Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

girmama ogansu.
Bai tsaya garesuba, horn kawai yayi d'an gwari yabud'e masa gate yashige da mashin d'in, suna su Taheer duk sai suka shiga.

Tunda su hajia babba suka sami nasarar baro hall d'in kaitsaye nan gida suka nufo afirgice, sunyi imani da cewar idan anan gidan suka fake khaleel bazai ta6a kawosu aransaba, tunda bai gansuba, amma hajia babba da idanunta taga khaleel.
Babu Wanda yasan sun shigo gidan, sai mutane kh'alilan, gaba d'ayansu arud'e suke, hajia babba kuka takeyi da idanunta, takasa zaune takasa tsaye, khaltum kam ba'a magana, dama kunsanta afagen tsoro, sai mutum biyu dasuka gudo tare, suma duk matane, d'ayama budurwace, d'ayar kam zata iya zama sa'ar khaleel.
Ko kafe mashin d'in baiyiba yasakeshi anan, sai cikinsu Taheer ne wani yagyara farking d'in mashin d'in.
Taheer ya nuna masa motar dasu hajia babba sukazo, khaleel baisan motarba, Dan bata gidan baceba, saikace mayunwacin zaki haka yanufi d'an gwari datun shigowar su khaleel yake arud'e, Dan yasan tabbas babu lfy yau agidannan, cikin daka tsawa khaleel ke tambayarsa waye yashigo da motarnan gidannan?!!.
Hargowar khaleel ce tafara jawo hankalin mutanenen gida, suka fara fitowa d'ai-d'ai.
Jikin d'an gwari rawa yakamayi, Dan yasan yau babu wargi ga khaleel, dama can bawasa yakeyi dawani acikinsuba, har taune harshe yakeyi wajen magana saboda tsoro, yace, "wasune, amma suna can ciki".
Shigewa khaleel yayi cikin babban falon gidan, Wanda zai iya sadaka dakowanne part Na masu gidan, hankalin kowa yatashi agidan, Dan sunsan yau khaleel amatsayin ma'aikaci yazo musu ba d'an gidaba.
Kowa yafito amma banda Momy, yagama binsu d'aya bayan d'aya da kallo, kad'anne daga cikinsu babu, kuma yarane, yace, " suwaye suka shigo gidannan awa 1:30 dasuka wuce?!!".
Yanda yay maganar dolene katsorata komin kusancinka dashi.
Hafiz ne yay namijin k'ok'arin fad'in driver yad'akko su Adeel daga school, sannan nima da ya muhseen yanzu muka shigo".
"Saiwa kuma!!?".
Umme Amarya tace, " nima bandad'e da shigiwaba, kusan tare kuma muka shigo da hajia babba".
Arikice ya kalli ummi amarya, "umme acikinku wanene mai farar mota?".
" hajia babba ce sukazo da ita, inaga motar bak'intace".
Wani irin huci mai azabar zafi khaleel yafesar, kansafa yafara juyawa, akid'ime yanufi part d'in Momy, dak'afa yadaki k'ofar, amma yajita a kulle, kuma dukanta yayi, nanma ko gezau.
Dukan k'ofarne ya farkar dasu Momy halin da ake ciki, hajia khaltum tace shikenan laura, dabararki bataciba, matsiyacin yaronnan yabiyomu.

Dukda baffah hankalinsa atashe yake, baihana dakatar da khaleel ba daga dukan k'ofar, 6angarensa Yakoma yad'akko wani key d'in yabashi, Khaleel yakar6a yabud'e k'ofar.
A tsaitsaye yatadda su Momy, yana shigowa Momy ta nunasa da bindiga, wlhy Ibraheem kana matsowa saina harbeka.
Mutuwar tsaye khaleel yayi, kallon Momy kawai yakeyi abirkice, kansa yafara juya masa, Dan harya fara ganinsu dishi-dishi, tafiya yarink'ayi da baya-baya yana hawaye, harya fito babban falo inda kowa yake atsaye, harsu Taheer.
Kowa zare idanu yayi danganin Momy nabin khaleel dake tafiya da baya-baya da bindiga.
Atsawace tace, "ka ajiye bindigar hannunka kona harbeka".
Sakin bindigar khaleel yayi yana hawaye, sannan yana nuna Momy da d'anyatsa d'aya, bakinsa yakasa furta komai, dukda d'unbin magana dake cikinsa.
Ammah tafara sallalami tana tafa hannaye, laure!! Dama ke 'Yar fashi da makamice? Yo inba d'an fashiba wake rik'e bindiga shiba ma'aikacib..........
Ammah batakai k'arshen maganarba sukaji k'arar harbi da ihun Ammah lokaci d'aya.
Momy ta harbeta ak'afa, tana fad'in "bara Na tabbatar miki hakan tsohuwar banza, aiduk kece sanadin komai".
Tsoro kama kowa yayi afalon, amma banda baffah, khaleel kam akid'ime yake, kwakwalwarsa tsaye take cak ta daina aiki, bashida maraba da gunkin tsakkiyar hanya.
Tabaya Aleeya ta daki k'afar Momy, saigata tazube ak'asa, bindigar tafad'i gefe, Auwal yay saurin d'auka.
Kallon mamaki kowa kema Aleeya, Dan basuyi zatoba, itako ko'a jikinta.
Ita kanta momyn baki bud'e take kallon Aleeya, dukda azabar zugi da k'arta keyi, cikin rawar baki tace, " Aleeya! Nikika daka? Ina matsayin wadda zaki auri d'anta".
Wani murmishin k'asaita Aleeya tasaki, tafara tafa hannaye tana zagaye momy.
"Hajia laurah, hajia laurah!, Aleeya bata shigo gidannan domin auren d'ankiba, nashigo gidannan domin yin aiki, aztonki kinsamo wadda zata taimaka miki wajen tarwatsa rayuwar Wanda kikeyin amfani dashi dason tara abin duniya, nasan bakisan darajar khaleel ba, tunda bakece kikayi wahalar rainon cikinsaba da nak'udarsa, shiyyasa kikaita yunk'urin kasheshi da wahalar da rayuwarsa........
Kowa afalon idonsa awaje yake, wasu tuni ruwansu yakai 180 saboda rud'ewar furicin Aleeya.....
Ammah dake zaune mama Na rik'e da ita, sai zufa takeyi saboda harbinta da Momy tayi ak'afa, cikin karfin hali tace, ''ke 'yarnan mikike son fad'ane haka?".
Murmishi Aleeya tayi tana kallon mama, hajia fad'ima lokaci yayi dazaki fasa kawai, lokaci yayi dakowa zaisan sirrin 6oye, lokaci yayi da khaleel zaisan mahaifiyarsa ta asali agidannan, lokaci yayi baffah zaisan komai, 6oye-6oye yak'are, dama burinmu bai wuce khaleel yakama Hajia laurah dumu-dumu da laifiba, to Alhmdllh, dakon shekaru 37 dakikayi kina rik'e wannan sirrin yakamata ayau ki fesar dashi kowa yasani, kodan khaleel yasan kansa shima, yakuma samu farin ciki irinna kowanne d'a aduniya.
Kowa afalon kallonsa yadawo kan mama, dake k'ok'arin kwantar da Ammah, "a'a fad'ima barni azaune, aini abinda kefaruwama yahanani jin zafin yanzun".

Kai jama'a, dakyarfa Ammah ke magana wlhy, amma bakinta yak'i mutuwa๐Ÿ˜‚.

Mik'ewa Mama tayi tana takawa ahankali cikin falon, gaban Anty Mamie taje tatsaya, ta had'e hannayenta waje d'aya alamar rok'o, Bilkeesu ki gafarceni, kikuma fahimceni, batajira amsartaba takoma gaban baffah, kaima kamin gafara Alhaji, kakuma fahimceni, banida za6i sainayin hakan, shima bata jira cewarsaba takoma inda khaleel yake uwa butun butumi, hannunsa takamo tarik'e, idonsa akanta, itama kallonsa takeyi, kayi hak'uri yarona, nayi hakane saboda nema maka kariya, idan bahakan nayiba nasan kasheka zasuyi, shiyyasa naza6i rik'e maganar araina har takawo yanzun, amma ban bartaba saida Na tabbatar kana zagaye daduk wani kulawata, had'eda kwakwkwaran bincike domin tabbatar da gaskiya yanda kowa zai fahimceni aranar dazan bankad'a komai".
Ya khaleel bai iya cemata komaiba, saidai kwayoyin razanannun idanunsa masu kamada Na jan gauta daya zuba mata, badamuba taja da baya gaban Momy da hajia khaltum da'aka gurfanar ak'asa, bayan Taheer duk yasaka musu handcuff ahannu.
Kukuma inason Ku maida tunaninku baya, shekaru 37 zuwa baya dasuka wuce".
Harara hajia khaltum tazubama mama, momy kam rok'on mama tafarayi, please fad'ima kibar zancennan, narok'eki, zan biyaki konawa kike buk'ata, bank'i kowanne sirrina yafitoba amma banda wannan sirrin......
Baki isaba laurah, bakida kud'in dazaki biyani, ko a baya ba tsoronkine yasakani shiruba, bakuma biyana kukayiba, nayi hakane saboda yak'inin Ibrahim zai kwato mana 'yancinmu agurinki wata rana, Dan nasan ubangiji bazai ta6a barin azzalumi nasaraba, nasan CIKI DA GASKIYA, wuk'a bata hudashi.


*_WANI LOKACI MAI NISAN ZANGO๐Ÿ˜ข_*

Bayan aurena da Alhaji Abdallah rashin zaman lafiyarmune nida laurah yasakashi auro Bilkisu, dukda kasancewar Bilkeesu k'arama acikinmu hakan bai canja komaiba, saima dad'a hargitsewa da komai yayi.
Cikina yazube har karo biyu dukmun d'auka tsautsayine, hankalina bai fara karkata akan hajia laurah ba sai lokacin dasuka haihu tareda Bilkeesu, ALLAH ya jarabcesu da nak'uda rana d'aya, amma laurah tariga Bilkisu.
Kuma tarigatama haihuwa, saidai k'in fad'a mana abinda laura ta haifa k'awarta khaltum tayi gatanan da ranta, har saida Bilkisu ta haihu.
Kafin afad'a mana abinda Bilkeesu ta haifa doctor yabuk'aci kayan haihuwa, da ruwa dawasu magunguna daza'a sakama Bilkeesu.
Ammah idan baki mantaba, kekad'ai muka bari, Alhaji yatafi d'aukar kaya damuka manto, nikuma natafi pharmacy d'in cikin asibitin, rabon inzo inga abinda ke faruwa Na yarda 'Yar takardar da doctor yabani, dawo nayi ina dubawa har k'ofar d'akin, ammah tarigada tajuyama d'akin baya shiyyasa bazata san mike faruwaba, naduk'a Na d'auki 'Yar takardar dana gani, d'ogowar dazanyi sainaga doctor shida wata nurse da khaltum sunfito da baby daga d'akin da Bilkisu ta haihu, suka shiga d'akin da laura take, da sauri Na afka d'akin, babu baby gaban Bilkeesu, itakuma tanata barcima, ina niyyar fita na fad'ama Ammah saiga nurse d'innan tadawo da da babyn ta kwantar gaban Bilkisu, jinayi hankalina bai kwantaba, amma nakasa cewa komai, gudun karyazam zargi nayi.
Fita nayi ina sak'e-sak'e harna Sayo maganin nadawo, natarar Alhaji yadawo, yana rungume da jaririya yana hawaye.
Tambayarsa nayi miya faru?, shine ya sashaidamin babyn Bilkisu batazo daraiba, hajia laurah kuma tahaifi namiji.
Tun anan nasan tabbas zargina gaskiyane, su laurah sun canja yaranne.
Amma bance komaiba har muka dawo gida, yaro yak'i shan nonon laurah, daga k'arshema da'aka matsa sai nononta yakoma fidda yellow ruwa maimakon milk, anyi-anyi kuma tak'i yarda Bilkisu ta shayar dashi, ga jariri nata azabar kuka.
Saida Ammah Tamata tatas sannan tayarda, Bilkisu sarkin hak'uri kuma tayarda zata shayar dashi, dukda rashin k'auna da laurah ke nuna mana, ana bashi nonon Bilkisu yakar6a kuwa.
Alokacinne naje hard'aki nama hajia laurah magana, nakuma fad'a mata subama Bilkisu d'anta kokuma Na fallasasu, ga laurah nan da ranta, itada khaltum sukaimin barazana da mutuwa, kuma sukace inhar maganar tafito wlhy saisun kashe jaririn da ita kanta Bilkisu, acewarta ita bata haifi namijiba wata shegiya acikinmu bazata haifaba.
Ba tsoron kurarinsu najiba, tausayin Bilkisu naji, dakuma kashe jariri dasukace zasuyi, danhaka nayi shiru inata addu'a daneman mafitar yanda zan ku6tar da jariri Ibraheem wanda yaci sunan mahaifin Bilkeesu, (yamata alk'awarin idan ta haihu namiji zai sakama yaron sunan mahaifinta), dakuma aka samu akasin haka tunda basusan miya faruba, sai yacanja zai saka sunan mahaifin laurah, ni naita rok'onsa da lallashi har ya amince yasaka sunan mahaifin Bilkeesu kamar yanda yay niyya, Na nuna masa hakan zai ragema Bilkisu rad'ad'in rashin tata jaririyar, bamuwani kai ruwa ranaba ya amince, aikam ansha rashin hankali aranar, tamkar za'a k'ona gidanan, Dan saida laurah ta hargitsa kowa, Alhaji kuma yaburgeni yace babu canji.

Ban fasa gayama ubangiji ba wajen Neman mafitar hanyar maidama Bilkisu d'anta, amma saiwata k'addara ta giftamin alokacin, nayi 6arin cikina, a sibiti kuma sukace magani nasha, dama shinake sha duk lokacin da cikina yazube, sun rufamin asirine kawai, kuma Alhaji yasamu maganin zuwabar daciki ad'akina, da wannan damar hajia laurah tace nice nayi yunk'urin zubda cikin Bilkisu abaya kuma, Alhaji Abdallah yanason yara, batareda binciken komaiba yasakeni alokacin.
Abu d'ayane yasakani bak'inciki da sakin nan shine sanin laurah ce ta k'ullamin, ga wulak'aci da Alhaji yamin lokacin saboda 6acin rai dayake ciki.
Natafi ina tausayin Bilkisu, dannasan zatasha wahala agidannan.
Tunda nakoma Kano aketamin barazana da rayuwa, kuma nasan laurah ce ta sanya, Dan akwai lokacin da'aka saceni, aka 6oyeni kusan wata 1, hankalin iyayena yatashi sosai, har aka sanya malamai addu'a sosai lokacin, ciki harda tsohon mijina Malam Abubakar.
Cikin ikon ALLAH nasamu ku6ta kuwa, munje yima Malam Abubakar godiya nida yayata ananne yaganni, yakumace yanaso.
Babu wani 6ata lokaci akasha biki, badan inasonsaba, amma kyawawan halayensa yasaka cikin kwanaki kad'an ya mantar dani Alhaji Abdallah, dukda har lokacin ban hak'uraba wajen son ku6tar da khaleel da mahaifiyarsa.

Mafita d'aya nasamu lokacin itace bintu, k'anwar mijina, dukda kowa yasan bintu jarababbiyace, nima tana nunamin halinta, sannan kuma tagogu da zaman bariki, ahankali naja bintu ajikina, wajen k'yautata mata, saida naga tasaki jiki sosai dani sannan nafad'a mata buk'atata nason zuwa tanemi aiki agidannan.
Babu musu ta amince, saboda itadama 'yarson hutuce, babu wanda yasan mike tsakanina da bintu saboda Na nuna mata karta wani nuna hakan, saboda aikin sirrine tsakanina da ita.
Bintu batadawo gidannanba saida aka haifi Amatullah, nikuma har sannan ban haihuba agidan Malam Abubakar.
Bintu tacigaba damin aiki, wajen kallon kowanne shigi da fici agidannan, batareda sanin kowaba, duk sun d'auketa amatsayin 'Yar raino.
Tafiya tayi tafiya bintu tazomin da labarin hajia laurah tashiga wata k'ungiya, kuma khaltum ce tasakata, itama la6ewa tayi taji hirarsu wata rana. Sannan k'ungiyar tanada had'ari, safarar yara mata sukeyi zuwa wasu k'asashen duniya, ana sakasu karuwanci.
Wannan labari yata6a zuciyata, nasan laurah zatayi abinda yafima haka, saboda tanada son kud'in tsiya.
Ancigaba da shurawa khaleel nata girma dawayo, lokacin yanada k'anne, Dan Bilkeesu ta haifi Rufa'i sultan mujahedeen, Amatullah, Ramadan, abinda yabani mamaki da laurah batayi yunk'urin kashe wad'annan yaranba, kokuma sacesu, wani tunanine yazomin, nafahimci laurah tabar khaleel ne danya zame mata wata Katanga nan gaba, tunda shine namiji babba.
Ganin hakan ne yasakani amfani datawa basirar domin yin wasa da hankalin laurah nima.

Bayan haihuwar Zunnurain da Mufeedah nasamo Saudah, k'awa ga k'anwata, Lokacin saudah tafara aiki, dan lauyace mai zaman kanta, narok'eta arzik'i akan ta auri Alhaji Abdallah, tunda dama tasanshi, yayanta abokinsane, , dafarko tak'i amincewa, saida Na zauna Na warware mata komai akan abinda ke faruwa, Na burin laurah dason tarwatsa gidan Alhaji Abdallah, dukda zai har sannan bansan kwakwkwaran dalilin laurah ba Na aikata hakan kaitsaye.
Jin haka Saudah ta amince, akasha biki kuwa, kundai gane wanake nufi (Ummie Amarya๐Ÿ˜‚)..............โœ๐Ÿฟโœ





Kaina yafara ciwo, amin afuwa muhad'u tomorrow insha ALLAH, danjin aikin mama, (Maman aysha๐Ÿ˜‰)
๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€



Ayya my sweet Dota Aneeluv ALLAH yabaki lafiya, fans kuma Aneesa A rimi addu'a batada lafiya wlhy sosai, kuhad'o da kayan dubiyafa๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹

*_Typing๐Ÿ“ฒ_*


๐Ÿคฐ๐Ÿป
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{๐Ÿ”ชwuk'a bata hudashi๐Ÿ—ก}_


*_Bilyn Abdul ce๐Ÿค™๐Ÿป_*


*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu๐Ÿ“˜)_

_gaisuwa agareku dafatan Alkairi, Ummu Ameer (comment naki Na k'ayatar dani) Maman Uswan (Ngd da k'yauna), fadeelah Ummu Amal (nagode kwarai da gaske da ziyarar daki kawomin hargida, ina alfahari dake), miss Maryam maintain (sak'onki ya iso gareni, thanks dear) mom of 12 (comment naki Na kasheni dear), Zarah maigari (keta dabance araina), Leemat (ngd sosai dear, ALLAH k'ara miki haske akan naki rubutun), Maman Aysha (ina k'aunarki sosai), fati tage (bilyn Abdul Na alfahari dake sosai wlhy) , Nana yakaku (comment naki nasakani Nishad'i da k'aunarki), Esha qadeer (ina k'aunarki wlhy), alkairin ALLAH yakaimuku aduk inda kuke, bilyn Abdul nayinku wlhy._
Kuna dayawa wlhy, amma insha ALLAH ahankali zakuga sunayenku๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹โคโคโคโคโคโคโค๐Ÿ’˜๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€.


4โƒฃ0โƒฃ

"Mama da saninki kenan aka kaini karuwanci?".

Gaba d'aya falon kowa juyowa yayi yana kallonta, Aysha ce tsaye abakin k'ofa, sai Khausar dake rik'e da ita, doctor Abraham kuma yana bayansu, kallo d'aya zaka mata tabaka tausayi, saboda rama datayi, sai uban haske da tsayi, idanu jajur saboda wahala.

Aleeya Ce tak'arasa garesu da sauri takama hannun Aysha, saman kujera takawota ta zaunar.
Doctor Abraham kuma yak'araso inda Ammah take, domin bata taimakon gaggawa.
Da k'yar tayarda aka mata allurar rage rad'ad'i, dantace babu mai mata allurar barci yahanata jin *Sabon al'amaree*, saida baffa dasu taheer sukaita lalla6ata sannan.
Ya khaleel kam nazaune tamkar wani hoto, shidai binsu kawai yakeyi da rinannun idanunsa, amma ko motsin kirki bayayi.
Dukda Aysha taji tundaga farkon labarin hakan baihanata tsare mama da kallon tuhumaba, tarasa yadda zata fassara abubuwan.

Ummi amarya tad'ora dafad'in........
............Hakane Aysha, dasaninmu kikaje islands UK, ammafa bada nufin turaki karuwanciba.
Bayan shigowata gidannan nacigaba dabin diddik'in hajia laura batareda sanintaba, saidai bangane komaiba saboda k'arfin rik'e sirrin k'ungiyarsu dasukeyi, babu wata kafa dasuka bari dawani zai samu shiga al'amuransu.
Nayi iyayina nagaji.
Saida Na zauna nayi dogon nazari sannan nagane yakamata ace munsami yarinyar dazataje anufin hajarsu, tawannan hanyarne kawai zamu ringa samun bayanan sirri.
Nasamu Yaya fad'ima da bintu dawannan batun.
Tashin farko bintu tace musamo yarinya daga k'auye.
Yaya fad'ima tace a'a, bazai yuwu mu tsare 'ya'yanmuba mu tozarta nawasu, inhar bazamu iya saka 'ya'yanmu awannan had'arinba, to babu d'an dazamu saka aciki, mudaije musake nazari.
Mun amince da maganarta kam.
Kafin muyi zama Na biyu Alhaji yasakani binsa Saudia yin Umrah, Dan lokacin inacikin hutun aiki Na k'arshen shrkarah.
A Wannan tafiyace ALLAH yahad'ani dawata matashiyar budurwa, masaukinta Na kusada namu, saiyazam kullum tare muke zuwa massalaci. Abinda nalura dashi ga wanan budurwa shine yawan kuka datakeyi dafad'in ALLAH ya canja mata rayuwarta, Dan ba'a son ranta takeyiba.
Banta6a tambayartaba, sai ana jibi zamukomo gida, nadai kasa hak'uri Na tambayeta, dafarko tayi kamar bazata fad'aminba, saida naita lallashinta sannan takwashe labarinta kaf tasanarmin.
Na tausayama yarinyar sosai, har hawaye nazubar mata, sannan kuma nayi farincikin jin tanada alak'a da k'ungiya mai tambarin๐Ÿฆ‚.
Bayan dawowarmu saudiya muka iske tashin hankalin rasuwar Rufa'i, lokacin kwana d'aya tak, rasuwarnan ta girgiza Yaya Bilkisu da khaleel ainun, hakama dukkan jama'ar gidanan.
Babu dad'ewa kuma sai mijin Yaya fad'ima ma yarasu.
Bayan lafawar wad'annan rasuwa mai ta6a zukata nasake dawoma Yaya fad'ima da zancen baya, harma da labarin matashiyar budurwa nan damuka had'u a saudia.
Lokacin kwanakin mijinta 5 kacal da rasuwa, gaisuwama naje mata.
Atake anan Yaya fad'ima tacemin muyi amfani da Aysha d'iyarta kawai.
Wannan magana bak'aramin razanani tayiba, nacema Yaya fad'ima hakan bazai yuwuba, yaza'ayi musaka rayuwar Aysha ahad'ari, tunda bamuda tabbas akan zata iya baro wajennan ba'a 6ata rayuwartaba.
Bud'ar bakin Yaya fad'ima saitace hakane, kuma tayarda da zancena, amma ita bazata saka rayuwar d'an kowa ahad'ariba, itakuma nata 'ya'yan a killace, ta sadaukar da Aysha danta ceto rayuwar yara masu d'unbin yawa daga gararin rayuwa, inhar rayuwar Aysha ta lalace awajennan tad'auki hakan amatsayin k'addara, amma tana rok'on ALLAH yama tsare mata ita, kodan darajar maraicinta dakuma sadaukarwa datayi amatsayinta Na uwa agareta.
Hummm Na jinjinama k'ok'rin Yaya fad'ima awannan lokacin, Dan masu irin zuciyarta k'alilanne aduniya, bakowane keda irin wannan k'yak'yk'yawar zuciyarba, kuma duk akan kishiya, wadda mutane dayawa suke d'auka amatsayin abin k'yama, (wlhy hakan datayi yakuma sakama zuciyata salama akan wani Abu waishi kishin banza, tabbas kishin taimakon juna shine kishi, ba kishin hauka Na wannan zamaninba), awannan lokacin naji araina ina addu'ar son dawowar Yaya fad'ima d'akinta Na asali.
Haka nadawo Abuja cikeda al'ajabin jarumtar mace irin Yaya fad'ima.

Kwanakina biyu da dawowa kacal saiga bintu d'ukeda Aysha kuwa.
Aysha bata sanniba, saboda duk sanda zanje gidansu saida nik'af nake zuwa, ko Ummah abokiyar zaman Yaya fad'ima bazata ta6a shaida fuskataba bare yaran gidan, bama koyaushe nake zuwa gidanba, saidai Yaya fad'ima tafito muhad'u awani waje.
Hummm wani al'amarin ubangiji hajia laurah naganin Aysha kuwa saita tanka, dama nasan dawuya hakan bata faruba, saboda Aysha tanada k'yau da tsarin halitta irinta mata, dukda alokacin yarinyace ita k'arama.
Wannan tankawa datayi kuwa bintu ta sallama mata bisa yanda muka tsara.
Hajia laurah suka d'auki mak'udan kud'i suka bama bintu, duk Na kar6ar Aysha.
Dukda yarinyar tana bani tausayi, amma haka muka kauda kai nida bintu aka tafi da ita, da taimakon wata mai dillacin yara muka samu akabama kubrah Aysha kamar yanda muka tsara, ita kuma waccan mai dillacin ba 'Yar k'ungiyar baceba, suna amfani da itane batareda tasaniba, saisu sakata samo yara daga k'auye amatsayin za'a sakasu aikatau, data basu shikenan sai'a rarrabasu k'asashen duniya batareda sanin iyayenauba da ita kanta wannan mata.
Alhmdllh Aysha taje islands UK, inda matashiyar budurwar nan take, kuma ana kaita ta ganeta, Dan nasanar mata komai akanta ta waya.
Hummm kuyi hak'uri, bakowa baceba budurwa nan face meerah!!...

Arazane Aysha tamik'e cikin dafe k'irji, tace, "Ummu amarya kina nufin Anty meerah ta?."

"Yes lil sholyna haka zancen yake".
Meerah tafad'a daga k'ofar part d'in Ummu amarya.
Kowa saida yajuya ya kalli meerah dake takowa cikin falon inda kowa yake.
" lil sholyna kiyi hak'uri, kuma kimin afuwa, banida za6in d'aya wuce hakan, saboda ceton d'inbin yara mata dake fuskantar mulkin mallaka irinnan k'ungiyar su hajia laurah, wadda akema lak'abi da saunan *('ya'yan kunama)*, tabbas sud'in 'ya'yan kunamane masu amsa sunan 'ya'yan sharri, Dan adalilinsu ALLAH kad'ai yasan yara nawa suka salwanta da matasanmu. Nadad'e ina neman hanyar ku6tar da 'yan uwana, amma babu mai taimakona, sai had'uwata da wanan baiwar ALLAH hajia saudah, itace ta k'arfafamin guywa da yak'inin zamu iya tarwatsa wanan k'ungiya da ire-irenta, amma saida k'arfin addu'a da taimakon juna.
Aysha shugowarki rayuwata itace mataki nabiyu danagane ubangijina ya amshi addu'ata danakeyi adare darana, akan ALLAH ya canjamin rayuwa, dukda sanadin kwad'ayin mahaufiyata Na tsinci kaina, tabbas kece kika canjani, dukda kasancewarki k'aramar yarinyar akaina.
Aysha nina shiga nafita nasamu aka sakaki makaranta, saboda ALLAH ya taimakeni john yanuna yana sonki, nasan kuma hakan daga ALLAH ne kawai, (maybi ALLAH yadubi sadaukarwar mahaifiyarkine, kokuma maraicinki, dakuma yawan ibadarki) yacusa soyayyarki a zuciyar john, harya kasa keta miki mutunci aranar daya fara ganinki, bayan kuma hakan baita6a faruwaba, Dan tunda nake banta6a ganin john yad'agama wata yarinyar da'aka kawo k'afaba komin k'ank'antarta kuwa, amma ke sai ubangiji yahanashi cutar dake.
Nasarar dana samu tasilar abokinsa kika shiga makaranta shine yazama matakin nasararmu tafarko akan k'ok'arin mahaifiyarki da kuma hajia saudah.


Please Login or Register in order to submit comment