Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sashen Lubanan suka wuce cikwda raha da kuma shewa,tamakar tarkon su yakama Toron giwa.
"Wai dagaske kike luby,nifah har yanzu ban yarda ba irin wannanan asirin yana duniyah,kina daganan saiki kasheta hankalinki kwance?"
"Ƙawarai ma kuwa,ki zuba iso kawai kigani,lokacin dana taho bata haihu ba dan haka mu hanzarta"
"Idan ta haihu shikenan bazai aiki ba?”
"Ahah ba aikine bazai yi ba,kawai so nake na haɗa itada abin cikin na kashe,kingane dai koh,tunda kema ƴar garice ai"
Ba'a falo suka zauna ba,saboda tsaro sai suka shige ɗaki.
"Wai lubby har yanzu tsoron Kucakan gidannan kike yi,i think no need,tunda kece kike aikatawa,kuma ma hakan yafi,ta hakanne kaɗai zasu ƙarajin tsoronki su daina aura masa mata,habaa mutum baza a barshi ya wataya da mijinsa ba ya more"
"Hmmm barsu mana,nafisu iya shege ai,kome suke ina daidai dasu, ko nace ma nafisu"
Tana maganar ne tana fitowa da ƴar tsanar daga cikin jakarta,sannan ta ɗauko jinin Hafsa ma a cikin kwalba,zubawa tayi akan ƴar tsanar gefen bakinta yana motsawa tareda bada wani shu'umin murmushi ganin alamun samun nasara a aikinnata.
"Kinga Seerah inaga aikin yayi,saboda jinin ya tsotse a cikin dollyn,yanzu zan fara ƙiran sunanta sau uku sannan saina fara kakkaryah ta"
Tana rufe baki kuwa ta fara aiwatar abinda ta faɗa a aikace.
"Hafsa....hafsaaa.......hafsaaaaa,kwananki ya ƙare ganinan kema gareki!!!!!"
Ƙaƙasss tafara kakkaryah jikin ƴar tsanar,wanda duk sanda tayi hakan sai wata ƙara tafita daga jikin abin,amma hakan ko tsoro bai bata ba bare tausayi,saima wani ƙara ƙwarin gwiwa daya bata tareda nishaɗin matsalarta tana shirin kauwa daga gabanta.
Ta ɗauki kusan minti talatin tana aikin,domin idan ta karyah saita jira kafin tacigaba dayi,badan komai ba sai dan tasake bawa kanta lokacin hakan.
Saida ta gama kafin ta jefar da ƴar tsanar a ƙasa tana maida numfashi,hannunta da kuma jikin tsanar dukka jinin hafsa ya bata.
"Nagama da ita itama seerah,itama ta tafi kaman yanda ɗayar ta tafi,babu wanda zan ƙyale,hakan alƙawari na ne danayi"
Ajiyar zuciya ta saki tareda komawa ta zauna a kusada seerah,kaman wacce tayi aikin daidai.
"Huh ya kike gani seerah,kina ganin ta mutu kaman yanda nake buri"
"Indai har da gaske kin yadda da aikin zulumgum,kuma kin tabbatar kinyi yadda yace,ni ina ga babu wani abin damun kai a lamarin,kinyi yadda ya dace,to yanzu yaya? Zaki kira kiji ko ta mutune ko kuma shuru zakiyi kar ace kece kaman koyaushe"
"Hmm ko nace nice ko kar nace nice dukkansu kowa yasan nice na aikata,abinda yasa kika ga banbar gidannan ba,saboda bahaka nabar mijina ba,duk aikin yasoni tamkar uwargijiyarsa bayyi aikiba,amma namasa aikin da bazai taba sakina ba,har mutuwarsa,saidai idan nice naga damar tafiyar.
Sukuwa bazasu so mutuwar ɗansu dan nabar gidan ba,dan haka a zauna a haka,su cigaba da kawo ƴaƴansu cikin gonata ina murƙushesu kaman ƴaƴan kaji"
"Heee gaskiya bakida dama lubeee,shiyasa fah a Club ɗinmu ke ta dabance,to ni kinga barina tafi,Old lady tana ta ƙirana zanje na ɗora abinci,saikinjini ko sai na jiki"
Daga haka seerah ta ɗau jakarta tayi gaba.

•••••••BACK••••••••

"Innalillahi innalillahi innalillahi..........".
"To sai salati kike kamawa amma bakya ƙarisawa,nasan yanda kuka shaƙu da hafsa Madeena,amma addu'a zaki mata ita take buƙata a yanzu"
Abdulmaleek ne yafaɗa cikin tausayawa,dan kowa yasan Madeenah batada wata ƙawa bayan Hafsan,kasancewar tare suka tashi,kuma kansu ɗaya.
"Yah Abdul kana gani fah,kalli yanda take shan wahala,jikinta duk ya lanƙwashe,shikenan fah bazata tashi ba"
"Am sorry sis ki dunga yi mata addu'a kinji,ikon Allah sai kiga ta tashi da ƙafafunta,komai nufine na Allah"
Ɗaga kai tayi Alamar taji abinda yace,bayan suɗin babu wanda yake magana a wajen,sai Lylah abu kaɗan taja tsuka ta turo baki,ita a dole an sakata zaman wajen babu yanda zatayi.
Hajiya zeenah ce ta juya ta rafka mata harara,har zatayi magana ko mai ta tuna sai kuma tayi shuru tareda minding nata business din.
Ƙarar ƙofar dakin tiyatar ne ta ankarar da dukkansu,inda kowa ya juya yana kallon waye zai fito daga ɗakin.
Doctor Basheer ɗinne ya fito ɗauke da hankerchip a hannunsa yana share ruwan gaban goshinsa.
Kallon su yayi da alamar bayason faɗamusu abinda yake kan fatar bakinsa.
"Am sorry munyi iya ƙoƙarinmu amma.........."
Abdulmaleek ne ya katseshi tareda cewa.
"Uhm doctor duk wajennan nine namiji,shin ko zamu iyah yin magana dakai a office tukunna,kafin saina faɗamusu,bai kamata ka dunga faɗan magana a waje ba irin wannan ,musamman da iyah a wajen"
Kowa na'am yayi da maganar abdulmaleek din,inda doctor yashige office shima ya bishi.
Ya ɗau kusan miniti talatin kafin ya dawo inda su hajiya zeenah suke,duk da yanda yake ƙoƙarin saita Yanayin fuskarsa,amma kana gani kasan ba ƙaramar magana bace a bakinnasa.
"Am sorry to said,she's gone,Allah daya fimu sonta ya karbeta Iyah,please dan Allah karki saka damuwa a ranki sosai kinji,ki ɗauka cewar Hakan shine abinda yafi mata Alkhairi akan rayuwar da take ciki."
Ɗan ja da baya Sayyada tatin tayi ta zauna a akan kujerar da take bayanta,saida ta saita ta kwantar da hankalinnata da taimakon Abdulmaleek kafin ta ɗaga kai ta kalleshi.
"Toh...toh ina yaron naji ance yana da rai kafin ayi mata tiyatar koh?"
"Ahah iyah,an fitar dashi da rai,amma kuma yabi bayanta bayan mintuna da yazo duniyah,saboda shima abin ya shafeshi sosai,bai daɗe ba ya koma ga mahaliccinta"
"Naaaa shiga uku shikenan jinin zainabuna ya ƙare a duniya,wacce nake ganin zata maye min gurbinta itama ta bi bayanta,hadda ɗan dazan riƙe naji daɗi shima ya tafi,yanxu wannan tantiriyar mayya mai yasa zata min haka mai yasa zata lagarta min rayuwar iyali.......yanzu........"
"Dan yarasulullahi Iyah sayyada ki taimakemu kiyi shuru,Hafsa Addu'a take nema a halin yanxu,naƙira baban su Abdul da kuma Abba ƙarami,dukkan su suna hanyar zuwa inshaaallah"
Hajiya zeena ce tayi maganar tana share ƙwallar da take idonnata,ita ba komai ne yasake girgizata da mutuwar ba sai yanda taga ci taga rashi,burin wannan ɗa yazo duniyah amma sai gashi wata ta kasheshi tun kafin ta ganshi.
Wani tirurine da kuma bakin ciki tareda muradin ɗaukar fansar jikanta suka turnuƙe a cikin ƙirjinta.
Babu abinda take ambata sai sunan Lubnah a zuciyarta.
Suna cikin tsaye xugum zugum Alhaji Abdullahi ne yashigo shida Jabeer,wanda kana ganinsa kasan abun ba ƙaramin dukan ƙirjinsa yayi ba sosai.
Bai taba zaton zai rasa hafsan ba inaga kuma Ɗannasa dayake jinsa tamkar tsoka ɗaya a cikin miya.
Tunda yazo wajen bayyi magana ba,banda rawa babu abinda jikinsa yakeyi,duk yadda Mutanen wajen suka kai ga jin haushinsa saida ya basu tausayi,duk da shi mutum ne mai sanyin rai,amma kuma da wuyah mutum yaga Lagwonsa ya karye kamar haka.
Ɗakin da hafsan take ciki ya nufah jiki a salu'be.
A kwance take akan gadon tiyatar an rufeta da farin kyalle,gefe kuma jinjirinne shima an naɗeshi da farin kyallen.
Kallo ɗaya yayiwa inda jinjirin yake ya ɗauke kansa,dan baya fatan ma ya buɗe yaga menene a ciki,saboda yasan hoton bazai taba barin zuciyarsa da tunaninsa ba,ya dunga farautarsa kenan har ƙarshen rayuwarsa.
Hannunsa yasaka na dama yafara yaye farin kyallen dayake kan hafsan,duk da yanda hannun nasa yake rawa amma yana iya koƙarinsa wajen ganin yayi mata kallon karshe,macen da duk namiji zayyi mafarkin samu a rayuwarsa,hankali,tunani,tausayi,uwa uba sanyi rai da sanin yakamata.
Ko mutum bai taba zama da itaba yasameta yasan sai ya ratsa duniyah kan ya samo irinsu,to inaga shikuma da dama yana cikin duhun rashin sa'ar samun mata,kwatsam lokaci ɗaya hasken yazo masa yafara haska duniyarsa....kashh sai kuma gashi ya ɗauke ya barshi a duhunsa wanda yafi ma na baya,saboda a da bai ɗanɗana hasken yaji ba,yanzu kuwa daya ɗanɗana yaji saiya ke ji tamkar duniyah sun taru sun juya masa baya.
Jajayen fatar bakin sa da suke rawa saboda tashin hankali ya fara motsawa tareda son furta wata kalmar.
"Meyasa meyasa.........lokacin da ban shirya ba......"
Ƙwallah ce ta ɗigo daga idonsa zuwa kan goshin matacciyar da take gabansa a kwance.
"Ki jirani nima ina nan zuwa wajenki kinji,banga laifinki ba da kika tafi,domin babu komai a duniyar sai rashin daɗi,kece kika fara nunamin ba yanda na ɗauketa take ba,saidai kuma yanzu dakika tafi nasan babu wanda zai sake nuna min yanda kika nunamin......ALLAH YA JIƘANKI HAFSA"
Yana gama fadin hakan yasaki mayafin yamayar mata kaman yanda ya ganshi,daga nan yafice daga ɗakin yana share hawayen daya taru a idonnasa.
A zaune take tasaka riga rabin ciki,da wando matsatstse,head phone akan ta,da kuma cocumber akan idonta tana jijjiga kai.
Da alama yanayin yanayi mata daɗi sosai.
Bishira ce tashigo falon jikinta har rawa yake domin da isar da saƙon da take ɗauke dashi.
"Hajiya hajiyah hajiya...."
Saida tayi ƙira sunfi biyar kafin Lubnah ta cire cocumber dake kan idonta ta kalleta.
"Menene kuma yanxu kike buƙata kika zo kika durkusamin kaman mai neman gafara,mayu kawai."
"Uhm hajiya dama .....wani labari naji wai Hajiya hafsa ta rasu a asibiti dazu"
"Oh an faɗi ta mutun,yaya hadda ɗan cikin suka rasu ko ya?"
Abin yaɗan bawa bishira mamaki amma ta danne,dan dama ko karen gidan ma aka tambaya ai yasan itace ta kasheta,to amma wazayyi magana,duk yanda gidan suke ji da taƙama da kuɗi,amma bazasu iya shari'a da lubna ba,saboda baban ta shine Chief private lawyer da abuja take ji dashi,kuma lubna ita kaɗaice ƴar sa mace,zai iya komai dominta.
Musamman daya zamo basuda hujjah bayananniya cewar an ganta ta kasheta,shiyasa take kashesu da boka take cin karenta babu babbaka.
"Eh hajiya naji ance wai harda yaron duk suka mutu,ana tahowa da su gida ma ayimusu sutura a binnesu"
"Huh naji daɗin wannan labarin naki"
Ta faɗa tana murmushi,gefenta ta juyah ta ɗauko dubu biyar ta miƙawa bishiran,dan dama dansu ta kawo mata labarin,duk da zagin data sha bai dameta ba tunda an bata kuɗin.
"Nagode nagode hajiya,zakuwa kijini da wani labarin idan nasamo"
Daga haka taja dabaya ta fita daga falon jikinta har rawa yake don son kuɗi.



🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are




____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]






*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________








Page 🖤04🖤



Ƙarar jiniyar motar asibiti ce tafara amsa kuwwa a gidan,wanda hakan ne ya shaida alamar shigowa da gawar Hafsa tareda jaririn yaronta cikin gidan.
Bayan motar asibitin ta shigo sai kuma motocin su Jabeer suma suka biyo bayanta.
Kowanne idan kaga fuskarsa kasan mutuwar ta shigeshi,yanda suke fitowa daga motar jiki a sanyaye.
Sashenta aka nufa da ita domin yi mata sallah a ɗakinta,duk abinda ake Lubna bata fito ba,bare tazo wajen yin suturar.
Sai bayan an tafi da ita kafin tafito da jumbulelen hijabi a jikinta fari tana rarraba ido.
Babu abinda kakeji a wajen sai kukan Sayyada-tateen,wacce babu yanda ba'ayi da ita ba,amma taƙiyin shuru sam,kowa tausayinta ne ya kamashi,saboda babu wanda baisan shaƙuwar da sukayi ba da hafsan.
Bayan dawowa Daga binnetan aka cigaba da karbar gaisuwa,Saidai duk wanda yazo yiwa Jabeer gaisuwa sai a ce bayanan.
Abinne ya ɗaurewa abokinsa kai Khaleel,wanda hakan yasashi shigowa cikin gidan nemansa.
Da madeena suka haɗu a hanyar shiga sashensu zata kaiwa ƴan uwan Hajiya zeenah Abinci.
"Am Madeena ina kuwa JJ( Jabeer Jaan) banganshi ba,gashi ana ta zuwa yimasa gaisuwa a waje"
Alamar mamakine yaɗan hau kan fuskarta,dan itama batasan inda yake ba,sannan babu wanda yaga shigowarsa,sashensu ma mutanene a wajen sosai.
"Ahah Banganshi ba,bansan inda yayi ba,kuma ina kyautata zaton baya Sashensu ma,dan wajen akwai mutane sosai. Amma ka ƙirashi mana kaji inda yake"
"Tun ɗazu nake ƙiran wayarsa switch off,tabbas mutuwar Hafsa ta girgizashi,amma bai taba yin haka ba ya kashe waya dukka,kuma a irin wannan yanayin da mutane zasu nemeshi sosai"
Dukkan shuru sukayi kowa yana tunanin shin a ina zasu ganshi,can bayan shurun nasu madeena tace.
"Uhm barina tambayi ummah kota san inda yake "
Daga haka ta wuce tabar Khaleel a tsaye,yana jiran fitowarta.
Wasa wasa anyi sadakar uku amma babu Jabeer babu Alamarsa,kowa yayi ta mamakin ina yashiga,anyi zaton ma ko ya bar garin.
Sai washagarin kwana uku mutane sun fara raguwa sannan yashigo gidan da motarsa.
A hankali yafito daga motar yana jefa ƙafa kaman mai koyon tafiyah,idanuwansa sunyi luhu luhu sai lumshesu yake kaman wanda yayi maye,kallon mutanen da suka kewayeshi yayi,amma babu wanda yayi wa magana,har hajiya zeenah wacce ta kafeshi da ido,da alamar tambaya a kallonnata.
Hanyar sashensa yayi kansa a sunkuye,bai juyoba har ya shige ya turo ƙofar.
Bai cire takalman ƙafarsa kana bai fasa tafiya ba har ya shiga cikin ɗaki.
Kan luntsumammen gadonsa ya faɗa a haka yana jan gwauron numfashi,tareda fesar da iska mai zafi.
Runtse idanuwansa yayi na tsawon sakanni kafin yafara buɗesu yana sauƙesu akan farin POP ɗin ɗakin.
Hawayene sirara suke bin gefen idanuwansa suna zuba akan zanin gadon,bai damu daya share su ba,haka yabar su suka cigaba da zuba har na tsawon wani lokaci.
Wayarsa ya fitar daga cikin Aljihun wandonsa ya kunnata.
Kaman jira kuwa takeyi,tafara amayar da saƙon da aka zubo mata lokacin da take kashe.
Ƙuramusu ido yayi suna ta shigowa,saidai ko kaɗan bai nuna alamar ma zai buɗe ko ɗaya daga cikiba,shidai yana kallonsu kawai.
A jiyeta yayi a kan drawer gadon ya shiga banɗaki,har sannan wayar bata daina ƙarar shigar massage ba.
Ya daɗe a wankan kafin ya fito sanye da towel a ƙugunsa,ɗaya kuma akan sa yana tsane ruwan jikinsa.
Farine ba sosai ba,sannan yana ƙirar jiki,da alama ba haka aka bar jikin ba ana motsashi.
Yanada baƙin gashi sosai,amma daga ganin yanayinsa kasan bashida laushi a nature sa,ana amfani da manyan mayuka ne wajen bashi gyara na musamman.
Kallo ɗaya yayi kansa a madubin dage gabansa yayi saurin ɗauke kai.
Da alama bayason kallon ramar da take kwancene a kan fuskarsa,kana da kuma launin idanwansa wanda har yanzu basu dawo da haskensu ba.
Riga da wando yasaka marasa nauyi yafita daga ɗakin da sauri,jin alamun ana buga ƙofar falon da ya sakawa key shigowarsa.
Da Madeenah suka haɗa ido lokacin daya buɗe ƙofar itada Maleekah,ɗauke da kulolin abinci a hannunsu.
Ganin kallon tuhumar da sukewa idanuwansa ne yasashi saurin ɗauke ido tareda komawa cikin falon ya barsu a tsaye.
Suma basu damu daya ce musu su shigoba suka biyo bayansa,dan sunsan ko za'ayi shekara bazai faɗa ba ɗin ba.
A jiye kayan abincin sukayi a kan center table ɗin dake gabansu, Madeenah ce tayi ƙarfin halin faɗamasa saƙon da aka aikota dashi.
"Uhm ummah tace idan ka gama tana nemanka a sashen Abbah"
Bayyi magana ba duk da tasan yaji abinda tace,dan haka kowa ke fama da halinsa na rashin magana shida Maleekah.
Har takama handle ɗin ƙofar zata fita taji muryarsa ƙasa ƙasa,inda akwai surutu a wajen ba lallai taji mai yake faɗa ba.
"Lubna tana nan?"
Haushine ya turnuƙeta sosai,bayan kwana uku daya ɗauka bayanan,ana nemansa an damu dashi,amma yana dawowa bai tambayi kowa ba sai wata Lubna.
"Bansani ba"
Shine amsar da Madeenah ta bashi a daƙile,kafin tayi wuff tabar sashennasa,kar ya huce akanta.
Fitowa yayi daga sashen ya nufi hanyar na Lubna.
Ga hasashensa kuwa bata nan kaman yanda yayi zato,ina taje oho.
Tun halinta yana bashi mamaki yanzu abun har ya zame masa jiki,lokacin da ake wani abin daya girgiza kowa a gidan,ita sannan zata shirya tabar gidan,ko kunya ma da kuma bakin mutane bata ji.
Jawo ƙofar yayi ya nufi Apartment ɗin iyayennasa.
A zaune yake mahaifinnasa kaman kullum akan Wheelchair,shekararsa uku kenan akai tunda ya samu paralyse na Accident,a lokacinne Jabeer ya karbi kujerar CEO na Companyn.
Maganinsa Hajiya Zeenah ta balla ta miƙa masa,tareda kofin ruwa.
Sallama Jabeer yayi a hankali can ƙasa ƙasa yanda za'a jishi amma kuma bada sauti sosai ba.
Hajiya zeenah ce ta waigo ta kalleshi daga haka da maida kanta wajen mijinnata.
Gaisawa sukayi da mahaifinnasa kafin daga bisani ya tambayeshi jikinsa.
"Jiki Alhamdulillah Jabiru,Naji ummanka tace kwana uku baka gida sai yau ka dawo?"
"Eh Abba dama......dama...."
"Bakomai nasan yanda kakeji a ranka,rashin mata da kuma ɗa,musamman a yanayinka abune da yakamata ayi maka uzuri,sannan kuma a jajanta maka.
Allah yabaka ikon yin haƙuri da kuma tawakkali,sannan kuma ka dage da addu'a da miƙa lamarinka ga Allah,watarana zai wuce sai labari"
"Inshaaallah,nagode Abba"
"Tabbas ansan anyi maka mutuwa,amma bai kamata ka kashe wayarka sannan kuma tafi batareda ka sanar da inda kake ba,Abokan kasuwancinka jiya suka zo daga india yimaka gaisuwa,sai tafiya sukayi basu sameka ba........"
Shuru Jabeer yayi yana jinta,yanda take faɗan baya nan,badan ta damu dashi ba sai dan ta damu da yanda aka zo ba'a sameshi ba,shikansa wani lokacin yana zama yayi ta tunanin shin Hajiya zeenah ce ta haifeshi,saidai ga sauran ƴaƴan ma haka takeyi,wanda yake nuna zai fiddata kunyah yayi kuɗi shine a gaban goshinta,gaba ɗaya batasan nuna soyayya ga ɗanta tsakani da Allah ba,saidan wani abun duniyar.
Haka ta horar dasu tun suna yara,burinta su zamo sunfi kowa,indai har wani ya fisu to anan zasuga bacin ranta a fili.
Shiyasa takeji da Jabeer saboda yana matakin farko a compayn nasu,abu ɗaya ne yake cimata tuwo a ƙwaryah,shine mata marar arziƙi da Allah ya haɗashi da ita,saikuma rashin haihuwa da bai samuba.
Lokacin daya auri hafsa ta samu ciki,tafi kowa farinciki,itama zata samu jika a daina yimata habaici,saidai kash Yanda taso bai yiyuba. Wannan dalilinne yasa ta ƙunshe vaƙin cikin Lubna a cikin zuciyarta.
"Haba Zeenatu wai meyasa kike hakane,yaronnan fah Matarsa ce ta rasu da kuma ɗansa,kuma kinfi kowa sanin yanda waƴannan mutane suke a wajensa,dan yatafi yabar gida,daga dawowarsa ki fara wai abokan kasuwancinsa sunzo bayanan basuji daɗi ba?"
Jumburo baki tayi tareda hararar Jabeer ɗin ta ƙasa ƙasa,
"Haba Alhj yanzu kai baka ga maganata akan gaskiya,yanzu daya tafi da wani muhimmin aiki ya taso fah,yakake ganin za'ayi,kuma dazakace haka duk waye ya jawo komai idan bashi ba,da bai auro waccar masifarba aida komai bai faruba. Hmmm ai bari ayi sadakar Arba'in,takardarta zai bata ya auri ƴar mutunci wacce zata haihu,ba ita ba juya"
"In kina so ma kice yasaketa yanzu,ai duk ɗaya ne tunda kin faɗi Abinda ke bakinki,ki dunga sararawa zuciyarki dai,kina yayyafa mata ruwan sanyi,dan yanzu girma yafara kamaki,inba so kike ciwon zamani ya kama ki ba"
Shuru sukayi dukkan su babu wanda yasake cewa komai,kana ganin Hajiya zeenah kasan da maganganu a ranta fal,ganin idon mijinnata ne yasata yin shuru badan ta haƙura ba.
Shikuwa dama Jabeer duk maganar da suke a iya zuciyarsa yake saƙasu,ko ɗago da kansa bayyi ba.
Alhj Aliyu ne yakalleshi cikin tausayawa tareda cewa.
"Tashi ka tafi Jabeer Allah yayi maka albarka,sannan yakamata ka ɗau hutun Aikin kaje wani waje nesa da gidan kaɗan huta na wani lokaci"
"Toh Abbah"

Alhaj Abdullahi ne ya fito daga mota ransa a bace ya nufi bangarensu.
Sauri yake zubawa kaman zai tashi sama,dan dama irin mutanennnan ne masu firitt jiki da kuma sauri.
Bai samu kowa a falon ba, dan haka Ɗakin lylah ya nufah.
A zaune take tana bawa Haneef Abinci a baki,wuyansa sai gilu gilu yake da ƙyar yake karban abincin.
Tsayawa yayi bakin ƙofa batareda yayi ƙyakykyawan motsi ba yana kallonsu.
Tunani yatafi yanda rayuwar su take kasancewa shida matar tasa,shekararsu sha shida kenan da aure,babban ɗansu haneef mai shekara Sha biyar,Allah ya jarabceshi a Lalura,ko kansa baya iya tsayarwa bare yayi wa kansa wani abun.
Saurna yaransu kuma huɗu dukka matane,shikaɗaine dansu namiji saidai dashi gwara babu a wajensu.
Yanada shekara ɗaya a duniyah yakoma haka,har yau babu wanda yasan meyasa ya koma haka,anyi na gargajiya anyi na asibiti amma abu yaci tura.
Haneef ɗinne ya juyo yakalli mahaifinnasa dake bayansu,aikuwa ya wangale bakinsa yawu yana zuba,alamar yana masa dariya.
Itama lylah juyowa tayi ta kalleshi tareda cewa.
"Ahh yaushe ka shigo,amma lafiya na ganka da wuri haka ka dawo,ɗazu fah kake cemin yau sai dare ka dawo"
"Hmmm kedai bari laylah,ni narasa yanda zanyi da wannan yaron,nine nafara sanin companynnan kafin yasani,amma dan tsabar babu wanda yake ganina da daraja a gidannan,wai aka ɗau kujera mafi matsayi aka damƙa masa.
Project ɗin danacemiki zan jagoranci aikinsa,saida suka zo yau da suka ga Jabeer baya nan wai bazasu yadda na jagoranci aikin ba,tunda hutu yatafi kuma ya kusa dawowa to zasu jirashi ya dawo"
"Kutt to miye dalilin daya saka bazasu baka ba,ba kaine Defuty CEO ba,duk wani aiki dayake ai kai yakamata kayi in bayanan.
Hmmm dama na daɗe da faɗamaka ai cewar duk gidannan ƴan baƙincikine,babu wanda yadamu da rayuwarmu a cikinsu,in ina faɗamaka kana ganin banason yan uwanka,yanzu ai gashi ka gani da idonka"
"Nagani kam,duk wani aiki danayi a companynnan banida daraja a cikinsa,yau inna faɗi na mutu babu abinda iyalina zasu tsira dashi,dolene na ɗau mataki akai"
"Hmm hakane kam,yanzu inka yarda a ɗau mataki to kabar komai a hannuna,nikuma zan saita komai yanda ya kamata,buɗar idonka kawai zakayi ka tsinci kanka a matakin CEO na JAAN company"
"Na baki dama kiyi komai ma yanzu,nima yanzu bazan saurara ba,dole na ƙwaci haƙƙina a ciki"
Wata dariyah gefen baki laylah tayi tareda kanne ido guda ɗaya.
"Ka zuba ido kaga aikin laylah masoyina,bazan baka kunya ba"




🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are




____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]






*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________







Page 🖤05🖤



"Ke Madeena zoki rakani gidan Hajiya ladi,na daɗe banje ba,kullum cikin samun abin tashin hankali muke"
"Kai ummah Binciken semina fah nakeyi,maleeka ta rakaki mana"
Haɗe girar ƙasa da sama tayi,tasani sarai babu wani bincike da takeyi,dan tana jin ƙarar game ɗin candy crush a wayar tata,Kawai dai dan kar tajene su haɗu da Al'ameen a gidan,Babban ɗan Hajiya ladi wanda suke son haɗata dashi,shi yana so,amma madeena kam kwata kwata bayyi mata ba.
"Banason shashanci dallah sanjo kayanki kizo mu tafi,yara ana nuna muku abinda zai taimakeku kuna wani abun daban"
Cikin zumbura baki babu yanda zatayi ta sanjo kayan harda guntun hawayenta.
Tasan badan komai mahaifiyarta take son haɗata dashi ba,saidan yanada kuɗi,ita kuma wanda takeso bashida kuɗi,tunda ummannata taji zancen a wajen Maleekah tayiwa tufkar hanci,a cewarta ƴaƴan ta bazasu auri talakawa ba.
Tafiya suke a motar Madeenah tacika tayi fam,babu abinda ma yafi bata haushi kaman yanda yadunga yi mata izzah,dan yasan mamuƙata ake a wajensa,kawai dan yasameta mai sanyi bata mayar masa magana.
Basuyi tafiya mai nisaba suka iso gidan Hajiya Ladin,shima gidane tankatsetse naji da faɗa,kana ganin tsarin gidan kaga jiji da kan yaran gidan,kasan sunayi ne da dalili.
Wanda hakanne yasa su Madeenah jin haushin ƴaƴan aminiyar uwartasu.
Suna fitowa daga mota ,wata mata tayi musu iso zuwa ainihin falon hajiya ladin,ba wanda take tarbar mutane haka ba.
A zaune take a falon suna taɗi da ƴar ta guda ɗaya mace JAWAHEER,wanda bazata wuce sa'ar Madeenah ba,dan set ɗin su ɗaya ma,saidai ita Business Admin take karanta,irin na Jabeer.
Dukkan ahalin guda biyu babu wanda baisan yanda ake muradin haɗa jabeer da Jawaheer aure ba,saidai kash lubna tayi musu cikass,tazame musu kaɗangaren bakin tulu,har kawo yanxu babu abinda basuyi ba,amma su kansu sun tabbatar Asirin lubna yafi nasu ƙarfi,babban tsoron su kar Jabeer ya aureta a yanxu itama ta kasheta.
Sakalci take zubawa son ranta,ita kuma hajiya Ladi tana shafa mata kai,wanda yake kan cinyarta,duk da shigowar su hajiya Zeenah ma hakan bai sa ta ɗago ta kallesu ba,saima ƙarawa abinda take ƙaimi.
Hajiya ladi ce ta kalli Jawaheer tareda cewa.
"Kai mana Baby waike ko kunya bakyaji yin fitina a gaban mutane,kuma hadda maman yayannaki koh,ki tashi ki gaishesu mana,sannan ki kawo musu ruwa"
"Toh amma ruwa kam su jenifer suna nan su kawo musu mana koh momy,kinji fa nace miki jiya jikina tsami yayi dana tashi a bacci"
Ƴar dariyah hajiya zeenah tayi,tareda cewa.
"Ohhh lallai Jawaheer ɗin mama,har yanzu dai kece da cinya koh,saiki sha magani ai ki huta"
Sakin baki Madeenah tayi tana jin abinda ummanta ta faɗa,tsamin jikine zai hana mutum kawowa baƙi ruwa,kuma ji abinda suke faɗa.....anya kuwa ba asiri hajiya Ladi tayiwa uwartasu ba,inba haka ba wannan ai ya wuce ɗaukar tunani.
Harara Madeenah ta gallawa Jawaheer,wanda itama ta rama a take,kaman ba itace take sakalcin ƴan shekara biyu ba,gaisuwar da akace tayin ma batayi ba ta tashi ta tafi. Half vest ce a jikinta sai bom short,su a dole suna kwaikwayon turawa,ko mahaukaci yagani yasan abin bayyi tsari ba,amma Hajiya zeenah idonta ya rufe akan mutunin nata (kuɗi) kwata kwata bata ga hakan ba.
Har taje bakin ƙofar fita daga falon ta juyo ta kalli Madeenah.
"Ahh Madeenah zamuje ciki mana na rakaki sashen Yah Ameen"
Kallon ta Madeenah tayi babu yanda ta iya tabi bayanta,saboda kallon da Hajiya zeenah tabita shi,na gargaɗin karta musa.
Itakuwa tasani sarai ba abin arziƙi bane yasaka Jawaheer ƙiranta,dan tafi kowa sanin wacece Jawaheer ɗin.
Kaman kuwa dama jira suke,Madeenah tabin bayan Jawaheer hajiya zeenah ta matso gefen Hajiya Ladi.
Labarin abinda ya faru tafara zayyane mata na mutuwar hafsa,kasancewar basu samu tattauna hakan ba ana abin mutuwar.
Wani murmushin ciki ciki hajiya ladi tayi,koba komai taji daɗin hakan,duk da taso lubna ce ta mutu,in suka tashi hafsa bazata yimusu wahalar kawar

Please Login or Register in order to submit comment