Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kam,tabbas yayi murna ta haihuwar innayi sosai,amma kuma har yanzu soyayyar Bombee a ransa ta dabance,don ko boyewa baya iyayi,abin kwanciyar hankalin ma shine inna laari batada dakuwa da hakan sosai,ita indai tana son ƴar ta shikenan.
Ranar daya gane inna laari bata son Bombee ta dunga kusantar innayi abin yabaci haushi,hakan yasa ya ƙirasu dukka a turakar sa,kallonsu yayi cikin kulawa kafin yace.
"Uhm uhm toda farko dai inason yimuku ƴar nasihane.
Duk garinnan babu wanda baya yabonku a zaman lafiyah,amma kuma sainaga abinda ya batamin rai,shine kuna ƙoƙarin raba kan ƴaƴanku da kakanku,musamman daga bangarenki Laari,kuma wai kece babba,hakan bai dace ba."
"Mlm kayi haƙuri,gani nayi data tabata ranar haihuwarta tayi kuka,kuma sannan larai tayi min kashedin na kiyaye"
"Saboda ita larai ɗin itace tafiki sanin yakamata,idan akwai abin citarwa a jikin Bombee kaman yanda mutane ke faɗa,ke ya kamata ki rigasu sani. Dan Haka dan Allah karku bari wasu su ruguzamin zaman lafiyar gidana,ku haɗa ƴaƴan ku ku rainesu tare,su tashi cikin ƙaunar juna"
Tundaga wannan lokacin inna laari ta daina abinda take,dan har ƙiran Bombee take tasaka mata ita akan cinyarta. Wannan abin yayiwa Bombee dadi sosai,don sakawa tayi a ranta wataƙila lokacin yayi da innarta tace za'a dunga bata itah.

Shigowa tayi da gudu tareda ɗanewa mlm Ahmadu wanda yake zaune a kan tabarma yanajin rediyo.
"Baba nayi ta ɗaya a makarantar Mlm Alwasu,kagama ya bani biscuit,sai mu raba nida innayi koh"
Tafaɗa tana nuna mlm Ahmadu allonta cikin murna"
Hannunta yakama wanda Allon yake tareda share ƙasar dake kan ciwon wajen,wanda yake fitar da jini.
Cikin tausayawa ya kalleta tareda cewa.
"Wannan kuma uwata a ina kikaji,faɗuwa kikayi?"
"Ahah su bello ne suka tureni akan itace suna cewa 'mayyah taci na ɗaya',baba wai sunana mayyah?"
"Ahah ba sunanki mayyah ba,mai kika ce musu toh"
"Ban kulasu ba,kawai cewa nayi idan ban ramaba Allah zai ramamin,yanda inna tace na dunga faɗa"
Kanta yadafa cikeda tsantsar ƙauna kana yace.
"Hakane uwata,hakane ɗiyar albarka,wanda aka zalunta bai ramaba Allah zai saka masa,kinyi daidai kinji,haka nakeso ki kasance kullum,ina alfahari dake uwata,Allah ya albarkaci rayuwarki"
Duk abinda suke su inna laari suna kallonsu,suna gyaran ganyan shayin mlm Ahmadun.
Sai bayan sun gama taɗinsu irinna uba da ƴa kafin ta nufi wajen su danejin ta nuna musu.
Kafin daga baya ta miƙawa innayi nata biscuit ɗin.


*forseen*
..............Babu wanda yake sonki,kifara son kanki,duk wanda ya ɗaga miki hannu ki karyashi,ke ba sa'ar su bace,muna tare dake fansa fansa fansa
Shuru tayi tanajin maganar da sheɗaniyar muryar takeyi a cikin kanta.!!!.................




🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are









____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]






*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________







Page 🖤16🖤







Saka ƙafa yayi yaƙara takata a ƙasa haɗeda cije baki.
"Faɗamin ina so ki amsa cewar ke mayyace,baƙar mayyah babu abinda ya dace dake sai duka dakuma hantara,kar ma ki sake gigi cigaba da zama a ajinmu.
Kunkoroki munyi miki komai amma kinƙi barin ajinmu ko,saboda ki nuna mana halinki na mayu,to idan muka koma gobe naganki a cikin ajinmu sai dakaki"
"Zulaiha ce taƙarisa faɗin hakan,ƙanwar bello abokin sule.
Da Bombee a primary 5 A take,saboda yanda suka maidata kaman jakarsu,yasa mlm Ahmadu yaroƙi alfarmar a maidata primary 5c.
To shiɗinma ajin su Zulaiha ne ƴan anguwarsu,duk yanda Bombee take iya koƙarinta wajen ganin ta ƙauracewa masu cutar da ita,abin yaci tura,kullum cikin fuskantar ƙalubale take.
Fatarta tayi baƙiƙƙirin,banda tabon izayar da mutane sukeyi mata babu komai a jikinta,tun tana kuka tana kaiwa Danejo kukanta har ta daina,ganin babu wanda zaima dubeta ballantana yaji kukantan ko kuma tausayinta.
Mata biyune a tsawon rayuwarta suke dubanta da idon rahama,daga Inna shatu mahaifiyar muruje sai kuma Innarta. MURUJE shine wanda takejin daɗin zama a kusada dashi,to shikuma yatafi boarding karatu,shekararsa biyu kenan da tafiyah.
Ɗago fashashshiyar fuskarta tayi tana kallon zulaiha,wacce tsayah akanta da hijabinta a ɗaure a kunkuminta tana rawar masifah.
"Ƴar gidan mayyah,daina kallona da wannan idanuwannnaki,kurwa ta kur in faɗamiki"
Tashi tayi tafara kaɗe uniform ɗinta tareda sake kallon Zulaiha.
"Menene kalmar mayyar nan da kowa ke bina dai tane,wane yaro naci a garinnan da wanann sunan yadace dani,hmm ke innayi zo mu tafi gida kar a ga mundaɗe bamu dawo ba"
Kama hannun innayi tayi wacce take tsaye da jakkunnasu a hannunta,ita ajinta biyu a primaryn,dan haka duk abinda ake bata saka baki,duk da itama wani lokacin tana karbar nata dukan,a matsayinta na ƙanwar Bombee.
"Idan kika kuskura kika bita,kema saina miki duka,inaso ki kalli cikin idonta ki faɗamin wacece Bombee"
Hannunta ta cire daga na Bombee tareda kallon idonnata.
"Uhm mayyace"
Zaro ido Bombee tayi jin sunan da ƙanwar tata taƙirata dashi itama,abinda tunda take bata tana zaton zataji ba,tun tasowarta bata san komai ba sai soyayyar ƙanwarta ta,a ganinta ko kowa yaƙita ita bazata juya mata baya,saboda ita jininta ce,shiyasa wani lokacin idan yara sunayi mata tsiyah fuk yanda zatayi takan kare ƙanwartata,amma kuma yau abinda taji daga bakin ƙanwartata ya kwance mata ƙwalkwalwa fiyeda tunanin mai tunani.
"In.....nayi kema .....mayyah kike ganina kuma .....dodanniyah?"
"Hhhhhh da alama bakisan mai ƙanwar taki take ba koh,to koda kinje wani waje kin buyah ita take zuwa ta faɗamana inda kike,komai da saka hannunta,mai kike tunani zaki samu wanda sai kareki wai ..........ke ba mutum bace,babu wanda zai yarda dake,ko uwarki ma nasan ba sonki take ba,dan haka idan zakiso kanki kiso kanki"
Rufe ido Bombee tayi gam,lokaci guda kanta yafara wainawa,wani tururi mai cikeda baƙin duhu yafara tasowa daga cikin kanta zuwa sassan jikinta.
Gabaɗayah abubuwan da akayi mata tsawon rayuwar ta tafara tunowa,duk lokacin da aka zalunceta babu wanda taba rama mata.
".....ni mayyace,babu wanda yake sona,dole naso kaina kuma na ɗau fansa........babu wanda zan ragawa daga yau koshi waye........sai na ɗau fansa.......saina rama"
Tunanin cikin kantane yafara cuɗanyah yana zama duhu,yayinda lokacin guda tunanin ta yatashi daga positive zuwa negetive.
Tafi minti biyar tana sauraron zugon da wata shaiɗaniyar murya take yima ta a cikin kanta,kana daga bisani ta buɗe idonta.
Sauƙeshi tayi akan Zulaiha wacce tayi shuru tana kallon ta tun sanda ta rufe idonta.
Zaro ido Zulaiha tayi ganin idon Bombee ya tashi daga Blue mai haske zuwa blue mai duhu,sannan kuma ga wani murmushi akan fuskarta kaman baƙin aljani yafito daga wuta.
Ja da baya tafarayi ganin tana tunkaro ta,cikin murya mai ɗauke da muradin ɗaukar fansa tafara magana.
"Bakince ni mayya ce ba,sannan kuma kinbani amsar dogon tunnain dana daɗe inayi a rayuwata,shine naso kaina babu mai sona.
Daga yau nafara son kaina,kuma babu mahaluƙin daya isa hanani ɗaukar matakin duk abinda wani yayimin.kema .....kuma a yau banga shegen da duk faɗin gembu zai ceceki a wajena ba,saina yimiki ƙasa ƙasa anan wajen"
Daidai da lokacin data gama maganar ta iso kaman Zulaiha,tamkar ƙaramar baƙar kububuwa.
Hannun Zulaiha ta kama tareda juyata ta baya,babu bata lokaci kuwa ƙashin hannunta na dama yabada ƙarar 'ƙarallll'
Bata barta iya haka ba ta bita duka ta ko ina kaman an aikota,tun Zulaiha tana kuka har ta daina sai nishi take kawai na wuyah.
Wani babban mutum ne zai wuce yakalli abinda ya faru,da sauri kuwa ya isa wajen ya dauke Bombee daga kan Zulaiha,wacce idonta ya rufe da muradin ɗaukar fansa.
Faɗa mutumin yafara yiwa Bombee,amma ko kallonsa batayi ba ta fisge jakarta daga hannun innayi tayi gaba.
Baki ya saki galala yana kallon yarinyar da ko kaɗan bata ɗaga ido,yau itace ta gallah masa harara hmmmm.
Juyawa yayi kan Zulaiha wacce take kwance sai zuba nishi take kaman mai shirin haihuwa.
Ɗaukarta yayi a kafaɗa ya nufi gidansu da ita.

"Haba gaji haba gaji,yau ki duba kigani,wai abinci kike rabawa,nan Robar kashice yara sunyi ba'a zubar ba,suma kuma ba'a wanke musu ba.
Ga ƙwanukan wanke wanke tun safe ƙuda yake bi amma ba'a wanke ba,sai yanzu da za'a raba abincin kafin ake wankewa ra ruwan ana zubawa.
Wai yaushe zaki gyara ne idan baki gyara yanzu ba?"
"Haba mlm nifah ka dameni ehe,kullum faɗan yau daban na jiya daban na gobe daban,baka ganin banida lokaci ne iyae,dawa zanji,dakai zanji ko kuma da ƴaƴan ka koda sana'a ta.
Da ciyar damu ya ishemu mana,idan ka wadatar damu aiki ya ragumin saina gyara,amma aikin banza babu zuciya sai shegen surutu,to karka dameni ni"
Tana cikin masifar ne kan gari ya gari sukaji sallama a wajen.
Mlm idi dama neman hanyar zillewa masifar Gajin yake,dan haka da sauri ya fita wajen.
Bai daɗe ta fitaba sai gashi ya shigo hannunsa riƙeda Zulaiha rai a hannun Allah yana salati.
"Ya ilahi gaji kinga fah,yanzun nan wani bawan Allah yaganta a hanyar makaranta ƴar gidan mlm Ahmadu ta hau kanta sai dukanta takeyi."
"Naaa shiga uku ni gaji,yau mai zan gani haka,ai wanann mayyar yarinyar,ko ba itaba kai?"
"Eh itadai,da farko nima saida nayi mamaki,yarinyar dako magana bata cikayi ba,wai itace tayi wannan aikinta.
Sai yacemin dayayi mata magana ba harara ta zabga masa tayi tafiyarta"
"Kai malm dubafah hadda karayah tayi mata,kan ubancan ni kuwa zanga shegen dazai rabani da su,shari'ah daga nan har gaban sarki,banza na haifawa ƴar dazata mata wannan aika aikar"
Tunda suka kamo hanyar gidan Bombee batace komai ba,itama Innayi bata kulata ba,tunda taga abinda tayi koh jerawa da ita taƙiyi.
Lokacin da suka shigo gidan ma Bombee batayi sallama ba,iya Innayi ce kawai tayi a ƙasan maƙoshinta.
Inna Daneji ce take rarraba abinci,yayinda inna laari kuma ta fito daga banɗaki ɗauke da buta a hannunta,shikuma mlm Ahmadu yana alwala zai tafi masallaci.
"Yau ma faɗan kuka sakeyi koh,waye kuma ya dakeki yau"
Daneji ta tambayi Bombee tana cigaba da aikinta,kana ganin fuskarta zaka hango tsagwaron tausayin ƴar tata,amma kuma bata da ikon yin komai akai.
"Ahah ba wani ne yadake ta ba,itac........"
Tun kafin innayi taƙarisa magana Bombee ta ɗauketa da mari tassss.
"Munafuka kawai,dankinga nayi shuru ban kulaki ba shine har kika samu bakin magana koh,kisake cewa wani abu saina yimiki fiyeda nata,kuma daga yau kika sake yin munafurcina a ko ina ne saina yanke miki baki"
Tana gama faɗin hakan tayi hanyar ɗakinsu tareda barin innayi a tsaye a tana kuka ta dafe kuncin.
Kowa daga cikin mutanen gidan,baƙaramin kaɗuwa yayi ba da abinda yafaru,babu ma yah Daneji wacce take ganin shikenan ta faru ta ƙare,komai ya gama faruwa.
"Ke innayi mai ya faru faɗamin"
Saurin jijijjga kanta tayi jikin yana karkarwa.
"Baba bazan iya faɗaba,tace zatayimin irin abinda tayiwa Zulaiha,baba wannan ba addah Bombee bace"
"Naji to kekuma mai kikayi mata taƙiraki da munafuka uhm"
Nan ma shuru innayi tayi kanta a sunkuye,da alamar rashin gaskiya a fuskarta.
"Ki fadamin mai yasa tace miki munafuka"
"Uhm dama.....dama....nice nake faɗawa su Zulaiha inda Bombee take idan suna neman ta"
"Meyasa kike faɗamusun toh,waye yace ki dunga faɗamusu,sune suka sakaki"
Girgiza kai innayi tayi,tareda ƙara sautin kukanta,hsr mlm Ahmadu ya buɗe baki zayyi magana inna laari tayi saurin katseshi tareda yin magana,dan dama tun sanda Bombee ta mari innayin tafasa shiga ɗakinta.
Tabbas kana kallon fuskarta zata tabbatar bataji daɗin marin da Bombee tayiwa ƴar ta ba,amma haka ta daure tareda cewa.
"Mlm yanzu dai duk wannan bashine abun yi ba,yakamata aji ita tabakin Bombee mai yake faruwa,saboda bata taba shigowa gida a haka ba.
Ke kuma innayi shiga ɗakina ki sanja kayan,karkije inda take yanzu saita huce.
Jijjiga kai mlm Ahmadu yayi tareda numfasawa,da alama ya yarda da abinda inna laarin tafaɗa.
Duk abinda ake Daneji batace komai ba,ta lume cikin kogin tunani,sai daga bayane ta tashi ta nufi hanyar ɗakin su Bombee.


.........mai zata gani??!!!!!😲😲😲.
Ku biyoni muje mugani gobe.......






🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are









____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]






*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________







Page 🖤17🖤






Jikinta sanyi kalau tashiga cikin ɗakin su Bombee,domin batasan mai zata ganewa idonta ba,saidai duk da hakan tana fatan Allah yasa karta ga abinda zuciyarta take raya mata.
Labulen ɗakin ta ɗauke ta rataye ,hasken rana yashiga ɗakin,domin yabawa ɗakin ishashshen hasken dazata ganta dakyau.
A kwance take ta rufe idonta kaman mai bacci,saidai kana gani kasan ba baccin take ba.
"Bombee"
"Na'am ta amsa a dake"
Shuru Daneji tayi kaman mai nazari kafin ta zauna a kusada ita.
"Shin menene ya farune kika sanja a lokaci guda,duk abinda akayi miki nasha faɗamiki kiyi haƙuri,karki bari bacin rai ya sanja miki rayuwa,abinda kikayi kimsaka mu damuwa gabaɗaya,so kike kijawo mana magana.
Yanzu inaso ki faɗamin mai kikayiwa Zulaiha danaji innayi tayi maganar?"
"Karya mata hannu nayi,sannan kuma nayi mata duka kaman yanda itama tayimin,sannan bandamu ba tacemin mayyah,amma ke tacewa mayyah,sannan tace inna isa nanuna ina son kaina,shiyasa na nunmata ina son kaina ɗin"
"Me Bombee karya mata hannu kikayi,wai nasan gaji bazatayi shuru wannan zancen ya tafiba saita ɗau mataki"
"Tsawon lokaci ai nima Zulaiha tana dukana baki taba cewa komai ba,shine ita danna rama saita ɗau mataki,to ta ɗau matakin mana"
"Kee Bombee yaushe kika fara yin maganar manya da wannan rashin ladabin haka,karki dauki wannan halin ki saka ranki,hakan babu kyau musamman ga mace"
Cikin halin damuwa Daneji tafara yiwa Bombee nasiha dajan hankali. Tun bayan kwana uku dama ta kulada yanda Bombee tafara sauyawa,koyaushe tana cikin fushi,abu kaɗan idan akayi mata saita ɗaukeshi da zafi,sannan idan abun mugunta yafaru tafi kowa dariyar mugunta.
Jiya da ragon mlm Ahmadu ya sunkuci inna laari a kunkumi,data fara dariyah har faɗuwa saida tayi,sabanin da da idan hakan yafaru saidai tayiwa mutum sannu.
Tun a lokacin Daneji tafara kula dacewar ba lafiya ba,kwana tayi tana sallah da daddare,tareda kaiwa kukanta ga Allah,akan Allah ya kare mata rayuwar ƴar tata.
Muryar Bombee ce tadawo da ita cikin tunanin data tafi,wanda hakan yasa tayi zumbur ta kalli Bombee,wacce take kallonta da mamakin wane tunani take haka.
"Inna nasan kina iya ƙoƙarin ki wajen nuna min rayuwa,sannan kuma keda baba ku kaɗai kuke nunamin so kaman yanda iyaye kewa ɗansu,nasan kuma kin kulada canzawa ta a yanzu wanda nima naji,saidai babu yadda zanyi inaga yanxu ne yanda nake,ba yanda kuke son na zama ba dafarko.
Bazan boyemiki ba,amma daga yanxu kaff garinnan samun zaman lafiyar yaro shine kar yashiga harkata,bazan iya yimiki alƙawarin zan ƙyaleshi ba"
Tun kafin Daneji tabawa Bombee amsa taji sallamar gaji a cikin gidan,wacce tajita dumm a ƙirjinta kaman ganga.
Har ta fita tadawo wajen Bombee tareda yimata gargaɗin akan karta kuskura tafito komai taji.
"Salamu alaikum ina mutanen gidanne ina ta raraka sallama,ehh zakuyi shuru mana sabo dodanniyar ƴar ku taje zata kashemun yarinya a banza. To bilahillazi bazan yarda ba,ko ni ko ku ne a cikin garinnan,mlm Ahmadu yazo yanzunnan yabani kuɗin ɗori da kuma nasiyan magani"
Tana cikin zazzaga masifarne Daneji tafito daga ɗakin su Bombee tana kallonta.
Tsayawa tayi bata ce uffanba har saida gaji takai ayah a kan masifarta tukunna.
"Naji duk abinda kikace gaji,haƙika yarinya bata kyauta ba,amma inshaaallah za'a ja mata kunne,dan Allah ayi hakuri a sasanta a hankali"
"Sasanto? Ke kika sanshi nibansanshi ba,yanzu haka ma nasaka mlm idi ya nufi gidan mai anguwa yafaɗamasa,dan baza tabs yarda ba,wannan abu ke keganinsa ƙaramar magana,amma a wajena tafi dutsen dala"
"Haba gaji,menene na kaiwa ƙara kuma,abunnan fah yara ne suka aikata ba masu hankali ba,kuma inshaaallah zan ja mata kunne bazata sake shiga harkar ƴar ki ba daga yau"
"Hmmm ke kuma tashafa,nidai sai an biya kuɗi a radu,kuma wlh zata fito waje ai saina saka an babballamin ita,gayyar tsiyah kawai"
Tana gama faɗin hakan taja tsuka tareda yin hanyar zaure,zaninta a hannun sai kuncewa yake tana gyarawa.
Kafafun nan furuuru,kana ganinta kasan daga gaban murhu ta taso.
Sai wajen goshin la'asar kafin mlm Ahmdu ya shigo gidan,suna can wajen mai gari kan case ɗin karayar da Bombee tayiwa Zulaiha.
"Sannu mlm ka dawo?"
"Eh sai yanxu muka samu ƙurar ta lafah"
"To Allah ya kiyaye ta gaba,ka basu kuɗin gyaran ina?"
"Ban basu ba,cewa nayi bazan bada ba ai tsautsayine,sannan kaff anguwar nan babu wanda bai san irin izayar da ƴayan mlm idi ke ganwa Bombee ba tun tana ƙarama,haka mukayi shuru muka kauda idanuwan mu,sai yanzu kuma dan tayiwa ƴar su ace nabada kuɗi,suma suje suyi jinyarta suji idan da daɗi"
"Amma mlm bakace haka ba,kafi kowa sanin irin hatsarin dake tattareda yarinyar nan idan zata dunga ɗaukar hukunci,bai kamata muyi shuru bamuyiwa tufkar hanci ba,saboda da alama tafara warewa daga yanda muka tukata"
"Zancenki haƙƙune,amma to yakike ganin zamuyi,mlm Alwasu yariga ya faɗamana akan kar mu kuskura mu koma gareshi,amma zan leƙa ta wajensa nayi masa bayani,wataƙila bazai rasa wani abu dazayyi mana ba"
Shuru sukayi jugum kowa yana saƙa abu daban a ransa.
Saida aka ɗauki kwana uku ana case ɗin Zulaiha da Bombee kafim abin ya lafah,itadai an barta da ciwon hannu,babu damar zuwa makaranta.
Yanzu Bombee ta ɗan samu lafiya a wajen yan ajinsu. Tunda ga wannan lokacin Bombee ta daina kula kowa,koyaushe harkar gabanta take,makaranta ma ba hanya ɗaya suke bi da innayi ba,da alama inna laari ta gargaɗeta akan karta dunga shiga harkarta.
Saida akayi darasi ɗaya aka sakeyi kafin Bombee tashigo ajin,da alama wani wajen tabi ,dan tunda wuri innayi tashigo makarantar.
Batayiwa kowa magana ba ta nufi wajen zamanta,haɗa ido sukayi da Zulaiha wacce har yanzu hannunta yana saƙale da wuyanta.
Wani mungun murmushi Bombee tayiwa Zulaiha,mai ɗauke da gagarɗi a tareda.
Aikuwa da alama saƙon ta dake son isarwa ya isa inda takeso,don lokaci guda jikinta yafara rawa,tayi saurin sunkuyar da idonta.
Bombee tana zama taji muryar malaminnasu yana magana.
"Ke Bombee tashi ki fita daga ajinnan,dan iskanci sai yanzu kike zuwa makaranta"
"Kayi haƙuri mlm,innata ce ta aikeni,kuma anyimin horon makara a waje"
"Babu ruwana da wannan horon,ki fitamin a aji yanzu nan,dama ana faɗan ke hatsabibiya ce ashe dagaskene,dolema ki bar makarantar nan"
Kallon mlmin Bombee take,tareda yin tunani a ranta. Kenan shima dama baya ƙaunarta kaman sauran mutane,saboda tanada ilimi shiyasa yake kulata ashe,duk wannan tsawon lokacin kallon hatsabibiyah yakeyi mata.
"Shikenan mlm zan fita,amma kaman yanda na aikatawa Zulaiha yauma zanyiwa Abdul ɗan nursery 3 a hanyar tafiyah,inya tambayeni menene dalili saina ce jawo maka akayi.
Yanzu hakama idan na fita ƙiransa zanyi muyi wasa a can gefe"
Zaro ido malamin yayi jin Bombee ta ambaci sunan ɗan sa dayake ji dashi,yaushe yarinyar nan tazama haka?
Ya faɗa a ransa,zaman sa lafiya ya rabu da ita,idan takaryawa abdul ɗinsa hannu yau ya zaiji.
"Ahah babu komai koma kiyi zamanki ma,basai kin fita ba"
Jijjiga kai tayi tareda faɗaɗa murmushinta kana ta zauna.
Kamo hanyar gida tayi ita kaɗai,bata da abokiya ko kuma aboki,iya ƙanwarta ce,itama kuma anrabasu tun ranar da abinnan yafaru,bazata iya cigaba dajanta jikinta ba,bayan tasan basonta take ba.
Maganar bello taji a bayanta,wanda hakan yabata mamaki,musamman da taji da ita yake,rabonta dashi tun sanda yayi mata duka wancan watan.
"Ke ki tsaya a inda kike,hhhhh bantaba zaton yanda kike har zaki iya karya wani ma,waninma ƙanwata,ke wacece face dodanniya abar kawarwa. Bakiyi mamaki ba daban tareki ba kaman ko yaushe a hanyar gidanku,gaji ce ta hanani sumar dake tun wancan lokaci,saboda abinda kikayi yana sabo,amma yanzu zanga wazai ƙwaceki a wajena,mutuwa ma zaitayi shakkar ƙwatarki yau a wajena,saina saitamiki notin dayake son kuncewa a cikin kanki.
Duk maganar dayakeyi Bombee batace masa uffanba,sai binsa kawai take da idonta a duk lokacin dayaje ya zagayota.
Abinda bai kuladashi ba shine,yanzu idonta a tsaye yake babu alamar tsoro ko firgici sa'banin da,da yanzu ta tsugunna tana bashi haƙuri.
"Ohh ashe naga da alama har ƴar jarumta kika samo koh?"
Toshe hancinta tayi da hannunta tareda cewa.
"Banta'ba kulaba sai yau,ashe kai mungun ƙazami ne,bnada ɗoyi babu abinda kakeyi,ga baki a dafe kana yaro ƙarami ka fara shaye shaye,shayeshayen ma na ƙananan ɗan iska,banza shashasha."
Daga bellon har su sule shuru sukayi suna kallon Bombee,wacce ta kafe bello da ido tana zubamasa magana babu alamar tsoro.
Hannu ya ɗaga ya zanga mari mari a fuska.
Haka tayi ƙiƙim bata matsa daga inda take tsayeba,tofar da yawun dayake bakinta tayi mai haɗe da jini.
"Waifah irin wannan marin kakemin da sainaji tsoronka koh,ashe ma bakada ƙarfi,duk yunwa da sigari ta cinyeka,amma bari kaji nawa yayake?
Tun kafin yagama haddace mai tace a ƙwaƙwalwarsa yaji wani mari a kuncinsa,ba iya marin ba harda wani zafi daya jiyarceshi a wajen.
Tangal tangal yayi kafin yasamu ya cake,hannunsa yasaka a wajen tareda zaro ido lokacin dayayi arba a hannunsa,jinine jajur a hannunsa.
Hannayenta biyu ta saka a wuyansa,ta nutsa faratanta a wajen.
Ihu yasaka iya ƙarfinsa saboda ciwon daya ziyarceshi.
"Banfara ɗaukar mataki ba saida nashiryah,ko babban mutum idan yanason cin galaba a kaina bazai iya ba ballanta ku ƙananan ƙwari,kusaka a ranku bazaku iyah cin galaba a kaina ba ko kaɗan,mai son gwadawa kuma ga wajenan,mai tsoro ka fasa"
Sakin wuyannasa tayi,ta barshi a tsugunne yana tarin wahala,kan kaceme jini ya wanke gefen rigarsa inda ta karzamasa zanen faratunta.
"Ana zugaka shugaban yara,nibanga sarauta anan ba,dan haka na karbi sarautar daga yau,ko kanaso ko baka so ka bani matsayinka,Sannan babban jan kunne kar kowa yasake ɗagamin yatsa cikinku,idan kunji kun tsira"
Tana maganar tana fita cikin murya kaman ba tata ba,sannan kuma tanayi tana wata irin dariyah kaman shaiɗaniya.
Kallon sule tayi wanda tun ɗazu ya jefar da bulalar take hannunsa ta dukan Bombee ɗin.
"Ka tahomin da jakata gida,sannan duk wanda yakeda niyyar ɗaukar mataki akaina shima kada ya fasa"
Daga haka ta bar lungun ta nufi gidansu.







🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are









____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]






*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________







Page 🖤18🖤





Wulgawar Bombee innayi tagani tana cin abinci, yaukuma ta dawo da wuri.innayin tafaɗa a ranta,kullum sai yamma liƙis take dawowa idan ta tafi makaranta,wani lokacinma sai dare yayi tukunna.Sau uku mlm Ahmadu yana kamata yana dukanta,amma ko kuka batayi,sannan kuma bata faɗi inda take zuwa ba,sannan kuma bata fasa kaiwa daren ba.
"Inna Daneji Addah Bombee tadawo tana ɗakinmu"
"Yauɗin kotaji magana babannku kai,amma a wanne yanayi tashigo"
"Uhm hannun duk jini har ya bata mata uniform ɗin jikinta"
Innayi ta faɗa a hankali,cikin sigar gulma,saboda kar addar tata tajiyo ta,aikuwa Alƙalamin ya ƙarye,dan duk maganar da takeyi a kunnenta sarai.
"Jini kuma wanne iri,yauni kuwa mai zangani a duniyar nan,hadda jini"
"Ahh toh Bombee ai tazama abinda tazama sai du'a'i,ke kuma ban hanaki shiga harkarta ba ne,sai tazo tana dukanki koh"
Inna laari tafaɗa tareda zabgawa innayi harara,yanzu kowa yasan inna laari haushin Bombee takeji,saboda a rana idan ta duka innayi yafi a ƙirga,wani lokacin ma wai dan kawai ta kalleta,a wajen kwanciya kuwa wajibine saita yi mata na bacci. In abun bai zo ba kuwa saitayi sati bata kulata ba.
Hanyar ɗakinnsu Daneji ta nufah tareda tsayawa akan Bombee,wacce take zaune a tsakiyar gadon ta bawa ƙofah baya.
Zaro ido Daneji tayi data kalli yatsun Bombee,dan dama su tazo gani domin da ta tabbatar da zancen innayi,aikuwa hakane farcenta zaƙo zaƙo duk jini a jikimsu tamkar faratun mayu,yaushe ta tara wannan faratun haka babu wanda yasani.
"Bombee menene haka a hannunki kaman jini,na wanene?"
"Jinin bello ne,yatareni zai ɗau fansar abinda nayiwa ƙanwarsa,nikuma na yanka masa fuska da farcena"
"Yanzu dan yazo ɗaukar fansa saiki yanka masa fuska,bazaki kawo ƙara ba gida,kinkuwa san hukuncin hakan"
"Nasani kuma babu abinda ya isa yayi daga shi har iyayensa,idan aka sake nima zan sake,batun nakawo ƙara kuma menene amfaninsa,shin tunda nake an taba ramamin idan wani ya zalunceni,saidai a bani haƙuri zancen ya wuce,dan haka ni gaskiya bazan sake yarda da wanannan tsarin ba,dole na kawo nawa tsarin nima".
Dan takaici Daneji bata sake cewa komai ba,saima fita da tayi tabar ɗakin,abin yafi ƙarfinta yanzu kam.
Fitowa tayi daga ɗakin tana miƙa tareda yin hamma,ruwa ta ɗiba a bokiti tashiga banɗaki tayi wanka. Lokacin data fito innayi tashiryah cikin kayan islamiyyarsu da jakarta a hannu.
"Ke wato ina jinki kina gulamata ɗazu koh,idan kin dawo daga makarantar ki wankemin kayana,idan basu fitaba kuwa........hmmmmm bazan ƙarisa ba"
"Bazata wanke ba idan ke kika haifamin ita,ko wankin kayanta banfara bata,amma ke kin fara bata naki dan mugunta"
"To karta

Please Login or Register in order to submit comment