Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan?"
"Kutt yanzu ne safiyar kuma ma zuwa wajenkine laifi komai,...naji abinda yafaru tsakanin ki da mijinki,gabaɗaya gari ya ɗauka Bombee tadawo gida bayan kwanan ta ɗaya a gidan miji?"
"Wata tsiyar ce dan nadawo to,ina kema kikace mijina bana wani ba,mutanen garinnan allah suna shiga hancina da ƙudundune,ke kuma ga munafurfur shine kika taho da rawar ƙafa ki faɗamin ko"
Juya ido sakeenah tayi tareda hararar Bombee,haka kawai jininsu ya haɗu,amma ko yaushe Bombee cikin nunamata isa take a dole ta fita da wata biyar.
"Kaiii ke wallahi Bombee tsiyata dake wanda yadamu dake ma baki barshi ba,koda yake laifina ne danake biyemiki"
A zuciye ta tashi zata bar ɗakin,Bombee tayi caraff ta rike mata hannu tareda cewa.
"Keɗince shegen surutunki ya miki yawa,naji menene yakawoki toh wajena,nasan dole akwai dalili"
"Hmm wai kura ce zatace da kare ya maye,kawai zuwa nayi tayaki zaman jimami,duk da cewar ko kaffara bazanyi ba nasan da gangan kika lahanta goje badan yakawo miki farmaki ba ko kuma dan kina tsoro ba,dama kin shiryah hakan tun sanda kika yarda da aurensa"
"To kin sani miyasa kike sake tambaya dama"
"Saboda share tantama ne"
"Hmm wato dan kiji daɗin zuwa kice ita tafaɗamin da bakinta dagangan ta maujeshi"
"Hhhhhh kinsan bazanyi hakan ba,nidama duk shirin auren da akeyi nasan bakiyi kama da wacce zataje ta zauna ba,ki kallifah kayanki na gida,duka sunanan babu abinda ya samesu baki bayar dasu ba ko kin tafi dasu.......ahhh to kayan auren fah,kinsan tunda baki daɗeba dole zasu karbi abinsu"
"Hhhh daga baya kenan,jiya naje nayi ciniiki na karbi kuɗinsu,yau zasuje a matsayin barayi suɗau kayansu yanda na tsara"
"Innalillahi keee Bombee to idan goje yaƙi sakinki fah yazakiyi"
"Hhhhhhh lallai kema gara ce,to ko kudin hajji aka bashi nasan bazayyi gigin ƙin sakina ba,kijira kiga zuwan takardar tawa,ɗan iska yaje yagama akuyancinsa da wasu,kuma tsabar dan ya raina rayuwata yace zan buɗe masa cinyata?....shi a dole wai ga miji ahh ubangida kai,tauren banza tauren wofi,na tabbatar yanda nayi masa dukannan bazai ƙara moruwa ba ta wannan fuskar kan,shida haihuwa kuwa saidai yaga anayi,naga da yanda zai sakeyiwa ƴaƴan mutane ciki"
"Kutt waikina nufin kinsan komai dama tsiyace"
"Da a tunaninki bansani ba,me kika ɗaukeni ne,dan kawai nace bansani ba shiyake nuna bansani,ke karki dameni bacci zan koma,ki tafi naki harkar.
Zan zauna a gida na sati ɗaya,daganan naɗora daga inda natsayah"
Takarisa maganar tana hamma tareda sake miƙewa akan gadon.
Jijjiga sakeena tayi tareda ficewa a ɗakin,Bombee ta wuce duk yanda take tunani.

Lokacin da suka isa asibitin su daayi sun ɗan tada goje da pilo,ana zubamasa ɗan ruwan shayi a baki yana sha.
Sannu da jiki mlm Ahmadu yayimasa,ya amsa daƙyar,inna daayi kam ko kallon sa batayiba.
Dan sandan ne ya matso inda goje yake tareda cewa.
"Goje yanzu muka dawo daga gidan su matarka,ga surukinka nan ma kana gani,munyi mata tambsyoyi da dama,amma a yanda ta bamu labarin abinda ya faru,alamu ya nuna cewa batasan komai dayake faruwa ba dangane da zaman aure. Tace mana tunkarota kayi kana ce mata zakayi mata irinna sauran matan datakejin labari,wanda hakan yasaka ta shiga cikin tsoro ta farmakeka domin kare kanta. Saboda a baya taga yanda matan daka lalata suke shiga cikin wani hali na damuwa,kuma yanda ake bawa mata labarin fyaɗe,abune da ake nuna musu mutuwa ce kawai tafishi.
Shin dagaske ka farmaketa ko kuwa"
"Ehh to lokacin dana dawo gidan ina cikin fushi ancemin tafita da safe,to.....shiyasa nace mata inna fara babu wanda zai iya ƙwatarta a wajena,na nufeta domin nasaka ta jin tsorona,daga nan bansan miyasa ba ina dabb da kaiwa hannuna kanta saijina nayi a wata duniya daban ina juyawa"
Ajiya zuciya ɗan sandan yasake tareda cewa.
"Alamu yanuna kenan labarin data bayar da gaskene,sannan koda ankaita kotu baza'a ɗaureta ba,saboda an tabbatar batada masaniya gameda abinda yake cikin aure,wanda iyayenta sun amsa cewa hakan laifinsu ne. Sai nabiyu kuma ta kaimaka farmaki ne domin kara kanta daga fyaɗen da take tunanin zakayi mata"
"Amma kowa yasani tunda matata ce,ai ba fyaɗe zanyi mata ba"
"Eh kowa yasani,amma ita da batasan komai ba akan auren bata sani ba,laifi nakane goje,dana iyayenta kuma. Dan haka mlm Ahmadu zai biya komai daya danganci maganin ka har ka warke"
"Wannan zancen banzane,wacce bata san komai bane zata iya wannan aika aikar,zancen nan dasake,inma mlm Ahmadu cin hanci yabaka domin ka faɗamana haka to bazan yadda ba"
Jauro ne yasaka hannunsa akan kafaɗar inna daayi tareda cewa.
"Kinga kibar wannnan kumfar bakin,babu wani cin hanci haka zancen yake"
"Huuh haka kam,Dan Allah kuyi haƙuri da abinda yafaru mlm jauro,haƙiƙa abu bayyi daɗi ba,saidai babu yanda za'ayi tunda yafaru,yanzu zancen gida nakawo kuɗin da akayi zan bayar,ayi hakuri dan Allah.
Yarinya kuma kozata koma gidanta ba yanzu ba saitasan komai tukunna"
Tun kafin mlm Ahmadu yagama bayanin dayake goje ya zare ido tareda cewa.
"Wacce yarinyar kake zance,banason sake ganinta a rayuwata,wannan ba mutum bace,in aurena ne dayake kanta ake haɗani da ita,to na sake ta saki dubu ma idan anayi,bana som hanya tasake haɗani da ita ta arziƙi saita ɗaukar fansa"
Hannu Inna daayi takai zata rufe masa baki,amma ta makaro ya aikata abinda take gudun.
"Kai shashashan inane,karka manta fah yanzu tamaida ka musaki wanda bazai ƙara haihuwa ba,daka saketa wacece kuma zata zauna dakai,amma da ka barta ina dole ta zauna dakai. Yanzu kuwa zataje tafara sabuwar rayuwarta hankali kwance"
Kuka inna daayi tafashe dashi tareda cewa.
"Burina shine naga kayi aure ka haihu,amma wannan burin yanzu yakau har abada babu shi. Zabin daya ragemin shine naje na tattaro ƴaƴan daka raba a titi na riƙe,dan sukaɗai yanzu suka rage,wani bazai zo ba.........wannan yarinya kwai tsinanniya,bantaba zaton idan ka aureta nakasa ka zatayi ba,ita ma dolene taga karshenta aradu"
Ganin fallashe fallashen da inna daayi take tana kuka ne yasa mlm jauro jijjiga cikeda takaici,jan su mlm Ahmadu yayi waje suka gama tattaunawa,daga nan zance ya wuce,aka bar goje da wahalalliyar jinyah.

Cikin ƙankanin lokaci zancen Bombee ta lahanta mijinta a daren farko ya karaɗe garin gembu,kowa sai mamakin labarin yake.
Ita kuwa Bombee yakan ko kaɗan bai dameta ba,dan dama da gangan tayi hakan saboda tasaka tsoron son aurenta a zuƙatan mutanen garin.
Aikuwa tayi nasara,dan tundaga wannan lokacin koshi mlm Ahmadu bakinsa yayi mutt dayi mata zancen aure.
Zuwa jeji kuwa wajen su inno bata fasaba,sukansu basuji daɗi abinda tayi ba,amma ya zasuyi macece da ba'a sakata tayi saitaga dama.
Babu abinda yafi damun Daneji da lamarin sai yanda Bombee tabata kunya a gaban ƴan uwanta,suka zama ganau ba jiyau ba akan abinda Bombee tayi.
Har kusa sati guda da faruwar hakan Daneji bata kalli inda Bombee take ba,saboda takaicin abinda tayi. Tana sane da fushin da innartata take da ita,duk da yana damunta amma ta basar,dan tasan zata hucene nan da wani lokaci.
Tana tsaye a bakin gadonta tana shirin fita Daneji tashigo ɗakin cikin ɗaure fuska.
"Ina zaki da yamman nan?"
"Uhm zan ɗan......"
"Jeji zakije koh,kafin ki tafi jejin bani kuɗin kayan ɗakinki da kika siyar,zan mayar wa ubanki kudinsa"
"Inna ni ban......"
"Nima ƙarya zakiyimun kaman yanda kikayiwa mutane lokacin da kika kashe mijinki a tsaye,a tunaninki bansan duk abinda kikeyi ba,harda zuwanki wajen maharbi uwaisu ba,nice nacewa inno Ta dunga saka ido akan ki.Hmmm nifa na haifeki Bombee mai zaki boyemin dangane da rayuwarki.
Ba wannan ne yakawoni ba,ke yashafa wannan rayuwarki ce,amma kuɗin kayan dakin kam banaki bane bani su nan"
"Dama inna kin...kinsan.....amma ina baki fadawa baba ba ko?"
"Meyasa zan faɗamasa,mekike nufi,sai na buɗe bakina na tozartaki a duniyah bayan wanda kike ciki. Nima ba auren da akayimiki nakeso ba,sanann kowa yasan halin goje ya cancanci fiyeda haka,amma ba goyon bayanki nake ki aikata wani irin sa ba.
Ki kulada duniyah dakuma wanne mutane zaki fuskanta a duk inda kike,jikina yana bani rayuwarki bazata tsayah iyah garinnan ba,zaki shiga duniyah da nisa,dan haka idan hasashena yabbata ki dunga tunawa mutunci yafi kuɗi,sannan ki maida Alkhairi idan akayi miki,kuma ki tuna abu uku.
Duk da bawani sanin mutuncin kanku kikayi ba,ku tuna cewar ke musulma ce kuma macece sannan kuma bafulana,kinuna asalinkin a ko ina"
Ƴar dariyah Bombee tayi,haka halin innar tata take,tana yimata hanya a cikin duhu tana takawa batareda tasani ba,....ko dabbar da aka haifa yau kuka take ƙoƙarin yi na neman uwarta,ko ɗan banza yana san uwarsa,komin ƙarfinka wajenta zaka nufa in duniya tayi maka zafi,Allah yamu ikon kyautatawa iyayenmu,idan ƙasa ta binne idanuwansu kuma Allah yayi musu rahama da jin ƙai.
Ciro kuɗin Bombee tayi a ƙasan kayanta ta miƙawa Daneji,karba tayi ta ƙirgasu tareda kallon Bombee.
"Komai zakiyi a duniyah kisani Sata bata bawa mutum daraja,ki samu naki koda kuwa ta wuyane,karki dauƙi na wani,kisa a ranki kinfi ƙarfin hakan,saikiga zuciyarki da sane da abin hannun mutane"
Ɗaga kai Bombee tayi cikeda jin daɗin maganar mahaifiyar tata,wanda lokaci guda tayi musu matsugunni a cikin taswirar rayuwarta.




_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼



____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤27🖤





Bayan shekara biyu.............



Kyakykyawa kana farar budurwace sanye da riga da wando farare,tayi ɗamara da wani jan ƙyalle a mulmulallen kunkuminta wanda yabaje yabada siffar mata masu cikakken diri,saidai daga ganin jikin kasan ana yawan motsashi,dan a tsikeyake tsama.
Juyi take tayi gaba tayi baya da sanda a hannunta,wanda take tafiyar dashi a iska cike da bajinta da kuma ƙwarewa.
Tayi kaman sa'a guda tana yi,amma batada alamar dainawa ko nuna gajiyarwata.
Sai can kaman da daƙiƙa uku ta tsayah tana maida numfashi sama sama.
Duk da rigar wuyanta nada ɗan sama,amma kasantuwar tsallan data sha nakusan awa guda,yasa wuyan rigatata yin kasa,da yanda mutum na iya kallon saman fararen albarkatun ƙirjinta.
Jan rigar tata tayi tagyara,har sannan bata daina fidda nimfashi ba sama sama.
Nufar wajenda ta ajiye kayanta tayi tareda ɗaukar gorar ruwa takafa a bakinta.
Da yawa tasha ruwan kafin tasaki ajiyar zuciya nauyayya..
Shuru ta ɗanyi kaɗan jin wani motsi yana nufo inda take,idonta ta buɗe a wajen da kunnenta yajiyo mata motsin..
Kasantuwar girman tafara suma idanuwannata sun samu damar ƙara yin dara dara farare tass,ƙwayar idonta kuma yanzu tasake yin wani shuɗi mai sheƙi sosai,Motsi shuɗin cikin idon yake yi,daga ƙarami yakoma babba daga babba yakoma ƙarami,sakamakon daidaita hasken ranar dayake haskawa zuwa cikinsa,wanda ganyen bishiya yake mata inuwa kuma yana karkaɗawa.
Dan shi kansa ganinta saidayi training sosai akai,yanda zata saita kallonta da rana da kuma dare.
Motsin datake jine yafara yawa kana kuma yana matsowa kusada ita..
Cikin zafin nama ta cafki kwari da bakarta tareda saita wajen da idonta ya tsaya akai.
Sauke kwari dabakar tayi tana kallon wani ɗan matashin yaro dabazai wuce shekarunta ba wato sha biyar.
Ɗaga hannu yayi sama alamar yayi sarranda lokacin data nunashi da kwarinnata,sai kuma yayi murmushi tareda jingina a jikin bishiyar da take kusada shi.
"Waye kai?"
Bombee tafaɗa cikin tsare fuska,alamar babu wasa a gameda tambayar datayi masa.
Takowa yafarayi a hankali har zuwa kusada itah,kana yasaka hannunsa yana shafa jikin kibau ɗim dake kan kwarin.
Har zuwa lokacin murmushin dayake kan fuskarsa bai bace ba.
"Shin zaki ajiye kwarin idan nace ni aljani ne?"
"Bana san shashanci ka faɗamin kai waye,ko kuma duk abinda nayi maka karka ga laifina akai"
"Ba shanshanci bane nima tambaya nayi miki,amma karki ɗau da zafi,sunana Aliyu,amma ana ƙirana da haidar,ina so muyi abota ne dake,shin zaki yarda dahakan"
Sake daure fuska Bombee tayi jin maganar wanda yakira da kansa haidar ɗin ya bafaɗa.
Harara ta gallamasa tareda sauƙe kwarinta tayi wajen da ta ajiye kayanta.
Ɗauka tayi ta saƙala a kafaɗarta tareda yin hanyar inda zata fitar da ita daga cikin dajin.
Binta yake a baya yana magana,amma ko waiwayowa batayi ba ballanta na ta kulashi.
Hakanne yasa ya dakata da binta,tareda yin dariyar gefen baki,shareshin datayi karon farko na haduwar ta dashi sai yaji ya burgeshi.
Tun sati daya dayayi yana yimata la'be yana ganin mai takeyi dama yayi tunanin hakan daga gareta.
Tunda yake bai taba haɗuwa da macen data burgeshi kamarta,ta yarda da kanta,sanann kuma bata kunyar nuna jarumtarta,duk da kasancewarta kuwa ƴa mace.
"Zamu sake haɗuwa Bombee dole sai na miki abinda zaki kulani"
Daga haka ya juya yayi wata hanyar daban yana jijjiga kai.
Itama Bombee a nata bangaren mamakin yaron data hadu dashi take,shin anya kuwa mutum ne,bata taba haɗuwa da wanda yakalleta batareda tsoron halittarta ba sai yau,idan tacire goje wanda shi bata sakashi cikin jerin mutane.
In mutum ne mai yakeyi a cikin jeji.....kai itama ai mutumce kuma take zuwa jejin,mutum ne ma dam bataji wani yarr a jikinta ba,irin wanda take ji idan mai aljanu ko kuma wajen da aljanu suka wulga ba.
Yanda taga shigar kayansa da kuma yanayinta,su kansu basuyi mata kamada irin na mutanen yankin su ba.
"Haiiidarrr???,koma waye kai bai shafeni ba,inka shiga gona ta ba raga maka zanyi ba"
Tafaɗa cikin ƙwarin gwiwa(confidence).
Gidan inno ta nufah,saida taci abinci tayi sallahr azahar kafin ta nufi gidansu.
Ko salama batayiba ta shiga gidan,babu kowa a tsakar gidan,dan haka ɗakinsu ta wuce kai tsaye.
Innayi ce a kwance kan gadonta ta tsuga mata sayi na baccin rana,dan dama ita tana fitsarin kwance.
Kallonta take tareda kama kunkumi tana kallon innayin,babu abinda yake tasomata a zuciya sai takaici.
Gashi dama babu wuyah sai ranta yabaci,ita kanta tana mamakin yanda koyaushe sanzawa take daga yanda take a baya.
Wani lokacin bata ganin laifin mutane idan suna aibatata,dan tasan tanayi musu abin muzgunawar ba bayanda zasuyi,saidia itama babu yanda zatayi,in anyi mata laifin daya bata ramaba ji take kaman zatayi hauka,muryar datake zugata a cikin kanta bazata taba barta tayi bacci cikin salama ba.
Dawo da tunanin ta tayi kan innayi wacce take jagab cikin fitsarin datayi mata kan gado.
"Yau zakici bantan innarki laari a gidannan innayi,dama ina taraki da gulamar dakikeyimin a cikin gari,shegiyar yarinya kai"
Takarisa magana tareda ficewa daga ɗakin tana cijan baki.
Fitowar inna laari daga ɗakinta taga wucewar Bombee cikin ɗakinsu ta bulali a hannunta dogaye guda biyu tana yimusu tuka.
Zaro ido tayi dan tafi kowa sanin mai Bombee zatayi dasu.
"Keeee Bombee wazaki daka da wannan bulalin haka?"
"Ki zuba ido kiga wa zan daka dasu mana,miye kike wani gaggawa"
Ta ƙarisa maganar tana watsawa inna laarin harara.
Tana shigewa ɗakin ta rufo ƙofar kirif,ko minti biyu ba'ayiba ƙarar dukan bulala ya jiyarci kunnenta,da kuma kukan ƴar tata wacce take har ƙasan maƙoshinta.
"Wayyo ku ceceni zata kasheni wayyo,innata innata ki taimakeni innaaaa"
Ganin inna laari bazata jure ihun ƴar tata ba yasa ta nufi ɗakin Daneji wacce itama take bacci,ga kwanannnan laulayin ciki take mai wahala,har ya yi wata biyar amma wahalar sa taƙi barinta ta huta.
"Daneji bakyajin Bombee ne zata kashe ƴar uwarta a ɗaki"
Zabura Daneji tayi ta tashi dakyar tareda nufar ɗakin su Bombee,wacce bakajin komai sai ƙarar bulalin dakuma ihun innayi wanda yafara dushewa.
"Ke Bombee ki buɗe ɗakinnan nagayamiki,wai meyake damunki nene kam a gidannan,anya kuwa kanki daya,ki bude dakinnan kafin raina ya baci inagaya miki"
Buɗe ƙofar tayi tana huci kaman sunyi dambe da bijimi,kanta a ƙasa bata bari sun hada ido da Daneji ba,wacce in kallo yana huda mutum daya hudata a lokacin.
"Mai tayi miki kika mata wannan mummunan dukan?"
"Fitsari tayimin akan gado,bayan tasan na hanata hawa min gado"
"Yanxu dan kawai rayi miki wannan lafin shine kika yi mata duka haka,"
"Faɗamata dai,anyi mata aure ta kasheshi da baƙin halinta,ta dawo gida ita ba auruwa zatayi ba tana musgunawa ƴan gidan.akan fitsari shine zakiyimata wannan dukan dan baƙin hali,nasan ma ba iya akan fitsari bane akwai wani mugun nufinki dai daban"
"Ehh akwai mungun nufin,tunda take zuwa tana munafurcina ko kuma takemin raini kin taba hanata ne,shine danna ɗau mataki za'a ga laifina,in kinji haushi ki rama mata mana,kiga in ban kasheta a gidannan ba muss har lahira kum.........."
Fasss bata gama kaiwa ayah a maganar tata ba taji Daneji ta wanketa da wani zazzafan mari a kumatunta,kafin ta juyo tasake daɗa mata a ɗayah kuncin.
Idonta har kanƙancewa yakeyi jikinta yana rawa saboda bacin rai,nuna Bombee tayi da yatsa tareda cewa.
"Bombee........yanzu har kinyi girman da a gidannan zaki buɗi baki ki faɗawa addah laari haka,ehh lallai yau na tabbatar da baka haihuwar ɗa kuma ka haifi halinsa,kin nuna min iyakata tabbas,kuma naji daɗi da nunamin wanann halin da kikayi kinji"
Kecewa da kuka inna laari tayi jin abinda Bombee tafaɗa mata akan idonta,wanda suna cikin hakanne mlm Ahmadu shima ya shigo gidan.
Tambayar mai yake faruwa yayi,amma babu wanda ya tanka masa,ita Daneji tana faman yiwa Bombee faɗa,yayinda ita kuma inna laari take aikin share hawayen idonta da gefen zaninta,itakuwa wacce tafi dakuwa kukanta yafi na kowa yawa a gidan.
Larai kuma taga kan katanga tana sallallamin jin abinda Bombee tayi ɗin,dan tun ihun innayi na biyu take kan katangar.
Shi mlm Ahmadu dayake ta faman tambayar mai yake faruwa,bai samu sanin hakan ba daga wajen su,sai a wajen inna larai wacce take kan katanga tana kwararo masa bayani kaman recorder.
Tun kafin tagama faɗamasa mai yake faruwa ya zari igiyar awakai dake gefensa ya hau Bombee da duka,wacce take tsaye ƙinkam yana dukannta.
Tun yana dukannata da igiyar har saida ta yayyage ta baje a hannunsa,amma Bombee tana tsaye ta rufe idonta,sai ya zabga mata bulalar taɗan runtse ido kaɗan.
Shatu ce itama dake kan katangar tasamu damar faɗin
"Yanzu Bombee bazaki gudu ba irin wannan duka da ake miki"
Bayan ita babu wanda yayi magana,kowa baki ya buɗe yana kallon Bombee,yayinda shikuma mlm Ahmadu duk bayan duka ɗayah sai zuciyarsa ta ƙara tafasa.
Jefar da igiyar yayi yasake tsinkar tashanyar su ya cigaba da dukan Bombee da ita.
Wanda ita kuma a nata bangaren ba dukanne yake wahalar da ita ba,illah ƙoƙarin datake wajen cin galaba akan muryar datake yimata amo a cikin kanta.
Ba abinda take umartarta dashi illah tarama dukan da mahaifinta yake yi mata a lokacin,wanda har abada bata fatan taga hannuwanta sun aikata hakan.
Salatin dataji su inna laari sunayine yasakata buɗe idanuwanta da sauri,ba komai ta hanga ba sai mahaifinta kwance a ƙasa yana dafe da zuciyarsa,wanda tasan ko tantama bazatayi ba ta sanadiyyartane hakan ta faru.
Abin haushin kuma duk yadda taso ƙwakwalwarta tasaka zuciyarta jin haushinta abin ya faskara,saima haushin mahaifinnata daya turnuƙeta.
Tsugunnawa tayi a hankali zatakai hannunta kansa,caraff taji an rike mata hannu.
"Karki kuskura ki taba shi,wlh bakida wannan damar,ki bacemin daga gani yanzunnan"
Daneji ce tayi maganar wacce idonta yayi jajur ta tsanar halin Bombeen.


Ohhhh nagaji......i hope dai yana sugar littafin koh????




_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼



____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤28🖤







Miƙewa tayi gwiwa a sabule jin abinda innar tata tafaɗa.
Hanyar waje tafita kanta a sunkuye,tana jiyo maganar mutane a bakin kofar gidan,wanda tuk yawancin maganar ta ne da abin tirrr da Allah wadai datayi.
Sauri take tayi nesa da maganganun,dan ba komai suke kara mata ba sai dake daskarar mata da zuciya,maimakon suyi tasiri wajen saka zuciyar laushi.
Sai dare yaraba tukunna tashigo gidannasu,sassafe kuwa kafin kowa yatashi ta fice a gidan.
A gari taji labarin an kai mahaifinta asibiti jininsa ya hau,saidai ba'a bashi gado ba gida suka dawo,tunda bayyi tsanani sosai ba.
Amma tunda suka dawo da la'asar har yanzu bai sake magana ba.
Runtse ido tayi lokacin da labarin ya riski kunnenta,babu makawa tasan itace silar hakan.
Saurin kawar da fuskar tausayin datake ciki tayi,tareda jan numfashi dogo kana ta furzarshi.
Kai tsaye cikin daji ta nufa ta mungun gudu,wanda kowa yakalli hakan yasan da gangan takeyi saboda ta gajiyar da jikinta,aikuwa abinda take nema ta samu,dan daƙyar da ƙarisa filin yin gwajinnata tana maida numfashi.
Idonta ne yasauƙa akan haidar wanda yake zaune akan reshen bishiya yana jin tuffah(Apple)a hannunsa.
"Wow irin wannan gudu haka kaman barewa,daga nesa fah nakejin ƙarar gudunki,anya kuwa ke mutumce,karfah nace da aljana nakeson yin abota"
Tubbbb ta tofar da wayu tareda watsa masa harara tace.
"Wai miye hadina dakaine,sannan da izinin wa kakeson shiga gonata?"
"Gona kuma,bakiyi shuka a wajen ba fah,in ma akwai ni bangani ba gaskiya"
Yakarisa maganar yana duban wajen a cikin fuskar zolaya.
Zaro ido yayi tareda matsar da kansa gefe guda,cattt kuwa ƙaramar wuƙar ta caku a jikin bishyar dayake kai.
Kafin ya dawo hayyacinsa sai ganinta yayi akan reshen a gefensa,fuskakokinsu suna tabb dana juna,ta zuba masa wannan fitinannun idanuwannata masu launin shuɗi a cikin nasa.
"Kutt kasheni zakiyi,sannan kuma yaushe kikazo wajennan iyeee?"
"Ba wannan na tambayeka ba,meyasa kakeson shiga rayuwata,wani ne ya aikoka? Sannan mai kake so dakake bibiyata,na daɗe ina kulada kai a wajennan tsawon sati guda,da farko banyi zaton nikake bibiya ba,sai daga baya na kulada hakan,waye kaiiiii?"
Tafaɗa cikin tsawa tareda dasa masa wuka a kan wuyansa.
"Habaaaa Bombee mai yayi zafi shiba wuta bane,babu abinda nake binki dashi,jarumtarki da kuma yanayinki ne kawai yake birgen,shiyasa nakeson ƙulla abota dake,bayan hakan kuma dama banga kowa a cikin wajenba wanda zanje wajensa"
"Daga ina kake?"
"Kaman yanda na faɗamiki sunana Aliyu,ni ɗan gidan General Muhammad Bello ne. An kawoshi nannne saboda wani case ɗin manyan yan fashi dayake wakana"
Gidanmu nacan ɗayar hanyar ba wacce kikebi idan zaki je gidan maharbinna ba."
Sauƙowa tayi daga kan bishiyar ta soke wuƙar a kumkumin ta inda tacireta.
"Kaine mutum na farko daya tunkareni da niyyar abota batareda wani dalili ba,kodayake yanada nasaba da cewar baka sanni ba"
"Menene yasa baza'ayi abota dake ba,you are very "interested lady"
"Wanne yarene haka kayi magana dashi,uhm kaman yana kama da wanda malamai da copper ko kuma masu bibiyar wannan jejin suke magana dashi"
"Kutt bakisan turanci ba kina nigeria"
"Nasanshi yanda kayine yamin kama da ba irin na sauran ba"
"Hhhh inaga saboda ba a ƙasar nan nake zaune bane,nazo hutune na shekara guda shiyasa na biyoshi nan domin naga ya wajen yake. Baki amsamin tambaya ta ba,meyasa suke tsoronki"
"Kai baka gani ba,a ganina dai kaiba makaho bane,suna ganin kaman ni ba mutum bace saboda idanuwana"
Dariyah Haidar ya sheqe da ita,wanda hakan yasa Bombee binsa da kallon kaman yasamu tabin hankali.
"Wani blue iris ɗinki,da farko nayi mamaki kam sosai,amma kuma nida na zauna a ingland naga masu irin idonki da yawa,hmmm saidai gaskiya nasu baya shining kaman naki,amma duk wanda yagani yasan ai normal ne,akwai masu abubuwa rare da dama a duniyah"
zaro ido Bombee tayi jin daya faɗa mata cewar akwai masu irin halittarta a cikin duniyar nan a wani wajen nesa da ita,lokaci guda sai kwaɗayin da haɗu dasu yafara shiga cikin ranta.
Tambayoyi Bombee take yimasa yana bata amsa,wani yayi mata dariyah wani kuma kawai yabata amsa.
Lokaci ɗaya sai tasamu kanta da sakewa dashi batareda ta sani ba.
Shikuma ganin tasake tana maganar arziki dashi,hakan ba ƙaramin dadi yayi masa ba haɗeda dauke kewa.
Basu ankaraba suna ta surutu sai gani sukayi rana tayi sosai.
Tashi Haidar tayi taga bakin ruwan dayake zaune ya kalli Bombee.
"Nikam barina tafi,sai anjima zan dawo,daganan zaki fara koyamun wasannan dakike da sanda"
Dariyah tayi tareda cewa.
"Lallai kuwa wasa,abinda nake yayi maka kama da wasa koh?"
"Komai dai menene nina tafi"
Ya juyah zai tafi saikuma taga ya tsaya,kasancewar ruwan take kallah batasan mai ya gani ba.
Muryar da bazata taba mantawa ba taji ya daki dodon kunnenta.
"Heheehhe iyeeee kice kin samu duniya kam,tunda har ɗan matashin saurayi kikayi bansani ba,da izinin wa kike gara rayuwarki haka"
"Da izinina mana,da dana wa zanyi,sannan menene ya kawoka inda nake?"
"Saboda na kwashi romon da bankai ga shaba kika katseni"
Ƴar dariya Bombee tayi tana kallon goje wanda yake tsaye tareda maza gudan huɗu ,bibbiyu a kowanne gefe.
"Ta yaya marar ƙafa zai hau tsani(bladder)? Uhm"
"Idan an hau masa ai ya wadatar,koda shi baxai iya hawa ba,a tunaninki dan bazan iya farmakarki ba shikenan zan bar abinda kikayimin ya tafi a banza ne,yau babu mai ƙwatarki a hannuna,saina maidake abun tausayi,abinda zanyi miki sai ya kafa tarihi a garinnan,dan ba'a taba yiwa wani mahaluƙi irinsa ba"
Yana maganar gashin bakinsa yana ɗagawa,sannan yana haɗawa da dariyar mugunta. Tashi Bombee tayi daga inda take tareda kallon Haidar.
"Haidar kabar wajennan yanzunnan kar abinda zai faru yashafeka,karka damu bazan bari su bika ba,kabi ta bayana ka gudu"
"Ke kuma fah,kina ganin zaki iya da wannan mutanen,su waye su ɗin,sannan me suke nema a wajenki"
"Karka damu dani,zancen suwayd kuma bazan samu damar baka bayani akai ba yanzu,amma idan na rayu ko mun sake haɗuwa za faɗamaka"
Tana gama maganar ta turashi ta bayanta tareda yimasa kallon umarnin dole ya bar wajen.
Yana tafiyah kuwa taji muryar goje yana cewa
"Iyeee kice dagaske ashe kina sonsa tunda har kareshi kike,karki damu babu abinda zanyi masa,zaifi ciwo ma idan yaga masoyiyarsa anyi mata fata fata,zan in yanada wayo shin zai ƙara sonki? Ku lahanta min ita tukunna mazaje"
Yafaɗa cikin

Please Login or Register in order to submit comment