Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tasake rungume ƴar ta a jikinta,tareda sunkuyar dakai,ji tayi kaman ƙasa ta buɗe ta nutse ciki,mai aka ɗauki ƴar tane,bayan zuwanta duniya su kaɗaine suka san lalurinta,yau ɗaya wata tagani harta tozartasu. Shin itama ba uwa bace da ɗa a hannunta,bata kunyar yiwa wata uwar haka a matsayinta na uwa?
Suna cikin hakanne ana ta hayaniya malm Ahmadu ya dawo wajen,inda ya tarar kowa yana nuna Daneji wacce take zaune kaman mujiya ta rungume Bombee.
Bankaɗe mutane yayi ya isa gareta,tareda tambayar ta mai yake faruwa.
Zayyana masa abinda yafaru tayi cikin ƙaramar muryah mai cikeda damuwa.
Aikuwa cikin tunzura ya juya ya kalli matar,wacce take tsaye tana zayyana yanda taga idon Bombee.
"Uhm malama na tambayeki mana,shin wannan da kike riƙeda shi ɗanki ne?"
"Eh ɗanane mana"
"Idan ace misali lokacin dayazo duniya sai kika kulada cewar gashin kansa korene,sai kike saka masa hula a koyaushe idan zaku fita waje,to ƙwatsam watarana sai wata mata itama mai ɗa,ta fara nuna ɗanki a bainar jama'a tana cewa.....wannan ɗan mayene ba mutum bane,dukkan mutane sai suka yi caaa sai sun ga ya ɗanki yake,wasu ma har zakinki suke.
Ita kuma tana tsaye a gefe tana sake bayyana yanda ɗanki ba mutum bane,shin ya zakiji a ranki a lokaci?"
"Meyasa kayimin wannan misalin,amma dai amsa a bayyane take,yanda nake son ɗana zanji tamkar ta daba min mashi a cikin zuciya,sannan zanji baƙin ciki a matsayinta na uwa bata gani ba take tozarta nawa ɗan"
"Alhamdulillah kinbawa kanki amsa,to waccer matar da kike tozarta ƴar ta fah,ita yazataji a ranta?.
Ita ɗin matata ce,yarinyar da kike ƙira kuma mayyace,ƴata ce ita ɗin,haka aka haifeta watan baya da kalar nata halittar idon,shin akwai mayen da ake ganeshi ta halittar idone,dan kawai ƙwayar idonta shuɗine sai aka ce itaba halittar Allah bace?.
Ita kin muzanta tata yarinyar,kuma sannnan ko kunya bakyaji kina tsaye kina ƙara maida bayanin,a matsayinki na uwa kuma tirrrr da halin wasu matan"
Malam Ahmadu yana gama faɗamata hakan ya nufi inda Daneji take sunkuye tana kuka.
Yayinda ita kuma kowa idonsa yakoma kanta,itama ta sunkuyar da nata kan cikeda kunya da nadamar abinda ta aikata.
A hanya suna tafiya malm Ahmadu yasamu waje ya faka mashin ɗin.
Itama Daneji ganin hakan yasa ta saƙƙo daga kan mashin ɗin tana kallonsa.
"Wai yaushe zaki bar wannan kukan iyee,shin kukanne magani komai,tun yanzu ma kina kuka inaga idan ta girma tafara shiga mutane fah,idan ta shigo gida an ƙirata da mayyah kuka zakiyi kaman yanzu?"
Jijjiga kai tayi alamar ahaha,sai can kuma kaman bazatayi magana ba tace.
"Mai likitan yace toh,sannan meyasa muka taho"
"Yace zuwa yanzu bazayyiyu muganshi ba,sannan ni daga ganin abinda ya faru nafara tunanin inaga abin bana asibiti bane,saboda babu wata jinya da yaro ke zuwa da irin wannan ido,nafi kyautata tunanin shafen aljanu ne,dan haka gidan Malam ALWASU zamu je,ya duba yaga koda maganin dazai iya bamu."
"To shikenan hakan ma yayi,nima dama bana tunanin abin asibitine wannan,bata kuka fah sai dare yayi,sannnan ............."
"Sannan me inaso ki fadamun mai kika gani bayan nan"
"Idan .....idan na haska fitila ko zan ɗauketa.....sainaga idon yanayin haske a cikin duhu,kaman idon kuliya ko kura idan an haska da daddare"
Cikin kiɗima mlm Ahmadu yazaro ido,jin abinda Daneji ta faɗa,tohhhh ikon Allah.
"Maza maza hau kan mashin mu tafi asibiti,wannan ba abune daza'a zauna ba,tabbas dagaji aikin aljanu ne"
Tafiya mai nisa sukayi kafin suka iso ƙofar gidan mlm Alwasu,tundaga bakin ƙofar gidan mutum yana gani yasan gidan mutanene rabi bokaye rabi kuma suna fakewa da harkar malantaka.
Almajiraine a ƙofar gidan birjik sunata karatu,sai ƙofar gidan a tsakiya,daga can kefe kuma wani ɗan zaurene na kasa,an lanƙaya su jajayen ƙyalle a jiki da baki,kowanne anyi masa rubutun larabci,duk maitarka baka isa faɗin mai aka rubuta ba.
Wani yaro suka tasa daga cikin masu karatun,tareda tambayarsa inda Mlm Alwasu yake.
"Kai ina mlm yake?"
"Yana cikin zaurensa suna ganawa da hajiya,zaku iya jira ko kuma ku dawo idan an jima"
"Ahah bari mu jirashi ba matsala,ku cigaba da karatu koh"
Suna nan tsaye wacce aka ƙirada hajiyan tafito daga cikin zauren. Tabbas Hajiya kam,dan itace mai neman kujerar chairman na Sardauna LGA a lokacin.
Ƙarisawa su mlm Ahmadu sukayi suma daga ciki,domin kaiwa tasu buƙatar.
Shiga sukayi tareda zama akan buzun dayake gabansa.
Har kusan tsawon mintina biyar da zaman su amma bai ce musu komai ba,yana zaune a inda yake ya rufe ido,hannunsa kuma ɗauke da wani zankaɗeɗen carbi yana ta ja.
Abinne yabasu mamaki,wanann ya kalli wanann wannan yakalli wannan.
Mlm Ahmadu ne ya buɗe baki zayyi magana,dan yafara ƙosawa da zaman,saidai tun kafin ya buɗe baki mlm Alwasu ya katseshi ta hanyar ɗaga masa hannu.
"Hmm karkace komai,barina gama da wannan tukunna"
Saida yagama ɗin kafin ya buɗe idonsa akan su.
"Inajinku yanzu mai yake tafe daku,na raka Hajiya ne ta addu'a har saida tabar yankinnan,shiyasa kuka ganni nayi shuru,amma yanzu ina jinku"
"Allah gafarta mlm dama lalurine yasamemu na aljanu,yarinya ce aka haifeta,amma kuma sai tazo da wani irin ido kaman na karashiya,sannan innarta gata tacemin bayan launin idon,har haske yake irinna kuraye idan aka haska da fitila da daddare,kuma kwana take bata bacci kullum.
Kaga kuwa wannan ba aikin kowa bane sai aljanu,shiyasa mukazo koda taimakon dazaka taimakemu dashi"
Ƙarisa magana mlm Ahmadu yayi ta sigar roƙo a wajen mlm Alwasun,wanda yayi shuru yana jin bayani.
"Miƙomin yarinyar naga mai yake damunta,tabbas daga bayaninka kam abin yayi kama dana aljanu,saidai shikansa shafen aljanu kala kala ne,bazamu gane wanne daga haka ba."
A jiye yarinyar yayi akan cinyarsa,tareda dafa kanta sannan ya rufe idonsa.
Ya daɗe a haka can ya buɗe ido da ƙarfi akan su mlm Ahmadu,hannunsa rawa yakeyi da kuma bakinsa,sai can kuma ya tsime kaman bashi ba.
"Tabbb tabbas abinda kuke tunani hakane,yarinyar tana ɗauke da baƙaƙen aljanu masu haɗarin gaske,saidai ba a jikinta suke ba,ajiya sukayi a cikin idanuwanta,shiyasa suka sanja kala,kuma take gani tamkar irin na aljanun"
Bazai yiyu mu iya cire ajiyar ba batareda mun tsire idon ba,saidai amma zamu iya 'boye ajiyar a jikinta,ta yanda bazasu tuno da ajiyar ba har abada,ta hakane zasu manta da lamarin su barta tayi rayuwarta.
Saidai da sharaɗin karku dinga barta kullum cikin fushi,sannan kada ku barta takai farmaki akan komai,daga lokacin da tayi ƙoƙarin buɗe wanann ajiyar da kanta,to fah kuma babu komawa da baya,dole saidai ku sallama ta,domin zata kasance tamkar mabuɗar bala'i a gareku.
Sai ku zaba shin ayi aiki ko kuma kar ayi?"
Tsuru tsuru su mlm Ahmadu sukayi,suna jin bayanin da mlm Alwasu ya basu,dama su tun wuri sunyi tunanin aljanu ne gareta,biri kuwa yayi kamada mutum,yau ya zasuyi a wannan duniya ta maliki yaumiddini.
"Mlm a boye ajiyar dayake jikinnata,zamu yi ƙoƙarin rainonta akan kartayi fushi kokuma shiga damuwa,bazan juri ganin an ciremata ido ba gaskiya,tunda dai kace bazasu san inda take ba to inaga hakan ma yayi"
Daneji ce tafaɗa tana matse guntun hawayen dayake idonta.
"To shikenan tunda kun zabi hakan za'ayi aikin daya tace,akwai maganin dazan baku yanzu a dunga zubawa a ruwan wankanta,sannan kuma dana turare wanda za'a dunga yimata da daddare.
Bayan sati ɗaya kuma zaku dawo ayi yanka ayi sadaka,sannan ayi anihin aikin daza'a boye ajiyar jikinnata"
"Mungode mungode Mlm Allah yasaka da Alkhairi,yanzu kenan nawane kuɗin abin sadakar"
"Abin sadaka sai nan da kwana bakwai idan nagama aikin,yanzu za'a fara shirye shiryen haɗa duk abinda ya dace"
"To shikenan mlm muzamu tafi,sannan za'ayi yadda kace,sai nan da zuwa ranar bakwai ɗin"
Daneji ce ta karbi yarinyar wacce take bacci abinta daga hannunta mlm Alwasu suka tafi"
Sai bayan sun fita da kaman minti talatin mlm Alwasu yasaki ajiyar zuciya.
"Tabb yau wannan yarinya mainene takamai mai abinda yake damunta,ni kaina duk iya ƙoƙarina duhu kawai nake gani,amma zanyi iya ƙoƙarina dai daga nan zuwa satin a gani"


🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are









____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]






*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________







Page 🖤14🖤




A haka suka koma gida cikeda ta'ajjibin abinda aka faɗa musu. Sannan kuma Daneji tacigaba dayi mata wankan maganin da mlm Alwasu yabasu.
Bayan sati daya dayin hakan suka sake komawa,aka yi yankan sadaka da kuma sauƙar karatu,sannan ya kuma basu wani maganin wanda za'ayi mata.
Sai a sannan ne hankalin su mlm Ahmadu ya kwanta,amma ba duk ba,saboda har yanzu idonta babu abinta ya sauya daga shi,saidai sun samu kwanciyar hankali jin cewar ta rabu da aljanun da suke jikinta.
Wasa wasa abu yayi ta tafiyah,har an shafe watanni biyar,tun su Danejo na boye Bombee idan sukaji sallama,har yazamo mutane sun gane abinda yake tattare da ido.
Dama ance idan rana tariga ta fito,tafin hannu bai isa rufeta ba.
Kuskus a cikin jama'a har zance yabaza gari ko ina ya ɗauka ƴar gidan mlm Ahmadu mayya ce,tun Danejo batajin mai yake faruwa har zance ya dawo kunnenta.
Inna laari tana sayar da kayan miyah,wanima da gangan yake tsallake anguwarsu yazo gidan su siyan abu,badon komai ba sai don yaganewa idonsa labarin abinda yakeji a gari.
Itakam inna laari cinikinta nunkuwa yake a kullum,ko kyaushe cikin siyeda siyarwa takeyi,kowa kuma idan ya shigo idonsa yana kan ɗakin Danejo,domin yaga ta inda zaiga Bombee.
Kullum a rana Danejo bata da aiki sai boyeta a cikin daƙi,saidai yanzu abin yayi mata wuyah,dan tafara rarrafe,ga ta da rawar kai bataji ko kaɗan,kota ajiyeta a ɗaki saita fito waje,wani lokacin inta takura bazata fita ba tasaka mata kuka,har abin ya isheta ta daina hanata fita wajen.
Batada ikon rufe bakin mutane ko kuma idanuwansu,amma kuma tana damar rufe nata idon da kuma bakin,shiyasa tasakawa idonta ƙyalle ta rufeshi,kunnenta ma ta tosheshi daga abinda zataji akan ƴar tata.
Inna laari ce take ƙirga karago itada mai talle.....basu fargaba sai ji sukayi yarinyar ta junduma ihu ta fita gudu waje.
Gefe suka kalla inda Bombee ke zaune kayan duk ya baci da rarrafen datayi,ashe mai tallan ta dafa zata tashi,itakuma kallon idonta yasa ta fita dagudu.
Shuru sukayi daga Danejo har inna laari,wannan abin ba barauba kenan a gidannnan.
Babu yanda inna laari batayi da ita tazo ta ɗauki kayan tallanta ba,dole sai ita ce taje zauren takai mata tukunna.
A bakin ƙofar ta haɗu da muruje yashigo cikin gidan,tundaga baƙin ƙofah yake tafi da hannunsa,itama Bombee da take zaune tana kwaikwayonsa,koyaushe tana zaune babu mai ɗaukarta ko yi mata wasa a yara saishi,shiyasa idan taganshi tayi ta ɗaga hannun ya dauketa.
"Ina mai idon kuliyar,kamata kamata gatanan gatanan,zatasha alewa?"
Waka yaketa reramata itakuma tana dagalemasa baki da haƙora biyu a ciki.
Kinkimarta yayi zai fita waje Danejo tayi saurin cewa.
"Muruje ina zakujene haka?"
"Gidanmu zan kaita wajen umma,mu bamuda yarinya a ɗakinmu,nasan inna zata karbeta"
"Ahah muruje ku zauna a nan kuyi a wasan,karka fitada ita kaji"
" toh Innar Bombee amma bari muje zaure toh"
Fita sukayi suka zauna a zauren,inda yahaɗa abubuwan wasa kala kala,shikaɗai yaketa maganarsa ita saidai ta bishi da ido,ko kuma inya haɗa abin wasan ta rugujemasa da ƙiriniyarta,gata da kazar kazar da zafin hannu.
Ɗaukar buta tayi bayan tagama shanyar kayan da Bombee ta bata tashiga banɗaki. Bayan ta fito sai taji babu motsin muruje da Bombee a zaure inda ta barsu.
A jiye butar tayi da sauri ta nufi zauren domin leƙosu,amma babu su babu ɗuriyarsu,gabanta ne yafaɗi rass,a ranta tace shikenan ta faru ta ƙare.
Kama katanga tayi ta leƙa gidanna su.
Yana nishi daƙyar ya ƙarisa zuwa cikin gidannsu yana cewa.
"Kai sule kagani nima nasamo tawa ƴar,daga yanzu inzamuyi wasa bakai kaɗane mai ƴar wasa ba,nima ina da ita"
Yaƙarisa maganar yana kallon sulen ɗan gidan larai,yanayi yana zukuɗa Bombee wacce tayi masa nauyi saboda ƙibarta dumur dumur.
Larai ce ta bankaɗa lalubulen dakinta ta fito,aikuwa carabb idonta ya sauƙa kan na Bombee wanda suke shining suna ɗaukar hasken rana.
"Lahh ilah haillallahu yau mai zangani,yanzu wannan mai idon mayun kaje ka jajibomana cikin gidan,a garin wato cusuwarka irinna uwarka koh,wannnan ɗa zakayi abu da yawa a rayuwarka.
Wato kalan ta lashemu dukka ku babu tsiyarku,.......uhmm wayasani ma abu a duhu ko kuiɗn tsarkakkune,dan dama ance duk inda mayu suke sunajin ƙanshin mutanensu idan suna kusa dasu,babu mamaki biri yayi kamada mutum kake nanewa a gidan wannan mayyar yarinyar. Maza tun kafin raina yabaci kafitamin da wannan annobar a cikin gidannan,kafin ma ta kawo mana baƙar sa'a"
Shatu ce datake ɗaki tana famada tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe taji hayaniyar taƙici kuma taƙi cinyewa.
Ja tayi da ƙyar tafito daga ɗakin dan ganin mai yake faruwa,dan tasan kullum zancen dai ɗayane baya sanja zani.
Larai ce itada muruje,ita ko kunya ma bataji,kullum idan aka jita to ita yarane ,tun yaran suna tsoronta har yazamo yanzu sun maidata tamkar mahaukaciyah.
"Kai muruje mai yafarune ,mai kayi kuma yanzu"
"Inna Bombee fah kawai na ɗakko zamuyi wasa,shine inna larai tace wai na maidata,kuma wasa kawai zamuyi,ba kuka take ba"
"Kaga maza kaita wajen innarta kartayi kuka kaji,kadaina ɗakkota,ka dunga zuwa can ɗin kuna wasanku kaji?"
"Toh inna"
Daga haka ya juya da Bombee tiri tiri zuwa gidanna su.
Duk abinda yafaru akan idon Daneji,wacce take tsayen tana kallon su larai,hawayen dayake kwaranya a idonta ta share tareda sauƙa akan katangar,bayan taga muruje yafita zai dawo da Bombee.
A bakin zauren ta tsayah,yana shigowa tasa hannu ta karbeta,tun kafin tayi magana muruje ya sunkuyar dakai tareda bawa Danejo hakuri.
Tausayinsa ne yakamata,ganin ashe shima koƙari yake yakai wacce zasu dunga wasa a gidannsu,saidai a halin da ƴar tata take ciki bazata iya yin wasan dashi ba yanda yakeso,dan tata ƙaddarar ne warewa daga cikin mutane,saboda halittar da take ɗauke dashi.
Ko a haka ma yaron yana burgeta sosai,yanda koda darana ɗaya bai taba nunawa ƴar tata ƙyama ba,saima burinsa shine yadunga fita da ita wasa,shima a ga tasa ƙanwar,kallonta yake a matsayin kanwarsa wacce bashida itah.
"Babu komai muruje kaji,nasan kanason fita da ita,amma baka ganin yanda take ne,mutane zasu gudu idan suka idonta,dan haka ku dunga wasan iya a zaure kaji,yanzu jeka gidan kar innarka ta nemeka"
Ɗaga kai alamar yaji kafin ya tafi yanayi mata bye bye,itama tana miƙa masa hannu alamar zata koma.

___***____***____***___


Wata ƴar fara yarinya ce bazata wuce shekara biyar ba tashigo gidan tana kuka,babu ɗan kwali a kanta,silifas ɗinta a hannu,jikinta yayi butu butu ta ƙasa.
Kana ganinta kasan tuburbuɗata akayi a cikin ƙasa,kai tsaye inda Danejo take ta nufah tana mitsitstsika ido.
Tsayawa tayi da busar hatsin datake ta kalleta tundaga sama da ƙasa tareda jijjiga kai.
Bata tsayah wani bata lokacinta ba wajen jin mai yake faruwa,domin abin kullum ne kamar faɗar Allah.
Tunda Bombee tayi ƙafa tana fita waje,kullum kwanan duniya saita dawo gidan cikin kuka,wani lokacin an fasa mata vaki,a kwai lokacin dazata dawo ma jikin jini yara sun jefeta da dutsi,kowa yana cewa ga mayyah tazo.
Duk yadda kuma Danejo tayi ta hanata fita abin ya gagara,kullum tana wajen cikin yara,a cizeta a jefeta a tumurmusata,amma hakan bazai hana idan an jima ta koma ba,haka zatayi tayi har sai dare yayi ta kwanta,tun Danejo na tambayar ta mai ya faru harta daina ma tambayarta,dan zancen kullum ɗayane.
Yanzun ma jawo tayi kusada ita,tareda matsar da garin tuwon dayake gabanta tana tankaɗe. Kama gefen zaninta tayi ta kaɗe mata ƙasar jikinta,har sannan idonta yana manne tana kuka.
"Saikiyimin shuru ai,buɗe idon naga miye a ciki"
"Inna inna ƙasa ce a ciki,shule(sule )ne ya zubamin,wai idona ya rife ya daina ganinsa,shannan kuma ya tureni a ƙasha dannan karbi abin washana a wajen rahama"
"To naji kiyi shuru kinji,kullum ina faɗamiki,idan kinga zasu dakeki ki gudo gida kinji,sannan kuma ki ƙyalesu,wanda yadaki wani bai ramaba allah zai saka masa"
Rarrashinta Danejo ta dungayi,daƙyar ta samu tayi shuru ta manta da zancen,jikin dukk tabon dukane da kuma rauni,inda yara sukayi mata,abinka dama da farar fata.
Suna cikin hakanne inna laari tafito daga banɗaki tana tura ciki,haihuwa ko yau ko gobe.
Da farko jinya tafara,wasa wasa abu ya dunga yin gaba,har mlm Ahmadu ya ɗauketa zuwa asibiti,aikuwa gwajin farko aka ce cikine da ita,murna a wajen mlm Ahmadu nan ma kasa misaltuwa tayi.
Tunda aka dawo gida yayi wanan yayi wannan,haka inna laari tacigaba da rainon cikinta,wanda kallo daya zaka mata kasan tanajinsa har a cikin ranta,sannan kuma tayi godiya ga Allah,da itama yayi mata kyautar da bata taba zaton samu ba,bayan tsawon lokaci data ɗauka da cire rai.
Danejo ma a fili takeyi mata murna tareda ƴan uwa da abokan arziƙi,lokacin da labarin ya isa ga mutane ,gidan cika yayi maƙil da mutane,wai ma ba haihuwar ba kenan,inaga idan haihuwa kuma tayi?.
"Bombee mai yafarune naji kukanki daga banɗaki,ko yauɗin ma dai jiya i yau,ke bazaki rama ba kenan,taya zaki kare ƙanwar taki kuma ko ƙaninki uhm?"
"Jan dukasu idan suka tabamiin ƙanwa,bajan barsu ba Inna yaari"
Dan murmushi inna laarin tayi tareda cewa,
"Ko kefah,haka ake son babba da jarumta kinji,ki bar kukan haka,barina kawomiki ƙarago,ko bakya so kai?"
"Inasho"
"Tam barina kawomiki mutumiyar,ladan samomin allura da kikayi,wacce nake nema jiya a ɗaki"
Tsalle Bombee tayi jin za'a bata ƙarago mai suga,ita kuma murmushi tayi sannan ta shige ɗaki.
"Karfah kiyi fada a waje fah,ina kinajina koh,duk wanda yayi miki abu kizo ki faɗamun kinji,karnaji kinyi faɗa"
Danejo ta faɗawa Bombee fuskarta ɗauke da damuwan halin ƴar tata.
"To innah bazanyi ba"


.......to sai muce Allah ya sauƙi inna laari lafiyah.........



🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are









____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]






*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________







Page 🖤15🖤












Tun safe inna laari take abu ɗaya a ɗaki,Allah ya haɗata da doguwar naƙuda.
Danejo kadai ke kai kawo a tsakar gidan,sai Bombee wacce take wasa a zaure,fuskarta bushe da hawaye tayi sabbabben nata wato kuka,a rana tayi kuka yafi sau a kirga,wani lokacin har zazzabi takeyi.
Larai ce tafito daga ɗakin inna laarin ɗauke da ledar mabiyya a hannunta,saida tatsayah tayi shewa tayi guɗa kafin ta kalli inda Danejo take.
"Mashaallah yarinya ta faɗo duniya,kyakykyawa fara jinin fulani usul,kuma Alhamdulillah idonta garau yake kaman na sauran mutane,da alama bayan wacce ta kawo baƙar kaddara ita kuma wannan ɗiyar albarkar farin haske ta kawo cikin gidannan"
Danejo tana jinta bata kulata ba,saboda tasan duk maganar datake da ita take.
"Iyar sule tunda ta haihu ko a zubo ruwan kai?"
Abinne ya ƙular da larai,ganin bata biyeta ba,saima sauya zancen datayi.
Ganin larai bata amsa mata bane yasa ta ɗebi ruwan tashiga dashi.
A zaune inna laarin take akan kujerar tsugunno,jaririyar kuma tana kan gado a naɗe da zani.
"Sannu addah laari,an samu kai kalau?"
"Lafiya kalau Danejo sannu fah da hidima"
"Lahh bakomai,barinaga ƴar tawa"
Cikin zumuɗi da farincikin Danejo ta nufi kan gadon da ɗauko jaririyar,buɗe fuskarta tayi,ba laifi kam kyakykyawa ce kaman yanda larai din ta faɗa,saidai bata da fari da kuma manyan ido irinna Bombee,saika kula ka gano kamanninsu,shima dan hancin baban su dukka suka iya shiyasa.
"Tufarkallah gatanan kam kyakykyawa da ita,addah laari kefa ta iyo,munsake samun Budurwa a gidan,allah ya rayata bisa imani"
Murmushin jin daɗi inna laari tayi,jin yadda ake gwaɗa ƴar tata.
"Ameen ya Allah Danejo,Allah ya bamu ikon rainonsu a bisa daidai dukkansu"
"Ameen"
Suna cikin zancene larai ta dawo ɗakin,harara ta watsawa Danejo,tunda ga kallonta zakasan bata sonta.
"Laari na kaimiki ruwan banɗaki,iyah maiganye ma tana hanyar shigowa yimiki wankan"
"To sannu da kokari larai"
Suna cikin hakane Bombee ta shigo ɗakin jikinta duk ƙasa,taga tsakar gidan babu kowa shiyasa tabiyosu.
Danejo ce takalleta tareda cewa.
"Yaki zokiga ƙanwarki ta iso to yau,kina ta tambayar yaushe zata zo,gashi tazo yau"
Aikuwa tana jin hakan ta taho gudu har tana zubar da kayan tasuke gabanta,wajen Danejo take rike da yarinyar ta nufah,inda itakuma Danejo ta iyo kasa da ita yanda zata ganta dakyau.
Hannu takai abinka da yaro zata tabata,larai ce tayi saurin cewa.
"Tsaya tsaya menene haka Danejo,saikace bakya kula,jaririyar da ko suna ba'ayi ba zaki bar wanann ƴar taki ta daba,idan kuma ta shafamata wannan idonnata fah,ni wlh yanzu haka a takure nake data shigo ɗakin,inaga kuma jaririyar da aka haifa yau"
Dagowa daneji tayi ta kalli larai tareda rike hannun Bombee wacce take ƙokarin taba fuskar jinjirar.
Cikeda bacin rai Danejo tace.
"Wai nikam larai mai na taremiki a rayuwane,koyaushe cikin jifana da kalam mayu kikeyi,ina kawar da idona ina raga miki domin girmanki amma bakya gani koh,fisabilillahi banda abinki yaushe wannan yarinyar tasan kalmar maita. Dazakice zata shafamata idonta,itakuma waya shafa mata kenan?.
Ni inada imani da tawakalli sannan kuma na yarda Allah ne yayi ta haka,domin haka yaso ya ganta,ina da labarin duk izayar da kike saka ƴaƴanki suyi mata a waje,na barine saboda fitina bbau daɗi........."
"Aikin banza kin daɗe baki bari ba,dan Allah ki ɗau mataki kinji,ke bakisan kema ragamiki ake saboda darajar mlm Ahmadu ba,banda haka da tuni an daɗe da korarku daga garinnan keda wannan mayyar ƴar taki,waye bai san irinku da harkar maita ba. Kullum saiki tura ta tana shiga cikin ƴayanmu kalan ta cinye su,hakan bai miki kin kawota kusada jinjira saboda ta lashi samuwar kuruwa koh?"
Suna cikin maganar ne Danejo ta manta tasaki hannun Bombee,aikuwa kaman jira take itama tarigima ta ɗora hannun akan jinjirar.
Tana ɗora hannun yarinyar ta callara ƙara kaman an zare mata rai lokaci guda.
Zaro ido Danejo tayi tareda kallon mai yafaru,dama haka larai take jira,aikuwa da sauri ta sure jinjirar daga hannun Danejo.
"Kingani koh kinga ni ko akan idanki,ke kuma laari barsu su kashe miki ƴa tun bakiji ɗuminta"
Buɗe baki Danejo tayi zatayi magana,inna laari tayi saurin cewa"
"Danejo kiyi haƙuri,amma larai gaskiya tafaɗa,bai kamata a dunga barin Bombee tana zuwa kusada yarinyar ba,musamman da yanzu tana jinjirar,saboda gudun kar wani abu ya faru,idan gaba ta girma babu matsala saita rabeta"
Lokacin da inna laari ta baɗi hakn,daneji ji tayi kaman an doka mata guduma a ranta,saidai yazatayi gaskiya suka faɗa,kowama inshine bazai yardaba,musamman yanda tayi shekara da shekaru babu haihu,lokaci ɗaya Allah yabata,zata iya komai domin kare ƴartata da mungun abu irin ƴar tata.
Ƙoƙarin maida hawayen idonta tayi,tareda jan hannun Bombee suka fita daga ɗakin,wacce take ta yunƙoron kamo jinjirar daga hannun larai,buge hannunta larai tayi tareda gallamata harara.
Hanyar ɗakinta tanufah idonta yana zubar da hawaye.
Zama tayi akan kujera tareda saka Bombee a gabanta tana kallonta.
Duk wanda yaga Bombee zai iya ɗauka cewar badaga nigeria take ba,farace sosai mai kyau,kana ganinta kaga fulani,bayan idanunta wanda su suka rana kamanninta da ƙasar tata,dan idan tana kallonka,mus

musamman idan ka zuba mata ido na wani lokaci,kana ganin yanda ƙwayar idon take girma sannan kuma tana ƙanƙancewa gwargwadon yanayin hasken dayake wajen,ga ƙwayar idon blue shar,kullum sake clear take da tana girma.
Babu wanda zai kalleta yace ba a ƙasashen turawa aka satota ba.
Kama hannunta Danejo tayi ta haɗasu kafin tafara magana cikim karayar zuciya.
"Zakiga jarrabawa a ratuwarki kala kala Bombee,amma kiyi haƙuri ki daure kinji,nidai fatana shine ki dunga haƙuri idan anyi miki abu,wanda yajefeki da sharri ki mayar masa Alkhairi,wanda yaƙyamaceki karki ji haushinsa,kiyi nesa dashi kawai saboda karya cutar dake,idan kinje wajen da bana tareda ke,ki tuna Allah na tareda ke kinji"
Tana gama faɗin hakan ta rungumota jikinta,tareda ƙara sautin kukanta.
A cikin kunnenta tajiyo ƙaramar muryar Bombee.
"Inna ki daina kuka,ko su sulene suka dukaki,insun dukaki bazan barsu ba,saboda dukan su da ciwo sosai"
Ƙara ƙanƙameta tayi jin abinda take cewa.
"Ahah basu dukani ba,in sun dukani ma zai wuce watarana,idan ban ramaba Allah zai ramamin,kuma inya tashi ramamin da zafi zayyi musu,suma suyita kuka"
Ƴar dariyah tayi kafin tace.
"Heer kuma nayi ta musu dariya yanda suke min idan ina kuka koh?,uhm inna barina je wajen yarinya"
"Ahah karkije wanka ake mata,sannan babu kyau a je wajen yarinya idan tana ƙarama,saita girma tukunna sai a goyamiki ita,ina kinaso koh"
"Eh inaso,zan jira ta girma toh saimuje wasa,nima shikenan nasamu ƴar wasa irinna su Sule"
A hankali da lallami Danejo ta dunga amfani da hankalin Bombee,har ta koyamata kartaje kusada ɗakin inna laari,saboda gudun abinda zaije ya dawo.

Ranar suna biki da bidiri akayi,inda yarinyah taci suna khadijah,mahaifiyar inna laari,ana ƙiranta da Innayi.
Haka akaci aka watse kowa yakama gabansa,aka bar mai jego da rainon ƴarta.
Haka rayuwar tasu tacigaba da kasancewa tareda ƴaƴannasu,Danejo ce mai yin girki kasancewar inna laari tana jego.
Ko yaushe idan ka jisu itada Bombee to akan taje wajen innayi ne,sau goma zata shiga ɗakin sau goma zata korota,tun abin yana da damun Danejo har tashafawa ganta lafiyah ta zuba musu.
Duk sanda a yanzu mutum ya zauna da inna laari batada aiki sai zancen ƴar ta,wani lokacin a shiryata a kaita gidan larai,sai tayi kuka a saka sule ya kawota.
Itadai Danejo ido ne nata kawai,dan tafi danganta hakan da inna laari tana son ƴar ne bata son Bombee ta rabeta.
A bangaren mlm Ahmadu

Please Login or Register in order to submit comment