Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

khaleel ba, har Ammah, Dan sunsan idan yana cikin irin wannan Fushin komaima zai iya faruwa, sannan komin kusancinka dashi bazai d'aga maka k'afaba, kuskure k'ad'an wani zaimasa yaci dukan banza.
Babu Wanda ya isheshi kallo acikinsu yaja zugarsa suka wuce 6angarensa.
Afili Ammah tace, " lallai gidannan gab yake da kamawa da wuta, tabbas inaji ajikina akwai gagarumin Abu dazai faru".
Kowa kallonsa ya maida kanta, amma batasake furta komaiba, kujera tanema ta zauna.
Suma duk sai suka nemi wajen zaman.

Su khaleel suna shiga yace, bincike mai k'yau nakeso, Dan tabbas akwai abinda bamu saniba, ajiya A'eesha bataci wani abuba agidannan, kowa ya shaida haka, amma dai ina zuwa.
Waya yaciro yakira Ammah, babu dad'ewa saigata tazo.
Suna zazzaune, itama saita nemi waje ta zauna. khaleel yace, "Ammah kamar yanda bincike ya nuna a 6angarenki Aysha take kwana, kuma kinfi kowa Sanin dukkan wani motsi akanta, shin jiya ko taci wani abinci kafin meatpia?".
Ganin yanda khaleel keyin magana ya tabbatarma Ammah ba fagen wasa ko sanayya akeba, yana fagen aikinsane, danhaka itama taci Serious.
" tabbas yalla6ai a 6angarena Aysha take, kuma saboda juna biyu datake dashi bakomaine takeciba, wanima idan taci amai takeyi, ajiya bataci wani abuba, idanma ban mantaba da rake ta karya, kuma har kaje kataho da ita bataci wani abuba a 6angarena, ban saniba ko zuwanku anan d'in taci".
"Anan ma bataci komaiba, koda mukazoma barci tayi, sai around 1 tatashi, meat pia ne kawai nasan ankawo taci, shima gutsura d'aya kacal tamasa, bama ta had'iyaba, ta furzar dashi. Kamar yanda doctor Faisal yace k'arfin gubar yana fara aikine cikin mintuna 20 kacal ajikin Wanda yaci, daga barinmu nan zuwa 6angarenki zaikai minti ashirin kafin A'eesha ta suma. Abinda Yakuma d'aure kammu shine, babu wata guba ajikin meatpia d'in Dana kwashe atsakar d'akinnan, Wanda A'eesha tazubar, kuma acikinsane taci. Wannan shine yarud'ar damu, akan son Sanin mi A'eesha taci?".
Dr Abraham yace, " sir, inabuk'ar ganin raken datasha".
Da hannu khaleel ya nunu masa ledar rake da fleet dasuke a falon, Wanda suna nan Inda suka barsu tun a jiya.
''Yauwa, kozamu iya ganin inda aka 6arar da meatpia d'in?".
Nanma Kansa ya jinjina musu, yamik'e suka bishi baya, harda Ammah.
'Dakimsa da abin yafaru sukaje.
Tangaran d'in d'aya fashe yana nan, Dan khaleel meatpia d'in kawai yatsince yabar fasashshen kwanon.
Wata Na'ura suka saka, wasu Na haskawa, Dr Abraham kuma nasaka wani d'an tsinke, kusan mintuna 7 Dr Abraham yace kozamu sami ruwa?".
Ammah Ce tafita da Sauri, babu dad'ewa saigata tadawo da ruwa.
K'ar6a Dr Abraham yayi ya yayyafa awajen daduk suke zaton meatpia d'in yazuba, sannan yasaka wani Abu kamar sirinji yazuk'e ruwan, aka tattara fasashen kwaonon aka zuba a Leda, d'an lallek'awa sukayi kozasuga koda wani guntun meatpia ne ad'akin, amma basu ganiba kuwa, sai can wani acikinsu yatsinto wani d'an mitsit a akusada wardrobe, shima da Alama dije bata Ganshi baneba, dukda dai k'ank'antarsa takai akasa ganinsa musamman idan mutum ba'a cikin nutsuwa yakeba.
'Daukarsa sukayi suka saka awata Leda aka d'aure.. Yo bandama dai binciken tsiya irinna ma'aikaci mizasuyi da wannan 6allin abun, saikacefa yaro mai k'yuya yabaka Abu da k'yarπŸ˜‚, gaba d'ayafa baifi Girman wannan gyad'arbaπŸ‘‰πŸ» (πŸ₯”).
Amma haka suka d'auka Dan zai iya Zame musu wani madubin dubawa.
Daga Nan fitowa sukayi, raken fleet Dana ledama Duk suka d'auka aka tafi dashi.
Asibiti suka koma, suma su Ammah asibitin suka tafi.
Sai lokacin Ammah taji cewar ankuma zuwa har Inda Aysha take kwance anbata gubane.
Kutt Amman iya bala'i kuma, aikam tashiga zazzaga masifa asibitinnan, catake ALLAH ka tona asirin kowanne tsinanne ke keson kashemin jikata, ALLAH katona asirin matsiyaci.
Bak'aramar sukan zuciyar Momy adu'ar ammah keyiba, jin Adu'arnan take tamkar tana k'onata da garwashin wutane, Dana tun d'azun arikice take, tarasa hanyar dazata bar asibitin, Dan tafa kula kwa6arsu zatayi ruwa, sotake taje su tattauna plan F, kafin agano yanda Aysha taci guba dakuma wadda aka bata, dije takirata tasanar mata su khaleel sunje gida dawasu doctors kuma taga bincikene Na bin kwakwkwafin tsiya sukeyi, ALLAH ma yasota sanda dije takira wayar tata tasami k'arfin dakewa kamar babu komai ta amsa mata, bama zaka ta6a zargin dawani take wayaba, saboda iyafis dake kunnenta, sauraren dije kawai tayi, amma batace uffanba.


*********
Su doctor Abraham sun kar6i dukkan bayanan hannun su doctor Faisal, suka tattara suka koma setetion d'insu, harda ita Ayshan, wadda aka d'auka kashir6an tamkar mara rai, babu Wanda baimata kukaba a 'yan gidan kuwa, duk da basusan barcine takeba, dansu anfad'a musu har yanzu tana cikin damuwa.
Khaleel yace, "baffa yakamata duk Ku koma gida, yanzun mundawo da case d'in hannunmu, sannan kukula sosai, Dan yanzun koma wanene zai iya d'aukar kowanne irin mataki".
Jinjina kai baffah yayi yana murmishi, yadafa kafad'ar khaleel yana fad'in " haka nakeso kadawo jaruminka, banason karikice kazama mai rauni, dan sun cutar da itane dama dansu raunana zuciyarka, ka karaya gaba d'aya, nikuma sonake hakan yazama allurar k'arin k'aimi suka maka yarona, ALLAH yabada nasara, ya kareminku baki d'aya, kaje, karkayi sanya, ka tabbatar kakama azzalumai Ibraheem!!! ".
Karo Na farko dakowa yaji wannan sunan abakin baffah, kuma yanda yay maganar saida kowa ya tsorata, Dan cikin daka tsawa furicin k'arshe yafita daga bakin baffan.
Kowama awajen da addu'ar samun nasara yabisu, dakuma tasamun lafiya ga Aysha, Momy ma ta daure tayi, amma dukkan mai hankali ya kalleta yasan bata cikin nutsuwa, su Taheer kuma duksun lura da haka, amma basuce komaiba, Dan basu ta6a kawo zarginsu akan Momy ba, tunda sunsan mahaifiyar Khaleel Ce.
Amma Samuel yad'auki alk'awarin bin kwakwkwafin Momy, Dan tund'azun duk wani motsinta akan idonsane, haka kawai yaji zuciyarsa bata amince da itaba, yana kuma kallon sanda take waya, dukda batayi maganaba wasu alamomi sun nunata.
Koda suka tafi shidasu khaleel shi dawowa baya yayi.
Cikin dabara yaytabin moticin gidansu khaleel abaya, wani guri nesa dagidan yasamu ya zauna, ya tabbatar inhar Momy batada gaskiya saita fito daga gidan.

__ __
πŸ‘ πŸ‘
πŸ‘ƒπŸΌ .
πŸ‘„
Nima ina nan sainaga fitowar hajia babbaπŸ˜‰πŸ€£πŸ˜œ.


__________________
Yinin yau zumbur su khaleel basu hutaba, dukkan wata kulawa ta musamman kuma Aysha tana samunta, lokaci-lokaci ya khaleel kanje d'akin datake kwance Wanda keda fasifar tsaro ya dubata.

*****

Sam.... Kuwa sarkin naci yana nan la6e har kusan bayan magribaπŸ˜‚.
Harya fara hasashen Barin wajen saiga wata tafito daga gidan su khaleel, cikin dogon hijjab da Nik'af.
Su Samuel sunsan kan aiki sosai, aikam baiyi k'asa aguywaba wajen bin matarnan, saida sukayi nisa da layin tatare taxi tashiga, shima tarewa yayi yashiga, adabara sukebinsu, har zuwa anguwar su hajia khaltum.
Sam....yagane gidan hajia khaltum, Dan shine yasato sakeena lokacin.
Da sauri ya sallami mai taxi, wayarsa yad'auka yakira number sakina, danya kar6i number d'inta alokacin, kuma ta tabbatar masa babu wanda yasan tanada waya agidan.
Saida takusa tsinkewa tad'aga, murya k'asa-k'asa tace, "yalla6ai wlhy kad'an yarage akamani, ina wajen bama bak'uwar hajia ruwa kakirani".
"Yauwa, wace bak'uwace".
" hajia Laurah maman yalla6ai khaleel".
"Da gaske?".
" ALLAH kuwa".
''Yauwa Sakina, kisaka musu ido, idanma da dama kiyi recording d'in dukkan wata hira dazasu kituromin, ki kula sosai".
"To shikenan, dama nazo had'a mata kunune, kuma nagama, zansan yanda zanyi Na ajiye wayar a d'akin idan nashiga".
"Yauwa, saina jiki".

**
Sakina tayi duk dabarar dazatayi ta ajiye wayar, bayan ta danna record, tabaro d'akin.
Su hajia khaltum basusan mike faruwaba suka baje faifan hira kuwa, sosai suka tattauna akan abinda yafaru yau, dakuma meeting dazasuyi Na k'ungiya gobe, kuma duk akan su khaleel ne..
Itako waya babu ruwanta, tanata nad'e komai.
Sai wajen around 11 hajia babba tabar gidan, driver zai maidata gida.
Hajia khaltum tatafi rakata sakina tayi wufff tashige d'akin, ta d'auke waya ta 6oye bayan tayi hanzarin saving d'in recording d'inta.
Tana k'ok'arin fitowa sukaci karo da hajia khaltum, kallon tuhuma Tamata, Dan babu wani d'an aiki da hajia khaltum ta yarda dashi agidan.
" k miya shigo dake d'akinane?".
"Wlhy babu komai hajia, nazo tartare kayan dakukayi amfani dasune, saboda zanyi wanke-wanke".
" shine kuma bazaki jira nakiraki ki d'aukaba, Kodai la6e kikaimin?".
"A'a Ammi, nicefa natasotama yanzu tana barci wlhy".
Babie Ce mai maganar tana fitowa daga d'akinta.
Shiru hajia khaltum tayi tana kallon babie, dawannan Damar sakina tazare jikinta tabar wajen, dama zuciyarta sai dukan 100-100 takeyi.
Saida tagama wanke-wanken sannan tashiga toilet d'in d'akinsu Na 'yan aiki ta turama Samuel record d'in.
Shikuma adaren yaturama Taheer.
Bak'aramin tashin hankali Taheer yashigaba, dan lamarin ya rikitashi, mahaifiyar mutum mai gaskiya da sanin darajar aiiki takasance cikin manyan criminals da suka gagari k'asa, wannan wace irin rayuwace?.
Shiyanzu yaza'ayi ya tunkari j da wannan batun?, kuma aii dolene yasan komai dangane da operation d'in, tunda bak'aramin aiki baneba.
Hakadai yayta k'ullawa da kwancewa, daya kasa hak'uri saiya kira youseef da Joseph ya shaida musu, sumafa zancen ya firgitasu ainun, sukaita tattauna yanda zasu 6ullowa lamarin, aganinsuma gara khaleel d'in yakamata dakansa akan su sukamata.
Sundai yanke shawarar sanar masa tawata sigar, amma ba gaba da gaba ba.


*******
A setetion khaleel yakwana yau, haka suma su Doctor Abraham sunata aikinsu.



*_Monday morning_*

Ranar litinin misalin k'arfe 9am khaleel yazo gida a gaggauce yay wanka yakoma setetion d'insu, babuma wanda yasan yazo gidan, harya fice.
Dama tunjiya babu walwala ga kowa, tamkar anyi mutuwa haka gidan yake, kuma kowa kwana yayi gaban ubangiji yanda mik'a kukansa akan wannan Matsala data tunkarosu.
Masu aiki wasu sunfita, wasu kuma sunata shiri, hakama masu zuwa makaranta.
Hajia babba tana cikin wad'anda suka fita.

Khaleel Na dawowa office yawuce kawai, zamansa dakamar mintuna 27, saiga Dr Abraham, izinin shigowa yabasa.
Dr Abraham yashigo, yay salute d'in khaleel sannan yabashi damar zama.
"Sir! Tabbas bincikenmu ya nuna Madam taci guba da farko, kamar yanda likitocin General hospital suka tabbatar, kuma taci abinne da mintuna 19 kacal yafa aiki ajikinta, saboda kad'an dataci yahana gubar k'arfinsa tasiri ajikinta, munduba raken da'akace tasha kafin meatpia babu komai acikinsa, kuma tsakanin shan raken dacin meatpia yad'auketa awanni 5 dawasu mintuna, sannan meatpia d'in da sauran mutanene gidan sukaci babu guba aciki, hakama Wanda ka kwashe bayan madam ta 6arar babu gubar".
" Amma gurinda meatpia d'in ya6are muka zuba ruwa tareda zuk'ewa ya nuna anan akwai guba, ('Yar zabura khaleel yayi, amma baice komaiba), Dr Abraham yacigaba dafad'in " dalilin dayasa muka gane gubar shine, akwai 6ar6ashin meatpia d'in awaken, Wanda ruwan damuka zuba ya narkar dashi har muka sami damar gane akwai guba. akwai kuma wani guntun damuka samu gabda zamu baro d'akin shima akwai guba aciki. Sannan kwanon shima maik'on mai daya manne ajiki yanuna akwai guba".
"Tabbas abinda nalura dashi Annan shine bayan madam ta 6arar da meatpia d'in, inhar kunbar d'akin to wani yazo yakwashe meatpia mai guba, ya canja damara gubar, Dan kenan wanda mutanene gidan sukaci shi babu guba aciki, Wanda madam tacine kawai mai guba".
" abin kuma mamaki Na uku shine gubar dake cikin meatpia d'in irintace aka bama David yasha aruwa..........
Babu shiri khaleel yamik'e tsaye tsaye, "doctor ka tabbatar hakane?".
" yes sir!, babu kokwanto a cikin aikina, ga dukkan bayanan Na tattara a file d'innan Kaduba kuma, harda Na David ma nasaka maka duk da nasan kanadashi".
Gyad'a kai khaleel yayi, shikuma doctor Abraham yafice.


Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai khaleel yake Ambata, kenan da gaske momyce tabada guba da hannunta dansuci? To Aysha tabamawa koko shi? Yasan Momy batason Aysha, amma baikawo zata iya yunk'urin kashetaba, to mima yasaka gubar tazama dai-dai da wadda Akabama David?.
Komawa yayi yazauna, yana duba file d'in da dukkan bayanan ciki.
Kusan awa 1 ya d'aukeshi.
Saiga Samuel yayi nock d'in door.
Izinin shigowa yabashi.
Bayan ya k'ame tareda salute Na khaleel yabashi izinin zama.
"Samuel yadai?, komun samu wani abunne?".
" yes sir, mai muhimmancima kuwa, akwai wani meeting d'in sirri daza'ayi yau, kuma harda matarnan hajia khaltum wadda taturama barau modibbi sak'o aciki".
" Masha ALLAH, a ina kenan Sam...?".
"Ga dukkan bayanan inda taron zai gudana annan, nima nasamu bayananne a majiya mai k'arfi, tun sanda kabani aikin bibiyar hajia khaltum banyi k'asa aguywaba".
" da k'yau sam..... Da irinku Muke alfahari a hukumarnan".
'Yar dariya Samuel yayi, yace, "aii tarbiyyarkace sir".
Khaleel baice komaiba, yafara duba bayanan.
Sosai yayi farinciki, duk da kwakwalwarsa da tunaninsa suna cikin wani yanayi, amma hakan bazai hanashi fuskantar wannan aikinba shima, tabbas yana kammalawa dashi zai maida hankalinsa kacokan akan Momy, daduk wani mahaluki dake gidansu.


Nace hummm, khaleel kenan, kwantarma da hankalinka, ALLAH ya sauk'ak'a maka.πŸ€ͺ.



__________________

*_4:30pm_*


*_IDAN KERE NA YAWOπŸ’, ZOMO NA YAWOπŸ‡, dolene wata rana agamuπŸ’πŸ‡πŸ€£πŸ€£._*

Su khaleel sungama shiryawa tsaf, anyima bindugu saves da bullet, hakama handcuffs and'iba dayawa.
Motoci kusan 7 aka d'ibi ma'aikata aciki, amma duk sai suka rarrabu, ko'a cikin setetion d'in bakowa yasan inda zasujeba, saboda tsaro, amintattunsune kawai aka d'iba.
Nesa dawajen taron suka ajiye motocin.
Duk sanye suke cikin Uniform d'in aiki, babu mai fuskar rahama acikinsu kuwa.
Cikin hikima suka sami wajajen mak'alk'alewa, Dan wajen meeting d'in cike yake da tsaron 'yan ta'addah.

Tsitt d'akin meeting d'in yake, su Momy duksun nutsu suna sauraren jawabin shugaban k'ungiyarsu............✍




To yaudai kam, zamuce k'arshen tika-tika tik, masoyan hajia babba sainace amin afuwa, dominfa gobe itace ranar bankad'ar sirrikan 6oye, ranar bayyanar abubuwan mamaki, Wanda bakowama yayi zaton hakanba, mutane dayawa dazasu bayyana muku ta sigogi da damaπŸ‘.
Tabbas akwai abubuwan mamaki, al'ajabi.
Nikaina bilynku nak'agara gobe tayi araduπŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ˜‚πŸ˜‚.


Happy day fan's

*_TypingπŸ“²_*


🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_


*_Bilyn Abdul ceπŸ€™πŸ»_*


*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyuπŸ“˜)_

*_ASSALAMU ALAIKUM MASOYANA!!_*

_Awannan ga6ar kam zan baku hak'uri, amin afuwa sosai, nasan wasu basajin dad'in yanda sukemin comments a groups amma bana magana, wlhy abubuwan yawa sukemin, zaka kula da Oga da safe, kafin yafita, yana fita aikin gyare-gyare zakayi, sannan nafita islamiyya, nadawo 12, wlhy ina dawowa typing kawai nake zaman yimuku, wahalar typing takan d'aukemu lokaci mai tsawo, saboda abune Na nazari, wani lokacinma saikin kusa gama page kiji baiyiba, ki goge kiyi wani kuma, kunga kafin mutum yagama kansa yad'auki zafi, sauri kake kagama ka fuskanci aikin gida kuma, wani lokacin kiyi bak'i, ko fita takamaki kekanki, ALLAH akullum ina gamo da messages Na PC samada 150, rasama ta ina zan fara nakeyi, gakuma Na groups, groups yakai 40 wanda nake a ciki, wasu kunyarsu take hanani fita kawai wlhy, lokacin dazan gama typing kaina yad'auki zafi sosai, saina dingajin gandan duba sakwannin PC, amma dankarkuga kamar inamuku wulak'anci nake daurewa naduba, shiyyasa nake d'auke idona ana groups, amma wlhy inajin dad'i sosai, kuna sakani farinciki ainun, badankuba banga amfanin rubutubba, tunda bazan rubuta danna karanta nikad'aiba, duk inda masoyina yake nima ina matuk'ar sonsa da alfahari dashi, babu abinda zance daku saidai ALLAH yabar zuminci, k'aunarkuce ke sakani wajen 6ata lokacin yin typing kullum da siyen data, I love you so much my fans, babu marubucin dabaison masoyinsa, duk muna k'aunarku wlhyπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹β€β€β€β€β€β€β€._
Amin afuwa please, kuna raina wlhyπŸ‘πŸ’˜.


3⃣9⃣

Su khaleel sunada yawa sosai, amma dukda haka su hajia babba sunfisu yawa, danma ankama wasu aciki, sauk'in d'ayane bakowa keda makami acikinsuba.
Dukda jikin ya khaleel a sanyaye yake, kuma baisan daliliba, amma hakan baihanashi aro jarumtaba ta musamman ya k'arfafawa kansaba, daboda gudun Matsala.
Acikin kwarewar aiki suke shiga wajajen, duk wanda akayi karo dashi kuwa cikin dabarar aiki suke gamawa dashi, basuda mafitar data wuce kashesu, saboda suma suna samunsu kashesun zasuyi tunda akwai nakamai a hannunsu.
Bawai k'aramar k'ungiya baceba, k'ungiyace data tara manyan mutane, masu muk'amai kala-kala, ga dukiya sun tara, saboda business kala-kala dake gudana cikin k'ungiyar, kuma Na manyan kud'i.
Karya wuyan wani da khaleel yayi bayan nannad'e kansa aleda yasakani rintse idanu, sosai tsoro yashigeni, danganin yanda zukatansu khaleel suka gama bushewa, basajin komai wajen kisan garatan nan.
Matsalar da aka samu shine cctv camera dake aiki acikin d'akin taron, wadda su khaleel basusan da itaba.
Wad'anda suke kulada cctv camera d'inne suka ankarar da 'yan k'ungiyar.
Tashin hankali kenan, wai Wanda ba'a saka masa rana, kusan shekaru 29 k'ungiyar Na aikinta. Amma basu ta6a gamo da makamancin tashin hankalinnanba, saidai amusu tsinci d'ai-d'ai badai gaba-da gababa, don ko kad'an basu aminta wani yafidda sirrinsuba, komai cikin ilimi ake yinsa.
Hargitsewa hall d'in yayi, masu makamai suka fara d'ana kunamin bindugu, irinsu Momy kam sai neman wajen 6uya.
Musayar wutane yafara gudana a tsakaninsu, bakajin komai sai k'arar harbe-harbe.
'Yan jarida kam dasu khaleel sukazo dasu sai d'auka sukeyi, lamarin kaikace film ne wlhy.
Shirin ma'aikaci da d'an ta'adda bazaizo d'ayaba, dukda gawurtar k'ungiyar su hajia babba takai taringa bama matasa training saboda gudun zuwan rana irin wannan ta kota kwana.
Tiyagas su khaleel suka fara jefawa cikin hall d'in, dama su sun d'auki matakan kare kai, dandanan wajen yakacame da tari da atshawa, gashi hayak'in yana saka hawaye, masu ciwon asma kuwa saidai addu'a kawai.
Jefa tiyagas yaba su khaleel damar shiga hall d'in, dukda haka akwai masu taurin zuciya dake harbi har yanzun.
Amma haka su khaleel sunata samun nasarar cafke wasu, Dan k'ungiyar ta tara maza da matane, harda wad'anda tunaninka bazai ta6a kawo maka ganinsuba awajen, saboda Girman milki ko dukiya.
Akwai k'ofofin fita da dama acikin hall d'in, wannan ne yabama wasu dama sulalewa, amma ina, wannan shine angudu ba'a tsiraba, dankuwa cikinsu khaleel wasu sun bisu.
Acikin masu guduwa kuwa harda hajia khaltum da hajia babba.
Lamarifa yaci tura, komai yagama hargitsewa, acikinsu khaleel dayawa sun sami harbi, 'yan k'ungiyar kam ba'a magana, bayan wad'anda aka antaya barzahu akwai masu harbi a sassa daban-daban.
Kusan awanni 3 aka d'auka ana Abu d'aya, lamarin kamarma bazai k'areba, kowa yafita hayyacinsa, Dan babu Wanda baiji jikiba, ansami cafke mafi yawa acikinsu, wad'anda suka samu raunuka akafiddosu waje, gawawwakinma haka duk an fiddosu, wad'anda suke k'alau kuwa handcuff aka saka musu, duk aka fito dasu waje, 'yan jarida sunata aikinsu.
Ya khaleel yafara bin ma'aikatansu yana dubawa, Dan a tantance wad'anda suka mutu, dakuma rauni, duk a wahalce suke.
Khalee yace, "amma akwai wad'anda babu acikinmu?".
''yes Sir! Wasu sunyi yunk'urin guduwane, shine suka bisu".
"OK!, yakamata azuba wad'annan amotocin da aka kawo, suma akirasu aji?".
" OK sir".

Wad'anda basa wajen aka shiga kira, wasu suce sun kamasu, wasukuma suce sunadai binsu binsu abaya har yanzu, amma suna buk'atar k'arin ma'aikata.
Taheer dai cayayi ahad'ashi da khaleel.
Faruk yamik'ama khaleel wayan cikin girmamawa.
A kunne yakara batareda yayi maganaba, daga can Taheer yace, "sorry sir idan bazaka damuba kazo da kanka, wasu mutane hud'u sun shiga gidanka, bazai yuwu mushiga babu izininkaba".
" gidana kuma Taheer?".
"Yes sir?".
''OK ina zuwa, kubani k'ank'anin lokaci".

Saida khaleel ya tabbatar anzuba sauran a mota, wad'anda suke buk'atar k'arin ma'aikata aka tura musu, wasu kuma suka tafi da motocin wad'anda aka kama, ma'aikatasu kam tuni anyi gaba dasu Dan basu taimakon gaggawa.
Ya khaleel kansa yasamu raunuka, amma bai damu da kansaba, Na k'asa dashi kawai yake son abama kulawa.
Key d'in mashin yakar6a ahannun wani ma'aikacinsu, yanufi gida zuciyarsa Na dukan 100-100 saboda fargabar abinda zai Tatar, kenan zarginsa yazama gaskiya, acikin gidansu akwai mai mu'amullah da k'ungiyar? jiyake tamkar zuciyarsa Zata kama da wuta saboda bak'in ciki da fargabar wanda zai tarar amazaunin d'an k'ungiyar.
Ak'ofar gida yay gamo dasu Taheer dake tsaitsaye, basu shiga gidanba, saboda

Please Login or Register in order to submit comment