Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba taji yafara jan motar. Dan haka iya faɗamusu tayi su suka belt,daganan kuma aka fara tafiyah.
Giya ya danna tareda takar motar ya ɗorata sama.
Ganin yanda yake shirin takar motar kaman yasameta a jari bola,yasa iliya koƙarin yimasa magana,saidai tun kafin yace komai yaji kaman an ɗaga motar a sama,saboda yanda suke ƙoƙarin hawa wani uban tsauni dayake gabansu.
"Hahhhah inason kallon wannan yamayin a fuskar abokan kasuwan ci,karku damu domin ƙiran sunana ku zageni,kuna cewa karka kashemu tsinannan Allah,banshiya mutuwa ba wayyo......to kuce min TORO sunan kenan,kunga zaku fi daɗin cewa ”Allah ya tsine maka toro” ihu shagali"
Yana gama faɗin hakan kuwa ya hango idon Hajiya zeenah,wacce tamanne a jikin kujerar bayan,idon ta sun firfito kaman an jijjiga bera a buta......
"Hajiya tundaga hawan farko har kin yi laushi,todai karki manta ki adana kuɗinki fah,don kowanne hawa akwai nasa ƴan fashin,in bakida kuɗi a miki dukan kuɗin.
Yawan hawanki da shiga duhuwar dajin gangirwal,yawan gamuwarki da rabonki.........muje zuwa......




🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are









____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]






*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________







Page 🖤08🖤




Hasashen sa kuwa bai tafi a banza ba,dan Hajiya zeenah tanajin an fara gangara ta mulmulawa toro ashar.
"Kai kuwa wanne ɗan rashin arziƙine,kashe mu zakayi bayan ka karbi kudi,wannan wane irin wajene na kawo kaina ni zeenatu,akan wata biyan buƙata ta duniyah. Juya juya damu na fasa zuwa garin waje saikace hanyar aljanu"
Juyowa toro yayi yana dariyah,tareda ƙarewa mutanen cikin motar kallo kafin yace.
"Ai hajiya tunda har muka ɗau hanya tofa sai munkaita casss,kuma banda abinki hawa ɗaya fah muka hau,harkin sare da tafiyar. Hm aikinci sa'a ma da ba motar ogah kika hauba,Aradu ta inaga mutuwa zakiyi muss kafin a isa,maza ma kwakwalwarsu juyewa take idan suka hau motarta zuwa gembu bareke.
Ki gode Allah ta ɗau hutu bata nan hanya bata haɗaku ba"
Duk maganar dayake Hajiya zeenah kwatakwata bata gane mai yake nufi,dan zuwa yanzu ɗankwalin ta ma yabar ƙoƙon kanta,batun gyale kam tun a hawan farko sukayi sallama.
Wani tsaunin ya nufa da mungun gudu,take kuwa su iliya suka sake zare ido tareda salati mai cikeda ihu.
A haka sukayi ta gwabzawa har zuwa wasu daƙiƙu masu yawa.
A lokacin duk wanda yaga Hajiya zeenah bazaice itace wannan matar ba mai kwalisa da kuma izzah,jikinta duk yayi dama dama da aman abincin dataci da safe,idonta yayi zuru zuru kaman wanda tayi azumin shige.
Zuwa yanxu sunyi hawa mai nisa akan tsaunin,dan sun fara shiga waje mafi duhuwa a kan wajen.
Ƙara gudun motar sukaga toro yayi tareda zurawa hanyar ido yaga ta inda wani abu zai bullo.
Aikuwa hasashensa bai tafi a banza ba,dan wasu mazane suka fito sun shafe dukkan jikinsu da da baƙin shuni,gasu murtuƙa murtuƙa,fuskar nan babu alamar rahama.
Kashe motar Toro yayi tareda waigowa ya kalli iyani,dan duk cikin motar ita kaɗaice mai ɗan dama dama a ciki,duk itama haka take kaman gawa taƙi rami.
"Keee ki kama wannan matar ki gyara,wani plan zamu haɗa,idan kuma ba haka toba tara ba har ɗari ma kunshiga a wajen wanann arnan dajin. Ni babu abinda zasu min,amma kukam bazasu ragamuku ba"
"Meyasa bazasu ragamana ba toh"
Iyani da samu damar tambayar sa cikin ƙarfin hali.
Wata soyayyar dariyah yayi kafi yasake zubamata ido wanda yasha kwalli marau.
"Iyata kenan aini da kike ganina bazasu tabani ba,saboda ni yaron BB ne,babu wanda ya isa taban a cikinsu idan na nuna musu tambarina na ƙungiyarta"
Yafaɗa yana nuna musu wani tatoo ɗin baƙar macijiya a wuyansa,an rubuta BLACK BLOOD CLUB(BB) a gefenta.
"Menene BB yake nufi kuma"
Kungiyarmu kenan,wanda shugaba take jagoranta,idan kanaso kayi tukin mambila kuma ka dunga fita lafiyah,to ka shiga kungiyar BB,muna kaiwa kudin duk wata wajenta,itakuma tana yimana shamaki da duk mai kawomana cikas daga cikin aranan jejinnan.
Suma kuma tayi yarjejeniya dasu bazasu taba yaranta ba,ita kuma zata barsu suyi nasu aikin"
"To baka ganin zasu kamamu dukka hadda kai,musamman ma idan yazamo bata nan bare ta ceceka?"
Iliya ne wanann karon ya samu damar tambayr tasa,dan bayan shugowar su cikin jejin,bayan wannan majanuniyar hanya ya kuma samun wani abin mamakin.
A yanzun ma saida toro yayi dariyah kafin yace.
"Hhhh duk yanda zan faɗamaka bazaka ganeba,duk da cewar akwai kishi kishin labarin cewar bata cikin jejinnan a yanzu,tana can kan ainihin dutse,tana rainon ɗanta data haifa wata biyu da suka wuce......duk da haka babu wanda ya isa ya taba ko dabba idan nata ne a cikin jejinnan bare kuma ku yaranta,inda badan suna tsoronta ba,mu kanmu bazasu barmu da sana'rmuba.
Amma yanxu duk wanda ya matso kusana na nuna masa tambarina amma kuma yaƙi barni,kawai dannan signal ɗin jikina zanyi,daga nan ita kuma zata ga inda duk nake.......hmmm karkuyi hasashen ma wane hukunci zasu fuskanta,saidai su tashi daga jejin gabaki ɗaya kafin tazo farautarsu"
"Tambaya biyu zanyi maka malam toro.
_shin taya zata gane sune suka tabaka to?
_sannan shin bata hanaku bayarda wanann bayanai nata mai hatsari,iyah a mota muka haɗu dakai,amma kuma harka bada wannan labarin dangane da ita,baka ganin kaima zaka iya sakata cikin matsala da wannan labarin?"
Kallon iliyah toro yayi bayan yaji mai faɗa,da wani mai shugabanne daya shiga tunanin irin bayanan daya basu,amma toro ko a jikinsa,saima ƙara kwanciya dayayi a jikin kujerar matuƙin motar.
"Amsarka ta farko,signal datake jikinmu ba guda ɗaya bace,idan mai bincike ne yakamamu da wacce zamu aika,idan aranan jejine da wanda zamu danna,idan kuma namun dajine shima da wanda zamu danna,idan kuma hatsarine shima da wanda zamu danna,in mutuwa kuma mukayi akwai wacce zata kawo da kanta.
Tambayarka da biyu kuma,bata taba cemana karmu bada bayananta ba,hasalima neman abu take wanda zata lakato wani,amma kuma babu wanda yake kulada sha'aninta,sannnan a yanda na kejin labarin ta,bata son masu mulki da masu kuɗin ƙasar nan,Sannan duk da kasancewarta jami'ar atsaro a ,yanzu kuma ko sunan bata sha'awar jinsa........
Lahh na manta abu ɗaya ma,wani naji kace bana tsoron kukai labarinta,dan yarusulu ku kai labarinta,intaga dama ko gawarka baza'a ganiba bare kakai labari,abun ai ba yanzu aka faraba........."
Shuru motar tayi kowa yana saka labarin toron a mahangar tunaninsa,indai abinda yafaɗa da gaskene,to kuwa wannan wacece haka ,mutumce kuwa?....
Shawarar da toro yabayar suka yarda da ita,duk da saida aka tsayah hajiya zeenah ta kintsa jikinta tukunna,fuskarta kaman tayi gudawa dan rama.
Shiryawa sukayi akan Hajiya zeenah ƴar uwar mahaifiyar ta ce,saikuma iliya da iyani yaranta ne.
Cikin ɗarɗar da addu'ar Allah yasa aikinsu yayi suka fara tafiyah zuwa cikin duhuwar jejin.
Wasu irin bishiyoyine a cikin dajin masu manyan manyan ganye,da alama suna samun ruwa yanda yakamata,duhuwar da suka bayarne yabawa arnan dajin samun damar kaiwa sumame batareda matsalaba.
Lura sukayi da yanda toro yafara tafiyar da motar ta siga daban,hakanne yaƙar hauhawar gudun da zuciyarsu takeyi zuwa wani mataki mai yawa.
Signa yayi Iliya dayake gefensa tareda yimasa alamar ya suna zuwa.
Aikuwa kaman kiftawa sukaga mutane sanye da baƙaƙen kaya sun dira a gabansu,hannunsu riƙe da bindiga wasu kuma da kwari da baka.
Hailala da salati hajiya Zeenah tafara tana zazzare ido,ƙiris take jira taji ta inda za'a kawomata farmaki.
Wani daga cikinsu ne ya matso inda motartasu take,da alama shine shugabansu,dan yana sanye da jan ƙyalle maimakon baƙi kaman na sauran.
Yare suka fara shida toro,wanda su Hajiya zeenah basa jin mai suke faɗa,da alama ɗaya daga cikin yaren yankinne,bayan kaman wani lokaci ne ya juyo ya kalle su,fuskarsa da alamar mutuntawa ba kaman ɗazu ba,babu tantama Toro yasanar dashi dangan tarkasu da ogar tasa kaman yanda ya tsara.
"Hajiya ina wuni fah ya gidah?"
Yafaɗawa Hajiya zeenah cikin hausarsa da daƙyar ake ganeta.
Gyaran murya Hajiya zeenah tayi tareds tattaro dukkan jarumatarta,ta amsa masa gaisuwar batareda da sake haɗa ido dashi ba.
"Hajiya ƴaƴan ki ba irin kayanki mai kyau jikinsu,ke wane irin uwane kam?"
Zuru tayi tana kallonsa,sai yanzu da kulada kayan jikin iliyan,wata maleliyar riga ce a jikinsa,da kuma wani wandon jeans koɗaɗɗe,gwanda ma ita iyani tasaka atamfa mai fasali.
Rufe ido tayi tareda cewa
'Iliya wataran shi zayyi ajalina da wannan shegen shigar tasa,badama a bashi kaya ko a bashi kuɗi ya siya saiya sayar ya kashe kuɗin'
Maganar toro ce ta risketa tana tsaka ta maganar zucin.
"Ka ganene,hakan ra'ayinsane,sannan kuma batare suke da hajiyan gari ɗaya ba,tafiya ce ta haɗasu yau"
Kallon rashin yarda ogan yabi toro dashi tareda cewa.
"Toro kasake rena mana hankali ne fah? Dama kayi mana wasu kwanaki fah?"
Mazewa toro yayi ganin suna son ɗagoshi tareda yin magana yana haɗe rai.
"Kaga ogah wannan ba irin na wancan bane,ni yaushe zan hanaka karbar kuɗi a wajensu,kawai dai aikin shugabane ne shiyasa,inkuma kana ganin na barka ka tabasu,sai ku ƙaƙare da ita toh"
Nazari ya tafi,yana shakkar ya kamasu kuma toro da gaske yake,yabarsu kuma toro ƙarya yake masa fah,gashi rukuninsa tunda suka fito basu kama ko ɗaya ba sai yanzu.
Haka suka cigaba da magana,babu yanda ya iya yabarsu suka wuce,dan idan yakamasu kuma toro da gaske yake to kashinsa ya bushe a wajen shigabansu,don idan BB ta tashi saita ƙwaci kusan kuɗin dasuka yi shekara suna tarawa.
Da haka su Hajiya zeenah suka tsallake tujarar mutanen dajin da taimakon toro.
Tafiyah suka cigaba dayi cikin hawa da sauƙa,zuwa lokacin babu zancen ihu ko kuma firgici,sunyi shuru sun miƙa lamarinsu ga mai duka,suna jiran sanda zasu jisu sun faɗa ko kuma toro yace musu sun iso.
Bayan gwarwarmayar da suka shiga daga ƙarshe sun kai ga isa garin gyembu shazaran majaran.
Iyani ce mai ɗan karfin hali a cikinsu,ita tasamu damar yiwa toro godiya da taimakon da yayi musu,dan har gida ta roƙeshi ya kaisu,saboda a halinda iliyah yake ciki bazai iya tuƙa motar ba
Duk abinda ake Hajiya zeenah bata sani ba,gabaɗaya hankalinta baya jikinta a lokacin.

.........Toh su Hajiya zeenah tundaga yanzu anyi laushi,burin zao cika a haka kuwa?......




🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are









____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]







*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________







Page 🖤09🖤



Buɗe ido tayi ta kalleta a wani ɗaki mai rufin zana,saidai yanayin zanar wata kalace daban mai ƙarfi da kuma adon rawaya rawaya.
Abinda ya farune yafara tariyowa cikin ranta.
Kama daga fitowarta daga gida neman wacce zatayi mata maganin lubna,harma da kuma shigowarta wata duniya sabuwa da tayi.
Zabura tayi ta miƙe tareda ya mutsa fuska,jikinta yayi tsamin kaman anyi mata dukan tsiyah.
Tambaya tafarayi a cikin ranta,akan nan ɗin inane,batakai ga samun amsar tambayar ta ba,kokuma son tunowa yaushe ta shigo wajen ba,ta kalli labulen ɗakin ya motsa,da alama wani ne ke son shigowa a cikin ɗakin.
Zurawa baƙin ƙofara ido tayi,yayinda bayan kowanne daƙiƙa zuciyarta ke hawar da bugunta zuwa matakin sama.
Sauƙe ajiyar zuciya tayi tareda runtse ido ganin ba kowa bace ta shigo face Iyani.
Tana sanye da wasu irin kaya da bata taba ganinta da irinsu ba,hannunta kuma ɗauke da akwashi guda uku akan akan faifayi.
Murmushi tayi tareda ajiye abin hannunnata kana tace.
"Ina kwana Hajiya sannu da tashi,ya jikin?"
Batareda ta amsa gaisuwar ba tafara jefowa iyani tambayoyin data kasa bawa kanta amsarsu.
"Menene ya faru bayan barin mu jejinnan,sannan nan inane?"
"Uhmm Hajiya suma kikayi lokacin da toro ya sauƙemu,bayan munshigo garine na roƙeshi ya kawomu har ƙofar gidanmu,kasancewar ni ban iya tuƙi ba,shima kuma iliya a lokacin bazai iya tuƙi ba"
"Yanzun wane lokacinne,tun yaushe nake kwance?"
"Eh tun jiya da yamma,yanzu kuma karfe 9:45am na safiyah.
Yakamata kici abinci kiyi wanka sannan ki rama sallolinki,kafin kuma muyi maganar abinda ya kawomu"
Tana gama bata amsar ta buɗe kwanukan da suke gabanta,ɗayah tuwon Doyane,ɗayan kuma miyace mai kala kalar ja da kuma baƙi,wanda Hajiya zeenah bata taba ganin irinsa ba"
"Wannan kuma mai nene?
"Uhm ɗayane daga cikin irin abincin nan yankin,muna dayawan doya sosai,shiyasa yawanci abincinmu muke sarrafata dashi,baƙin cikin miyar kuma kifine da kuma busashshen inibi,kici akwai daɗi sosai."
Daga haka tabar ɗakin domin bata damar samun cin abincin.
Kaman mai tsoron kada taci ta mutu haka ta tsoma hannunta a cikin miyar takai bakinta domin ta ɗanɗana.
Uhm babu laifi fuskarta ya nuna abincin yayi daɗi,babu bata lokaci tafara yankar tuwon doyar tana ci,har saida taji cikinta ya ɗauka tukunna.
A ranar basu samu damar fita zuwa gidan su Bombi ba,saboda har yanzu jikinsu bai dawo normal ba daga tafiyar da suka niƙo.
Iyanice ta kalli mahaifiyar su wacce take zaune tana bushe tsinkayen da suke cikin ganyen shayinta,maganar da iyani tayi ne yasakata tsayawa da abinda take takalleta.
"Inna ina labarin Bambi kuwa,wacce da addah ke bani labarinta?"
"Oh ɗiyarnan,ke kuma mai zakiyi da labarin bombi har kike tambaya,na daɗe banga mai son yaji sunanta ba ma ,ballantana kuma labarinta"
"Ayyah inna inaso na haɗu da itane,akwai abinda nakeso muyi magana da ita akai,gidansu zakiyi min kwatance?"
"Handi mee Iyani,ki haɗu da Bombee?,akan wanne babban dalili haka?"
"Lahh bafah abune babba sosai ba,dama Hajiya ce takeson yin magana da ita"
"Hajiyannaki dan batasanta bane hala,tun wuri ina yimuku kashedi ku fita a harkar wannan yarinyar,dan ita ɗin tauraruwa ce mai wutsiya,ganinta bashida alheri ko kaɗan,maza ma basuja da sunanta bare kuma ku da baƙine,bakusan komai a gameda garinnan ba da kewayensa"
Shuru iyani tayi tana kallon mahaifiyar tata,da alama bazata samu amsar da takeso ba a gareta sam.
Tashi tayi ta nufi ɗakin da Hajiya zeenah take,tun kafin tace wani abu Hajiya zeenah ta dakatar da ita tareda cewa.
"Naji duk abinda innarki tace iyani,tabbas daga yanda nakejin labarinta a bakin mutane,ita yarinya ce mai hatsarin gaske,saidai nayi tafiya mai nisa nazo garin da take,bazan iya tafiya haka hannu rabbana ba batareda na ganta ba,idan itace taƙi amincewa buƙatata to shine zan haƙura"
'Jinjina taurin kai da kuma Ra'ayi irinna hajiya zeenah tayi,a zatonta jin labarin inna zaisa tace ta fasa,amma kuma ashe abin ba haka bane'
"To shikenan Hajiya zamu je gidanna su a gobe inshaaallah,koma menene sai muji mai zatace"

___ ____ ___

A bakin wajen wani mai shayi iliya ya tsayah ta motar,tareda fitowa ya nufi wajen da samarin ke zaune a waje.
Sallam yafara yimusu suka amsa,kafin ya tambayesu abinda yake nema.
"Bayin Allah idan bazaku damu ba dan Allah gidan su Bombi muke nema?"
Kowa zaro ido yayi yana kallonsa ,wani kanma daya kurbi shayi da biredi,bai san lokacin daya furzar dashi ba yana kallon iliyan.
"Kai amma kai baƙone a garinnan koh,rabon danaji ance gidan su bombi shekaru da dama,ai kawai kace mana gidan su Innayee,waye ma yasan gidannan danasu bombi,ko mutanen gidan bazasuso ka haɗata da gidansu ba,amma jirani nagama shan shayi na rakaka gidan,maƙwantanmu ne katanga ɗaya"
Yana gama faɗin hakan ya cigaba da cusa biredinsa,iliya yana tsaye yana jiransa har yagama kafin yazo suka nufi wajen motar.
"Kai kuma daga cewa zaka tambayo gidansu saika yi tafiyarka, kaman an aiki bawa garinsu,wannan kuma wanene a tareda kai,a shegen surutunka har kayi aboki a garinda baka sani ba koh?"
"Ahah hajiya wannan ɗin ɗan anguwarsu su bombinne,na jirashi yagama shan shayine,akan zai rakamu gidan"
Kallon ta fahimta tayi musu kafin da ɗauke kanta.
Zagayowa yayi ta zauna a wajen zaman banza ba gefen drivern kafin suka fara tafiyah.
Tunda suke tafiyah babu wanda yace uhm a cikinsu,sai iya saurayin dayake nunawa iliya inda zaibi,da haka har suka ƙariso ƙofar gidan su bombin.
Sallama yayi musu tareda cewa.
"To ga gidan da kuke nema kun ƙariso,Allah ya baku sa'a sannan ya fitarku matsala,ni nayi nan"
Baƙin ƙofar gidan suka ƙarisa tareda yin sallama,da har sun sare akan babu wanda zai fito,sai kuma sukaga wani dattijo fari sol mai ɗan tsayi kaɗan ya fito daga gidan.
Gaisawa sukayi hannu da hannu da iliya kafin yayi musu iso zuwa cikin gidan.
"Lale maraba daku,daga ina haka kuka zo"
"Eh to tafiya da nisa malam,ko zamu iya shiga mu zauna"
"Eh to mai zai hana"
Tun daga bakin zauren gidan yake ƙwalawa matar tasa ƙira.
"Yawuro ina kike so munyi baƙi daga waje mai nisa"
Farar dattijuwa ce tafito daga ɗakin,fuskarta cikeda fara'ah,kana ganinta kaga wayayyiyar mata.
"Lale marabanku da zuwa,sannunku da zuwa"
Cikin annashuwa da sakin fuska ta tare su,duk da kasancewar bata sansu ba.
Ruwa aka kawo musu mai sanyi tareda kindirmo,domin kowa yakallesu dama yaga wayayyun fulani masu cikeda ilimi,domin duk yankinsu su dama fulanine a wajen.
"Innayee maza kizo ki gaisheda baƙi mana,sau nawa nake faɗamiki banason wannan halin na kunyah sosai"
"Lahh mace ai ana sonta da kunya,musamman a wannan lokacin"
Hajiya ta faɗa itama cikin fara'ah.
"Eh to hakane,musamman ma kinga mu fulani hakan a cikin jininmu yake"
Suna cikin maganar ne farar yarinyar tafito daga ɗakin kanta a sunkuye,a gaban su Hajiya zeenah ta tsugunna tareda gaishesu ƙaramar murya mai sanyi,kayan Makaranta a jikinta,da alama islamiyyah zataje.
"Ina kwana Hajiya ya hanya"
"Lafiya kalau,makaranta za'aje kenan,to Allah ya taimaka"
Motsin mutum sukaji yana shirin fitowa daga wani ɗaki take kallon na Yawuron.
Wata matace tafito daga cikin ɗakin tana shashima bangon da take bi.
Duk da kana kallon yanyinta zaka hango tana cikin yanyin laluri,amma kuma fatarta fari sol,ga idonta kuma dara dara,saidai da alama basa aikinsu da kowanne ido yakeyi.
"Innayi innarki daneji ta fito,rakata banɗaki dannan buta a hannunta,da alama bayi zata zaga"
Tun kafin ta rufe baki innayin ta tashi tareda ƙarisawa wajen wacce aka ƙira da Danejin.
Duk abinda yake faruwa su Hajiya zeenah suna kallo,har innayi takai matar banɗaki ta dawo da ita ɗakinnata.
Sallama tayiwa su Hajiya zeenah da kuma innar tata,kafin ta tafi makaranta.
Malam Ahmadu yashigo gidan tun bayan da yayiwa su Hajiya zeenah iso ya fita.
"To Hajiya muna jinki mai yake tafe dake,domin bamu wayeki ba,gashi kince mana wajen mu kika zo"
"Eh hakane malam wajenku nazo,idan baxaku damu ba dama wajen ƴar ku nazo da magana muhimmiya,shin kozan iya ganinta?"
Murmushi Yawuro tayi,da alama hasashenta yazama gaskiya,neman iri hajiyan tazo nema a wajen su.
"Ai Hajiya kin riga kin ganta,saidai ko kuma maganar manyan yanzu daza'ayi"
"Ahah baki fahimceni ba,bombi nake nufi,akwai abinda nakeson tattaunawa da itah"
Tsitt wajen yayi kaman an ɗauke ruwa,yayinda murmushi da kuma fara'ar dayake fuskar mutane biyun ya bace nan take,babu abinda ya maye gurbi zai mamaki da kuma baƙinciki.
Baki buɗe suka tsaya suna kallon Hajiya zeenah,kafin daga baya mlm Ahmdu yasamu ƙwarin gwiwar cewar.
"Uhm Hajiya inaga kinyi batan gidane,amma ni ƴata guda ɗayace Khadeejatu(innayi),bayan ita kuma banni da wata"
"Amma mlm an ce mana nan.........."
"Ya isa haka hajiya,tun inaganin girman ki,kina ganin nawa ki daina kawomin wanann zancen,idan kuma kin dage dole saikin samo mai sunan da kika ambata,to ki tafi jeji can inda yadace da mai sunan,amma banan ba gidan mutunci"
Yana gama faɗin hakan yatashi yayi waje.
Itama yawuro kallonsu tayi tareda cewa.
"Dan allah kozaku iya tashi,ina son naɗe tabarmata da kuke zaune akai"
Cikeda mamaki Hajiya zeenah suka tashi suna kallon Yawuron da lokaci ɗaya ta sauya daga matar da ta tarbesu.


Toh fah yaya takene?.......


🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are









____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]






*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________







Page 🖤10🖤




Har suka fito daga cikin gidan su bombin babu wanda yacewa wani komai,saboda ɗumbin abin mamakin da suka gani.
Magana suka ji a gefensu,suna waigawa suka ga ashe saurayin daya rakosu gidanne,yana jingine a bakin motar tasu.
"Sannunku da fitowa,na tabbatar masu samu amsar abinda kukaje nemaba"
"Taya kasan hakan,ko shiyasa ka tsaya kana jiran mufito,kenan kasan inda take?"
"Eh to nasani bankuma sani ba,kunsan ance ba'a aikin banza,zan nuna muku hanyar dazaku bi ku sameta dai.
Amma daman batun ku tsaya cikin gari kuna nemanta bazaku taba samunta ba,wanda suka sani ma bazaku kaiku ba,saboda gudun abinda ke iya zuwa ya dawo."
Karisawa wajen motar sukayi inda saurayin yake tsaye,Hajiya ce ta kalleshi cikin maganar serious tace,
"To shikenan naji zan biyaka idan ka fadamin inda take,amma kafin sannan inason nasan ita wacece daga abinda ka sani,saboda daga yanda naga iyayenta fuskarsu sauyawa tayi lokaci guda,dan na ambaci sunanta,menene dalilin hakan.
Tunda kace maƙwantansu ne kai,to bashakka kasan wani abu dangane da rayuwarta"
"Zaro ido yayi kafin yayi murmushi,dan da alama bayyi zaton zata nemi sanin tarihin bombi ba,amma kuma koma wanene yaga abinda ya faru,dole zai zargi wani abun"
"Tabbas hakane nasan bombi ciki da bai,kuma inaga bayan mutanen gidansu babu wanda yasan ta kamanni,kasancewar ni ɗan ɗakin mahaifiyarta ne ina yaro,saidai amma saikin biyani,sannan kuma saikin min alƙawari babu wanda zai san na faɗamiki wanann labarin,saboda kar in kinji labarin ta ki fasa neman ganinta"
"Namaka alƙwarin babu wanda zaiji,sannan kuma zan biyaka kamar yadda ka buƙata,kawai burina shine ka faɗamin gaskiya"
"Inshaaallah zan faɗamiki gaskiya,amma kafin sanann mu shiga daga motarku,gudun mutane kar su ganmu,dan idon mikiya ne da ita,tana da mutane a wurare da dama a ko'ina.
Ina tsoron kar na samu matsala"
Amincewa sukayi da zancen saurayin,koba komai hakan yafi da tsayuwarsu a wajen.
Barin ƙofar gidan sukayi,tareda kama hanyar da yace su bi.
"Da farko kafin mu fara sunana Umar,ana ƙirana da MARUJE,labarin daya faru shekara ashirin da biyu baya,ya fara ne.................

_______*****________




Ayyiriri ayyiriri,Malm Ahmadu ya iyo amaryah a hayin Fulanin yanki, masu ƙura,itace ta farkon mace wacce aka aura da Garesu.
To ikon Allah,shikuma mai takaishi auren ƴarsu,ana fa cewa iri irinsu mayune,shine yaje ya ɗakkowa kansa irinsu,ƙyan ɗan macijine fah dasu wayannan mutanen,lallai Inna laari taga takanta,saita san irin zaman dazatayi da ita. Su fah maza kana zaman zamanka sai su ɗakko maka alaƙa ƙai,daga kawai ta shekara uku babu rabo shine har ya manta soyayyar da sukayi dandali ya auro mata fulanin ƙaurah"
"Hmm kema dai kya faɗa,muma ina gashinan masu haihuwar ma anyi mana kishiyar daga shekara biyu da aure,maza ai sai a barsu"
"Larai ta faɗa tana nuna Innar muruje da baki,wacce take alwalar Azahar"
Duk abinda suke tana jinsu,amma ko ci kanku bata ce musu ba,saima shigewa ɗaki da tayi.
Dare yana kawo kai guɗa ta cike anguwar tasu da kuma raye rayen fulani sama sama,wai hakan ma ba'ayi wani bidiri da al'adu ba,kasancewar iyayen yarinyar basason auren.
Malm ahmadu ne yadage akan sai ya aureta,lokacin daya ganta takai nono gonarsu talle,dayake yana kuɗi a lokacin sosai,duk anguwar babu wanda yakaishi girman Gonar Ganyen shayi,gashi yanada hanya sosai a kamfanonukan da suke siye da siyarwa dasu.
Tun daga bakin ƙofar shigowar tasu LAARI ta fito da fara'arta ta tarbi Amaryartasu. Al'amarin daya bawa aminanta ma mamaki,ba iya su dangin amaryarba,dan kafin shigowarsu babu irin abinda su Larai da danginta basuce ba akan abokiyar zamannnata ba,amma tayi shuru tai biriss da abinda suke cewa,sai daga shigowar amaryar ta bawa kowa mamaki.
Duk da hakan ba abine dama da bazai iya faruwa ba,kasancewarta mace mai shuru shuru kuma marar hayaniya,sannan kuma ta yarda mijinta,tunda tasan badan yana ƙinta yayi mata kishiyar ba.
Har ƙofar ɗakinta ta rakata tareda buɗe mata kai.
"Sunan Laari,nice Abokiyar zaman ki dakika shigo gidannan kika tarass,ina fatan zaki ɗaukeni kema abokiyar zama,sannan kuma zaki bani hadin kai mu samar da zaman lafiyah,Allah yasaka albarka da zaman lafiya a zamantakewar mu"
"Ɗan murmushi Daneji(an samo sunan ne daga Alamar "fari" a harshen fillanci,Ainihin sunan ta shine Fatima,taci sunan mahaifiyar baffansu. To kasancewarta fara sosai ko a gidansu yasa ake ƙiranta da Daneji).
"Inshaaallah zaki sameni mai binki sauda ƙafa Addah laari,nagode da ƙaunarki gareni,bansan da wane kalmomi zan yaba miki ba"
"Bakomai ki nuna min a ta fuskar halayyarki ma ya isa"
Daga haka Inna laari takoma turakarta wajen mutanenta,tabar Daneji da Nata ƴan uwan a sabon gidannata.
Sai bayan kwana biyu da kawowa amarya kafin ƴan biki kowa ya watse,aka bar amarya daga ita sai halinta.
A zaune take ta tafi tunanin yanda rayuwarta a sabon wajen zai kasance,musamman da tasam cewa yan uwanta na daff ta yin ƙaura zuwa arewancin nijeria,dan dama su ba mazauna bane,abinda iyayenta suke tsoro kenan dama ita kanta,shine su barta a wajen da basuda tabbacin dawowa.
Saidai komai yayi rintsi maganin sa Allah,haka iyayennata suka koyar da ita,dogaro da Allah a kowanne lokaci,duk da kasancewarsu masu tashi basuyi boko ba,amma karatun addini kam ko na garin bazasu nuna musu ba.
Saurin share guntun hawayen daya gangaro mata tayi,jin motsin mutum ya shigo ɗakin.
Inna laari ce ɗauke da ƙwaryar abinci a hannunta.
Ƙarisawa tayi inda Daneji ke zaune a hankali tareda dafa hannunta.
"Nasan kuka kikeyi,saidai bazan hanaki ba, ko kuma naga laifinki,domin kowa yasan abin sai anjure tukunna

Please Login or Register in order to submit comment