Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wa ba a cikin tsarin.
"Toh naji mai kikace Zeenatu,amma ya kike ganin zamuyi yanxu toh,wanann idan muka barta bamu san wani irin barazana zatayi ta kawowa ba,sannan gaskiya bazan yadda Jawaheer tazama surukarki ba wannan matar tana gidan"
"Nasan da haka,abin da yafi mu zauna a mukawo shawara kawai,ni burina shine ta fita daga rayuwar ɗana,yazamana cewar inada iko dashi yanda naga dama"
"Plan biyu zamuyi yanzu,na farko shine ki ƙirasu dagashi har matar tasa,kafinnan ki tabbatar yasha wannan maganin a abinci tukunna.
Komin asirin dayake jikinsa to a take zai daina aiki na minti talatin,a lokacin saiki umarceshi da yayi mata saki uku,kinga koya dawo asirin dai aikin gama ya gamu.
Idan kuma wannan bayyi aiki ba,to inaga wata matar zamu aura masa,mu nuna mata muna tareda da ita,ta dunga yin duk abinda muka ce,idan tayi nasara akan Lubnah itama saimu kawar da ita,idan kuma batayi nasara ba itama ta kasheta,shikenan kinga dai ba ƴar mu bace dai abin ya faɗa kanta ba"
"Wanann aiki yayi,kai ai ƙawance dake Hajiya ladi nasara ce,da duk ban tuno haka ba......."
Suna barin falon sashen Jawaheer suka nufa.
Part ne mai zaman kansa dukka natane,komai taga dama shi takeyi a ciki,da ƴan aikinta da komai.
Zama tayi akan kujera tana kallon Madeenah wacce take tsaye batace komai ba.
"Ki zauna mana ko sai na zaunar dake,bar ganin ina kallon inda kike,wallahi albarkacin kin haɗa jini da masoyin xuciyata kike ci,idan ba haka ba ke kin isa kiga inuwa ta ma.....gayyar tsiya kawai,kin tsaya akaina babu wani nuna ladabi,kaman ba yayan ki zan aura na"
"Ai koh yayana zaki aura?...meyasa har yanzu baki aureshin ba toh,wannan zancen har ya gunduri masu jinsa,anaso ana tsoro,in sonsa kike da gaske ki aureshi mana yanzu ƙirr,ina baki jiki a kabarinki ba,ƙaramar ƴar iska kawai.
Batun na nuna miki girma kuma,ke inban da na jefa yayanki a gwandon shara na ƙi aurensa,ai da yanzu na daɗe da zama babbar yayarki,kuma......."
Kafin Madeenah ta cigaba da magana Jawaheer ta wanketa da wani mari mai ƙara,wanda hakan yasata yin shuru da abinda take faɗa ta dafe kumatunnata,ɗaya hannu kuma ta wanke Jawaheer itama da mari.
Faɗa suka fara da doke doke,inda Madeenah ta buga Jawaheer a akan tiles ɗin falon,daidai shigowar su Hajiya ladi kenan,ƴar aiki ta shaida musu mai yake wakana.
Da sauri hajiya ladi ta ture Madeenah akan Jawaheer tana salallami.
"Yau mai zan gani,Madeenah karya min ƴa zakiyi ki fallasheni,ji wani bugawa da kika mata wanda tunda na haifeta bata yi ba"
Jawaheer najin haka ta fashe da kuka tana yarfe hannu,kaman ba itace tafara takalal faɗan ba.
Hannu hajiya ladi tasaka a fuskar Jawaheer tana shafa inda Madeenah ta mareta,wanda yayi jajur yaji fuskar ƴar hutu.
"Mari!!!.....?"
Shine abinda Hajiya ladi ta faɗa cikin bacin rai.
Dukkansu su ukun Madeenah suka tsaya suna kallo harda Hajiya zeenah,ganin hakan yasa itama tayi saurin cewa.
"Itace tafara marina,dan kawai nace idan tanason yaya Jabeer ƙirr ta aureshin mana,shiyasa nima na ram......"
Wani marin Hajiya zeenah tasake zabga mata a ɗaya kuncin,sanann cikin bacin rai ta haɗa da cewa.
"Dan tana son yayanki shine zaki dunga yimata haka,ai tafiki tunda ana saka ta yin abu tayi,da kika bugata a ƙasa idan kika karyata fah,dallah wuce mutafi gida,batun aurenki da Aminu kuma ba fashi,ina akan hakanne kike hucewa akan ta,mai baƙin hali kawai"
Masifa Hajiya zeenah ta dunga surfawa Madeenah,yayinda ita kuma Hajiya ladi ta rungume Jawaheer tana shafa bayanta,har sanann bata daina ihu ba kamar ƴar yaye.
Hawayene yake zuba akan fuskar Madeenah,badan zafin marin da aka mata ba,saidan zafin takaicin yanda har yanzu mahaifiyar tasu ta kasa gane mai yake faruwa,idonta ya rufe kirif akan muradanta,ko ƴaƴan ta bata iya buɗe ido ta gani,bare wani abun taban.
Sallama Hajiya zeenah tayiwa Hajiya ladi tareda bata haƙurin abinda ya faru,har sanann bata wani huce ba,ciki ciki take amsawa,ita a dole an taba mata rabin rayuwarta.
Takaici in yayi dubu to ya kama Madeenah har maƙoshinta.
Suna shigowa gida Madeenah ta shige ɗakinta tareda rufo ƙofah,har wajen magriba bata fitoba,Hajiya zeenah kuwa batabi ta kanta ba,dan ita ta manta ma da ita.
Tafiya take tana zuwa tana dawowa a falon,gabaɗaya abinda aminiyar tata hajiya Ladi ta faɗa mata take tunawa na jiya. Shin zayyi aiki ko bazayyi ba bata saniba,da aika a ƙiramata shi,har yanzu bai shigoba,so take ta ƙirashi cin abincin safe yau.
Maganar Iyani ce ta dawo da ita daga kogin tunanin data tafi. Amintacciyar mai aikinta,koh su Jabeer ma tashi sukayi suka ganta a cikin gidan,komai nagidan kaff tasani,saidai ba komai take saka baki a cikiba,mijinta kuma shine masinjan Alhj Aliyu,wanda bayan ya sauƙa a kujerar CEO ma,bai yasar dashi,sai yace suzo gidan su zauna.
Abinda Hajiya zeenah bata hana na da taji zancen,saboda tanajin daɗin aikin iyani sosai,komai tagani bazaka taba jinsa a wajen wani ba.
"Hajiya angama haɗa abincin yanda kika ce"
"Okay shikenan bari su ƙariso"
Tana nan tsaye a wajen Jabeer ya shigo shida Lubna,fuskarsu ɗauke da mamaki wai Hajiya zeenah taƙirasu karin kummallo a sashenta,abinda bai taba faruwa ba kenan,har lubna tace bazata zo ba,saidai kuma komai yakamata kaje kaga menene.
Kujera suka ja kowa ya zauna bayan sun gaisheda itah,iya Jabeer ta amsawa,luban kam ko kallonta batayi ba,itama data ga haka ta yatsina fuska.
Iyahni ce ta zuba musu abincin dukka kafin ta koma gefe.
Abincin suka fara ci,har sun kuka gamawa Hajiya zeenah ta miƙawa Jabeer kunun gyaɗa a cikin jug mai sheƙi.
"Ka kunun gyaɗa anyi,kaine mai sonsa sosai,nasan kuma yanzu baka samun arziƙin shansha tun mutuwar matarka"
Kallon lubna yayi ƙasa ƙasa kafin ya ɗauki jug ɗin ya tsiyanya a kofi.
Itakuwa lubna ko uhm batace ba,dan dama tasani sarai dan aci mata mutunci aka ƙirata wajen.
Bayan sun gama karawar ne wayar Jabeer tafara ƙara,yana dubawa yaga khalil ne.
Goge bakin sa yayi zai tashi,amma maganar Hajiya zeenah daya doki kunnensa ne yasashi komawa ya zauna.
"Koma ka zauna akwai abinda zaka min"
Tana gama faɗin hakan ta ciro paper da biro ta ajiye masa a gabansa.
Kallonta yake sanann kuma yana kallon paper da alamar tambaya akan fuskarsa.
"Ummah wanann kuma fah,wani saƙo zaki aika"
"Eh saƙo zan aikawa ta kusada kai,yanzu nnan basai anjima ba inaso ka rubutawa Matarka saki uku a jikin takardarnan ka miƙa mata"
Zaro ido Jabeer yayi yana kallon Hajiya zeenah,wacce ta turbune fuska kaman a soja a fagen ya ƙi.
"Ummah saki kuma,mai yayi zafi haka"
"Ba zafi ba har ƙonewa ma yayi,yanzu nan ka rubuta kana batamin lokaci,kuma umarni ba wai shawara ba......koka rubuta mata ka bata,ko kuma na tsine maka yanzunnan.......!
Wanne ka zaba??????"


🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are









____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]






*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________







Page 🖤06🖤



"Saki kuma ummah?"
"Eh saki haka nace,ko baka jiba kurmane kai nasake maimaita maka,ka rubuta sakinta ka bata tabar gidannan,bana sonta a cikin gidannan"
Yawu ya haɗiya mai nauyi kafin yakai hannunsa zuwa kan takardar,tambayoyine suka fara kwaranya a cikin ƙwaƙwalwarsa,meyasa sai shine,meyasa komai shikaɗai zai dunga faruwa dashi? Daga ya fita cikin wanann ifila'in sai kuma yasake shiga wani. Koyaushe shidai bazai daina fita daga chaƙwakiyar mata oho.
Biro ya ɗauka tareda takardar baya ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi.
Hannunsa yana rawa yakafa biron akan takardar,ko meyasa hannunsa da dukkan gabobin jikinsa suke bijirewa umarnin mahaifiyar tasa,zuciyarsa sai bugawa take a matakin daya fi na bugawar kowacce zuciya,ji yake kaman wata boyayyar igiya ta riƙe hannayensa ta hanashi aikata abinda aka umarceshi dayi.
Sautin amon dariyar Lubnah ne ya hanashi fara rubutun.
"Hahhaha Hajiya zeenah kenan,a tunaninki dan kawai kin ƙiramu kinyi wani ƙulunbotonki na lokaci kaɗan,saiki samu abinda kikeso daga gareshi?
Indai har duk lokacin dana ɗauka ina tsaye akan sa,wannan maganin naki zayyi aiki mai nayi kenan duk tsawon lokaci?
Hmm to bariki ji na faɗa miki,.....koda kinyi nasarar fitarda Jabeer daga cikin ikona,bai isa ya sakeni ba dakansa,kuma ya waye washagari da numfashinsa,saidai idan nice da kaina nace ya sakeni.
Anriga an gama maganin,an zuba a kogi ruwa ya tafi dashi,aikin da baya taba karyewa kenan,sai ankai ruwa rana.
Kinga kuwa kozai karye ba'a wajenki ba.
Zabi ya rage gareki Hajiya zeenah,zaki iya sakawa ya sakeni yanzu,amma shima zai mutu,saiki zaba shin zama dani ko kuma gawar ɗanki?"
Tana gama faɗin hakan ta tashi tabar falon ɗauke da murmushin mugunta akan fuskarta,inda ta bar Hajiya zeenah a zaune tana buɗe baki a sake.
Maida kallonta tayi ga Jabeer wanda ƙarfin maganin ya sakeshi,ya kwanta a wajen jiki a sake,da alama bacci yayi ma bai san mai sukeyi ba.
"Me....me nakeji haka ni zeenatu da kunne na?"
Tashi tayi daga dinning ɗin ta nufi ɗakinta,ko kallon Jabeer bata sake ba wanda bacci ta ɗaukeshi a wajen.
Bayan ta tafi iyani ce ta matso wajen tareda ɗebe kayan wajen,a ranta tana mamakin rayuwar masu kuɗi,ita kanta haushin Lubnah takeji,tana ga babu wanda yakaita jin haushinta,itace sanadiyyar mutuwar ɗanta.
Dan kawai ya karza mata mota ta saka akayi ta dukansa saida ya suma,bayan sati guda a asibiti yace ga garinku. Wannan abun yana ran iyani,wanda bata ganin zai gushe daga ranta,har randa ƙasa zata binne mata ido.
Ƙarar waya ce ta tashi Jabeer daga baccin da yayi akan dinnimg table ɗin,yana dubawa ya missed call ɗin Khaleel har wajen goma.
Mamaki abin ya bashi,musamman yanda ya kwanta bacci akan table ɗin cin abinci..
Lokacin wayarsa ya duba,kusan ƙarfe Goma,awa kusan guda kenan da rabi yana bacci. Motsa jikinsa yayi wanda yayi masa nauyi sosai. Tsayawa yayi cakk tunowa da yayi da abinda Hajiya zeenah ta umarceshi dayi.
To shida aka ce yayi saki mai yasa kuma yayi bacci,wata ajiyar zuciya yayi da godiya ga Allah da muryar lubna ta ceceshi dayin sakin,duk da baiji abinda take faɗa ba.
Lokacin dayake niyyar sakin baiji wanann tsoron dayake ji idan zai saketa ba,yanzu kuma tsoron yadawo cikin zuciyarsa sabo fill,bayason ma yaga takardar balle ya rubuta sakin a jiki.
Miƙewa yayi daga kujerar ya nufi ɗakin Hajiya zeenah,duk da cewar bayason abinda take buƙatar ya aikata,amma kuma yanajin babu daɗi ya tafi batareda yaji mai ya faru ba.
A zaune take akan Kujerar madubi tana kallon madubin.
Sallama yayi a hankali amma bata amsa ba,har zai ƙara wata sallamar a zatonsa bata ji mai yace ba,saikuma yaji maganarta.
"Sai yanzu ka tashi daga baccin?"
"Uhm mai ya farune na kwanta bacci nan take,sannan mai kuka tattauna da lubna"
"Babu komai,yayi kyau da baka san mai ya faruba,ka tafi aikinka kawai,nasan za'a nemeka,babu abinda ya faru,karka saka wani dakuwa a ranka"
Duk da cewar muryar mahaifiyar tasa ta faɗa masa sabanin abinda take faɗa,amma kuma tunda tace ba komai shikenan,shima sai yabarshi a akan.
Yana fita ya shiga motarsa driver yaja shi,har suka isa companyn yana tunani,amma yagagara samun ƙwaƙƙwaran wani abu guda ɗaya da tunanin ya bashi mai ma'ana.
A bagaren Lubnah kuwa tana fitowa daga sashen Hajiya zeenah ta cize fatar baki,dama tunda taji wai ƙiran zuwan karin kummalo tasan ba abinda arziƙi bane,saidai ta yanke shawarar taje taji damai surukarta ta tazo,ga zatonta kuwa wani abu suke kitsawa.
Basu sani ba dukkansu tafi ƙarfinsu,kallonsu kawai take daga iya gudun ruwansu,da tayi niyyar a asirce Jabeer karya kula kowacce mace a duniya sai ita,amma yanzu ta sanja shawara,hakan ya nuna tamkar tsoro take bata yadda da kanta ba kenan,dan haka zata bar koma wacece ta shigo cikin gidan,koba komai tasamu abinda zata dealing akan mijinta.
Murmushin mugunta tayi taresa ciro wayarta tana neman number bokan nata,da alamar shawarar data yanke tayi mata,zata ga wace marar tsoronce zatayi kishi da ita,babu wacce take kawowa a ranta sai Jawaheer,wacce dama tasan tana crush akan mijinta,saboda tana tsoronta ne shiyasa taja birki.
Ringing biyu wayar tasa tayi ya ɗaga tareda sakin wata dariyah.
"Madam Lubnah kin bani tazara,kuɗina sunyi kasa fah,gashi ke ba a ganinki sai kinzo muhimmin aiki,ke kaɗaice kike ƙirana na ɗauka nayi miki aiki batareda kinzo ba"
"Kaga zulumgum ba wanann ba,wannan aikin dazayi min akan Jabeer,kabarshi kawai na fasa,bashshi ya kawo duk wacce yakeso cikin gidan,sanann suma iyayensa su aura masa duk wacce suka ga dama.
Inaso ne kowacce tayi danasanin saninsa,bazan iya hakan ba sai kowacce tashigo cikin gonata,sanann zan ɗana tarko na kama akuyar data ke cimin Danga"
"Yanda kika ce madam,hakan ma yayi,ta nanne zaki dunga yin aikinki akansu kina horar dasu"
Sun ɗan daɗe suna maganar a wayar,dukka bai wuce na kisa ba da kuma na yanda zatayi nasara a rayuwa.
Iyani ce ta shiga ɗakin Hajiya zeenah ɗauke da lemo da kuma kofi a hannunta,dan dama ta saba takan kaimata lemo mai sanyi idan tayi irin wannan tunzurar,saidai na yau kaman yafi na ko yaushe,dan tunda ta shiga ɗakin da safe har azahar bata fito ba.
Hakanne yasaka iyani cikin tunanin ko ƙalau.
A zaune take a bakin madubin kaman ɗazu da Jabeer ya sameta.
A hankali iyani ta dan matsa kusada ita tareda yin magana a hankali.
"Hajiya yakamata ki dunga daurewa kina barin wani abun,girma yafara kamaki,karki jawa kanki wata matsala,tabbas babu dadi kam,amma wani abun a dunga bashshi shine yafi dacewa"
"Iyani iyani iyani na barshi ya wuce?.... Ke ganau ce ba jiyau ba akan abinda wannan tsinanniyar yarinyar tayimin,nifa na haifi yaron amma ta maidashi gabaɗaya ƙarƙashin ikonta,har faɗamin take tafi ƙarfin babu abinda na isa nayi..
Taya kike ganin wannan abin zai fita a raina na mantashi? Ji nake kaman nayi a hauka a halin yanzu,wannan la'ananniyar ta kaini bango fiyeda yanda kike zato,ta kashe wasu ta ƙuntatawa wasu,ta zalunci wasu,tunda tazo gidannan babu wanda ya taba jin daɗinta,ƙarin baƙincikin shegiya juya ce,bata komai saidai taci tayi kashi........."
"Eh to hajiya idan har abin ya dameki kuma kinaso kiɗau fansa har haka,mai zai hana nabaki wata hanya,saidai kafin nafaɗamiki zangaya miki gaskiya........Ki gwada neman amincewar BOMBEE (BAƘAR AYAH)wataƙila ta yarda ta aureshi,idan ta baki wasu sharuɗɗan,tabbas zata magance miki duk abinda Lubnah take ji dashi,saidai fah.........."
"Saidai me inajinki wacece ita a ina take?"
"Uhm kawota cikin wanann ahalin naki tamkar kin ɗau wuƙa kin dabawa kanki ne,domin ko ke dakika kawota idan abinta yazo kanki bazata raga miki ba sam,ita din annoba ce da ba wanda ta bari,ko makiyinka bazaiso manna maka itaba ballantana kuma masoyinka hakan ma ke uwa ki aurawa ɗanki ita......ina gwanda miki fitinar Lubnah da nata fitinar"
"A wane waje take,ki sanar dani naje na sameta,sannan menene labarin ta"
"Uhm a garinmu take,saidai nima bantaba haɗuwa da ita ba,kasancewar ba a garin na girma ba,a wajen yan uwana nakejin labarinta,ƙarshen labarinta da naji ance wai Barikin sojoji sun koreta saboda fitinarta bazasu iya ba,ta koma jejin Garinmu da zama a can Gyembu"
"Soja kuma,soja ce ita?"
"Eh sojace tun tana da ƙananun shekaru da shiga,ban san mai yafaru ba dai kasancewar bandamu nasanta ba,amma naji dai ance ba kasafai yanxu ake ganinta ba,saidai in wani ya tabata tazo yimasa hukunci"
"Shekarar ta nawa,kinganin zata amince da abinda zan nema a wajenta,kincemin babu wanda yake sakata abu tayi sai taga dama,sannan kinsan fah lubna da asiri take kashe kishiyoyinta,bakya ganin itama zata kasheta? Koda yake in hakan yafaru ma babu abinda yadameni,indai zata min abinda nakeso shikenan"
"Hhhhh hmmmm hajiya kenan,ni kaina da labari kaɗan naji,nasan hakan bazai faru ba sam,amma dai tunda kinga zaki iya shikenan sai mu kama hanyar gobe inshaaallah,.....amma fah kiyi shawara kafin"
Iyani da faɗawa Hajiya da alamar ta farka da abinda take tunanin zatayi tun kafin lokaci ya ƙure mata.
Saidai Hajiya zeenah tayi nisa batajin ƙira,akan cikar muradinta na rusa Lubnah babu abinda bazatayi ba,inyaso koma mai zai faru ya faru daga baya.
Daga haka ranta yayi fari,ganin ta samu mafita akan abinda yake cimata tuwo a ƙwaryah.
Washagari da safe,da shirin tafiya Hajiya zeenah ta tashi,ina tayiwa Alhj aliyu daɗin bakin ta samowa Jabeer ne mata wacce zata aura masa,babu yanda bayyi ba akan karta kashe ƴar mutane a banza,amma kuma ta ƙeƙasa ƙasa,shiyasa ya ƙyaleta ya zuba mata ido. Wanda yace zai haɗiye gatari saika sammasa ƙota.
Itama iyani a daren tabawa mijinta labarin abinda yake faruwa,shi bai ce komai ba,dan dama hanyar dazai rama abinda Lubnah tayimasa yakeyi. Dan haka zanice ta tadda muje.
Bayan itada iyani sai mijinta,daga nan babu wanda yasan abinda zataje yi,shikansa Alhaji Aliyu bata sanar dashi wacece ba.
Da haka suka kama hanyar jihar taraba Hajiya zeenah iyani da kuma driver,sai tsarabar da sukayiwa iyayen iyanin.
Ita gaba takaita,koba komai zataje gida batareda ta kashe komai ba..........
Muje zuwa,yanxu labarin zai fara..........




🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are









____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]






*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________







Page 🖤07🖤



_________________________



GEMBU babban garine dayake Tsibirin MAMBILA a Sardauna local government dake jihar Taraba a nigeria.
Shine gari na karshe daga nan sai a shiga ƙasar camaroo,hakan nw yasa ya zamo gari mai tarin ƙabilu da kuma tarun yaruka,kama daga irin su Bummi wanda sune manyan ƙabilun garin,sanann kuma akwai Mbubo, Ngebu,Fulani. Wannan sune mafiya yawan mutane da ake samu a yankin,saikuma sauran mutane kaman su Igobo,Hausa,da yaruba,dama wasu daga cikin ƙasar camaroo,wanda mafiyansu kasuwanci ne ke kaisu wajen.
Gembu garine mai tarin ni'ima da kuma ban mamaki.wanda yana ɗaya daga cikin gari mai ƙasar noma ganyen shayi,ba iya ga nigeria ba har ma a africa.
Hakanne yasa wajen yazama mai albarka da kuma tarin hanyoyin samun kuɗi.
Saidai abu dayane yayi wa garin cikas,shine rashin hanyoyin shiga masu kyau,domin nan ma ba iya Nigeria ba,harga duniya baki ɗaya,hanyar garin gembu na ɗaya daga cikin hanya mafi hatsari wajen binta. Saboda manyan manyan tsaunukan da hanyar tabi ta kansu,wanda ake ƙiran su da "Gangirwal" wato a harshen Hausa yana nufin Dutsen mutuwa kenan. Tsaunukane masu matuƙar duhuwa da kuma halittun daji a ciki.
Wannan dalilinne yasa duk da kyawun garin,da kuma albarkarsa baya shiga ran mutane da dama,saboda hatsarin hanyar daza'abi wajen zuwan sa.

Kaɗan kenan daga labarin Gembu,wasu abubuwan zakuji idan muna cikin labari.

___________________


Tun sassafe suke tafiya har rana ta take,kafin suka isa garin Taraba,kasancewar basuda wanda suka sani,hakanne yasasu yanke shawarar kwana kafin gobe su haura mambila,wannan shawarar iyani ce,dan ta fisu sanin wajen.
A super market suka tsaya suka ci abinci,da kuma ɗan hutawa kafin su wuce hotel din da drivern yayi musu booking.
Hajiya zeenah ce takalli iyani wacce take cin abincinta hankali kwance,da alama dama ta saba da irin wannan tafiyar,ba kamar itaba wadda yawanci a jirgi takeyin tafiye tafiye,wannan ma dan tana so ya kasance sirrine shiyasa tayi ta a mota,amma babu laifi tanaji a jikinta kam sosai.
"Wai yanayin hanyoyin basu da dadi bi,gabaɗaya cikina ya hautsine,abicin ma na gagara cinsa da yawa"
"Uhm amma Hajiya inaga kici abinci sannan kuma ki huta sosai,da safema ki karya sosai,don abinda yake gaban mu babban aikine"
"Wane irin aiki kuma,duk wannan jololon drivern ne yaƙi gudu,da yanzu mun haura garin ai,ni na matsu na haɗu da yarinyar nan,naga ya take"
Hajiya zeenah tafaɗa tana yatsina fuska tareda zefah yankan wainar ƙwai a bakinta.
Itadai duk abinda take kallonta kawai take,kallon farko dan zakayiwa Hajiya zeenah kasan batasan wane irin abune yake gabansu ba,a zuwa cikar burinnata.
"Koda yayi gudu ma,bazai yiyu muyi kasadar haura mambila dare yayi mana a wajen ba,saboda hanyar tanada hatsari sosai,inshaaallah saidai gobe mu kama hanya da safe.
Daga haka Hajiya zeenah bata sake cewa komai ba,bayan kaman wasu mintuna ne wayarta tayi ƙara,tana dubawa taga sunan hajiya Ladi.
Kallon iyani tayi wanda itama tagani amma ta ɗauke kai,saboda abinda bai shafeka ba saika bishi da ido.
Da kaman bazata ɗauka ba,saikuma ta ɗauki ƙiran tareda ƙaƙalo murmushin dole tayafa a fuskarta,dan ita kanta tasan idan Hajiya ladi taji abinda yake faruwa,baƙaramin bacin rai zatayi ba,musamman daya zamo so take da tunda tsara komai idan ya danganci auren Jabeer ɗin.
"Hajiya ladi yakk ya kuma yaran?"
"Yara ƙalau,nace dan Allah batun business ɗina ne na dubai,ko zaki shirya ki rakani zuwa jibi,wlh wacce muke tafiya fa itane Yaronta ba lafiya"
"Ahah gaskiya nima bazan samu damar zuwa,dan yanxu haka ma bana gida na tafi ziyara gida,kuma zanyi a ƙallah sati kafin na dawo"
Ɗan jimm Hajiya ladi tayi,kafin kuma sukayi sallama ta ajiye wayar.
"Hmm bazan faɗamiki mai yake faruwa ba harsai na dawo,saboda karma kice baki yarda ba,abinda bazan iya jiba kenan,dan indan akan muradin tarwatsa lubna ne da ahalinta,banajin akwai mai yimin burki"
Duk maganar can ƙasa ƙasa takeyinsa,ita kanta iyani dake gabanta kaɗan kaɗan take jin abinda take faɗa.
Bayan sun isa masauƙinsu nan ma ba kwanciya sukayi ba,duk yanda iyani tayi da Hajiya zeenah ta huta ƙin amincewa tayi,dole saita bata labarin rayuwar garinnasu,wanda rabin tambayar duk akan Rayuwar Bombee ne,
Da safe ƙwanƙwasawar drivern ne ta tashesu,mai suna Iliyah,yaje kawo musu abi karyawa.
Nan ma bayan sunci sun shiryah kafin suka cigaba da tafi.
Kalle kalle suke ta windowa,ganin manya manyan duwatsu,ga kuma yanayin weather daya sanja nan take,yakoma liff liff har a jikin fata.
"Kai iyani amma garinku yana da kyau,wai dama haka yankin taraba yakene? Wanda bai zoba baiyi kallo ba"
"Kallo ma tukunna hajiya,nan bakiga komai ba"
"Koh ?"
"Uhm"
Suna cikin zancene aka ƙariso daidai inda hanya zata hau sama,tasha ce a wajen cike da mutane,drebobi kala kala,wasu suna saƙƙowa da motoci,wasu kuma suna hawa dasu.
Faka motarsu sukayi a gefe inda iyani tacewa Iliya ya tsayah,ita kuma tafita zuwa wajen direbobin.
Bata daɗeba sai gata tadawo wajen gefen hajiya zeenah.
"Hajiya munyi sa'a,munsamu drivern dazai haura damu,mungama ciniki dashi kuɗin zaki kawo a bashi.
Lokacin da Iyani ta faɗi kuɗin saida Hajiya zeenah ta zare ido tareda cewa.
"Ke wai wane irin driver kenan,inada driver ki hayomin wani yanzu nan kuma ki zugamin kuɗi,?"
"Hajiya wanann ai yayi kuɗin aikina na shekara,hauka ake?"
Iliya ya faɗa cikin ƙufula,ganin kuɗin da ake shirin bawa wani kawai ya haura dasu,bayan shi duk abinda yayi a shekara kenan.
"Haurawar banza,muja motar mu mana mu haura da kanmu,dole sai wani ya haura damu,shekara da shekaru muna tuƙi duk a haka zai tsayah"
"Toh koh daga haihuwarka kake tuƙi,babu ta inda zaka iyah haura hawan mambila batareda ka faɗa,abin ya wuce yanda kuke tunani.....,..Hajiya ki bashi kuɗin ya haura damu,idan ba haka ba wasu zasu hayeshi,saidai mu jira zuwa nan yamma kuma in wani ya saƙƙo"
Hajiya zeenah tanajin haka ta ciro kuɗin ta miƙawa iyani,bawai kuɗin ne batada shiba,kawai yanda ta bada kudinne a abunda bai cancanta ba take jin takaici.
Saidai kuma ya zatayi,iyani tariiga ta ga logonta,indai akan cikar burinta ne,ko ya ninka wannan ma zata bayar,yanzu ma jin zasu jira hardai yamma ne yasata miƙa mata kuɗin.
Shikuwa iliyah ganin dagaske kuɗin za'a bawa wani lokaci guda,yasashi jin takaici a ransa,har yafara yankewar cewa zai dawo wajen da aiki.
Bayan iyani ta tafi da bashi kuɗin,sai gashi sun dawo taredashi,kansa irin cibi cibi ɗinnan,baki baƙiƙƙirin,gashi irin mutanennan ne kaman iska zata huresu,cikin ƙaƙau kamar itace.
"Heee hajiya gaskiya fah kinyi sa'a mace kika turo akayi cinikin,bilahillazi da banni da tausayi akan mata koh ninkin wanann kuɗin bazan karba ba,dandai ina son kaiwa balance wajen ogah ne a yau,shiyasa ma na karba wallahi.
Yaya kun shirya ne mu haura,ko kuma zaku sake shiryawa"
Ya ƙarisa maganar yana cize baki"
Zaro ido Hajiya zeenah tayi tana kallon iyani,wacce bataji tsoro ba kaman itada drivern. Wai wannan ne zamu shiga cikin mota ɗaya dashi muyi tafiya?
Ganin sunyi shuru basuce komai bane yasashi buɗe gaban motar yana shirin zama akan iliyah.
Sauri yayi ya matsa,yayinda wani warin gardawa ya bugeshi,cikin ƙanƙanin lokaci ya kaure cikin motar.
Koƙarin toshe hanci Hajiya zeenah takeyi,saidai kuma tana tsoron su haɗa ido da sabon mutumin ta madubi,yagane danshi suke toshe hancin. Tunda ya takalleshi sau ɗaya wani mungun tsoronsa ya zartu cikin zuciyarta,batajin zatayi gigin tunzura zuciyarsa bare taga mazayyi.
A wajen iliyah ma hakan take,abinne yabashi mamaki ganin yanda yakusa zama akan cjnyarsa,amma ko kulada shi ma bayyi ba,hankalinsa yana kan motar daya shiga yanzu.
Abubuwan ta ya fara duddubawa yana wage baki,da alama yanayin motar yayi masa yanda yakeso.
"Heeeehuuuu kai kai,rabona dana tuƙa lafiyayyar motar zuwa gembu harna manta,kullum saita yan iskan direbobin hanyar nan,amma yau kam za'ayi ɗiba tafiyah bilahillazi,irin wannan mota haka mai girma?"
Ya faɗa bayan yagama kurma ihun,sanann kuma ya ƙara da dariyah irinta tantirannan.
To to bil'adama a ɗaura belt maza,zamu hau ga sansanin aljanu,yanzu zamu fara da sama ta ɗaya,har zuwa sama ta takwas,daganan kuma sai ayi gangara,wanda bayason yayi karoda abinda zai dunga farautar mafarkinsa,wato masu ƙananan kuruwa a cikinku su rufe ido,zamu fara aiki.
Duk maganar dayake kallonsa kawai suke,da duk cikinsu iya iyanice kawai tasan mai yake nufi,ita kuwa batasamu damar faɗa musu abinda yake nufi

Please Login or Register in order to submit comment