Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanke,wannan bai dameni ba,tunda na riga na faɗa mata shikenan"
Da sauri innayi tayi magana cikin muryar kuka kafim inna laari tasake cewa wani abun.
"Ahah inna zan wanke mata kayan idan nadawo daga islamiyya,na iya wanki fah"
Cikin takaici babu yadda zatayi ta jijjiga kai.
Riga da wando tasaka irinna pakistan,wanda mlm Ahmadu yasiyo musu a taraba dayaje kasuwanci,hula da saka kanta kawai,babu hijabi tayi hanyar waje.
"Ke ina zakije haka babu hijabi,dama ba islamiyyah zakije ba naga kinyi wanka"
Daneji ta faɗa,tun dazu sai yanzu tayi magana,dan tasan idan tayi ma aikin banza tayi,an doki kashi.
"Wancan Alwasun yace karna ƙarayin kusada makarantarsa satin daya wuce,nice dama nacigaba da zuwa,saboda akwai abinda nakesom ƙarisawa,yamzu kuwa na gama.
Yawo zanje kawai cikin jeji idan wani abune a aika innayi takirani,tasan inda nake.
A bakin ƙofar gidan sukaci laro da gaji,aikuwa caraf tariƙe kunnen Bombee suka shigo gidan tare.
"Dan bantan ubanki mai kikayi wa bello a fuska,dan tsabar abinnaki yawuce gona da iyaka shine kika yimasa yanka da wuƙa a fuska ko,da nayi haƙuri,amma yanzu kam bazaja sabu ba,kotu zan yi kararku a zo a daureki,abun ai yayi yawa shege da hauka,gabaɗaya a kwanaki kaɗan kin dasawa ƴaƴan anguwa tsagwaron tsoronki?"
Tunkuɗa Bombee tayi a ƙasa a gaban Daneji,har sannan bata bar masifa ba ita ƙarfinta.
Zagi takeyi da uwa ta uba,inda tashiga batanan take fitaba,bakinta har kumfah yakeyi dan masifah.
"Wallahi bazan yarda ba,ku jirayi sammaci a gobe,ƙara zan kai gobe,bama a cikin garinnan ba can Sardauna zan kaiku ƙara kuma da kuɗin tara mai yawa.
Har ina da wannan abun,yaro yana can fuska tayi sumtum idon wajen ko gani bayayi tashi,jiki ya dau zafin zazzabin wahala kamar motace ta bugeshi.
Kuma a goben saita fadawa Alƙali mai tayi masa,daga nafara maganar ɗaukar mataki jikinsa zai fara rawa,yarinya ƙarama tasakashi a cikin asirinta,dolen uwarki ma idan kikaji wahala zaki kunceshi da kanki"
A haka tagama faɗan ta son ranta tafita ta bar Daneji ta sharar ƙwallar baƙinciki,hararar Bombee tayi wacce zaune a ƙasa idonta a soye kaman faɗan ba'a kanta akayi shiba.
Ɗakinta tashige tafara ribzar kuka kozata samu ta huce da suyar da zuciyarta take mata.
"Mtswww ji yanda ta batamin kaya kuma tasaka innata kuka,aradu zanyi maganinki ne,bar ganin ki tuleliya bai dameni ba"
A hankali tayi maganar tana tura baki,kafin tajuyah tabar gidan,ta nufi inda tayi niyyar zuwa tun farkon barinta gidan.

Sallama Daneji tayi a gidan gaji da sassafe washagari,dan dama sunyi magana da mlm Ahmadu da daddare akan zataje sasanto gaji kan abinda yafaru.
Wata ƙatuwar tukunyace akan murhu ann ɗumame yara zasuci su tafi makaranta.
Ga gidannan duk tarkacen kayan wanke wanke.
Faɗa gaji take rabawa tsakanin Zulaiha da yayarta akan kunun wai,fa'izah taɗau Zulaiha bayan itace na ashirin ta siyo bana talatin ba.
Sallama Daneji ta cigaba ta kwararawa amma har yanzu gaji bata jitaba,saida wani yaro yakirata tukunna kafin tajuyo takalli danejin.
Ɗan alamar tsorone akan fuskarta amma tayi saurin kawar dashi tareda ƙaƙalo murmushin dole.
"Ahhh Daneji kece sannu daxuwa,ga kujera zoki zauna a zubo miki ɗumame"
"Ahh nagode ma,an tashi lafiyah ya gidan"
"Gida kalau,lafiya naganki da sassafe haka,hala dai mutane gidan kalau"
Abinne yabawa Daneji mamaki har takasa boye mamakin nata akan fuskarta.
"Uhm gaji nace ba,akan zancen kaiwa kararnan nazo,dan Allah a ƙara haƙuri,a sansanta cikin rufin asiri,kaiwa kotun bashida daɗi.
Mlmn ne ya turoni nasake baku haƙuri,sannan za'a biya kuɗin maganin inyaso".
"Laah karki damu bakomai fah,faɗan yarane dabaka iyarmusu,babu komai yawuce bazai sake faruwaba,ki faɗawa mlm Ahmadu bakomai ya wuce baza'a sake ba"
Kasa jure tantamarta tayi,hakan yasa ta tambayi gaji mai yafaru.
"Amma gaji dan Allah mai ya faru naga kin sanja daga iya jiya,ina fatan dai hakan bayada nasaba da Bombee koh"
"Uhm Daneji kibar zancennan dai kawai,amma tunda kin matsa saƙo daya nakeso ki kaimata,dan Allah ya kice mata ƴaƴana bazasu sake shiga harkarta ba,itama ta taimaka tafita daga rayuwar mu,kowa hadu da daidan sa a yanzu"
Baki sake cikeda mamaki Daneji ta baro gidan gaji,a hanya babu sakar jakin da batayiba akan shin mai Bombee tayiwa gaji da ƴaƴan ta kuwa,kodai zancen mutane dagaskene kai,kai anya kuwa,in akwai wanda yasanta to bayana ne ai,kuma a sanina da ita bata tsafi bare nace shi tayi musu,to mai yake faruwa?
Tana cikin hakanne ta isa gida,zuwa lokacin rana ta fito yara sunata tafiyah makaranta,suma su Bombee sun shirya zasu tafi makaranta.
Daneji bata 'baata lokaci ba takama hijabin Bombee tareda janta cikin ɗaki.
"Maza maza ina jinki yimin bayani mai kikayiwa gaji naga ta sanja a dare guda?"
Ɗan murmushin dama nasan haka zata faru tayi,kafin ta jijjiga kai.
"Ni babu abinda nayi musu mai zanyi musu"
"Bombee ki faɗamin gaskiya mai kikayiwa gaji take haka,tabbas akwai wani abu,kuma kece kikayi ba kowa ba"
"Inna baki yarda dani ba ne?"
"A da kenan,amma vanda yanzu dakika sauya daga yanda kike"
"Eh to ba wani abu bane babba,kawai dai na ɗan leƙa gidansu ne da daddare nayi musu gagarɗi"
"Gargadin me,ke ƙarama dake zaki iya bawa wannan ƙatuwar matar gargaɗi,ai koni ban isa yimata kashedi ballantana ke,ki faɗamin mai kikayi musu Bombee,ni yanzu kin fara bani tsoro da halayyarki"




............Daren jiya..........


Karfa labari ya gundureku kunga an tsaya a waje guda ɗaya,komai da sannu ake warwareshi.
Dafatan zakuyimin hakuri dai....😏😊😊😊.






🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are




____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤19🖤





A zaure mlm ya hadu da Bombee tashigo gidannasu,shikuma zai fita sallahr magriba.
Kallonta yayi na ɗan sakanni kana ya jijjiga kai,inda duka da faɗa suna yin aiki,da sunyiwa Bombee a ƴan watanninan,amma abinnata gaba gaba ma yakeyi kaman ana watsawa wuta fetur.
Shuru tayi taji mai zaice,saidai ga mamakin ta,waucewa yayi batareda yace mata komai ba,sauƙyƙyƙyiyar ajiyar zuciya tasaki,dan dama hakan takeso kada yayi mata maganar.
Kao tsaye ɗakinsi ta wuce tacire kayan jikinta,ta canza wasu daban,sallah tayi kafin tafito wajen cin abinci..
Ƙwanon nata abincin ta ɗauka a gaban Daneji wacce take zuba miya akan tuwon dawar da sukayi.
"Hmmm wai ke bana mijiba,amma saiki saka kai kifice daga gida sai magriba ki dawo,idan kika saka masa ciwon zuciya ya mutu ai saiki nemi wani uban koh?"
"Inna daga yau bazan sake fita da yamman ba,nagama fitan yamman dama yau"
"Ohh duk maganar da akayi baki dainaba saida kikaga dama tukunna,kenan bama bacin raina ne ba yanaki fitar,gama fitar kikayi?"
Shuru tayi bata amsawa innartata maganarta ba,inda wani ne dai da yanzu ya karbi amsa.
Cikin dare can misalin ƙarfe sha ɗayah Bombee ta tashi innayi wacce tayi nisa cikin Bombee.
"Ke dallah tashi ki rufe ƙofah ta ciki zan fita"
"Amma addah in baba yakamaki watarana kina fitar darennan fah,ko shiyasa kikace kin daina fitar yamma kin dawo ta dare?"
"Ina ruwanki toh,sauran naji ko wani zance mai kamada shi,saina babballaki a gidannan"
Gadon Bombee innayi ta kalla,inda ta haɗa tsummokara kaman itace akai a kwance,saboda ko baba zai iya leƙosu cikin dare.
Tashi tayi tabi bayan Bombee ta rufe ƙofar bayan ta fita.
Baƙaƙen kayane a jikin ta riga da wando sai hula,rufe idonta tayi kafin ta buɗe su a duhun gidannasu,ga gari yayi baƙiƙƙirin abinda da damuna.
Dan murmushi tayi ganin idonnata yamayar mata duhun zuwa haske,tarau take gani kaman safiya.
Kama katangar gefen ɗakinsu tayi ta ɗale kaman biri.
Kai tsaye gidan su bello ta nufah,nan kam bata tsaya bata ƙarfinta wajen hawa katanga ba,ta ƙofa tayi shigowarta,kasancewar ba ƙyaurene dasu ba,wani ɗan buhu kawai aka saka a bakin ƙofar gidan.
Tumaki suna kwance a tsaƙar gidan ta tsallekesu ta wuce ɗakin gaji.
Ƙyauren ta tura a hankali,tayi sa'a kuwa babu sakata,dan tsabar rashin tsoro duk barayin da ake fama dasu a garin amma ko sakata basu da ita a jikin gidansu.
Gaji ce a kwance ita malm idi akan gadon,ƙasansu kuma ƴaƴane guda uku anyi musu shimfiɗi suna bacci.
Babu abinda yake tashi a cikin ɗakin sai ƙarar gwartin gaji da kuma idi,ƙaremusu kallo Bombee tayi a duhun ɗakin,tareda yamutsa fuska tana toshe hanci,hamamin damuna da warin fitsari ya haɗu da ƙarnin jikinsu,da kuma warin bakinsu da miyar kuka yabada wani irin mummunan wari mai tada zuciya.
Kai barina gama abinda yakawoni nabar ɗakinan,irin wannan wari haka?"
Tsallaka wa tayi kansu tareda hawa kan ruwan cikin gaji,wacce take ɗaya bangaren akan gadon.
Cikin bacci gaji jin an hau ruwan cikinta tafara cewa.
"Kaifah mlm tsiyata dakai kenan,banda jaraba bakada aiki,yaushe ma kayine dazaka sake dawowa,so kake saika tsamamin jiki nakasa sana'ar gobe koh"
"Ba mlm ɗin bane buɗe i donki kiga waye"
Ihu gaji taso kurmawa lokacin data buɗe ido taga Bombee akan a zaune.
Kafin tace wani abu ta tura mata zanin data ɗauka a tsakar ɗakin.
Wuƙar Daneji ta zaro a kunkuminta ta mannawa gaji ita a wuyanta,wacce dama tun jiyan take kaifata,tayi kaifi sosai sai ƙyalli takeyi.
Wani yawun tashin hankali gaji ta haɗiye muƙutt tana zazzare ido.
"Tashi mijinki yanzu nan,sonake nayi muku kashedi kiji shima ya ji,kuma idan kikayi ihu saina girba miki wukar nan a wuyah,zanga dawane kan zaki dafa abincin siyarwar gobe"
"Dan Allah karki girbamin wannan wuƙar,ki bari tsaya yanxunnan na tasheshi,m...alllammm malam ka tashi"
"Uhn menene kike tashina ne,banace miki idan akayi ruwa bazani masallaci ba,ki bari da safe zanyi sallahr"
"Dallah ba sallah bace,in sallah ce ina ruwana dakai,kabarinmu ɗaya,sanda lawakiri yake tafkarka mai ya dameni,wannan rayuwata ce,katashi ka gani ni lusari kawai"
Idonsa ya buɗe yana rarraba ido,tareda lalumo fitila gefensa ya kunna.
Wani madoki ya ɗakko a gefensa tareda buge Bombee dashi saida ta faɗa ƙasan gadon.
sai a lokacinne gaji ta tashi ta zauna tana maida numfashi,.
"Ahh mlm ashe kai jarumine bansani ba,yaudai kayi abin kai,kullum ina cewa kadaina kawomin madoki ɗaki,ashe dai zayyi amfani"
"Me yarinyar nan take a ɗakinna da wannan dare haka"
"Ina zansani nikuma,yanda ka ganta nima haka na bude ido na ganta a kaina ta saka min wuƙa a wuyah"
"Wuƙa kuma mekika mata haka"
"Ina zan sani,inaga danna yiwa innarta kashedin zamukai ƙarane shiyasa,da Alama kasheni tazoyi"
Suna cikin maganar ne Bombee ta tashi ta tsayah tana jujjuya wuyah inda mlm idi ya ɗan sameta.
Hasketa yayi da fitilar hannunsa,take kuwa idonta yakama hasken fitilar,lokaci ɗaya shima yakoma tamkar fitilar dan haske.
Murmushi Bombee tayi jin yanda suke bada sautin mamakin abinda suka gani,amafani tayi da hakan ta wafce fitilar da take hannun mlm idin.
Maida hasken tayi kansu tana enjoying tsoron dayake kan fuskarsu,wanda yake sauƙar mata da nishadin a cikin ranta.
"Hhhhhhh daga kallon idona harkun razana dayawa haka,ohh dama duk gulmar da kuke yaɗawa akan idonnawa na mayune,bakuma gama saninsa ba.
Wani abun dazai ƙara baku mamakin shine,bakwa tunanin yaakayi na fito daga gidanmu da wannan duhun har nazo nan batareda fitila ba......saboda inagani a duhu tamkar rana.
Mai zai faru idan na kashe fitilar ni ina gani ku kuma bakwa gani,sannan kuma ga wuƙa a hannuna?"
Tana gama fadin hakan kuwa ta kashe fitilar ƙitt,duhu ya gwauraye ɗakin,wani irin ɗurar ruwa cikin gaji yayi,sai karkarwa take tana hada gumi.
"Hmm baban Zulaiha ka ajiye wannan itace takake saitawa,ohhh baka yarda dani ba danace ina kallonka,ko na fara faɗamaka a duk lokacin daka motsa,ko kuma idonka ya ƙifta?"
"Wannan ƴa kekuwa mutum ce?"
"Nima ban tabbatar ba tukunna,saidai ku kunriga kun yanke hukunci ai,cewa ni mayyace ina koh?"
"To ina wani abu kike,meyasa kika tsallake gidaje dayawa kika shigo mana nan,mai muka miki,sannan mai kike nema"
"Hhhhh abu daya kuka min sannan abu biyu nake nema.
Innar Zulaiha taje har gida taciwa innata mutunci,dan kawai narama abinda ɗanka bello yayimin,har tana cewa zatakai kotu.
Abinda nakeso shine ta fasa kaiwa ƙarar nan,sannan kuma babu ita babu gidanmu,idan su bello sukayimin abu kuwa babu mai hanani ramawa.
Wannan shine abinda nake nema,inkuma naga sabanin abinda na nema,zan dawo watarana,inna dawo kuwa duk ɗakinnan sai yankaku kuna bacci baku sani ba,kuma bazan bar shaidar ninayi ba,ko an kamani ma kukam kun tafi ai"
Ta karisa maganar tana dariyah.
"Munji hakan ma bazata faruba aniyarki tabiki,dan Allah kuma ki ƙyaleni nida ƴaƴana,yau na yarda ke wacece kam"
"Yarjejeniya ta ɗauru,ni barina tafi gida kar a gane bana nan"
Tana faɗin hakan ta fita daga ɗakin,hankalin ta kwance aikin ta ya kammala.


An dawo labari.........


Tunda wanann abin yafaru babu yaran dayasake tsayawa a hanyar Bombee,komai ta fadawa yaro da sauri yake yi babu bata lokaci. A da itace ke shan azaba a wajen yara,amma yanzu tashi ɗaya ya juyah itake zaluntarsu,idan yayanka ya daketa tasake kamaka ta dakaka,haka za'ai tayi har sai kahana yayannaka da kanka,uwar ɗa ma idan taga abin yaƙi dole ta zubawa sarautar Allah ido.
A makaranta kuwa tana shiga aji zayyi tsit,lokacin da takejin yin magana haka zata saka su suna bata labari,idan bataga dama ba babu wanda ya isa ko motsin kirki yayi a ajin.
Ta daina jarrabawa,karatu kam da su jinga ba'a magana,bata komai saidai tazo ta zuba tantirancinta ta tafi gida.
Bata cikin prifect ɗin makarntar,amma hatta head boy saitaga dama yayi abu.
An sha kaita office ɗin head master za'a koreta. Haka zata ce idan aka koreta saita bunkawa office ɗinnasa wuta da daddare,haka dole suka rabu da ita,a samu a tama gama kowa ya huta.
Shiyasa maganin hakan kowa ya daina shiga harkarta,take cin karenta babu babbaka.
Shirye shiryen fara exam ɗin common akeyi a makarantar su,tun waccan shekarar tayi da ƴan ajinsu bata ciba,hakanne yasa mlm Ahmadu sakata akan tasake jarrabawar,yayi niyyar makarantar kwana zai kaita kowa ya huta,shima ya huta da karbar ƙararta,dan abin ƴar tasa yazama sai zubawa sarautar Allah ido. Suje can suyita mata horo kowa ya huta.



Forseen


........"kee Bombee yanzu dan zabar baki ɗaukeni da daraja ba,ashe dana sakaki kije ki zana jarrabawar bakiyi ba,kika cemin kuma kinyi?"
"Danajene an gama shiyasa"
"Hmm to shikenan,ki rubuta ki ajiye,aure zan miki kawai na huta dake,tunda kinƙi karatu saiki tafi gidan miji?"
Ƴar dariyar tayi irin bata ɗauki maganar da ɗumi ba kafin tace.
"Aure kuma baba wai niɗin?".

😁😁ya kukace toh mutanen bombee?😁😁





____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤20🖤






"Nayi wa headmaster ɗinku magana,kan cewar zakije kosake rubuta common,tunda wancan din sun bata miki ita saboda tantirancinki,na roƙeshi ya yarda,dan haka ki shiryah kije ki rubuta,idan kinci zan turaki makarantar kwana"
"Baba waini bokonnan dolene ne,duniyar ma fah takusan tashi kowa yasan inda zai shiga"
"Yanzu duk abinda nayi haka kika ce,wai tukunna ma kinji mai nacene.
Idan duniyar ta tashi ai irin bakwa cikin rabo,ki faɗamin wane abin arziƙi kikeyi guda ɗaya da za'a shaideki da ita"
Yamutsa fuska Bombee tayi tareda tashi daga tabarmar mlm Ahmadu.
"To shikenan baba zanje nayi jarrabawar tunda haka kakeso,babu matsala"
"Yawwa uwata kin kyauta,gwanda kiyi karatu hakan zaifi kyau"
Tundaga wannan zancen mlm Ahmadu yayiwa headmaster maganar jarrabawar tata,ranar daza'a yi kuwa ta shiryah tasaka uniforma ɗin da mlm Ahmadu ya ɗinka mata,dan cewa tayi fafur bazata saka tsoho ba wanda aka aro mata a anguwa.
Dole sai sabon akayi mata,idan tasaka saita bawa innayi shi.
Fitowa tayi daga ɗakinnasu ranar jarabawar,tasha sabon uniform da sandal da safa,sai goge kayan take da handkerchiep kaman gaske,kayan kuwa blue Burberry ne yayi mata kyau sosai.
A bakin ƙofar gida ta hadu da mlm Ahmadu yana zaune a majalisar dattijai,nufarsa tayi tana bubbuɗawa,kana ganinta kasan anyi marar ji,ga kyau irinna maciji.
Sallama tayi a wajen tareda tsugunnawa a gavan su.
"Baba zan tafi jarabawar,a bani kuɗin cin abinci,dan sai yamma nadawo"
"To shikenan kokefah uwata,hakan ai yanada kyau sosai,maza ki rubuta mai kyau saboda kiciyo makaranta mai kyau,nasanki da ƙoƙari dama"
Ɗari biyar ya ɗauko a aljihunsa ya damƙawa Bombee,tasa hannu biyu ta karba tareda yin godiya,kafin ta juya ta tafi.
"Ahh ikon Allah anya kuwa itace?"
"Mlm Audu baban su muruje yafaɗa yana jijjiga kai"
"Ita ce mana,girma ne yafara zuwa an fara hankali"
Mlm Ahmadu yafaɗa ɗauke da murmushi akan fuskarsa,saboda jin daɗin yadda Bombee ta nuna hankalin nata a gaban dattijan. Addu'a yayi a ransa akan Allah yasa tacigaba a haka.
A bangaren mutuniyar kuwa tana shan kwanar gidannsu maimakon ta ɗau hanyar gidansu sai tayi hanyar jeji.
A hanya tashiga wani gini ta sanja kaya,daganan kuma tayi cikin jejin kanta tsaye.
Tadaɗe tana tafiyah a cikin jejin kafin ta iso wani gida a dokar jejin.
Hayaƙin dayake tashine mutum zai gane cewar akwai mutum a ciki.
Sallama tayi a bakim ƙofar gidan,muryar wata mata ce ta amsa mata dattijuwa.
"Bombee kece da hantsinnan,shugabannki baya nan yashiga jeji ɗazu"
"Gabas yayi ko yamma?"
"Ahah Bombee bazaki bishi ba ke kaɗai kina mace,kinfi ni sanin bayason kina shiga cikin dajinnan ke kaɗai batareda shi ba"
"Haba Inno har yanzu na,babu indan bansani ba a jejinnan,bariki gani"
Tun kafin wacce aka ƙira da inno tace wani abu Bombee ta nausa cikin jejin da gudu.
Gudu takeyi ta hanyar gabas maso kudu a cikin jejin,daga yanda take gudun tana tsallake itatuwan da suke kan hanya mutum zai tabbatar tasan takan hanyar gaba da baya.
Catt taja ta tsayah tanacikin gudun,kaman wanda wani yabata umarnin hakan.
Shuru tayi na wasu ƴan mintina tareda rufe idonta na ɗan wani lokaci.
Sunkuyawa tayi har saida ta fadi a ƙasa,mashin dayazo ta samanta kuma yah caki a jikin bishiyar gefenta.
Tashi tayi tareda yamutsa fuska tana duba bayan rigarta da lakar wajen ta 'bata mata.
"Haba shugaba,kasa na bata rigata a cikin wajennan"
Wani mutum ne mai tsantsan jiki,farin bafulatani ne,amma kana ganinsa kasan ƙaƙƙarfane sosai,duk cewa shekaru sun fara nunawa akan fuskarsa.
Dariya yakeyi tareda tafa hannyensa alamar jinjinawa.
"Da kyau ashedai bakya training a banza,menene yasa kika biyoni cikin daji,sannan ya akayi kikasan ina nan"
"Uhm na karbo kuɗin siyan nima kwari da bakata,tsawon lokaci ina tara kudi yau nagama tarawa.....tabb har yanzu bansan inda zan sameka ba,yau fah litinin,nasan dama tanan zaka iyo ai"
"Hmmm da alama ba iya idonki ne yafina sauran mutane fah harda jinki da kuma tunaninki,kinyi ƙoƙari dakika kaucewa harina,ya akayi kika lallami Babanki har ya baki kuɗinnan"
"Uhm bani yayi na siyah kayan kwalliyah,shine na taho nan"
"Meyasa bakya son yin abinda iyayenki suka ce toh,kullum ina faɗamiki kinada lokacin sanja ra'ayi akan bin hanyata,saboda ke macece ba namijiba"
Shuru Bombee tayi baya amsa masa ba,shima dama yasan bazatayi maganar ba,duk sanda yayi mata maganar tasanja ra'ayi.
Abu ɗayane yasa bai koreta ba shine,yasan idan ya korata gida ma bazata haƙura ba,zatabi wata hanyar ne inda babu mai kallonta ballantana ya kulada itah. Shikuma haka kawai yake jinta a ransa kaman ƴar sa wacce shi Allah bai bashi ba.



______****______***_____


Tun ranar da jarabawar su Bombee ta fito yake ta jelen wajen dubawa jarrabawar sa.
A zuwansa na ukune gidan headmastern,ganin abin yazama haka ya faɗamasa gaskiyar abinda yake faruwa.
"Mlm Ahmadu nasan kanason maryam (Bombee)tayi jarrabawa domin tayi karatu,amma fah ita ba karatunne a ranta ba,dan dama haka mukayi ta fama da ita lokacin tana gabanmu,tayin wani lokacin sati ma zatazo makarantar ba,duk lokacin data zo kuwa ba iya ɗalibai ba,mukammu saita caja mana ƙwaƙwalwa.
Badan mutuncinka ba dama bazata gama a makarantar muba korarta zamuyi,to yanzu ma zancen danake maka batayi jarabawar taka roƙa tayi ba.
Ko mai kama da ita bamu gani ba a wajen jarabawar,dan haka saikaje ka tambayeta da kanka.
Amma karka ce nina gaya maka,dan tace sai tayiwa ɗana duka idan na faɗamaka bata zoba,saboda nasan zata aikata yasa nayi shuru. Amma ganin yanayin daka shiga yasa na faɗamaka"
Yana gama faɗawa mlm Ahmadu haka yakoma cikin gida yabarshi a tsaye.
Haushine ya kama mlm Ahmadu jin abin Bombee tayi masa,wato dan iskanci babu wata makaranta da taje,shine harda karbar dari biyar babu ko kunya taje ta kashe.
Hanyar gidannsa ya nufa yana saƙawa yana kuncewa. Dabb dazai shiga gida dabara ta faɗo masa. Murmushi ganin yasamu mafitar tunanin dayake ciki.
Yana shigowa gidan yau ko sallama bayyi ba idonsa ya sauƙa kan Bombee,wacce taketa wurga sakwarar da inna laari tayi musu da ranar.
Daneji da Laari kwanonsu ɗaya tare suke ci,sai innayi kwanonta daban itama Bombee haka,da farko tare sukeci,tashi ɗaya Bombee ta tada tsiyah sai an raba musu kwanon abincin.
Masifah mlm Ahmadu yafara,ta inda yashiga batanan yake fita ba,kana ganinsa kasan ransa ya baci sosai.
"kee Bombee yanzu dan zabar baki ɗaukeni da daraja ba,ashe dana sakaki kije ki zana jarrabawar bakiyi ba,kika cemin kuma kinyi?"
"Danajene an gama shiyasa"
"Hmm to shikenan,ki rubuta ki ajiye,aure zan miki kawai na huta dake,tunda kinƙi karatu saiki tafi gidan miji?"
Ƴar dariyar tayi irin bata ɗauki maganar da ɗumi ba kafin tace.
"Aure kuma baba abokaina ma fah ba amusu aure ba?".
"Su suna da hankali,sun ɗauki iyayensu da mutunci,sannan kuma dasuka sakasu makaranta sunyi,basuyi taurin kai ba kamar ke,dan haka ko kinƙi ko kinso aure zan miki da ɗan gidan Jauro da suke ƙauyen gefenmu,BUBA,dama yace yana sonki nace karatu zakiyi,shima kuma ɗan tijarane kaman ke,saiku haɗu kuyi da rayuwa tare har lokacin nutsuwa yazo muku.
Ke kuma saiki fara shirye shirye,nan da wata ɗaya zansaka bikin,yanxu haka ma wajensa zan nufah"
Yana gama faɗin hakan ya kaɗa babbar rigarsa ya nufi waje.
Daneji takai lomar abinci bakinta,bata ƙarisa taunata ba ta tashi a wajen cin abincin,abin duniyah duk ya isheta.
Zama tayi a bakin gadonta tayi shuru tana kallon tagar ɗakin,rayuwar ta a baya tafara tunawa,yanda ta taso a gidansu cikin kulawa da kuma gata.
Bata taba tunanin zata tsinci kanta a irin wannan rayuwar ba,da farko batayi tunanin yin aureba ba acikin danginsu ba. Haka ta wayi gari tana wajenda babu danginta ko ɗayah,idan wani abu ya sameta,batada kafaɗar dazata jingina tayi kuka,har yau ta gagara sabawa da kaɗaicin datake ciki.
Aka zo zuwa lokacin data samu ciki,farincikine ya kamata,ko ba komai zata bude ido taga jininta a gefenta. A haka tafiya tayi tafiyah lokacin guda ta buɗi ido ta kalli ƴar ta kuma jininta a hannunta,a sannan tayi tunanin wahalar ta yanke zata raini ƴar ta cikin gata da soyayya kaman yanda ta samu,Saidai bata saniba ashe tsugunne bata ƙare ba. Sai ƴar ta tazo duniyah ta wata halitta taban,wanda tun a lokacin ta fara hangon irin ƙalulabalen dazasu fuskanta itada ƴar tata,musamman daya kasance cewar dama bakowane ya yarda da ita ba,kullum cikin zargi take akan ita mayyace.
Cikin dadi da babu daɗi ta raini ƴar tata har zuwa girmanta,a tunanin idan ƴar ta jure wahalar yarinta watarana sai labari.
Tashi ɗaya sai rishe ya juye da mujiya batareda tayi zato ba,sai yazamana abinda take gudun shiya afku.
Wato ƴar tata tayi nasara buɗe shaiɗanin dake cikin jikinta,wanda sukayi iya ƙoƙarinsu wajen binneshi a jikinnata.
Maimakon zaluntarta da yara sukeyi,sai ya zamo yanzu yaro idan bata ga dama ba ko fita daga cikin gidansu bai isa yi ba.
Abinda take gudun a ƙira ƴar ta dashi yanzu ya gauraye bakin mutanen garin.
"MAYYAH HATSABIBIYA"
To bayan wancan kuma ga wata sabuwar itama ta 'bullo,auren rashin gata mijinnata ke shirin yiwa ƴar tata,duk da tasan laifin na ƴar tata ne,amma kuma zuciya babu ƙashi,takasa daure hakan a cikin ranta.
Yanzu fargabarta ma ɗaya shine,shin Bombee zata yarda ta zauna a gidan auren idan ayi mata,babu abinda ya canza a halittar jikinta na ƴan adam ta take fuskantar haka,inaga kuma ita a wani yankin daban.




____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤21🖤



Bombee ce tashigo ɗakin,ta iske innar tata zaune cikin tunani,batasan mai take saƙawa ba,amma tasan bazai rasa nasaba da auren da baba yake shirin yimata ba.
"Inna......inannnaaaa"
Zabura Daneji tayi tareda ɗagowa ta kalli Bombee wacce take tsaye akanta. Alamar itama damuwa ce akan tata fuskar,don duk abinda take bata son kuma abinda zai saka innarta cikin damuwa,musamman idan yazamo wani ne taban yayi sanadiyyar hakan,kowaye shi saitayi maganinsa.
Kasancewarta ba babba ba,amma tana maganin manyan ta hanyar baraxana akan ƴaƴannasu,dan ta kula mutanen agwagine,basu san komai ba sai soyayyar ƴaƴan su.
"Inna ki daina wannan damuwar haka,indai akan wannan aurenne ni zan iya sakawa a fasashi idan bakyaso"
"An zo wajen,ba auren dazai miki ne abin tashin hankali na ba,ke abinda zakiyi a aurenne abin tashin hankalina"
"Kaman yaya inna,taya zanyi shuru amin wai aure,wazai ganni yace nakai aure,ni babu abinda nasani akan wani aure,dan haka kuma bazanyi shi ba"
"Kinga koh,do wannan ne yasakani damuwa ba aurennaki ba,inkinason farincikina kuma ki daina ganin dakuwa ta,to ki dunga jin duk abinda babanki ya umarceki dashi,bana son kinayi masa musu akan abinda yasakaki"
"Hmmm nifah bawai inason yimasa gardama bane,kawai ni banson duk abinda nakeso shikuma yahanani,abinda bana so kuma kullum shi yake sakani,ni bana so

Please Login or Register in order to submit comment