Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ana shiga rayuwata irin haka,abinda ma yafi bani haushi shine,sai munyi magana dashi akan zanyi wani abu ya amince,daga baya kuma sai yaxo yacemin abinnan bai yarda dashi ba.
Taya inna kike tunanin zan yarda kullum yadunga yimin haka kuma........"
"Saurin buge bakin Bombee Daneji tayi,tareda yin magana cikin bacin rai"
"Wani nikam yaushe zakiyi hankali ne kam,kullum kina girma kina cin ƙasa,wannan harkar maganar tantiran zaki zo kina min anan kina cije min baki,kuma wai duk da mahaifinki kike. Kenan bashida ikon sakaki abu komai koke nufi?.
Aure kuma saura naji kinyi wata tsiyar akai nida kene dan kinga ana ƙyaleki koh? Tashi ki bani waje,aure babu fashi"
Cune baki Bombee tayi tareda barin cikin ɗakin.
Sauke ajiyar zuciya Daneji tayi,tabbas dolene tayiwa tufkar hanci,idan tana son su shiryah da Bombee da kuma ubanta.
"Allah kayi mana maganin matsala"
Tafaɗa cikin kasalalliyar murya.
Shirye shiryen bikin Bombee aka farayi da GOJE ɗan gidan jauro,wanda suke wata Ruga nesa dasu kaɗan.
Goje mutum ne majanuni,saidai shi ƙarin tsiyarsa harda innarsa wacce take ɗaure masa gindi,kullum idan yayi abu sai tace bashi bane,daga kan satar gaji ya fara,har yaxo kan satar shanu suje su sayar.
Yanzu har ta kai yana haɗa baki da ƴan daba ayi babbar sata,wani halinsa ma na takaici shine har fyaɗe yanayiwa ƙananan yara,idan an kai ƙara wajen HARƊO sai ya shafe zancen,saboda maƙudan kuɗin da Goje yake bashi.
Tun Bombee tana yarinya goje ya ganta yace yana sonta,da jauro yazo ya samu mlm Ahmadu da zancen ya fatattakeshi,akan ƴar sa saliha babu abinda zatayi da wani goje. Haka jauro yakoma yafaɗawa ɗansa abinda mlm Ahmadu yace,duk da shikansa da farko dama yasan abin bayyi ba,DAYEE ce matarsa ta dameshi saida yaje,wato mahaifiyar goje.
Yanzu kuma kwatsam jauro yana wajen shanu saiga mlm Ahmadu yazo ya sameshi,nan yake faɗamasa cewar ya amince da auren Bombee da goje,abin yabawa jauro mamaki,saidai yayi shuru bai ce komai ba,a ganinsa koma menene bazai zafafa ba,dan burinsa shine ɗannasa yayi aure kozai shiryu yazama mutum.
Lokacin da aka faɗawa goje baƙaramin farinciki yayi ba,danshi saboda kyanta dakuma idonta yake sonta,dan dama shi mutum ne mai son kayansa yazama daban dana kowa,lokaci guda aka tashi gyaran ƙofar gojen wacce take cikin gidansu,yaransa kullum cikin gyara suke duk na zuwan amaryar tasa nan da sati biyu masu xuwa.
"Goje ana maka sallama a waje"
"Wanene?"
"Bansani ba yace dai jauro yake nema,to da nace masa baya nan saiya ce kazo kai ɗin"
"Buge Indo yayi ƙanwarsa wacce tace anayi masa sallamar kafin ya fita waje"
Hayaniyace ta fara tashi a wajen,kana jiyo muryar goje dakuma wani daga cikin gida.
Inna dayee ce tayafa mayafinta tareda nufar ƙofar gidan.
"Kai goje mai yake faruwane,kaida waye haka,kace musu jauro bayanan yatafi Gassol jiya"
Idonta ne ya sauƙa kan wata yarinya a bayan wata mata,shikuma namijin sunata magana shida goje.
"Zakace haka mana ka bata mana yarinya,gatana ai bazata yi maka ƙarya ba,ka musa idan bakayi mata fyaɗe,aradu daga nan wajen jauro zan wuce nayi ƙararka"
"Ƙara akan me naji ana zancen ƙara kuma,wani akayi maka,kayanka akaci Mlm?"
"Ina kayana ɗanki yaci ai da sauƙi,ƴata ya lalatawa rayuwa,in baki yarda ba kata ki tambayeta,kaita lungu yayi yai mata fyaɗe,sannan kuma ya gargaɗeta akan kada ta faɗa.
Jiya yarinya tafara amai ashe ciki gareta,saida nabata azaba kafin ta faɗamin gaskiya. To bazan yardaba aradu sai anbimin kadu.
Kuma yarinya dole ya aureta tunda ya lalata ta"
Dariyar rainin hankali inna daayi tayi,tareda tafa hannaye.
"Heeee sai yanzu ka sosa inda yake maka ƙaiƙayi mlm,kace kawai ƴar ka tagama yawon dambaɗewa kanason mannawa ɗana ita saboda kaji zayyi aure,to ahirrr dinka munfi ƙarfinka munfi ƙarfin wanda ya tsaya maka ma.
Ba wajen jauro zaka kai ƙaraba ka kai cikin gari ma idan kanaso,haka kawai kowa sai yazo yana laƙawa yaro sharri,dan kawai kunga yayi farinjini yaki auren ƴaƴan ku,duk ina sane da abinda kuke ai,kowa so yake ƴarsa da auri goje saboda ta haifamuku ɗa namiji kuci dukiya,toh aradu baku isa ba.
Kaikuma ka bacemin daga ƙofar gida,ko kuma nacewa arɗon kunzo har gida kunyimana sharri.
"To shikenan tunda haka zakice,kowa a rugar nan yasan tsiyar da ɗanki keyiwa Al'umma,amma saiku danne kurufe,saboda kuna da hanya a wajen Manya,babu komai a akwai Allah,zakuga yanda zaku ƙare dashi.
Lalatacciyar uwa mai boye laifin ɗanta,zaki samu wanda zai yi maganinsa kuma babu yadda zakiyi"
Mahaifiyar yarinyar ce tafaɗawa inna daayi cikin muryar kuka,hannunta rikeda dana yar tata wacce itama take kukan.
Dan takaici shi uban ko magana bayyi ba,sai turasu dayayi suka tafi. A hakan ma daayi bata barsu ba tana iyowa daga bakin ƙofar gidanta.
Sai bayan sun 'bacene Inna daayi ta juya takalli goje wanda yake yangara hakora yana hura hanci,shi a dole an bata masa rai,amma kana ganin idonsa kasan bashida gaskiya a lamarin.
"Yanzu duk yanda nayi dakai akan kadaina wanann halin yanzu aure zakayi baka daina bako,a hakan kake tunanin zasu baka auren idan suka san haka kake?"
"Na nawa kuma ai sun riga sun sani,a tunaninki haka kawai zasu bani aurenta tana hankali, hmmmm itama tantiriyace lamba ɗaya.
Saikiyi shirin karbar tantiriyar suruka inna"
Zaro ido inna daayi tayi tareda jan ajiyar zuciya.
"Kuma kasan hakane ka nace saiak aureta,yanzu duk ƴaƴan dana kawo maka ka aura kaƙi,dama dan ka auromin irinka ne cikin gidannan,aikuwa zan saita mata zama,dakanta zata bi yanda kowacce mace take a gidan aurenta"
"Hhhh a tunaninki zan kawo matata ki dunga yimata izaya ina kallo,ba iya son Bombee ne yasakani aure nan ba,saboda naga yanda zatayi dake a cikin gidannan ne,baki san halinta ba sunanta kikeji,amma kije ki buncika ki gano da kanki"
'Dama hakane ?' ta faɗa a ranta.

_____*_____*_____*___


"Ungo karbi kisha yanzu nan"
"Wannan ɗin menene inno?"
Bombee tafaɗa tana yamutsa fuska
"Kinci gidanku banace karki tambaya ba,ki shanyeshi yanzu nan,wacce zatayi aure ai saida gyara,kuma gobe ma ki tabbatar kin dawo,sannan dama na riga na hanaki bin Shugabannki jeki,karki ƙara yin tsalle tsallen nan bana mata bane"
Duk abinda inno tak faɗa Bombee tana jinta,ba abinda takeyi sai dariyah ƙasa,ita mantawa ma take da zancen sai anyi maganar tukunna.
Haka gidama tashi ga tafita,sunata aikin shirye shiryen biki. Jiya fitowar ta takalli ana shigowa dakayan gado cikin gidan,babu abinda take ayyanawa a ranta sai irin kuɗin dazasuyi idan ta siyarsu.
"Lahh inno gwanda dakika tunamin,dama fah inason naje nayi ɗan bincike akan shi wannan gojen"
"Ahah karki je dakanku,ki bari Mlm yasaka ayimiki,wai sau nawa zan faɗamiki ki daina hakane kam,tashi ki tafi gida ma ya isa haka,sai gobe kuma"
Tashi Bombee tayi batareda tayi musu ba takaɗe rigarta,wajen da yayi ƙasa.
Hanyar ƙofar gidan tayi batace komaiba ta kamo hanyar barin jejin.
Jijjiga kai inno tayi tareda yin ɗan guntun murmushi,duk cewa batayi mata musu,amma hakan bashi ke sakawa tayi abinda tasakata ba. Tasan ko tsafi take da zaba Bombee bazata haƙuraba sai tayi binciken dakanta.
Haka take wata irin murɗaɗɗiyar yarinya ce itah,da kaɗan kaɗan tsoro sai barin cikin idanuwanta yakeyi,a hankali take sauyawa zuwa wata macen taban.
Da farko abin kaman ƙuruciya,amma kuma tana girma tana ƙara fitar da halayyarta na tsayawa akan ra'ayinta.
Duk da kasancewarta ba mai sabo da mutane ba,amma haka kawai Allah ya haɗata da jinin Maharbi Uwaisu,shida matarsa inno,basuda ɗa ko ƴa shiyasa sukejin Bombee har cikin ransu,duk su kansu sunsan batada daɗin sha'ani.

Hasashen inno bai tashi a banza ba,maimakon Bombee takama hanyar tafiyah gidansu,saita kama hanyar da zata kaita rugar su goje a ƙafa.
Tana tafiyah tana ƴar waƙa,irin wanda takeji a gidan rediyo,harta isa ga rugar.
Lokacin anyi magriba duhu ya kawo kai,wani mai gasa masara ta haɗu dashi a bakin hanyar yana da aikinsa.
Tsugunnawa tayi kaman abin arziƙi tace.
"Uh dan Allah bawan allah idan bazaka damuba tambaya nake"
"Allah yasa na sani toh"
"Inaso ne ka faɗamin duk abinda kasani gameda Goje dake rugar nan,kama daga mugayen halayensa harma da abinda yake aikatawa"
Kallon bakida hankali yayi mata,tareda yin dariyar rainin hankali.
"Mai yasa kake dariyah,bazaka faɗamin ba ko kuma kana tsoro"
"Tsoro? wazanji tsoro,tambaya ma kike akan meyasa bazan faɗamiki,dallah tashi ki bani waje tunda bakida hankali"
Kama bakin tiren gashin masarar tayi kaman mai shirin watsa masa garwashin a jikinsa.
"Ke me kike haka?"
Rashin hankalin nakeso na nuna maka banida shi kaman yanda kake tsammani,shin zaka faɗamin ko kuma sai na gasaka kaima da abinnan.
Zaro ido yayi tareda cewa.
"Keee ki bari aradu ina tsoron faɗamiki,zance yadawo ace a wajena kikaji"
"Tom tunda tsoro kake sai zabi na biyu,kwatanta min gidansu"
Kwatancen yafarayi mata batareda musu ba har ya gama.
Tashi tayi zata tafi,maganar sa ce ta ƙatseta ta tsaya catt.
"Mm....me zakiyi a gidansu,yarinya bazai ƙyaleki bafah idan wani abu kike nufinsa dashi,sannan kuma innarsa ta ɗauremasa gindi,ko ƙara kika kai baza'a saureriki ba"
"Wow kaga ka bani amsoshin tambayoyina dayawa,karka damu ba wani abu zanyi masa ba,kawai zanje gun innarsa ne na tambayi waye shi,dan nasan tafi saninsa fiyeda kowa"

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼



____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤22🖤




Kwatancen da mai masarar ya gwada mata tabi tiryan tiryan har ta samu kanta a ƙofar gidan su goje.
Tsayawa tayi a bakin dangar gidan ta riƙe kunkumi tana kallon gidan.
"Hmm wai nan gidan baba yakeson nazo na zauna na ƙare rayuwata,nida nakeda burin fita daga nahiyar nan,shine zanzo wannan wajen na zauna,lallai baba yanzu na tabbatar ya rainamin hankali ba kaɗan ba,shi bayyi zaman irin gunnan ba saini Bombee?"
Maganar ce daga bazata kaita ba,dan haka kawai tasaka kai cikin gidansu goje babu ko sallama.
Inna Daayi ce a zaune akan tabarmar datayi sallah tana cin tuwon da indo ƙanwar goje ta kawo mata gabanta.
Ɗaga kai tayi cikin bazata ta kalli yarinya a kanta,yatsine fuska tayi kafin ta ɗora cewa.
"Ke lafiya yarinya kika shigo ko sallama babu,kufah yaran zamaninnan haka kuke,gabaɗa kaman an saka ku a kwano an raba,ba'a jin daɗinku sam.
Idan cukui kikazo siya babu saina kaɗa gobe in allah ya kaimu"
Duk surutunna da take Bombee batace kanjil ba,hannunta riƙe a kunkuminta tana nazartarta.
Saida ta gama kafin ta zauna a kujera ƴar tsugunno dake tsakar gidan.
"Uhhh in kingama surutun inna dama wajenki nazo,tambayarki zanyi,kina amsamin zan tafi.....amma kafin sannann dan Allah zanyi sallah,kuma yunwa nakeji,ƙanshin miyarki yasa cikina yayi kuka yana neman abinda zai haɗiya."
Kamar wanda akayiwa asirin wucin gadi,haka inna daayi tabawa Bombee buta tayi alwala,ta ɗau hijabin inna daayi tayi sallah,sannan indo ta zubo mata tuwon taci tayi nakk.
"Yawwa Alhamdulillah ciki ya ɗauka,ki faɗa yar ki ta iya abinci,da alama baza'aji kunya ba"
"Ke yarinya wai daga ina kikene,hala ba batan hanya kikayi ba?"
"Babu wani batan hanya,ina kece Daayi matar jauro uwar Goje"
Ɗaga kai inna daayi tayi,duk da taji haushin rashin kunyar Bombee na ƙiran sunna su ba sakayawa.
"Na shigo garinnnan ne saboda naji waye goje,mai yake taƙama dashi da har yake shirin shiga min hanci da ƙudundune,to wlh kijawa ɗanki kunne hawainiyarsa takiyayi ramata,tun muna shaida juna nida shi,idan ba haka ba kuwa dagake harshi zakuji babu daɗi,dan kun tabo marar daɗin.
Naji ance taƙadari ne,to duk tsiyarsa na fishi aradu,karya ganshi zabgege ya gannni kaman itace karmami yanemi ya rainani,shaidar ɗan maciji da kyansa tamm"
Duk magana tanayi ne idonta ɗaya a kanne,yatsa ɗaya kuma tana nuna idon inna daayi bako tsoro.
Saida tagama tass kafin tamiƙe tayi hanyar waje tana faɗin.
"To nina tafi badan dare yayimin ba saidan kar inna ta nemeni,hhhhhhhh wai amaryar daza'a saka lalle wani satin tana yawo"
Ita kanta saida abin yabata dariya,ƙarin mamakin ta ma wai ta yarda ayi auren.
"Yarinya wai wacece ke,sannan menene ma'anar wannan gargaɗin dakikayi,kina cikin wadda goje yayi wa fyaɗe ne? Inma kina ciki ina faɗamiki tun wuri kisan me kike,dan bazaki iya ja dashi ba,kuma shi aure ma zayyi wani satin.
Inso kike ya aureki ma tun dare bai miki ba kima wani hannun"
"Fyaɗe???? Tabbb ya isa ma dan ubansa,yama fara mana.......so kike kisan wacece ni? Sunana Bombee ƴar gidan mlm Ahmadu kuma wacce Goje zai aura nan da wani satin.
Nasan dole dama kunyi mamakin meyasa babana ya yarda da auren koh,bayan yasan tantirancin goje,. Saboda kar tasan kar ce,niba banida daɗi ra'ayina nake bi naci karena babu babbaka,tunda ɗan ki kuma yaɗau kasadar son shiga rayuwata bismillah.
Ni nayi nan sai mun haɗu wani satin kuma Su.....ruuuukkaata DAAYI hhhhhhhhh.
Wai ikon Allah Bombee da suruka kaman mafarki"
Ita kaɗai bayan tagama tujarar tafara tambayar kanta na shaƙiyanci tana bada amsa.
Buta ce a gefen ƙofar gidan,da alama ta jauro ce an cikata da ruwa.
Kallon butar tayi tareda yin bolll da itah ta wajen saitin inda daayi take zaune.
Da sauri kuwa ta matsa ruwan ta zube akan tabarmar,bayan butar ta fashe.
"Karbi wannan kafin nazo ki dunga tunawa karki barshi ya goge innar mijina"
Tana gama faɗin haka tajuya ta bar gidan.
A hanyar fita sukayi kicibis da jauro zai shiga gidan.
Ko kallo na biyu bata sake masa tunda tayimasa na biyu,dan dama ba wajensa taxo ba.
Kai tsaye ta tasamma dajin dayake gabanta babu koh ɗar bare alamar fargaba.
Bujen wandonta ta naɗe zuwa ƙwanji kafin ta nausa da gudu cikin jekin kaman lokacin rana,abin ya haɗu mata biyu,ga sanin jejin ga kuma ganin idonta daya ƙaramata taimakon gani a cikin duhun daren.

"Ahh ke Daayi inata magana nadawo kinyi shuru,sannan wannan yarinya ƴar inace marar ɗa'a,munyi karo da ita amma ko sannu batayiminba ta fita.
Ke indo miƙomin buta nan na wanke hannu"
"Ga nan butar a kusana"
Daayi tafaɗa tana haska masa butarsa wacce Bombee tafasa,duk ruwan yajiƙa tabarmar daayin"
"Ahah wannan kumafah,ko indoce ta jefar ta"
"Hmm surukarka ce ta ta cankofa tun daga hnayar mashiga,itace wacce kake cewa kun haɗu bata kulaka ba"
Nan take Inna daayi ta kwashe abinda Bombee tayimata ta faɗawa jauro.
Jijjiga kai kawai yayi,saidaga baya yayi magana bayan yagama gajeren tunani.
"Hoɗaan wato goje yagamu da gamonsa kenan!"
"Oh hakama zakace jauro,to aradu kuwa tunda tazo tayimin wannan ɗanyen aikin saita zama abin tausayi a cikin gidannan,da nayi niyyar nuna mata soyayya saboda tana matar goje,amma yanzu na fasa,saina koyamata hankali"
"Ahh to ga fili nan kuma gamai dokinnan saura sukuwa muke jira mu kallah,ni bari kiga nayi masallaci kar ayi sallah bandani,da ina faɗamiki ki daina yiwa yarannan riƙon sakainar kashi amma ƙinƙi ji,yanzu gashinan goje ya zame mana Ciwon ido sai haƙuri,sai yanzu da muke son maganin abin kuma Alƙalami ya riga ya bushe.
Sai muzuba sarautar Allah ido kawai mu basu waje muga wacce wainar za'a toya,danni kam dama bani cikin sha'anin zaman sa da wannan yarinya,kece sai yau kikaji labarin ta,ni dama naji labarinta tun ranar da mlm Ahmadu yace wai ya amince ƴarsa ta auri goje,na tabbatar akwai lauje cikin naɗi,dan ruwa baya tsami banza"
"Toh Allah ya kyauta wai rago yasha ƙida"

Cikin sanɗa ta shigo gidan siƙaff siƙaf,har takai bakin ɗakinsu zata shiga taji murya a bayanta.
"Daga ina kike,bana hanaki fitaba tun wancan satin,wai kekam wacce irin yarinyah ce ne,daba dama a faɗamiki abu kiji,kullum idan bakiyi wata tsiyar ba bakyajin daɗine"
Sauke ajiyar zuciya tayi irin ta faru ta ƙare dinnan tunda an kamata,jefar da takalmanta tayi wanda take rikeda su a hannunta.
"Yi haƙuri bazan sake fitaba daga yau shikenan,"
"Baki amsa min tambaya ta ba,daga ina kike a wannan tsohom daren,tukunna ma kinyi sallahr magriba da isha,bata zancen la'asar da azahar ma akeba,wanda bana tunanin kinyi su"
"Wai inna nace miki ina sallah,dukkansu nayi su,isha da magriba ma sukam ƙasaru nayi....."
Tana faɗan hakan tayi saurin rufe bakinta tana zaro ido,ganin su'butar bakin da tayi.
"Ƙasaru wanne gari kikaje da ƙasaru takama ki,kiyimin bayani naji"
"Uh....uhm rugar su goje naje,acan nayi sallah harma naci abinci"
"Rugar su goje,ni ɗiyar nan mai kikaje yi a rugar su goje da wannan daren,kai kai wai nikam mai kikeso ki jawomin ne a wannan rayuwar Bombee,zo nan biyoni yanzu nan,maganar bata waje bace,saikin faɗamin wane halin kikaje kika nuna a gidan surukan ki uhmmm"
Daneji taƙarisa maganar tana tafa hannaye cikin kiɗima da abinda taji Bombee ta faɗa.
"Babu fah abinda nayi,kawai zuwa nayi naji waye shi a wajen innarsa"
"Kuma yanzu dan zakiji waye shi ki rasa mai faɗamiki waye shi sai innarsa Bombee,wannan tsaurin ido damai yayi kama haka?"
Fincikar Bombee Daneji tayi cikin bacin rai suka shiga ɗakinta,jangwabata tayi akan gado da ƙarfi kafin ta zauna a bakin kujera suna kallon juna.
"Gobe za'a fara sha'anin bikinki,kuma daga goben gidannan zai fara samun mutane,banida lokacin yimiki wata muhimmiyar magana,shiyasa dama na yanke yau zan miki. Amma saboda rashin hankali irinnaki tun safe bakya gidannan sai yanzu kika dawo,abinda kikeyi ko na miji bayayin irinsa,ki fice sanda kikaga dama,ki dawo sanda kika dama saikace shikan wawa.
To ki buɗe kunnenki kijini da kyau,Aure ba abin wasa bane,karki ga yanzu kinada ƴan cinki,idan akayi aure komai naki yakoma ƙarƙashin mijinki.
Yi nayi bari nabari,banda musu kuma ƙorafi ko kuma ƙiwuyah. Sannan kiyiwa uwar mijinki biyayya tamkar ita tahaifeki,ki rungumi ƴan uwan mijinki ki nuna musu soyayya,banda shashanci Bombee ina faɗa miki......"
"Inna dare yayi yakamata ki kwanta,ba'ayi aurenba tukunna kike wanann zancen,ina auren kawai akace nayi to zanyi,amma gaskiya sauran abubuwa kuma banyi alƙawarin zanyi yadda akeso ba,yanda nakeso zanyi su.
So ake yayimin abu na ƙyaleshi,shima fah ba mutuncin ne dashi ba,sai a dameni ƙadai,komai ni"
Cikin bacin rai tagama maganar,Daneji tana ganin hakan tace.
"Tashi ki tafi mukwan lafiyah,Allah ya shiryeki"
"Ameen"
Babu buƙatar sake magana bayan abinda ta faɗamata,dan tasan ko tsafi take da baƙar jaba bazatayin ba tunda tace haka.
Abinda aka sakawa lokaci bashida wuyar zuwa,Auren Bombee ya kam kama ka'in da na'in da angonta goje.
Duk da rashin abin hannu da kuma rashin ƴan uwa a kusa na Daneji,hakan bai hanata taka rawar gani wajen gyara ƴar tata ba.
Tun ana sauran ƙwana uku da aure aka farayi mata wankan madarar shanu,sannan kuma takoma ruwan shanta.
Bata zuwa ko ina koyaushe tana ɗaki,abinka da fata dama haka take. Nan da nan tayi wani haske fatarta tana sul'bi da sheƙi.
Ranar Asabar aka ɗaura auren Bombee da goje a masallacin ƙofar gidansu,kan sadaki Dubu talatin lakaɗan ba Ajalan ba.
Babu laifi kuwa ya tara ɗumbin mutane masu shaiɗa daurin auren,kasancewar shima mlm Ahmadu ba baya ba wajen mutane.

To an ɗaura Auren Bombee da goje,sai muce Allah ya basu zaman lafiya.....😀😀😀....


_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼



____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤23🖤




Ana gama ɗaura auren yaji wani nauyi ya sauƙa a ransa,duk da cewar ba haka yaso auren yar tasa yazo ba,amma kuma yaji daɗi ganin ya aurar da ita kafin tagama fin ƙarfinsa.
Yaso tayi karatu tazama wani abu a wannan rayuwa saboda takare kanta,amma kuma kana naka Allah yana nasa,inaga wannan shine tata kaddarar ba wacce yake zata mata ba,fatansa shine allah yabasu zaman lafiya da mijinnata.
A ranar kuma Daneji ta haɗu abun bazata,wanda bazata ta'ba mantawa ba.
Shatu ce tayi mata magana daga ɗaki kan tafito tayi baƙi.
Yayunta ne biyu maza da kuma dadarta wacce take auren ɗan Yayan baffansu da ƴaƴanta itama masu aure guda biyu.
Kasa gasgata ta tayi,dan har ta fito ta tsayah a gabansu gani take kaman idonta ƙarya yake faɗamata gameda bayyanar tasu.
Saida ta tabbatar da gaskene kafin ta fashe dakuka ta faɗawa tayi kam Addar tata,wacce dama kusan ita tarene ta ba innarta ba.
Fillanci aka juyeyi na ɗan wasu lokuta,kafin tajasu ɗakinnata tafara basu labarin abinda yafaru,yawancin labarin ma bata basu ainihin yanda yakeba,ta boyemusu abubuwa da dama.
"Ahh Danen Baffah kene da auren ƴa ohh,aida mai saƙo ya iskemu wai inji mlm Ahmadu cewar za'ayi auren Bombee munyi mamaki sosai"
Kallonsu Daneji tayi da alamar tambaya,mlm Ahmadu kuma? Dama yasan inda suke?"
"Kinga bai san inda muke ba,inaga yatura masu saƙone da dama wani ya iskemu ya fadamana. Da Allah yasama zamu iso akan lokaci kinga ashe damu za'ayi"
"Koma ta ina yasameku gaskiya naji dadin ganinku,ina innatah tana lafiyah"
Shuru HADIZA tayi Addar daneji jin tambayar da danejin tayi mata.
"Kiyi haƙuri Daneji amma inna kam tayi shekara kusan goma da rasuwa,saidai muyi mata Addu'a Allah ya jiƙanta"
Shuru Daneji tayi tareda sunkuyar dakai,sai can kuma tashare ƙwallar idonta tareda ƙaƙaro murmushi,shikenan babu komai,amma da ansamu wani ai yazo ya faɗamin lokacin?"
"Kiyi haƙuri,amma baffah ne yace kar a faɗamiki lokacin,kema ga ga halin kaɗaicin dakike ciki,kiyi haƙuri kiyi mata Addu'a kawai,dan shi take buƙata a yanzu.
Ina Amaryar ne tunda muka shigo banganta ba"
"Gaban Daneji ne yafaɗi,ita kwata kwata ta manta ma da bikin ƴar akeyi,tsabar ganin ƴan uwanta ya kaɗe mata hankali"
Toh fah ina Amaryah manya,bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida.......!!!
Tashi Daneji tayi tanufi ɗakin su Bombee domin ƙiranta.
A kwance take tana taunar cingam irin na aurenta wanda ta zaro kwali guda ba'asani ba.
Babu kowa a ɗakin sai innayi wacce take taya shatu gyarawa Bombee kayanta.
"Addah Bombee a saka wannan ko kin ban shi"
"Ahah ban baki ba,wai wayace ma ki tattaramin kayana ne dukka,cewa aka ce miki bazan dawo na tafi kenan saikace ɗaukar rai"
"Inji waye yace zaki dawo toh,koni kinga na koma gidanmu,canne gidanki daga yanxu,nasakeji kinyi zancen dawo zaki gamu dani,kenan da shekara ma idan na ganki a gidannan zakiga yanda zanyi dake"
Daneji ta amshe maganr wacce shigowarta kenan tazo ƙiranta,shatu tana ta aikin gyaramata kayan dazata tafi dashi batayi magana ba,dan tasan halin Bombee ba ragamata zatayi ba,wanda bai bar iyayensa ba wazai bari kuma.
"Sannu Innar muruje da ƙoƙari,kina fama da ita koh?"
"Uhm lahh ba komai itada ƴar uwartata ne suke gardamar bankwana,zatazo kuma tayi kewarta nan gaba"
"Hmm batada hankali ai,tana girma tana cin ƙasa,wai wannan akayi aure....allah dai ya kyauta kawai,tashi kixo wata innar taki tana ƙiranki,addah ta Hadiza sunzo dasu kawunan ki,harda ƴaƴan ta,addodinki"
"Hmmm yanzun mai yakawosu kuma,duk tsawon lokaci dakikayi kina tunaninsu da kewarsu basuzo ba sai yanzu,mai yahaɗani dasu mai zasumin?"
Bombee tafaɗa tana yatsina fuska tareda tauna cingam ɗin bakinta yabada ƙarar ƙasss"
Duk Daneji takaiwa Bombee a bombom dinta,dan dama a kwance take tayi bake bake akan gadonnata,wanda zata barshi yau.
Saurin tashi tayi tana zumbura baki,tareda gallawa innayi harara wacce suka haɗa ido,da sauri kuwa ta ɗauke kanta,dan tasan tsaff zatayi mata dukan bankwana kafin ta tafi.
"Dallah wuce muje ki gaishesu,ƴan uwannawa kikeyiwa wannan maganar,sauran kuma idan kinje ki nuna musu ban isa dake ba"
Boll tayi da kayan dasu innayi suka gyara kafin tafita daga ɗakin,itama Daneji tabi bayansu yana jijjiga kai na takaici.
A bakin ƙofar ɗakin ta tsayah,saida ta ƙaremusu kallo kafin ta taka ƙafa zuwa shiga ɗakin.
Wata mai kamada innarta fitik ce,saidai tafi innartata ɗan duhu da kuma manyanta,sai kuma wasu mata guda biyu,wanda a kallah ƙaramar ma zata bata shekara biyu a haife. Dukkan su fararrne ƙall jinin fulani gaba da baya.
Murmushi babbar tayiwa Bombee,da alama tanada sanyin rai ba kamar ƙaramar ba. Suna haɗa ido tasake murtuƙe fuska,ita a dole innarta ta daketa akansu.
A kan kujerar ɗakin ta zauna tana binsu da ido ɗaya bayan ɗaya,sai can kaman bazatayi magana ba tace "ina Wuni" a cikin ƙaramar murya.
Yanda ta kalli Addah Hadiza taƙasan idone kawai zai nuna da ita take,shima dan sun haɗa ido da Daneji ne,wacce take bakin ƙofa ta kafeta da ido.
"Lafiya"
Ta faɗa cikeda mamakin Bombee,sukuwa sauran ko kallonsu bata sakeyi ba.
"Su baki gansu bane ko bazaki gaishesu ba?"
"Inna sufa yarane ba iyayena ba,kuma.....kinsan rabona da gaisuwa na daɗe,ni na manta yanda akeyi ma,tunda sun ganni ai shikenan,basu zo lokacin ina kan gaisuwata ba da sun shata har sun ƙoshi"
"Ohh wato kinsan da kina gaisuwar kenan?"
"Nasani mana,lokacin tun shaiɗan yana dan ƙyauye bansan mai nake ba lokacin,amma yanzu kam hmmmm......."
Dukkan su zuba mata ido sukayi kaman sun samu TV,yanda Daneji ta basu labarinta ma har yafi haka.
"Amma Ƴar uwa Bombee kina gani sosai kuwa da yanayin idonki?"
Babbar ƴar Hadiza mai Sunan Bombee wato Maryam ta tambayeta.
"Lalumen katanga kikaga inayi dana shigo?"
"Kinga tashi kije zaure wajen kawunan naki suma ki gaishesu,Dan Allah kuma kiyi aikin hankali,banda shiririta"
"Tom"
Tana faɗin haka zuruff tafice,dama kaman akan ƙaya haka take jinta,gabaɗaya an cika gidan da hayaniya,idan akwai abinda ta tsana bai wuce tarin mutane ba,shiyasa tafi kare rayuwarta a jeji gidan Maharbi Uwaisu. Musamman idan dare yayi halittu suna fitowa kala kala,wasu har wajenta suke zuwan sunyi zaton bata kallomsu kaman sauran mutane,yanayin yana yimata daɗi sosai.
Tun yamma gidan yafara karbar baƙuntar mutane ƴan ɗaukar amarya daga rugar su goje,dan dama su sannan ne bikin zai fara idan dare yayi.
Shirye shiriye aka fara na kaiwa amaryah da misalin ƙarfe 11:30 na dare,hakanma dan mlm Ahmadu ya nuna

Please Login or Register in order to submit comment