Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hankalin Aysha yayi masifar tashi, Dan batasan dami mutanene sukazoba, amma amamakinta saitaga ya khaleel ta Kansa kawai yakeyi bawai damuwa da mutanenba, Dan haryanzu yana manne da jikinta, data yunk'ura danta tashi zaice please karki barni, sanyi nakeji, Abu goma da ashirin inji Aysha.
Motsi sukafaraji alamun ana ta6a k'ofar d'akin, amma anjita GAM a kulle, sunata k'ok'arin sakab. k'arfennan dansu bud'e amma sun kasa, saboda key d'in yana ajiki ya khaleel bai zareba.
A tsorace Aysha tace, "ya khaleel zasu shigofa, Dan ALLAH katashi, wlhy k'ila kashemu zasuyi".
Tabashi tausayi, amma bashida k'arfin tunkarar kowa awannan yanayin dayake ciki, shikad'ai yasan halin dayake ciki, baita6a tsintar kansa acikin wannan halin ciwonba tunda yay wayo, yasandai yana ciwo, tunda yasha kwanciyama a asibiti, amma baita6a jin mai azaba irin wannanba, gabad'aya ga6o6in jikinsa kwankwatsa sukeyi, ga bala'in sanyin dayakeji.
Ahankali yace, "ki kwantar da hankalinki gasu Adams nan zuwa, bazasu iya bud'e k'ofarnanba saboda akwai key aciki, kibar kuka".
''Ya khaleel idan suka 6allafa?".
Shiru yayi yakasa bata amsa, ana cikin haka sukajiyo alamar ana dukan Abu, ya khaleel ya sauke ajiyar zuciya, Dan yasan su Adams sun iso, magana suke jiyowa sama-sama.
Su Adams ne suke dakama su gwaska tsawa, bayan sun tattaresu waje d'aya, katafila ne zaimusu gaddama Samuel ya dakesa, shine su Aysha sukajiyo.
Su Samuel suka tasa k'eyar su gwaska zuwa waje, mamaki yakama Adams ina ogan nasu yashiga haka? Har wawayennan suka shigarmasa gida?, gashi yaji maganarsa kamar a mawuyacin hali d'azun daya kirasa, tomeke faruwane?. wayarsa yad'auka yakirashi.
Ya khaleel yad'auka murya a dakushe yace, " Adams kunzone?".
"Ye sir, harma mun kamasu, amma kana inane?".
Da k'yar yace, " inan ad'aki kwance banida lfy, kuje dasu kawai, saida safe idan naga yanda natashi zan shigo".
"Oga kodai akira doctor k muje asibiti?, nake ganin baikamata kazauna cikin ciwoba".
" karka damu kuje, da safe zan kira Dr Abraham".
Badan Adams yasoba yace, "to shikenan Oga, ALLAH yak'ara afuwa".
"Ameen". ya khaleel ya amsa yana yanke wayar.



_______________________________
Haka suka kwana suduka babu mai isashshiyar lfy, duk agalabaice suka wayi gari, da k'yar ya khaleel ya iya raba jikinsa dana Aysha dake barci a wahalce itama, yana layi ahanya ya Isa toilet d'in, cikin dauriya yahad'a ruwa maid'an zafi yayi wanka tareda wankan tsarki, wani ruwan yakuma had'awa sannan yafito, yad'anji k'arfi ajikinsa, amma haryanzu zazza6in yana nan, kuma yanajin sanyi sosai, jallabiya yasaka da rigar sanyi mai kauri, ya dogara yay sallar Asubahi a d'akin, Dan bazai iya fita konan da tsakar gidaba.
Bakin gadon ya zauna yana cije la66a, idonsa nakan k'yak'yawan face d'in Aysha dake barci, dagani batajin dad'in barcin, yasan dukda wahalarnan dayake aciki tafisa, Dan bak'aramin wahalar da ita yayiba, kasa control d'in kansa yayima shi gabad'aya wlhy.
Ya lumshe idanunsa dake jajur sannan yabud'e akan Aysha, hannu yakai ya yaye bargon, Aysha tabud'e ido, kallo d'aya tamasa tamaida ta rufe saboda kunya.
Huci ya furzo a bakinsa, yad'an huro hancinsa alamun baya jin dad'in jikinsa, yace, "zaki iya tashine A'eesha?".
Shiru Aysha tayi masa, amma tad'aga kanta.
"Daure to kitashi kiyi wanka, kar lokacin sallah yashige", dagaji kasan a wahalce yake maganar.
Cikin zubda kwallah tace, " to kabani hijjab d'in nasaka".
Hijjab d'in yatashi da k'yar ya d'akko akan sofa, yamik'a mata, tana a kwancen tasaka, ta yink'ura zata tashi, amma azabar zafin dataji yasakata fad'in ya sallamm!!.
Tausayi tabashi, dukda jikinsa babu k'arfi haka yad'auketa cak yanufi bayin da ita, Aysha kasa bud'e ido tayi ta kallesa, ya direta, karki cutar da kanki, kishiga ruwan zafi sosai, zakiji sauk'in zafin kafin doctor yazo.
Kanta ta iya gyad'a masa kawai, amma takasa amasawa da baki.
Fitowa yayi, yacire bargon saman gadon, sannan ya cire bedsheets d'in gaba d'aya, ya nannad'eshi waje d'aya ya ajiye, wani bedsheets d'in yad'ako ya shimfid'a, batareda tsayawa wani gyarawaba ya haye yakwanta, ya k'udundune cikin bargo.
Aysha kam tanacan tashiga ruwan zafi, jin zafi yaratsata tamik'e zaram, kuma d'ibar ruwan sanyi tayi ta surka ruwan, zafin ya salamce, ahaka tashiga, shima batawani dad'eba tafita tayi wankan tsarki.
Fitowa tayi tana tafiya kamar wata y'ar kac.....🀭.
Saboda bata gasa jikin da k'yauba.
Ganinsa kwance yasakata ficewa daga d'akin, tanufi d'akinta, a can ta sauya kaya sannan tayi sallah a daddafe takoma kan gado ta kwanta.

Ya khaleel yanajin fitar Aysha, tun yana sauraren dawowarta harya fidda rai, yanda tafito daga bayin dawuri ya tabbatar masa batawani tsaya Gasa jikinta da k'yauba, yasan zata sha wahalane, saboda jikinta zai k'ara tsami, amma bashida wani k'arfin taimakonta.
Waya ya d'auka yakira doctor Abraham, dukda likitansune ta fannin aiki ya yarda dashi, duk wata Matsala ta ciwo Indai zata taso masa shi yake nema.
Babu dad'ewa kuwa saiga Dr Abraham d'in, ashema Adams ya Sanar masa yazo tunda Asubahi, Dan haka ya khaleel yay mamakin zuwan nasa da wuri.
Kwatancen d'akin yamasa yashigo, ya khaleel Na kwance suka gaisa, yace, "ashema kana kusa Na kiraka?".
" yes sir!, dama Adams ya sanarmin tun d'azun, nad'an dakatane gari Yakuma haske nazo, INA kan hanyar zuwama kakirani".
Ya khaleel ya jinjina kai yana lumshe idanu.
Bai 6oyema Dr Abraham ba, yasanar masa abinda yakawo ciwon.
Sorry sir, inaga ka Tara sha'awane shiyyasa, kadad'e kana buk'atar mace amma Baka d'auki wani matakiba akai, shiyyasa yau daka fidda (S) Ya haddasa maka da zazza6i da jin sanyi, sometimes irin hakan yana faruwa, idan mutum yakai age d'in buk'atar mace amma baiyi hakanba, sai (s) yarink'a taruwa amararsa, yakan haddasa masa yawan mantuwa, 6acin rai, ciwonkai, so duk randa yasamu damar fitarwar saikaga kuma ciwo mai tsanani ya sameshi, kamardai yanda katsinci kanka aciki, please Oga akiyaye gaskiya, Dan hakan had'arine ga lafiyar Dan adam".
Jin Nina kai ya khaleel yayi yana fad'in "OK doctor insha ALLAH".
Allura yamasa, sannan yabashi magunguna.
Ya khaleel yace, "itama yakamata kad'an bata magani, dannanga kamar zazza6inne ajikinta".
"OK sir! Amma ita NATA ba damuwa baneba sosai, gajiyace darashin sabo, tasha wannan maganin insha ALLAH zatajita normal".
"Amma yakamata kusha koda tea ne yanzu kafin kusha maganin, musamman kai da akama allura, Dan tanada k'arfi".
"Babu damuwa doctor, ngd sosai".
Sallama Dr Abraham yayi masa yatafi.


Tunani yafarayi akan waya kamata yakira danya taimaka masa akan Aysha, yakamata yasamu mai tsayawa akanta danta Gasa jikinta, Inda Anty zuwairah mutuniyar kirkice ai saiya kirasa, tunda dai y'ar uwarsace, kuma yayarsa, yaja guntun tsaki, garama yakira anty shukrah ko Amatullah.
Amatullah k'anwarsace, bara kawai yakira Anty shukurah d'in, tunda yaga ita halinta ya banbanta da su Anty zuwairah.
Harya fara nemanta saikuma yadakata, wani tunanine yazo masa, kodai yakira Ammah, Dan ita kakarsuce, akwai d'an k'arancin jin nauyinta tartare dasu, yanda zai iya fad'a mata damuwarsa itada Anty Mamie ko momy bazai iya fad'awaba.
Gaskiya kuma yanajin kunyar Anty Mamie matuk'a, Anty shukurah d'inma saiyaji kamar da kunya, garadai Ammah, dukda itama yanajin kunyar tata Amman dad'an sauk'i akan sauran.
Wayar Ammah yakira, bugu d'aya kuwa ta d'auka.
"Iro! Injidai lfy?".
Bayason iro d'inan, amma babu yanda zaiyi da Ammah, murya a tausashe yace please Ammah kid'anzo mana".
''Kaini kamin magana da yaren dazan gane, miye wani falis koma uwarmi kace?".
Dukda halin dayake ciki saida ya murmusa, aransa yace, " Ammah jaraba kenan, afili kuma yace, "to yi hak'uri, kizo bamuda lfy muduka".
Subahanalilahi, to ganin zuwa, aidama inada shirin lek'oku yau, amma dakam sai anjima, to amma ganina yanzu.
To saikinzo.


___________________________
Hhhhhh🀣, momy dai har Around 7am bata farkaba, tanata kwasar barci, babu Wanda yatada ita, su azatonsuma tatshi tayi sallar Asubahi takoma barcinne, basusan hajia momy ko motsima batayibaπŸ˜†.
(Aikin amma yayi k'yauπŸ˜‚πŸ‘πŸ»).



__________________________
Har barci yafara figar ya khaleel yajiyo Ammah Na kwad'a sallama daga falo, bai iya amsa mataba, Dan bashida k'arfin hakan.
Jiyota yayi tana fad'in "yoni halima ina kuke y'ay'annan?, yad'an murmusa yana gyara kwanciyarsa, can saiya jiyo ta turo k'ofar d'akinsa, talek'o kanta, saida ta hangoshi sannan ta ida shigowa, "o, kajimin d'an nema, iro dama kanajina inata kwad'a sallama amma kamin banza?".
Yi hak'uri Ammah, banida k'arfin amsa mikine".
''Wayyo, to sannu, ina ita Aysha d'in?, tun d'azun tafita, inaga tana d'akinta kwance".
''To ALLAH ya sauwak'a", tad'auki maganin tana dubawa, kaikace tasan mi'aka rubuta, cikin tsokana ya khaleel yace, " Ammah kina karantawane?".
Ta ta6e baki, "yoni iro minasani a wannan shirmen?, to wayazo yabaku magani kuma? Kotun jiyane ciwon?".
" A'a Ammah, yanzu doctor yatafi, yamin allura, yacene nasha tea da Sauri saboda allurar tanada k'arfi, ita kuma tasha wannan maganin".
''To bara na had'a maka shayin, amma ni halima nata6a ganin ciwo da salo, kakama mata kakama miji, iro wai miyema yasamekune haka?".
Yawu ya khaleel yahad'iye da k'yar, yad'an sosai saman girarsa yana fad'in "um, um, Ammah kedai dakin bani tea d'in k'awai, kingafa rawar sanyi nakeyi, ga zazza6i mai zafi ajikina.
Tofa, ninaga wannan aiki, wai kishiya tara rana d'aya, tafice tana tsogumi akan momy, kai laure ko y'ar banzar yarinya, dasotayi tasaka yara cikin tsaka mai wuya, kullum tahana yaro samun ladan aure, aikinga danayi maganin tsagerancinta yanema ma kansa mafita, shima da munafiki yana min mazurai bayason auren, to yanzu ubanwa ya aikeshi gunta hardasu ciwo, mtsoww yaran zamani aii akwai iyayi da firfirta, yo inba firfirtaba miye nakirana wai basuda lfy?.
Koda dayake daya fad'ama tsagerar uwarsa d'incan aii gwamma nid'in, Dan nasandai Bilkisu bazai iyaba, bare waccan shema'un da bata shiga sabgar kowa (umme amarya🀣).
Tana had'a shayi akicin d'insu take wannan tsogunguman nata, (nace kai Ammah ikon ALLAHπŸ˜€).

__________

Dakanta tabashi tea d'in, danta lura da gaske bashida lfyar, dauriyace kawai da jarumta irin tasa, saida ya shanye tas sannan yanuna mata yanda zata bashi maganin yasha, tace, "to kwanta kahuta, itama Ayshan bara naje kanta, ALLAH yak'ara afuwa".
Cikin gyad'a kai yace, " Ameen ammah".
Bargon ta gyara masa, ta lullu6eshi da k'yar sannan tafice.
Barci mai nauyi ya figesa, tunaninsa nakan Aysha, duk tausayinta yacika zuciyarsa, shi ga halin dayake ciki bare ita kuma daya wahalar.


**************

Akan gado amma ta iske Aysha kwance, itama ta k'udun dune cikin bargo, tazauna kusada ita tana sakamata albarka, tabama jikanta farinciki, jikanta datafi k'auna aduk cikin jikokinta, jitai k'aunar Ayshan takuma yawaita azuciyarta, tanason jarumin mutum, sosai mama takuma kima a zuciyar Ammah.
Ammah ta yaye bargon da ayshan take k'udundune ciki, dakar Aysha ta'iya bud'e baki tace, "wayyo ya khaleel please kayi hak'uri, wlhy sanyi nakeji, kuma nayi sallan aii".
Idonta arufe take maganar, duk zatonta ya khaleel ne yabiyota d'akin.
Murmushi Ammah tayi, tace, " kwantar da hankalinki, ba iron baneba, nicenan".
Zunbur Aysha tatashi zaune, ganin Ammah sai kunya ta kamata, tace, "Ammah ina kwana".
Lfy lay d'iyar albarka, yajikin?.
Kan Aysha ak'asa tad'an motsa bakinta, amma takasa cewa komai, wata kunyar Amman takeji sosai, gani takeyi kamar ya khaleel d'in yafad'i komai.
Dariya Ammah tayi tareda mik'ewa tashiga toilet d'in Aysha, babu dad'ewa saigata tafito, tacema Aysha taso.
Babu musu Aysha ta sakko, saida tana tafiya tana hard'e k'afafu, batason Ammah tafahimci halin datake ciki, dukda azabar datakeji wajen tafiyar.
Batasan Amman kar take kallontaba, kafinma tazo wajenta tuni ta gane komaiπŸ˜‚.

Ammah taji tausayin Aysha, Dan bak'aramar 6arna khaleel yayiba, sosai ta taimaka mata da dabarunsu irin Na tsoffi, tayima Aysha gashi Na musamman Na y'an gata, ita kanta Aysha taji sauyi sosai ajikinta, Har tana iya tafiya babu laifi, bakamar d'azunba dasai ta ware k'afafu.
Itama tea mai kauri Ammah tahad'a mata, itakam ba gwanar shan shayin baceba, saida Ammah ta lalla6ata sannan tashanye, tabata maganin da ya khaleel yace abata tasha, itama ta kwanta.
Saida Ammah taga barci ya d'auke Aysha sannan tafito daga d'akin takoma Na ya khaleel.
Zanin gadon datagani a k'udundune saman sofa yad'auka tabud'e, flowers d'in dake ciki suka zubo, wasu duksun d'an 6aci, cikin ta6e baki amma tace kajimin iyayi irinna yarannan, sunwani zuba filawa agado saikace wasu kafirai, mtsowww wlhy bokon nan ta6ata mana yara dai, aiimu a al'adar Malam bahaushe farin k'yalle muka Sani bawata filawar banzaba, dukda zanin gadon farine inma al'adar zasuyi saisuyi irin tamu.
Hakadai tayita jaraba tana zazzagewa, Leda tasamo tazuba flowers d'in aciki taje tasaka abola tana tsaki.

(Ho Amman ho Amman!, maganin kowane shege🀣🀣🀧).

A wishing matching tasaka bedsheets d'in, tawanke fes tazagaya zan bayan d'akunansu ta Shanya inda aka d'aura igiyar, sannan takomo falo tazauna tana gadin tashinsu.

Muna godiya Ammarmu, ciki da gaskiya fans suna mik'o gaisuwar ban girma, suna nan suna had'a miki k'yaututtuka Na musamman danjin dad'iπŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ», xoxo tace, "tabaki k'yauta homajeep, amma sai Aysha ta haihu za'a kawo miki.πŸ€­πŸ˜†πŸ‘πŸ».


______________,,___,__________
Wajajen 8:36am momy tafarka afirgice, sunan khaleel tafara kira da k'arfi.
"Ibraheem! Ina Ibraheem!? Badai yatafi can d'inba? Ibraheem! Kana inane?".
Anty zuwairah ce tajiyo sambatun momy, dasauri tashigo d'akin tana fad'in "momy kintashi?".
" eh zuwairah, ina Ibraheem yakene?".
"Yo momy k'yaga khaleel nankuwa, yana 6angarensu mana".
"kambu, kina nufin a can ya kwana? Amma kuka gaza hanashi?".
" to momy waya isa hanashi tafiya, waccan fitinanniyar tsohuwar Na kammu, gakuma baffah da waccan munafukar".
Shikenan Ibraheem kagama dani, inhar ka kusanci shegiyar yarinyarnan karuwa, zuwairah muje 6angaren nasa, muje muje da sauri.
Momy yakamata kufara yin sallah ko, dan nazata kinyi sallah, amma tunda naji kina Neman khaleel nagane baki farkama".
Danma dai kawai, "to amma bara nayi sallar, amma anyi munafukar tsohuwa, kenan allurar barci tasaka akaminfa zuwairah?".
"Wlhy kuwa momy, aini nak'agara tsohuwarnan tamutu, dukda kasancewarta uwar ubana, amma nagama tsanarta tuni wlhy".
Gaba d'aya momy lissafinta a jagule yake, ahaka tashiga tayi alwala.
Sallarma dai tayitane kawai, amma babu wata nutsuwa aciki, Anty shukurah Na falo suka fito, tace, "lah momy kintashi?, bata kulataba suka fice itada Anty zuwairah, ganin haka tamik'e da sauri danson ganin inda zasuje.
Suna huci suka nufi 6angarensu ya khaleel...........






πŸ˜„momy afito lfy🀭








πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
[9/17, 8:59 PM] Aysha Galadima: *_TypingπŸ“²_*



🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_



*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*



*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🀲🏻😭



*_part 2_*
(littafi na biyuπŸ“•)


1⃣7⃣

Ammah Na kacire saman kujera doguwa ta kurama TV data kunna idanu, kaikace tanajin yaren da'akeyi, tanason canzawa amma tarasa yanda zatayi, kunnan tvn dai ta iya.
Daga momy har Anty zuwairah babu Wanda yalura da Ammah, itakam tun shigowarsu idanunta Na Kansu, k'iyarsata yanda zataci mutuncin momy azuciyarta kawai takeyi.
Momy daketa harare-harare da hura hanci tafara kwalama ya khaleel kira. "Ibrahim! Ibrahim!! Kobaka jinane?".
"yaza'ayi yajiki? Bayan yanacikin halin ciwo Laure!".
Afirgice suka juyo suduka suna kallon Ammah, Anty shukurah dake k'ofar d'aki tsaye tayi murmushin jin dad'in ganin Ammah, shiru momy tayi takauda kanta daga kallon Ammah, zuciyarta sai suya da zugi takeyi.
Anty zuwaitah ce tasamu k'arfin halin Jan k'aramin tsaki, tana ta6e fuska.
Ammah tace, "kinyiwa Abdillahi da Laure, mara mutunci fitsararriya, mai girman kwabo kawai, 'Yar banza magajiyar uwarta".
"nidai badai uwataba ehe".
Tassssss!! Kakeji afuskar Anty zuwairah, gaba d'ayansu suka waigo dansan ganin Wanda yay marin, bakowa baneba face baffah da Anty shukurah takira awaya tasanar masa gasu momy can suntafi 6angaren khaleel.
Dafe kunci Anty zuwairah tayi, tunda ta girma tayi hankali baffah baita6a ko dungurintaba, amma yau harda mari? Da girmanta, ga zagada-zagadan 'ya'ya.
Momy kam baki bud'e take kallon baffah, tama rasa abin fad'a.
Ammah tataso tana tafa hannaye, ''kayimin dai-dai, kuma tabbas nahaifi d'an halak, kekuma kince badai uwarkiba?, to saitawa kenan?".
Cikin zubda hawaye Anty zuwairah tace, "nidai aii ban fad'aba ko".
Ammah zata sake magana baffah yace, ''kiyi hak'uri Ammah Dan girman ALLAH, basai kincigaba da 6ata rankiba akan rashin tarbiyya irin ta wannan mara mutuncin da uwarta ba, namuku biyayya Na auri Laure badan inason halayentaba, ayanzukam ina rok'on alfarma agareki, abisa madadin baba zan saki Laure yanzunnan, saboda halayenta sun isheni, banajin dad'inta, banajin dad'in 'ya'yanta sai shukurah da mu'azzam kawai, dan ALLAH Ammah kibari nasaketa kawai".
" humm bazaka saketaba Abdullahi, saboda wasu dalilaina, munhad'a aurenka da ita saboda darajar zumincin dake tsakanina da jummai mahaifiyarta, sannan kuma akwai 'ya'ya tsakaninku yanzu, to taci darajar y'ay'an dakuka haifa, d'ayan sirrin kuma nabarma zuciyata, dan haka kabarta duniyace zata koyar da ita hankali kwanannan".
Wani irin kallon momy take bin Ammah dashi, maid'aukeda abubuwa da dama, tsoro, tsana, k'iyayya, k'yama, hasala, bak'inciki, wai agaban 'ya'yanta wannan tsohuwar take cin zarafinta itada d'anta, lokaci yayi dazata d'auki mataki akan baffah da uwarsa, batareda tace komaiba tajuya afusace tabar falon.
Anty zuwairah ma baya ta take mata.
Baffah ya dakatar da ita, "kije yanzun ki tattara kayan 'ya'yanki da naki kibarmin gida Dan ubanki, kuma wlhy karna sake ganin k'afarki agidannan Harnan da shekaru biyu, inkuwa bahakaba saina sa6a miki kamanni Mara mutunci kawai, karna fito Na iskeki cikin gidana wlhy kinji Na fad'a miki shashasha".
Wannan hukuncin yamin dai-dai, Dan in ba hakaba wannan makirar saita kashema iro aurensa, Dan itace ke zuga uwarsu, Na tabbata ko wannan ciwon k'aryar da Laure taitayi harda bakin 'yar banzar can".
Anty shukurah tamatso jiki a sanyaye tana Bama baffah da Ammah hak'uri.
Albarka sukaita saka mata, sannan Ammah Tamusu bayanin ya khaleel d'inma bashida lfy.
Har d'akin ya khaleel baffah yashiga, khaleel Na kwance idonsa biyu, tun fara maganar Ammah dasu Anty zuwairah ya farka, komai akan kunnensa yafaru, bak'inciki da k'yamar halin mahaifiyarsa da 'Yar uwarsa yahanashi fitowa, dukda abin yahad'ama darashin jin k'arfin jikinsa.
Su Ammah na shigowa ya lumshe idanunsa, baya buk'atar Susan idonsa biyune, Anty shukurah tajawo stool d'in madubi ta ajiyema baffah gaban gadon, kusada ya khaleel, zama yayi yanamai tausayin d'an nasa, saboda halin mahaifiyarsa, yasan kokad'an khaleel bayajin dad'in mahaifiyarsa, hak'uri kawai yakeyi kasancewarsa mutum mai kawaici da had'iye damuwa, kokai waye Baka isa tantance damuwar khaleel ba, mutumneshi mai taka tsantsan da iya zaman duniya, komansa namasu nazari da dattakone, gashidai yaro amma akwai halayen manyan mutane tattare dashi, wannan baiwace da ALLAH yamasa tun yana k'araminsa.
Ahankali baffah yakai hannu yana shafa kan ya khaleel d'in, cikin taushin murya yace, "ALLAH yamuku albarka kaida sauran 'yan uwanka, ALLAH yabaka lfy".
Ammah da Anty shukurah sukace ameen.
Ammah tace, " aii zazza6in ya sauka ko? Dan sanda yakirani yanajin jiki sosai, amma dayake iro jarumine baka gane hakan".
Murmushi baffah yayi, "Ammah da d'an sauran zafi kam ajikinsa, amma ba sosaiba".
"To Alhmdllh, aidayake likita ya dubasu".
Baffah ya jinjina kansa yana kuma fad'in " ALLAH dai yak'ara sauk'i, ina ita matar tasa?".
"Itama tana d'akinta babu lafiyar, Shukurah duba ita kiga tashi".
" to Ammah".
Addu'a ya khaleel yakeyi azuciyarsa ALLAH yasa kar Ammah tamasa 6arin makauniya a gaban baffah, kaidata gama kasheshi wlhy.......
Tunaninsa yakatse lokacin da Anty shukurah tadawo tana fad'a musu haryanzu Aysha barci takeyi.
d'akin Ayshama saida baffah yashiga, sun isketa tanata barcinta itakam hankalli kwance, itama baffah yamata addu'a sannan suka fito.
Suna fita Aysha tabud'e idonta, Ashe itama idonta biyu, duk badak'alar da akeyi acikin kunnenta, jin motsin tahowarsu yasakata rufe ido harda d'an munsharin k'arya.
Jitai wata k'aunar surikin nata kuma mijin mahaifiyarta na ratsata, tareda kakar mijinta, surukar mamarta, dakuma d'iyar mijin

Please Login or Register in order to submit comment