Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jinki, akwai matsalane?".
Kanta ta girgiza masa tana shagwa6e fuska.
Ya tattaro dukkan hankalimsa akanta, fuskardai babu walwala, wannan yasaka Aysha jin Shankar masa tambayar dake ranta, dantasan halin kayanta sarai.
Ganin tayi shiru saiya d'alli la66anta da d'anyatsa, baki taturo masa, ashagwa6e kuma ido cikeda kwallah tace, "kai ya khaleel, ALLAH mugunta babu k'yaudai".
"uyimmm hakanefa, bara Na daina miki karfa nima ama d'iyata wataran".
Kunya takama Aysha data tuna lokacin data fad'a masa maganar, hannu tasaka ta rufe fuskarta.
Bakinsa yad'an ta6e yana guntun murmushi.
Har yanzu idonta arufe yake, tace, " inban takurakaba, kafad'amin miyasa kayita bibiyata har k'asar Islands?".

'Dan murmusawa yayi, Dan dama tun d'azun yalura da abinda takeson tambayarsa kenan, danyaga kallon tuhuma datake jifansa dashi tun suna asibiti, ya lumshe idanunsa yanamai tariyo komai tamkar yanzun yake faruwa.
Itakuma ta tsuramasa idanu tana sauraren amsarsa.
Kusan mintuna 5 sannan yabud'e idon akanta, cikin murya k'asa-k'asa kamar mai gudun kar wani yajisu yace, "miyyasa kikeson ji? Miyasa kikeson tunomin abinda yawuce?, tuna abinda kike buk'ata tamkar tuno wasu muhimman abubuwan da zuciyarsa ke buk'atar mancewane, baki labarinnan tamkar ruguza tubalin hak'uri da juriya dana fara tanadama rayuwatane, fad'a miki tamkar sake dawo da abubuwa masu cimin zuciya da cizonsune, please & please my Noorulhayat d'ina, karkice saikinji, karkice saina fad'a, karki tono komai, barni Na manta, kid'auka Na manta komai, kid'auka nid'in sabon mutumne, Wanda yafara rayuwa daga shekaranjiya waccan zuwa yau, kimanta komai A'eesha, kimanta please, kimanta kamar yanda Na d'auka Na manta Nima............
Da sauri Aysha ta rungumeshi tareda sakin kuka, ''kayi hak'uri ya khaleel, ka gafarceni, bannemi kafad'a d'inba danna tada maka da ahankali, inason jine akwai, kaikanka Idan kafad'a zuciyarka zata rage nauyi, zakaji sassaucin abubuwan da suka maka dabaibayi azuciya, barin abubuwan arai sukan assasa bak'inciki da damuwa mai tsanani, sukan gusar da dukkan farinciki ko walwalawar mutum, sukan ruguza dukkan wani security mai kare lafiyar garkuwar d'an Adam, kafad'a koyayane ya khaleel, kafad'a please, karkacemin a'a, kafad'amin koda sau d'ayane domin fiddani daga rud'ani, kafad'amin kodan nayi farinciki, kafad'a kodan naji araina banyi nadamar aurenkaba, Dan ALLAH ya Ibraheem.
Tsam suka rungume juna, zukatansu suna k'una, sunkai tsawon lokacin ahaka, saman khaleel yad'ago Aysha daga jikinsa.
Amamkinta saitaga yana murmushi.
Kallonsa takeyi cikin mamaki.
Yad'age mata gira sama, muryarsa a sanyaye yace, "kinsan mizaisa Na iya fad'a miki?".
Kanta ta girgiza masa.
Ya kauda kansa yana furzar da huci abakinsa, dawo da kallonsa yayi kanta, yad'auki hannun damarta yahad'a da nasa yad'ora saman cikinta, " zanfad'ane kodan yarinyata ko yarona, zanfad'a domin idan sunzo duniya kibasu labarin wahalar da mahaifinsu yasha akan soyayyar mamansu, zanfad'a kodan suji cewa mamansu taciri tuta, kuma itad'in lucky ce wajen janye zuciyar mahaifinsu a KALLON FARKO, wlhy ked'in kinzamemin maganad'isu, zanfad'a koda kowa bazai yardaba, harke kanki matata. Domin kin tankwara zuciyar Ibrahim alokacin danakejin babu wata mace datakai isar hakan, kin ruguza dukkan kurina da cika baki alokacin dani kaina nakejina on top, kece kika canja komai A'eesha, kece kika sauya Ibrahim khaleel alokacinda nakejin babu wata mace datakai isa ko k'arfin ikon hakan, alokacin danake d'aukar soyyaya shirme, wasan yara, rashin aikinyi, da k'arancin k'arfin zuciya."
Dolene yau d'inan kiji tushen soyayyar Ibrahim Abdallah *(J!)* akanki 'yammatana😉👍🏻...................✍🏻




*_Ayya jiya kunjini shiru, murace tamin kamun kazar kuku👩🏻‍🍳, da k'yar aka tsamoni a tukunya😂_*.


Kumuje zuwa my guys😉🤪👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻.



Bilyn Abdul ce🤙🏻👯‍♀.










*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu baki d'aya._*😭😭😭😭🤲🏻🤲🏻.


*_Typing📲_*


🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_


*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*


*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu📘)_

*_kuna cikin zuciyar bilyn Abdul kuma, kuna dabbane wlhy my fans_*

@⁨Maryam Muhammad⁩, @⁨Safiyya Danmusa⁩, @⁨Khadyinde.⁩ @⁨Fulani, Shamcydurling🥛🥛🥛,⁩ @⁨きαmiια チiκα💖⁩,@⁨Jamila zozo🧕🏼,⁩ @⁨Fadeelah Goje⁩, @⁨LAILA⁩ @, @⁨Mom Abdulmalik⁩ @⁨MOM MEENAL💃🏼⁩ @⁨Maimuna Ado⁩, @⁨Momyn Afnaan 😊⁩ @⁨Dallua⁩ @⁨Fadila DM⁩ @⁨Zainab Mshinkafi⁩ @⁨🎀ummu~ maryam🎀⁩, @⁨+234 703 972 6966⁩ @maijidda abbas. @SADDIQA BAFFA. Fatima saleh, khairat, karima, princes rasmah, habiba dakare,asiya saidu, marcy, 1, Sukhailah Hassan Umar or Ummu Sadeeq 2, Maryam Adam Abdullahi 3,Souraya,Nana yakaku, Mum shureym, 76uwaniy, Ummu iman, Mrs usman, Mahdauwalu, Anty saa, Ummu suhylerh, Munauwara bature, Zainab Gadaka, Mom Amar, Marry beauty, Maman khalil,, Mummyn ihsan, Itz sury d one, Safiyya Aminu, Maryam G wada Garba, Baby mommy, Rabiyat, Teemah, MamanHumaira, Hadizan baba, Babybluv, Saadatu Ibrahim, Rukayya bala kamilu, Beeky, Buy your chebe powder, Bilkisu isah, Maryam sulaiman, Ayshatu UST, Maman waleeda, Aisha, Khadijat umar said, Fauziyya sidi, Wisdom is a gift , Inna sokoto, Hafsat Ahmad Muhammad, Akori kishiya aci Daula, Mrs fawwaz, Mmn xee, Maryam yahya umar, Maryam Hassan, Hasana Ibrahim, Maimuna baba, Fatima ZANGINA, Mum rukky, SARATU SABO, Innan noor, Sadiya TELA, Maman faty, Dija dankakalo, Aisha yero, Sarauniya Fatima, Maman humaira, Ummu ameera, Umcycool , Umhana kabeer, Maryam Abdul aziz, Fazla ardo, Ummu salsabil, Jiddatul khairr, Rabi at nasir83, Ruquyya saleh, Ami, Nice one, Maman fati, Maman muhammad.

_Alkairin ALLAH ya iso gareku cikin salama ababen alfaharina._
❤❤❤💋💋💋👍🏻👍🏻👍🏻


4⃣3⃣

Idon Aysha k'yam akan ya khaleel, yayinda shikuma ya lumshe nasa, bayansa ya maida ya jingina da kujerar, tamkar mai karanta labarin novel ko maibada labarin wani film dayake shauk'i.
Hannunsa d'aya nakan cikin Aysha, d'ayan kuma yana shafa sumar kanta ahankali.😉👍🏻

"Hummm karon farko da Ibraheem khaleel yaji fad'uwar gaba yayin kallon mace, wadda bama takai macenba. aranar dana dawo daga k'asar Tanzania bayan aikin kwanaki 70 danayi a can, kaitsaye nabama su Adams damar wucewa dani gida, saboda matuk'ar gajiya da kasalar jiki dake tartare dani. Ina cikin shauk'in son ganin mo... Momy aranar, saboda sayo mata wata sark'a data dad'e tana so, amma bata samu sayaba, nikuma cikin ikon ALLAH saina samu wannan sark'ar zinari acan, wannan ne dalilina Na d'okin ganinta."
"Sabon labari a shafukan tarihina, koda Na sakko amota sainaci karo da tauraruwa mai wutsiyar alkairi........
Da sauri Aysha tabud'e idonta, shima yabud'e, suka kalli juna, cikin turo baki Aysha tace, " nice tauraruwa mai wutsiyar?."
Guntun dariya yayi, yaduk'o ahankali ya sumbaci goshinta, "a'a fa, bakiji minaceba? Tauraruwa mai wutsiyar alkairi".
Baki Aysha tamurgud'a tana kauda idonta daga kansa, shima kauda kan yayi yana murmushi.
Yacigaba da fad'in, ''akanki idona ya sauka kaff yawan jama'ar dake harabar gidan, bak'aramin fad'uwa gabana yayiba lokacin dakika d'ago manyan idanunnan naki kema kina kallona kuna magana keda d'iyar iya hama, bansan yazan misalta miki halin dana shigaba alokacin saboda rud'ani, (small girl like you kina Neman sakani Na rasa tunanina) bak'aramar jarumta nayiba wajen tattare dukkan hankalina namaida kansu Ammah, gaisawa nakeyi dasu ammafa dukkan hankalina nakanki, burina kawai nasake kallonki, amma hakan batafaruba.
Bamma sake ganinkiba saida Mamie takawoku domin yimin gyaran d'akina.
Hummm bazaki ganeba A'eesha, wlhy lokacin dana bud'e k'ofa wa Anty mamaie naganki zuciyata bugawa tayi tamkar zata fito, saida Na had'a da addu'a gudun kar Anty Mamie ta fahimceni.
Inakan Sani nasakaki wankin toilet alokacin, sannan kina shiga natura bishirah kar6omin tea badan inason shaba, saidan kawai nagankine atsanake.
Zaman jiranki nazaunayi har kika gama kika fito, lokacin dakika fito kintadda ina latsa waya ko? Bakomai nakeyiba face video d'inki, duk abinda kikeyi inata kallonki ta wayane, harnabaki umarnin cigaba da aikin, da lokacin da kika d'auki bedsheet zaki shimfid'a Na hanaki........
......."kadai dakamin tsawa".
Aysha tayi maganar tana cije la66anta.
Murmushi yayi, kawai yana cigaba da zagaya hannunsa akan cikinta.

Daban Daka miki tsawarnanba da tabbas babu makawa saikin harbor jirgina alokacin. natsuwarki itace Abu nabiyu daya kuma zuzuta wutar sonki araina, inason mace mai yawan nutsuwa, gakidai k'arama alokacin amma komai naki mai ajine.
Bank'i nakasance dakeba tun alokacin, saidai k'ank'antarki tamin katanga dahakan, kuma kodama kinkai girman dazan iya aurenki alokacin to tabbas, tarbarki nace inasonki shine babbar matsalata, Dan maganar gaskiya bazan iyabama.

Aysha tace, "sabodami?".

" saboda banason raini". 'Yay maganar yana jan hancinta".

K'aramar dariya Aysha tayi tareda salute nashi, cikin salon kissa tace, "agaida boss".
Dungure kanta yayi yana mata hararar wasa, shima yace, " agaida 6arauniyar zuciya".
Atare suka tuntsure da dariya, saida sukayi mai isarsu sannan khaleel yacigaba da fad'in.
"Kinsan wani Abu?".
" a'a saika fad'a".

Bak'aramin kamu kikaiminba A'eesha, abubuwa dayawan gaske sunfaru alokacin, Wanda tariyosu ayanzu 6ata lokacine, amma nasan kema kin sansu, bantsinci kaina adamuwaba sai lokacin dana daina ganinki gaba d'aya. narasa wanda zan tambaya agidannan yabani amsata, kwatsam ranar inacin abinci dainaji musleem Na tambayar Maman yara ina kike?.
Sosai maganar tasu taja hankalina, ni saima ranar nasan Maman yara takawoki gidan.
Yanda Maman yara take amsama musleem maganganunsa sainaji ban yarda da itaba, domin ni mutumne da inhar zakayi maganar dabata dace da tuharkaba saina ganeka, tawannan hanyar nakanyi saurin cafke mutum mai laifi.
Daga wannan ranar nafara bibiyar Maman yara batareda tasaniba.
Abinda nafara cin karo dashi akan Maman yara shine mu'amulla da momy a6oye, dakuma mu'amullah da Ummi amarya a6oye, bankawo komaiba sai munafunci irinna 'yan aiki akan masu gida, wannan ne yasakani rashin maida hankalina akan wannan matsalar, burina kawai nasan inda kike, dukda dai Maman yara tace kinje karatu.
Acikin bibiyartane nagane cewa zaku bar Nigeria, kuma tabbas ta Abuja zaku tashi.
Nayi amfani da wani abokina dake aiki a nan airport, kullum yana cikin sakamin ido akanki, har yagano ranar dazaku bar k'asar, alokacin bana nan, nima nayi tafiya.
Yaturamin dukkan bayanai akan tafiyar taku, harda biye-biye wasu k'asashe Wanda bansan miye dalilin hakanba, inda ace aranar dazaku tafi INA nan, nagakuma Kubrah, to tabbas dolene nazargi wani Abu, kuma dolene nafara binciken kubrah, amma sai'aka samu akasin hakan, bana k'asar, kuma bayanai akanki kawai Na nema banda Wanda zakuyi tafiyar tare.
Tunda nasan k'asar da aka kaiki nasaka Naufal fara bibiyarki, yana kawomin bayanai sosai akanki, amma baita6a sanarmin akwai wani sirri a tafiyar takiba.
Naje Na dubaki a islands batareda kin saniba, sannan bayan kin kammala karatu alokacin narasa mizan baki amatsayin taya murna, koshi Naufal baisan komai gameda keba, kawaidai ina fad'a masa k'anwatace ke.
Naje Spain alokacin nida Adams da Joseph, saimuka shiga wani shago domin munabin wani alokacin, babu abinda ake siyarwa a shagon sai irin furanni da kayan masoya d'innan, jinai kawai shauk'i yakamani, da tunanin nesa tazo kusa agareni, awannan shagon nasayi wannan ruwan mai d'aukeda k'ananun kifaye aciki, tareda flower, itakam wak'an dana rubuta ajikin takardarnan awajen Adams najita yanaji, kawai sainaji baitin yayi daidai da shauk'ina, shine narubuta nasaka a sak'on, nabada aka kaima Naufal domin yabaki.

Nashiga rud'ani alokacin da baffah yatakura min akan maganar aure shida Ammah, saidai momy bata ta6a nunamin tadamuba, wannan ne yasakani samun k'arfin guywa, naje nasaka Dr Abraham yarubutamin takardar bogi ta rashin lafiya nabama baffah, Alhmdllh daganan nasamu baffah ya dainamin maganar aure, akayi bikin su Sultan.
Kinsan wani Abu kuwa? Tun ranar dana fara ganin mama a Jigawa gabana yayta fad'uwa, dominkuwa zallar kamanninki nake gani a tattare da ita, ban gaskataba saida nabud'e wayata nakalli picture naki nakalleta, tun a sannan zuciyata tafara rawa alokacin, naso kauda lamarin azuciyata domin Na d'aukeshi amatsayin maganar nan ta bahaushe *kama da wane bata wane* amma saina kasa.
Har muka dawo gida tunanin kamanninki da mama sunkasa 6acemin, daga time d'inne nafara bibiyar mama.
Da sauri Aysha tatashi zaune tana zaro ido waje😱, "sabodami kuma?".
Maidota yayi ya kwantar, cikin basarwa yace, " saboda inaji ajikina akwai alak'a mai k'arfi tsakaninki da mama, Dan kamanninki yawuce haka kawai, dolene akwai Na jini.
Tsaf nasamu labari akan mama A to Z, nata kullawa da kwancewa alokacin, ga aikina kuma a gefe yad'auki zafi.
Mafita d'ayace tadace dani alokacin shine maida auren mama da baffah, bak'aramar wahala naciba A'eesha naganin Na maida aurenan, Dan baffah ya amince dana kawo masa shawarar, amma mama dana had'a hannu da kawu bilyamin k'in amincewa tayi Sam, Alhmdllh ummi amaryama taita nata kai kawo akan mama, harta San yanda tayi takai bayanin komen mama ga hajia khaltum, itakuma tazo tasanar momy, momy kuma sukaje kano, wannan shine yazama sila Na komowar mama.
Alokacin kuma nafara sanin tabbas akwai alak'ar sanayya tsakanin mama da ummi amarya, dukda basa nuna hakan ga kowa, nima kuma nayi-nayi nasan wani sirri akansu amma nakasa wlhy Aysha, dominsu Na yarda matane masu kaifin basira da k'yak'yk'yawan tunani, sun iya takunsu, sunkuma iya tafidashi yanda komai wanene wajan bin kwankwanto dolene kabarsu.
Abu d'aya nafahimta atattare dasu, shine aiki sukeyi akan wani agidannan, saidai kuma wanene?.
Wannan shine abin tambayar A'eesha.
Harkika koma Canada da zama bansamu bakin zarenba.
A Canada ma nata bibiyarki batareda kin saniba, sai lokacin damukayi karo dake, nakumayi hakanne da gayya, Dan ina buk'atar kusantuwa dake, kozan samu sassauci akan k'aunarki daketa azabtar da zuciyata, komai nakeyi saida tunaninki, duk mitsina wlhy A'eesha saikin fad'omin arai, har mamakin wannan soyayya nakeyi, nasan dazan bama wani labarin sonda nake miki wlhy saiya k'aryatani, nikaina daba Dan akaina tafaruba saina k'aryata akwai irin wannan soyayyar.
Randa mukai karonnan badan nakai zuciyata nesaba da rungumeki zanyi, amma haka Na daure, alokacin kuma Na fahimci lallai A'eesha na ta girma, tunda har idonta yayi tsaurin yimin murgud'e😊.
Lallai kinbani k'yak'yk'awan sak'o alokacin Wanda yazamemin abin tunani dayawan murmushi, bakomai baneba illah murmud'ennan.

Cikin waro ido Aysha tace, "kai ya khaleel, amma shine alokacin hardamin mugunta?, harfa nakoma gida bakina baibar zafiba wlhy".
Dariya yayi sosai tareda kuma k'ank'ameta, acikin kunnenta yace, " duk cikin sone burin zuciyata, hasken rayuwata."
Shiyyasa muna rabuwa alokacin nabada tukuyci wa Naufal yabaki.
Idan zaki tuna sak'on farko kifayene kawai k'anan acikin ruwan, sai flower, nabiyu kam tsuntsaye da rings guda biyu had'e da juna, saikuma wani ring d'in daban Na diamond💍.
Sannan turare.
Alokacin yakamatama ki gane nine saboda wannan turaren, Dan shine k'amshin turarena dakika faraji ajikina ranar Dana dawo, lokacinda Anty Mamie takaiku Ku gyaramin d'aki.

Zaune Aysha tatashi, "tabd'i Jan, ammafa ya khaleel kasameni wlhy, ingaya makafa, nata tunani dason tuno inda nasan k'amshin nan, amma wlhy nakasa, gashi nasan tabbas nasanshi, amma nakasa tunawa, dole Na hak'ura, wlhy kadad'e kana wahalar dani", 'tak'are maganar da jan hancinsa."

"To Amma, miye karubuta ajikin takardar nan? harna Gaza ganewa."
" Bazaki ganeba aii, Dan banyi yanda zaki gane d'inba".

*Æ*
*_ALLAH ahsni leelahk meeharbI ratam ahsee'A_*
_atayicuz aksah iam alitif ekay, asna'knij ad asramrafla nimod eknim akallam ay ALLAH._

_😘(j) halladbA meeharbI._


Wannan shine abinda narubuta aii ko?.
yay maganar yana nuna mata tafin hannunsa.

Da sauri Aysha tagyad'a kanta tana tashi zaune sosai.
Murmushi yayi, yace to kar6i pen d'innan, kifara kwafar rubutun daga k'arshe, ma'ana k'arshe yakoma farko, farko kuma yakoma k'arahe, kiga mizai bakai".

Kar6a Aysha tayi, tagyara zama sosai tayi copy d'in rubutun tafin hannun nasa.
Ido tazaro tana kallon abinda yabata kai tsaye, tajuyo cikin mamaki tana kallonsa.
Shima idonsa nakanta, ya kanne mata ido d'aya yana murmushi.
K'ara maimaita karanto rubutun tayi afili, tamkar mai bitar karatu agaban malaminta...........👇🏻

Æ
_A'eesha matar Ibraheem khaleel insha ALLAH._
_ALLAH ya mallaka minke domin alfarmarsa da jink'ansa, yake fitila mai haska zuciyata._

_Ibraheem Abdallah (j)😘_


Ayasha nagama karantawa saita fad'a jikin khaleel kawai tasaki kuka.
Bashida za6in daya wuce kar6arta, saiya k'ank'ameta shima yana murmushi, cikin lallashin buga bayanta ahankali yace, "sorry kinji sholyna, dolece tasakani 6oye miki kaina, Dan inhar nanunama duniya kece za6ina, to tabbas babu makwa sai an cutarmin dake, sai mak'iyana sunyi amfani dake wajen ruguza komaina, wannan ne dalilin dayasa na nuna bijirema aurenki alokacin da baffah yataramu.
Ashe hakan alkairine agareni, domin dana nuna inasonki, momyce zata fara salwantar dadukkan burina, dakanta zata tarwatsani alokacin, A'eesha na yarda da momy, amma taci amanata, matsayin uwa mahaifiya nabata, Ashe kuskuren hakane, nadad'e ina fuskantar wariyar launin fata daga gareta da innah jummai amma banta6a fasa bak'inba, nadad'e dakula momy tafison yaranta mata akaina, amma ban fassara zancenba.
Nadad'e ina mamakin k'aunar Anty Mamie da shauk'in son kasancewa da ita dake d'awainiya dani, amma ban ayyana komai arainaba, A'eesha miye dalilin momy na aikata hakan? Miyasa tarabani da mahaifiyata? Mina tare mata tadawo farautar rayuwata? Wane burine yakai momy shiga k'ungiyar ta'addaci Irin wannan? Bayan babu abinda tanema tarasa arayuwarta?.
A'eesha wanene zai fassaramin dukkan wannan k'ullin? Wanene zaibani amsar tambayoyina?, miyasa kika ringa aikata abinda zan zargeki ke kanki?".

Mik'ewa Aysha tayi tana murmushi, dukda batajin k'arfin jikinta haka tadake, kallon ido cikin ido sukayi itada khaleel dake binta da kallo.
Ta d'aure fuskarta tamau, cikin salon Aysha na jarumtar zuciya tace, "hajia laurah yakamata kama dukkan wannan tambayar? Tabbas amsoshinsu suna wajenta, itakad'aice mai amsoshinsu, bakai kad'aiba, kowama wannan yakesonji, minene dalilin faruwar KOMAI???????!!!!".

Nikuwa bakomai yasakani yimaka wasu abubuwanba sai gane cewar kasaka ana bibiyata, tasaki murmushin basarwa.
Ya khaleel nasan kaine kasaka Zeenat bibiyata agidannan dadukkan motsina, sannan kaine kasaka Afrah bibiyata awajen aiki, nasanka kai mutumne mai kwakwalwa da azabar bin kwakwkwafi Wanda kwazon aikine yad'oraka akan wannan nasarorin da kishin k'asarka da al'ummarka.
Amma tabbas tunaninka baita6a kaimaka cewar Aysha da ido d'aya take barci agidannan ba.
Ya khaleel nafara sonka aranda kafara sona, nata dakon soyayyarka kamar yanda kayita fama datawa, saidai ni tsoro da fargabar kafi k'arfina tahanani koda kwakwkwaran motsi na Isar maka da sak'o koda na sirrine Wanda kai kadinga min.
Ya khaleel tun ina k'aramata ni mutumce mai bak'incikin RASHIN GASKIYA, banason munafuki ko azzalimi, inason rayuwar mutum tsayayye mai ra'ayin kansa, maiyin Abu kaitsaye batareda son birge wasuba ko k'untata wasu.
Kaf halayennan saina samesu agareka, acikin d'an tsukun zaman danayi dakai aganin farko, dakuma abinda yayta faruwa agidannan narashin jituwar momy da Anty Mamie, tun alokacin nafahimci tabbas akwai 6oyayyan Al'amare tsakanin momy da Anty Mamie, Dan tafi nuna zafin kishinta akanta fiyeda ummi amarya.
Naso samin damar bincike amma sai aka datseni ta hanyar barin k'asar dani.
Tun randa nabar k'asarnan nad'auki aniyar tarwatsa hajia laura da hajia khaltum, daduk wani azzalumi dake kark'ashin mulkin masarautarsu, k'ank'antata baisa narasa kwarin guywan gaza Neman 'yancin mulkin mallaka da wasunmu ke samuba.

_ya khaleel mata suna cikin bak'incikin rayuwa a nahiyar Africa, wad'anda suka samu damar yin aure basu tsiraba, matar k'auye kullum tana cikin wahalar bautar mulkin mallaka na d'a namiji, abincin kirkima baigama isartaba, basuda aiki saina d'aukar ciki da haihuwa, gashi babu wani tallafin da yaran ke samu, sukan saka namiji makaranta, amma mace data tasa sai aimata aure, shekara d'aya saikaji ayuriyiri ta haihu, kafin wata shekarar tadawo ankuma samun wani cikin, shekaru uku kad'ai zakabata agidan mijin idan kakoma bazaka ganetaba, saboda tagama lalacewa tafita hayyacinta, babu abinci babu kwakwkwarar kulawa gamijin, daganan sai afara kiranta tsohuwa, itakanta zuciyata ta raunana, atunaninta shikenan tagama yayinta, saikuma 'ya'yanta, musamman idan yakasance 'yarta tafari macece, saikaji ana fad'in kwana nawane itama tazama surukar wani. Hummm._
_Dazaka duba, duk k'auyancin k'auye saika samu mai suyar kifi, mai tukubar nama, sannan tebirin mai shayi, kuma kowanne saiyayi sana'arsa arana kuma tak'are._
_shin abin tambayar anan, suwaye ke siye tulin bread da indomin tebirin mai shayi? Harda kwai. Sannan suwaye kecinye gasashshen naman tukubar mai nama?, sannan suwaye kecinye kifin tebirin mai kifi?._
Amsar d'ayace, mazan k'auyen.
_kullum da an idar da sallar isha'i saika gansu zagaye dawad'an nan tebiran, k'ilama harda k'arin mai soya doya da kwai da kaji agarin, amma kafin safiya duk ancinye, amma dazaka bincika babu matar mutum d'aya acikinsu dataci wad'annan kayayyakin, watama masarar tuwo ko dawa kad'ai aka bata, ita tayi wahalar k'ud'in nik'a dana daddawa dad'an barkono, koda babu manja da isashshen magi haka zata kad'a miyar suci itada yara su kwanta, mijin yadawo yana mazurai, bayan yagama kacaccala arayuwarta a tukubar mai kaji._
_da'an kwana biyu kuma yahango wata saikaji zancen zai k'ara aure, sukuma iyayen babu tunanin komai sud'auka su bashi waidon suhuta daganin wannan d'iyar tasu tana yawo agari ana zaginsu, kaico dawannan bahagon tunani._
_da tsautsayi zai gifta yasaki matar tasa, kwana biyu takoma gida saikaga tamurje takoma d'as yarinya d'anya sharaf da ita, da tsohon mijinta yaganta saiya rikice dafara hura hancin son komawa cikin masu takarar Neman aurenta._
" kasan miyasa hakan ke faruwa kuwa?".
Kamar sakarai khaleel ya jinjina mata kai alamar a'a.
Murmushi Aysha tayi, tacigaba da fad'in.
''Alokacin aii ya gama durk'usar da waccan amaryar daya aura yasaki wannan dominta, itama ya maidata tsohuwar k'arfi dayaji, kaga dole yakoma hange-hangen watakuma, koda ace waccan tsohuwar matar tasa bata koma garesaba, zai nemi auren wata kuma, dawad'annan abubuwan kullum aketa kashe rayuwar matan k'auye, da'an samu mai raunin zuciyata saita 6alle tazo takafa dabar 6arna da jagorancin tarwatsa rayuwar sauran 'yan uwanta dasuka tsinci rayuwarsu arin halinta.

_Macen binni kuwa zaka sameta daci dasha, da suttura, amma babu kwanciyar hankali, koyaushe

Please Login or Register in order to submit comment