Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hak'uri khaleel yayta bata.
Takama hannun Aysha itama tana Neman gafararta.
Aysha tace babu komai wlhy, tayafe mata, itama tayimata afuwa akan abubuwan dataita mata narashin girmamawa.
Momy tace babu komai, aini najama kaina Aysha, kuma tabbas nayi nadama, ina ALLAH wadai damasu irin halina, Bilkeesu kuyafeni keda fad'ima Dan ALLAH, kema Ammah ki gafarceni."
Gaba d'aya kowa yace ya yafe mata.

Haka suka barota suna kewarta, itakuma tana kuka dak'arar nadamar abinda ta aikata, gashi inda rayuwarta tak'are abin bak'inciki da dana Sani.
Amma taji dad'i da d'iyar mufeedah ta mutu, data rayu haka zata taso taji tarihin azzalumar kakarta, wadda tazama sanadin saka uwarta ahali mara k'yau.
Ga ubanta a prison, yayar ubantama a prison duk cikin labari guda d'aya.
ALLAH ngd maka.


"Hummm ALLAH Sarki momy, yaukam tabani tausayi gaskiya😒, ya ALLAH karabamu da hassada.


*******

Haka rayuwar tacigaba da tafiya, Su Aysha sun kammala arba'in, tasha gyara kam sannan aka maidata d'akinta, suka cigaba dakashe juna da soyayya itada Sadaukinta, suna tattalin d'ansu junior, Wanda kowama keso agidan.
Ya khaleel yadage wajen k'yautatama mahaifiyarsa, hakama Aysha, ba'a barta abayaba, sosai take bama mama da Anty Mamie kulawa, hardama ummi amarya.
Zuminci da 'yan uwanta kam ba'a cewa komai, kowa tana basa hak'insa.

Ansha bikinsu musleem dasu tasleem.
Saidai muce ALLAH yabada zaman lafiya kuma.

Zuwa lokacin junior yayi 6ul-6ul dashi, abin sha'a da birgewa.

Ya khaleel kam sai k'arin kwazo yake awajen aikinsa, nak'asa dashi sunajin dad'in rayuwa dashi, shima haka take agareshi.




___________________________
*_4year's ago._*

Bayan shekaru hud'u nalek'a su Aysha.
Natadda abubuwa dayawa sun canja agidan, amma suna cikin aminci da farinciki, tareda soyayyar juna.
Ammah nanan bata canjaba😎, saima abinda yay gaba, ga tsufa sosai yakuma kamata, danma akwai kulawa daga 'ya'yanta da matan 'ya'yanta, da jikoki.
Ganin kowa yana cikin aminci agidan saina zarce 6angarensu Aysha.

A falo Na iskesu suduka.

Khaleel Na kwance a doguwar kujera, yalumshe idanunsa tamkar mai barci, amma idonsa biyu, tsabar tunanine kawai.
Aysha nazaune a kujera maizaman mutum d'aya, tana danna waya, gefenta kuma ga yankakken Apple tanaci, saidaifa tana fama da k'aton cikinta🀰🏻, haihuwa yay ko gobe.πŸ˜‚πŸ‘πŸ»

Junior yafito daga d'akinsa d'aukeda buk, yaro yagirma masha ALLAH, kamanninsa sunkuma fitowa da babansa sosai, gashi d'an orobo hakannan.
Shekarunsa hud'u kenan aduniya amma sai wayon tsiya da surutu.
Gaban Aysha yaje yatsaya, yata6a hannunta yana turo baki gaba.
d'ago ido tayi tana kallonsa, yanuna mata khaleel dake kwance har yanzun.
Murmushi tamasa, sannan tamasa magana da ido.
Yasan mitake nufi, Dan haka kaitsaye yanufi inda khaleel ke kwance yahaye saman cikinsa.
Firgigit khaleel yadawo duniyarsa, tareda sauke ajiyar zuciya, yasaka hannu biyu ya rungume junior sosai ajikinsa tareda sumbatar sumar yaron.
"My j miyafune? dama ba barci kakeba?".
Girgiza kai junior yayi, yad'an turo bakinsa alamar shagwa6a irinta yara.
Yace, " Abbah batun d'azun nazoba amma kak'i kulani, sai Ummie ce tamin maganama".
Murmushi khaleel yayi, sannan yatashi zaune dashi, kallon Aysha yayi fuskarsa d'aukeda murmushi haryanzu, itama kallonsu take tana murmushin, tareda d'age gira sama.
Khaleel yajanye idonsa akanta yamaida akan junior, ''sorry my j, miyake faruwane?".
"Abbah homework, gobefa Monday, Ummie tak'imin wai batada lfy, uncle Usama zai zaneni inbanyiba".
" babu mai zanemin baba a school, bara yanzun muyi, Ummie kam barta, zamu ramane, zamuje yawo next week amma banda ita".
"Yauwa Abbah, karmuje da ita, baffa ma yabani sweet d'azun bazan bataba itada unborn d'inta ko?".
Daga Aysha har khaleel dariya sukayi kawai.
Yagama koya masa homework d'in sannan ya lalla6ashi yay barci ajikinsa.
Kwantar dashi yayi akujerar yakoma kusada Aysha dahar yanzun taketa latse-latsen waya.
" waini mikikeyi hakane dakika sharenima?".
Cikin dariya Aysha tace Kodai ka shareni sadauki, badan junior ba bansan sanda zaka dawoba."
Cikinta ya sumbata. tareda kumatunta, ''sorry my sholyna, natafi tunani akan aikine, kinsan kullum matsalar kenan."
"Hakanekam sadauk'ina, ALLAH yacigaba da tsaremin kai daga idanun mak'iya."
"Amin sholyna, wai yaushene zaki haifomana sabon babynmune? Nida junior mun k'agara, kullum zuba ido muke."

Kamar wasa Aysha tad'an yatsine fuska tana fad'in yauma zai iya zuwa, Dan tunjiya nakejin alamun hakan".
Da Sauri ya khaleel yace, "da gaske?".
Kafin tabashi amsa taji an tsikareta amara, 'Yar k'ara tasaki, wadda tasaka khaleel rudewa.
Kamar wasa saiga k'aramar magana tazama babba.
Adaren dai Aysha a hospital takwana, gabbanin asuba ta sunkuto d'iyarta mace, maikama da babanta Ibraheem khaleel, kuma yayanta Junior.

Fad'a muku farincikin da wannan familie ma suka shiga aii 6ata lokacine, yarinya taci suna haleematu, sunan Ammah jar wuyaπŸ˜‚πŸ‘πŸ».

Aikam bakuga murna wajen Ammah ba, ansaka sunanta.

Har prison aka kaima momy baby haleematu, aikam tasha addu'a.

Haihuwar haleematu babu nisa mufeedah ma ta haifi d'anta namiji, Dan tuni tayi aure itama, haihuwarce dai ALLAH baikawo dawuriba sai yanzun.



*********

Wai nikam wane janrai akemin hakane? tun d'azun naketa jiranki amma kinwani manta dani?."
Juyowa Aysha tayi tana kallonsa, saikuma ta kauda kanta tana murmushi, ''babu wani Jan raifa, banaga kana tareda abokan hiraba?".
"Humm bayan sunyi barci tun d'azun, junior ma yariga haleematu yin barci, kinbarni inata dakon jira". 'Yay maganar yana rungumeta tabaya.'
Hannu tasaka ta shafo fuskarsa, ahankali tafurta sorry my lollipop sadauki, aini takace, inanan ina shiri dominka".
Cikin shinshina wuyanta yace, " shiyasa kullum k'aunarki sake k'aruwa take araina, tunda nafara ganinki bakibar zuciyata ta hutaba, I love you so much my sholy".
Wlhy nima haka sadaukina, kamantar dani kowa, ka mantar dani komai.
I love you trillionsπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹β€.



To masoya nimafa I love you trillions agareku.


Tammat bi hamdullah.


_Anan nakawo k'arshen wannan labari nawa, Wanda naima ba daidaiba acikinsa ya gafarceni, banyi dancin zarafin kowaba, ALLAH yasa mu ammafana da sak'on dake cikinsa, kuskuren danayi ya ALLAH ka gafarta min, sannan kuma Ku watsar da kuskuren ciki gefe, Dan nima 'Yar Adam ce ajiza._.


*_bansan irin godiyar dazan nuna mukuba akan k'aunar buk d'innan dakukayi, saidai nace kawai ALLAH yabar zuminci da k'aunar juna, ngd ngd harma babu adadi, inata k'aunarku har k'arshen numfashina. Bakuma zanta6a mantawa daku acikin ruhinaba da tarihin rayuwata, wad'anda basuga sunansuba Dan ALLAH sumin afuwa, bawai bana k'aunarsu bane, a'a wlhy, sunanan aran Bilyn Abdul koda ban sansuba.πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹β€β€β€β€β€β€β€β€._*



_Masoyan UMMIE GARKUWA, saiku fara baza idanu, domin gwanar tamu tanan d'aukeda sabon buk d'inta mai suna KHAIRIYYA!!, shimafa zaizo muku da sabon salo tamkar yanda ta k'ayatar damu aciki buk d'inta mai suna JENNIFER._
_karku manta da sunan KHAIRIYYA, yana nan tafe insha ALLAH._






Alhmdllh




✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻Daga alk'alamin Bilkeesa Ibraheem
(Bilyn Abdul Ce)β€β€β€πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹




SharhiπŸ‘‡πŸ».


*_πŸ“²Typing_*


🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......_*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_


*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*


*_HASKE WRITERS ASS......._*
_(Home of expert and perfect writers)_


*_part 2_*
_(littafi Na biyuπŸ“™)_


*_MIYE MANUFAR BILYN ABDUL A LABARIN CIKI DA GASKIYA?_*


_Tambaya mai muhimmanci, wadda kafin kowa yamin, niyakamata nayima kaina._

_ba burina idan kun karanta labarin *CIKI DA GASKIYA* kubarsa ananba, a'a, burina kud'auki muhimman abubuwan ciki Ku amfana dasu, labarin *ciki da gaskiya* dunk'ulallen labarine, amma mai tafiya da harshen damo. labarine dayazo muku da abubuwa da dama._

Bara nafara da jarumin matashi Ibrahim Abdallah, Wanda yataka rawar gani ajigon labarin.


_Ibraheem Abdallah matashin saurayine dakowane matashi yakamata yayi koyi da tsarinsa dagashi har abokansa, Taheer, Joseph, youseef, harma da Adams._
_bashida tsoro ko kad'an, sannan da zuciya d'aya yake aiki, ko sigari wannan bayasha, baya neman mata, akullum kuma yak'i yake da k'arya, gashi da zuciyar taimakon nak'asa dashi, yana kuma girmama nasama dashi, a fannin familie nasa da iyayensa kowa yabonsa yakeyi saboda k'yawawan halayensa._

Shin abin tambaya anan, duk mi yakawo wannan?.

_kai tsaye zan iya nuna muku yarik'e martabarsa ta matashine, wadda ayanzu hakan yayi k'aranci ga matasanmu, kullum idonsu nakan 'yammata, burin yin kud'i kota halin k'ak'a, d'aukar shaye-shaye amatsayin wayewa, raina nagaba dasu saboda sunaji da tashen balagar samartaka, rashin yin biyayya ga iyaye saboda jahiltar wayewar zamani, dakaga kakai tsawo shikenan iyayenka sunzama abokan wasanka, fifita ilimin boko fiyeda Na addini._
_Dan ALLAH tayaya za'a samu nasarori arayuwa? Tayaya zaku iya zama Ibrahim Abdallah j?, k'alilannefa acikinku masu irin wannan k'yak'yk'yawan tunanin, k'arancinsu yasaka kowa ganin tamkarma babusu._
_Dan Allah Matasanmu Ku gyara please, kune ginshik'in kowacce al'umma, daku duniya take alfahari, kudaina shaye-shaye, domin kullum ruguzaku yakeyi, yaruguza k'ashenmu da al'ummarmu, kudaina zina, kullum durk'usar daku takeyi tana k'ask'antar daku, kudaina barandar siyasa, inbahakaba kullum a 'yan Turin mota zaku k'are, Ku turasu sukoma kan mulki suna zaginku dafad'a muku kune lalatattun matasa, dole kuma kuringa amsawa, Dan bakuda za6in daya wuce hakan, rayuwar j abin birgewa daban sha'awa, amma miyasa yazama haka?, saida yakasance mai yawan hak'uri da gaskiya, yature Duk wani abun jin dad'i da samarin yanzun suke d'aukarsa amatsayin ado wa rayuwarsu, sannan yazama mai yawan nasara. Dan Girman ALLAH kufarka daga nannauyan barcin daya d'aukeku, Ku daidaita rayuwarku, kunutsu kuyi karatu, kudaina karatu domin burin aiki, karatu wata katangace agareku, idan kun mammala kobabu aiki Ku kama Sana'a, kubar girmankai, k'ila wannan sa'ar itace mafi alkairi arayuwarku, amma kullum idonku nakan k'aton offices, why?._
_Dan ALLAH kucanja kodan kuma Ku amfana, kuzama jarumai irin Ibrahim Abdallah, bafa wai jaruman littafi sunfuku wani abubane, suma mutanene tamkarku, muna kafa musaline dasu domin kuma kuyi koyi da halayensu, hartakai mun rubutaku duniya takarantai labarinku._

ALLAH yasa mudace.



_Lamarin Aysha abin birgewa da k'ayatarwa ga kowacce mace, matashiya kokuma babbar mace. anrabata da iyayenta tana 'Yar k'aramarta, ankaita wata k'asa mai nisa, batada kowa awajen sai ALLAH daya halicceta, abin birgewa dukda k'ank'antarta bata mance dafad'ama ALLAH kukantaba, haka tadage dare da rana wajen kai lamarinta ga ALLAH, Wanda shikad'aine zai iya kawoma rayuwarta mafita, duk kuma Wanda yarok'i ubangiji zai amsa masa, Aysha tarok'a kuma ya amsa mata, datasamu damar k'aratu batayi wasa da damarba tanutsu tayi, cikin wad'anda ba k'abilarsu d'ayabama, amma bataji shayi ko burin kasancewar gazawarta ba agaba-gaba ba wajen nuna kwazonta da jajircewa_.
_sannan kuma taginu akan wani k'yak'k'yawan buri nason ku6tar damata dayawa dasuka tsinci Kansu cikin irin rayuwar datake, walau dasaninsu, koda tirsasawar wasunsu, ahakan hartasamu ceto rayuwar meerah, wadda tafidda rai dagama shiriya baki d'aya, alokacin kuma data samu damar k'arfafa mijinta saitazama mai k'arfafashin, da nuna fushinta wajen son yataimaki matan wannan al'ummar damuka kasance cikin gararin rayuwa, bayan addininmu yamana gata, amma wasu tsiraru acikinmu suke nuna zalinci da k'arfa-k'arfa akan hakan._
_yakamata 'yan uwana mata muyi koyi da Aysha, muzama masu kishin junanmu dasanin darajar juna, muzama masu k'arfafa zukatanmu wajan fallasa asirin wasu 'yan jari hujja dake wargaza rayuwarmu komin kusancinmu dasu kuwa, da wannan jarumtar Aysha tasamu damar fallasa asirin su momy har aka d'auki hukunci akansu, datayi shiru tsoro yahanata haka rayuwar zatayita tafiya da walagigi da sauran mata. Kuma wlhy abinda su momyn nan suke aikatawa agaske yana faruwane yanzun, saidai shugabanninmu sunyi burus da lamarin😭._
Mata muzama Aysha, koda k'ar6ama rayuwarku 'yancintaπŸ€·πŸ½β€β™€.


_Mama, mama ta birgeni kwarai da gaske, zan iya cemukuma tafi kowa birgeni, Dan bata d'auki kishin banza da wofi mara amfani da amfanar da matan wannan zamaninba ta yafama kanta, tazama adalar abokiyar zama, mai mutunta mutuncin zaman tare, danuna adalci irinna koyarwar addininmu, uwa tagari, maiso ceto wasu 'ya'yan dasuka shiga gararin rayuwa, tayi tawakkali dayin abinda bakowacce uwa bace zata iya, wajen hana cutar da 'ya'yan wasu, ta sadaukar da rayuwar tata d'iya._
_ALLAH mai alkairi, saiya dubi k'yak'k'yawar zuciyarta yatsare mata tata d'iyar kuwa, abinda yay k'aranci awannan zamanin kenan, wanima bai Isa tsawatarma d'an waniba, bare har takai ga sadaukarwar cutar kai wajan ceto wasu, iyaye mugyara Dan ALLAH, mudunga duba gobenmu bawai jiyanmuba, Dan tarigada tawuce saidai labarinta, ALLAH yabamu k'yak'yk'yawar zuciya irin ta mama, mai sauk'ak'ama kanta kishi da bak'inciki, dawatace saitace INA ruwanta, aii khaleel ba d'anta baneba, d'an kishiyane, idanma ya salwanta batada asara, amma baiwar ALLAH batayi hakaba, saita jajirce har saida tamaidashi hannun mahaifiyarsa._


_dolene Mamie ta birge kowa, kodan hak'urinta da kawaici akan cinkashi da hajia baba taita mata, sai bata zamo tanamata rashin kunyaba, komin zafin abinda Tamata bata daina girmamataba, amatsayin uwargidan mijinsu, tahad'a 'ya'yan agidan tarik'e baki d'aya, vata Nuna banbanci agaresu, hakan yasaka taita bama d'anta kulawa batareda tasaniba, tarage masa rad'ad'in rashin samun kulawar daga momy wadda yakema kallon mahaifiya, dabata jasa ajikiba koda gaskiya tafito bazaiji soyayyartaba aransa, saboda zaicigaba da kallonta amatsayin kishiyar uwane.._
_saimu gyara 'yan uwana mata, mudinga lura, idan Kane agidan miji amatsayin amarya karmu hantari 'ya'yan Uwargida, bakasan ranar dazasumakaba anan gaba, Dan doledai 'ya'yankane zasuzo amatsayin k'anana, idan Kana cutar da 'ya'yan Uwargida, sumafa zasu ringa huce haushinsune akan 'ya'yanka, ko bayan idonkane kuwa, please saimu kiyaye, kowacce Matsala kagani akwai tushen k'irk'irarta wlhy, mata muyi koyi da wannan baiwa Anty Mamie, ALLAH yasa Mugane amin._


_dolene ayabama Ummi amarya itama, Dan awannan zamanin bakowane zai iya abinda tayiba gaskiya, musamman idan mukayi dubi da yanda kishi yake awannan zamanin, yarinya kafin tashiga gida tafara kishin iyayen agidan, hakan ba daidai baneba, Ummie amarya tayarda da Auren baffah domin taimakon mama akan manufarta mai k'yau, mata masu irin zuciyar ummi amarya sunyi k'aranci, burin kowa ya Auri mai dukiya yazauna shikad'ai babu kishiya, please mugyara kafin lokaci ya k'ure mana_.


_samun iyaye irin baffah awannan zamanin kad'anne, musamman idan akwai wasu 'yan canji a hannunka, zakiga kullum Baka maida hankali akan tarbiyyar 'ya'yanka, uzurinka yafi kulada familie naka, aganinka karigada katara musu dukiya, shikenan buk'atunsu da nauyinsu akanka yak'are, gobe kana waccan k'asa jibi kana wancan taro, bakada lokacin iyalinka ko kad'an, dasunzo maka da buk'atar kud'i sai zaka biya musu awuce wajen, maganar tarbiyyarsu kuma kabarma matan gidanka, bayan kuma hannu d'aya bayan d'aukar jinka, musamman awannan zamanin da duniyar tarikid'e gaba d'aya, iyaye Dan ALLAH kunutsu akan tarbiyyar 'ya'yanku, walau kaid'in talakane komai kud'in, Dan wannan zamanin bawai 'ya'yan masu kud'i bane kad'ai lalatattu, wlhy tawani fanninma 'ya'yan talakawa sunfi 'ya'yan masu kud'in lalacewar, Dan haka ko'ina akwai Na kirki akwai Na banza, ALLAH dai ya gyara mana kawai, ALLAH ka shiryemu dai baki d'aya._



_idan muka d'auki jigon labarin baki d'aya ZAMU kula yatafine akan hassada baki d'aya, domin hassada itace tazama tushen komai._

_badan innah jummai tatashi da hassadar Ammah ba da komai baikasance hakaba,, hasaada tasakata gur6ata tarbiyyar 'yarta d'aya tilo, hassada yasaka d'ora momy a keken 6era Na burin zama wani Abu wajen Tara dukiya domin akirata da suna hamshak'iyar mace, badan wannan dalilinba da momy bata Shiga k'ungiyar ('ya'yan kunama ba), datayi hak'uri tazauna agidan mijinta lafiya, dabatayi tunanin cin gadon Alhaji Abdallah jigawaba, bare harta dinga kallon haihuwar mata amatsayin dakushewar komanta, har takaita ga sace d'an abokiyar zamanta, domin kawai yazama jari a burinta, wannan hassadar Ce hartakai ga shafar mufeedah batajiba bata ganiba._
_hassada masiface wlhy, domin kunga innah jummaice kawai taginata, amma tacigaba da zagaye mutane masu d'unbin yawa acikin masifa, innah jummai ta Reni momy akan hassada, momy kuma tareni 'ya'yan ta gallabar rayuwar wasunta irinsu mama da Anty Mamie, hartazama sanadin salwantar wasu mutane dayawa._
_Amma abin kaico, dukkan abinda suke burin akansa ALLAH yabasu, daga k'arshe kuma saiya zama rugzajje, Mara amfani agaresu, saima yazame musu sanadin nadama da Dana Sani, k'ask'anci da d'umbin kunyar rayuwa, Yakamata Mugane hassada tamkar tubalin toka take, koda kaginata danisa watarana saita ruguzo idan tatashi da mutuncinka kuma zata rushe. Hassada babu k'arama babu babba acikinta, komin samanka kuma saika fad'o idan kakasance mutum mai hassada, koda bakayi k'arshe irinnasu innh jummaiba kuwa, kuma mafi yawan mai hassadama wlhy sanadin bugawar zuciya yake mutuwa, ko hawan jini._

_a wannan zamanin ko kishi damata keyi hassada tafi yawa aciki, Dan ba'a kishi irinna matan manzon ALLAH (s,a,w), wannan nabama kowacce mace dama tazauna tayi nazari akan hakan kuma._πŸ€·πŸ½β€β™€

_soyayyar Khaleel da Aysha abin birgewa, kowacce mace tana burin samun irin wannan rayuwa, gashi kuma itace tayi k'aranci, Dan mazajenmu sunfi fifita Neman kud'i akan iyalinsu, k'alilanne acikinsu ke bama matan kulawa, amma da anyi aure wata uku tayi yawa soyyaya tazama tarihi saikuma zaman hak'uri dana 'ya'ya, wlhy ko kar6uwar novels damaida hankali wajen son karatun buks Na soyayyar damukeyi yasamo asaline daga k'aranci kulawa ta mazajenmu akanmu, towatama batasan irin wannan soyayyarba sai novels, shiyyasa idan muka saka tayi yawa saikiji ana k'aryatamu, Dan ALLAH maza kugyara, ko yawaitar zinace-zinace da buri irin Na mata yana tafiyane wajen k'arancin kulawar damuke samu, kishin kansa damata keyi harda rashin kulawa, domin ita kanuna mata soyayyar awaje, amma tana shigowa gidan sai komai ya canja, kakuma koma hangen wata awaje, kana bata kulawar dabaka bama wannan tagidan, kaga kuwa kataro March wlhy, amma muma matan dazamu nutsu muyi hak'uri dasaikiga abin mamaki, itamafa tana shigowa gidan rabin shekara yayi yawa zata fara kwasan makamancin d'acin dakika d'iba sanadin shigowarta, Dan itama kwanaki kad'an idonsa zai fara komawa kan shinshino wata kuma awajeπŸ˜‚πŸ€­, bulalar data doki uwargidafa, itace zata jibgi amarya watan watarana._
_mun kasa fahimtane kawai, amma maza sun maidamu sakarkaru wlhy, ahanaki zaman lfy da jituwa tsakaninki da 'Yar uwarki jinsinki, sannan sukuma kullum suna gefe suna dariya dakiranku mahaukata baki d'ayaπŸ€•._
Saimu farka idan munga zamu gane, idan bazamu ganeba kuma muyitayi, muke tareda wahala, sudai babu ruwansu.



_kobabu komai Ammah jar wuya tsohuwar arzik'i ta nishad'antar dakuπŸ˜‚, kowa zaiso yasamu kaka irin AmmahπŸ˜‰πŸ‘πŸ»πŸ€£._



Bara nabarku haka, badan nagajiba, saidan watarana cikakken sharhin wannan labari zai iya zuwa muku kaitsaye daga k'ungiyar haske, bayan antaceshi an tankad'e kuma an rairaye.

Takuce har kullum, mai sonku da k'aunarku.

Bilkisa Ibrahim
(Bilyn Abdul)


Marubuciyar.✍🏻

*_Rashin sani!!._*
*_auren k'addara ko biyayya?_*
*_k'anwar uwace ko kishiyar uwa?_*
*_Nida aminiyata!!_*
*_Nawaff!!_*
*_Sabon al'aree!!_*
*_kukan kurciya....!!_*
*_Ban saketaba!!_*.
*_Abdul-maleek bobi!!_*
*_Karayar arzeek'i!!_*
*_sanadin bikin sallah!!_*
*_ciki da gaskiya!!_*.


_duk zaku iya nemansu Ku karanta, karkuma kiji tsoro ko kunyar tunasar dani wani kuskure danayi acikinsu, kifad'amin ta k'yak'yk'yawar sigar dazan fahimceki vatareda cin zarafiba._


_banyi ciki da gaskiya domin cin zarafin kowaba, hakama sauran buks d'inna, saboda yanayin rayuwama nak'i fad'ar wani matsayi daga 6angaren aikin khaleel, shikansa ban fad'i girman igiyar kakinsaba, so hakan yafi sauk'i._
Idan kin karanta saiki gyara abinda kikeyi Mara k'yau, kodan gudun fad'awa hanya Mara k'yau, idankuma burin yi ne dake saiki cireshi aranki.


ALLAH yasa Mugane, mu anfana da abinda muka samu aciki, Wanda yazama kuskure ALLAH ka yafe mana baki d'aya.



ALLAH ka gafartama iyayenmu dadukkan musulmai dasuka rigamu gidan gaskiya.


Duk Wanda na6atamawa ayayin rubutun wannan labarin ya gafarceni, nayine akan rashin sani, ALLAH ya yafe mana baki d'aya.



Abaya nace next novel d'inna ABINDA KASHUKA.... Tom yanzun naga ana rubuta abinda ka Shika, so watak'il zan iya canja sunan nawa labarine idan hali yazo da hakan, idankuma naga babu sunan daya dace dashi to zanyi amfani da wannan sunan nafarko.


Insha ALLAH a next year zakuga Sabon buk d'inna.


Inama kowa fatan alkairi.




Bilyn Abdul Ce.πŸ˜‰πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»


Ngd kwarai da gaskeπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹β€β€β€β€β€

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment