Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kullum suke shigowa cikin gidanba dama.
Su iya hama duk sunyi mamakin ganin yamda gwaggo bintu tafita hayyacinta, amma basuda ikon tanbaya, Dan damacan tsoronta sukeji, bishirah ce taita bama gwaggo bintun kulawa, (itama tazama budurwa sosai) harma ansaka mata ranar aure, zata auri wani d'an uwansu a can Kaduna. Amma zai zauna da'ita a Suleja, anan yake 'yan kasuwan cinsa...................โœ๐Ÿฟ










*_Fatan alkairi agareku, inafata ansha bikin sallah lafiya?, ALLAH ya maimaita mana ta bad'in bad'ad'ad'a, Yakuma gafarta mana ayyukanmu Marasa k'yau dasuka wanzu a cikin wannan shekarar, ALLAH ka gafartama mahaifanmu, ka yace musu, kabama marasa lafiyarmu lafiya, muda Muke da ita ka k'ara mana, ALLAH ka yaye ma kowa damuwarsa, ka kawo mana sauk'i cikin al'amuranmu Na yau da kullum, ALLAH ka d'ora musulinci akan kafirci, ka karya kafirci da kafirai, ka d'aukaka musulinci da musulmai, katsare mu muda addininmu daga hannun azzaluman duniya, ALLAH kaza6a mana shuwagabanni nagari, ka k'arama shugaban k'asarmu lafiya, ka kareshi ga dukkan Sharrin masu burin cutar mana dashi, ya ALLAH ka zaunar da k'asarmu lfy, ka shirya al'ummar musulmai Baki d'aya, kabamu damina mai albarka, ka tsarkake mana zukatanmu duniya da lahira._*

Ameen ya rabbi๐Ÿคš๐Ÿปโœ‹๐Ÿป๐Ÿ˜ญ








Barkanmu da dawowa, acigaba da gashi my Guy's๐Ÿ˜š๐Ÿ˜‰.





๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[8/24, 8:20 PM] Aisha Galadima: *_Typing๐Ÿ“ฒ_*



๐Ÿคฐ๐Ÿป
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{๐Ÿ”ชwuk'a bata hudashi๐Ÿ—ก}_



*_Bilyn Abdull ce๐Ÿค™๐Ÿป_*



*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*๐Ÿ˜œ


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
๐Ÿคฒ๐Ÿป๐Ÿ˜ญ



*_part 1_*
(littafi na d'aya๐Ÿ“•)

_wannan gaisuwa takuce ku kad'ai 'yan group d'in *CIKI DA GASKIYA FAN'S* sak'onninku na isowa agareni, ina yinku 100%, ina sonku wallah, alkairin ALLAH yakai gareku._
๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜โคโค


3โƒฃ3โƒฃ

Kwanan sa kusan uku kenan da dawowa k'asar amma baije gidaba, saboda wani aiki daya rik'eshi, wani mutumi sukesan kamawa, kuma yanada had'arin gaske, kasancewar sa tsohon d'an ta'adda.
Sun d'ana masa tarko sosai tun wajen wata 5 daya wuce, har yanzu ALLAH baisa ya fad'a a tarkonba.
Mutumin a Rivers state yake, cikin port-harcourt.
Cikin shirin Uniform d'in police interpol yake, yaukam da bindugu biyu yafito, kokad'an fuskarnan babu alamar sassauci, duk lokacin da ya khaleel yad'ora hular aikinsa yakan k'ara kwarjini da cikar haiba๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚.
Sosai Uniform kemasa k'yau, gashi dogo mai suffar k'arfi masha ALLAH, cikakken training daya yasamu yakansaka suffarsa tsorata mazanma ba mataba kawai, ga tsare gida irinnan jaruman ma'aikata nagartattu.
Cikin Nutsuwa yake tafiya, wadda hakan tamkar halittarsace, komai ya khaleel zai maka anutsuwarsa yake, komai zafin daya d'auka awajen aiki ko rikiCewar abubuwa kuwa.
Bayansa Joseph ne da Youseef, Samuel, Adams, Taheer, saikuma mutum uku wad'anda bansansuba kam, da alama dai cikin k'ananun ma'aikatan suke.
Da sauri d'aya aciki yabud'e masa motar, harya taka zai shiga saikuma yajuyo yana kallonsu, in serious tone yace, ''komai zakuyi kuyi da kula, saboda anguwar tanada jama'a, banason aikinmu yashafi wani mara laifi, so Ku kula.
Kowa zaiyi tafiyarsa shi kad'aine, Adams shiga muje.
OK sir!!! Suka fad'a tareda Salutes nasa.
Batareda maida murtaniba yashige motar ya zauna abaya, yayinda Adams & Emanuel ke a gaba.
Kwantar da kansa yayi jikin kujera ya lumshe idanu, addu'oin Neman nasara ga ubangiji kawai yakeyi, yayinda gefen zuciyarsa take masa hasashen idan ta kwa6e ko ansami nasara.


Daka gansa kaga tibiran mahaukaci, kokad'an babu wata hujja dakakeda ita wadda zaka nuna rauninsa da amsa sunan mahaukacin, zaune yake kusada wani mai shayi Wanda yakasance ba haushe d'an balaguro, gefe d'aya kuma mai gasa naman tsirene da balangu, dandazon matasane awajen anata hirar duniya, wasu ta siyasa wasukuma ta yanayin rayuwa, harma da masu ta ball.
Wani matashin saurayi dayaci indome yarage yamik'e zuwa gaban mahaukaci daketa zane-zane ak'asa, kaikace lissafin kud'i yakeyi kona shekarunsa.
Mik'a masa filet d'in yayi, babu musu ya kar6a, saidai maimakon yaci, saiya juye cikin bak'ar ledan buhu datake hannunsa akowanne lokaci, yamik'ama matashin saurayi filet d'in yana tuntsura dariya.
Girgiza kai kawai matashin saurayi yayi yakoma rumfar mai shayi ya zauna.
Wani yace nifa kunsan wani Abu?.
Akace a'a.
Tunda mahaukacin can yazo wajennan, kimanin watanni uku kenan, banta6a ganin yaci abinciba, komi zaka bashi saidai yazuba abuhun ledar can, kuma kullum anan yake kwana.
Wlhy gaskiyanka ne, amma k'ila yanaci mune bama maida hankali shiyyasa bama ganewa.
Wani yace, nifa tausayi yake bani, ruwan shekaran jiya duk akansa yak'are.
Wlhy haka yakeyi, ammafa ni a kwanakin baya sonayi nad'an rud'e, sainaga mahaukacin daya fara zama awajennan tamkar yafi wancan d'in suffar k'arfi dad'an tsawo? Danni farkonma zuwansa ban yarda mahaukaci baneba.
Ashe bani kad'ai nakula da hakanba, kasan ALLAH nima sainake ganin tamkar ba wannan baneba Wanda yafara zuwa, ni wannanma baifi sati 2 ba nafara ganinsa anand'in, saikuma na daina ganin wancan.
Kudai kuna masa kallon tsorone, k'iladai aljanunsa ke canjashi, wani matashin saurayi ne mai wannan maganar, tun d'azu kuma baisaka baki a hirarba sai yanzu, yanata danna waya abinsa.

Jin shigowar sak'o yasaka ya khaleel bud'e shanyayyun idanunsa, wayar yad'auka yaduba, cikin d'an rikita yace, "Adams akwai matsala kenan?".
Da sauri Adams yace sir! Matsalarmi kuma? Naga komai yana tafiya yanda muka tsarashi.
Hakane, amma wai mutanen wajen sun fara tantama akan Mahfouz, yanzu katura masa sak'o yabar wajen, yaje inda muke had'uwa zanzo na samesa.
OK sir!, Adams yafad'a yana k'ok'arin tura sak'o da wayarsa.

Sunata hirar mahaukaci, Wanda ko alamar yasan misuke fad'a baiyiba, kamar an tsikaresa sukaga yatashi yana lalube-lalube abuhunsa, barin wajen yayi yanata surutai kamar yanda yasaba, babu Wanda yadamu dabarinsa wajen, harya 6acema ganinsu.

Mintuna kamar 20 dabarinsa wajen saigashi yadawo, yanata 'yan surutansa, yakoma inda yasaba zama ya zauna.
Mai Nama yace kai jama'a, ALLAH kuwa nafara gaskata maganar guy d'incan daya tashi, kugafa mahaukacin nan yanzu.
Suduka kallonsu suka maida kansa, yanata zane-zane ak'asa, mai shayi yace kakula yanzu kuma yad'an k'ara tsaho da k'iba, kai aljanima shaid'anine, babu abinda baya iyawa, kai Malam wannan bawan ALLAH da k'alau yake aii wlhy bak'aramin namiji za'ayiba.
Gsky kam, irin wad'annan suka damk'eka aii saidai lahira Dan babu mai kwatarka kuwa.
Suna cikin hirar mahaukaci saiga wasu ratsa-ratsan motoci sunshigo anguwar.
Wannan bawani sabon Abu baneba ga 'yan anguwar, akwai wani gida kad'an da rumfar mai shayin, kullum haka suke ganin manyan motoci nashigi da fici agidan, kowa yasan wani gawurtaccen tantirine agidan, amma kasancewar baita6a cutar da 'yan anguwarba shiyyasa ba'a damu dashiba, ko police shakkar zuwa anguwar sukeyi, Dan sosai ake tsoron anguwar a garin na port.
Kallone yakoma sama lokacinda mahaukacin nan yaje gaban motar farko yakwanta a akan titin, sunyi horn d'in duniya yak'i tashi, ganin haka boss d'in yafito a fusace.
Hakama dukkan yaransa da bodyguard d'insa.
Har d'aya ya saita bindiga zai harbeshi boss ya dakatar dashi tahanyar d'aga masa hannu.
K'arasawa yayi gaban mahaukacin yana lek'en fuskarsa.
Wata wawura mahaukaci yayma boss.
Kunsan abin mamaki da al'ajab๐Ÿ˜จ๐Ÿ˜จkuwa??.
Bindigace a hannun mahaukaci ya saita kan boss d'in dashi, yayinda yake fad'in kuna motsawa saina alburushe kansa wlhy, kowa ya ajiye bindigarsa.
Shiru sukayi basu ajiyeba, kowa sai huci yakeyi, 'yan anguwa kam anyi irko-cirko ana kallon ikon ALLAH, masu tsoro kuwa tuni sunsha agida.๐Ÿƒโ€โ™€
Boss d'in ya jinjinama yaransa kai alamar su sauke bindugunsu, wasu sun ajiye, amma wasu basu ajiyeba.
Alokacine matashin saurayi mai cewa aljanu suke canja mahaukaci yak'arso wajen, yagaggun kayan yafara yagewa daga jikin mahaukacin.
๐ŸคฅBakowa baneba face ya khaleel, k'asan kayan haukarsa kam Uniform d'in aikinsane, sai alokacin su taheer da police masu yawan gaske suka fara fitowa daga ma6oyarsu, nanfa aka fara musayar wuta, tsakanin 'yan ta'adda dasu ya khaleel.
Kowa Yakama gabansa yana Neman ma6oya, bakajin komai a anguwar sai k'arar harbe-harbe ketashi.
Wai idan bakayi bani waje, inji masu iya magana.

๐Ÿƒโ€โ™€๐Ÿƒโ€โ™€๐Ÿƒโ€โ™€๐Ÿƒโ€โ™€.

Misalin awanni biyu aka d'auka anguwar a hargitse, ansamu nasarar kwamushe wasu yaransa, wasunsu kam an iza k'eyarsu barzahu, wasu kuma sun sami harbi da raunuka, acikin 'yan sandama wasu sun sami harbi, wad'an da aka kama duk aka zubasu amotoci, Ambulance ๐Ÿš‘kuma takwashe police d'in dasuka samu rauni, Dan dama da guzurunsu sukazo.
Saida ya khaleel ya tabbatar an kammala iza k'eyar kowa sannan, shida sauran jiga-jigansa irinsu Adams kawaine awajen, Samuel yasamo masa ruwa yafara wanke fuskarsa daya shafe da bak'in Abu, hakama Mahfouz.
Sai asannan 'yan anguwar sukad'an fara fitowa, suma masu k'arfin halin kenan.
Sun shiga cikin gidan, bincike sosai sukayi, dukkuwa abinda suke buk'ata sun samu, suka fito kowa yanufi mota.
Sai kallonsu akeyi, wani yace, "wlhy ko rantsuwa zanyi babu kaffara aciki, wancan (ya khaleel) shine Wanda yafara zuwa wajennan a matsayin mahaukaci, sati biyune dasuka wuce aka canja da wancan (Mahfouz).
Gaskiyar ka wlhy, hakane.
Ya khaleel dake jinsu yayi murmushin k'asaita, sannan yataka yashige motar da'aka bud'e masa.

Tabbas ya khaleel ne yafara zuwa a matsayin mahaukacin, sati biyu dasuka wuce wani aiki yataso masa zuwa Saudia shine Mahfouz ya maye gurbinsa.

Tunda suka tafi kwance yake kawai ajikin kujera, duk abinda yafaru sai dawo masa yakeyi azuciya tiryan-tiryan, lamarin tamkar shirin film ko novel, baita6a tunanin zasu samu sauk'i hakaba wajen kama tantirinnanba saboda had'arinsa, amma Alhmdllh ALLAH ya sauk'ak'a komai, dukda and'an sha gimurzu dai.
Ahaka suka isa hotel d'in dasuka kwana, kafin da yamma jirginsu ya tashi zuwa Abuja.


____________________________
Komai cikin fargaba da yanayin kasala take yinsa, tanajin Raudat na kuka tun d'azun amma takasa lallashin yarinyar, kukama ita kanta takesonyi amma takasa saboda soyewar da zuciyarta tayi.
Ahaka ya Naufal yashigo d'akin ya sameta, kai tsaye wajen d'iyarsa daketa tsanyara kuka yanufa, ya d'auketa da sauri yana ra6ata da jikinsa tareda fad'in oh my dear mah-mah, waye yata6amin ke?.
Duk abinda ke faruwa idon meerah na akansu, amma azahirin gaskiya zuciyarta bata atare dasu, girgiza kai kawai ya Naufal yayi shi Kansa meerah tausayi take bashi, tun jiya batada wani sukuni, bare safiyar yau, kamata yayi yaud'in tazama ranar farin cikinta da zumud'in ganin mahaifiyarta da 'yan uwanta, amma ko kad'an babu d'igon hakan daga gareta, sa6anin Aysha daketa murna.
Shinfid'ar da Raudat yayi akan sofa, yamatsa kusada meerah data zuba tagumi har yanzu kuma idonta akansu.
Rigarta yad'auka data ajiye asaman cinyarta yafara k'ok'arin saka mata, bata hanashiba, Dan batada wani k'arfin shirya kan nata, tsaf yagama kimtsata, ya d'akko gyale ya lullu6a mata, sannan yad'auki Raudat da handbag d'inta irinta masu goyo, yakama hannun meerah batareda yace uffan ba suka fice.
Tuni su Aysha duksun fito, dad & mom, safwan, Iklas, duksun shiga mota.
Sai ifteehal da Aysha dake a tsaye jikin motar Maheer.
Da ido ya Naufal yamasu Aysha magana akan sushiga mota, yabud'ema meerah tashiga itama, sannan yashiga gaba kusada Maheer, ifteehal na tsakkiya, Aysha na gefe kusada Maheer.
Suna fita daga gidan wasu zafafan hawaye suka zubo a kumatun meerah, bata bari kowa yaganiba taja gyalenta tarufe, ya Naufal ne kawai yalura da ita, saboda dukkan hankalinsa na akanta.
Dama Raudat tana hannunsa.

Tun Aysha na d'agowa suna had'a ido da Maheer dake binta dawani mayen kallo harta bari, Dan duk jikinta itama yayi sanyi k'alau, musaman dataga yanayin da anty meerah take aciki, wadda yakamata tafita murnar ganin family NATA, kasancewar shekaru 9 bata k'asarta, gakuma alkairin haihuwa data samu tasanadin aure, amma duk wannan bai k'arfafa guywar Anty meerah ba tayita zumud'i.
To barema ita da iyayenta basusan mi'aka turata tayo a turaiba, tunda yaudararsu akayi.
Tafiyar 3hours ce takaisu Kaduna, dayake ba gudu sukeyiba, saboda yin driving irinna turai, tundasu komai nasu yana tafiyane da doka, bakamar nan Nigeria ba da ba'a binta.
Meerah tafad'a musu anguwar dazasuje, kasancewar dad'ewa bata k'asarma gaba d'aya bare garin yasakata manta hanyoyi, gashi kuma ansamu cigaba nawasu al'amuran, koda sukaje anguwarma saida sukayi tambaya, kasancewar gidansu meerah sanannene saboda mamansu tanayin markad'e da, shiyyasa akece mata mama mai markad'e.
Sun tanbayi wani d'an dattijo dake facin tayoyin keke a k'ofar wani shagon provision.
Dattijo yay shiru alamar tunanin gidan, zuwa can yace, "kai ban ganeba, amma bara muji komai shagonnan yasani.
Ak'ilu! Dattijo ya kwad'ama mai shago kira.
Ak'ilu ya amsa yanamai lek'o kansa ta window n shagon, yace, "m. labaran miya farune?".
A'a dama mutanen nan ne, suke tanbayar gidan mama mai markad'e, koka santane?.
Ak'ilu yace kai dallah k'aba kawai, gidansu 'Daheera 'yar maye fa, wadda aka guntule k'afar babarsu sati hud'u dasuka wuce.
Wata fad'uwar gaba meerah taji, har ganinta yakau Na wucin gadi.
Ta tsinkayo muryar labaran nafad'in okey ai namantama wlhy, kuje ga yarona yarakaku, kai auwalu tashi karakasu gidan, aika sani ko?.
Eh, Awwalu yafad'a cikin zumud'in murnar zai hau babbar mota.
Motarsu mom yashiga, saboda tasu ya Naufal d'in acike take babu waje.
Har k'ofar wani tsohon gida yakaisu, Wanda gefen katangar hannun haggu tazube, anyi katangar da ledar buhu, meerah tarintse idonta tana ambatar innalillahi'wa inna ilairraji'un.
Tabbas wannan gidansune, koda tahad'a shekaru tara bata cikinsa koda yaushe zuciyarta Na ciki, gidan dukya fita hayyacinsa, kamar bashi baneba tabari yana sabo, Sai d'aukar ido da burgewa yakeyi alokacin, amma yanzu kaikace almajiraine ke'a ciki, saboda tsabar fita kukkurjewa da bangon yayi.
Jiki a sanyaye duk suka fito, amma banda meerah, wadda saida ya Naufal yafito da'ita dakansa, Raudat tana hannun Maheer.
Ya Naufal da meerah ne Agaba, kama hannunta dayayine ya tilasta mata binsa badan tasoba.
Su Aysha Na take musu baya, yayinda mom & dad ke'a k'arshe.
Da sallama suka tura tsohon milk d'in gate d'in suka shiga, tsabar daud'ar dayayi yakoma brown kuwa.
Mama daketa faman Jan d'uwawu, saboda babu k'afa 1, an yanke, tafito daga toilet tad'ago tana amsa sallamar tasu.
Cak numfashinta yad'auke alokacin datayi tozali da'abar begenta, ko shekara 100 Ameerah tayi basa tare saita gane abarta, barema shekara 9..................โœ๐Ÿฟ





Nace humm๐Ÿค•





*_Kutttt sosaifa nakeyinku my sweet Guy's, kudai kawai ALLAH ya kaimu ranar bikin babyna, duksai kunyi rawar one corner_*๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜‰
[8/25, 9:17 PM] Aisha Galadima: *_Typing๐Ÿ“ฒ_*



๐Ÿคฐ๐Ÿป
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{๐Ÿ”ชwuk'a bata hudashi๐Ÿ—ก}_



*_Bilyn Abdull ce๐Ÿค™๐Ÿป_*



*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*๐Ÿ˜œ


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
๐Ÿคฒ๐Ÿป๐Ÿ˜ญ



*_part 1_*
(littafi na d'aya๐Ÿ“•)

_Kuna raina *HAUSA NOVEL FARIN CIKI* kuma, bilyn Abdul bata manta dakuba._
_ina yinku aradu_๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜


3โƒฃ4โƒฃ

To masu iya magana nacewa d'a da mahaifa sai ALLAH, hakance tafaru da meerah, dukkan wani 6acin ranta da tsanar mahaifiyar tata datayi, hakan bai hanata kwace hannuntaba dagana ya Naufal tanufi mama da gudu tana kuka, kanta tafad'a tana rubzar kuka mai matuk'ar tada hankalin mai saurarenta.
Ya Naufal dasu Aysha duk sunyi tsaye suna kallonsu, wasunsuma kuka sukeyi suma.
Kusan mintuna 4 meerah da mama nata kuka, kuma suna'a rik'e da junansu.
Ganin kukan zaiyi yawane yasaka mom matsawa ta janye meerah daga jikin mamar saboda ganin halin ciwo da mama take aciki.

Rasa inda mama zata ajiye wad'annan 'yan gayu tayi, sukam su mom babu ruwansu, tabarmar dake a falon suka zazzauna, Raudat cedai keta kuka saboda zafi bata sababa, gashi dama yaud'in da akwai rana.
Maheer daketa faman jijjigata akan tayi shiru yace waimike damun Raudat ne? Dukta rud'e wlhy.
Mom tamik'a hannu ta kar6eta, cikin hausarta dabatama iyaba sosai tace maybi zafine, tafara k'ok'arin cirema yarinyar Riga, mafici mama tamik'o Dan ama Raudat fifita.
Dad yakar6a yana fifita Raudat data fara rage kukan tana sauke ajiyar zuciya ajikin mom, kai kace wata babbace.
Saida ta tsagaita da kukan sannan mom tamik'ama ya Naufal dake kusada ita, Naufal mik'ama Meerah tabata abincinta.
Kar6arta yayi tareda sumbatar goshinta, my dear mah-mah sorry kinji, zafine kawai yamiki yawa nasani, yamik'ata wajen Meerah da gaba d'aya hankalinta na'akan mamanta.
Saidama ya zungureta sannan tajuyo tana kallonsu shida d'iyar tasa, da ido yamata nuni yunwa.
Batace komaiba takar6eta tad'ora a cinya, mama dai tana kallon ikon ALLAH, da al'ajabin abinda ke shirin faruwa, wai Meerah da d'iya.
Bata k'ara gaskatawaba saida taga tafara shayar da yarinyar sannan.

Dad datun d'azun yake kallon mama a sace, yadai daure yace nikam baiwar ALLAH Na tambayeki mana?.
Mama tace ina saurarenka Alhaji.
Dad yagyara zamansa, yayinda duk idon yaran ke'a kansa Dan mamakin furucinsa ga maman meerah.
Yanisa sannan yace, kama kikemin dawata a sokoto mai suna Zainabu 'yar Dije.
Mama da idonta yacika da hawaye, tace tabbas itace, kuma tunda kashigo nake maka kallon Sani, saidai banida tabbas akan ko yahaya ne k'anin malam Abdul'majedu?.
'Yar zabura dad yayi, bakinsa har rawa yakeyi yace tabbas shine, Abu kina nufin da gske kece?, ina d'an uwana Abu? Kardai kice Ameerah jini nace? Karki cemin haryanzu baki canjaba Zainabu?.
Inna lillahiwa'inna ilairraji'un, dad yashiga ambata yana hawaye.
Tofa falo yayi tsit ana kallon ikon ALLAH, mama da dad duk kuka sukeyi, Wanda babu Wanda yasan ma'anarsa cikinsu ya Naufal..



____________________________
Tunda suka zo gidan gwaggo bintu batada lfy, wannan yasaka matan gidan babu Wanda yasan da zuwanta gidan.
Sun sandai zuwairah tazo, itakam dama babu matar datake gaidawa agidan, saima tazo tagama zamanta baifi tahad'u dasu Anty Mamie sau uku ba, shima sai idan tata ta fiddota daga 6angarensu, amma bada nufin gaida matan gidanba, to yanzuma girma yak'aru ga daraja, saboda dawowar mama tayi alk'awarin tadaina shiga 6angaren ko waccensu.

Iya hama ce takaima mama gulmar dawowar Gwaggo bintu gidan, harda halin datake ciki.
Anty Mamie akwai tausayi. Wannan yasaka hankalinta tashi tanufi gefin masu aikin taduba gwaggo bintu, ganin halin datake ciki yasakata kiran Hafiz yayi driving nasu zuwa asibiti itama tana nan tahowa zata gama wani aiki.

Hafiz yad'auki iya hama da gwaggo bintu dake kashir6an cikin halin rashin lfy yatafi.
Komai shiyayita k'ok'ari aka mata, har aka basu gado, sai a sannan Anty Mamie ta k'araso itada ya Zunnurain daya kawota.
Da taimakonsu aka kammala komai, gwaggo bintu tafara samun kulawa.



___________________________

Saida sukayi kuka mai isarsu sannan falon yay tsit, dad yace Abu miya dawo daku Kaduna? Nidai nasan harna bar k'asarnan kuna sokoto?.
Hawaye mama tashare, cikin nadamar abinda ta aikata tace yahaya ka gafarceni, tabbas ni azzalumace, kuma na cutar dakai kaida d'an uwanka.
Tabi su ya Naufal da kallo tana hawaye, tace bara nabaku labarin wacece zainabu 'Yar dije.


*Tuna baya*
Kamar yanda kuka sani mu 'yan asalin sokoto ne, amma a k'aramar hukumar Gwadabawa, Ni bama cikin gwadabawa nakeba, ina awani k'auyene Bamana, tallar kayan koli ke kawoni cikin gwadabawa, a k'auyenmu na Bamana babu Wanda baisan Zainabu 'Yar dije ba, tun ina k'aramata banajin magana, Dan ko'a gidanmu babu Wanda ya isa yasani nayi, babata dije bata yarda ko hararata ayiba agidan, kasancewar nikad'ai tahaifa aduniya.
Tallan kayan koli danake zagawa k'auyika da cikin gwadabawa yasaka idanuna suka k'ara bud'ewa, kokad'an bansan bariba.
Ayawon tallata nahad'u da Abdul'majedu, soyayya kuma tak'ullu a tsakaninmu, har akayi aurena da Abdul'majidu danginsa basason auren, musammanma yahaya, Dan yasanni sosai, idan nakawo talla har majalissarsu nake zuwa.
Wannan k'iyayya da yahaya ya nunamin yasakani tsanarsa, kokad'an bana raga masa bayan na auri yayansa, kullum babu abinda nakeyi sai had'asu fad'a, saidai abdul'majidu baya kulawa.
Hakan yana k'onamin rai, dan aganina Abdul'majidu yafison k'aninsa dani.
Saida mukayi shekaru goma bansami haihuwaba, zuwa sannan yahaya yayi aure. Harma matarsa tayi 6ari, 6arin datayi yatada hankalina, gashi tafini samun jin dad'i ajaken mijinta, hasalima arzik'insu mikeci.
Wata ranar talata muka tashi da alhinin rasuwar mahaifiyarsu yahaya, sosai yahaya yayi rawar gani akan hidimar rasuwarnan ta mahaifiyarsu, yabon da akaitama yahaya awajen rasuwar ya6ata raina Dan haka na kullaceshi a zuciyata.
Shiryawa nayi naje k'auyenmu, na fad'ama tsohuwata komai, ita tabani shawarar abinda yakamata nayi yahaya yabar gidan, shawararta kam tayi tasiri, Dan ina dawowa washe gari nakira yahaya d'akina akan zamuyi magana, lokacin Abdul'majidu baya gida.
Saida yashigo d'akina da sallama, ina la6e abayan labule nikam, yayta sallama nak'i na amsa mishi, saiya nemi guri ya zauna Dan azatonsa ina band'akine.
Ina nan ala6e ban fitoba saida naji motsin dawowar Abdul'majid, wuf nafito natsala ihu ina kiran kwarti-kwarto.
Kankace mi gida yacika da jama'a, yahaya dukya rud'e, mutane kuma sai tsinarsa sukeyi, babansu harda kuka da matarsa, awannan karonkam

2 Comments On CIKI DA GASKIYA PART 1
avatar
nusaiba-4-8

12 months ago

Reply

Inason in karanta saboda Ina Jin Dadin littafin marubuciyar

avatar
taskar

12 months ago

Reply

Replying to nusaiba-4-8

ki yi subscription namu sai ki downloading

Please Login or Register in order to submit comment