Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana kallon wani dutse dayake gabanta,wanda yayi kore sharr dashi. Idonta a rufe tajiyo muryar HILYAAAN daga cikin mota tanayi mata magana da hausarta da bata gama iyawa ba.
"Anty Maryam (Bombee),shin zan sanarda su Zeezah da Khamees shigowarki ne?"
"Ahah kyalesu ba fadata zan tafiba tukunna,zanje gidane,sai an koroni saina tafi nawa gidan da dalili"
"Kaman ya ban gane ba,sai an koroki kuma,ai gidanku a cikin garinnan da waccer shekarar mukaje?"
"Eh shifah can zan tafi in sun koremu saimu shige can ɗin,karki faɗamusu zuwana,duk da nasan inashiga garin zasusan isowata,inasone naje naga wanne aiki sukayimin a wajen,sannan wannene kuma a cikin dajin ya tsallake umarnina,uhhhhh kinsan inason naga mutum yayimin kuskure,na matsu naje naga wannne irin gini sukayimin.
Saidai nafison naje naga ya fuskar tsofin can zatayi idan suka ga mai zan kai musu hhhhhh"
"Toh shikenan,ya labarin wannan matar kuma dakikace zakiyi maganinta,koba yanzu bane lokacin?"
"Ba yanzu bane lokacin,sai nan da zuwa wani lokaci kaɗan...........ina baby boy ɗina yayi bacci yanzu ko har yanzu bai koma baccin ba?"
Juyawa Hilyaan tayi bayan motar inda kyakykyawan jaririn yake kwance yana zuba baccinsa hankali kwance.
"Yayi bacci,saidai kinsan jikinsa yayiwa wajennan kaɗan,satinsa fah biyu,kema kuma bakisha maganinki bah na 4:00 pm."
"Mtsww nagaji da wannan maganin wlh,jiri yake sakani sannan kuma yana ƙaramin yawan jin yunwa"
"Uh ai dole kisha tunda wannan kika zaba,babu yanda dr Na'im bayyi ba wajen karkiyi zirga zirga amma kinƙi ji"
Dawowa motar Bombee tayi tashiga,kafin Hilyaan ta tuƙa motar zuwa cikin garin.
Tun a nesa da bakin kofar gidan Hilyaan ta ajiye motar,tareda ɗakkowa jinjirin a showel dinsa tabiyo Bombee a baya,wacce har ta fara tafiyah zuwa cikin gidannansu.
Wani yarone yasha gabanta tareda cewa.
"Lahhh Bombee soja ta dawo ta dawo"
Cakk Bombee ta tsayah jin abinda yaron yafaɗa,hannunsa ta riko tareda juyashi kansa yana kallon ƙasa,yaran wajen ta kalla tareda cewa.
"Wani ya ƙiramin uban yaronnna lo uwarsa yanzu nna"
Da gudu kuwa labari ya iske larai saigata ta fito,dan jikanta ne ɗan ƴar ta wanda yake wajenta.
"Ke wane shegene zai kashemin jikan........"
Kirifff taja bakinta ganin Bombee ta ɗaga yaro yana wutsil wutsilll.
"Ohh ashe kece kika dawo,dan Allah meya miki haka yaro dashi"
"Tambaya ma kike mai yayimin,amma a sanina kinsan halina,bana tsallakewa daga ƙarami har babba koh. Ƙirana yayi da wancan sunan,wanda yanzu na tsaneshi fiyeda mutuwata........misali zanyi akan sa kowa yagani,idan na kuskura naji wani yakirani da wancan sunan uwarsa ta haifi wani a garinnna kowaye shi kuwa"
Taugunnawa larai tayi tana roqon Bombee,amma haka tayi mursisi tasaki yaron yafaɗo takayi,larai dama tana ganin idon Bombee ta saita faɗowar sa,dan haka da sauri tayi kifiyah ta cafeshi a hannunta,jikinta har rawa yake saboda tsoron Bombee da kuma tashin hankalin data gani.
Dauke kai tayi tashiga gidannansu,wanda kafin sannan har labarin isowarta cikin garin da abinda tayi ya zagaya a bakin magulmata,kuma daman takeso.
Yanzu zuciyarta tayi baƙi ta dafe,batajin ƙwarin gwiwa sai mutane suna yaɗa abinda ta aikata,tun gulma tanayi mata tabo har tazamo maganinta nasha a yanzu.
Ko sallama batayi ba tasaka kai cikin gidan,bata samu kowa ba dan haka ta wuce ƙofar ɗakin innarta.
A zaune take akan kujerarta ta zubawa gabas ido.
Bombee ta daɗe a bakin ƙofar ɗakinnata tana kallonta batareda tace komai ba.
Muryar inna laari ta jiyo tafito daga ɗakin girki,da alama abinci dare takeyi,dan laasar tayi sosai.
"Wanake gani a ciki gidannan yau mun shiga uku"
"Ba tara ba iya uku kika shiga laari,niɗince dai ganinan da raina ina shaƙar iska"
Tafaɗa tana jan iskar da ƙarfi,tareda yin wani dan banzan murmushi.
"To komai kikazo dashi ma munfi ƙarfinki,ta allah bataki ba,tun wurima kizo ki fice daga gidannan"
"Saboda gidan ubanki nake ciki,saiki bari mai gidan yazo ya koreni da kansa,hhhh kika ce wai kin fi ƙarfin abinda nazo dashi,wannan kuma zancene,abinda na zo dashi baki tabayi ba laari,saboda nafiki iya shege ta wata sigar,duk da nasan ta wani gun kinfi gaban kwatance,saboda keɗin kurace da fatar akuya kike zaune a garke"
Zaro ido inna laari tayi baki sake tana kallon Bombee,anya kuwa bata shaye shaye take gaya mata wannan maganganun.
"Bombee kekuwa ɗiyar arziƙice,karki manta fah innarki tana jinki kike wannan maganganun"
"Saime dan tanaji,tunda bazata iya hanani ba kuma bazata ganni ba ina amfani jin toh,keda kike ji dake nake"
Yaron dayake hannun Hilyaan ne yafara kuka da alama ya tashi.
"Ohh laari bani kujera zan zauna na shayar da jaririna mana"
Bata ɗauki maganar Bombee da wasa ba dan haka ta gara mata kujerar cikin gatse dan a tunaninta Bombee duk iya shegenta ne.
Ga mamakin ta kuwa ta zauna a tsakar gidan babu ko kunyah a ƙarkashin inuwar bishiyar gidan tafara bashi mama,bayan ta ɗan ɗage gyalen dayake wuyanta.
Zaro ido inna laari tayi tareda cewa.
"Yau ni laari mai zangani,ƴar nan ɗan me nake gani haka"
"Ɗana ne mana,mata mazace ni danna haihu kike mamaki,shikenan mutum bazai iya haihuwa ba,ko ke kaɗai ce mace kai. Zaki wani tambayi tayaya,ta yanda mlm Ahmadu yayi miki cikin Innayi mana,nima ta haka nayi cikin nawa ɗan tareda wani daga cikin mazajena"
Mari inna laari takaiwa Bombee cikin zafin nama,jin abinda Bombee take fadamata,wanda ko kare bazai ciba.
Saurin riƙe hannunnata Bombee tayi tareda wullata can gefe tafaɗa cikin kwatar dake wajen wanke wanke.
Tashi tayi daƙyar saboda yanda kwankwasonta yabugu,daidai lokacin tana ɗagowa ta hangi mlm Ahmadu wanda yake tsaye yana kallon su.
Kuka inna laari tasaka tareda fitowa daga wajen.
Hanyar ɗakinta tayi tareda cewa.
"Mlm barin na tattara kayana natafi garinmu nikam,kishiya bata fiddani ba,amma wannan ƴa kam bazan iya da ita ba dam annoba ce"
"Ina zaki laari,duk naji munanan kalaman data faɗa,basai an maimaitamin ba,miye na tafiya tunda bada ita na gina gidan ba ai yanzu zata barshi basai anjimaba.
Kizo ki fitamin a gida na sallamaki,sannan abinda kika zo nunamin naganshi na kuma gode,bana son duk abinda zai tunamin ke daga yau"
Wani murmushi Bombee tayi mai dauke da ma'anoni kala kala.
"Har zan wuce gidana na tuna cewar karka bar gida har sai an koreka,shiyasa nazo a koreni na tafi fa dalili,amma kafin sanann bari ɗana ya ƙoshi tukunna.
Kayi haƙuri baba da naso yimaka mai suna,sai kuma nasaka masa sunan.......kodayake shikenan dai"
Tafaɗa tana jan numfashi,a yanda take magana kaman ba ita ubannata yafaɗawa kalmomi masu girgiza duk wani ɗa ba,musamman ƴa mace.
Miƙewa tayi tareda miƙawa Hilyaan ɗanta Haidar,wanda take ƙira da young Haidar.
"Toh baba ni zan wuce saina shigo garin sainaxo mu gaisa,Laari karki manta fah wasa tsakanina dake bai soma ba tukunna.....sai wani jiƙon"
Duk maganar datake mlm Ahmadu bai cemata kanzill ba dan takaici,mai zaice mata da wannan maganar,shi bai taba ganin wannan iftila'i ba a rayuwarsa,idan wani yace masa Bombee zata zama haka zai iya buga ƙasa yace bai yarda ba.
Daga haka tafita daga cikin gidan cikin izza da ƙasaita.





_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼



____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤32🖤




Hamma Hajiya zeenah tayi tareda kallon muruje wanda yakai karshen labarin dayake basun.
Kuɗi ta ciro daga cikin purse ɗinta ta miƙamasa tareda yimasa godiyah.
"Mun gode da wannan labarin daka bamu,koba komai yanzu munsan mai yake wakana,mu bari mutafi gida,yamma tayi bazamu hau cikin jejin yanzu ba"
Zaro ido muruje yayi tareda cewa.
"Hajiyah wai har yanzu baki haƙura da zuwa wajenta ba,bazan tambayi mai kike nema ba a wajenta,nagode ni bari na tafi"
Fita muruje yayi daga cikin motar yakama gabansa,yabar su Hajiya zeenah cikin nazari.
Iliyah ne yakalli Hajiya zeenah tareda cewa.
"Hajiya gaskiyar wannan ɗan yaron fah,kinaga bazamu hakura dazuwa wajenta ba kuwa,ni aradu bana fatan ma nahaɗa hanya da ita tunda naji labarinta,batayi kama da wacce wani zai haɗa hanya da itah,kinaji fah ko iyayenta ma ba a bakin komai duke ba a wajenta"
"Kai rufemin baki,dama kaine kasakani zuwa wajennan komai,rashin mutuncinta danaji dama shiyasaka nazo nemanta,dan naji labarin hakan bashine zaisa na janye daga kuɗirina ba,saidai idan itace da kanta taƙi amincewa da buƙatata"
Daga haka iliyah bai sake cewa komai ba yaja motar suka bar anguwar su Bombee zuwa gidan su Iyani.
A hanyar sune ta dawowa Hajiya zeenah ta kira Jabeer.
Yana zaune sun gama hayaniya da lubna idonsa a rufe ya jiyo ƙarar wayar.
Da kaman bazai duba ba saikuma yaga an rubuta "Mommah"
Sallama yayi,tun kafin ta amsa sallamar tafara faɗamasa dalilin ƙiran.
"Jabeer shin private plane yana nan kuwa?"
"Ehh yana nan hajiya,ban fita ko ina na ina nigeria"
"Toh karka fita dashi nan da sati,dan zan kiraka a cikin satinnan azo a ɗaukeni a Gembu"
"Gembu kuma,dama can kikaje,wajen wa kenan?"
"Uhmm naje yin wani abune wanda zai taimaki rayuwarka,Aure zan yimaka wanda sandiyyarsa zaka rabu da wannan jarababbiyar matar taka,sannan idan nadawo ma zamuyi magana.
Zaka koma ainihin Side dinka na gidan,zaka barwa su Abdulmaleek wajensu"
"Amma Hajiya naga basu tashi aure ba,sannan kuma wancan side din ya fiye girma dayawa sannan yayi ciki kaɗan,sannan........."
"Sannan me Jabeer bazanyi abinda zai cutar da rayuwarka ba,yarinyar nan baka buƙatar sakata cikin rayuwarka,zatazo ne domin kawar da lubna a rayuwarka.
Bangama tsaida abun ba tukunna,zai iya yiyuwa a fasa,yansu dai jirgin nafi buƙata a ready idan zan dawo,dan bazan sake bin wannan hanyar ba karna mutu.
Komai yafaru zan ƙiraka ko abbanka gobe"
Tana gama faɗin hakan ta kashe wayar.
Ɗan murmushi yayi yana kallon sunanta a gaban wayar tasa,yayinda cikin ransa kuma yacika da matuƙar kaɗuwar jin abinda mahaifiyar tasa take shirin yi.
"Hmmm dama kina tsoron mutuwane Ummah....kai Allah ya kyauta.
Daga nan side ɗinsu yawuce wajen abbansa,saboda ƙarajin labarin a wajen,dan yasan bazai rasa sanin mai yake wakana ba.

______*****______

Biron dayake hannunsa ya ajiye,ganin yayi kusan minti talatin amma yagagara yin signing ɗin da bazai daukeshi sakanni ba,saboda yawan tunani dayake fama dashi a kodayaushe.
Ƙarar bugun kofar da akayi ne yasashi jefar da biron akan paper tareda jan ɗan ƙaramin tsaki.
"Banda kaima kasake ɗoramin wani tension din,a tunanina dai baka buƙatar saina cemaka ka shigo koh?"
Cikin kasala yayi maganar kamar shima buɗe bakin aikine a gareshi.
Khaleel ne ya buɗe ƙofar ya shigo yana murmushi,akan kujerar datake kallon table ɗin Jabeer ya zauna.
"Mai ya farune mutumina,yanzu kullum haka ake ganinka,yakamata fah kaga likita idan wani abune yake damunka,An tafi wata uku da mutuwar Hafsa amma kaƙi barin lamarin a cikin ranka"
Ya mutsa sumar kansa yayi tareda fesar ɗa iska,dan jijjiga kai yayi alamar shima kannasa ciwo yake yi masa.
"Hmmm Khaleel ba iya wannan ne matsalata ba,inaga Hajiya so take takasheni tun kwanana bai ƙara ba,nifah inaga bata kallona mutum,tafi tunanin ni robot ne"
Ƴar dariyah Khaleel yayi jin furucin abokinnasa,wanda bazai ga laifinsa ba akan maganar kam,dan ko mahaukaci ya kalli Jabeer yasan yana cikin yanayi na buƙatar hutu ba kaɗan ba,sannam kuma yanada buƙatar wanda zai kwantar masa da hankali.
"Menene yafaru kake wannan furucin Jabeer,komai zai faru kasan Hajiya mahaifiyar kace,sannan kuma kasan bata nufin ka mutu ta kowacce siga"
"Hmm baxaka gane bane,kasan yanzu zancen danake maka kwananta uku kenan bata gida,wai tatafi yimin aure a can gembu,ka duba yanayin danake ciki ban gama warwarewa da mutuwar matata ba,ga ita wancar har yanzu nagagara jin daɗinta dama,yanzu kuma ta tafi can uwa duniyah zata auromin wata,wadda ni bansan ma ita mai zan tarar a gareta ba.
Kuma wani abin tashin hankali ma Khaleel,auro waccar ɗin fah dan na auri Jawaheer ne fah?"
Zaro ido Khaleel yayi jin abinda Jabeer yafaɗamasa.
"Jawaheer kuma,ehh nasan yarinyar tana sonka kam,amma banyi zaton dagaske abin yake ba"
Ƴar dariyar takaici yayi kafin yaƙara da cewar.
"Khaleel kenan,to tunda aka haifi Jawaheer Hajiya rabi tabani ita,rashin aurenta da banyi ba saboda suna tsoron kar lubna tayi mata illah ne,yanzu kuma idan suka auramin wata anan zasu samu hanyar yanda zasu saka Jawaheer a gidana"
"Tohh gaskiya abinkan ba ƙarami bane,toh amma kai taya kasan hakan dukka"
"Jiya ta ƙirani take faɗamin wai na shirya jirgi za'aje dakko ta a gembu.
Abin yabani mamaki,akan mai takeyi a gembu,nan take faɗamin wai aure taje yimin,kaji fah irin wannan zancen Khaleel,dan ta sameni mai yimata biyayya akan buƙatarta,bai kamata kuma ta dunga yin biriss da abinda zuciyata keso ba"
"Eh to hakane,amma kuma kacigaba da haƙuri,inshaaallah biyayyar dakake mata ma bazai bari ka dawwama a cikin wannan halin ba,inshaaallah allah zai kawo maka mafita"
"Ba wannan ba ma Khaleel,karka manta bafah iya anan abin zai kareba idan ta kawo wannan. Duk neman mafita ne na yanda Jawaheer zata zauna a gidana,nakasa cire tunaninnan a raina tun daren jiyah"
"To a ina duk kaji wannan ne,zai iya yiyuwa ita Hajiya kawai Lubnah ce bataso a cikin rayuwarka,ka rabu da itamana kawai,ni inaga Jawaheer ɗin ma tafi maka lubanan"
"Inda zan iyah sakin Lubnah da tuni na rabata da rayuwata kodan saboda sabanin danake samu da dangina akanta,amma abin ya ci tura duk iya koƙarin danayi. Hmmm Jawaheer din ma dakake gani ba kanwar lasa bace wajen rashin daɗin zama,tsawon rayuwarta ba'a cemata tayi tayi,taya kake gani zan sakata abu tayi,ko kuma zatayi wani abun amatsayinta na matar gida. Sai uwa uba ita wacce ake shirin mannamin banma santa ba kwata kwata"
"Uhmm kaman kace Hajiya tafaɗamaka zaka koma Ainihin side ɗinka,meyasa kenan"
"Baka san meyasa ba,saboda yana babbane yana ɗauke da Side guda huɗu,tana shirin yimin tanadin zama da mata uku,shiyasa ta buƙaci nakoma can"
"Mashaallah nabaka wata shawara mana?"
"Hmmm wacce shawara ce zatayi maganin wannan abin dayake shirin tunkaroni a yanzu"
"Mezai hana tunda kace side ɗin na ɗauke da bangare huɗu,kuma mata uku take son saka zama dasu. Kaikuma saika auro kamilar yarinyar mai addini da nutsuwa wacce tasamu tarbiyya ka aura,kaga idan sun kunna maka wuta zaka samu wajen zuwa a kwantar maka da hankali"
"Hhhhhhh amma Khaleel yau na yarda kai mungune,ina koƙarin janye jikina daga wanann matan kaikuma kana shirin ƙaromin wani bala'in,kajanye wannan shawarar tun batayi nisa bama"
"Nizan tafi Jabeer Allah yakawo maka sauki akan lamarin nan,amma dai kayi tunani akan abinda na faɗamaka,inaga idan kasamu wata yarinya a rayuwarka kaman hafsa abin zaizo da sauƙi,koda wancan din suna nan"
"Hmmm naji abinda kace,yi sauri ka fita ka bani wajen Khaleel,nakula bazaka gane yanakeji ba"
Jijjiga kai Khaleel yayi ya fita a office din,cikeda tausayin abokinnasa wanda yagamu da Jarabawar mata a rayuwarsa.
"Nakaro aure bayan waɗannan..........kai wannan ba shawara bace ma,gwanda nacireta cikin raina kawai"
Daga haka shima ya tattara shirginsa ya bar companyn ma gabaɗaya,bai koma gidaba wata hanyar yakama zuwa wani wajen daban,wanda yake ɗaya daga cikin sirrinsa da yabarshi a iya saninsa kaɗai sai mahaliccinsa.

_____*****______****_____


A bangaren su hajiyah zeenah bayan sun karya suka fito daga cikin gidan su iyani.
Ƙaryah sukayiwa mahaifiyar iyani,dan idan tagane Daji zasu shiga inda gidan Bombee yake,koda wasa bazata barsu su shigaba.
Key iliyah yayi wa motar,amma kuma baisan ina zai dosaba daga haka.
"Hajiya ina zamu nufah daga nan"
"Meyasa kake tambaya ta,nima nasani,nansan kuma da wuyah a samu wanda zai rakamu wajen cikin garinnan"
"Ahh Hajiya ranar da muka shigo Toro yabamu number sa akan ko zamu koma zai maidamu"
"Mezamuyi da wannan yaron kuma yanzu,ko karen hauka ne yacijeni ai bazan yarda nasake gangarawa ta wanann hanyar ba"
"Ahah ba zancen komawar ba,gani nayi kaman fah yana daya daga cikim yaran Bombee,kin manta mai gace mana,cewar a jeji gidanta yake,kuma itace shugabar kungiyar su ta BB. Kaman yayi kama da labarin kungiyarta da Muruje ya bamu jiya"
"Ehh kuma fah hakane,iyani tayi gaskiya Hajiya"
"To danna ki ƙiraman shi,yafaɗamana inda take"
Fita iyani tayi daga motar tashiga gida dakko inda tarubuta number tasa.
Sakawa tayi tareda miƙawa iliya ya ƙirashi.
"Salam ina magana da toro ne?" mune mutanen da ka shigo dasu rannan,dan Allah muna tambaya ne akan inda shugabar ku take,muna son zuwane"
Bayan ɗan wani lokaci iliyah ya sauke wayar a kunnesa yana kallon hajiyar.
"Mai yace bazai faɗamana ba?""
"Ahah yace wai gashinna zuwa yana kusa danan wajen,amma fah da alama yanace wani abu zamuyi mata,bakya ganin bazaiyi shunen mu ba a wajenta"
"Haba dai wane irin shune kuma,tun kafin Hajiya zeenah tayi magana taji bakin bindiga yana zungurar ƙeyarta ta window mota........

Tohhh fahh🤣🤣🤣🤣




_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼



____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤33🖤











Muryar wani mutum taji daga bayanta yana cewa.
"Ku shiga ciki ku ɗauresu,sannan ku zubaminsu a bayan mota,karku manta da ɗauremusu fuskokinsu"
"Okay toh"
Mutane guda biyune suka shigo motar tareda ɗaure musu hannayensu da igiyoyi,bakin kyalle aka saka a fuskokinsu,daga aka tasa ƙeyarsu zuwa cikin wata motar.
"Maza kai toro jawo motar tasu ku tafi,zamu miƙasune ga itah,sai sun faɗi dalilin dayasa suke nemanta,sannan kuma wanene ya aikosu"
Daga haka su Hajiya zeenah basu sakejin komai ba sai gungurawar motah.
Tafiyah akayi mai nisa dasu zuwa wani waje daban wanda basu samu damar sanin inane ba,sauƙa akayi daga motar aka fara zansu zuwa wata hanyar. Nan ma saida akayi tafiyah mai nisa kafin aka basu damar tsayawa.
Jikin su Hajiya zeenah banda rawa babu abinda yake,dan sun saddaƙar gidan yankan kai aka kawosu.
"Yau nashiga uku nakawo kaina kabarina da kaina"
Hajiya zeenah tadaɗa a hankali,muryah murdaɗɗen mutum taji yana cewa.
"Mun iso ku ciremusu ƙyallen fuskarsu"
Kafin ya rufe baki sukaji an fizge yadin dayake fuskarsu,kamar za'a rana kansu da gangar jikinsu.
A hankali suke saita hasken wajen da kuma ƙarfin idonsu,babu wani haske a wajen,saidai saboda yawan ƙofofi da wajen yakeda shi,kai tsaye mutum sai ƙarewa abinda yake wajen kallo.
Wani irin ɗakine mai girman gaske,babu abinda yake jikin bangon ɗakin sai hotunan mutane kala kala anayi musu azaba salo salo.
Wasu irin winduna ne a cikin ɗakin ƙanana kuma a can saman silin ɗin ɗakin.
Ga mutane masu baƙaƙen kaya guda kaman goma a gabansu sunyi cirko cirko.
Kallon ɗaya mutum zaiyiwa ɗakim hantar cikinsa ta kaɗa,dan kana samunka cikin ɗakin karon farko zakayi tunanin ba a duniyah kakeba.
Wani na daga cikin mutanen ya matso gabansu ɗauke da zarto a hannunsa babba.
Cikin kakkausar muryah yafara magana mai amsa amo.
"Shin bazaku faɗamin maiyasa kuke neman shugaba ba,ku faɗamin wanene ya aikoku yanzu nan,kafin na gundule kan tsohuwa"
Kunna abin hannunsa yayi yafara ƙara,wanda kowanne ƙara ke sake gusar da ɗan nutsuwar zuciyar dake jikin su Hajiya zeenah.
Cikin karfin hali da tattaro dukkan jarumtarta tayi magana,wanda take ganin ita kaɗaice zata ceceta a halin da take ciki.
"Bada niyyar cutarwa muke neman Bombee ba,saboda wani taimako dazatayiminne. Sannna babu wanda aikoni,buƙatata ce ta kawoni wajenta"
Tsayawa yayi cakk jin abinda Hajiya zeenah tafaɗamasa,
"Shin kozaki faɗamana dalilinnaki?"
"Zaifi kyau idan iya nida ita mukayi maganar,abin bai shafi wani abin cutarwa ba,inzaka iya ka haɗani da ita akan maganar"
Suna cikin hakanne wata farar matashiya tashigo wajen,
"Khamees ka tsayah da wannan abin,Anty maryam ta buƙaci ganinsu a sashenta yanzunnan"
"Meee daga zuwansu har zata gana dasu....."
"Haka tace na sanar dakai"
Sauƙe makamin hannunsa yayi yana kallon su Hajiya zeenah ƙasa ƙasa,juyawa yayi yabar wajen sauran ma suka bishi a baya.
Sauƙe ajiyar zuciya Matashiyar tayi tareda kallon su Hajiya zeenah tasake tattausan murmushi.
"Hmmm karku damu yanada saurin fushine,kuyi haƙuri da abinda yafaru....sunana Hilyaan,ko zaku iya biyoni zuwa wajenta"
Lokaci ɗayah Hajiya zeenah taji hankalin ta ya kwnata,saboda abinda yarinyar tafaɗamata.
Cikin sanyin jiki suka fara bin bayanta zuwa barin wajen,har sannann hankalin su bai kwanta ba.
Bayan sun fita daga ɗakin wata hanya sukabi wacce tayi hanyar wani ɗan ƙaramin gida a can gefen inda suka fitan.
Suna tunkararsa ƙyansa da kuma ƙawatuwarsa yana ƙara fitowa fili,babu wanda zai ce akwai irin wannan gidan a jejin inba gani yayi da idonsa ba.
Dan haka yakasance tamkar an ɗakkoshi an ɗorashi a wajen.
Suna shiga cikin wajen wani ƙyatacce ƙamshi yayimusu sallama a cikin wani mayalwaci falo.
Nuna musu wajen zama tayi kafi tayi wata hanyar da wani corridor yabi.
Bata dade ta tafiya ba wata mata mai dan shekaru ta shigo falon dauke da tiren kayan marmari a hannunta.
Ajiyemusu tayi cikin sakin fuska kafin tabar wajen.
Haɗiyar yawu iliyah yayi ganin yanda kayan marmarin suka nuna lutsa lutsa,tashi ɗaya sha'awar ya luma haƙoransa a cikin tuffan(apple) dayake gabansa ta taso masa.
Hannu yakai a hankali zai ɗauke,Hajiya zeenah ce tayi saurin buge hannunsa tareda yin magana ƙasa ƙasa.
"Wannan a kwaɗayinsa sai ya jawo mana abinda zai kashemu,wani inya ganshi zaicd bayacin kayan gabass"
"Ko ɗayah bazai mutu ba dan yaci wannan abin,shin a yanda kukaji labarina nayi muku kamada wacce zata sakawa mutum guba a abinci ta kasheshi......ahah ahah bana kaiwa farmaki ta baya kaman matsoraciyah ta gaba nake tunkarar koma waye,konayi nasara koshi yayi ni hakan shine nasarata"
Dukkansu ɗaga ido sukayi a tare suna kallon mamallakiyar muryar datayi maganar.
Fara ce sol amma ta sirka yellow bakaman fatar masu jan kunneba,tanada tsayi da kuma mulmulallen jiki wanda babu alamun tarin tsokar ƙiba a jikina.
Duk inda aka zayyano fulanin usul akan siffanta su da kyansu daidai gwargwado,ita baza'a cireta daga irin nasu kamanninba,saidai ita koma bayan su ,tana ɗauke da shuɗiyar ƙwayar ido,wacce tabata kamanni irinna turawan yamma,harma yafinasu yin kala da kuma radiating ɗin haske.
Idanuwannata dara dara ne farare,da suka samu baƙin ƙwalli da shudiyar ƙwaya,saita bayyana kaman ba daga duniyar tamu tazo ba.
Shuɗiyar doguwar rigace a jikinta,amma bata kamata har can ba,tana jingine a bakin ƙofar shigowa falon,da alama bata cikin gidan yanzu da shigo.
Ɗauke hannunta tayi daga bakin ƙofar inda ta dafa,kafin ta ƙariso cikin falon,a kan kujera mai ɗayah ta zauna wacce take facing ɗinsu.
"Sannunku,bansan ku suwaye ba,amma labari yazo kunnena tun lokacin da kuka buɗi baki cewar kuna neman Bombee a karo na farko. Lokacin danaji labarin wai wasu sunxo nemana nayi mamaki.
Mai kuke nema a gareni haka, dahar kukebin gari kuna nemana,koma menene nasan babban abune. Dan a lokacin da muruje yabaku labarina nayi zaton zaku haƙura kukoma inda kuka fito,saikuma kuka bani mamaki,dasafe ma sai aka ganku kunsake fitowa nemana"
Tsuru tsuru sukayi,lallai wannan matar taci wannan labarin da sukaji,wato duk yawon dasuke na nemanta tana sane kenan.
Har Hajiya zeenah ta buɗi baki zatayi magana kukan yaro ya ƙatseta,wanda Hilyaan ta shigo dashi tareda nufar inda Bombee take zaune.
Hannu ta miƙa ta karbeshi tareda tambayar Hilyaan ɗin.
"Mai yasameshi hakane,baya kuka irin haka akai akai,kuma likitan yazo ya dubashi kaman yanda nace?"
"Eh ya dubashi,inaga fah kaman ɗan zazzabine yake damunsa,sannan kuma kaman madarar da aka fara bashi jiyane yajawo hakn"
"A daina bashi madarar nan sai yayi wata shida tukunna,har yanzu bai girmaba,nidama nasan madarar nan rayiwa jikinsa girma,ki fita da ita daga gidannan,nafasa bashi ita,zan rage aikin zirga zirga na dunga shayarshi kawai,he need my time too,not only my matter"
Karban yaron tayi tana shirin fitar masa da mama,Hajiya zeenah ce tayi sauri bugar iliyah akan yabasu waje,da sauri kuwa yatashi bayan ya suri tiren kayan marmarin.
"Ohh sorry fah,banida manner ne sosai wani lokacin"
Bombee tafaɗa ko a jikinta lokacinda take sakawa yaron abincinsa a baki.
"Uhm ......uhm bakomai ne ya sakani tasowa daga inda nake nazo wajennan ba saidan wani taimako danake son kiyimin"
"Taimako wanne iri kenan kuma a guna?"
"Inasone ki auri ɗana na wani lokacin ƙayadadde,daga baya kuma sai a raba auren"
"Aure nikuma????? Kinsan mai kike cewa kuwa?"
"Ehh aure,karki damu babu abinda zai haɗaki da ɗana idan shi kike tunani,aikin dazakimin ba akansa bane,akan matarsane"
"Hhhhh nikuwa nasan ba abinda zai haɗani da danki,a labarin da aka baki da kuma wanda kika gani,kin shaida inada ɗa batareda aure ba,babu uwar dazata yarda ta haɗa ɗanta da mace irina,dole akwai abinda kike buƙata gameda kalmar auren.
Karki ɗaukeni jahila kaman yanda kikaji labari,wancan a dane ba yanzu ba,ki tafi kaitsaye ki faɗamin me kikeso"
Taƙaitaccen labarin lubna Hajiya zeenah tabawa Bombee,da irin ƙarfin ikon ubanta da kuma abinda take aikatawa. Sannan kuma taƙara da cewa.
"Ta hanyar aurene kawai zaki iya min maganinta,kasancewar ubanta yanada babban matsayi a kotu,idan abu kikayi mata ta hanyar kishi baza'a zargeni da komai ba.
Tana da ƙarfin hanya ta kowacce siga,idan nace zan turasashi yasaketa kuma tayi masa asirin dazai mutu a ranar,dan haka nayi bincike naga ke kaɗaice nakeda wacce zaki iya yimata abinda dakanta zata nemi sakin batareda matsala ba"
Ɗan guntun murmushi Bombee tayi,danta fahimci inda zancen Hajiya zeenah ya nufah.
"Hhhhhhh kuma a yanda kika ban labari sai kikaga nayi kama da wacce mutum zai taso yazo yasakani abinda yake so na matsalarsa na magance masa,shin kama nayi miki da mai taimakon gyara aure?"
"Ba taimakona zakiyi kawai ba,aiki na kawomiki,auren iyah Wata shidane kawai,ko kuma gwargwadon yanda kika karya lagwonta,sannan zan baki Miliyan Ashirin idan kikayi min aikim"
"Hhhhh miliyan Ashirin?? Kibar wannan zancen,nizan tsara komai yanzu,shin na yarda da zanceki ko kuma akasin haka.
Hilyaan zata karbi bayanan komai danake buƙata gameda lamarin,zanyin

Please Login or Register in order to submit comment