Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miji namata dodorido da sake auro irin jinsinta na mace domin k'untata, sannan yanacan awaje yanacin zarafin mutuncin 'Yar uwarnan tata mace a hotel ko'a office. datayi maganar Neman 'yanci yace zai saketa yamaye gurbinta da 'Yar uwarta mace, kullum mazan birni cikin had'a wutar masifa suke a tsakanin mata, dakaga mace tadage tana haki da hura hanci da taune harshe wajen tanki intaka to akan namijine._
Sannan kuma sai'a ringsla samun mata 'yan jari hujja irinsu hajia laura da hajia khalum suna safarar matannan domin kaisu k'ashen duniya amatsayin hajar siyarwa mafi tsadar farashi da yalwatuwar riba mai tsoka.
Karka d'auka gwamnatin k'asashen Africa da jami'an tsaronmu basusan da wannan gur6atacciyar sana'arba.
Sun Sani sarai, sunkuma son anayi.
Kasan miyasa suka gaza d'aukar mataki kuwa?.

Tasaki guntun murmushi mai ciyo, sannan tacigaba.
Sungaza hanawane saboda suma suna amfanuwa da wannan kasuwancin, Koda amfanuwa ta fannin aljihu, kokuma amfanuwa ta fannin biyan buk'atunsu, da wannan kud'in cin zarafin Matan suke yima matayensu nagida hidima, dasu suke ciyar da 'ya'yayensu dake killace agida, dasu suke jar fata da mazurai acikin al'ummarsu, sannan dasu suke amfani wajen keta martabar sauran Matan dasuke killace agidajen iyayensu ko mazajensu, tunda anmaishe da mata 'yan tsaki, da'an watsa mana tsaba saimu fito muna tsatstsaga.
Abin bak'in cikin bamuna tsatstsagar tsabar bane domin son murayu cikin salama, kosan mu k'arfafa rauninmu wajen Neman 'yancin ketama Junanmu mutunci, a'a muna tsatstsagar wannan tsabarne domin gyara halittar jikinmu ta daidaita mu burge mazajennan dasuka watsa mana tsabar, munyi hakane domin gobe mufito cikin nagartar burge wad'annan mazajen, haka zasuyita watsa mana wannan tsabar munaci nuna gyara kammu dominsu, ahaka har rayuwarmu ta lalace mukoma jagororin ingiza saida mutuncin sauran mata nak'asa damu.
Inda za'a zauna tebirin tattaunawa saikaji ance mata sun lalata duniya, mata sunfi shaid'an shed'anci, shin idan mace shaid'aniyace? Dawa take shaid'ancin? Kuma danwa take shaid'ancin?.
Wad'annan tambayoyin nakeasn duniya damazan duniya subani amsarsu๐Ÿ˜ญ.
Ya khaleel Kasan kuwa d'umbin mata dake rayuwa cikin k'unci da bak'inciki kuwa?, kullum ana k'wasar yaranmu ana kaiwa saudia cibiyar addinin islama dasunan aiki amma hajace ta tallatarwa wa mazan wannan k'asa, kaimu akeyi domin k'ask'antarwa da tozarta Kimar 'ya mace da mutuncinta, ana amfani da rauninmu wajen wargaza dukkan martabarmu, shin bakwa tunanin raunin mazajen k'asarmu wajen sakacin rik'e mata agidajen aure yake kawo wannan kwad'ayin na mata Masuson tafiyar wasu k'asashe bayan angama yaudararsu?.
Kuje kuga Matan dake zuwa saudiyya danufin aiki acan, a k'ask'ance suke, marasa daraja ake kallonsu, kullum cikin mulkin mallaka aikatau da fataucin mutuncinsu ake, (ita batayi zaman aureba, bakuma tayi bautar ALLAH ba cikin nutsuwa) haka ake binsu kamar tumaki dagudu ana kamawa, why? Ya khaleel. Mata why dabazaku farkaba?.๐Ÿ˜ญ
Inhar k'asa irin saudiyya bazata San mutuncin daraja rayuwar 'ya'ya mataba to bansan ina mace zataje tasamu mafakaba aduniya ya khaleel, inhar za'a iya tarwatsa mutuncin mace a k'asa mai tsarki to tabbas babu wata k'asa da 'ya mace zataje ayi tunanin dawowarta da mutuncinta.
Inhar dagaske kakeyi ya khaleel, inhar da gaske kaid'in ka banbanta da sauran jami'ar tsaro dake k'asarnan to katashi domin ceto rayuwar mata dayawa da'aka salwantar da sanin iyayensu koda rashin saninsu, da yardar Matan koda tilastawar azzalumai 'yan jari hujja irinsu hajia laura, ninan namaka alk'awarin taimakonka da sirrika masu yawa danake dasu batareda sanin kowaba๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ.

Tak'are maganar dafashewa Dama tsanancin kuka mai cin rai da zuciya.
Da Sauri ya khaleel yataso yatareta saboda tangad'in hajijiyar fad'uwa datakeyi.
Cikin kakkasar murya tace, "karka ta6ani saikamin alk'awarin zakayi, saikamin alk'awarin bada kwakkwkwarar gudunmawa, saikamin alk'awarin fara nuna misali akan momy, karka duba wahalar raino datasha akanka, karka duba shak'uwar dake tsakaninka da ita.
Katuna 'ya'yanmu masu tasowa, katuna wannan cikin dake jikina indan nahaifi mace wace irin rayuwa zata tsinci akanta?, katuna da su momy sunci nasarar tarwatsa rayuwata wane bak'inciki zaka tsinci kanka.............?

Bai bari ta k'arasa ba yace..............โœ๐Ÿป













๐Ÿ˜ฑ๐Ÿ˜ฑ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹โคโคโคโคโคmata ku farka

*_Typing๐Ÿ“ฒ_*


๐Ÿคฐ๐Ÿป
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{๐Ÿ”ชwuk'a bata hudashi๐Ÿ—ก}_


*_Bilyn Abdul ce๐Ÿค™๐Ÿป_*


*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu๐Ÿ“˜)_

*_kud'in nadabbane agareni, dolene gaisuwarkuma tazama tadaban, ina k'aunarku ainun, domin munzama 'yan uwan juna, ALLAH yabar mana zuminci 'yan group d'ina, my diamonda d'ina, kune gold d'in bilyn Abdul๐Ÿ˜‰๐Ÿ˜‰๐Ÿ˜‰๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜โคโคโค_.*

hajara gambo (uwargida), fatima Muhammad (mom Ammar), Zainab Zubairu Maitama( Zeezu byr Mytama, Ummu abdulnasirr(Ainah Buhkari), ummul Ahmad momy twice, khadija Auwal(maman Farhan), Hassernath Jalingo, zahra abbakar (Ummu unborn), Sadiya Aminu, ๐Ÿ’…๐Ÿผteemahcute๐Ÿ’…, Aysher Bello, Nanerh๐Ÿง•, Beentahmk, khadija Muhd (Dee), Deeyerht, NANA YAKAKU, AISHAT UST, preety zee๐Ÿง•๐Ÿผ, zainab Gadaka, ๐Ÿ‘‘๐Ÿ’…๐ŸผUmmu iman, Mrs usman, Beeky, mummyn ihsan, Mmn zeey baby, rahma salihu, Xynab, Hauwa magaji, Falmata Ibrahim, Falhat, xaenab ibrahim, Mmn walida, Fatee Ibrahim umar, โˆ‚ั”ั”ื ฮฑัะฝโœ, Smart lady, maman zeey, Falmata Ibrahim, Maryam Lanko, Zakiyat, Jamila Fika, Saddiqa musa, Aeasher2๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜, Rukayyah R K Y๐Ÿ˜๐Ÿค, Nanah๐Ÿ˜, Deeyerht, Ameera๐Ÿ˜˜,Rukky, Aysha Mustapha, Aeesha Isah, Zainab Ibrahim, Dr hairas H~, Mmn Khalid da sajida, RUKAYYA BALA SURU, binta a abubakar, Aysha rabiiu, khadija Mustapha, Bilkissu๐Ÿ’‹๐Ÿ’„, Aisha Dantanko, Bilkissi Niger , Maman Umar, Aisha Awais, Meenasko, Maman sudais, Ommeetah, Hafcee, Amina lawal, Bilkis , Maijidda (mamin mua'azzam), Meenasko, Hadiza (mom yasmin), Teemah yola๐Ÿ’…๐Ÿป, Asmy smiler , Hafsat Ahmad, Akori kishiya Aci daula, Aysher, Mom Afrah๐Ÿ˜, Ummun Hajiya, Surayya Auwal, Eashan mamanta๐Ÿ˜๐Ÿ‘ธ, Hassanat ismaeel๐Ÿง•, *Muneerah Muhammad (M3)*, Aaeesha, xeeyhert Muhammad , Lawisa sani, Zeetah๐Ÿ˜˜, Mrs Shariff, Mom aysher, faryderh โฃโฃ, Sadiya abdulwaheed, Deedee gwarzo, Zainab maman zainab.

_bilyn Abdul ta gaisheku k'yauta๐Ÿ˜‰๐Ÿ‘๐Ÿป_.


4โƒฃ4โƒฃ

"Kinga nutsu muyi magana mana".

Cikin kuka tace, "bazan ta6a nutsuwaba ya khaleel, sai mahukuntan k'asarnan sunyi tsawatarwa akan 6arnar dake faruwa ga mata, gidanjen aure bamu tsiraba, kullum mace tana fama da damuwa, idan zaka zauna da mata dubu to wlhy d'ari tara acikinsu dukzasu fad'a maka suna zaman aurene saboda 'ya'yansu, ammafa badan jindad'i agidan aurenba, kullum mace saidai ta karanta tattali da soyayya a cikin novels, shiyyasama wasuma suke ganin zak'ewar writers wajen rubuta yawan tattali da soyayya anovels, sabida su basa gani agidajen aurensu, shiyyasa mata sukafi kowa yawan kallon films, saboda anan kad'ai suke ganin ana sayyaya maiban mamaki, ba'a barmu agidaba, ba'a barmu amakarantaba, lectures da students 'yan uwanmu kullum suna farautar mutuncinmu, sunsan dukkan hanyoyin dad'in baki dazasubi domin janye hankalin yarinya su lalatata, lectures kullum suna kadamu a jarabawa idan mun hanasu kammu, sukan bama wadda tabiya buk'atarsu koda bata cancanci samun wannan makinba, ta wannan hanyar anruguza rayuwar wasunmu bada sonsuba, a offices ba'a barmu ba, kullum manya nasama damu farautar rayuwarmu sukeyi, idan kin bada had'inkai a k'ara miki girma, idan kin bijire a k'ask'antar dake ko'a koreki daga wajen aikinma gaba d'aya. K'ananun makarantu Na primary da secondary nanma mata basu tsiraba, komin k'ank'antarki sai'an samu malamin dazai dinga bibiyar mutuncinki, kan hanya kullum taremu ake ana mana fyad'e, yaranmu da manyanmu, amma koda ankai kotu babu wani Abu da alk'alan sukeyi, k'arshema sai a koro k'arar ace bakuda shaidu, idan kuwa an yanke masa hukuncin to bazai wuce Na shekaru uku ba, kuma harda tara, daya biya taran shikenan sai'a sakeshi ya tsira, itakuma ya haddasa mata bak'incikin dahar tamutu bazata ta6a mantawaba, hakama iyayenta, yanzu kuma abin bak'inciki anmaidamu tumakin ciniki akowacce kasuwa, daidai farashinka daidai aljihunka, dakabiya saika kama, shikenan kasamu dabban tirkawa, kullum kabata dusa domin tattalinta, itakuma yunwa da kwad'ayi yasakata lashewa, ribarka sada ita kazuba kud'in aljihu, kokuma kaita ga mahauta su yanka maka, aimaka filla-fillah da namanta kazo ka soya kanaci ahankali kana nishad'i.
Haba ya khaleel, shin maza sunmata uwace ta haifesu? Inhar uwa nada daraja a idanunsu baikamata sudunga keta mutuncin sauran mataba, kosun manta sun haifi 'ya'ya matane? Sun manta matane abokan rayuwarsu? Sunmanta Nana Aysha macece? Sun manta Aminatu (mahaifiyyar Manzon ALLAH s,a,w) macacece? Sun manta Nana Maryam macece?, sun manta Nana fad'ima macece?, sun manta Nana khadeejah macece? Sun manta..... Sun manta dayawa?, shin miyasa darajar kimar mata tafad'i awannan zamanin???.
Mata wannan tanbayar daku nake, kune yadace Ku amsata ba mazaba, domin kune lalacewar kanku, banta6a ganin gidan karuwai Na mazaba, banta6a ganin namijin da suturarsa ta mutunci ta banbanta data banzaba, haba mata, atunaninku shigar banzace wayewa? Atinaninku tallata kankune mutunci?, kwad'ayine da son asani yajefa mata duk cikin wad'anna had'arin Na rayuwa, kuzauna kuyi tunani, kuyi tunanin gyarawa sannan maza suji Shankar keta mutuncinku, kucirema zukatanku kwad'ayi dason burga inhar kunason tsira da muncinku wlhy, idanfa 6era nada sata, daddawafa nada wari, sai bango yatsage k'adandagare kesamun gurin kwana, duk Wanda yakwana lafiya shiyyaso, wani lokacin laifinmu yafi namazan yawa, bazaki ta6a ganewaba saikin nutsu akan kura kuranki..............

Da sauri yatareta tafad'o jikinsa, saboda juwar datayi hajijiya da ita, ak'asa suka zube, rungumeta yayi dak'au yana shafa bayanta, muryarsa a tausashe yace, "kiyi hak'uri hakanan A'eesha, tabbas da ace mata nada irinki dabasu tsinci kayinsu ahalin dasuke cikiba yanzu, namiki alk'awari insha ALLAH zanyi amfani da aikina wajen kawo gyara, koda ban gyara dukaba zanyi iya bakin gwargwado, nasan baza'a rasa mai irin burinaba dazai d'ora daga inda natsaya, ki kwantarmin da hankalinki, kinga bake kad'ai baceba, banason babyna yafara fuskanta damuwa tun yana ciki kema INA buk'atar lafiyarku kinji.
Kanta ta jinjina masa, tana cigaba da zirar da hawaye, shikuma yana share mata, saida yaga tadawo cikin 'Yar nutsuwa sannan yad'auketa suka nufi d'akinta, shirin barci sukayi suka kwanta bayan khaleel yamusu addu'a, dukda yana buk'atarta haka ya hak'ura danya kula yau masu rigimarne akusa, shi baima ta6a tunanin haka A'eesha takeba, Ashe itama akwai zuciya, jiyayi k'aunarta nakuma ratsa dukkan sassan jikinsa da 6argo, ya furzar da huci tareda k'ara k'ank'ameta๐Ÿ˜‰๐Ÿ’‹.



_____________________________

Kwance take tana kallonsa haryagama tsane ruwan jikinsa, ya d'akko mai yadawo bakin gadon kusada ita ya zauna, idonsa akanta yad'ora hannunsa Na dama bisa gishinta.
"My sholy tunda zazza6in ya sauka kidaure kitashi hakanan kiyi wanka ko?."
Yatsine fuska Aysha tayi tana d'ora hannunta kan nasa, murya a sanyaye take magana, ''ALLAH Sadauki banajin tashinne, bank'i nawuni kwanceba batareda nayi komaiba, gaba d'aya sainaji jikina a kasalance."
Lumshe idanunsa yayi yana murmushi, ''karki damu komai zai dai-daita idan cikin yay kwari kamar yanda Amman tace, amma kuma ahaka da kikemin kurin komawa aiki?".
"ALLAH sadauki sonake nagama bautar k'asana cikin salama, kagafa wata biyu kacal ya ragemin".
" hakane, insha ALLAH kuma zaki k'arasa kinji. tashi muje namiki wankan mu shirya, karya zam mukad'ai ake jira kuma".
"Kai sadauki, ina zamujene haka wai? Kuma duk mutanen gidan?".
" basai nafad'aba, kedai kawai tashi Na shiryaki zaki gani aii."
Batace komaiba ya taimaka mata ta sakko, kayanta tacire ta d'aura towel.
Yace muje to.
"A'a kayi zamanka Na hutashsheka, gamma naringa k'arfafa jikina, yanzu kwatsam tafiya ta taso maka wazai dinga tattalina haka? gamma Na daureda koyaya inayin wasu abubuwan ko?."
Kansa ya jinjina mata yana murmushi, azuciyarsa yana jinjina wayo da hikima irinnan Aysha, ita komai nata dabanne.
Mai shima yashafa, sannan yafice d'akinsa domin shiryawa.
Itama Aysha bata 6ata lokaciba tafito, adaddafe dai tad'an shafa mai, tasaka doguwar riga ta material, kayan sunmata k'yau, ta d'aukko madaidaicin gyale tayi rolling, tsaf tafito kamar wata balarabiya, tana cikin zuba d'an abinda zata iya buk'ata koda sun fita a jakka ya khaleel yaturo k'ofar yashigo da sallam.
Bata d'ago ta kallesaba amma ta amsa masa sallamarsa. tsaye yayi abakin k'ofa ya jingina da bango yana kallonta, tamasa k'yau sosai, hardai yakasa hak'uri ya tanka.
"Yanzunan da wannan shigar zaki fita?".
d'agiwa tayi ta kallesa, sanye yake cikin uniform d'in aiki, sunyi masifar zaunamasa ajiki, tajanye idonta ahankali ta maida kan jikinta, " haba sadauki miye aibun wannan shigar tawa?, ko inafa Na jikina arufe yake, tafin hannuna da fuskatane kawai ake gani.
Guntun murmushi yayi, yatako ahankali har zuwa gabanta, jawota yayi jikinsa ya rungumeta, a cikin kunnenta yace, "bazaki ganebane kedai, ina kishin aganemin wannan k'yak'yk'yawar surarne sholyna, ALLAH ya halicceki domin nine kad'ai, danhaka Na haramtama kowa ganeminke."
Cikin jin dad'in kalamansa tashafo fuskarsa, akasalance tace, "ngd Sadaukina, bara Na canja to".
''No barsu, amma next time akiyaye".
"Angama boss", tafad'a tana kanne masa ido d'aya, da salute nashi".
Shima k'amewa yayi yay salute nata.
Atare suka tuntsure da dariya, yakama hannunta suka fice suna cigaba da dariyarsu, idan kagansu dolene su burgeka.
Cikin gida suka shiga, afalo duk suka tadda ahalin gidan, sunyi cirko-cirko suna kallon innah jimmai daketa zuba tsiya, ajiya labari ya isketa, da yamma ta'iso Abuja, saita kwana gidan wata mata dasuke mutunci, shine yau ta k'araso nan gidan domin jin ba'asin kama mata d'iya da'akayi.
Daga Aysha har ya khaleel, babu Wanda ya kalli ko inda take, khaleel ma saiya nufi dining inda su sultan ke zaune suna breakfast shida muhseen da Ramadan.
Duk gaidashi sukayi, muhseen yace, "ya khaleel wai baffah yahana atakama tsohuwarnan birki, please, kamana maganinta mana".
d'an ta6e baki khaleel yayi, yad'au mug d'in shayi yana k'ok'arin had'a shayin, " to inbanda abinka muhseen, tunda baffah yace abarta, aii sai kowa yazuba mata Na mujiya, lokacintane tayi, anjima kad'an koda kud'i aka had'ata tayi tari bazatayiba. kaga mik'omin kularnan tagabanka Ramadan, minene aciki?."
"Fankasunefa yau Anty Mamie tayi agidan, ALLAH nifa banason abinnan".
" saika zauna da yunwa aii, koka saka matarka ta girkamaka wani abun, ai su Mamie nema suka barku, kunyi aure amma har yanzun kuna nane dasu suna wahalar girka muku abinci, Ni kaga Zubamin guda uku".
Dariya mujahedeen dake k'ok'arin zama yayi shida Sultan, Sultan yace, "to ya khaleel kaimafa kana cikinmu, tunda gakanan a tebirin gandu".
Guntun murmushi yayi yana kur6ar tea, idonsa akan Aysha dake zaune kusada Anty Mamie tana 6ata fuska, Anty Mamie nabata abinci abaki, da'alama tsareta akayi kawai.
Ya kauda idonsa yamaida kan Sultan, " aini kasan lalurace yaro, dan matana batada lfyne kawai, amma soon bazaku ganniba anan".
Dariya sukayi gaba d'aya, wadda tak'ular da innah jummai, azatonta da'ita suke.
Dawowa tayi Inda suke tana zaginsu, babu Wanda yama kalli inda take acikinsu, bare tasamu amsa, saima cigaba da firarsu sukayi suna dariyarsu hankali kwance.
Sai kawai innah jummai tafashe da kuka, wai baffah da Ammah Nagani su Khaleel Kecin zarafinta, dama tasan Ammah Ba sonta takeyiba, kaza......kaza...haka taita surutai marasa d'ad'inji, babu Wanda yay koda tari barema ya tanka mata.
Har kowa ya kammala abinda yakeyi suka fito, motoci duk suka shishshiga, ganin haka itama innah jummai tabi ayari.๐Ÿคฃ๐Ÿ‘๐Ÿป


**********

Tafiyar mintoci kad'ance takawosu station d'in su khaleel, kowa yayi mamakin miyasa ya khaleel zai kawosu nan?.
Ganin ya khaleel ma'aikatan wajen sukayo caaaa akansa, sai k'amemasa sukeyi da Salutes nashi, suna tambayar ya jikinsa.
Su Aysha dai sai kallon ikon ALLAH sukeyi da girmamawar da khaleel kesamu daga ma'aikata nak'asa dashi, kuma sunsan wannan yana cikin adalcinsa da sassauci.
Su Kansu sai gaidasu akeyi cikeda girmamawa, kuma abin birgewa musulmai da wad'anda ba musulmanba kowa girmamasu yakeyi.
Ana cikin haka saiga Adams, saida yafara k'amewa da salute Na ogansa sanann Yakoma kan surukansa, ya gaishesu cikeda girmamawa.
Suma cikin fara'a suka amsa masa, da tambayarsa yadawo aiki?.
Yace eh.

Su Joseph ma duksun k'arasu, sun gaida su baffa sannan suka maida hankalinsu wajen khaleel dake magana.

Adams akaisu hall d'incan su zauna, ina zuwa, youseef ina buk'atar ganawa da momy".
Yay maganar cikin d'acin murya.
"OK sir".
Youseef yafad'a a girmamame.

Tafiya yake cikin karkashi da sassarfa, zuciyarsa Na harbawa da sauri da sauri, fuskarnan tamkar baita6a sanin miyema dariyaba.
Youseef yabud'e d'akinda hajia babbah take.
Kallo d'aya khaleel yamata ya kauda kansa saboda tashin hankali, dukta fita hayyacinta saboda k'aniyarsu da'akeci.
Daka ganta kasan atsorace take, duk gadararnan da tink'aho yagudu, aii bakin rijiya bawajen wasan makaho baneba, amma kunsan mutuniyar takufa, ganin khaleel saita d'auka yazo fiddatane, danhaka saiwata sabuwar d'agawa ta iso zuciyarta, tawatsa masa muguwar harara maicikeda tsana da bak'inciki.
Kauda kansa yayi yana k'ara tamke fusaka, yajuya yafita ahankaki, da yatsu biyu yayima taheer wata alama.
Kai kawai taheer ya jinjina masa, danya gane miyake nufi.
Tafiyarsa yacigaba dayi ahasale.

Su taheer d'aukar hajia babba sukayi aka fito da ita, saitaji kanta yak'ara fad'i da girma, aidama tasan dolene khaleel yazo ya fiddata, kobayaso tasan sai baffah yasakashi dole.
Wani k'aton d'aki aka kaita, suna ajiyeta suka fito.

................wata bajinta da k'arfin zuciyane ke k'arfafashi, sune suka taimaka wajen maidashi Ibraheem Abdallah d'insa jarumi, wanda baya d'aukar raini, cikin bajinta da jarumta jininsa ke zagayawa adukkan sassan jikinta, babu abinda fuskarsa ke nunawa sai fusata da harzuk'ar fushi.
Tunda yashigo d'akin momy kebinsa da kallo, bata ta6a ganinsa awannan yanayinba sai yau, lallale dolene kowa yadinga fad'in yana tsoron Ibraheem, ita kanta zuciyarta sai bugawa takeyi da k'arfi.
Da k'afa ya shuri kujerar dake kwance ak'asa yamaidata zaune dai-dai, cikin k'asaita irinta gadarar jarumta yazauna tareda crossing k'afarsa d'aya kan d'aya.
Momy takalli kanta ak'asa zaune, wani d'acine ya ziyarci zuciyarta, wai itace a k'asa Ibraheem Na zaune asama cikin sarautar gadara.
Zatayi magana ya dakatar da ita.
"Kinutsu, anan bada d'anki kike tareba, da Ibraheem Abdallah (j) kike tare, shikuma baya d'aukar raini awajen aikinsa, so ki kiyaye".
Cikin kwalo idanu waje momy tace, iyee, lallai Ibraheem, wuyanka ya Isa yanka, ka kalli tsabar idona kafad'amin haka?.
Kauda kansa yayi gefe, yace, " hajia laurah, ina fad'a miki kinutsu!!!!!!".
Yay maganar amatuk'ar tsawace.
Arajane hajia babba tad'anja bawa, baki bud'e idanu waje๐Ÿ˜จ.
Saikuma taja tsaki tana watsa masa harara, "kai Ibraheem kashiga hankalinka, wlhy zan sa6a maka kammanni".
" ban hanaki hakanba kuwa, domin har yanzu kinada kimar amsa sunan uwa a idona"....
"Mtsoowww aikin banza, ina amsa sunan uwar takane kakecin zarafina ayanzu?, nagodema ALLAH daban 6ata lokacina wajen rainonkaba, wlhy Ibraheem danasan haka zaka zamema rayuwata, datun randa kazo duniya zan shak'eka kamutu, dabakazo gabana kanamin gadara da d'agawaba kuwa?.
Murmushi khaleel yayi mai ciwo, ya furzo huci mai zafi daga bakinsa, k'ok'arin maida kwallan data cika idonsa yayi, sannan yajuyo yana kallon hajia babba da razanannun idanunsa masu matuk'ar kwarjini da kad'a hantar mara gaskiya.
Aiko hajia babba ta razana ainun, dole tajanye idanunta daga kallonsa.
Cikin kakkausar murya yace, " hajia Laurah! Tabbas da ace kasheni kikayi alokacin sainafi jin dad'in hakan, dace kin kasheni alokacin dabanyi rayuwa da wannan zilwa jahainin fuskar takiba, daban rayu cikin gur6atacciyar tarbiyar azzaluma irinkiba, wlhy hajia laurah, saikin gwammace kasheni kikayi akan barina araye dakikayi, ninan Ibraheem Abdallah, saina sakaki yin nadama keda ire-irenki....
Da k'arfi ya tafa hannayensa.
Saiga Adams yashigo, da ido yamasa magana.
Adams ya jinjina kai yana komawa da baya.
Babu dad'ewa saigashi yadawo shidasu baffa, yajawo table dakecan gefe ya maido gaban khaleel, jakkar hannunsa ya ajiye, yashigo warwareta akan table d'in.
Bindugune dawasu wuk'ak'e aciki.
Su baffah sunyi cirko-cirki suna kallon ikon ALLAH, da tunanin mi khaleel zaiyi dawad'annan makaman.
Shikam har yanzu yana zaune cikin k'asaitarsa, sai hura hanci yakeyi cikin zafin rai.
Bayan Adams yagama khaleel ya kallesa, akausashe yace, "ina buk'atar khaltum anan wajen."
"OK sir!, angama".

Bindiga khaleel ya d'auka, yad'auki bullet hud'u yazuba acikinta.
d'akin yayi tsit, kowa fargabace ta kamashi, kardai khaleel yakashe hajia babba, su Anty zuwairah duk sunyi k'asa da Kansu suna kukan zuci, kokad'an basuga laifinsaba, sunsan akan dai-dai yake, tunda akan aikinsa yake, summafi jin zafin momy da laifin data aikata, Su Hasnah ma sun kasa kallo, duk cusa Kansu sukayi acinyoyinsu suna kuka ahankali.
Zuciyar inna jummai tashiga tsitstsinkewa dan tsoro.
Ana haka saiga Adams yataso k'eyar hajia khaltum, ita harma tafi hajia babba jigata, duk raunukane ajikinta, sai layi takeyi ahanya tamkar mashayiyar giya.
Rakwam tazube gaban khaleel kusada Aminiyarta.
Khan khaleel na a d'uk'e.
Kusan mintuna 3 sannan yad'ago idanunsa dasukayi jajur saboda 6acin rai, yazubasu akan hajia babba.....
Nunata yayi da bindigar ya d'ana kunamar, cikin kauda kai yace, " zan kiraki da momy akaro Na k'arshe, momy miyasakaki aikata dukkan wad'annan abubuwan?. wlhy inhar baki warware wannan k'ullinba saina tarwatsa kanki da wannan bindigar, bawasa nakeba, bakuma burga nakemikiba ko tsoratarwa, abinda ke raina nake fad'a.............โœ๐Ÿป




_please kuyi manage da wannan, yau ina busy sosai wlhy._


*_Typing๐Ÿ“ฒ_*


๐Ÿคฐ๐Ÿป
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{๐Ÿ”ชwuk'a bata hudashi๐Ÿ—ก}_


*_Bilyn Abdul ce๐Ÿค™๐Ÿป_*


*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of expert & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu๐Ÿ“˜)_


*_Gaisuwarku ta dabance sister, ALLAH yak'ara haske a rubutunku kuma, yasaka albarka arayuwar 'ya'yanmu baki d'aya, ngd da bibiyar buk d'innan dakukeyi, ALLAH yabar

Please Login or Register in order to submit comment