Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewar bayason ɗaukar darenne tukunna.
Ɗakin mlm Ahmadu dake zauren Daneji ta rakata,babu kowa a ɗakin daga mlm Ahmadu sai inna laari,saikuma Daneji ta itama ta zauna a ɗaya gefen mlm Ahmadun.
Ita kuma uwar gayyar tana tsugunne a gabansu an rufa mata farin mayani akanta.
"Toh bismillahi da Sunan Allah......Maryama kamar yaune aka haifeki na riƙeki akan tafukan hannuna ina murna da zuwanki duniyah,bayan tsawon lokaci dana fidda rai da rabon ganin jinina a duniyah. Yau kuma gashi na ɗaura miki aure zaki tafi kema gidan mijinki inda zakiyi taki rayuwar.
Nasihar dazanmiki shine,kizama mai haƙuri da kuma biyyah sannan da juriyah,sauran halaye kuma idan ke mai yawo ce nasan kingama ɗaukar su daga wajen innarki a yau da kullum.
Duk da bakan abokiyar zama za'a kaiki ba,amma ina shawartarki da ki kwantar da hankalin ki idan wata taxo ta sameki cikin gidanki,kiyi koyi dasu innarki anan gida,yanda suka haɗe kai suke zaune ƙalau.
In bada ƙwaƙwƙwaran dalili ba banyadda naga ƙafarki cikin gidannan ba dasunan kinkawo kara ko kuma kinyi rigima,sannan karki yarda yakawomin kararki nan. Idan hakan yafaru bazan hanaki zaman gidannan ba a matsayin ki na mace,amma zan fita lamarinki bani bake,dan haka kizauna lafiya da mijinki da kuma ƴan uwansa.
Wannan shine iya abinda zan faɗamiki a matsayina na mahaifi"
Bayan yagama yimata jawabin,itama inna laari tayi mata nata na jan hankali,inda ita harta kara dsyimata bayanin haƙƙin miji dake kanta..
Duk abinda suke faɗa Bombee tana zaune gungurun,bata motsa ba sannan kuma batace uffan ba har suka gama.
Inna laari kam itada Daneji harda ƴar ƙwallarsu,da alama sun tuna sanda suka bar nasu gidan,amma ita wannan mai tafiya yanzu ma,tana zaune kaman dutsi,duk maganar da akayi mata babu wacce tashigeta kaman an tsikari kakkausa.
Inna laari ta tashi ta kama hannunta suka fita,dan dama itace mai rakata ɗakin itada Inna Hadiza.
Babu laifi kofar tata an gyara to sosai,dan ginin bulon siminti ma yayi mata,gashi an ja ƙofar an kewayeta daga cikin gidan.
Kayama mlm Ahmadu yayi mata masu kyau an saka mata,kowa sai yaba kyan ƙofar yake da yanda tasha kaya.
Ɗakine guda ɗaya sai kicin da gefe da kuma banɗaki,saidai ɗakin babbane sosai,dan yacinye dukka kayan harda sauran fili.
A kan kadonnata aka zaunar da itah,wannan aikin inna laari ne,ita ta matsa dole saida aka yimata jere kafin akaita,kuma hakan yakawomsu sauƙi,dan babu wani sake yin jere washegari.
"Toh Bombee ga ɗakinki mun kawoki,mu yanxu zamu tafi,dan mlm yace karmu makwana komin dare mu koma gida. Dan Allah kiyi amfani da abinda aka faɗamiki jiya kinji?"
Shuru Bombee tayi bata kulata ba,saima wangale mayafin da aka nannaɗeta dashi take ƙoƙarin yi.
Da Sakeena suka haɗa ido ƴar gidan Shatu wacce take kusan sa'ar Bombee ce,da kaɗan Bombee tafita dama. Ita kadaice wani lokacin suke maganar arziƙi da Bombee,shima dan tanada shuru shuru ne bata biyeta,hakan ma ba koyaushe take kulata ba,saidai idan tayi wani abun ta tambayeta itakuma da bata amsa.
"Hmm kinajin tanayi miki magana kikayi banza da ita Bombee?"
"Sau nawa zan faɗamiki cewar matar nan batayimin ba,haka nakejin bana sonta a raina yanxu"
"Dama wakikeso tunda kika zama haka bada kanki,ni barikiga na tafi,saina zo miki"
"Dama yanzu zan koreki in baki tafi bama,kinsan ba abinda na tsana kaman wannan wa'azin,inkikace zaki dameni to zan daina kulaki"
"Hmm nina tafi kafin ki huce akaina saikin ganni"
"Hhhhhh wani saikin ganni,saikun ganni dai,nufinku shikenan daga nan na tsayah daga farawa,mai ma nayi toh"
"Bombeeeee!!!! Kinji fah mai Babanku yace idan kikayi wani abun?"
"Ina ubana kikace ba ubanki ba uwar iyayi"
Gum sakeena tayi da bakinta tareda barin ɗakin tabi yan rakiyar amaryah.
Tana ganin sun tafi babu kowa tasake ajiyar zuciya tareda kwantawa akan gadon.
Baje ƙafafunta tayi,ita kaɗai ta saka dariyah kaman mahaukaciyah sabon kamu.
A haka bata saniba har bacci yayi awon gaba da ita.....



_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼



____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤24🖤




Bugun ƙofar da ake ne yafarkar da ita daga baccin gajiyar daya ɗauketa.
A hankali take buɗe idonta har ta waresu akan rufin ɗakin,wanda aka haɗa da zare da kuma jarida.
Tashi tayi ta zauna a tsakiyar gafon tareda yin wata kyakykyawar hamma,kaman wanda ta shekara bataci komai ba.
Kallon gabas da yamma kudu da arewa tayiwa ɗakin,ta tabbatar dai ita kadaice ta kwana a ɗakin kenan,angonnata bai shigoba da alama,to mai yahanashi zuwa ta faɗa a ranta,ganin hakan zai bata mata lokacin yasa ta bar ma zancen.
Sake bugun ƙofar akayi a karo na ba adadi,sai sannan ma ta tuna da abinda ya tasheta.
Cikin kasalalliyar tafiyah ta nufi ƙofar tareda buɗewa.
Da indo suka haɗa ido tana rike da kwano a hannunta,saida tayi mata kallon sheƙeƙe kaman bata girmeta ba kafin ta ce.
"Menene kike ta bugun ƙofah kaman naci muku bashi,dama ake yiwa baƙo ne?"
Kallon ta indo tayi na ƴan sakanni kafin ta ajiyemata kwanon ta tafi,danta kula neman magana ne a gun amaryar yayannata,dan tun ranar datayi tujarar nan tasan an kawo musu wata alaƙaƙai ɗin,gwanda ma tayi aurenta ta tafi ta huta,banda mutuwar da mijinta yayi na farko ma da bazata ganta ba bare tayi mata.
Sai bayan taga ƙulewar indo tukunna ta tsugunna ta ɗauki kwanon tareda buɗewa.
Doyace da ƙwai aka soyata sai ƙyalli take,haɗiyar yawu Bombee tayi kafin tace.
"Hhhhh nasan ba wannan abincin suke ci ba ni akayiwa saboda ina baƙuwa,hmmm kar nake ma ko sunsaka guba a ciki fah....kai yaushe zasu saka guda hauka ma suke.
Kai koma menene ciki aradu sainaci,inabanci ba gaba ba samu zanyi ba,kuttt sai yanzu ma na tuna,ance ana kaiwa amaryah kaza in ankawota,dan tsabar iskanci shine suka kawomin iyah doyahhhh wlh sun rainani"
Ai tana gama faɗin haka ta rufe kwanon tareda yin cikin gidan,dan sauri kaman zata tashi sama.
Jauro shida iyalinsa suna karyawa kawai sai ganin Bombee sukayi a kansu rike da kwanon da indo takaimata yanzu.
Suma abinda aka kaimata suke ci,da alama ƙwan irin na kajin gidanne ta ci karo dasu sunata yawo.
Jauro ne yaɗaga kai dan tana kusada shi yace,
"Yarinyah lafiyah koba kya cin doyar ne a samo miki wani abun"
"Da ansan da wani abun aka kawomin doyar,ni nayi zaton nikadai ma akayiwa ashe hardakuma ita kukeci.......kowacce amarya ina ance kaza ake bata idan an kawota sai taci ta ture,shine ni za'a kawomin iya doyah dan an rainan"
"Tohh yarinya wannan fah abincin karyawa ne,kaza kam ina mijinki yakai miki jiya da daddare koh?"
"Jiya yaushe aka kaimin wata kaza,an kaimin zanyi karyane,ni banga wata halitta ba a ɗakin nan bayanni,bare kuma wani abu waishi miji"
Jauro yanajin abinda Bombee tafaɗa yajuya ya kalli Inna daayi da Alamar tambaya.
"Kee daayi yarinyar nan dagaske take goje bai dawo gida ba jiya?"
"Eh....eh to mlm ni banganshi ba nima bai faɗamin inda yaje ba"
"Yanzu a ɗaura masa aure jiya a kawo matar amma kuma yazagaya yayi tafiyarsa,saboda ya maidamu ƙananan mutane kon"
Saida yagama faɗansa Bombee tana tsaye kam batada alamar tafiyah,juyowa yayi ya kalleta tareda cewa.
"Kinga kiyi hakuri yanzun kije kici wannan ,in yaso yanzu zansa Indo ta dafamiki kazar akawo miki,karki damu zan yi masa faɗa kinji,kuma don Allah kar iyayenki su san wannan maganar"
Lallaba Bombee jauro yafarayi,saidai ita duk maganar dayayi bata dameta ba,abinda yafaɗa wanda tagane shine dayace za'a daho mata sai taci ta ture,shine abinda yasakata tafiyah tabasu waje.
Ruwa ta kandama a randar inna daayi tayi wankanta da safe,da ɗauko sabon kaya daga cikin kayan da akayi mata saka.
Doguwar rigace sai mayafinta data ɗora a kanta,takalmi ma sabo da tasaka,daga nan tafito zata fita wani wajen.
Indo ce taga zata fita,da gudu taje da faɗawa inna daayi abinda yake faruwa.
"Inna ga can Bombee fah zata fita waje"
Zaro ido inna daayi tayi tareda saurin fitowa daga ɗakin.
Hanyar wajen ta nufa daidai lokacin da Bombee take shirin fita.
"Ke mekikeyi haka, zaki fita daga kawoki jiyah,anya kuwa baki samu tabun kai ba wannan?"
"Hhhh tabun kai,ai kannawa ma inaga a rushe yake ba tabun kai ba,miye laifi a ciki dan an kawoni gidan jiya zan fita yau,kuɗin wani naci daza'a tuhumeni,ko kuma da wanda nace yaraka ni wani wajene?.
Kinga dan Allah kina bata min lokaci,ina da wani abu dazanyi ne ba zan daɗe ba,inkin dafamin kazar a jiyemin a ɗakina"
"Huh to in daga gidanku aka kawo kazar saikisaka a dafamiki ai,ƴar rainin wayo kawai"
Indo ce tafaɗa cikin hassala,dan taga abin Bombee yawuce a zuba mata ido,tunda take bata taba ganin wacce aka kawota gidan miji jiya da daddare ba,kuma da safe tashirya ta fice,abin ai ko hankali ma bazai dauka ba.
"Badaga gidanmu aka kawo ba,amma tunda ubanki yace a dafa sai an dafa,wlh idan nadawo ba'a dafamin ba,duk saina kashe kajin gidannan a yau basai gobe ba,in kuna tantama ku gwadani dan Allah"
Cikin gadara take maganar tana nuna garken kajin dasuke wani fili a cikin gidan.
Haka ta fita tabarsu basuda ko bakin magana.
Tunda tafita da safe ba ita tadawo ba sai bayan la'asar. Kofar ta tawuce kai tsaye bata ko shiga cikin gidan ba.
Da kwano taci karo a bakin ƙofar ɗakinnata,tana buɗewa kuwa taga farfesun kaji ne guda biyu manya,wani murmushin jin dadi tayi tareda cewa a ranta.
Ashe kuna son kajinnaku da alama,da karku yimana ku gani,banda shiga shirgin mutum ina ruwanku da fitata,ko baban bai isa hanani fitaba ballanta ku.
Zama tayi baje baje taci tayi nakk ta kora da ruwa,kafin ta tuntsire a wajen sai bacci,da alama dama a gajiye ta shigo gidan.
Lokacin data buɗe idanuwanta duhu ya fara,rana tana shirin faɗuwa,tashi tayi ta cire kayan jikinta tareda sake yin wani wankan kafin magriba tayi.
Ana sallahr magriba taji muryar wani gardin a tsakar gida,kana jin maganar kaji irinta tantirannan wanda suke yinta a shashshaƙe cikin isa da gadara.
"Huh inna kenan me kike so kicemin ita harta ta isa ma tafice batareda izinina ba,menene take taƙama dashi dan babarta a garinnan,hmmm zakuwa ta yabawa ayah zakinta,ki barni da ita,zanyi maganinta,zatayi laushi ta yanda sai abinda naga dama zata aikata"
"Yawwa goje nasan bazaka bani kunyah ba,so nake kamaida ta komai na gidan nan ita zatayi shi,badai tana ji da yarinta ba.
Yawwa wai ina ka tafine? Ran mlm ya baci sosai da fitar ka jiya.
Bai kamata ace a kawomaka amaryah jiya baka nan ba"
"Kinga inna wai miyene za'a takuramin dan kawai nayi aure,nine fah nace zanyi aurennan ba wani ne yasaka ni ba,dan haka abinda naga dama zanyi.
Sannan naji kina wani zancen zata dunga yi muku aiki,kar na sake jin wannan zancen,nina kawota gidannan,nikaɗai nake da ikon sakata aiki ba wani ba. Tana ina tadawo ko kuma har yanzu tana waje?"
"Bamu sani ba,da babu wanda yaga shigowarta"
Bagazam bagazam yayi hanyar ƙofar tasu kaman zai tashi sama.
Duk abinda suke Bombee tana jinsu,wani murmushin gefen baki tayi tareda cize baki jin furucin mijinnata. Tana nan tsaye a baranda kuwa ya shigo ƙofar yana muzurai.
"Oh kin dawo ma kenan,nasan duk abinda nake faɗa kina jina,ina so kifaɗamin gidan uban wa kikaje dazu,sannan kuma da izinin wa kika fita?"
Shuru yayi domin bata damar amsa tambayarsa,amma har tsawon minti biyar Bombee bata ce komai,saima juyawa datayi tashige ɗakin.
Hakan datayine yaƙara ƙular da goje,dan dama a sama yake ya bankami angurrr.
"Ke ina miki magana kika yimin banza,da uban me kike taƙama".
Nan ma batace masa komai,hakanne yasa cikin bazata ya sauƙe mata mari a kuncinta na hagun.
Dafa wajen tayi da hannunta na daman,tareda saka manyan idanuwan ta a cikin jajayen nasa idon.
Ko ba'a faɗaba duk wanda ya kalli idon nata a bayyane zai hango tarin baƙin cikin dayake ciki.
Rintse ido tayi tareda haɗiyewa abinda yake shirin taso mata,matsawa tayi daga gabansa takoma bakin gadon ta zauna tana kallon wani wajen daban.
Har sannan bata buɗe bakinta ba ballantana wani harafin yasamu damar fita.
Takowa inda take yasake yi tareda shafar gefen fuskarta,sannan kuma yafara magana cikin sanyin muryah mai cikeda yaudara dakuma son cikar muradi.
"Ohh kiyi hakuri fah,kece kika batamin rai sannan kika kaini bango,amma idan ba haka ba mai zai sa nakai hannuna kan wannan lallausar fuskarta ki da niyyar cutarwa.
Saidai karki damu,indai zaki kasance mai biyayya hakan bazai sake faruwa ba,idan san ladabtaki ma ta hanyar jin daɗi,nasan zaki so hakan koh??,har yanzu ban huce da fitar dakikayi ba,saboda bansan wajen wa kikaje ba,saidai zan hukunta ki fa hanyar samunki akan shimfiɗina.
Banajin zan iya binki ta hanyar sauƙi,duk da kuwa kedin sabon hannunce,dan daga ganinki zakiyi daɗi sosai,dannasan baƙaramin shirya min ke akayi ba"
Yana maganar yana matsowa inda take,har saida yazamo ya zauna a bayan ta yana shafa bayan ta.
Saƙalo da hannunsa yayi zuwa cikinta,a hankali yaɗaga rigar ya zura hannunsa yana shafa fatar cikinta.
Saurin buge hannunsa Bombee tayi tareda tashi ta tsayah tana kallonsa,jin yana mika hannunsa sama zuwa ga albarkatun jikinta.
Sai a sannan Bombee take ƙaremasa kallo saboda hasken da fitilar ɗakin tabayar ta batir.
Farine tass yana da gashin baki,sannan kuma yana ɗan jiki sosai,musamman ma tasaman ƙirjinsa,kana ganinsa kasan ƙaƙƙarfane sosai,kuma babu alamar mutunci a tattare dashi.
Murtuƙe fuska yayi ganin yanda Bombee ta buge hannunsa lokacin dayake tabb ta kaiwa ga muradin ransa.
Tashi yayi yafara takawa zuwa inada take,yana nufarta tana matsawa harsaida yakaita bangon ɗakin.
Kallon idonsa takeyi wanda suka fara ƙaduwa ganin yanda Bombee take sauke numfashi kirjinta yana ɗaga tacikin rigar dake jikinta.
Bata ankara ba sai gani tayi ya sutale dogon wandon dage jikinsa,zaro ido tayi kaman zasu faɗo ganin abinda tayi arba dashi.





_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼



____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤25🖤






Sauƙe ajiyar zuciya tayi ganin ashe akwai ƙaramin wando a cikin dogon daya cire,saidai kuma an gudu ba'a tsira ba,gani tayi wandonnasa yana ɗagawa kaman wani abune yake motsi a cikinsa.
Dariyah ya kece dai ta ganin inda idonnata ya sauƙa,wato kan hajiyar sa.
"Hhhh ƙwaila kenan,tun ba akai ga komai ba harkin fara karayah,ima tsiwar taki da aka bani labari toh,ki shiryah yanzu zanyi miki abinda nake wa sauran ƴaƴa wanda kike ji da kunnenki a gari.
Naji dama ance kinzo gidannan neman sanin wayeni koh,to inaga bakya bukatar sanin mai zai faru.
Yanzu nan zan aikata miki abinda nake aikata wa,saidai ke ta hanyar au............"
Bata bari ya ƙarisa faɗin abinda yake shirin amayarwa ba tazage iya karfinta ta cankeshi a gabannasa,bayan ta tabbatar yagama sake lagonsa.
Giff ya rufe bakinsa baikai ga karisa maganar dayake mata ba,lokaci ɗayah abubuwa dayawa suka shiga kwakwalwarsa,Azaba,razana da kuma yanda abin yazo masa a bazata.
Kafin yayi wani yunƙuri ya sheme a kasa warwars ko motsi bai sakeyi ba na kirki. Babbar alama ta nuna baƙaramin lahani Bombee tayi masa ba,sanadiyyar dukan data kai masa.
"Yanzu sai naga wane abun zakayi mana abinda kake iƙirarin aikatawa ai,da tunaninka tun farko tsoronka nake,hmmm da alama baka je ka tambayi wacece ni ba,bayan ni nasan waye kai"
Tsugunnawa tayi wajen saitin fuskarsa ta wanke shi da mari tasss.
"Marina dakayi na rama,ina ka mutu ma bana binka bashi,dan hakan sai ya dameni,idan na tuna ka mareni ka mutu ban rama ba"
Mayafinta ta ɗauka yafa kafin ta dauki duk abinda tasan tana buƙata ta tsallakeshi ta bar dakin.
Batareda kowa yaganta ba tafita daga gidan sai cikin garinsu.
Lokacin data isa dare ya ɗan yafara.
Babu kowa a tsakar gidansu lokacin data shiga,dan haka kai tsaye ɗakinsu ta wuce,babu kowa a ciki da alama innayi tana ɗakin innarta.
Gadonta ta kaɗe hankali kwance ta kwanta.
Sai muce saida safe.....................



Da safe indo ce yauma takawo musu abinci kaman jiya,mamaki tayi ganin ƙofar wangale ko turata ba'ayi ba.
Har ta juya zata tafi sai kuma tagano kaman ƙafar goje yana kwance a tsakar ɗakin.
To shikuma yau kwayar kwanciyar ƙasa ta gara masa,hmmm ko ya murƙushe ƴar mutane har saida yagaji kai,maganinta ai ba ita marar kunya ba.
Ajiye kwanon tayi zata tafi,har ta bar ƙofar saikuma ta dawo tafara kiran Bombee.
Kira uku tayi mata amma shuru ba'a amsa mata ba.
Uhm barina duba koya jimaya rauni,ƴar mutane ta mutu mana mushiga uku.
Tura ƙofar ɗakin tayi ta leƙa kan gadon,amma babu kowa akai,sannan babu alamar an kwana ma akai,dan shinfiɗinsa yana nan rass.
Wajen banɗaki taje nan ma babu alamar mutum a ciki,hakanne yasa ta dawo ɗakin ta sauri domin ta tashi goje.
Shurarsa tayi taƙafarta amma shuru bai tashi ba,hasalima ko motsi bayayi,kuma numfashinsa ma baya fita kamar na mai bacci.
Jini ta gani yafito ya bushe a ƙasan gajeren wandonsa dayake mai haske ne.
Ihu ta kurma iya karfinta tana ƙiran inna daayi.
Jin ƙiran bana lafiya bane yasa ta taho da gudu zaninta ma a hanya ta karisa gyarashi,don ita duk a zatonta ma goje ne yayiwa Bombee aika aika,dan dama tun jiya sun saka tsammanin faruwar hakan.
Saidai tana zuwa wajen saita tarar sa'banin abinda take tsammani.
Indo ce akan goje har sannan tana jijjigashi amma yaƙi tashi,sai ihu take tana ƙiran sunansa.
Suna cikin hayaniya ne jauro yashigo wajenna su jin suna kiran sunan goje suna salati da kuma ihu.
"Yau nashigesu ni daayi,mlm zoka gani anya kuwa ba barayine suka shigo gidanann ba,shi yana kwance da alama dukansa akayi,itakuma Bombee batanan,kar ko ɗauketa sukayi kai?"
"Kinga bar wannan zaton,maza maza ɗakko mayafinki barina je wajen garba yazo da motarsa mukaishi cikin gari asibiti"
Cikin ƙanƙanin lokaci jauro yadawo suka ciccibeshi zuwa cikin motar sai asibiti.
Suna zuwa kuwa aka shiga dashi ɗakin gaggawa,zuwa lokacin ya farfaɗo,amma daƙyar yake motsi,kana ganinsa kasan yana cikin mawuyacin hali.

Tun takwas suka kawoshi asibitin,sai wajen goma kafin ya farka sosai,shima dan anyi masa alluraine dakuma bashi magunguna da karin ruwa.
Dan sanda jauro yaɗakko domin abin dole saidasu a ciki,saboda ana buƙatar sanin wanda yayi masa wannan lahani har cikin ɗaki.
Tareda ƴan sandan dakuma jauro aka shiga ɗakin asibitin inda goje yake kwance.
Dare ɗaya har ya rame ya fita a hayyacinsa,silin yake kalla yayi shuru,da alama yatafi kogin tunani,cinyoyinsa kuma an ɗaɗɗauresu da wasu karafuna a jikin gadon.
Dan sandanne ya kariso inda yake a hankali cikin jimamin halin dayake ciki.
"Sannnu fah ya jikin,dan Allah idan bazaka damu ba shin zaka iya faɗamana mai yafaru?"
"Bbboombiiii"
Dukkansu zaro ido sukayi,dansun fahimci inda zancennasu ya dosa,dan dama likitan yafadamusu farmakarsa akayi a gabansa da duka,wanda hakan ya jawo masa matsala,har sannan basu gama gano mai yake faruwa ba.
"Wacece Bombee kuma,ko wacce nasani ƴar gidan mlm Ahmadu??"
"Eh ita fah,kuma matarsa ce jiya shekaranjiya aka kaita ɗakinsa"
"Tohh abin daban mamaki,yanzu dai muje gidannsu muji mai ya faru,dan bazata wuce gidan ba,tunda mungane ba wasune suka farmakesu ba"
"Hoɗan wannan yarinya anya kuwa mutum ce?"
Jauro ya faɗa cikin mamaki.
"Aiko aljanace sai tasan tayi wannan aika aikar,kuma fah babu itace a ɗakin wanda ta dakeshi dashi"
"Hakane kam inna,ita sai anyi mata hukunci daidai laifinta,ni da kasheta ma sukayi"
Inna daayi ce ta kwabe mata bako ganin dan sandan yana wajen.
Shawarar ɗan sandan suka bi,ita inna daayi da indo suka zauna a wajensa,shikuma jauro da ɗan sandan suka nufi gidansu Bombee.
Tunda ta nuƙo hayar kyauyennasu tashigo gidansu ,data kwanta ba ita ta tashi ba sai ƙarfe goma.
Buɗe ɗakin tayi tafito daga tana mika tareda yin hamma,alamar mutum yayi bacci ya more.
Da inna laari suka haɗa ido tana bakin ƙofar ɗakinta.
"Innalillahi wa inna ilaihi ra ji'un mai zan gani haka ni laari,ko gizo ne take min kai"
"Mai ya faru yawuro kike wannan salatin,gamo kikayi da safiyah"
"Malm inaga gamo nayi,Bombee fah nake gani tafito daga ɗakinsu,anya kuwa kalau nake"
Daneji dake daki tana shiryawa Addarta Hadiza kayansu zasu tafi,batasan lokacin da ƙirjinta yai wani daramm ba,duk da hakan ba abune da zata gasgata ba,saidai kuma hmmm Bombee ce fah?
Maryam ce tashigo ɗakin bayan ta ajiye butar hannunta tareda cewa cikin hausarta mai haɗe da fillansi.
"Inna Daneji dagaske fah take Bombee ce a tsakar gida,kuma daga yanayinta kaman a gidanann ta kwana,dan fuskarta yayi kama da wacce ta tashi daga bacci"
Tun kafin Daneji tagama jin ƙarishen maganar ta daka tsalle sai gata a waje.
Haɗa ido sukayi da Bombee wacce tayi saurin dauke idonta tana kallon kasa.
Shurune ya ratsa wajen na ƴan wasu mintuna,kowa yarasama mai zaice mata.
Ɗaga idonta tayi a hankali tana ƙarewa mutanen dasuke wajen kallo,ƴan gidannasu ne dukka inka ɗauke innayi datake makaranta,sai kuma ƴan uwan Daneji dasuke shirin tafiya a lokacin. Daga gefe kuma Hajiya Dadda ce yayar babansu wacce take zaune a taraba,itama shirin tafiyar take a ɗakin inna laari,tajiyo wani sabon batu wai amarya a gidan ta kwana,sai yanxu suka ganta kwatsam da safe.
Mlm Ahmadu ne ya buɗe baki zayyi magana bayan yagama shurun takaicin.
Baikai ga cewa komai ba sukaji muryar Jauro a ƙofar gida,da kuma muryar wani mutum daban da basu wayeshi ba.
Fita yayi wajen gun sallamar,dan yasan bazai wuce ta dalilin Bombee ba.
Shigowa yayi dasu cikin gidan,dan inya tsayah yi musu magana ma bai san mai zaice musu ba,wataƙila ma sunfishi samun masaniyar abinda yake faruwa.
"To ga surukinki nan,saiki faɗamana meyasa kika dawo gida,kuma ma dan iskanci wai a gidana kika kwana ban sani ba,bayan na kaiki ɗakinki shekaranjiyah"
"Hmmm mlm Ahmadu kenan,ɗazu fah naji kururuwar iyalina,ina zuwa na tarar da goje a kwance kaman gawa. Nan muka ciccibeshi sai asibiti,da farko nayi tunanin wasune suka kawo masa farmaki.
Amma abin mamaki daya farfaɗo sai yake faɗamana wai matarsa ce tayi masa haka wannan aikin.
Zancen danake masa yanzu haka likita yabamu bayanin da ƙyar ya iya haihuwa,saboda dukan datayi masa a gabansa da daddaren"
"Meeee????"
Dukkansu suka haɗa baki suna kallon Bombee wacce ta cuno baki,lokaci ɗaya kuma tafashe da kuka kaman ba ita ba,ihu take jikinta har rawa yake,cikin marairaiciyar murya ta kalli babannata tareda cewa.
"Baaaba wlh kaman yanda nace muku na yarda ayi auren banyi niyyar yin komai ba. Ranar da aka kaini baidawo gidan ba,sai jiya da daddare yashigo min ɗaki yana maganganun maye na shaye shaye,bance masa komai ba yah wanka min mari,kaga ma wajen." Ta faɗa tana nuna marin dayake kwance a fuskarta.
"Daga nan kuma yafara tahowa inda nake ina matsawa har jikin bango,ni bansan mai zaimin ba sai yacire wandonsa yana dariyah.
Abin mamaki yabani ganin babba yacire wandonsa,kuma sai ya fara maganar data bani tsoro.
Wai abinda yakeyiwa mata a gari nima shizaimin wato fyaɗe,cikim tsoro saboda na kare kaina nakai masa duka a wajen,saboda a ganina hakan zaisa ya ƙaleni. Bansan zai faɗi ƙasa ba aradu......kkkuma tsoro naji danaga yanda yayi wa Atika akace ta suma ankaita asibiti,shiyasa na kaimasa naushi,daga haka ban kwaɗa masa komai ba,inaga bayan na tahone saboda kar ya tashi ya rama,wani kuma yaje ya dakeshin...."
Ƙarisa maganar tayi tana share hawayen dayake fitowa a idonta.
Duk wajen a yanda suka saurari zancennata sun tabbatar,batada ilimi akan abinda goje ke shirin yimata,sannann batayi tsammanin dukan datayimasa zai masa illah haka ba.
Inna laari ce takalleta tareda cewa.
"Kina nufin kice bakisan abinda goje zai miki,shin ina maganganun dana faɗamiki kafin akaiki gidannaki?"
"Iyeee nifah banji mai kuke cewa ba a ɗakin baba rannan,dan kafin mu shiga na toshe kunnena,saboda kar naji abinda kuke faɗa nayi kuka. Ji nayi ana cewa wai duk wanda yaji abinda ake fada masa kafin akaishi gidan miji to zayyi ta kuka,nikuma banason nayi kuka shiyasa na toshe kunnena"


Toh fah ga wata katobarar ta kawo kai,Bombee bataji hudubar da akayi mata ba🤣🤣🤣🤣.



_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼



____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]





*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________





Page 🖤26🖤




Dukkansu sakin ajiyar zuciya sukayi na takaicin sakarcin Bombee ɗin,saidai babu yadda zasuyi ba laifinta bane,tunda kowa yasan ita yarinya ce,sannan a yanda take da kasada,da kuma yanda goje ya farmaketa,koma waye iya abinda zayyi kenan.
Malm Ahmadu bashida zabi illah ya ɗora kusan dukkan laifin a kansa,tunda shine ya aurarta batareda tasan komai ba.
Shiryawa yayi shida su jauro suka nufi asibitin,domin ganin jikinsa tanan kuma zasu wuce police station akan case ɗin.
Bombee kuwa ganin kowa ya dauke kansa daga kanta bai sake cewa komai ba,yasa ta tabbatar labarin data basun ya samu karbuwa a xuƙatansu,dan haka itama sai tasaki ranta,tareda ɗiban abincin karyawa ta shiga ɗaki, dama yunwa ce ta tasheta daga baccin.
Bata ƙarisa gama cin abincin ba sakeenah tashigo cikin ɗakin ɗauke da sallama,amma mutuniyar ko amsawa batayi ba,duk da tasan sakeenan ce.
"Hmmm sallamar ma bazaki amsa ba Bombee,mai yayai zafi haka?"
"Wutah.....wuta ce tayi zafi,mai ya kawoki wajena da sanyin safiyar

Please Login or Register in order to submit comment