Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kina nufin bai dawoba har yanzun Anty Mamie? to kodai aikine yamasa yawa a office?".
.....bana tunanin haka, sultan, kasan zuciyar babana, kuma hankalinsa atashe yake yanzun, nafi tunanin badai lafiyaba gaskiya".
''Bara muga nakira Adams naji".
Wayar Adams sultan yakira, ko gaisawa basuyiba yace, ''Adams ya khaleel fa?".
Cikin muryar barci Adams yace, "bayana gidaba ya sultan? nazata tare kuka tafi d'azu da safe aii?".
" A'a, kasan yama rigamu barin hall d'in".
Babu shiri Adams ya janye Amal dake jikinsa tana barci yatashi zaune."
"Ya sultan kana nufin baya gida?, barato naje office na duba, amma idan har Oga ba aikine dashiba bayakai wannan time d'in a office gaskiya."
"OK nima ganinan zanzo, muhad'u a can, dukda nasan bazasu barni na shigaba".
" A'a kajirani amota idan kaje, idankuma narigaka zuwa shikenan".
"OK".
Bayan ya Yanke wayar ya kalli Anty Mamie da Aysha dake tsaye tafito daga toilet, taji dukkan abinda yafaru, wannan yasakata cigaba da zubar da kwallah, tana addu'ar ALLAH ya tsare mata mijinta aduk inda yake.
"Anty Mamie bara naje office Na duba, zamu had'uda Adams a can, Dan bazasu barni nashigaba idan nikad'aine".
" hakan yayi, amma kira mujahedeen kuje tare, Dan dare yayi, har 12 takusa".
"Anty Mamie da'an barsa, k'ilama yayi barci yanzu, zan iya tafiya nikad'ai babu damuwa".
"Shikenan, amma dai daka duba ko Muslim ne kuntafi tare".
"to bara Na duba idan baiyi barciba, saimun dawo".
Addu'a Anty Mamie tamasa yafita yana amsawa, ta maido kallonta ga Aysha da har yanzu take a tsaye.
" k'araso kiyi sallan kinji Aysha, insha ALLAH yana nan lfy, ki kwantar da hankalinki".
Jin jina kai Aysha tayi, tak'araso tad'auki hijjab ta kabbara sallar isha'i dabatayiba tana barci.


*******
6angaren su muslim ya sultan yashiga, a falo ya iske Muslim yana kallon kwallo, cikin mamaki Muslim yace, ''ya sultan lfy kuwa a wannan time d'in?".
"Da dai sauk'i Muslim, ya khaleel ne bai dawo gidaba har yanzu, shine zamuje office mu duba".
Da Sauri Muslim ya mik'e yana fad'in "ya salam, mujeto ya sultan."


_____________

A k'ofar gate suka iske Adams yana jiransu, yarigasu isowa.
Fitowa yayi yashiga motarsu sannan suka k'arasa gaban gate d'in, dukda sun gane Adams hakan bai hanasu bincikensuba, saida suka tabbatar babu komai ajikinsu sannan aka barsu suka shiga.
Kai tsaye office d'in ya khaleel sukaje, sunyi knocking yafi sau goma amma basuji ko motsiba.
Komawa tacan baya Adams yayi yalek'a ta window, office d'in dind'um da duhu, ya kunna fitilar wayarsa ya haska, can ya hango khaleel zaune a kujerarsa ya kifa kansa bisa table d'in gaban kujerar, ajiyar zuciya Adams ya sauke, yazagayo wajen k'ofar indasu Sultan ke tsaye suna knocking har yanzu.
Dukkuma knocking d'in dasukeyi khaleel najinsu, amma ko motsawa baiyiba barema yay tunanin tashi ya bud'e musu.

Adams yace, "ya sultan yana ciki, amma nasan bazai bud'eba, bara nagani kozan samu Oga Victor Na nan asamo wani key d'in."
"To Adams, ALLAH yasa adace".

Kusan mintuna 40 saiga Adams yadawo da keys d'in, saida yagwada kusan 4 sannan aka dace k'ofar ta bud'u.

Kunna fitilar office d'in Musleem yayi, haske ya gauraye ko ina, har alokacin khaleel bai d'agoba, kuma duk yanajin motsin shigowar tasu.
Da sauri Sultan yak'arasa gareshi, " ya khaleel mike faruwane haka? kasaka hankalin kowa yatashi agida, Aysha sai kuka takeyi tun d'azun, hakama Anty Mamie hankalinta atashe yake".
"Please ya khaleel katashi muje gida Dan ALLAH. kayi hak'uri ya khaleel?".
Da k'yar khaleel yad'ago manyan idanunsa dasukayi matuk'ar jajur, ya zubasu akan sultan, sannan yamaida ya lumshe.
" please mana ya khaleel ".
Girgiza kai khaleel yayi, yamusu Alama da hannu alamar sutafi su barsa.
" A'a ya khaleel, yazamu tafi mubarka a wannan halin, bayan hankalin kowa nacan atashe, kayi hak'uri dai mudafi gidan kawai". 'Musleem nevyay maganar muryarsa nazuga alamar tahowar kuka'.

Adams yamatso kusada Sultan, murya k'asa-k'asa yace, "ya sultan inaga yakamata kakira Anty Mamie kawai, k'ila idan itace tamasa magana ya yarda yabimu, amma inhar damon mune bazaijeba".
Cikin na'am da zancen Adams sultan yace shawararka tayi.

Anty Mamie Na zaune akan sofa, Aysha ta kwanta ta d'ora kanta bisa cinyarta, barci 6arawo ya saceta batareda ta shiryaba, wayar Anty Mamie Ce tafara ring, ganin sultan ne tad'aga da hanzari.

" Anty Mamie please kimasa magana da kanki, mudai yak'i saurarenmu, gashinan a office ya kulle kansa, dak'yar Adams yasamo wani key d'in aka bud'esa".
"Bashi wayar".
A Hans free sultan yasaka wayar, Dan yasan ya khaleel bazai kar6aba.
Lallashi da ban magana Anty Mamie taitayima khaleel, saida k'yar ya amince zaizo gidan, sultan ya yanke wayar sannan suka taimaka masa yatashi suka fito, bayan musleem ya tattaro dukkan wayoyinsa da laptop d'insa, Adams ya kulle office d'in suka taho.
" Adams kawuce gida kawai, Dan dare yayi".
"Bara Na rakaku kawai ya sultan".
" A'a kaje Kawai, saida safe".


_____________

Gidan shiru kowa yayi barci, dama babu Wanda yasan sun fitama.
Har khaleel zai nufi 6angarensu Sultan yace, ''aii Ayshan tana wajen Anty Mamie ".
Baice komaiba yajuya yashiga babban falon, sukuma suka bishi abaya, zaune suka tadda Mamie Aysha kuma tayi barci ajikinta.
Ahankali Anty Mamie tafurta Alhmdllh.
K'arasowa khaleel yayi yazauna gaban Anty Mamie, shima d'ora Kansa yayi bisa cinyarta kusada kan Aysha.
Ahankali Anty Mamie Takawo d'ayan hannunta saman kansa tana shafawa kamar yanda take shafa Na aysha.
Jin hannun mahaifiyarsa bisa kansa sai yaji wasu hawaye masu zafi Na ziraro masa, ahankali suka ringa sauka bisa cinyar Anty Mamie.
Rintse idanunta Anty Mamie tayi, domin jin saukar hawayen khaleel ajikinta, itama saiga NATA hawayen suna kwarara, jikin sultan da Muslim yayi sanyi k'alau, sultan KASA daurewa yayi yajuya yafita kawai, shima idonsa cikeda hawaye.
Musleem kam jingina yayi da bango yana kuka shima, hakannne yak'ara k'arfin kukan Anty Mamie, da sauri musleem yafice ad'akin, Dan bazai iya sauraren kukan mahaifiyar tasuba.
Har kusan 12:43pm suna nan zaune ahaka, babudai Wanda yace uffan, jin shirun yayi yawa yasaka Anty Mamie lek'a fuskar khaleel, murmushi Anty Mamie tayi, ta duk'o ahankali ta sumbaci kan Aysha, shima sumbatar kansa tayi sannan ahankali tace, "babana".
Bud'e idanunsa yayi dasuka koma k'anan saboda barci, ya kalli Anty Mamie.
Tashi kaga nasamo maka wani abun kaci, saika d'auki Aysha kuje Ku kwanta, dare yayi.
Kansa ya girgiza mata alamar ya k'oshi.
" ban yardaba, tashi kaidai".
Bamusu yajanye kansa daga cinyarta, cikin dabara tajanye Ayshama ta maida mata kanta bisa filo.
Maida kallonsa yayi kan Aysha, tausayinta yakamashi, ganin fuskarta duk jirwayen hawaye.
Matsawa yayi yad'ora hannunsa akan gashinta yana shafawa ahankali, yakai fusakarsa kusada tata ya sumbaci goshinta da kumatunta, akan la66ansa yafurta I love you so much A'eesha".

Babu dad'ewa Anty Mamie tadawo d'aukeda mug d'in tea, sai k'aramin fleet ta d'oro cake.
'Dan janye jikinsa yayi daga kusada Aysha saboda kunyar Mamie, itama guntun murmushi kawai tayi ta ajiye masa kayan hannunta, daure kad'ansha koda tea d'inne, saikasha magani ku kwanta, Dan jikinka kaima zazza6ine, Aysha dai nata ya sauka.
Kansa ya jinjina mata yana kar6a, k'asan zuciyarsa nawani tsitstsinkwa saboda k'auna da tattali irin Na uwa mahaifiya, Wanda abayyane yake kallon nisan banbanci tsakanin momy da Anty Mamie.
Wardrobe Anty Mamie tabud'e tad'auki kayan barci, sannan tad'akko magani tamik'a masa, "gashinan kasha idan kagama, saiku rufemin d'akin indan kunfita, baffanku Na jirana".
Murya a shagwa6e wadda shikansa baisan dad'in yima uwa shagwa6aba sai yau, yace, ''Mamie anan zamu kwana kawai".
Murmushi tayi, tace, " to ALLAH yabamu alheri, ni nayi nan."
Bata jira amsarsaba tafice.
Tana fita yashare hawayensa. Kad'an yaci cake d'in, amma ya shanye tea d'in, yasha magani sannan yamik'e, kayansa kawai yacire, yazauna dagashi sai vest da boxer, yashiga toilet, wanka yayi yay alwala yafito, har lokacin Aysha barcinta takeyi.
Wayar Muslim yakira yace yakawo masa jallabiya d'akin Anty Mamie.
Babu dad'ewa ko saiga musleem da jallabiya, dayake shima badaga bayaba wajen tsawo, haka yake shima tamkar khaleel d'in.
Sallah ya kabbara, yana tsaka da sallan Aysha ta farka.
Da sauri tabud'e idanunta akan khaleel dake sallah, babu shiri taduro a kujerar, gabansa tadawo domin son gaskatawa, ta zauna tazuba masa idanu tamkar yaune tafara ganinsa.

Atsanake yake sallan harya idar, yay addu'oinsa sannan yamaido hankalinsa kanta, fuskarnan dai babu walwala ko kad'an.
"Sholyna ya jikin?". 'Yafad'a cikin lumshe idanu'.
Ajiyar zuciya ta sauke, saikuma tafara hawaye, " haba ya khaleel, inakaje haka? Kasaka hankalinmu dukya tashi, nata kiran wayarka kuma kak'i kayi picking call d'ina, why?!".
Baice mata komaiba, sai jawota dayayi jikinsa ya rungumeta, ahankali yake buga bayanta.
Itama saitayi luf ajikinsa batareda takuma tambayarsaba, Dan tasan bazai tankaba, kusan mintuna 10 suka d'auka haka, sannan yamik'e da ita ajikinsa, gadon suka koma, ya kwanta tareda kwantar da ita ajikinsa, yaymusu addu'a. Shiru nawani lokaci hardai barci farawo ya sacesu sudukan.


To asuba tagari🤸🏻‍
♀🚴‍♀.


____________________________

Hajia babba dai ciwo ya kankama, ko magana bata iya yi saida gefen baki, yawu kuma Na zirara, hakama 6arinta Na dama babu abinda ke aiki, hatta da idonta, sai'an kwantar sai an tayar, babu lalal6awar da su Taheer basima khaleel ba akan yashiga su dubata yak'i, saisu kad'ai sukaje, kuma yak'i fad'ama kowa halin datake ciki agidan.
Yanzu yakoma wani shiru-shiru, ko magana kamasa saiya gadamar ansaka, kummlum fuska babu alamar yasan miye dariya.
Dole baffa da Anty Mamie suka duk'ufa wajen tofa masa addu'oi aruwa yanasha, hakama Aysha tana nata k'ok'arin, Dan kokad'an itama takasa gane kansa.
Anty zuwairah itada Anty shukurah dasu mufeedah har 6angarensa sukazo suka nemi yafiyarsa, musamman ma Anty zuwairah, har Aysha saida ta rok'a ta yafe mata, hakamasu mufeedah.
Aysha tace babu komai wlhy, dama bata rik'esu araiba itakam.


**********

Yau kuma Ammah tasaka baffah ya tara kowa agidan, bayan jawabi da nasiha mai ratsa jiki aka fara tattauna abinda ya had'asu.
Kusan dai suk akan abinda yafarune, baffah da Ammah duksun yima mama godiya, hakama ummi amarya da gwaggo bintu, baffah yace bashida abinda zai saka musu dashi, musammanma mama, yana Addu'ar ALLAH ya sakakanka musu da aljannah, sannan yana neman afuwar mama akan abinda yafaru alokacin daya saketa, hakan tafaru akan rashin Sani da ajizanci irinna d'an adam,.
Mama tace babu komai wlhy, dama tuni ta yafe masa, tunda tasan ba laifinsa baneba, kuma komai yawuce, tunda gashi har ALLAH ya k'addara zasu sake zama tare, gashima harda k'yautar 'ya'ya uku ya azurtasu dashi.
Itama tabasu hak'uri akan 6oyewar datayi, sannan tayima ummi amarya da gwaggo bintu godiya akan taimakonta dasukayi, takumayi addu'a da fatan alkairi ga family d'in baki d'aya, sannan tabama su Anty zuwairah hak'uri akan su gafarceta, batayi hakan domin cin zarafin mahaifiyarsuba, batada za6in daya wuce haka, saboda rayuwar yara mata dabasujiba basu ganiba dataketa salwanta, inhar irin wad'annan abubuwan zasu cigaba da faruwa muna zuba idanu saboda 'yan uwanmu na a ciki, to haka zamuyita rugujewa, watarana kuma 'ya'yanmu za'a d'auka asaka acikin irin wannan gararin rayuwar, danhaka kumin afuwa Dan ALLAH.

"Babu komai wlhy mama, muduka mun fahimceku, kuma hakan shine dai-dai, Dan gashi kuskuren momy harya shafi mufeedah, to watarana Kansu Najwa zai dawo, wlhy bazan ta6a bama momy goyen bayaba akan zama shugaba wajan yaryad'a mutuncinmu akan titiba, nasha damuwa dama akan amintakar dake tsakanin momy da hajia khaltum, amma kona nemijin ba'asin wani abunda sukayi dabai daceba sai momy tacemin sirrine, nadad'e inason Sanin wannan sirri nasu, Ashe bana alkairi baneba, khaleel Kaine kafi cancanta abama hak'uri, domin momy tayi walagigi da rayuwarka, ni nasan wannan tun ina yarinya, saidai zuciyata bata ta6a d'arsamin wani Abu dabanba, saboda nayi nisa wajen kwaikwayo da koyin halayen momy, Dan ALLAH kamin afuwa dagakai har Aysha, Dan itama nasaka hannu wajen k'untata."
Jin jina kai khaleel yayi, yace, "babu komai Anty zuwairah, komai yarigada yawuce, har gobe kuma momy nanan dakima a idona, saidai hakan bazai hananin hukuntata akan laifintaba, nima Ku gafarceni tawannan ga6ar, sannan mama ina godiya agareki, kece tushen komai, lallai da ace akwai irinki dayawa agidan aure da kowacce mace tabar kishin banza da wofi, an sace d'an kishiyarki, amma kullum idonki abud'e yake wajen Neman hanyar ku6tar dashi, lallai ked'in jarumace, maihalin dayakamata mata suyi koyi, suzama masu kishin junansu, bamasu kishin abinda zai iya kaisu wutaba, Dan kishin yanzu babu komai cikinsa sai shirme. Ummi amarya kema dolene a jinjina miki, Dan kema kintaka rawar gani irinta jaruman mata masu zuciya Saliha, ALLAH yabiyaki da alkairinsa, gwaggo bintu kece fitilar komai, Dan dabaki bayyana firar momy da hajia khaltum ba babu Wanda zaisan wannan sana'ar tasu, ALLAH yabiyaki da mafificin Alkairi, wannan abin alkairin naki. Yasakani biya miki saudia, sannan namiki alk'awarin siya miki gida a Kano madaidaici tunda bakida 'ya'ya, daga yanzu kuma duk kan buk'atunki dakikejin zaki iya fad'ama d'anki yamiki toki sanar dani su, karkiji nauyin hakan."
Kukan dad'i gwaggo bintu tafashe dashi, su Ammah Kuma suka shiga saka masa albarka, kowa kagani sai washe baki yakeyi saboda halaccin da khaleel yayi.
Yamaida kallonsa akan Aysha, cikin murmushi yace, "ngd matata, tabbas nagama dacewa, babu abinda zance ga Ammah saidai godiya, kinsha gwagwarmaya domin ganin kin ceto sauran mata 'yan uwanki, gakidai k'arama amma mai kwakwalwa da tunanin manya, irinku k'asarmu take nema, namiki alk'awarin cigaba da sonki daganan har k'arshen numfashina, sannan Na tanadi k'yaututtuka kashi-kashi agareki, amma dagani saike zan bayar, inama iyayena albishir dacewa damacan Aysha ce za6in raina, tunkan sumin tayin aurenta, tun sanda tazo gidannan tana 'Yar mililiyarta...............................................................kaf yakwashe labari yabasu.
Nanfa akaita masu dariya, Ammah tasakasu gaba da tsokana.
Farincinkin kowa yadawo, kaikace wani Abu bak'in ciki baishigo familie d'inba.
Daga k'arshe Anty Mamie tarufe taron da godiya mai yawa agaresu, tareda addu'oin fatan alkairi, sannan tace daga ranar tayima mama k'yautar ya khaleel gaba d'aya, Dan itace tafi cancanta da zama uwa agaresa, kodan wahalhalu datasha adalilinsa, dakuma sadaukar da d'iyarta jininta datayi wa duniya duk adaliln tushen abinda yafaru dashi, takumace daga wannan ranar Aysha ta zama daga cikin 'ya'yanta, dama tun sanda tafara ganinta saida taji hakan aranta.
Gaba d'aya aka d'auki kabbara, baffah da Ammah duk suka saka mata albarka, baffah yace, "tabbas nima randa nafara ganin Aysha saida naji fad'uwar gaba, amma narasa tamicece, tunkuma alokacin naga tsantsar kamarta da fad'ima, nayidai shirune kawai Dan banida tabbas, amma lallai Aysha tayi namijin k'ok'arin data cancanci yabo da jinjina ga kowa". ' yak'are maganar da tsokana'.
Yace.
"Koda yake, kuganefa Aysha gadon jarumta tayi fa".
Gaba d'aya aka saka dariya, Aysha ta saka tafin hannunta tarufe fuskarta saboda kunya.
Annanne baffah ya yanke hukunci akan hasnah da Husnah su fidda mijin aure, sannan mufeedah takoma gaba d'aya 6angaren Ammah har ALLAH ya sauketa lafiaya itama tasamu mijin aure, yace kuma ya yafe mata, danya d'auki hakan amatsayin k'addara, daganan yakumayin nasiha agaresu, danuna musu illolin hassada, Dason zama wane, dakuma burin Tara abin duniya, Wanda duk ta dalilin hakanne hajia babba ta tsinci kanta a wannan halin, Wanda hud'uba irinta uwa tayi tasiri aranta, amatsayinku Na iyaye kudinga nunama 'ya'yanku abinda zai zama alkairi arayuwarsu ba sharriba, sannan karku ringa zagin wasu agaban 'ya'yanku ko gulmar wani agabansu, koda kuwa mutuminnan yamuku ba daidaiba, hakan nasaka 'ya'ya sutashi da k'iyayyar wani azuciyarsu, harma da burin d'aukar fansa akan laifin dabasu akayimawaba, muzama masu k'yak'yk'yawar zuciya dason junanmu, muruk'e zuminci domin babban abune da ALLAH yamana albishir Na zuwa aljannah a sanadinsa, muzama masu yafiya wa juna alokacin dawani yayma d'an uwansa laifi, ALLAH ya albarkaci rayuwarku gaba d'aya, yasaka k'aunar juna da hak'uri azukatanku, ALLAH ka gafarta mana."


Gaba d'aya aka amsa da amin baffah, daganan dai kowa yanemi gafarar d'an uwansa, baffah yace, Anty zuwairah da Anty shikurah su shirya sukoma d'akunansu hakanan, tunda komai yalafa, sukuma cigaba dayima mahaifiyarsu addu'a.
Ammah ma tasakama kowa albarka sannan tarufe taron da addu'a kowa yakama gabansa...................✍🏻




Jiya kunjini shiru, anguwa naje tareda Oga wlhy, nadawo kuma a late, babu damar typing a time d'in, ga gajiya kuma.






*_ALLAH ka gafarma mahaifanmu baki d'aya, dadukkan 'yan uwa musulmai😭😭😭🤚🏻✋🏻._*
[10/26, 4:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*


🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_


*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*


*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu📘)_


_d'ingimemiyar gaisuwa ta iso agareku_
*_pherty xarah (ALLAH yakaimu ranar aurenki muzo sokoto musha shagali my kakus💃🏻🤸🏻‍♀) & Ummu Aysha (ALLAH ya kaimu ranar auren Aysha muyi rawar shaku-shaku😂🤸🏻‍♀)_*.

_ALLAH yak'aro muku haske a rubutunku kuma, ALLAH katsare k'ungiyar Haske dadukkan writers d'in dake cikinta 🤚🏻✋🏻, wannan shafin nakune gwarazan marubuta👍🏻👍🏻👍🏻_



4⃣8⃣


'Dakin taron tsit yake, da alama khaleel ake jira kawai, Dan kowa ya hallara, kayan hannunsa ya ajiye tareda had'e hannayensa waje d'aya alamar ban hak'uri da Lattin dayayi🙏🏻.
Duk manyansa ne awajen, shikad'aine k'aramima, kwazonsa da jajircewarsa akan aikice tasakasu shigo dashi cikin meeting d'in, Dan abinda za'a tattauna akai shine jigonsa.
Bayan bud'e taro da addu'oi suka fara abinda ya tarasu kai tsaye.
Jawabai sosai akayi, mafi yawa tashafi k'ungiyar su momyne kuma.
Khaleel aka bama damar tashi yayi jawabi akan nasarorin dasuka samu, dakuma abubuwan da aka kama k'ungiyar dasu.

Bayan khaleel yayi gaisuwar ban girma agaresu, yayi add'u'oi, sannan yafara jawabi cikin nutsuwa a harshen nasara ingilishi.

_"munkama mutane 57 dake cikin wannan k'ungiya, tareda bindugu 16, sai hodar ibilis (cocaine) datakai nauyin cg 1800,0 dawani abu, sannan akwai kwayoyi masu had'arin gaske suma masu yawa, saikuma yara 'yammata damuka ku6tar awani gida su 84, wasu acikinsu anyimusu viza za'abar k'asar dasu, akwai kuma 21 damuka samo a wasu k'asashe guda biyu"._
_har yanzun muna farautar kusan mutane 109 dake k'ashe daban-daban tareda yara kusan kimanin 800 da aka fitadasu tawasu hanyoyi daban-daban ak'asarnan. Akwai uku cikin wad'anda suke hannunmu suna kwance babu lfy acikin asibitinmu, saikuma 26 da suka mutu tawasu dalilai, wasu aciki mune muka harbesu, wasukuma sunmutune kawai, akwai mutum d'aya da aka bashi guba yamutu, Wanda munan muna bincike akan hakan, insha ALLAH kad'an garage mukawo sunayen masu hannu acikin kisan nashi."_
Saikuma mutun kusan 78 dawasu k'asashe suka samu kamawa 'yan Nigeria, wad'anda aka tabbatar sunada alak'a da k'ungiyar, suma munata k'ok'ari wajen ganin mun kar6osu, andawo dasu nan gida Nigeria ammusu hukunci dai-dai dalaifinsu. Da akwai mutane 13 ahannunmu dasuka fito daga k'ashen k'etare suma, wasu k'ashen suna buk'atar mubasu 'yan k'asarsu domin sumusu hukunci a k'ashensu, to badai muce musu komaiba har yanzu, munanan muna tattaunawa akan batun dai.
Saikuma jami'an tsaro dasuka fito a fannoni daban-daban guda 11 damuka samu cikin wad'an nan criminals, bincikenmu kuma ya tabbatar akwaima wad'ansu dabasu halarci wannan taronba aranar da'a kamasu, kuma gaskiya acikin manyane, dole saida had'inkan Ku za'a samu Damar kamasun, dukda akwai shirin damukeyi ta k'ark'ashin k'asa akansu.
Wannan shine bayanan da k'ungiyar tashafa, saikuma wad'anda basuda alak'a da k'ungiyar, muna shirin mik'a wasu kotu.
Suma d'in zamu shirya kaisu kotu acikin next week insha ALLAH.
AKWAI mutane uku dake hannun hukuma sss, d'aya d'an k'ungiyarne, biyu kuma laifinsu daban, munason suma subamusu danmu saka d'ayan cikin 'yan uwansa.
Yak'ame tareda salute Nasu Baki d'aya, sannan yadawo wajen zamansa ya zauna.

Gaba d'aya aka d'auki tafi, jikake raff raff raff!!!.

Lallai dolene hukumar police Interpol tamik'a gagarumin jinjina dayabo akan wannan gwarzon ma'aikaci nata, wannan hukuma da Nigeria harma da duniya baki d'aya bazasu ta6a mantawa da Ibraheem Abdallah ba, j! gwarzon ma'aikacine dayakamata ayi koyi dashi akowanne fanin d'ammara Na kaki, yakawomana nasarori masu yawan gaske, Wanda bamu kad'aibama duniya gaba d'aya dolene tayi alfahari dashi, yaje k'asashen duniya daban-daban yagudanar da aikinsa cikin nasarori, sannan wasu k'asashen sun gayyacesa domin taimakonsu duk Dan kwazonsane kuma, wannan k'ungiya damuke magana akanta ankai kusan shekaru 16 ana bincike akanta, amma bamu samu wani bakin zareba saida aikin yakoma hannun j!, jinjina agareka Ibraheem Abdallah, ALLAH yacigaba da haskaka rayuwarka kaji, ALLAH yasa ka d'ore ahaka kar watarana ka canja.
Gaba d'aya aka amsa da ameen.
Yacigaba da fad'in akwai ganawa da shugaban

Please Login or Register in order to submit comment