Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aurennan da Momy tatasoshi gaba akansa, yanzu haka yauma saida tace yaje ya d'akko Aleeya idan ta sauka a airport, da to kawai ya amsa mata, amma bayajin akwai yarinyar data Isa ya6ata lokacinsa wajen wani tarbarta, yaja siririn tsaki Wanda har saida Adams yajuyo ya kalleshi, yana mamakin miya saka boss tsaki haka?.
Babu dad'ewa suka iso setetion d'in nasu, nanfa aka Shiga gaisheshi damasa murnar aure, shikuma yana musu godiya da halartar dasukayi.
Duk saida yashiga office's d'in oganninsa yakai gaisuwa, sannan yadawo nashi, shima wad'anda suke k'asa dashi suka shiga zaryar zuwa gaidashi, dakawo masa aiyukan dasukayi bayan baya nan.
Aiki kam ya iskeshi jingim, damma su youseef nayin wad'ansu.
Su Joseph ma sunshigo sunyi gaisuwa amatsayinsa Na ogansu.
Kowanne yakawo masa aikin dayayi dawanda suke kai, sosai yau aiki ya rinca6e masa, gaba d'aya yagaza samun kansa.
Wajen 12:30mp yaji shigowar sak'o a familie phone nasa, baibi takan massage d'inba, saboda aikin dake gabansa.
Zuwacan kuma sai kira yashigo, nanma bai d'agaba, saida aka kira kusan 3times bai d'aukaba, daganan aka daina kira.
Nock d'in k'ofar office d'in akayi. Yabada izinin shigowa, Basheer ne wani ma'aikacinsu, ya k'ame tareda salute Na khaleel.
Kansa ya jinjina masa sannan yanuna masa kujera alamun ya zauna.
Basheer ya zauna a kujerar dake kallon ya khaleel, sannan yamik'a masa wasu files dake hannunsa.
"Sir ga bayanan damuka samu akansu, wannan kuma sunayen mutane 17 ne damuka kama acikinsu, akwai 13 anan setetion d'in, saikuma 3 a hannun police, 1 yana hannun hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyi".
"OK, yakar6i files d'in yana dubawa, saida yagama tsaf yad'ago yana kallon basheer, "wanene Dr Sageer!?".
"shine likitan da aka kama Na Osun d'innan, Wanda ake zarginsa da saida kwayoyi ta asibintinsa, amma ya tabbatar mana bashi kad'ai baneba a bayanansa, hukuma sha da fataucin miyagun kwayoyi tana bincike akan sauran mutanensa".
"Kukuma kuna aikinmi? Kuna zaune kawai kuna jiran su kawo muku bayanai kenan?".
" a...a'a sir, Bahaka baneba".
"To yayane? Bansan miyasa kuke sakaci akan aikinkuba, kunada damar kwatar cases a hannun kowace hukuma idan kukaga tanada rauni wajen hukunta mai laifi, amma saiku zuba idanu yayinda aikin had'aka yashiga hannunku, ni narasa mike damun tunaninku?, shin kunada tabbacin za'a hukuntasu yanda yakamata acand'in? Shiyyasa kullum muna aiki amma bamu samun alk'aluman cigaban wahalarmu, idan muka toshe can saikaga can ya 6alle, sakacinkune kuma kejamana wannan fad'uwar tasar".
Sorry sir, insha ALLAH za'a gyara".
" zancen kenan kullum, za'a gyara za'a gyara, amma haryanzun gyaran baizoba, haka za'a gama yayinmu bamukawo wani sauyiba a k'asarmu kan 'yan ta'adda, muwuce wasuma suzo Suyi tsarinsu suwuce, haka-hakadai kullum k'asa nak'ara ta6ar6arewa da lalacewa, mtsoowww aikin banza kawai".
"Basheer dai yanata bada hak'uri".
files biyu ya khaleel yamik'a masa bayan yasaka hannun, kakai wad'annan office d'in Taheer, wad'annan kuma yasaka hannu kakaima Mahfouz su".
" OK sir, thanks you sir".
Kansa kawai ya jinjina masa, yajanyolaptop d'insa yacigaba da aiki, shikuma basheer yafice, yanamai jin k'auna da sha'awar halayen Ibraheem Abdallah j!, yana addu'ar ALLAH yabashi ikon yin koyi dashi..
Dan bakowa keda makamancin k'yak'k'yawan hali irin nasaba, nason a gyara k'asa, musamman masu girman matsayi irin nasa, da Wanda suka fishi, harma da wad'anda basu kaishiba.


*******
Kiran wayarsa da'aka k'arayine yasakashi yin k'aramin tsaki, batareda yaduba mai kiranba ya d'auka yasaka a kunne yanayin sallama, yayinda hankalinsa kenan aiki a laptop.

"Ibraheem Aleeya ta saukafa, tace tanata kiran wayarka Baka amsaba".
" wlhy Momy aiki yamin yawa a office, please ki aika driver ya d'akkota mana, kokuma cikinsu Muhseen idan wani yana gida yaje ya d'akkota".
''ni babu wasu su muhseen dazan saka, dadai zaka daure saikaje ka d'akkota minti nawane kwata-kwata".
"Hummm Momy bazaki baneba wlhy, kinganni kuwa a office?, yanzu haka sallah nakeson natashi nayi nadawo kan aikina, kisankusa kwanaki goma bana office, please amin afuwa Dan ALLAH driver ya d'akkota".
Shikenan bara nama driver magana, sai suje da 'yan biyu".
OK saina shigoto, baijira cewartaba ya yanke wayar yana mita.
"kajiminfa Momy dawani zance, ita hartakai Isar dazanje airport d'aukarta, haba saikace wani lusari, mtsoww, wlhy kemafa Momy kinada matsala, haba kullum zance d'aya, yay maganar yana mik'ewa saboda Kiran sallah da akayi Na azhur.
Wayar yad'auka yaduba number data kirasan, saiyaga harda miss call d'in Aysha, itacema tafara kira, saikuma Na Aleeya guda biyu.
Kansa yadafe, Dan baiyi tunanin kiran nataba, yama manta yanada number ta, yakar6ane wajen mama tun lokacin gabatowar bikinsu data tafi Kano, tunda yakar6i number ma baita6a kirantaba, ita kanta ayshan batasan yanada number d'intaba.
Massage d'in da'aka turo yaduba Dan ganin number ayshane.

_"Sadaukina ya aikin?, kakasance cikin farinciki da kwazon aiki irinnan gwarazan sadaukai mijina"._
*_Sholynka Ce_*😘

Murmushin dabai niyyaba ya su6uce masa, yakuma maimaita massege d'in, aransa yana jinjina baiwar Aysha, gata 'Yar k'arama sai wayon tsiya.
Masallaci yafice Dan gabatar da sallah.

Bayan idar da sallah suka had'u dasu taheer. Cikin tsokana Taheer yace, "kai alhaji kaga kuwa k'yawun daka k'ara? Lallai ango kana kwasar amarci yasin".
" mtsooww! ALLAH ya shiryeka Taheer, kaidai bazaka ta6a canjawaba ko? To dan k'aniyarka muni kakeso Na k'ara saboda nayi aure?".
Cikin dariyar shak'iyanci youseef yace, "A'a bak'inciki yakeson maka, k'ilan soyay kadawo aiki wujiga-wujiga ko? Katina lokacin daya dawo hutun angwanci, ALLAH Taheer harwani yallew-yallew yakeyi saboda gara daya kwas.........."
.......Bai k'arasaba taheer yakai masa rankwanshi.......
Youseef yamatsa yana dariya. "Kai Malam ALLAH ka rankwasheni ramawa zanyi, koka manta Na girmeka tunda narigaka aure?".
"To uban 'yansan girma, munji karigamu aure saime to? abinda kake tak'amar kasani mumadai yanzu mun sanshi koko Taheer?".
" A'a j bakada bakin maganama kaikam, tunda kaine auta acikinmu".
"Kuttt ammafa ka sameni, d'an iska zan ramane, nakula tonon silili zakamin cikin yara, bara nawuce office aiki nacan jingim yana jirana, ni dama banje wannan hutuba".
" hhhh tab wlhy ganganne, muzaka saka a kwali, kagama dirzar amarci da young girl d'inka kazo kanawani daddojewa🀣".
"Banza d'an iska banida lokacinka, kagama tafiyata", 'ya khaleel yay maganar yana barin wajen, fuskarsa d'aukeda murmushin iskancin da youseef kemasa'.
Suma dariya sukayi, youseef ya kalli taheer, "d'an uwa Alhmdllh, kagafa j yasamu kwanciyar hankali wlhy, gaskiya Na yarda aure na k'arama mutum daraja arayuwa".
"Hakane youseef, kagadai kamar wasa duk munzama masu iyali, ga matarka harda ciki, kai Alhaji kaimafa shegen samane, kafayi aiki alkur'an".
"A, yoni Na wasane aka gaya maka?, inagamafa matar Joseph itama takamu, dan jiya nakirasa yakecemin sunje Asibiti madam babu lfy, nikuma d'an mutuncin bansake kiraba, gashi yau tun safe sukatafi Zamfara shidasu Zakariyya".
"ALLAH ya inganta mana to, baka saniba, dolece tasaka Joseph zuwa Zamfara d'innan wlhy, dan babu yanda zai kaucene".
"aini tunda naji jiya j yayi maganar naketa addu'a kar sunana yafito amasu zuwannan wlhy, haka kawai, bakagama amarciba asambad'aka daji".
"Hhhhh wlhy kaji haushi taheer, aikam saina zugashi ansaka sunanka a masu zuwa Lagos insha ALLAH".
" munafiki basai kabadaba".
Cikin dariya youseef yabar wajen, dan yasan Taheer ya shak'a.πŸ˜†.lol.



Sai kusan 6 ya khaleel yadawo gidan, yaukam motocin har cikin gida suka shigo, saboda sun saka mai gadi suma.
Kamar yanda aka saba Adams yarakoshi da kayansa har barandar 6angarensu.
Anan ya kar6a, "uhmm Adams inagafa yau munada fitar dare gaskiya, dan d'an iskannan Moxies ancemin yana 9ja, nagane club d'in dayake zuwa, tom inaga dolene daren yau mu ziyarci club d'in, ni da kai kawai zamuje, saimunga yanda wajen yake sannan inma muna buk'atar wasu saisuzo, tunda bamusan yawan yaransaba da mabiya, so ka sanarma su Samuel, suzama cikin shiri".
"OK sir ALLAH ya kaimu daren, amik'amin gaisuwa wajen antynmu".
" Zataji tunda dai kak'i zuwa ka gaidata".
" ayi hak'uri boss insha ALLAH Wannan weekend d'in zan shigo".
" ALLAH yasa to".
Sukayi sallam ya khaleel yashiga ciki.
Babu kowa a falon. Saidai yanata tashin k'amshi, ko INA k'al-k'al yake, yayinda karatun alkur'ani ke tashi cikin sifikun, wata nutsuwa yaji ta saukar masa, dukkan gajiyarsa tatafima baki d'aya.
d'akin Aysha yalek'a, saiyajiyo motsinta ruwa a toilet tana wanka, "badai sai yanzu yarinyarnan tadawo aiikiba?", 'yay maganar yana kallon agogon hannunsa'.
Babu mai bashi amsa, danhaka yajuya zuwa nasa d'akin danya d'an watsa ruwa............✍








Wayyo kaza zanciπŸ˜©πŸ€§πŸ‘»






😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍
[9/23, 8:35 PM] Aysha Galadima: *_TypingπŸ“²_*



🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_



*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*



*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🀲🏻😭



*_part 2_*
(littafi na biyuπŸ“•)


2⃣2⃣

Babu dad'ewa Aysha tafito daga wankan, simple makeup tayi tasaka wandon jins blue dawata lemon green d'in riga wadda Tamata masifar k'yau, ta gyara kanta ta d'aure, bawai Aysha Nada wani uban gashi baneba, amma daidai gwargwado yanada tsayi.
Kasancewar ba sallah zatayiba tafito falo, kwanciyarta tayi saman doguwar kujera tana sauraren karatun alkur'anin data saka, kokad'an tunaninta bai kawo ya khaleel yadawo gidanba.

Shima a d'akinsa wanka yashiga, ya d'auro alwala yafito, jikinsa kawai ya goge da k'aramin towel ya zira jallabiya blue black ajikinsa, turare yafesa kad'an sannan yafito zuwa masallaci.
Ganin Aysha a kwance idonta kuma alumshe saiyayi nufin tsokanarta, cikin sand'a yak'araso kusada inda take, k'afarta datad'an lek'o Yakama babban yatsanta yaja, da sauri yaduk'e bayan kujera.
Kawai Aysha jitayi an matsa mata yatsan k'afa, aiko tamik'e a firgice tareda kwallah k'ara, sosai ta firgita, ta wawwayga kuma bataga komaiba, hakan yakuma tsoratata, sai tasaka kuka da kiran mama ta shiga uku, anturo abu zai kasheta.
Yanda take dire-diren k'afafu da kuka tamkar taga dodo ido da idone abin yabama ya khaleel dariya, duk k'ok'arin rik'ewa dayakeyi Baisan dariyar ta kwace masaba.
Aysha takuma tsorata, saida taji muryarsace sannan tagane shine.
Yafito daga wajen 6uyarsa yana cigaba da dariya sosai.
Tunda Aysha take bata ta6a ganin dariyar ya khaleel irin hakaba, saita samu kanta da shagala kallonsa.
Shikam baimasan tanayiba, yaga mugunta dariya ta tik'eshi, ya zauna kan kujera yana dariya.
Saida yayi mai isarsa sannan yad'ago yana kallon Aysha wadda ta cuno baki gaba saboda jin haushin dariyar dayake mata.
"Wai dama haka kike da tsoro? Hhhhhhh, wlhy kinbani dariya, to dakika tashi ina zakije ne?".
"Cikin shagwa6a Aysha tace, " yoni wlhy nama rikice, narasa INA zan dosa, d'aki ko waje, towai yaushe kadawo ban sanibane?".
"Kina wankafa nashigo, harnayi wankama, masallaci zanje kawai naganki kwance ido arufe, shine naji sha'awar tsokanarki, kinzata miye to?".
" yo aljani mana".
"kinajin karatu wane aljani ya Isa zuwa kusadake, kedai shegen tsorone dake, saikuma tsiwar tsiya fal kanki".
"Wlhy bazaka ganeba ya khaleel, natsorata wlhy, kaikuma kanatamin dariya, dama haka ka iya dariyar mugunta?".
Bai bata amsaba yamik'e, ''kinga bara naje massalaci karna lalace anan ashiga sallah".
Binsa kawai Aysha tayi da kallo tana murmushi dajin dad'in ganin dariyar mijin NATA murd'ad'd'e, dama yana dariya har haka? Oni shatun mama, su ya khaleel an iya mugunta.
Saina rama aii Nima".
Lallai yarinya zaki rame dai, naje madallaci".
To adawo lfy.

Saida akayi sallar isha'i yadawo gidan aysha takawo masa ruwa ya kar6a yana fad'in "thanks", yana gama sha ya ajiye cup d'in yana satar kallon Aysha k'asa-k'asa, kwalliyar tata tamasa k'yau, amma dayake ya khaleel akwai iya shariya, bazaka ta6a zaton yama damu da itaba.
Danne-danne kawai yakeyi a waya.
Aysha tace aranta aljanun miskilancin sun motso kenan?......
Maganarsace takatse tunaninta, tad'ago tana kallonsa, Dan bataji miyaceba sosai.
"Kin tsareni da idanun kinnan, canayi ki dafamin shayi".
Kad'an Aysha ta murgud'a Baki, azatonta baya kallonta, Dan haryanzu waya yake dannawa, tanufi kichin tana 'yan k'unk'uni.
Yana kallom murgud'a bakin data masa, dakuma k'unk'uni datakeyi, saidai bayajin mitake fad'a, ransane ya6aci, "shin mi yarinyarnan ke nufi? Kodan taga Na sake mata ina wasa da ita?", kwafa yayi yacigaba da danna wayarsa.
Kusan mintuna 10 Aysha takawo masa shayin, tasha jinin jikinta dan ganin fuskarsa cid'in-cid'in ad'aure, duk kuma saitaji babu dad'i, koba komai tana shiga farinciki idan taga ya khaleel Na walwala.
Kofin tea d'in ta mik'a masa, batareda ya kalletaba ya kar6a, baisake bi ta kantaba, yacigaba da shan tea d'insa yana danna waya.
Itama Aysha tayi shiru cikin kujera tana kallo, amma duk Rabin hankalinta Na Kansa, sai satar kallonsa takeyi.
Ahaka hasnah tayi sallama tashigo ta samesu.
Aysha ce kawai ta amsa mata, amma Oga ko ido baid'ago ya kallesuba.
Hasna sai Harar Aysha takeyi, yitai tamkar batasan tanayiba, Dan bata gabanta, arantama sai ayyanawa takeyi, yarinriya da uwarki laura zanyi badakeba, danke kinmin kad'an a filin daga.
Kusada ya khaleel hasnah ta k'arasa, ta rissina tana fad'in "'ya khaleel Momy tace kazo tana kiranka".
Saida ya6ata mintuna biyu sannan yad'ago ido ya kalleta, "naji to, inazuwa, kinzo kinmin tsaye akai". 'Yak'are maganar da hararta'.
Fita tayi tana tutura Baki wai ya dizgata gaban Aysha.
Bai fitaba saida yagama shan shayinsa.
Fita yayi batareda ya kalli ko inda Aysha takeba.
Aysha ta ta6e baki cikin hanlin ko inkula, yana fita takira Rufaida da Sadiya a waya, tahad'asu waje d'aya suna hira, dayake shashashune kowacce k'uruciya Na d'ibarta, sai sukaita bama juna labarin first night d'insu.


Nace, "ALLAH ya shiryaku".😏


******
Afalo ya iske k'annen nasa duk, har samarin suna kallon kwallo, 'yan matan kuma suna d'ayan group d'in kujerun kowacce da waya a hannu, masu charts nayi, masu karatun novels nayi, k'annensa ne 'ya'yan Momy kawai babu, damasu basa shiga cikin yaran gidan..
Gaidashi suka shigayi yana amsawa da k'yar, dan abinda Aysha tamasa ya 6ata masa rai.
Musleem ya k'unshe baki da hannu, cikin magana k'asa-k'asa yacema zunnurain, ''ya zunnurain bakaga ya khaleel yak'ara kaurin wuyaba da haske?".
Zunnurain ma dariyar yayi yace, "gulmamme ALLAH yasa yajika, kaikam aure aiba wasaba, Nima kwannan zan shigo da maganata gida, tuzurancin nan ya isheni, bazanso nayi tuzuranci irin Na ya khaleel ba gaskiya, yanda yanzun ake yayin mutuwarnan farat d'aya".
Dariya duk sukayi, dansinji mi zunnurain d'in yace.


A 6angaren momy ma kowanne da hidimar dayakeyi, wasu waya wasu laptop, gaisheshi suka shigayi, yakuma kicin-kicin da rai, Dan ganin bak'uwar fuska cikin k'annen nasa, wadda ya tabbatar itace Aleeya.
Aleeya kam dukta rikice, ashema guy d'in yafi had'uwa a fili fiyeda hoto, ita saitagama picture d'insa data gani kamar anrage masa k'yawune, tama kasa cewa uffan, saibinsa take da kallo kawai.
Yazauna kusada Momy da itama idonta ke kansa, ita batasan irin wannan hali Na Ibraheem ba.......
Maganarsa ta katse mata tunani.
"Momy gani, ance kina kirana".
''To ba doleba na kiraka Ibraheem, koka mance munada bak'uwane?".
" hummm, kusan haka d'in momy, kinsan aiki yasha kaina ga iyali, amma amin afuwa. Ita bak'uwar bata iya gaisuwa bane?".
Murmushi momy yayi, tasan d'an nata dason girma, "ta iya mana Ibraheem, Aleeya ga Ibraheem nan".
Da k'yar Aleeya ta iya saita kanta, gaba d'aya tagama raina ajinta agabansa, amma abinka da wayayyiya girman turai, ido yarigaya ya bud'e, saita wayance, "o!, sorry my boo.., ya aikin naka? Ina fata komai normal?".
Bai amsaba, hakama bai kalletaba, sai harara daya makama k'annensa, aii da sauri kowacce tatashi tabar falon, momy ma saita mik'e, tasan Ibraheem akwai kunya, bazai ta6a amsawa Aleeya magana tana wajenba, " bara Na watsa ruwa nima".
Aleeya Ce kad'ai tace, "to momcy afito lfy".
Ya khaleel kam bai tankaba, Dan haushine yakuma kamashi akan rashin kunyar yarinyar, Dan rashin mutunci agaban mahaifiyarsa zatawani kirashi da boo!, "mtsoow" yaja siririn tsaki.
Wanda yasaka Aleeya kafeshi da idanu, 100% ya khaleel yamata, tanason namiji mai aji da mulki, duk kuma tagansu agunsa.

"Bakida abincewane? Natashi natafi, nabar matata ita kad'ai".
Murmushi Aleeya yayi, dukda maganarsa ta k'arshe tamata zafi saita danne, cikin salon wayayyun mata tace, " my boo, ajinkafa yafi tsada, tsada, nazacima fiye dahaka agareka, domin irinka ko'a masarautun duniya kad'anne, saidai nalura kaiba Prince baneba, king ne da kansa gabad'aya, ina alfahari da samunka amatsayin miji, Wanda nadad'e ina bulayin nema, dukda zuciyata nayawan gargad'ata akan azar6a6i, harda tsoratar dani akan nacika kaud'i, bana bama karatunta muhimmanci, Dan ina alfari banta6a neman Abu narasaba".
Tayi crossing k'afarta, tana kad'ai idanunta manya, "hummm kasan wani Abu kuwa?", batajira amsarsaba tacigaba..
" Aleeya nada tarin masoya, turawa da bak'ak'e, kuma duk sun zauce akan sonta, duk burinsu shine su mallaki Aleeya, idan zan kafa za6en mijin aure, to tabbas sama da mutum babu adadi zasu jefa k'uri'ar Neman za6in aurena, amma abin al'ajab. Kallo d'aya tak namaka ajikin hoto sai zuciya da kwanji suka fara azar6a6in gogayyar kar6arka amatsayin mijin aure, Dan zuciyata tayi dai-dai da samun irin tsarin da kullum take zana taswurarsa, aganina babu Wanda ya cancanci samun k'uri'ar aurena sai babban gwarzon jarumi irinka, so Aleeya tabaka makullin zuciyata kawai, basai kasha wahala wajen lalubeba".
Tunda tafara magana yake danna wayarsa, ko kallo bata isheshibama, wannan surutunma datake zubawa, kallon mai kwantaccen notikan kai yake mata, (lallai Aysha ta cancanci zama matarsa 100%, dukda kasancewarta k'aramar yarinya akwai aji da sanin darajar kai, wani lokacin yakanyi zargin Aysha Na sonsa, amma iya kamun kanta da jan ajinta yakan ruguza hasashensa), abin mamaki yau saiga ballagazar mace agabansa, dukda yasha gamo da irinsu Aleeya, amma yakula farashinta yafi nakowa sauka acikinsu, ahaka kuma momy take fata tazama uwar 'ya'yansa, lallai akwai babban aiki agabansa, gatadai afuska kamar mai aji, amma a zance wawuyace.....
"My boo!.. Naji kayi shiru, kobaka gamsu da bayanina baneba?".
"Naji, zan duba", yamik'e yana kallon agogon hannunsa, "uhm kinga bara naje, kina neman Shiga time d'in matata".
Mamaki da tsoro suka lullu6e Aleeya, yandafa take tunanin guy d'innan yawuce nan, irin wannan rainin haka, ta sauka k'asarnan takirashi a waya bai d'aukaba, yadawo aiki bai nemi inda takeba saida aka kirashi, tsabar ya maidata 'Yar iska, tasaki baki tana masa magana Yakama danna waya batareda ya kulataba, shine dankuma cin fuska zai mik'e yace wani tashiga time d'in matarsa, hummm".
Harya kama handle d'in k'ofa zai fice momy ta katseshi, " a'a Ibraheem harkun gama gaisawar?".
Juyowa yayi yana k'ara d'aure face, cikin dakiyar murya yace, "eh momy bara naje muyi magana da baffah".
Momy ta washe Baki, "to maddalah yayi k'yau".
Ita azatonta zaije akan maganar aleeyane, tace, " zaka dawo tanan kenan?".
"A'a momy, zanje Na kwanta danna gaji"
"To shikenan, ainaga da sauran dare, dadai yadawo kunsake gaisawa, da safe saikuyi maganar da baffan naku".
Aransa yace, " jifa momy dawani zance, itakuma matatafa?", amma afili saiyace "a'a momy gwammadai naje d'in, ita saitayi hak'urin goben".
"Babu damuwa ALLAH ya kaimu goven, daughter tashi kimasa rakkiya ko".
"OK momcy".

Shikam baima jira k'arshen zancenba yafice.
Afalo duk k'annensa suka zubo musu ido, babu mai damar cewa wani Abu, amma kowanne mamaki da

Please Login or Register in order to submit comment