Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gunji.
Farmakarta sukayi a tareda da nufin kaimata mungun duka,saidai cikin sa'a tasamu nasarar tsallakewa ta hanyar yin tsalle tareda riƙe rishen bishiyar da take samanta.
Wuƙar kunkuminta taciro ta sokawa ɗayah a gadon bayansa,aikuwa yafasa ihu yayinda yaji azabar ta ratsashi.
Komawa dabaya sukayi ganin an shafe kusan daƙiƙa ashirin basu samu nasarar tabata ba.
"Kai ogah yarinyar fah ta iya faɗa da alama,ya kake ganin za'ayi?"
"Kuje mata kuma salon dabara mana"
Suna cikin hakanne goje ya sanɗeta tajuya baya ya sake mata sanda a gadon baya,kasa jure zafin dukan tayi,dan haka tafaɗi kasa tana maida numfashin wahala.
Wani sandan goje yasake narka mata a ciki,tasaki kukan mai nuna Alamar dukan ya shigeta.
"Wai ke mai iya faɗa koh,birice ke yau taki taƙare"
Duka yacigaba da kaimata ta ko'ina,babu tausayi babu imani. Tun Bombee tana nishi har yazamo jin dukan take kawai yana shiga jikinta.
Tsugunnawa yayi saitin fuskarta yana kallonta ɗauke da murmushi mugunta akan fuskarsa.
"Kai tulezi ku buɗemin ita ku fara yimata fyade har saina ce ku daina tukunna"
Rufe idonta tayi kirif tana jira taji ta inda zasu shigeta su keta mata mutunci. Duk iya kokarinta wajen ganin ya motsa gabobin jikinta abin ya faskara,dan kamar basa karbar saƙonta ma ballantana su motsa ɗin.
Shirinyewa tayi ta saddaqar tata taƙare daga wajen,a sama sama tajiyo hayaniyar mutane da kuma sautin takalmansu,wanda ta tabbatar bana masu yimata aika aikar bane.
Sakin ta taji sunyi sun nausa cikin jejin,yayin da karar sawunsu yake yin nisa,ƙarar na wasu kuma ya dunfarowa inda take kwance.........bata san shin masu cetonta bane ko kuma masu cutar da ita.
Ɗagata taji anyi an sakata a cikin wani abu mai tafiyah.


Sorry ayi hakuri a barshi haka,🤣🤣🤣🤣 bansan mai zance ba












_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼



____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤29🖤




A hankali take bude idanuwanta wanda sukayi mata nauyi tamkar anɗora mata dutsi akai.
Saurin yunƙurawa tayi zata tashi,amma saitaji jikinta tamkar an ɗaɗɗauresu da wasu boyayyun zarurruka.
Ɗakin haskene dashi amma bana hasken rana ba ko kuma fitila,sai na tsabar farin fentin cikin ɗakin.
Alamar motsi tafaraji a kanta,a hankali take daga kannata harta sauƙeshi akan fankar datake wainawa tana bawa ɗakin wadatacciyar iska.
Baki tasake cikeda mamaki ,dan tunda take bata taba kallon waje mai irin haka ba a rayuwarta.
"Na ɗanɗin inane,sannan kuma waye ya kawoni wajen?"
Ta faɗa sanyaye,bata kai ga tantance hakan ba daga mariƙar ƙofar ya murɗa,wanda lokaci dayah ya murɗa da tunaninta,dan kuwa batasan wata ƙofa mai hannu yana motsi ba.
Haidar ne yashigo ɗakin,fuskarsa ɗauke da mamakin ganin idonta a buɗe.
Ɗaga murya yayi yanda na wajen ɗakin zai jiyoshi yace.
"Mommy kizo da sauri ta farka"
Ƙarisowa yayi cikin ɗakin tareda zama a gefen gadon da take kwance.
"Sannu Bombee yakinki,amma wannan mutane basuda imani a ransu"
"Meyafaru bayan wanda ya auku a jejin,sanann inane nan haidar ka kawoni"
"Muna zuwa mutanen suka gudu,sannan yau kwananki uku a kwance,nan kuma gidanmu ne"
Yana cikin yimata bayaninne wata ƴar dattijuwar mata ta shigo ɗakin,a kallon farko zaka hango kamanninsu da haidar ɗin,saidai matar tafishi hasken fata da kuma manyan idanuwa.
Murmushi tasakar wa Bombee mai taushi tareda zama akan kujerar dake madaidaicin ɗakin.
"Sannu yarinya yajikinnaki,gaskiya a yanda suka dake gidannan kinji jiki sosai,mai kikayiwa wannan mutane haka?"
"Babu abinda nayi musu Mommy,yaran tsohon mijina ne da muka rabu shekara biyu baya"
Tare haidar da mahaifiyar sa suka haɗa baki wajen cewar.
"Tsohon mijinki shekara biyu baya,yanzu ma nawa kike daza'ace shekara biyu baya kinyi aure?"
"Uhm hakana babana ne ya auraminshi saboda naƙiyin jarabawar tafiyah makarantar kwana,to a ranar farkon aurenmu ne.......yazo yimin fyaɗe na farmakeshi shine..........aka raba auren. Yanzu kuma yazo daukar fansar abinda nayimasa,saboda illar danayi masa na bazai sake haihuwa ba"
Dakatar da Bombee Hajiya tayi da maganar,dan tun a bayani farko tagano abinda ya faru,ita kanta tayi mamakin karfin halin Bombee ɗin,amma kuma saita barshi akan tayine dan ƙoƙarin kare kanta.
"Kinga ki daina yawan magana dan baki gama warkewa ba,Allah ya kiyaye nagaba,haƙiƙa kinyi bajinta sosai,dan dama haidar yasha bani labarinki tun kafin yamiki magana,koyaushe sai yazo yacemin yaga mace a jeji tana koyon faɗa.
Yanzu dai ba wannan ba,yakamata ki faɗamana gidanku domin a sanar da inda kike,danna san dole zasu nemi sanin mai ya faru dake"
Shuru Bombee tayi tareda tafiyah tunanin abinda yafaru kafin zuwanta jejin a ranar,abinda ta aikata a gidansu tasan babu wanda zai nemi sanin inda take,kuma ba wannan ne ma babban abin dakuwar ta ba. Ita kanta innarta fama take da lalurar rainon ciki,sannan asibiti sun tabbatar ba'ason ta dunga shiga damuwa,sannan kuma ga uwa uba abinda tayiwa mahaifinta.
Babu abinda take sakawa iyayennata sai tashin hankali,dan haka lokacin yayi daya kamata ta dakata da wannan abin haka.
Numfasawa tayi kafin tace.
"Iyayena basanan,a wajen maharbi uwaisu nake zaune"
"Uhm kaji ba dama saida nace maka mukaita can kace wai bananne gidansu ba,kana ganinta tana shiga gari"
"Eh inazuwa gidan yan uwana ne s garin"
Bombee tayi saurin kare kanta kafin wani ruwan yasake bullowa.
"To shikenan amma tunda yanzu kika tashi,ki bari nan da gobe sai mu maidaki can ɗin,yanzu zansaka haidar yaje ya faɗamusu abinda yake faruwa"
"Ahah Hajiya nagode da ɗawainiyar da kukayi dani na wannan lokacin,amma inason tafiya yau"
Hajiya Zulaiha ce mahaifiyar haidar ɗin ta taimaka mata tayi wanka da dabara. Saboda har yanzu akwai ciwuka a jikinta sosai,ƙarfin hali kawai take danta nuna taji sauƙi.
Abinci Ta haɗamata marar nauyi taci,tareda magungunan da mahaifin haidar ɗin ya siyo mata wato Janar Muhammad Bello.
A leda Hajiya Zulaiha ta ɗaure mata maganin dakuma wasu abubuwan makulashe wanda zasu tafi dashi.
Ɗakin da take kwanca ta shiga,suna ta hira da Haidar cikin raha da nishadi,kaman sun shekara da sanin juna.
Dukkan hiran dayake mata bai wuce na labarin yayunsa biyu mata ba,da kuma ƙannesa ma biyu mace da na miji,wanda suka tafi makaranta basu dawo ba.
"Uhm kace kana da yan uwa sosai,ni kam mu biyune kawai a wajen mahaifinmu,daga ni sai ƙanwata,itama tana wajen innarta"
"Bombee kin shiryah tafiyar kuwa yau,bazaki sake yimana kwana ɗaya ba"
"Ahah zan tafi ai zan dunga kawo muku jiyara"
"Wai ai inaga nanda sati ɗayah zamu tafi,kafin sannan kam ki kawo mana ziyara idan kin samu sauƙi,yanzu ki fito Baban su haidar na nemanki a falo,zai maidaki gida shida Haidar"
Ɗaga kai tayi cikin girmamawa alamar taji abinda Hajiya Zulaiha tace.
Mutum ne mai yawan murmushi kaman haidar ɗin,sannan gashi dogo kakkarfah......uhm soja mazan fama kenan.
Tsugunnawa Bombee tayi kaɗan ta gaisheshi cikin girmamawa.
Ga mamakin ta kuwa bai ƙyamaceta ba kaman ƴan garinsu,dan da fara'ah ya amsa mata. Har yana tsokanarta wai tafi ɗannasa jarumta.
"Da haidar yabamu labarin yanda kika tareshi har ya samu guduwa a lokacin naji kin burgeni sosai,kuma fah ko kunyah bai jiba yana namiji wai mace tatare masa faɗa,mai makon ya tsayah yaji dasu......"
Dariyah dukka wajen aka saka banda haidar wanda ya cune fuska kaman ƙaramin mai yaro mai feeder.
Kuɗi ya ciro ya miƙa Bombee,amma juyin duniyar nan taƙi karba,dan ita tun lokacin da Innarta tayi mata magana akan kuɗi,sai ya zamo bata fiyeson ko kyauta tadunga karba a hannun mutane ba,ballanta na kuma sata.
Haka dole ya ƙyaleta ganin duk ƙoƙarinsa amma taƙi karba,Hajiya Zulaiha yabawa a ƙarshe kan tayimata siyayya to takaimata.
Da haka Bombee tayi sallama ta matarda taji tashiga ranta,bayan innarta da kuma inna shatu Hajiya Zulaiha itace mace ta biyu data jita a ranta.
A bakin ƙofar gidan suka ajiyeta,bayan Haidar yabata ledar ta Hajiya Zulaiha tace yabata.
Inno tana tankaɗen tuwo taganta tashigo tana tafiyah a hankali,alamar babu lafiya,dan dama kwana biyu tana cikiyarta shuru.
"Ahhh Bombee mai ya sameki haka?"
Bata kai ga amsawa ba taji muryar Haidar yana gaisheda inno,mamaki tayi dama biyota yayi?
"Uhm baka tafi bane dama?"
"Ah iya abbane ya tafi,ni sai anjima zan tafi idan naci tuwon inno"
Yakarisa maganar yana ƙifta mata ido,bai san mutane ba amma har ya shige gaba,ta faɗa a ranta,a fili kuma tana binsa da harara.
Shine yabawa inno labarin abinda ya faru,inda suka jajanta sosai.
Sai bayan ya tafi da daddare Uwaisu yanayimata sirace na maganin gargajiya yake cewa.
"Kwananki uku kenan a gidansu,amma kuma maimakon ki wuce gida sai kika iyo nan meyasa,innarki fah jiya taxo nan tana tambayar ko kinzo nan,inno tace mata kinzo amma kin fita.
Nasan tayi hakanne domin ta kwantar mata da hankali,nima tun a jiyan nake nemanki"
"Ahah baffah bazan iya komawa gida yanzu ba,saina samu sauƙi tukunna,Saboda abinda na aikata,wanda kuma duk inna laari ce ,ni banason matar nan wlh,inna kuma ji takeda ita kaman innarta,shikuma goje.......hmmmm"
Tafaɗa tana cizon baki.
"Kee Bombee to miye dalili ciki danta ji da ita,ke kanki shaidace yanda ta riƙe innarki hannu bibbiyu sanda aka kaita gidanku,kowa yana shaidan halinta na kirki"
"Eh kowa yana shaidanta,amma ni zuciya ta abu daban take faɗamin gameda itah,kuma da sannu zan gwadata domin share tantamata. Shikuma goje aradu ko banyi masa komai ba dolene na ajiye masa Gargaɗi mai tsaurin gaske"
Shuru sukayi babu wanda ya tankama ballantana ya bata yawun bakinsa.
Washagari da safe Bombee ta tashi da ƙarfin jikinta ba kaman jiyan ba,saboda magungunan da take sha akan lokaci.Ranar bata fita taje ko ina ba.
Da daddare bayan anyi isha inno ta shiryah domin zuwa sanarwa innarta labarin ganin Bombee.
Bata hanata yin hakan ba saboda itama tanason kar innar tata tashiga damuwa sosai na rashinta.
Tare suka fita da inno har zuwa ƙofar gidannsu kafin tajirata tashiga tafito.
Duk wanda zai shige tana daga zaune tana kallonsa,harda mahaifinta wanda yadawo daga masallci. Ƙureshi tayi da ido har yashige gidan.
Tunawa tayi da idan yadawo daga isha a irin daidai wanann lokacin yake sake niyamata karatu,sannan suci abincin dare tareda.
Runtse ido tayi tareda saurin kawar da tunanin hakan a ranta,dan a ganin ta bashida amfani a wajen yanzu ba,domin ba komai zai ƙaramata ba sai baƙin ciki.

A zaune suke a bakin ruwa inda suka saba zama kullum,dan tun bayan abinda yafaru da ita,bata koma gidaba yau sati guda kenan.
Haidar ne ya kalli Bombee tareda cewa.
"Yanzu kam kin samu sauƙi sosai koh,dan Allah kidaina yawan biyewa mutane,wanda yanuna baya ƙaunarki ki ƙaurace masa kawai shiyafi,bakiyi tashin hankali dashi,ki tuna koma mai zai faru kefah macece"
"Bakaine nafari wajen faɗamin haka ba,sanin ni macece yasan ma nakeyin hakan,duk rintsi bazan bari wani yaci mutuncina yanda yake so ba,sannan duk wanda yayimin abu naji bazan iya bariba to saina rama "
"Oh mai yayi zafi ni bance kada ki rama ba,kawai dai ina faɗamikine saboda jibi zan bar garinku ba,wanda nasan banida tabbacin sake haɗuwa dake nan gaba"
"Hmm kuma wannan shine maganar bankwanar dazaka min,maizai hana kacemin duk wanda yayi miki ki rama.
Jiya danaje gidnasu na kula Abba naso kazama soja,a haka zaka zama da wannan zuciyar?"
Dariyah haidar yayi tareda cewa.
"Hhhh shiyasa fah inaga jininku yazo ɗaya da Abbanmu saboda kinada zafin zuciyane wanda ake so a wajen sojoji.
Yanzu ya maganar tsohon mijinki,i hope zaki barshi ya wuce koh?"
"Babu wannan maganar,yau zanje izuwa gareshi kuwa da daddare"
Zaro ido haidar yayi daga nan bai sake cewa komai ba.






_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼



____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤30🖤




Sauri take tayi cikin duhun dare,da alama fitsarine ya kamata sosai.
Tazo daidai hanyar shiga banɗakin taga alamar wulagawar mutum a sashen goje.
Ƙiftawa ido tayi tasake ƙiftawa,dan zaton ko aljani tagani,saidai kuma ta kawar ta hakan a ranta ta wuce banɗakin.
Bayan tafito harta nufi ɗakinsu saikuma tashi alamar motsi a sashen kumadu.
"To waye ne yashige sashen goje,shekara biyu kenan yadaina kawo mata,tunda kowa yasan babu abinda zai iya yi musu,to waye kuma a sashennasa?"
Harzata shiga ɗakin kuma wata zuciyar tace baritaje ta duba tagani.
A hankali cikin sanɗa ta nufi sashennasa har ta samu shiga.
Kofar abuɗe take,hakanne yasake tabbatar mata cewar akwai mutum a cikin ɗakin.
A baƙin kofar ta tsayah tana shirin leƙawa,bata ankara ba sai ganin mutum tayi yafito daga ɗakin da sauri cikin baƙaƙen kaya.
Shima bai kulada indo a wajenba dan haka sai suka yi karo tareda faɗuwa a tare.
Mayafin fuskar mutumin indo takama saboda karta faɗi,aikuwa tajawoshi zuwa hannunta.
Hasken farin watane yasakata gane waye a gabanta.
"Bombee!!!!?"
Tafada cikin sanyin murya haɗe da razani kuma.
"Shiitttt tace tareda shaƙe wuyan indon. "Eh nice,kuma naji labarin kinganni a gidannan zakiga yanda zan miki ehe"
Taƙarisa maganar tana boye wukar datake hannunta duk jini a jikinta.
Tsallaketa tayi ta fita daga gidan da sauri,indo na nan zaune a wajen bata samu damar tashi ba har kusan Assalatu,dan tsoro takema karta tashi Bombee tadawo tasake yimata wani gargaɗin.
Ita kuwa tana fita daga gidan jeji ta nufah gidan su inno.
Har tazo shiga ɗaki taji uwaisu yana cewa.
"Ke Bombee daga ina kike da tsohon darennan,keda ba lafiya ce take ba sosai?"
Mayafin data rufe fusakarta haɗe da sukar ta boye a bayanta tareda cemasa,
"Bakomai baffah,kawai kawai wani ɗan abu nayi a jeji"
"To shikenan,amma jejinnan fah ki kiyayeshi Bombee"
"Tamm"
Daga haka ta wuce ɗakinta,bukkar datake gefen tasu.
Jijjigata taji anayi.
A hankali ta buɗe idonta tana kallon inno dakuma uwaisu a kanta,idanuwansu ɗauke da tashin hankali.
"Ke Bombee jiya ina kikaje da daddare dana ganki"
Shuru tayi bata basu amsaba,sai daga baya kuma tabuɗe baki a hankali tace......
"Uhm gidan su goje naje"
"Mekikayi masa a gidansu da tsohon dare"
"Uhm...uhm.."
Tana cikin inyinar ne goje nuna mata wuƙarta da kuma mayafinta na jiyah,wanda tana zuwa kwanciya tayi bata tsayah wanketa ba.
"Bombee na riƙeki tamkar ƴa ta,inda wani ne yazo yafaɗamin abinda kikayi,ba wai nina gani da idona ba,bazan taba yarda ba,Bombee kisa kisa fah kikayi,ina zakije da ran dayah rataya a kanki yanzu.
Duk wani rashin jikinki haka naji nagani na ɗauka,saboda nasan yarinta ce watarana zaki daina,amma kisa Bombee bazan iya rufemiki ba,inna faɗamiki zan taimakeki akai nayi ƙaryah"
Shuru Bombee tayi tanajin mai yake faɗa,runtse idanuwanta tayi da alama tatafi cikin wani tunanin.
"Yanzu bazancen bata lokacin bane,Bombee yakamata ki fita daga gidannnan ki buya wani wajen,domin indo tasanarwa ƴan sanda taganki kin fito daga ɗakin goje da tsakar dare,ɗauke da wuƙa mai jini.
An bazama ko ina ana nemanki tun safe,nan ma ba wajen buya bane zasu iya zuwa,domin gidanku sunsan kina nan wajen.
Dan Mlm ma yace gidanku sunce kina nan wajen,nasan bazai wuce innarki ba,dan ita kaɗai tasan inda kike"
Tasho Bombee tayi cikin sanyin jiki ta yafa gyale akanta,wuƙar tata dake gefen Uwaisu ta ɗauka ta saƙala a kunkuminta.
Bakin ƙofa ta nufah kafin tayi magana cikin sanyin rai.
"Nagode da hidimarku a rayuwata,haƙiƙa a yanzu nakai matakin da bazan kusanci masoyana ba,saboda suma bazasu iya tsira daga kaidina ba.
Ni makashiya ce yanzu a idon kowa,dan haka wanda yarabeni ma za'a fara ganin sa a matsayin hakan.
Nizan tafi sai wata rana"
"Ina zaki tafi yanzu"
"Inno ta faɗa cikin raunin murya"
"Can da nisa,inda nima bansani ba,amma zanyi iya koƙarina wajen ƙauracewa nan wajen"
Daga haka tasaka kai tafita a cikin gidan.
Saida tayi gudu mai nisa kafin tajuyo ta kalli gidan da yake ɗauke da rabin yarintarta,motar ƴan sanda taga ta nufo gidan,hakanne yasa ta tabbatar da maganar baffannata,kuma bazata ga laifinsu ba gameda furucinsu gareta,ta cancanci fiyeda hakan ma a gun kowa.
Cikin dajin ta nausa ta gudu,ko ganin gabanta batayi sosai,har saida takai gejin iya yanda jikinta zai iya ɗauka.
Gari ko ina ya ɗauka cewar Bombee takashe goje har cikin ɗakinsa,dan da safe ana zuwa aka sameshi anyi masa yankan rago a wuyah.
Bayan an ɗaɗɗaureshi da igiyah anyi masa duka.
Abu wasa wasa yakai ga ko ina labari ya watsu,Bombee kuwa anyi neman duniyar nan babu ita babu labarinta,ta bace battt kaman bata duniyar.
Mlm Ahmadu tunda yashigo da safe bayan labarin ya riskeshi yake cikin ɗakinsa,ko fitowa bayyi ba ballantana yace wani abun.
Danejo ce ta tashiga ɗakinnasa,yana zaune akan dadduma yayi shuru.
"Sannu mlm,baka ce komai ba shin anganta ne"
"Hmmm ina za'a ganta,ni ina kyautata zaton ma yanzu haka bata garinnan,domin bayan yanka shi datayi,wai hadda kuɗi ta ɗiba maƙudai a cikin ɗakinnasa,kinga kuwa mai zata zauna tayi a garinnan"
"Kuɗi?.....hadda sata kenan aka a ɗakinnasa?"
"To yanzu ai ba ta sata ake ba,ta kisan da akayi ake,wama yake ta wani kuɗi yanzu"
Shuru Danejo tayi tana maimaita ɗiban kuɗin a ranta,saidai bata ce komai kawai ta tashi tabar ɗakin.
Yanayin damuwar data shiga da ita ɗakin taragu daga kaso Ɗari zuwa kusan kashi talatin,dan tunda taji zancen hadda sata tasakawa maganar ayar tambaya.
Taga haka bata sake bi takan zancen ba ta nufi ɗakinta.
Saida Bombee tabari dare yayi kafin ta fito daga maboyarta.
Babban hijabi ta zunduma har ƙasa haɗeda nikaf.
Hanyar cikin garin ta nufah domin gani mai yake wakana.
Can nesa da ƙofar gidansu ta tsayah,yara sunata wasan dare.
Ahhh kaman hakan bai faruba a rayuwarta,saidai ta sabanin farincikin da sukeyi itakuma cikin baƙin ciki take. Koyaushe saidai ace mata zai wuce,bata taba tunanin dagaske bane sai yanzun daya wuce tagani.
Wani yaro da ƙira yazo wuce ta gefentada kwano a hannunsa.
"Kai dan Allah ɗan zo na aikeka gidan can mana"
Zuwa yayi ya tsayah a gabanta,wata takarda ta fitar a nannaɗe a cikin hijabinta tabashi.
"Ka shiga gidan ka tambayi wacece Danejo,sannan sai ka bata,karka bawa kowa sai ita kaɗai"
Ɗaga kai yayi alamar yaji,daga nan yashiga gidan.
Jimm tatsaya tayi domin jiran fitowar dan aikan,bata ga ɗan aikaba shuru har na wani lokaci.
Wasu mutane tagani samari guda uku suna iyo hanyar da take,sannan kuma da yaron a bayansu yana yi musu magana.
Dan murmushi Bombee tayi ganin sakarcin da suke nuna mata,a zotonsu shin wayo suke mata zasu kamata,da alama labarin tana kallo da daddare bai gama karaɗe garin ba.
Saurin juyawa tayi tana tafiyah da sauri sauri tanufi jeji,suma suka bita a baya.
Sun danyi tafiyah mai nisa,dan zuwa yanda gudu suke itada dasu na tafiya.
Da alama ga wanda zata bawa saƙon subawa mutanen gari,ta faɗa a ranta.
Su su biyar ne,kasancewar darene kuma basanin hanyar wajen sukayi ba,nan da nan tayi nasarar rarrabasu a jejin.
Bayan wani ta dawo yana dube dube ta kifa masa naushi a kusan wuyansa,hakanne yasa ta jube yana dafe wajen.
"Kayi haƙuri da dukan danayi maka zaka warke,ni zan tafi daga garinnan,ina so kaje ka sanarwa gari bai ƙare iya nan ba ina nan dawowa watarana"
Daga haka tayi saurin barin wajen kafin abokanannasa su tarar da ita.
Hanyar gidan su haidar ta nufah,ta zauna a can nesa da gidan,tana jiran wani a cikin gidan ya fito,amma shuru har bacci ya ɗauketa a wajen.
Ba ita tafarka ba har saida alfijir ya keto.
Mahaifinsu Janar Muhammad Bello tagani ya fito daga gidan ɗauke da wani abu kaman drawer,a wajen motarsu ya ajiyeshi inda wasu kaya suke,da alama tafiyar zasuyi kenan.
A cikin booth ɗin motar yasaka inda wasu kayan suke,dayake Helux ce tanada ishashshen wajen ɗinban wasu kayan.
Duk abinda yake Bombee tana kallonsa har yagama ya koma cikin gidan.
Lallabowa tayi har zuwa bakin motar.
Idan tashiga motar nan zata samu damar barin garinnan batareda matsala ba,kuma dama batasan hanyar dazata bi ta tafi ba.
Cikin booth din motar da tsilliga tareda shiga ƙasan drawer daya saka a cikin motar.
Tana gama shiga kuwa haidar yazo da wata jaka ya ɗora a saman,yanda yayi mata sauƙi wajen buyar batareda gajiyah ba.
Sauƙe ajiyar zuciya tayi tareda fatan Allah yasa hakan da tayi shine daidai kuma mafita kaɗai a gareta.
Muryar haidar taji yana cewa.
"Bombee??me kike a cikin mota kuma,hakan ma a drawer,tsawon wannne lokacin kike ciki?"
Saurin buɗe idanuwanta tayi ganin hasken rana akanta,ga kanta wanda yakeyimata azabar ciwo,saboda gangarar dataji anayi a hanyar tafiyar har yasakata yin suman wahala.
Bata iyah buɗe baki tasake yimasa magana ba tafara komawa wata sumar,saidai taji muryar Hajiya Zulaiha tana cewa.
"Abban haidar kawai kashiga da ita cikin jirgin,bamusan mai yasa ta zabi biyomuba amma tabbas akwai dalili,kuma a yanayinta yanzu tana buƙatar hutu,mu kammu mun jijjaga da hanyarnan inaga ita"
Tana gama jin maganar taji an ɗagata ciɗak zuwa cikin jirgin.


__________DAWOWA WAJEN SU HAJIYA ZEENAH__________



Tunda aka tafi bada labarin,hajiya zeenah tareda idi masu yi wani kyakykyawan motsiba har aka gama.
"To wannan shine labarin rayuwar Bombee a garinnan tundaga tashinta,kuma itace wacce kuke nema,duk da bansan mai yasa kuke neman ta ba,amma wancan tana yarinya ne kukaji"
"Kan buuuuu Hajiya Inaga mukoma ki huta gobe mu ɗau hanyar gida kawai"
"Iliyah yafada yana dauƙe ajiyar zuciya"
"Ahah Muruje to ina kuma labarinta a wajen su Hajiya Zulaiha ɗin,sannan kuma ya akayi ta dawo garinnan har kacemana tana cikin garinnan?



Todai nasan kuma zakuso ku sani koh?????😂😂😂






_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼



____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤31🖤




"Uhm karki ce mai yasa na tambayeki,amma menene haka kike nema a wajen wannan yarinyar,abinfah ya wuce yanda kike zato.
Bayan bacewarta daga garinnan komai yafara tafiyah normal,saidai kuma mahaifiyar ta inna Danejo bata manta da batan ƴar ta ba,dakuma mummunan zagin da ake binta dashi. Hakanne yasa abin yafara damunta da kaɗan kaɗan,ga kuma dama ciki mai wahalarwa.
Ba a tashi sanin mai ya faru ba har saida tazo haihuwa matsala ta tashi gadan gadan. A nanne mlm Ahmadu ya kaita asibiti amma tagagara haihuwa,dole sai dawowa gida sukayi,dan su inna laari sun matsa kan ayi na gida mana.
An fara na gidan,a daren ta haifi ɗa namiji wanda dama ya daɗe da mutuwa a cikimta,dan har hakan ya shafi mahaifarta itama tabiyo ɗan tare.
Jinya tafarayi duk da bayan rashin ɗan.
Koyaushe tana ɗaki komai sai anyimata na taimakawa.
Sai bayan wani lokaci abin yaƙi mlm Ahmadu ya maidata asibiti shida inna laari,a nanne aka tabbatar masa da cewar ta kamu da matsanancin hawan jini.
Wanda shiya taba mata ƙwalkwalwa da kuma idanuwanta,wanda sanadiyyar kullum da zurawa waje ɗaya babi ƙiftawa har suka mutu suka daina gani.
Magana kuwa duk abinda za'a faɗa babu wanda zata amsa,shima duk yanada nasaba da ciwon daya sameta"
Lokacin da muruje yafaɗawa su Hajiya zeenah matsalar Danejo haƙiƙa sun tausaya mata,kuma daman sun ganta a hakan ai lokacin da suka shiga gidan.
"Wai amma tayi tsawon rai,hawan jini yayi mata wannan cin amma tana raye?"
Hajiya zeenah ta faɗa cikeda mamaki.
"Shekara uku kenan data samu lalurar,dan tadaɗe tana jinyah kafim hakan yasameta,kuma har yanzu ana yimata maganin gargajiya dana asibitin"
"To ya Bombee kuma tayi data dawo taga yanda innarta ta koma,sannan yaushe ta dawo"
"Hmmm Bombee fah watan ta kwata kwata biyu da dawowa garinnan da zama, dan da zuwa tayi ta koma a cikin mission ɗin aiki, shima kuma daman ba'a gidansu take zaune ba,dan mlm Ahmadu yace badai gidansa ba,farkon dawowar a gida ta sauƙa,wani abu da tayi masane yace bazata zauna a gidansa ba.
"Mai tayi masa?"
Hajiya zeenah ta faɗa cikim zaƙuwa.
"Ummm bayan dawowarta garinnan tayi taimako ɗayah amma kuma tayi lahani shima.
Zuwan ta ne takafah ƙungiyar Black blood,wanda tayita da taimakon wasu mutanenta fararen fata guda biyu da kuma masu baƙar fata guda uku,dukkansu kuma matane masu jarabar ƙarfi.
Duk wanda yashiga ƙungiyar zai dunga yin tuƙin hawan mambila,ita kuma in yana wajenta babu wani ɗan fashin dazai tareshi a hanya,da sharaɗin zai kaimata kuɗin ta itakuma duk wata.
Matasa ƴan iskan gari da sukaji haka tuni suka shiga,aka basu training ɗin tuƙi na musamman,ga kuma yanda take basu lasisin yin abinda suka ga dama,indai ba gonarta suka shiga ba,nan da nan tafi uwarsu ma muhimmanci a zuƙatansu.
Ta gina wani gida a can cikin duhuwar daji,inda take masa laƙabi da yankinta kuma fadarta,saidai har sannan bata komaba"
"Meyasa to ta ginashi idan ba shiga zatayi ba"
"Zuwan ta shekara biyu baya kafin ta ginashi a gidansu ta zauna,wanda dama wannan ba zuwa tayi zaman dindin ba.Tazone kaman gida daga aiki,wanda aka turo ta garin tareda wasu sojojin. A lokacinne ma tafara kafah kungiyar dana baku labari a bayah"
"Eh munji labarin wannan kungiyar muma shigowar mu cikin garin a bakin wani mutumi toro"
"Hakane tana da mutane masu tarin yawa a ƙarkashinta"
"Dawowarta zaman dindin shine ko dariyah bata fiye yiba,sannan kuma bakowa ne yake kallonta ba saida gaske,ita kaɗai ta dawo daga ita sai wata matsashiyar budurwa kaman sa'arta,sannan yanayinta batayi kamada ƴar ƙasar nan ba.
A lokacin ko sunan sojiji batason a anbata a kusada ita,bamusan dalilin ba,wata biyu kenan da faruwar hakan.


______***DAWOWAR BOMBEE GEMBU***_____





Shaƙar iska tayi a bakin ƙofar shigowa garin daga cikin baƙar motarta ƙirar daraja😀.
Hakan dataga bayyi mata ba fitowa tayi daga cikin motar ta tsayah

Please Login or Register in order to submit comment