama.
Duk abinnan dake faruwa mama nad'aki kuma tanajiyo komai, ita sotayima khaleel d'in yazane ayshar wlhy.

Anty Mamie tahad'ama Aysha ruwa mai zafi sosai, kije kiyi wanka Aysha, kid'an shiga ruwan kona minti gomane.
Tana hawaye tajinjinama Anty Mamie kanta.

Shima yana shiga d'akinsa yafara cire jik'ak'k'un kayan jikinsa, sai tsaki yaketa zubawa, sosai yakejin sanyi, dakewa kawai yakeyi, shidamacan koyaya ruwa yata6ashi saiyayi mura, ko wanka yacikayi da ruwan sanyi tosai yayi mura bare wannan dakusan durom goma yak'are akansa.
Gashi anfara kiraye-kirayen sallar magriba, da hanzari yashiga bathroom yahad'a ruwa mai zafi sosai yashiga ciki, baiwani 6ata lokaciba yafito saboda za'a shiga sallah, jallabiya yasaka da hanzari yafice.
Sakamakon anad'an yayyafi har yanzun aka had'a sallar har isha'i.
Gabad'ayan mazan gidan suka shigo, sun sako baffansu tsakkiya abin sha'awa, a babban falo aka yada zango.
Harya zauna yamik'e, kai bara nasaka rigar sanyi, wlhy sanyi nakeji.
Idan kasako rigar sanyin kuzo ga shayi nadafa muku mai kayan kamshi, Dan ita ayshama fuskar dukta kumbura, harma zazza6i yarufeta.
Anty Mamie ce mai maganar.
Baffah yace subahanallah, ina ayshar?.
Tana d'akina k'udundune abargo baffansu.
Ya salam, yakamata akira doctor kuwa, Sultan kira Dr Kabeer abokinka.
To baffah

Khaleel najinsu amma yay shigewarsa 6angarensu batareda ya nuna alamar yamaji zancen nasuba, d'akinsa yashiga, yacire jallabiyar jikinsa yasaka k'ananun kaya, dogon wando amma, yakawo rigarsanyi yasa, hular yaja har samankansa sannan yadawo falon.
Hamdiyya takawo masa tea d'in da Anty Mamie tadafa musu, yanasha suna hira da baffah da y'an uwansa.
Ana haka Dr Kabeer yakira sultan akan yak'arso.
Bismillah Doctor shigo kawai ciki.
Cikin girmamawa Dr Kabeer ya gaisa da baffah, yabi dukkan samarin yabasu hannu sukayi musabaha🤝🏻.
Baffah kaine babu lafiya?.
A'a Kabeer, d'iyatace, mu'azzam kuje yadubata ko.
To baffah.
Yana gaba Dr Kabeer Na binsa abaya har d'akin Anty Mamie.
Dr Kabeer yatsa a k'ofar d'akin Dan amasa iso.
Shikuma khaleel yashiga.
Tana kwance bisa gadon Mamie, gaba d'aya tarufe jikinta har kanta, saida yamata kallon minti d'aya, sannan yatako a hankali har gaban gadon, hannu yakai ya yaye bargon, Aysha dake k'ank'ame da filo tanata rawar sanyi, dukda sanye take da jibgegiyar rigar sanyi kuwa, kanta kuma nad'e da towel.
Jin anyaye mata bargo tad'ago kanta da k'yar, ganinsa tsaye akanta yasakata tashi zaune da hanzari, wani mugun tsoronsa takeji aranta, yanzunma fuskarsa a d'aure take babu alamun wasa, wannan yasaka Aysha takasa koda satar kallonsa, dama ga idanunta sunyi nauyi saboda marukan datasha.
Baice komaiba yabama Dr Kabeer damar shigowa, tunda yaga kayan mutuncine ajikinta.
Dr Kabeer yashigo da sallam, khaleel yanuna masa sofa ya zauna, shikuma ya jingina da madubin tareda zaro wayarsa a aljihu yafara danne-danne, saika rantse dukkan hankalinsa akan wayar yake, amma bahaka baneba, hankalinsa natareda su Aysha da Dr Kabeer kema tanbayoyi tana bashi amsa murya a sanyaye.
Aransa yace trouble marker anyi laushi yau, fukarta tad'an tasa, takumayi jajur abinka da fara, tad'an bashi tausayi kad'an, amma haryanzu halayenta mamaki suke bashi, dan kullum da sabon salo take zuwa masa, amma wasu abubuwan nata nasakashi nishad'i kad'an......
Maganar Dr Kabeer takatse masa tunanisa, ya Khaleel kozamu samu tea tad'ansha saboda za'a mata allura, kuma zai taimaka mata tarage jin sanyin.
OK.
Harya yunk'ura zai fita saikuma yafasa, bazai iya barinta itada Dr kad'aiba.
Wayar Muhseen yakira, yana d'agawa yace ka kar6o mata tea wajen Mamie.
Baijira amsarsaba ya yanke wayar.
Babu dad'ewa saiga Anty Mamie da Muhseen sun shigo, lokacin Dr Kabeer yagama ware mata magani, harya fara had'a allura.
Aysha sai hawaye takeyi Dan batason allura dama can.
A'a Aysha kukan kuma namiyene?.
Anty Mamie wlhy banason allurar.
Dr Kabeer yatsaya da had'a allurar yana fad'in to kiyi amfani da maganin kawai...
No, cigaba da had'a allurarka Kabeer.
Jinjina kai Dr Kabeer yayi, yayinda Aysha ta rushe da kuka.
Ko kallo bata isheshiba, Anty Mamie Ce kawai ke lallashinta, muhseen kuwa dariyama yake mata, khaleel yad'ago ido ya kallesa.
Zoka fice.
Fitayay yana kunshe dariyar karta fito.
Anty Mamie tarik'ekata Dr Kabeer yamatsa zai mata allurar, takware baki zatayi kuka ya khaleel yadawo kusadasu batareda yayi maganaba.
Kallonsa kawai tayi tsoronsa yakamata, damacan tana tsoronsan, rashin kunyar datake masa ita kanta batasan sanda hakan ke faruwaba, amma tana danganta hakan da son danne soyayyarsa dake nuk'urkusar zuciyarta..
Har aka gama allurar batace uhumba. Saidai hawaye ke zurara.
Murmushi Anty Mamie tayi kawai, tasan baban nata ba namijin wasan kowa baneba.
Tasha tea d'in, saitasha maganin ta kwanta Mamie.
To Kabeer sannu, kaima babana Aida ka kar6i maganin mura ko?.
To Anty Mamie, amma ni normal ma nakejina, dukda dai nasan dolene sainayi murar.
Shima magunguna Dr Kabeer yahad'a masa, sannan yamusu sallama yafita.
Kan sofa Yakoma ya zauna, Anty Mamie tabama Aysha shayin.
Tanasha tana satar kallonsa, tak'oshi amma tana tsoron fad'a yahau kanta da masifa, haka tadaure ta shanye tas, Anty Mamie tabata maganin tasha.
Saida yaga ta kwanta, har barci ya sureta sannan yafito, kowa yashige d'aki, saboda sanyi, 6angaren Momy yashiga suka gaisa a tsaitsaye yafito.
Shima d'akinsa yakoma yay shirin barci ya kwanta abinsa.



_____________________________

Kwanaki biyu Aysha Na jinyar kanta, amma alhmddlh da sauki, dantana samun kulawa gun Anty Mamie, yanzu tama koma can gaba d'aya, ko fita batayi, ya khaleel ma sai idan yashigo gaida Anty Mamie take ganinsa.
Dukda talura shima kwanki biyun baya zuwa ko ina agida yake yini, Dan shima Murar ta tasoshi gaba.

Yau kuma tunda safe sunata shirin zuwa zariya d'aurin auren bishirah, Dan and'agane dama.
Kowa yafito fes dashi, duka gidan kowa zaije amma banda hajia babba da umme amarya.
Su Aysha sunci gayu cikin wani material mai k'yau Orange color, ammasa d'igon milk, danhaka d'ankwalin suma ya kasance milk da sark'a dadai sauransu.
Baffah da mama da Anty Mamie motarsu d'aya, baffah da driver Na gaba, mama da Anty Mamie Na baya, sai ammah motarta ita d'aya da gwaggo bintu, y'an uku, nuriddin da Ummunoor.
Su hamdiyya, shukurah, Amal, Hasnah, Husnah, Naseeba, Mufeeda wad'anda ya khaleel yasakasu dole zuwa motarsu d'aya.
Sai Aysha, maleeka, Tasleem Ummu aymana (matar ya sultan) da Abashiyya (matar ya mujahedeen).
Sai samarin gidan suma, sun kasu biyu.
Duk hangen Aysha bataga ya khaleel a tafiyarba, haka sukatafi kowa zuciyarsa cikeda farinciki, amma banda hasnah da husna mufeedah, dansu tafiyar dolece agaresu.
Da wuri suka isa zariya, anmusu tarbar mutunci, tamkar sune sarakunan zariya.😜lol.
Bishirah kam tayi murnar zuwansu Aysha, Dan sune suka Zame mata abokai Aysha, tasleem, maleeka, tunda sanda girma yazo mata tana gidansu, anan batada k'awaye.
Bayan an d'aura aure su Aysha dake makwaftan su bishirah sukad'an fito wai zasu zagaya gari.
Gaban ayshane yafad'i lokacin da idonta ya sauka akan ya khaleel dake jingine jikin mota, sanye yake da dakakkiyar shadda Ash color, yasaka hulama ash, yayi masifar k'yau, tunda take yaune karon farko data gansa da manyan kaya, jitai inama zata iya tamasa pic, inda zata fad'a yaji databashi sahawara akan yamaida manyan kaya suturar sakawarsa......
Ihunsu Tasleem ne yadawo da ita duniyar mutane, maleeka tace woow wlhy ya khaleel yahad'u yau, kamar ranar aurensa.
Tasleem tace ALLAH saina masa pic....tayi maganar tana zaro wayarta ajaka, hotuna suka shiga yimasa batareda yasanibashi, Dan waya yakeyi dawani abokinsa daga Canada, kokad'an hankalinsa baikaima kansuba.
Tasleem tace kai Aysha Dan ALLAH kije wajensa mu d'aukeku.
😳kuttt, amma tasleem bakida hankali wlhy, to badaniba.
Dariya sukayi, suna fad'in matsoraciya kawai, kwana nawane zakuyi barci a gado d'aya...
gaban Aysha ne yafad'i, tadubi ya khaleel d'in da k'yau tadubi kanta, aranta saitaji tausayin kanta.
Afili kuma tace ALLAH ya shiryeku wlhy.

Kamar wasa yaga haske nata haska glass d'in motar dayake a jingine, mamaki yakamashi Dan hasken kamar Na camera.
d'ago azababbun idanunsa yayi ya saukeau Kansu tasleem, kai, kajimin yara da iskanci, waidama nisuketama photo?.
Yakai kallonsa akan Aysha data koma gefe tana waya, aransa yace kodawa take waya?.
Ganin ank'ara haskashi yace k! Tasleem kuzonan?.
Atare suka zabura, suka juya zasu gudu, muryarsa mai tsoratar da marajin magana tasauka akan kunnensu, kugudud'in naci ubanku agarin mutane.
Dole suka tsaya, kowa guywa a sanyaye suka nufoshi.
Dankun rainani shine kuketa wani min hoto ko?.
Wlhy ya khaleel k'yau kamana ne, please kayi hak'uri, tasleem tafad'a kamar zatayi kuka .
Ita waccan dawa take waya?.
Wlhy yaya bamu saniba muma.
Jeki kiramin ita.
Dasauri maleeka taje takira Aysha.
Gaban Aysha sai fad'uwa yakeyi tak'araso wajen, a d'arare ta gaidashi.
Batareda ya amsaba yace shiga mota kirakani wani waje.
Kukuma kujirata yanzu zata dawo.
Suka amsa dato, Dan babu damar musu.
Idon Aysha cikeda da kwallah tace ya khaleel please, wlhy........
Ruf tarufe bakinta saboda azababbiyar Harar daya zuba mata, yanuna mata k'ofa alamar tashiga.
Harta fara matsar kwallah tabud'e motar tashiga, yarufe sannan yazagaya shima yashiga yabar anguwar...
Motar nabarin wajen su maleeka suka shek'e da dariya suna fad'in soyayya ruwan Zuma.........😂✍🏿











One luv my sweet Fan's💋💋💋💋❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤.
[9/6, 2:40 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*



🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭



*_part 2_*
(littafi na biyu📕)


7⃣

Tunda suka tafi babu maima wani magana, duk tsoro yacika Aysha, tunani takeyi ina zai kaita.
Yamik'a mata hijjab Fari tas, sai k'amshi yakeyi.
Kar6a tayi tana dubawa, yadin yamata k'yau sosai, batace dashi komaiba tazame gyalenta tasaka, tana k'unk'uni k'asa-kasa akan INA zai kaitane?, batayi zaton yajitaba.
Saidaki zanyi bak'auya kawai, muryar ya khaleel taji batareda tayi zatoba.
ALLAH yabaka hak'uri, tayi maganar a sanyaye, Dan ita wlhy tsoronsa k'aruwa yake aranta, tunda taga yajibgi guys d'innan, dakuma Marin daya mata.
Bai tanka mataba.
Gani tayi sun shiga cikin makarantar A.B.U. zariya, mamaki takeyi mizasuyi anan kuma?.
Guri yasamu agefe yayi parking, d'alibai nata hada-hada, dukda yaud'in ba ranar karatu baceba.
Harya fita Aysha bata motsaba, yalek'o yana hararta, kosaina fiddokine?.
Jiki a sanyaye tabud'e motar tafito, nanfa idon d'alibai Yakoma kansu, y'an mata anga had'ad'd'en gaye duksun rikece, su kallonma ayshar sukeyi amatsayin k'anwarsa, k'ilan yazo nema mata addimetion a school d'inne.
Cikin takunnan nasa Na jarumta yake tafiya, dolene duk mace mai lfy ta k'yasa.😉.lol.
Dukda cikin nutsuwarsa datazama tamkar halittarsa yake tafiya hakan baihana ya zarta Aysha ba, ita tanama had'awa da y'an sassarfa atata tafiyar.
K'ofar wani office sukaje da aka rubuta professor Al-hassan ibn Mahmud, Knocking yayi aka bashi izinin shiga.
Dattijone maicikeda kwarjinin kamalar addini, zasuyi sa'anni da baffah.
Cikeda fara'a yake fad'in lale marhababinka Ibraheem bin Abdallah.
Ya khaleel yak'arasa suka rungume juna kamar yanda larabawa keyi, sanan ya durk'usa har k'asa ya gaidashi, ganin haka itama Aysha tadurk'usa ta gaidashi cikin girmamawa.
Cikeda fara'a ya amsa yana fad'in masha ALLAH sannunku dazuwa d'iyata, bismillah kuzauna kuzauna.
Ya khaleel da Aysha suka zauna a kujerun dake gaban babban tebir nasa, Aysha tayi k'asa da kanta saboda kunya.
Mamaki yayi mugun kama Aysha lokacin dataji ya khaleel yajuya harshe suna larabci shida dattijon, dole tad'ago manyan idanunta masu yalwar gashi ta kallesa, suka had'a ido Dan lokacin yajuyo yana gabatar da ita wajen dattijon amatsayin matarsa dazai aura.
Janye idanunsa yayi yamaida kan sheaik Al-hassan.
Masha ALLAH Ibraheem khaleel, masha ALLAH, cikin harshen larabcin yayma Aysha barka dazuwa akaro nabiyu.
A mugun mamakin ya khaleel d'in shima saiyaji Aysha ta amsa da larabcin, daganan tacigaba da amsa tanbayoyin sheaik Al-hasan da larabcin.
Shagala yayi yana kallon bakinta dake sarrafa larabcin cikin kwarewa danuna tabbas ta ilimantu a 6angaren addini, bak'aramin birgeshi tayiba, Dan baiyi zaton hakaba tunda baffah yasanar masa daga k'asar waje tadawo karatu.
Sheaik Al-hassan ibn Mahmud malamin ya khaleel ne, ahannunsa yay karatun addini a Abuja, aikine yadawo dashi A,b,u zariya.
Sundad'e basu had'uba saboda yanauin aikin ya khaleel d'in, shiyyasa dayazo d'aurin

Please Login or Register in order to submit comment