Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tanaja da baya, " A'a fa Surukata, karkiyi wannan kuskuren, akwai jikanki anan", tanuna cikinta, "sannan ta6ani babban kuskurene dazai iya 6allo ruwafa, nidama shawara nazo Baku, aganina daku zauna tada jijiyoyin wuya kan k'yautar jika da ALLAH yabaku, gamma kulura da abinda ke tunkaroku fa, kuyi azamar bincika ina Kubrah? yau tsawon kwanaki 3, itada tace zataje Lagos tayi kwana 1".
" sannan kekuma k'awar surukata kibar tada jijiyar wuya akan beeb guy, 🤣🤣kema yasama miki jika kuma d'a ajikin 'yarki babie🤪".
"Please & please aminan juna, abar fad'a fa, kusan masu iya magana nacewa *_SHARRI 'DAN AIKENE, DUK KUMA INDA KA AIKASHI SAIYA DAWO YASANAR MAKA YAJE😉_*.
Bye, har Aysha tafita tadawo, "o, wlhy Na manta suruka, dama inason fad'a mikine idan za'a siyama mufeeda kayan haihuwa atuna da d'an jikalle🤨, tayi maganar tana nuna cikinta🤣🤣, tafice tana 'Yar dariyar mugunta.

Rasa wanda zai iya motsawa acikinsu akayi, maganganun Aysha sungama dukan zukatansu, kowanne arikice yake, hajia khaltum ta kalli hajia babba, itama kallonta takeyi, " Aminiya da gaske yarinyarnan keyi? Habibu yayima babie ciki, kuma ankama kubrah?".
Cikin marairaicewa hajia babba tace aminiya ban saniba, amma ina mamakin rashin dawowar kubrah dama, Dan kwana d'aya tace zatayi, gashi tunda tatafi bata kiraniba", hajia babba tayi maganar tana zama agado ja6ar'.
Itama hajia khaltum zubewa tayi, sai zufa sukeyi kamar babu fanka ad'akin, jiki Na rawa haji khaltum ke Neman number Kubrah, amma switch up, tagwada yafi sau 30, maida akalar kiran tayi kan wata mata, ko gaisawa basuyiba tace kubrah tazo?".
Daga can aka sanar mata batazoba, amma tabbas sunji k'ishin-k'ishin cewar an kamata....
Aii zabura hajia khaltum tayi itada hajia babba, kowacce tarasa inda kemata dad'i, sai faman zagaye d'aki sukeyi suduka, sun rasama wane tunani zasuyine, zuwacan hajia babba tace, "Aminiya miye mafita?".
Wlhy aminiya kaina ya toshe, kibani nanada gobe, inaso naje Na binciki babie yanzunnan".
"OK saikin dawo".

___________________________

Tunda Aysha takoma 6angaren Amman yanayinta ya canja, daka ganta zakasan tana cikin farin ciki, hardai Ammah takasa hak'uri ta tambayeta.
Murmushi Aysha tayi, "tace babufa komai Ammah".
Ammah bata sake cewa komaiba.

**********
Tunda ya khaleel yabar office baizame ko inaba sai Cinema, abakin k'ofa yatsaya, duk wani mai shiga da fita akan idonsane shida Taheer da youseef da Joseph, suna nan tsaye kuwa saiga beeb guy da 'yanmata biyu, saikuma abokansa, cikin nishad'i suka kar6i ticket suka shiga, suma su ya khaleel suka kar6a a sannan, su habeeb na gaba su ya khaleel Na bayansu, can kallo yay nisa habeeb yamik'e zaije fitsari, asace Youseef yabi bayanshi har toilet d'in.

Habeeb nacikin fitsari youseef yashigo, juyawa yayi yad'an kallesa ya janye idonsa, youseef yad'anyi kamar shima fitsarin yakeyi, Habib nagama youseef yayo kansa, yaje yatare k'ofa.
Cikin kallon sama da k'asa habeeb yace, " Malam lafiya kuwa?".
"Dadai sauk'i, dama zan fad'a makane kasan an kama kubrah kuwa?".
" kubrah fa kace?, wasa ko gaske?".
"Mizaisa namaka k'arya, idan kanason tabbatarwa zomije kagani".
" a tunaninka kai tsaye zan yarda dakai?". 'Cewar Habib'.
Murmushi youseef yayi, yazaro waya a aljihunsa yanuna masa k'aramin video lokacin da'ake kama kubrah, yace budurwatace, dakanta taturomin video d'in nan kafin su kwace wayar, kaga sak'on data turomin akan Na nemeka mu tatatuna yanda za'a ku6tar da ita".
Kar6a Habib yayi, yaduba sak'on, tabbas no d'in kubrah ce, babu musu yabi bayan youseef har waje, suna zuwa jikin mota yafaki idon mutane ya shak'a masa abunda ke cikin hanky d'insa, tuni jikin Habib yasaki, yasulale zai fad'i, youseef yay saurin turashi mota yarufe, sannan yakira number khaleel yace aiki ya kamalla, sufito kawai.
'Dai-d'ai suka ringa fitowa, sabida tsaro ba tsoroba, daganan ya khaleel gida yawuce.
Youseef da Joseph kuma suka wuce setetion dansu kai Habib.


Sanda yashigo gidanma su Ammah harsun rufe k'ofa alamar sunyi barci kenan.
6angarensu yawuce kawai, shima yayi duk abinda yadace yakwanta.
Har yau maganganun Aysha suna masa yawo a kwalwar kai.

___________________

Hajia khaltum kuwa tana zuwa gida tatasa babie gaba sukaje asibiti, gwajin farko yanuna babie batada ciki, ajiyar zuciya hajia khaltum tayi, hankalinta yad'an kwanta, suka dawo gida, mamakinta babie taitayi, dan batasan ma'anar gwajin ciki da ammi takaita aka mataba.

🤣hajia khaltum batasan cikin yana jikin salima baneba, Aysha tayi yawo da hankalinta ne kawai..........✍🏿
🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀

*_Typing📲_*


🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_


*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*


*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of expert & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu📘)_


3⃣6⃣

Yau dai babu laifi Aysha antashi dad'an k'arfi-k'arfi, saidai tunda farar Safiya tatashi da jarabar son rake, Ammah na zaune afalo tana shan kunun tsamiya, k'a'idane kullum Safiya saita shashi, idan 'yan tsiyarma Na kanta saida k'osai, haka takecewa tagaji dawad'an nan maik'on banzan😂.
Aysha tafito daga d'akin Ammah, dakaganta dukta rame, sai uban haske data k'ara, har wani yellow-yellow takeyi, kusada Ammah ta zauna tana sauke numfashi.
Amma tabita da kallo, sannu indo, kai wannan ciki nabaki wahala, gashi ALLAH ya had'aki da birkitaccen miji, ni tsoroma nakeyi karki haifo irinsa".
Murmushi Aysha tayi.
Tace, ''kai Ammah, kedai kullum kintaso ya khaleel gaba, kemafa doguwarce, awajenkima yakwaso tsawon, nibama wannanba, ina zan samu rake dan ALLAH Ammah?".
Ammah ta kur6i kununta tana ta6e baki, kai wannan ciki naki yacika shegen hange-hange, shiyyasa nacemiki ina tsoratar miki haihuwar irin iro, Dan yahalin cikinki ya halin dogon banzarcan".
Baki Aysha taturo gaba, "duk kigama fad'a saina sanar masa gulmarsa dakikeyi".
" yo kifad'a mana, angaya miki tsoronsa nakeji, dagake harshi saina had'aku nayi k'uli-k'ulin kubrah daku".
Dariya sosai Aysha keyi, hakama Musleem daya shigo kusan mintuna hud'u, maganganun Ammah akan kunnensa suka faru.
Hararsa Ammah tayi, "to kaikuma d'n kwairo wakakema dariya?".
Had'e fuska musleem yayi, " waike Ammah kowama agidannan saikin saka masa sunan banzane? Nifa shiyyasama Mafison kitafi jigawa".
"Yo basai ka kainiba d'an banza bakwai, aii dai gidan d'anane, babukuma mai iko dashi sama dani, faratun banza kawai".
"oho dai, farin aka gani aka rud'e". Yamik'e yana hararta, "nikingama tafiyata, Anty Aysha bara nasa akawo miki raken".
" yauwa ya musleem, ngd sosai, Ammah kinji dad'inki, kedai dakowama karawa kikeyi, ya Sultan ne kawai bakwa fad'a".
"Aishi Sultan mutumin arzik'ine, ba irinkuba, amma d'aya bayan d'aya zanyi maganinku, d'an banzancan zigawa zanyi amasa auren dole kwannan, kekuma aure zansa iro yak'ara, kuma 'Yar k'auye zan za6o masa wadda haushi zaiyi kamar ya karsa....
Tsayawa Aysha tayi da dariyarta, ta had'e fuska tamau, mi Ammah zatayi ba dariyaba, afili tace, " ja'ira, ashedai kinason dogon banzan can mai zuciyar tsiya, amma lokacin auren hardasu kuka".
Shiru Aysha tama Ammah, daga waje akayi sallama.
Ammah tace, "kowaye shigo kaji, d'akin tsohuwa aina kowane".
d'aya daga cikin drivers d'in gidanne, har k'asa ya durk'usa ya gaida Ammah, yamik'o leda viva, gashi inji musleem yace akawo".
Aysha najin haka takar6e da sauri, yauwa sannunka.
Rakene mai yawan tsiya aciki, irin wanda aka yanka k'ananunnan aka d'aura afarar Leda, Ammah tayi dariya, ''yoshi wannan duk raken yasiyema mai tallan ko?, saikiyata sha har kigaji".
"Wlhy kuwa Ammah, dama mafarkinsa nayi a barcin asuba d'innan Dana koma, bara kiga nayo brosh nadawo".
''Dama bakiyi burushi ba kikazo kika zauna kinata had'iyar k'azamin yawu?, ke indo kirage k'azantafa".
" k'yadai jidashi Ammah, aikinsan idan nayi brosh babu abinda zanci amai nakeyi dai", batareda tatsaya jin mi Ammah zataceba tashige bedroom, Mufeedah Na kwance d'ai-d'ai tana shak'ar barcinta, dama ita cikin nata sai saka barci.
Brosh Aysha tayo tadawo falon, tatarar Ammah tazuba mata raken cikin fleet bayan ta wanko matashi, ankuma ajiye roba na zuba datti.
"Yauwa Ammarmu, shiyyasa nake yinki sosai-sosai".
"Kedai kika Sani" cewar Ammah tana shigewa kichin d'inta.
Aysha tama bayanta gwalo, tafara shan rakenta, harda mik'e k'afafu kamar tasamu gasashshen kifi🤪.

Tayi nisa sosai da shan rakenta, harwani lumshe idanu takeyi Dan dad'insa datakeji, ya khaleel yashigo da sallama, sanye yake cikin k'ananun kaya, blue dogon wando da oxblood d'in sheart, sunmasa k'yau sosai, kwarjini da cikar kamalarsa ta k'awata k'yawun haibarsa, yad'an rame kad'an saboda yawan tunani da cud'ewar aiki dasuka tasoshi gaba.
Kokad'an Aysha bataji sallamarsaba, idonta alumshe tanata shan rakenta, dariya tabashi, Dan haka yajin gina da bango yana kallonta, sai murmushi yakeyi, ganin abun bana k'are baneba yafiddo wayarsa a aljihu yashiga mata video. Oho Aysha batasan yana yibama, Ammah Ce tafito daga kicin taga abinda ke faruwa. "Iro mikakeyi haka?".
Harara yazuba mata, "waya sanya dakene jar wuya?, kinzo kin 6atamin show", 'yay maganar yana save d'in video dayayma Aysha'.
Itama idanu tabud'e da dauri, kokad'an batayi zatonsa yanzunba, danta manta yau Saturday, babu aiki.
" kai iro ka kiyayeni wlhy, naga kwana biyunnan jaraba kakeji, nimafa Na iyata mota-mota, bar ganinka sangamemen k'ato batsoronka zanjiba ehe😏".
Yanda tayi maganar da murgud'a baki, saita bama ya khaleel dariya, yasanta da nacin tsiya, idan tafara nacin maganarnan yinin yau babu sauk'i.
Yace, "hakanefa jar wuya, ni nama manta kece, kinga zauna muyi hirar arzik'i".
" ato inda arzik'in kazo basai ayiba, nidama nemanka nakeyi".
"To gani Ammah ta".
Aysha dai dariya kawai take musu, Dan ita lamarin nasu dariya yabata, Ammah da ya khaleel tamkar tom & jerry haka suke.
Khaleel kam dukkan hankalinsa nakan Aysha, sauraren Ammah kawai yakeyi, sosai dariyarta take narkar dashi, dama kwana biyunnan hak'uri kawai yakeyi, yamatso kusada ita yana fad'in " a lallai kinji sauk'i, hardasu dariya?".
Murmushi Aysha tamasa mai kashe zuciya, tace, ''Alhmdllh, yau natashi babu laifi, harma inajin zan koma aiki ranar Monday".
Girarsa d'aya yad'e yace, "da gaske?".
Jinjina masa kai kawai tayi.
" to ALLAH yak'ara lfy". 'Yay maganar yana kuma shigewa jikinta, Dan Ammah tashiga bedroom yin wanka. Murya can k'asa yake mata magana, "waya siya miki rake da safiyarnan".
Kuma narke masa tayi ajiki tace, " ya Musleem mana, wai ina kashigene jiya, har nayi barci baka dawoba, bayan wahalar danasha tun wajen 6pm Nake amai, saida doctor yazo yasaka min k'arin ruwama".
Da sauri ya kalleta, "da gaske kikeyi".
" ALLAH kuwa".
Tausayinta ne yakuma kamashi, azuciyarsa yace kai uwa dabance, (ALLAH ne kawai zai biya mahaifiya gaskiya), Ahankali ya sumbaci goshinta, "sorry kinji my pretty na, yanzu inane kemiki ciwo?".
" babu ko ina, yau dad'an sauk'i aii".
"To Alhmdllh, kinga yau agida zan yini, yakamata mud'anje 6angarenmu muyi hira ko? Naduba babyna mu gaisa dashi".
Aysha bata gane nufinshiba, tace, " idan Ammah tayi fad'a fa?".
"Babu wani fad'a dazatayi, tashi mujema kafin tafito".
Kamardai Aysha bazatajeba amma yamata wayo tabishi, shiya d'auka mata raken fleet d'in dana ledan, tacan baya sukabi dankar agansu, sai 6angarensu.
Komai fes Aysha ta iskeshi, Dan kullum sai Maleeka da Tasleem sunje sun gyarashi, afalo suka yada zango, suka zube bisa doguwar kujera, ya khaleel ya kwantar da Aysha bisa cinyarsa tana shak'ar daddad'an turarensa, sai lumshe idanu takeyi, Dan wani barcine taji yana fisgarta.
Idonsa akan fuskarta yana shafa kwantaccen gashinta da hannunsa Na dama, Na haggun kuma yana kan shafaffen cikinta maikama da babu komai aciki, " my pretty badai barciba?".
Bud'e lumsassun idanunta tayi akansa, saikuma tamaida tad'an lumshe takuma bud'ewa, muryarta harta fara sark'ewa tace, "ALLAH barci kawai naji nafaraji".
" lallai 'yar gata, rakenfa to?".
"Nakuma k'oshi".
Guntun murmushi yayi yana kauda kai daga kallonta, itakuma tamaida idonta talumshe.



______________________________

Adaren jiya gaba d'aya Momy takuma fita hayyacinta, zuwa yau kam jininta yagama kai k'ololuwar hawa, gaba d'aya daren jiya bata rintsaba, tunani dai babu kalar dabatayiba a daren jiya, amma har yanzu tarasa matsaya, dama d'ayace tarage mata ayanzun, kuma zuciyarta tafi karkata awajen, tana tsaka da tunanin ne aka kira wayarta, cikinta har rawa yakeyi tad'aga saboda ganin number hajia khaltum, babu batun gaisuwa hajia khaltum tafara shaida mata cewar ankama habibu, cikin kuka hajia khaltum keyin maganar, kasa cewa komai hajia babba tayi, saima wayarce ta sulale tafad'i k'asa, aikam tayi kwatsa-kwatsa, abinka da tayis, abin mamaki saiga hawaye a kumatun hajia babba, sai gudu sukeyi kuwa, wasu Na korar wasu, kusan mintuna 20 tad'auka awajen, sannan saigata ja6ar ak'asa tayi zaman 'yan bori🤣🤣🤣🤣.


🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀Reefat amin afuwa🤪.


_________________________
Ammah na fitowa taga babu khaleel babu Aysha, babukuma ledar rakensu, "amma dai ALLAH ya shiryeka iro, dama satarta kazoyi kenan?, zan kamakane aii, INA zaune shararren wajena zakazo ka iskeni, tayi kwafa".


************
Ya khaleel kam tunda yaga Aysha tayi barci ajikinsa saiya d'auketa zuwa d'akinsa, saman gado ya shinfid'ar da ita, shima yakoma gefenta ya kwanta, dama bawani isashen barci yasamuba, babu dad'ewa shima barcin ya sureshi.

Basu farkaba har 12:56pm afirgice ya khaleel yafarka, saboda mafarki yayi anata sallah amma shi yana zaune, kansa yadafe yana addu'ar tashi abarci, saiyaji ana sallamar idar da sallah, waigawa yayi yana kallon Aysha dake barcinta har yanzun lafe ajikinsa, ahankali ya zameta yasakko daga gadon, alwala yashiga toilet yad'auro a hanzarce, ganin koma yatafi masallacin anrigada an idar, saikawai yashinfid'a sallaya yayi ad'aki.
Tun yana raka'a ta biyu Aysha tafarka itama, cikeda sha'awa take binsa da kallo, bak'aramin burgeta yayiba yanda yake sallah a tsanake, kuma komai cikin k'a'ida, tana nan tashagala da kallonsa harya idar.
Bayan yayi sallama yajuyo ya kalleta, danyaji ajikinsa ana kallonsa, d'an murmushi yamata, " my pretty kintashi?".
Kanta ta girgiza masa batareda tayi maganaba.
"To sakko kiyi wanka ki sallah, time yana k'urewa".
Sai yamutse fuska takeyi haka ta sakko, ganin yanda take tafiya kamar wadda batada laka ajiki yasaka ya khaleel shafa addu'ar yabita toilet d'in.
Taddata yayi zaune wai tana hutawa, yay murmushi tareda girgiza kai, dakansa yahad'a mata ruwan wankan maid'an zafi, ya taimaka mata tacire kayan, dukda tanata wani nok'e-nok'e, dakansa yamata wankan, amma da manufa biyu, taimako da bincike, (ko d'igon zanene tattu bai gani ajikin Aysha ba, barema wata kunama🦂, hakan bak'aramin d'aure kansa yayiba. Bayan sun fito ta tak'ark'ara tayi sallar Azhur.
Tana idarwa yay sama da ita zuwa gado, Dan dukta birkita masa tunanin sanda yake mata wanka. ganin lamarin nasu yafi k'arfin alk'alamina, Dan tamkar mayunwata haka suke kissing d'in juna, dagani Kasan sunyi missing d'in junansu.

🚴‍♀🚴‍♀dolene nakama gabana, kafin su koyamin fitsararsu😏.


____________________

Momy dai tayanke d'aukar matakin k'arshe, kamar yanda suka yanke shawara itada Aminiyar tata, dakanta tashiga kichin, ta kori mashi'a, filawa naga ta kwa6a kala biyu, babu dad'ewa tagama had'a meat pie d'inta, kowanne tagasa a oven, abinda yabani mamaki shine rarrabashi datayi.
Gaba d'aya yanayinta kuma yakoma Na farinciki, bakamar d'azuba datake cikin tashin hankali.
Ita kanta Anty Zuwairah taga wannan sauyin Na Momy, bata zargi komai arantaba, Dan tunanunta sauk'in data samune.

Wajen around 2 tafito zuwa 6angaren Ammah, afalo ta iske Ammah da Mufeedah, saisu Abashiyya matasu ya sultan, harda su maleeka, hira suketa sha, Amma nabasu labarin zamanin da, kowa yayi mamakin ganin Momy, duk suka gaidata, wani k'arin mamakin ta amsa da sakin fuska, aladabce kuma ta gaida Ammah.
Sai binsu takeyi da kallo Ammah bataga Aysha ba.
"Ammah badai jikin Aysha ya matsanta mataba ko? Naga dukga yaran amma ita babu ita?"..
Cikin shan k'amshi Ammah Tace, " a'a jikinta da sauk'i, tanacan tareda mijinta a 6angarensu, da safennan yazo ya saceta".
Duk falon saida akayi dariya, amma banda Momy dataji kamar Ammah ta soka mata mashi.
Tayi dariyar yak'e "ayya amma, dama meatpia ne namata datacemin tanasonci, kuma ganaku, bara aina aiki hasnah Takai musu".
''A to kin k'yauta gaskiya, sunacan".
Ajiye musu Nasu tayi tafice, babu Wanda yazargi komai suka faraci, sai Santi sukeyi, yayi dad'i, dama Momy ta iya kayan snacks d'innan muguntace kawai Dason jiki ke hanatayi.
Bata zame ko inaba sai 6angarensu ya khaleel.

*******

Sun fito wanka kenan Aysha tace masa yunwa takeji wlhy, Dan harta fara ganin jiri, k'arasawa yayi kusada ita ajikin madubi, ya rungumota tabaya, hannayensa duka nakan cikinta, kansa yad'ora gefen kafad'arta suna kallon juna ta madubi, my sholy kinfa zama consumer, kad'an-kad'an saici".
"Kai sadauki, duk yaufa banci komaiba sai rake, nidai kaje kasamomin abinci acikin gida, ALLAH harna farajin tashin zuciya".
Sumbatar gefen wuyanta yayi, cikin kunnenta yace, " idan naje aikennan nikuma miye tukuycina?, hannu tasaka ta shafo kumatunsa, sannan tad'aga masa gira🤨, saika dawo zaka gani".
"Wata sassanyar dariya yasaki acikin kunnenta, yana shinshinar wuyanta yace, ''yanzu kuwa zan samo abinci, kuma duk kukanki saina kar6i tukuycina".
Baijira cewarta ba yasaketa yafice.
Murmushi Aysha tayi tana binsa da kallo ta madubi, akan la66anta tafirta I love you so much sadaukina, kabani farinci yau d'innan, bakuma zanta6a mantawa da hakanba😊".
Shima abinda yake ayyanawa aransa kenan, fuskarsa d'aukeda murmushi sukayi karo da Momy afalo zaune.
" Momy kece?".
Juyowa tayi ta kalleshi, bak'incikin ganin fusakarsa a farinciki yadaki zuciyarta, amma saita dake, "nine my lovely son, zonan mana, kwana biyu ana fushi da Momy ko?".
Murmushi yayi, yak'arasa gefenta ya zauna tareda d'ora kansa a kafad'arta, yace, ''I miss you momyna".
" miss you 2 my dealing, ykk?".
"Alhmdllh momyn, saidai missing naki danayi, kiyi hak'uri kidaina fushi dani, ranarma sharrin shaid'anne, kinsan banida kamarki duk duniyarnan".
"Karka damu kaji Ibrahim, komai ya wuce, ina d'iyata d'in Aysha".
Kunyace takamashi, yad'an Sosa kansa yana murmushi, da hannu yanuna mata d'aki.
Murmushin yak'e Momy tayi.
Khaleel yace, ''dama zanje cikin gidane samo mata abinci, wai yunwa takeji".
" ayya gama meat pia na kawo muku, dama itace tacemin tanaso jiya, shine nayishi yau, kamaji da zafinsa saika kaimata taci, ni bara naje, Dan zuwairah na shirin tafiya".
Dad'ine ya lullu6e khaleel Dan ganin momy tafara basu kulawa shida matarsa, yamata godiya tafice, shikuma yanufi d'akinsa, tararwa yayi Aysha kwance bakin gado, yunwa tahanata ta6uka komai.
Kwanon tangaran d'in kawai yamika mata, jikinta har rawa yakeyi tatshi zaune, kusan tare suka d'auka, amma tarigashi gutsura, harta fara taunawa tatsaya, waini Sadauki inama kasamo meat pia ne haka? da zafinsa.
Harzai gutsura yatsaya bata amsa, momyce takawoshi yanzu, tace dama jiya kikace mata tamiki". (Acikin d'oki yake gaya mata).
Da sauri Aysha ta furzar dana bakinta, shima tayi saurin ka6e na hannunsa daya gutsura, bayi dasauri, fuskarsa a murtike yace, "k miye haka?".
Hankad'a kwanon Aysha tayi yafad'o k'asa ya tarwatse, Aysha tayi azamar tura hannu cikin bakin khaleel tana kwakulo Wanda ya 6allah, dama ko taunawa bayyiba.
Hankad'ata yayi tabigi gado, bata damuba, tunda tasami nasarar Ciro na bakin nasa.
" waike wane irin iskancine sannan? Uwatafa nace takawo ba uban waniba!!!".
Itama Aysha a tsawace tace, "ko itad'ince takawo bazakacishiba, kasan miye cikinsa?!!! To gubace ta kasheka inbaka sanib...........
Bai bari ta k'arasaba ya d'auketa da mari, ''k!!! Karfa kiga ina wasa dake kiringa kawomin iskanci, kina nufin uwata data tsugunna ta haifenice zata kawo guba tabani naci na mutu!!!!!?".
Hannun Aysha dafe da kuncinta tana kuka tace, " wlhy koda zaka kasheni saina fad'a, nace gubace aciki, bai dameni da matsayin Momy agarekaba, inma bakai tayi nufin kashewaba nitazo kashew........
Da sauri yamatsota, itakuma tamatsa baya, duka takuma kaimata ta kauce, ya wawurita tafice da gudu, shima binta yayi har cikin gida.
Basu zame ko inaba sai 6angaren Ammah, yanda Aysha tashigo aguje yasaka kowa mik'ewa, saiga ya khaleel shima, Ammah ce tayi jarumtar tareshi, sai huci yakeyi tamkar kurar daji.
Aysha da bakinta bai mutuba, saboda rud'ewar datayi, cikin kuka takuma fad'in wlhy koda zaka kasheni yau agidannan saina fad'a, gubace Momy tabamu muci a meat pia muci mu mutu, idankuma bahaka baneba tazo ta gardama mana.......
Kuma yunk'urowa yayi kanta, baffah daya shigo yanzu yay saurin rik'eshi, dandanan 6angaren Ammah yacika daduk Ahalin gidan.
Daga Aysha har ya khaleel sunkasa nutsuwar da za'a tambayesu, sai Aysha daketa fad'in ko khaleel zai kasheta saita fad'a guba Momy tabasu suci su mutu,

Please Login or Register in order to submit comment