Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a saba. Dan haka kema kiyi ƙoƙarin daurewar kuma ki saki jikinki,komai zai wuce kaman bai faruba inshaaallah.
Da haka cikin sigar lallashi da jan hira Laari tayi nasarar saka murmushi a fuskar danejin.
Har suka fito tsakar gidan suna aiki tare,yar hira suke kaɗan kaɗan,yawancinta kuma Laari ce keyi,sai ta tambayeta ne tace,uhm ko uhmuhm.
Haka zamannasu ya fara gudana,cikin zaman lafiya da kuma mutunta juna,abin ba ƙaramin faranta ran malm Ahamdu yayi ba,ganin matannsa sun rungumi junansu suna zaune lafiya.
Inna laari ce keyin Abinci,ita kuma Daneji tayi wanke wanke da kuma shara,sannan ta gyara mata kayan abinci.
Bayan sati da kawo Danejine su Larai suka shigo ganin amaryah.
Tundaga zaure ta rankwaɗa Sallam,dan dama itace a gaba sai kuma Shatu tana binta a baya,ta riƙe hannun ɗanta Muruje,wanda ko sati bayyi ba da yaye.
"Salamu alaikum masu gidannan,gamu munzo ganin baƙuwa ta ganmu mu ganta,ta kuma ganemu"
Inna laari ce ta amsa mata wacce take cikin ɗakin girki tana hura wuta.
"To sannunku da shigowa,sai yai kuka zo ganin amaryar?"
"Iyyi to ya zamuyi,munyi ƙoƙari ma,ita ina bata nememu ba,sai mune muka zo ganinta"
"Hayen wuri kukayi ai,dama tana shirin zuwa muku"
Duk zancen tsakanin larai da Inna laari akeyi,shatu kan da daneji basuce komai ba. Sai bayan an gama gaisawane suka shiga ɗakin Amaryar.
"Ahhh babu laifi kam ɗaki yayi kyau,zamuga shin za'a kawo kazantar ɗaki,ko kuma dai duk sammakal ne"
Larai ta faɗa tana fitstsina ido tareda dukan ɗan ƙaramin kunkuminta.
Shatu ce ta kallin Daneji itama ta kalleta,amma larai ko a jikinta,saima surutu da ta cigaba dayi,da kuma ganin ƙwakwaf.
Itada kanta da abin ya isheta tabar ɗakin,tareda nufar ɗakin Inna laari,a bakin ƙofa ta tsayah kafin tashige ta kalli shatu.
"To ni barina yi ɗakin yawuron gidan,ta inda muke muyi namu yakin,wanda ko an fadama mutum bazai ganeba,saura kuma a zunguri hancina idan anga na kauda ido"
Itadai shatu bata ce mata komai,saima maida kanta da tayi kan Daneji wacce take zaune a bakin gadonta.
"Hmm kiyi haƙuri fah amarya,yanayin zamanne sai haƙuri,bazaka iya sanja mutum ba,saidai dole kasha maganin zama dashi.
Sannan abinda zan faɗamiki kiyi taka tsantsan sosai,karki saki jiki ki bada yardarki dabaɗaya,za'ayi miki abinda bakya tsammani.
Murmushi Daneji tayi,da alama bata ɗau maganar shatun da gaske ba,saima kauda zancen da tayi ƙoƙarin yi.
"Ayyah Addah shatu babu komai dai,Inshaaallah babu wata matsalar........kai ɗan saurayi ya sunanka?"
Ganin duk yadda take ƙoƙarin nusar da Daneji bata damuba,saima dauke zancen da take shirin yi,yasa itama Shatu tabar zancen tareda cewa.
"Ohh wannan sunan Umar,amma yara sun saka masa Muruje,kiji wani suna kaman na Warjayi"
Ƴar dariyah Daneji tayi,da alama sunan da kuma yaran sun bata dariya,haka ta zage tana ta tsokanarsa shikuma yana yi mata ƙiwuyah.
"Inasonsa ki bani shi innar muruje"
"Hhhhh baban sa zai dawo gidannan kenan,in kikayi haƙuri kema zaki haifi naki kaman yaune,saidai zai dunga zuwa miki yawon yamma"

Larai ce a zaune ta baje ƙafa kan kujerar Laari zance yayi zance,wanda yawancinsa duk na Adashen da suke ne a anguwa.
"Uhmm daikuma naga yarinya tasake abinta tayi mursul,ga kulawar miji ga kuma ta kishiya,abin har ya taru yayi mata yawa"
"Ke larai,banda abinki dama ai jajir take lokacin data zo ma"
"Ohh to inaga idona ne yagani badaidai ba,nikam da badan nasanki ba,sai nace yarinyyar can asirin tayi miki,dan inajin labarin duk abinda kike mata a wajen malm,insun zauna malam ahmadu na bashi labari. Yayi tayimin tujara kenan wai ni naƙi a zauna lafiya."
"To kema ki riƙeta ku zauna lafiya mana larai,ni banga laifin shatu ba......"
"Ahah ahah nina gani inke baki ganiba,idan dole haka kawai banason ta saina ce inayi,gwanda tasan bani sonta,ta tsare tata rayuwar nima nayi tawa,innace zamuyi zaman da kuke da itama nayi ƙarya bazan iya ba"
"Kiji gulma irin ta maxa,wato mlm ne yake bashi labari?"
"Tabb yau kika sani,gulma ai ta daɗe da tarewa wajen maza,idan sun zauna a wannan majalisar,basa lazumi ko salati,sai aukin cin tsire da gulma,shiyasa kiga cikinsu tula tula kaman ƙore,kai sun barka da ɗumame da kuma cikon cefane"
Larai ta ƙarisa fada tana tashi tareda nufar ƙofa.
"To mu munyi nan,sai kun shigo,dan Allah kicewa magajiya zanyi ɗaukar wannan watan na adashen,auren ƴar yayata ya taso"
"To shikenan zan faɗa mata"
Daidai fitowarta daga ɗakin,itama shatu ta fito daga ɗakin Daneji,sallama sukayi musu suka fita.

............"uhhhhhh uhhhhhh" .........."laari Daneji fah amai take kwarawa tun daren jiyah,lafiya kuwa????.............




🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are









____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]






*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________







Page 🖤11🖤



Kwanaki sunzo sun tafi,a ƙallah Daneji ta samu shekara guda babu kaɗan gidan malam Ahmadu,kuma har yanzu babu wata matsala data fito tsakanin ta da mijinta,ko kuma kishiyarta. Tana binta ta sau da ƙafa,itama kuma tana kyautata mata a matsayinta na babba.
Tun bayan watanta uku a gidan Malam Ahmadu yafara zaton samun ɗa,amma ganin shuru shuru yasa shi dole ya bar zancen.
Daga lokacin yafara zaton wataƙila wata matsala ce daga gareshi.
Hakanne yasa ya nunka kulawar dayake basu fiyeda a lokacin baya,domin sasu manta lalurar tasa.
Daneji ce a cikin ɗakin madafah tana girki,tun jiya take jinta wani iri,amma haka ta daure,dayake ansan mace da dauriya da kuma murƙushe kanan nan ciwo da laulayi.
Doyar da take dafawa zatayi sakwara ta buɗe,saidai ƙamshinta yana bugunta taji amai ya taso mata.
Da sauri tayi waje tana ƙoƙodon amai.
Inna laari ce ta fito daga ɗakinta domin ganin mai yake faruwa.
Ruwa ta debo mata ta gyara bakinta tareda yimata sannu,suna cikin hakanne shima Malam Ahmadu ya shigo gidan ya dawo daga wajen ɗaurin auren daya fita da safe.
Inna laari yafara tambaya mai yake faruwa,saidai kafin ta bashi amsa Daneji tacigaba da aman da takeyi,saidai takai ga ta amayar da duk abinda taci da safe.
Kafin lokacin ƙalilan ta galabaita ta fita hayyacin ta,kamata inna laari tayi suka shiga rumfah ta zaunarta,inda shikuma malam Ahmadu ya fita ƙiran ƴar mai ganye,dake tsallaken gidansu,domin ta duba taga mai yake faruwa.
Basu daɗe ba suka shigo tare,takalmanta fantala fantala zani a tsangale,sai jijjiga kai take ƙanƙanin. Hannun danejin ta kama tayi shuru,kafin tafara wasu ƴan dube dubenta,can ta waigo ta kalli mlm Ahmadu tareda cewa.
"Iyyyeeee Alhandu alhandu,Yarinya ciki gareta,ƙaruwa ce ta samu sai kuyi murna ku godema Allah"
Tun kafin tagama maganar Mlm Ahmadu yafaɗi ƙasa yayi sujjada,tareda fashewa da kukan murna.
"Daneji ɗiyar arziƙi,allah shi miki albarka,haƙika kin sakani farinciki dana daɗe ban shiga ba a rayuwata,Allah ya saukeki lafiya. Inna ƴar mai ganye kinada kyauta ta musamman na wannan albishir ɗin,yanzu dame dame take buƙata kenan"
"Babu abinda take buƙata,illah tarage yawan aikace aikace amma ba wai kartayi ba,sannan a kulada abinci masu gidan jiki sosai,nagode nagode mlm Allah yayi albarka,ni bari na tafi toh Allah ya raba lafiya,zan aiko yaro da ruwan saiwoyi ya kawo mata ta dunga sha"
"Shikenan iyah mai ganye mun gode"
Duk abinda ake iya Iyah mai ganyece da kuma Malm Ahmadu,inna laari bata ce komai ba itada Daneji,wacce take ɗan sauƙar da numfashi a hankali.
"Sannu mai zakici toh,bari a nemo miki Kwankwason akuyah a dafa miki"
Ɗaga masa hannun Daneji tayi alamar yabari,amma mutumin ko kallonta baiyi ba,sai ma fita da yayi da sauri bajam bajam da babbar riga.
Binsa inna laari tayi da kallon kafin ta jijjiga kai tayi ɗan murmushi.
"Zaki iya isa ɗaki ko kuma na rakaki? Zan ƙarisa abinci"
"Ahah zan iya Adda laari nagode da kukawarki"
"Babu komai kisamu hutu sosai jikinki yayi laushi,bari yakawo naman saina dafa miki,Allah ya sawwaƙe ya raba lafiya"
Daga haka Daneji ta ƙoƙarta tashige ɗakinta,ita kuma inna Laari tacigaba da aikin abincin data bari.
Tundaga wannan rana Daneji ta gagara lafiya,kullum cikin laulayi take,yau da lafiya gobe kuma babu,abinci kuwa kusan kowanne kala bata iya cinsa.
Tun malm Ahmadu yana ɗokin magaji har zuwa yanxu abin yafara bashi tsoro da tausayi,inda yafara tambayar dama haka goyon cikin yake.
Inna laari ce take rawa take kidanta a tsakar gidan,ita kam daneji Ba sosai take fitowa tsakar gidan ba,in mutum ya ganta to zagawa zatayi makewayi ko kuma alwala.
Haka rayuwar tacigaba da tafiyah,da daɗi da kuma babu,har yazamto cikin daneji yayi girma sosai,ana saka ran ko yaushe zata iyah haihuwa. A lokacinne kuma aka dage dabata dan taimako,ita kanta inna laari ba'a barta a baya ba,takan samo mata ɗan taimako daga wajen mahaifinta,dayake shima malamine.
Ɗakin Danejin inna laari tashiga da ƙwaryar magani a hannunta,magana tayi mata kasancewar ta juya bayanta bata kallonta.
"Daneji tashi kisha maganinnan ya tsumu sosai,karkuma yazo ya sane"
Duk maganin da Inna laari take bata a dole take sha saboda rashin dadinsu,saidai saboda karta nuna mata kazawarta a ƙoƙarin datake da ita yasa ta yunkura ta tashi. Alkhairin da inna laarin tayi mata bazata iya ƙirgasu,ji take a yanzu bata da kowa na kusada ita kaman ta,musamman daya kasance batada kowa a garin,ƴan uwanta tunda suka tashi batasan a yanzu inda suke ba.
Karbar maganin tayi dayake cikin ƙwarya takaishi bakinta tana yatsine fuska.
Da kyar tayi kurba uku kafin ta miƙamata ƙwaryar ta koma ta kwanta.
Cikin dare malm Ahmadu ya zabura ya tashi,jin ana jan bayan rigarsa daga ƙasa,lalumar fitilah yafara yi domin ganin mai yake faruwa,don yasan bazai wuce Daneji ba,don yana shashimawa yaji bata wajen data ke kwance ɗazu.
Yanzu haka haihuwa ce,yafaɗa a ransa,don dama tun shigar watan haihuwar tata inna laari ta lamunce masa ya koma ɗakinta da zama,saboda kar haihuwa tazo mata cikin dare babu kowa a wajenta.
Baiƙi karbar tayinta ba,saima godiya dayayi mata,dan hakan baƙaramar dabara bace.
Haska fitilar yayi a wajen dayake jiyo motsin danejin,tana durƙushe ta kifa kanta da bakin gadon,ƙasanta duk ya jiƙe da ruwa yana ta malala mai haɗe da jini.
Salati malam Ahmadu yafara tareda buɗe ƙofar da sauri ya nufi ɗakin inna laari.
Tana bacci sai jin muryarsa tayi yana ƙiranta,cikin magagin bacci tafara tambayarsa.
"Lafiyah malam naganka a razane,ko haihuwarce kai tazo?"
"Ehh.....ehh itace ,maza kizo ki gani koda wani abu dazaki taimaka mata dashi"
Tashi inna laari tayi tabi bayan malm Ahmadu zuwa ɗakin danejin,wacce take kwance har yanzu a inda yatafi ya barta.
Ƙarisawa wajenta tayi tana kallon yanayin da take ciki,saidai da alama haihuwar takawo kai amma kuma dasaura,don babu alamar tahowar ɗan har yanzu.
"Inaga har yanzu fah da saura,amma barina kawo ruwa a goge mata jikinta,sanann kuma tacire wannan riga da zanin,suma bazata ji daɗinsu ba"
To kawai malam Ahmadu yace mata,domin aikinsa kallone kawai,bashida tacewa bayan hakan.
Yana nan zaune a gunta har inna laari ta dawo da ruwan dagama gyara mata jikin,sannan tabata fallen zani ta ɗaura.
Kaman jira kuwa take tafara nishi da yunkuri,har wajen fitowar asslatu suna kanta,tana nishi amma babu haihuwa,saidai yafi na ɗazu,tunda ana ganin kan yaron,aikinne dai har sannan da saura.
Yanda suka ga rana haka sukaga dare akan Danejin,wacce take fitar da nishi mai haɗe da ƴar ƙara na galabaita da gajiya.
A hanyar zuwa masallacine malam Ahmadu ya biya gidansu iya mai ganye,yake faɗamata abinda yake faruwa,aikuwa nan da nan ta shirya tanufi gidan,jiki yana bari taji daɗin kyautar da yayi mata wajen faɗar haihuwa.
Sai bayan rana ta fito gadan gadan haihuwar ta taho,inna laari tana gogemata goshi,ita kuma iyah mai ganye tana taimaka mata wajen fitoda jijirin.
Kaman jira shima yake kuwa ya canyare wajen da kuka,har makwantai ana jiyoshi.
Ɗago dashi iyah mai ganye tayi tana duddubawa,take kuwa tasaka guɗa.
"Ayayyyyyriririrrri malam Ahmadu yasamu ɗiya mace,barkanki dazuwa duniya ɗiyar Albarka"
Sai bayan tagama guɗar kafin ta kalli Daneji wacce take maida numfashin gajiya.
"Sannu sannu ƴar nan,sannunku keda abokiyar zamannnaki,dole kisha wuya kam,yarinya tafarkallah mashaallah,ga tanan kuwa jajir da ita kaman uwarta,ta amsa sunan ƴar Daneji.
Laari saiki taimaka mana da daro ruwan zafin da zasuyi wanka itada yarinyar."
"Ruwan kan daman an ɗumama tun tazu,saidai ko na kaimuku banɗakin kiyi mata wankan,kafin ku fito itama jaririyar sai a gyarata"
"To shikenan hakan ma yayi sannunki da ƙoƙari"
Kaman yanda ta faɗa ruwan takai musu banɗaki,inda iya mai ganyen zatayiwa mai jego wanka,yayinda itama ta haɗa wani a baho zatayiwa jaririyar.
Shigo ɗakin tayi da ruwan wankan ta ajiye,kafin ta nufi inda jinjirar take kwance a tsumman mahaifiyar tata,ɗaukarta tayi a hannunta tareda yin murmushi,kana kuma tashare guntun hawayen dayake kan fuskarta.
"Allah sarki jinin Mlm Ahmadu ne a hannuna,ashe zanga jinin malm Ahmadu da raina,duk da cewa banice na haifa masa ba,amma nayi maka murna dakaga jininka"
Lokacin da su iyah mai ganye suak fito daga wankan inna laari na zaune a ɗakin tana tsane ruwan jikin yarinyar,wadda tayi shuru a cinyar inna laarin tana jin ɗumin dayake ratsata.
Iyah mai ganye ce tafara magana tareda cewa.
"Hoɗan kiji yarinya tayi shuru kaman ba haihuwar yau ba,kokukanta bamuji ba na wanka"
"Ko kishi kike kai kinganta da juriyah zata ƙwace miki kujera kai iyah"
Inna laari ta amsawa iyah mai ganye cikin sigar zolaya. Suna cikin hakanne kuma kaman an tsikareta ta canyare da kuka kaman ansaka a speaker.
Nannaɗeta tayi a zanin tareda miƙawa daneji ita akan ta gwada bata nono.
Itama iyan mai ganye ƙara ƙarfafa mata gwiwa tayi cewar tashayar da yarinyar,musamman da sukaga tana kauda kai akan yarinyar tana nuna halin fulani.



...............Shuɗiyar ƙwayah kuma(blue iris),kodai bata gani kai.........daneji da faɗa a ranta.




🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are









____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]






*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________







Page 🖤12🖤


Hannu tasa ta karbi jaririyar tareda mannata a jikinta,wata irin tsagwaron ƙaunar yarinyar ne ya jiyarci tsakiyar zuciyarta,tareda muradin kareta a ta kowacce fuska.
Idanuwanta ta sauƙe akan jar fuskar jinjirar,wadda yake ɗauke da ƙankanin kyau mai tafiyar da duk mai kallonta.
Hancinta babu makawa kowa yakalleta yaga na ubantane,sai bakinta kuma data biyo irin na mahaifiyar ta ɗan ƙarami,motsashi take a hankali tana neman inda zataji abincinta ya isa gareta,wanda hakan yasa ainihin Cute feature ɗinta fitowa fili.
Boyayyan murmushi Daneji tayi ganin halittar yar tata farincinkinta tareda gode ma Allah daya azurtata da itah.
Maman ta buɗe na hannun dama inda yarinyar take,tareda ƙokarin saka mata a baki da taimakon iya mai ganye wacce take tsaye a kanta.
Saida taga yarinyar takama nonon kafin tabi bayan Inna laari zuwa wanke kayan data bata.
A hankali take jan ruwan nonon cikin rashin iyawa zuwa cikin bakinta,yayinda ita kuma Daneji ta tsareta da ido,ko da wasa ta gagara ɗauke idonta daga kanta.
Idonta ne yafara motsawa alamar zai buɗe,wanda hakan yabata mamaki matuƙa,yarinyar da aka haifeta yanzu tana shirin buɗe ido,kawar da hakan tayi a ranta ganin daƙin da duhu,sannan kuma idan aka buga larasi da ƴaƴan zamani hakan bakomai bane.
"Daga haihuwarki yau har kina ƙoƙarin buɗe idonki,lallai kina da wayo sosai t.........."
Tsaida maganar tayi a ƙasan maƙoshinta,ganin launin idon dayake kallonta,ba baƙi ba ko kuma mai ruwan ƙasa ƙasa ba,da ake samun wasu yaran sukan zo dashi,nata launin idon shuɗine ne siɗik,kaman ba idanuwan bil'adama ba,duk wanda yarinyar takalleshi da idanuwan idan bayyi jarumta ba zai iya jefarta yagudu,saboda yanda suke ɗauke da wata haiba a cikinsu,da ko babban mutum bazai samu ba.
Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce ta jiyarci danejin a karo na ba'a adadi,ganin irin halittar da ƴar tata take ɗauke dashi,wanda tayi amanna tunda take bata taba ganin irin ta ba a rayuwarta.
Duk yanayin buɗe idon kaɗan kaɗan take irin na jarirai,amma hakan bazai hana mutum gano abinda yake tattare da yarinyar ba.
Runtse idonta tayi na wasu mintina kafin tasake sauƙesu akan ƴar,wacce zuwa yanzu ta rufe idanuwan da alama tayi bacci a bakin nonon. Cireta tayi a hankali,ta sake lullubeta a cikin zanin da take,kafin ta maidata wajen da take kwance ɗazu..
Tashi tayi tafara gyara ɗakin tareda ɗauko kayan dazata saka,har sannan jikinta a sanyaye yake na abinda tagani,a jima kaɗan ta kalli wajen da yarinyar take,a jima kaɗan ma ta kalleta,abin ya tsaya mata a rai takasa fitarwa.
Tana cikin hakanne malm Ahmadu ya shigo ɗakin kaman an jehoshi,labarin sauƙarta lafiya ya risƙeshi a waje.
Kai tsaye wajenda take ya nufa tareda ɗaukota ya rungume a jikinsa da rawar jiki.
Sumbatarta yafara ta ko'ina kafin yafara yimata ƙiran sallah a kunne.
Itadai Daneji tana tsaye da tsintsiya a hannunta bata ce komai har yagama rawar jikin.
Ɗagowa yayi ya kalleta da murmushi akan fuskarsa yace.
"Mashaallah nayi mata huɗuba,sannan kuma nasaka mata sunnan mahaifiyata MARYAMAH"
"Allah yaraya ta bisa imani,sannan kuma Allah yasa halin mai sunanta ya bita"
"Ameen ya Allah,kema Allah yayi miki albarka yabaki lafiyar shayarwa"
"Ameen kasake yiwa Addah laari godiya da ƙoƙarinta a gareni"
"Shikenan"
Kafin dare yayi mutane ƴan uwa da abokan arziƙi suna ta zuwa ganin Ƙaruwar haihuwar da akayiwa malam Ahmadu,wannan su shigo wannan su fita.
Har ƴan uwan su inna laari ma saida sukazo daga ƙyauyensu,Amma babu wanda yazo akace daga bangaren mai jego,duk da kowa yasan ƴan uwanta basanan amma abin yayi mata ciwo sosai,rashin danginka a kusada dakai abune mai ciwo matuƙa.
Da daddare saida Daneji tasha kukanta ta ƙoshi na rashin danginta,babu wanda zai zauna a gunta daga bangaren yan uwanta,sai dole yadikon su malam akan ce wata tsohuwa tazo yi mata zama.
Gashi yanzu tafara tara dangi itama nata na kanta,shin wa zata nunawa Ƴar ta a matsayin danginta zuwa gaba,ko kuma haka zata tashi batasan kowa nata ba,wanda itama tanada yaƙinin nangaba zata iya mantasu idan lokaci ya tafi.
Har akayi kwana uku da haihuwa babu wanda yagane cewar idon Jinjirar bana mutane bane,sai iya daneji ce kawai tasani,har yanzu kuwa babu wanda ta faɗawa,kullum fargabarta shine idan mutane sun gano mai zasuce gameda hakan.
Abinda yafi bawa Daneji mamaki shine idan har ita datake bata nono tagane ƙalar ƙwayar idanunta inaga mai wanka kumafah inna laari,tana da tabbacin Inna laari taga abinda tagani gameda yarinyar,amma ko kaɗan bata nuna tagani ba,ko kuma bata gani bakai?
Ita kaɗai take tambayar kanta take bata amsa a ranta,abinda yashare mata tantama shine,lokacin da jinjirar ta shaƙi sabulu ta buɗe idonta kuma akan idon inna laari,amma batayi mamaki ba ko kuma nuna alamar zata sanar da wani abinda tagani.
Duk abinda take bata kulada Daneji tana kallon sanda taga idon yarinyar ba,hakannne yakara tabbatar mata ba lokacinne kallonta na farko ba a gameda lamarin,tasani tunda farko,boyewa kawai takeyi,to miyasa?.
"Addah Laari shin bakiga wani abu a tattare da yarinyar nan ba wanda ba irin na mutane ba?"
"Nagani mana,ƙwayar idonta ba kalar ta mutane bace,saidai babu yadda Allah baya halittar sa idan yaso,shi yayi nufin yaganta hakan,dan haka babu mai ja da ƙudurarsa"
"Hmmm hakane kam,nayi mamakine da kika gani amma bakice komai ba"
"Uhm mai zance Daneji,saina bi duniya nayi ta yaɗawa ƴar mijina an haifeta da wani irin ido?ribar mai zanci akan hakan,innayi hakan nima ai kaina na tozarta ba kowa ba,sannan ya mutane zasu kalleni kenan,idan Allah yayi kwananta ta fita kowa ma zai gani,fatana shine Allah yasa mutane su gane halittar Allah ce itama kamar su,karsu nuna ƙyamatarsu gareta"
Maganar da inna laari tayi baƙaramin faranta ran Daneji tayi ba,sai ta nemi kashi hamsin na fargabar halin da yar tata zata shiga ta rasa,yazamana itama tasaka a ranta cewar Allah ne mai halitta,kuma shi yayi nufin ya ganta a haka ba kowa ba.
Ranar suna gadan gadan aka hau abinci da yanke yanken kaji,bayan tunkiyar da aka yanka na aƙiƙa.
Mutane an ciki gida maƙil,a lokacinnne kowa yashaida yarinya taci suna Maryam,mahaifiyar malam Ahmadu.
Bakinnan kaman gonar auduga,kowa rana yasan malm Ahmadu yana cikin farin cikin marar misaltuwa.
Duk abinnan da ake Daneji kaffah kaffah take da Maryam,wanda tafara ƙiranta da BOMBEE,saboda kar mutane sugani su tsegunta,ana tsaka da taro kowa yaɗauka a ƙirƙiri abinyi na gulma.
Dan haka sai itada inna laari suka haɗa baki akan yarinyar bata lafiya,kowa idan yazo saidai ya kalleta daga nesa,itama data rufa musu asiri wuni tayi tana bacci.
Bayan anyi taro an watsen makwanta su larai suka tsayah aka gyara gidan tareda su,kafin bayan magriba sukayi mmusi sallama suka nufi nasu gidan.
Dare yayi gari yafara shuru Bombee tace batasan kwanciya ba,dawa Allah ya haɗata idan bada kuka ba.
Tun tanayi Daneji na rarrashinta har abu yafara fin ƙarfinta,dan shiɗewa take muryarta har dunshewa take dan Kuka.
Shikansa malm Ahmadu take ɗakin inna laari yayi sawu yakai sau uku,kl yaushe idan yazo sai yace tabata tasha,tun tana ce masa taƙi karba har ta rabu dashi.
Ruwa ta ɗebo a kofi tana tofi tana shafe mata jikinta,tunda ta kula babu zazzabi a jikinta,sannan cikinta bai kumbura ba bareta ce ciwo yake mata.
Haka tayi ta shafe ta da ruwan addu'o'i,sai kuma tayi sa'a tafara sauƙe ajiyar zuciya lokaci lokaci,can wajen asuba tayi ƙitt kaman an kashe rediyo.
Ida tai Daneji yanda taga rana haka taga dare,ga gajiyar bikin suna,sa'arta ɗaya ma Ba sallah zatayi ba ko girki,dan haka da rana ta samu damar rama baccin.
Wasa wasa an kusa shafe wata ɗaya dayin suna,kullum babu fashi sai Bombee ta kwana tana ihu,idan asuba kuma tayi tai shuru kaman ruwa ya ɗauke.Tun abun suna ɗaukarsa kukan jinjirai har abun yafara sakasu dasa ayar tambaya. Bangaren Daneji kam harta fara mantawa da wani baccin dare yanzu.
Bankaɗa labulen ɗakin tayi zata shiga ta fito daga wanka,turuss tayi a bakin ƙofar ganin malm Ahmadu rike da Bombee a hannunsa yana kallon idonta,ita ma kallonsa take da shuɗayen idanuwan nata na yara,kana kallon kan fuskarsa zaka hango tsagwaron mamaki da kuma irin mutum yaga abu a karon farko.
Ɗago fuskarsa yayi ya sauketa akan Daneji wacce ta shigo daƙin jikinta yana ɗigar da ruwan wanka.
Saurin sunkuyar da kanta tayi bata bari sun haɗa ido ba,dan babu alamar wasa a idanuwannasa,tambaya ya jeho mata kai tsaye.
"Fatima menene wannan?"
"Idanuwanta ne"
"Dama haka suke tun farko,kokuma yanzu sukayi?"
"Haka take dasu aka haifeta"
"Meyasa kuma ina matsayin mahaifinta baki taba faɗaminba,kenan da bangani ba shikenan harsai ta girma ta fita naji a bakin mutane kome,idan kuma hakan ciwone kika barta dashi ya wuce gaban kwatance fah,yakike ganin za'ayi,kullum ina faɗamiki banason wannan shuru shurunnki,zai iya kaiki ga aikata danasani"
"Kayi haƙuri banason ka shiga damuwane idan ka gani,sannan bansan ta yanda zan sanar dakai ba,na faɗawa addah laari ma tafaɗa maka tace baruwanta"
"Eh baruwanta mana,ke kinga laifinta a ciki,tazo ta faɗa ace dama Allah allah take ya faru ta faɗa? Maza saka kayanki mutafi wajen maganin gargajiya da kuma na nasara,wannan abin ai bana zama bane,waya sani ma ko bata gani ke baki sani ba,inaga ma yanada alaƙa da kukanta da daddare,ko ciwo ma suke mata"
"Tana gani fah dasu"
"Taya kika san tana ganin"
"Idan nasaka mata haske ina tafiya dashi tana bin hasken"
"Ni ban yarda da wannan zancen ba,maza shirya mu tafi asibiti a ji shin mai yake damunta"




🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are









____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________








Page 🖤13🖤

Babu 'bata lokaci daneji ta shirya domin su tafi asibitin,har sannan Bombee na hannun mahaifinta,motsi kaɗan idan tayi ya leƙata,gani yake tamkar ƙwai ne a hannunsa,zai iya fashewa a kowanne lokaci.
Ƙosawa yayi darashin shiryawar tata da sauri,dukkuwa da yanda take iya ƙoƙarinta wajen yin saurin,gani yake kaman jinkirinta a lokacin wani abun zai iya faruwa.
Fitowa sukayi daga ɗakin tareda yiwa Inna laari sallama kana suka kama hanyar asibitin a mashin ɗinsa.
Yana tafiyah yana waiwayen ƴar tasa.
"Ki kulada ita fah kar wani abu yasameta kafin mu isa.......yi shuru uwata kinji,bari muje a baki magani su daina yimiki ciwo,irin wannan ido haka akan wane daliline bazayyi ciwo ba,hmmm Allah dai ya kyauta."
Magana yake tayi shi kaɗai,itadai Daneji bata cemasa ci kanka ba,sai rarrashin ƴarta da take tayi,har suka isa asibitin wanda bashida nisa da anguwarsu.
Kafe mashin ɗin yayi,ya kar'bi ƴar suka shiga asibitin..
Nan ma dayake litinnin ne layi har bakin asibitin,kasancewar kuma yahaɗa yanayi da damina,jinyace jinyace sunyi yawa.
Wani bakin banci yasamu a gefe ya nunawa Daneji ta zauna,kafin yabada yarinyar ta riƙe,shikuma yashiga ciki domin yayiwa likitan magana akan lalurar tasu.
Feeder Daneji ta fitar tana bawa Bombee ruwa,wacce taga kaman alamun fatar bakinta ya bushe babu ruwa. Dadai lokacin ne kuma wata mata itama da goyo tazo ta zauna zata since yaron ta tabashi abinci..
Daneji bata kulada ita ba sai gani tayi ta miƙe dasauri,hannunta yana rawa ta toshe bakinta.
Ja da bayan da takene tana nuna inda Daneji take,yasa kowa hankalinsa yadawo wajen da sauri.
Bakinta yana rawa tafara cewa.
"Wayyo ba mutum bace,wani abu nagani a radu a hannun matar nan"
Kowa maida idonsa yayi kan Daneji,wacce

Please Login or Register in order to submit comment