Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwantaccen sajensa zuwa baki.
Sakina dai atsorace take sosai, tunda take bata ta6a ganin bindiga ido da ido hakaba, saidai ta 'yan sanda, itama daga nesane.
Kusan mintuna biyu baisake cewa komaiba, sai zuwa can yajeho mata tambayar data gama rikita dukkan illahirin halittar jikinta.
"Hakan yana nufin basu yarda dakeba kenan kema? Dukda tsawon shekaru Biyar dakika d'auka kina aiki agidan? Shin wacecema talatuwa agidan?".
Tsoro, razana, kad'awar ciki data zuciya duk suka riski sakina lokaci d'aya, takasa cewa komai, sai zufa dake keto mata takowacce ga6ar jikinta.
Cikin daka tsawa yace, "nace wacece talatuwa agidan dakike aiki?!!".
"yalla6ai fad'ata tamkar salwantar rayuwatane narantse maka, sannan bansan miyasa basu yarda dani d'inba".
Wani murmushin k'asaita yayi, tareda fad'in ''dak'yau yarinya, anzo wajen".
"Ki fad'amin, kokuma kafin ki koma wajensu su kasheki, ni zansaka alburushin bindigata acikin kanki, saidai akai musu gawarki su tambayeta".
Hawaye masu zafi suka fara zarya akumatun sakina, tace, " yalla6ai zan fad'a maka, amma Dan ALLAH karufamin asiri karkace nina fad'a".
Kansa ya jinjina mata yana lumshe idanu, amma baice komaiba.
Tace, "shekaruna kusan biyar ina aiki agidan, lokacin da'aka kawoni banwuci 14 ba, kuma talatuwace ta d'akkoni daga k'auyenmu Na boza a fika Local Government, jihar yobe, mahaifina da hannunsa yabadani wajenta, bayan tabashi mak'udan kud'ad'e, ina kuka mahaifiyata Na kuka aka taho dani. Koda aka kawoni Abuja wani gida aka kaini, agidan akwai 'yan mata dayawa, k'anana da manya, kuma kowanne irin yare dake Nigerian zaka samu, hardama 'yan Niger dawasu k'asashe makwaftan Nigeria, banfahimci abinda yatara wad'annan mata agidanba aka d'akkoni aka dawo dani gidan Alhaji mustapha, nikaina bansan dalilin yin hakanba, amma daga nanne nacigaba da aiki agidan, Alhaji mustapha ba mazauni baneba, shiyyasa gidansa yazama k'ark'ashin mulkin matarsa, dukda dai nakanji masu gidan sukan tattauna akan hajia khaltum tanada kishiya, kuma alhaji mustapha yafi zama a can, yalla6ai satar amsa 1 zan baka, nasan kaid'in kwararrene Dan nakanji firarka awajen yaran gidan, suna yawan yabama kwazonka saboda soyayyar da baby take maka".
Da Sauri ya khaleel yataso daga jikin kujerar, ''kinga fad'amin wace satar amsace?, bar batun wancan shirmen".
Sakina ta jinjina kanta tace, " yalla6ai mafi yawancin masu zuwa gidan wajen hajia khaltum, namiji ko mace zaka samesu dawani tambarin hoton tarttu na 🦂kunama a damtsen hannunsu Na haggu, tabbas wannan shine tambarinsu, wannan kawai Na iya fahimta tartare dasu yalla6ai, wlhy iya gaskiyata nafad'a maka, Dan ALLAH karka kasheni, kuma karkace Nina fad'a".

Kwantar da hankalinki, zansa a maidaki yanda bazasu fahimci komaiba, da sauri yad'auki ☎waya yayi kiran office d'in Mahfouz da Basheer.
Babu dad'ewa saigasu sunzo kusan atare, saida suka k'ame, tareda salute nashi, sannan ya khaleel yace, "Mahfouz! Amaida yarinyarnan, amma yanda za'a iya fahimtar saceta akayi".
"OK sir"
"Kibishi kuje, inhar ina buk'atar k'arin bayani zansa akuma d'akkomin ke".
''To yalla6ai ngd, tayi maganar tana hawaye, Dan bata fatan akuma kawota wannan wajen".
Saida aka d'aure idonta kamar yanda aka kawota sannan aka fita da ita.
Ya khaleel yamaida hankalinsa akan Basheer dake zaune, ''Basheer ina buk'atar hotunan gawar David".
" OK sir!, bara na kawo, amma akwai Na binciken k'arshe da akayi suna hannun Oga Joseph ".
Jin jina kai khaleel yayi, yakira Joseph akan yakawo masa file d'in binciken mutuwar David.
Babu dad'ewa saiga Joseph ya iso, kar6a khaleel yayi yafara bincike, zuwa can yad'auki wani hoto da David ke shinfid'e a table doctors nata aikinsu akan gawar, damtsen 💪🏻hannunsa ya khaleel ya kalla, cikin zare ido yace, "Joseph hoton miye wannan?".
Kar6ar picture d'in yayi yana kallo, sir! Inhar hasashena yayi dai-dai wannan kunama ce🦂, dukada ba'a gani dak'yau".
Da sauri ya khaleel yamik'e yana fad'in Joseph inason ganin gawar David yanzunnan.
" OK sir!, idan ka shirya saimuje".

Cikin takunsa Na jarumta da isa yake tafiya, yanayinshi kawai zaka kalla kagane ransa a 6ace yake, sunshiga inda akan ajiye gawawwakin wad'anda wahala tasakasu mutuwa, ko aka kashesu, kokumadai Abu mai muhimmanci yasaka aka ajiye gawar tasu, Dan ayi bincike akanta.
Ma aikatan wajen sai k'amewa sukeyi, kasancewar suma police ne, amma likitoci.
Bakai tsaye su ya khaleel suka shiga wajenba, saida aka basu wata Riga suka saka, suka rufe dukkan jikinsu👨🏻‍🚀, har hannayensu da hanci sannan suka shiga, doctor Sadam mai bincike akan gawar David yabud'e abinda aka lullu6eshi, bayan anjawo gawar daga cikin wani glass, fitulu aka kunna saitin gawar David.
Doctor Sadam yabama khaleel wata fitila mai haske🔦, suna haska damtsen hannun David Na haggu saiga hoton kunama🦂.
Hoton wajen Joseph ya d'auka har sau biyu sannan suka fito.
Ahanya khaleel kecema Joseph, ''wato da muna aikine a birkice, ko kad'an mun Gaza samun bakin zaren matsalarmu sai a yau, tabbas akwai masu laifin dake da alak'a da juna a setetion d'innan, amma wad'anda suka kashe David basusan wannan sirrinba, mu kanmu bamusan da hakanba, wannan tambarin kunamar yana nufin tambarin wata k'ungiyane kenan?".
Maganarka gaskiyace sir, amma ya akayi kagane wannan tambarin kunamar?".
Ya khaleel bai bashi amsaba har suka k'arasa office d'insa, yacema Joseph kiramin Taheer, youseef. Adams, & Solomon".
☎duk yagama kiransu cikin mintuna k'alilan.
Babu dad'ewa saigasu sunzo.
Yana shan shayin daya had'a suka shigo, kowa yazo saiyayi gaisuwa sannan ya zauna, kowa yayi shiru yana sauraren boss.
Khaleel yamik'e hannunsa d'aukeda mug d'in tea yanasha a hankali, idonsa a kansu, "kunsan dalilin kiranku?".
Atare sukace a'a sir!.
Remote yad'auka, ya danna TV d'in office d'in, saiga hoton kunamar dasuka d'akko ajikin gawar David, "wannan kunamarce, ita wannan kunamar takasance tambarin nawata k'ungiya, kuma nasameta ajikin David, ranar Taheer kasanarmin kana zargin alak'a tsakanin David da barau modibbo ko?, to yanzu inason abinciki wannan kunamar ajikinsa, bama shi kad'aiba, harda duk wasu criminal's da ake zarginsu da safarar miyagun kwayoyi kamar David, sannan David yana safarar yara shima, kenan dukmai alak'a dashi akan bigire d'aya suke?".
"Zamu gudanar da aikinmu da lura, shiyyasa Na taraku kud'in amintattuna, bana buk'atar asaka wasu yara a aikin, dakanmu zamuyi, saboda akwai magoya bayan su David acikinmu, wannan ne yasakasu kasheshi dankar yafad'a mana komai".
Gaba d'ayansu suka jinjina kai.
Adams yace, " sir!, aikuwa akwai wannan hoton kunamar a hannun Moxies".
"Da gaske"?.
" am telling you sir".
"Kenan Moxies yanada alak'a da David?".
" zamu iya cewa hakan".
To inkuwa hakane, Ku bincikamin Ruth da aka kama da yara a air port zataje Dubai, sannan Solomon miye labari gameda bincike Dana sakaku akan email d'in sirri da'aka turo sunayen su Ruth aciki?".
Sorry sir, munata k'ok'ari, amma gaskiya mai email d'in mutumne mai wayo, Dan saida yabi matakan Kare kai daga binciken kwankwanto kafin yafara aikinsa, kuma tabbas yasan computer sosai, inhar ba k'arya zan makaba zan iya cewa bamu samo komai game dashiba, saidai kuma yin maganar kunama mai tambarin k'ungiya yatunamin dawani Abu, tabbas mai email d'in yasan wani Abu dangane da wannan k'ungiyar, domin duk sak'on dazai turo akwai hoton k'aramar kunama da bindiga kusada ita, bara kaganai". 'Solomon yay maganar yana bud'e laptop d'insa, mik'ewa yayi yay connecting da TV d'in office d'in, tana gama searching saiga jerin sakwannin mai email d'in sirri, acan gefe mak'ale kunamar take, 🦂🔫, sannan an nuna kunamar da bindiga.
Huci mai zafi ya khaleel ya furzar daga bakinsa, ya ajiye kofin hannunsa tareda matsawa jikin tvn, nazarin komai yakeyi cikin kwarewar aiki, saikuma ya jinjina kansa, yajuyo yana kallonsu youseef, ajerin sunayen damai email d'in yaturo guda biyar, macece ta uku, kuma yabamu tabbacin zata sauka Nigeria aranar 17-ga watan 4, watan dazamu Shiga kenan, zata tasone daga k'asar Malawi, ta sauka Dar es salaam, babban birnin Tanzania, washe garine zata k'araso Nigeria. Jirginta zai sauka a Kano state ne, daganan yabamu za6in kamata a Kano, kokuma a Abuja, acewarsa wannan yarage namu, shi yagama nasa".
Gaba d'ayansu sunyi shiru, kowa da abinda yake tunani, ya khaleel yakatse shirunsu dafad'i "so ina jinjina kwakwalwar mai email d'innan, koda criminal ne shi tabbas yanada kwakwalwa, kamar yanda yabamu satar amsa akan kama Moxies haka yabamu akan wannan matar, saidai bazamu saki jiki kai tsaye da bayaninsaba, saboda tsaro".
Youseef, kaida taheer Ku tattaramin bayanin David, da Moxies awaje d'aya, tunda sunada alak'a da juna, Joseph kaida Faruk da Mahfouz kucigaba da bincikamin Duk wani mai wannan tambarin dake a setesion d'innan, Solomon kanemi su Kausar acigaba da bibiyar mai email d'in sirrinnan, nasan dolene watarana yayi kuskuren dazamu samu wani bayani akansa".
"Nida Adams da Samuel Zamu cigaba da farauta".
" komai yazama da kula, banason kuskure kuma kunsani, duk Wanda yamin wasa da hankali acikinku koyaci amanata wlhy dakaina zan fasa kwakwalwarsa da bullet, koda kuwa cikinsu youseef".
Ku kula da k'yau, Adams ina buk'atar Ak'ilu Abbas agabana yanzunnan, kukuma zaku iya tafiya".
Atare suka mik'e baki d'aya, duk sukayi salutes d'insa, murtani ya maida musu, sannan yakoma kujerarsa ya zauna, sukuma duk suka fice.



___________________________

"Aminiya agarin Yaya kikayi sakaci baici maganinnanba?, anya kuwa kinsan bala'in dake tinkaromu?, kekankifa kinama cikin saka idanun k'ungiya, dansu gano cewa Ibraheem d'ankine, kuma shine yake mana tsinci d'ai-d'ai, k'ungiya ta bada date d'in daza'ayi zama Na musamman domin Ibrahim kai tsaye, Alhmdllh munsami damar ku6tar da talatuwa daga hannun police, Dan munyi gamo da d,p,o kwad'ayayye, yanzu haka talatuwa Na gida".
"Alhmdllh, naji dad'in hakan, sannan karki damu aminiya rashin cinsa bashi yake nuna ya tsiraba, Dan nakafa masa wani tarkon ma, k'ungiya kuma zan fahimtar dakowa komai kai tsaye, Dan banason d'ana yafuskanci wani Abu daban, inasonsa fiyeda tunanin mai hakali".
" tsaki kawai hajia khaltum tayi, amma batace komaiba".
Hajia babba tace, "aminiya zan kashe matar Ibrahim".
" miyasa? aminiya, ita mitamiki?".
"Kinsani aii".
Dariya hajia khaltum tayi, tace, " bazan hanakiba aminiya, dama a k'ungiyance kisa yarinyar ya cancanta agareta, saboda gudun tonuwar asirinmu, dannasan wani daga cikin sirrinmu. Damacan ina shirya abubuwa akanta tuni, sonake sai mungano Inda meerah take, kisan Aysha tamkar munkashe macijine bamu sare kansaba, inhar meerah Na numfashi a duniya, wannan ne dalilin dayasa nabar Aysha bansake waiwayartaba".
"Shikenan aminiya nabar komai a hannunki".

Aysha dake bayan windown hajia babba tazaro ido, danjin maganar su momy, dasauri tabar wajan tana sauke numfashi, tabbas maganar su tadaki zuciyarta, amma bata tsorataba, haka takoma 6angarensu tana juya maganganunsu, takira Anty meerah ta zayyane mata komai.
" lil sholy kibani kwanaki biyu zanyi tunani, kema kiyi tunanin mafita saimu had'a tunaninmu waje d'aya muga miya dace muyi".
"Shikenan Anty meerah babu damuwa".
Yauwa ki kwantar da hankalinki, insha ALLAH babu abinda zai cutar damu, kisa aranki *_CIKI DA GASKIYA..._* wuk'a bata hudashi da yardar ALLAH".
" To Anty meerah ngd".
"Aha saimunyi waya".

Bayan Aysha ta yanke wayar takwanta taci kukanta, da mamakin hatsabibanci irinna momy da hajia khaltum, lallai tasan zukatansu sun gama bushewa.
Dama dawowarta daga aiki kenan, driver ya ajiyeta saiga hajia khaltum, shinefa tabi bayanta ta mak'ale ta window hartajiyo abinda suke tattaunawa.
Saida tagaji da tunane-tunane sannan tatshi tayi wanka, kichin tashiga ta tanadarma ya khaleel abinci kafin yadawo, dukda batada tabbacin zai shigo gidan dawuri, tunda wani lokacin yakan kai 10 Na dare a office ma.


_______________________
A d'arare Ak'ilu Abbas yashigo office d'in, shima sanye yake da uniform na police Interpol, saida ya k'ame tareda salute d'in khaleel sannan yabashi izinin zama.
Ya khaleel yad'ago manyan idanunsa ya sauke akan Ak'ilu Abbas, shikuma saiyayi k'asa da nasa idon, Dan mara gaskiya baya iya kallon ya khaleel ido cikin ido.
Murmushi ya khaleel yayi, yajawo iPad d'insa yamik'ama Ak'ilu Abbas.
Kar6a yayi cikeda mamakin mizaiyi da itane?.
"Nasan kana mamakin mizakayi da ita ko?, akwai game aciki, kuma shikad'aine, inaso kaje kayishi, iya inda kasamu game over kakawo min, idankuma kawuce abinda kasamu har sau uku to zan gane zaka iya tafiya".
Cikin rawar murya Ak'ilu Abbas yace, " sir? Nikuma miye had'ina da game?".
''Basai kasaniba, banason yawan surutu jeka".
Duk Ak'ilu Abbas ya rikice, baisan dalilin yin hakanba gareshi, tabbas yasan wanene j!, kuma baya Abu saida manufa.
Koda yak'arasa office d'insu su kusan 20 aciki, sai yake gayama abokinsa wanda sukafi shak'uwa.
"Tab wlhy Ak'ilu kashiga tarkon Oga kawai, shiyyasa naita kwa6arka al0kacin amma kak'i, yanzu wa gari ya waya".
" please Sha'aibu kabani shawara mana".
"Yoni shawarar mizan Baka?, kayi abinda yace kawai".
Shiru Ak'ilu Abbas yayi, Dan yasan shi'aibu ma mutumne mai gaskiya, aransa yace shikenan nashiga uku nikuma, anbani kud'i Na aikata abinda zaiyi sanadin k'ask'antuwata, gashima kud'in harsun zama labari, tunda naje karuwai sun cinye .............✍🏿



Nidai nace, " hummm".



*_Ayya my sweet Xoxo, ALLAH yabaki lafiya, yasa kaffarane, yatashi kafad'a, fan's Ku had'o kayan dubiya tawan babu lafiya😞._*


*_Typing📲_*



🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_



*_part 2_*
(littafi na biyu📕)


2⃣9⃣

Akwana atashi babu wahala awajen ALLAH, kwanaki nata gudu lamarin tamkar k'yaftawar idanu, kamar wasa saikaga seconds sunkoma minutes, minutes sunkoma hours, hours sunkoma day's, days sunkoma weeks, weeks sunkoma months, months sunkoma years, baka fargaba saikaga kanka amatsayin gawa😭. Da d'an Adam yana tunawa akwai k'alubalen mutuwa agabansa dabai aikata wata 6arnarba, hummm kunsan wani abu kuwa?, (wlhy dayawanmu gani muke bazamu mut yanzuba, dukda munsan tabbas mutuwa gaskiyace, Dan inba'a d'auki mamankaba, and'auki babanka, ko yayanka, ko k'anwarka, ko mijinki, ko mataraka, ko k'awarki, ko makwafciyarki, amma lokacin da'akayi mutuwarne kawai zakiga hankalinmu yatashi, kwanaki k'alilan zamu koma dukkan ayyukanmu, wani gani yakeyi shifa k'aramine mutuwa bazata d'aukeshiba yanzu), kai👉🏻🧕🏻👳🏻‍♀d'an adamu wanene kai?, mikake tak'ama dashi?, karinga tunawa mutuwa tana d'aukar d'a acikin uwarsa👉🏻🤰🏻, tana d'aukar jariri a hannun uwarsa👉🏻🤱🏻, tana d'aukar yaro d'an shekara 1👉🏻🙇‍♀tana d'aukar masu shekaru biyu👉🏻👫, tana d'aukar budurwa ko saurayi masuji da tashen lokacin k'uruciya👉🏻🙎🏻‍♂🙍🏻‍♀, tana d'aukar magidanci. Mai fafutukar Kare martabar iyalinsa wajen cigar dasu da tufatar dasu👉🏻👨🏻, tad'auki miji gaban matarsa, 'Yaya gaban iyayensu, uba gaban 'ya'yansa, bazatabar tsohoba komin tsufarsa👉🏻🧔🏼, Duk k'arfin mulkin mai sarauta saita d'auka👉🏻🤴🏻, duk yawan dukiyar attajiri da alfarmarsa saiya tafi, Duk iskancin d'an iska koyakai shaid'an 👹tantiranci wajen bijirema ALLAH sai anshafe tarihinsa watarana.
Shin miyakaika shagala yakai bawa?, miyasaka mantawa da k'alubalen mutuwa?, miyasa? duniya da kayan cikinta sukafi tasirantuwa azuciyarka fiyeda tunawa kwanciyar kabari daranar hisabi, ranarda kowa aikinsane makaminsa, wane rud'in shaid'anne ke d'awainiya dakai har kakasa jin kunyar ubangijinka daya halicceka danka bauta masa kake aikata zina agabansa, kake shaye-shaye agabansa, kake luwad'i agabansa, kake mad'igo agabansa, kake sata agabansa, kake bin bokaye agabansa, kake cutar da d'an uwanka saboda ALLAH yabaka wata dama ta mulki ko k'arfin iko, miyasa yakai bawa?, shin baka tsoron randa za'a shiryo rundunar mala'iku domin kar6ar ranka?, aranarfa aikinkane kawai guzurinka?, anya kuwa bawa yana k'iyasta kansa amatsayin gawa idan yanutsu, kokayi wannan tunanin, kobakayiba wlhy billahi saika mutu👉🏻😭😭😭.



________________________________
Bikinsu Amal nata matsowa, gaba d'aya yau saura kwanaki 6 kacal d'aurin aure, kusan zan iya cewa duk masu aikin gidan da 'yammata harda matansu sultan dasu mama duk suna kichin, chin-chin d'in gara dakuma rabo akeyi.
Aysha ce kawai babu awajen, tana d'akin Anty Mamie kwance, yau kusan satinta d'aya kenan, Dan ya khaleel yayi tafiya zuwa France tun last week, shine yace tadawo d'akin Anty Mamie harsai yadawo.
Kusan kwanakinta uku kenan batajin dad'i, k'irjinta namata ciwo, dauriya kawai takeyi bataso kowa yagane.
Wajen aikin chin-chin d'inma hartaje takasa zama saboda jiri datake gani kad'an-kad'an.
Batacewa kowa komaiba tazaro jiki tadawo d'aki, kwance take shiru tana tunanin ya khaleel, tunda yatafi sau hud'u kacal sukayi waya, ko kiransa tayi saiyace aiki yakeyi, lamarin ya khaleel Na damunta wlhy, ita yanda take karanta novels taga mazan ciki Na tattalin matansu, harma sukan manta da ayyukansu, duk motsinsu yana gidansu, soyayya kaga harta fitar hankali, catake haka zata dinga gani ga ya khaleel, amma yayinda ta auresa saitaga sa6anin hakan, dai-dai gwargwado yana nuna mata kulawa da soyayya, saidai batakai ko rabin wadda ake nunama matan novels ba, shin ko ita bata iya tattalin miji baneba kamarsu? To amma ai matan novels ma girki, iya kwalliya, tsafta, kusan shine sukema mazajen, itama duk tanama mijintashi, hardama biyayya, wadda take ganin mafi yawan matan novels basuda ita, (hummm indai hasashenta gaskiya ne to tabbas zata iya cewa irin wannan mahaukaciyar soyayyar da miji kan nuna ga matarsa, harkiga yana mata kuka to sai'a novels, saboda k'arancin samun irin wannan soyayyar a gidajenmu yasaka mata raja'a wajen karanta hikayoyin marubuta, musamman ma buk na batsa, Dan suna kallon hakan amatsayin soyayya, mukuma yawanci bama samun irin wannan soyayya agidajenmu) "ya ALLAH ka gyara gidajen auranmu", Aysha tafad'a tana share hawaye.
Wayarta tajawo ta dialing d'in number ya khaleel ta France, harta tsinke bai d'agaba, saida takira sau biyu. Ana uku harta kusa katsewa sannan yad'auka.
Cikin dauriya tace, "Assalamu alaika".
Ya amsa yana fad'in "o, nayi laifi fa, jiya nace zan kiraki ban kiraba, amin afuwa aikine wlhy A'eesha".
Danne zuciyarta tayi tace, " babu komai sadauki, Na fahimceka, ya aikin?".
Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke, yakuma jingina sosai da kujerar motar tareda lumshe ido, yace, "Alhmdllh, ngd sosai dakike fahimtata akowane lokaci, haka akeson mace tazama maima mijinta uzuri, Dan itadama rayuwar aure tagaji hak'urine kawai, bakomai ake nema asamu 100% ba".
Aysha tace, " hakane".
"Yauwa ya shirin biki?".
''Gashinan anatayi, duk sunacanma suna chin-chin".
"Tofa, kekuma kina ina".
" ina d'aki kwance, wlhy haka kawai naji inajin d'an jiri, bansan daliliba, amma yanzu yadaina".
"Sholyna kodai asibiti zakije?".
" lah karfa ka damu, wlhy da sauk'i, yanzuma zan koma wajen aiki, yaushe zaka dawo".
"Tom ALLAH yak'ara afuwa, Indai kinji bai tafiba karkiyi shiru, kifad'ama Anty Mamie kuje asibiti, Nima insha ALLAH zuwa nanda 4days zandawo k'asar".
"anafa jibi d'aurin aure kenan?".
"Eh, insha ALLAH, ko kina kewatane?".
Cikin shagwa6a tace, " wlhy sosaima kuwa".
"Humyim, karfa nadawo kice kuma Na gundureki".
"ni wlhy babu waninan, kadawo please ".
Guntun murmushi yasaki, yayinda shagwa6arta ke rura masa wata kasala mai kashe jiki da sanya jini gudu da sauri, muryarsa can k'asan mak'oshi yace, " my sholy karki kasheni da salonkifa, kinga bana kusadake, please karki saka sadaukinki cikin wani hali kinji".
Dad'ine Yakama Aysha, tasaki siririyar dariyar data kuma narkar dashi, aii babu shiri ya Yanke wayar gaba d'aya, yay saurin kifa kansa jikin sitiyari yana sauke numfashi a hankali, tabbas Aysha dabance wlhy, yafad'a cikin furzar da iska daga bakinsa, kashe AC d'in mortar yayi, danshima k'ara sakashi kasala yakeyi, dajin buk'atuwar kasancewa da matarsa.

Aysha ko yana kashe wayar ta tuntsure da dariya, dama da gayya tayi, wai itama sotake tagwada Na matan novels tagani zaiyi tasiri, dad'i kamar zai kasheta, sai juye-juye takeyi agadon ("kai dagaskefa marubutannan suna fad'akar damu wlhy, infa zaka d'auki Abu mai k'yau kagwada ga mijinka zakaga kana canjashi kamar mijinki novels, Kodai bazai lalace akankaba kamar mazan novels to zaka samu farinciki kaima) aii idan akace matar novels tayi wanka sau uku Arana, kekuma saiki kamanta yin biyu, (suma marubutan suna saka hakane Dan ka kamanta ba dole sai d'in kayi kamar ta novel ba, idan sunce 1 akayi, kekuma wataran bazakiyi d'ayan bama, abunda yasa bama amfanuwa da abinda marubuta suka rubuta, saboda muna karanta books d'inne dan kawai nishad'i, burinmu muji soyayya ruwa-ruwa, matsa can kamacan, badukanmune Muke maida hankali wajen fahimtar wane sak'o writer suke son isarwa a buks d'insuba, soyayyarce kawai damuwarmu, amma bamabin matakan mizamuyi musami soyayyar muma agidajenmu, wata Indai ta karanta labarinki yasakata dariya ko haushi anan zata kakka6ar miki da kayanki, bazata amfanu da komaiba, kota gwada danta samu mafita agidanta ko cikin al'ummar datatsinci kantaba, nikam danayi wannan asarar 6ata lokacin, aigarama ace ban karantaba wlhy).
(Yakamata dai reader's sudinga fahimtar writers bamuyita wahalar banza da asarar data ba, ALLAH yasa nun fahimta).


____________________________

Momy madai tanata shirya d'iyarta mufeedah, daka shiga 6angarenta kasan ana bikin 'Yar gata, danma babu Anty zuwairah, Dan baffah yahanata zuwa gidan kusan harna

Please Login or Register in order to submit comment